DR TAHEER CHAPTER 11 BY UMMU ASHRAF - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DR TAHEER CHAPTER 11 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 11 BY UMMU ASHRAF

- - Post a Comment

 DR TAHEER CHAPTER 11 BY UMMU ASHRAF          WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Tun tana kokawan kwace bakin nata har ta hakura ta dena...lokaci daya tayi luff tana karban saqon da yaketa faman aika Mata... har yanxu Kuma wahaye bai dena sintiri kan face dinta ba...zuwa yanxu tasan ko tacigaba da kokawa dashi din ma ba iya kwatan kan nata zatayi ba..don ji tayi gaba daya wani irin kasala ya rufeta...shiko Taheer tun yanayi don rarrashi sai abin ya fara fita out of his control...duk yanda yake kokarin dakatar da kanshi amma he couldn't...Saida yayi da gaske snn ya iya zare bakinshi a nata...sai Kuma ya sake rungumeta gagam idanunshi sun sake yin jaa..yanajin yanda heart dinshi ke sauya bugu kafin a hankali yace"baby am sorry..am so sorry for hurting you..but you have to believe me baby.. I love

you..only you baby..nasan bazan taba son wata mace a duniya bayan keba..so baki min adalciba if har kika tunanin son da nake maki bai taka Kara ya karya ba..wlh I love you..Ina sonki fiyeda yanda nake son kaina..so dn Allah kiyi hakuri ki dena hurting kanki...I love only you"...a hankali Layla dake rungume jikinshi ta lumshe idanu wasu hawayen farin ciki da kuma dadin kalamanshi suka wanke Mata fuska...lokaci daya ta nemi damuwan da take ciki tarasa..wato Allah yayima daddy baiwan iya tsara kalamai..duk yanda takai ga fushi dashi minti 2 yayi yawa indai zata tsaye ta saurareshi sai yayi winning dinta...ta sake tura kanta a chest dinshi tana smiling kmr ba gobe...shi Kuma Taheer ya dago face din nata yana kallon yanda take sinne kai..sai ya saki murmushi tareda ja dogon hancinta yace"my stubborn baby..kin cika rigima wlh"...Layla ta sake hugging dinshi tana cigaba da murmushinta tace"nidai daddy ko taci gaba da nemaka banaso kana kulata plss..I know she loves you..bazata taba dena sonka ba ni Kuma am scared..I don't want to loose you to anyone..I love you so much"...a hankali Taheer ya sake maida hannayenshi ya rungumeta a jikin nashi tight..ya lumshe ido yanajin yanda tsantasar farin ciki ke sake lullubeshi..wato ba karamin dadi bane kaso mutum kuma shima ya soka back..ba yau ta fara furta tana sonshi ba amma na yau din sai yajishi different..na yau din sai yajishi very unique and special...yasan har ya mutu wnn moment bazai tana gogewa daga memory dinshi ba..it's among abubuwanda bazai taba mancewa dasu ba saidai a kaisu kabari tare...a hankali ya matso da bakinshi saitin kunnenta kafin yace"babyna na gode..thank you so much for loving..I love you too..and plss ki dena ma tunanin zanso wata macen apart from you..bama Sameera ba ko wacece zata soni baby saidai tayi hakuri wlh..bazan taba iya hadaki da kowa ba..Ina sonki sosae"...a hankali Layla dakejin tamkar an tsundumata a aljanna don dadi ta shiga mikewa daga jikinshi..har yanxu bata dena murmushi ba...ganin tana kokarin kwanciya Taheer ya riketa yana kallon cikin idanunta yace"what?.."Saida ta dan lanagabar da kanta snn tace"I want to sleep"...ba musu Taheer ya kwantar da ita a kan gadon..sai Kuma ya sunkuya forehead dinta ya sakar mata kiss a wurin..ya sake sunkuyawa yayi ma cikinta ma kiss din kafin ya kamo hanunta a rikeshi gam cikin nashi..murya can kasa yace"kiyi baccinki babyna..am going to watch you sleep"... murmushi Layla ta sakar mishi sai Kuma ta maida idanunta ta lumshe don da gaske baccin taji tanaji...bata dade ba kuwa baccin yayi awon gaba da ita...Taheer kuwa na zaune yana kallonta tana baccin kmr yanda ya fada...bashi ya tashi a wurin ba Saida aka fara Kiran sallahn magrib...+


A bathroom dake nn parlon yayi alwala snn ya tafi masjid...ana idarwa ya dawo amma har lokacin bata tashi ba..yanaso ya tasheta tayi sallah amma baison ya katse Mata baccin tunda yasan ba wani baccin kirki take samun yi da daddare ba...haka yacigaba da zama yanata aikin kallonta kmr bai taba ganinta ba...bata farka ba Saida ya dawo daga masallaci sallahn Isha...ta mike tana yatsine fuska kmr zata mai kuka...shi Kuma ya janyota jikinshi yana kallonta yace"menene?.."Saida ta kwabe fuskanta kmr zatasa kuka snn tace"yunwa"...Taheer yayi dariya kawai gamida girgiza kanshi...yanda tayi da fuskan nata sai kace toy sai ya bashi dariya...Saida ya tsagaita da dariyan snn yace"to me zakici?.."ta danyi shiru tana tunani kafin tace"danwake"...ya wara idanu sosae yana kallonta still smiling yace"yau baby ce zataci danwake.. unbelievable"...Yana gama mgn sai ya mike yana kokarin fita daga dakin kmr zatasa kuka tace"daddy ni zan bika"...baiyi Mata musu ba ya dawo tareda kama hanunta cikin nashi snn suka fita daga dakin tare...shi ya fadama su ummi wai tanason danwake..aiko ummi da kanta ta shiga kitchen zatayi mata..shi Kuma ya rakata toilet tayi alwala snn tazo ta fara sallah...bata jima da idar da sallahn ba ummi ta kammala danwaken snn ta kawo Mata..nan tasashi a gaba ta faraci kmr bata taba cin abinci ba...shiko Taheer zama yayi a gefenta yana kallon ikon Allah...a iya saninshi da ita yasan batacin danwake..ko ganinshi ma bata sonshi amma yau danwaken takema wnn cin kmr ba itane ta tsaneshi ba..lallai ciki ba abinda baya haifarwa..

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sati 4...

Layla na kwance dakin ummi tana bacci ita kadai...tun yamma take wnn baccin har zuwa yanxu karfe 8:30 na dare...Ummi da Umma suna parlor...shi Kuma Taheer sai 9 zai baro clinic tunda evening yake...Ummi ta mike tana fadin"bari in dubo yarinyar nn Aisha..najita shiru tun dazu"...umma tace"gsky dai..nima banji motsinta ba"...ummi na shiga dakin ta sameta zaune a tsakiyar gadon sai hada zufa takeyi...takarasa kusa da ita da sauri tana fadin"ke lafiyanki kuwa..meya faru"...da kyar Layla ta iya bude baki tace"ummi bayana ciwo..kmr zai balle wlh"...a rikice ummi ta shiga neman wayanta tana cewa"bari in Kira Taheer infada mishi..da kyar idan ba haihuwa bace"...da sauri Layla tace"ummi ba sai kin kirashi ba ai ya kusa dawowa..yanxu alwala nakeso inyi zanyi sallah"...ba musu ummi ta ajiye wayanta dake hanunta snn ta kamo Layla ta riketa..Saida ta rakata har bathroom snn ta fito...ita Kuma a daddafe tayi alwalan ta fito...ummi ta sake kamata suka koma dakin..ta shimfida Mata sallaya ta bata hijab snn ta tayar da sallah..ita Kuma ummi ta fita parlor ta fadama umma wai Layla na ciwon baya...tare suka dawo dakin suka zauna har Saida ta idar da sallahr..tana idarwa ummi ta sake komawa inda take tana tambayanta ya bayan...tace yayi sauki snn ta yunkura tareda mikewa daga wurin da tayi sallahn..ummi ta taimaka mata ta sake komawa ta kwanta..sudai duk sukai zuru suna kallonta...ita kuwa tana kwanciya ta lumshe idanunta...tanajin yanda ciwon bayan nata ke tsananta..tun tana dauriya har bata san time din da ta fara juye juye a kan gadon ba... ummi tayi kanta da sauri ita Kuma umma ta fida daga dakin don dauko wayanta ta Kira Taheer..


Yana kan hanyanshi na dawowa gidan wayanshi ya fara ringing..bai bata lokaci ba ya samu wuri yayi parking snn yayi picking call din...umma tayi kokarin daidaita muryanta tace dashi"Taheer kana Ina?.."cikin wani irin tsoro da fargaba da Kuma faduwar gaba da suka diran mai lokaci daya yace Mata"am on my way umma..meke faruwa?.."umma tace"it's nothing..dama inaso inji ko ka taho ne..sai kayi sauri ka karaso"...a rikice Taheer yace"umma please..meyake faruwa Mana..tell me is baby alright"..."she's alright Mana..na fada maka I just wanted to see you..ka nutsu kayi driving dinka a nutse Taheer..babu abinda ya sameta"..umma na gama fadan haka tayi hanging call din...shiko Taheer sake tashin motar yayi da sauri yaci gaba da tafiya...Allah ya sani dama tun dazu jikinshi ke bashi kmr baby ba lfy..shiyasa ma ya baro clinic din da wuri... yanxu kuma Kiran umma ya sake tabbatar mishi da cewa akwai matsala..."Ya Allah make it easy for her plss..Allah ka bata da sauki..Allah karka wahalan min da ita na rokeka... innalillahi wainna ilaihi rajiun..my baby am coming for you"... abubuwanda yaketa maimatawa knn while Yana driving a guje...gaba daya yayi loosing nutsuwan nashi..dama yasan duk baby tazo haihuwa Allah kadai yasan yanayin da zai shiga..shi din da ko menstrual pain take sai yaji gaba daya duniyar ta mai zafi inaga ciwon haihuwa Kuma..he's a doctor and he knows exactly how women are suffering duk suka zo haihuwa..ciwo ne wanda duk yanda zaa Kai ga yi maka bayani bazaka taba fahimta ba sai yazo kanka..ciwo ne Wanda bashi da wani magani da zai rage maka ciwon indai ba haihuwa kayi ba...gaba daya tunanin nn ya sake dagula mishi lissafi...da yana cemata da cikin ya shiga 9 months zai mata cs ya dauko abunshi but he never meant it..he was only kidding..Yana fada Mata haka ne don kar hankalinta ya tashi..yanxu kuwa dukda bai je yaga condition din da take ciki ba sai yaji kawai cs din zaiyi Mata ta huta..he can't watch her suffer like this...da wnn tunanin ya karasa gida...Yana shiga ciki ko parking din kirki baiyi ba ya bude motan ya fita da sauri har yana hadawa da gudu...Yana shiga parlor ya fara jiyo nishinta daga daki...ai baisan time din da ya kara gudun tafiyan nashi ziwa dakin ba...Yana bude kofa ya ganta kwance jikin ummi...numfashi ma da kyar takeyinshi...sai jujjuya Kanta take from one side to another.. idonta ko digon kwalla babu...wato idan azaba yayi azaba ko daman kuka mutum bazai samu ba...idan kaga mutum na kuka kan ciwo to lallai ciwon baikai a kirashi da ciwo ba...gashi dai duk raki da langwai irin na Layla yau ko energy din yin kukan bata dashi...kawai sai ganin Taheer sukayi from no where yana kokarin dago Layla daga jikin ummi...muryanshi a matukar raunane..jikinshi har shivering yakeyi tsabar rudewa..Yana girgiza kanshi Yana cewa"baby am sorry..am sorry you have to go through all these pain because of me..am so sorry plssss"...ya karasa mgnr tareda hade hannayenshi da nata..at this point Yama manta da batun wani asibiti balle Kuma yayi tunanin he's a doctor...ummi ce tace"asibiti ya kamata mu tafi Taheer..a wnn yanayin da kake nasan ba iya dubata zakayi ba..tashi mu tafi"...ummi na rufe bakinta ya mike zumbur shi sai yanxu ma ya tuna da asibitin ya kamata su tafi...yasa hannu ya kinkimi Layla da har yanxu bata bar girgiza kai tana cije baki sbd azaban da takeji ba...tare suka fita daga dakin...umma ce tayi saurin dauko car key snn suka fita waje...ita ta bude motan..Taheer dake daukeda Layla a jikinshi ya shiga back seat...umma ta shiga driver seat tunda ita zatayi driving din..ita Kuma ummi tana zaune a gefenta...gaba dayansu ba Wanda bai shiga tashin hankali ba...lokaci lokaci suna juyawa su kalli Layla dake jin jiki sosae ko Kuma ta mirror...

Mintina 20 ne suka kaisu clinic dinshi...da kanshi ya fito ya sake daukanta..ko su umman bai jira su fito ba yayi cikin asibitin da ita...staff dinshi sai kallonshi suke suna mamakin wnn rudewa da yayi..wasu Kuma basu mamaki as sun ringa sun wacece baby a wurinshi..sun Kuma San irin kaunar da yakeyi mata tun ba yanxu ba...Yana karasa shiga ciki wasu nurses suka shiga kokarin amsanta a hannunshi amma yaki bada ita...Kai tsaye ya nufi maternity da ita...sai da ya shiga har cikin labour room snn ya kwantar da ita kan bed shima ya zauna kusa da ita...ya dubi nurse din da ta shigo yanxu yace mata"is doctor Fatima around?.."da sauri nurse din tace"yanxun nn ta tafi sir..saidai doc Afiya itace zatayi night"...tana rufe baki yace"go go go..jeki karamin ita yanxun nn plss"...da sauri nurse din ta fita zuwa office na doc Afiya...bata jima da fitaba suka dawo cikin labour room din tare...su Kuma su ummi suna waiting area duk hankalinsu a tashe...doc Afiya na shiga cikin labour room din tace"yau Dr.Taheer da kanshi a labour room"...tana rufe baki yace"zo ki dubamin ita plss..yi mata VE muga ko haihuwan ne"...ba musu doc Afiya ta dauko hand glove dake cikin wani drawer tasa a hannayenta..tana gamawa ta matso inda Layla ke kwance tana murkususu don ciwon kara gaba yakeyi ba bayaba...Saida ta fara dage dogon rigan dake jikinta zuwa cikinta snn ta sunkuya zata zira hannun nata ciki...Taheer dake kallonta ya runtse idonshi da sauri.. bai son gani kwata kwata..dukda shi ba mace bane amma yasan yanda mata kejin zafin VE din n da akeyi musu..Yana ganin yanda suke yatsina wasu har ihu ma sukeyi idan zaayi musu...so sai ya lumshe idonshi don baison gani..ba don dole ba da babu Wanda ya isa yasa mishi hannu a gaban matarshi wlh...dukda doc Afiya mace ce ba karamin kishinta yaji ba...yasan idan yace zaiyi da kanshi ma ba iyawa zaiyi ba...gaba daya yayi loosing nutsuwarshi and ba patient din da zai iya dubawa right now bare kuma ace baby da kanta...bai bude idanun nashi ba sai da yaji doc Afiya na fadin"she's 2 CM doctor"...a rikice Taheer ya bude idanun nashi tareda zuba Mata su...2 CM fa ko labour ma bai kankama ba... innalillahi yanxu a 2 CM take Shan wnn wahalan...gashi yasan cervix dinta dole zaiyi taking time before fully dialation tunda she's primip...Ya Ilahi ya zanyi..kodai inducing dinta zasuyi ne...sai Kuma ya Kau da tunanin da sauri...sai zufa ke keto mishi sai kace shine ke labour din...doc Afiya ta shiga kwantar mai da hankali tareda alkawarin she will help..zatayi iya bakin kokarinta wajen ganin Layla ta sauka lfy...dukda haka shidai gashi nn ne kawai..bashida burin da ya wuce a haihu da wuri don baiso ta galabaita...yace ma doc Afiya ta kula mai da ita zaije yama su ummi bayani ya dawo...

Yana fitowa su ummi da sukai cirko cirko a waiting area ko zama sun kasayi suka nufoshi da sauri...nan yayi musu bayanin komai tareda fadin haihuwan nata zai Dan sauki lokaci amma ba wani matsala bane InshaAllah...yace zai kaisu office dinshi su zauna Amma Sam sukaki yadda..dole haka ya sake komawa cikin labour room din ya barsu a wurin...yana komawa ciki ya samu har yanxu tanata fama...ya rike hannunta gam cikin nashi hawaye na wanke mishi fuska yake fadin"baby am sorry kinji..am right here with you InshaAllah ba abinda zai sameki..zaki haihu lfy Bi'iznillah"...Layla da zufa ke zubo mata da kyar ta iya bude baki tace"daddy..dadddy zan mutu..mutuwa zanyi daddy...the pain is unbearable..I can't bear this pain daddy mutuwa zanyi"...da sauri Taheer ya toshe mata baki yana girgiza kanshi yace"InshaAllah bazaki mutu ba baby..I don't want to loose anyone of you..I want to live with both of you so ki dena cewa zaki mutu InshaAllah ba inda zakije ki barni..I love so much..bazan iya rayuwa babu ke ba"...da kyar ta sake"nima I love you sosae daddy...I love like crazy but dd"...tun kafin ta karasa Taheer ya sake rufe Mata bakin...ya goge hawayen dake zubo mishi yana cewa" na fada maki ba inda zakije ki barni..stop saying Zaki mutu indai ba so kike ni in rigaki mutuwa ba..am right here with you and I know we can make it together..I love the both of you"..daga nn Layla bata sake cewa komai ba..sai nishi da taketa faman yi tana hada gumi...doc Afiya kuma nata kokarin assisting dinta..tana bata duk wani taimako daya kamaceta.A takaice dai Saida Layla ta kwashi tsawon awanni tana labour amma haihuwa yaqi zuwa...zuwa yanxu karfinta ya gama karewa kaff don tun tana samu tana pushing har ta kasa yi Kuma...Taheer da har yanxu ke tareda ita duk yayi zuru zuru shima sai kace shi yake nakudan...doc Afiya har yanxu na tareda ita...su ummi ma suna waje tun suna sa rai zaa fito ace musu ta haihu har suka fara tunanin Allah yasa lfy...Saida Taheer ya fito da kyar ya samu ya lallabasu ya kaisu office dinshi don dare yayi sosae...har zuwa yanxu Kuma ko Nafeesa basu Kira sun fada Mata ba...ummi tace gara idan an sauka lfy sai a Kira duk Wanda ya kamata...shi Kuma Taheer bayan ya gama dasu ya sake komawa labour room...aikam kmr jira ake ya  shigo ciwo ya sake dawowa gadan gadan...ya kama hannunta ya rikeshi cikin nashi...doc Afiya Kuma ta shiga kokarin taimaka mata...a takaice dai sai asuba snn suka samu Kai ya fito..shima Saida doc Afiya ta Mata episiotomy('Kari)snn aka samu ya fito...Layla ta saki wani wawan ajiyan zuciya don relieve sosae taji ta samu just by fitowan kan...doc Afiya ta taimaka tareda karasa ciro babyn...Saida ta yanke cord snn ta nade babyn a zani ta mikawa nurse dake tareda su...tayi withdrawing oxytocin tayi mata snn ta fara yi dinke mata wurin data Kara din..sai yanxu Layla ta samu bakin kuka..ta ringa kwalla musu ihu kmr ba itane take cewa zata mutu ba jiya..shiko Taheer idanunshi na rufe ruf don ba son ganin dinkin yakeba..yana kuma rikeda hanunta har yanxu..har aka gama dinkin nn Layla bata dena kuka tana kurma masu uban ihu ba...daga nn Saida ta tabbata ta fitar Mata da jinim da yayi saura a jikinta snn tayi Mata parking tareda hada mata ruwa ta shiga wanka...ita Kuma ta shiga gyara wurin...Taheer kam tunda yaga an fito da baby lfy ya lumshe ido yana maimaita"Alhamdulillah"cikin zuciyarshi...yana rikeda Layla dukda yanda yakejin zuciyarshi na fisgarshi kan yaje yaga babynshi amma baije inda takeba Saida ta shiga wanka...ya karasa inda nurse din dake rikeda babyn nashi take...ya Mika hannunshi kawai tareda amsan babyn da har an gama shiryawa an Sanya mai Kaya...ya lumshe ido tareda hugging babyn a kirjinshi...cikin ranshi yanayin duk addu'a dayazo bakinshi...yanajin yanda son babyn ke ratsa ko wace kafa ta jikinshi...wato haka iyaye keji a kan 'ya'yansu...ya dago face din babyn yayi addu'a tareda tofa mai snn ya dubi nurse daketa kallonshi tana smiling yace Mata"me aka Haifa"...tana fara'a tace dashi"it's a girl"...Taheer ya sake lumshe ido yana Kara godia ga Allah daya cika mashi burinshi...ya bashi 'ya macen da yake matukar so...a hankali ya sake maida idonshi kan babyn sai ya kasa gane dawa take kama...tanadai da haske sosae Wanda ko baa fada mai ba yasan wnn hasken Layla ne tunda tafishi fari nesa ba kusa ba...a hankali yayi kissing goshinta murya can kasa yace"I love you"...

Inshort dai Saida Taheer ya bata lokaci sosae yana kallon babaynshi yana Kuma surutu shi kadai snn ya tuna dasu ummi...ya mikama nurse babyn da sauri snn ya fita zuwa office dinshi...su ummi na ganin ya shigo suka shiga tambaya ko ta haihu...Saida ya sakar musu kayataccen murmushi kafin yace"ta sauka lfy Ummus..an samu baby girl"...lokaci daya suka shiga fadin"Alhamdulillah"a tare kowacce face dinta daukeda tsantsar murna..shi sai ya kasa gane ma Wanda yafi wani murna a cikinsu..

+

Bayan doc Afiya ta taimaka Mata tayi wanka ta gyara jikinta tsaf snn ta kaita zuwa post natal..nurse ta biyota da babynta...suna shiga ta hau gado ta kwanta ko babyn nata bata tambaya ba bacci me nauyi yayi gaba da ita...nurse na kokarin kwantar da babyn daketa tsala kuka a cradle dake cikin dakin suka shigo gaba dayansu kowa daukeda farij ciki...dama suna zuwa labour room da sukaga basu nn Taheer yace suzo post natal yasan dole can zaa kaita...tsakanin ummi da Umma har rige rigen daukan baby sukeyi...karshe dai ummi ta dauka tana fadin"ai nice babba sbd haka ni zan fara ganinta"...tana gama fadin haka tasa hannu tareda yin Bismillah ta amsa babyn da har yanxu bata bar kuka ba...ta kua mata ido tana kallo sai taga tamkar Taheer dinta lokacinda aka haifeshi...face dinta irin na Taheer ne sak sai fari Kuma data dauko na Layla...a hankali ummi tayi addu'a tareda tofa Mata a fuska...ta mikama umma tana fadin"Allah ya rayaki ya maki Albarka..Allah Kuma yasa ba halin kukan Layla Zaki dauko ba..don naga tunda Muka shigo dakin nn bakinki baiyi shiru ba"...umma na dariya itama ta karbi babyn...kallon nata itama takeyi tana kuma ganin kamrta da Taheer din kmr yanda ummi ma ta gani...tayi Mata addu'a itama ta shafa mata tana cewa"Allah ya maki Albarka..Allah ya raya mana"...da sauri Taheer dake kallonsu with so much love yace Ameen...doc Afiya tayi sallama dasu zata tafi Taheer yasa hannu cikin aljihunshi ya debo kudin da shi kanshi baisan adadinsu ba..ya Mika Mata su fuska daukeda murmushi yace"accept this little gift of mine plss..na gode sosae da taimako na da kikayi Allah ya saka da alkhairi"..doc Afiya na murmushi ta amsa kudin tareda yin godia snn suka fita daga dakin..ya rage daga ummi.. umma..sai Taheer da Kuma Layla dake bacci...Taheer ya matso jikin umma a hankali tareda rungumeta yana cewa"Umma am a father now..she's my daughter umma I can't believe this..Allah na gode maka ya Allah..Allah Alhamdulillah"...da sauri ummi tazo inda suke tareda amsan babyn dake hannun umma tace"kaidai zanga randa zaka nutsu wlh..dubi yanda kazo ka wani rungumeta ga yarinya Kuma a hanunta ko so kake ka yar daita Oho"...sudai basu tanka Mata ba..shikam Taheer cikin ranshi yace"ai yanda nakejin son yarinyar nn ummi ko kuda bazan iya bari ya sauka jikinta ba balle Kuma ni in yar daita kasa da kaina"...ita kuwa umma shafa bayanshi ta shigayi tana tayashi farin ciki...ita kuwa ummi kan daya daga cikin plastic chairs dake dakin ta zauna ta Dora yarinyan kan laps dinta snn ta dauko wayanta ta shiga neman layin Nafee.. ringing din farko Nafeesa ta daga kmr dama jiran Kiran take...hankali a tashe tace"Ummi haihuwan yazo koh"...Saida ummi ta saki dariya kafin tace"ai an rigama an sauka Nafee..kin ganni rikeda babyn a hannuna"...Nafeesa ta saki wani Hamdala..muryanta cikeda murna tace"dn Allah da gaske ummi..yaushe ta haihu..meta haifa...ya akai baku kirani ba ummi"...ummi na cigaba da dariya tace"duk wnn tambayoyin haka Nafee da wanne zan fara...tun daren jiya ake abu guda wlh amma sai asubahin nn ta haihu..an samu mace"...Nafee tace"MashaAllah ummi..Allah yaraya yayi Albarka..Ina Laylan take"...Saida ummi ta dubi inda Laylan ke bacci kasadan snn tace"she's sleeping..tunda ta haihun ma inaga ko babyn bata ganiba.. amma dai lfynta Lou"... Nafee ta sake cewa"To Alhamdulillah tunda she's fine..Allah ya Kara Mata lfy ya raya mana baby..Nima Ina nn zuwa ummi ko yau na samu available flight zan taho InshaAllah"...ummi tace"to shknn Allah ya kaimu"...daga nn sukayi sallama...ummi ta maida dubanta ga Umma da Taheer da har yanxu bai bar jikinta ba.. bai Kuma dena sambatun da yake ba..kawai he's happy yau shine da 'ya ta kanshi..jininshi...ba abinda zaiyima Allah daya wuce godia..he's forever grateful...

STORY CONTINUES BELOW

3 Hours Later...

Saida Layla ta samu baccin good 3 hours snn ta tashi...a lokacin Ummi ce kadai a dakin..umma da Taheer sunje gida don su taho musu da abubuwan da suke bukata...Saida ummi tayi mai Jan ido ma snn ya tafi..don da farko cewa yayi bazai iya tafiya ya bar matarshi da 'yarshi ba...


Da sauri ummi ta karasa kusa daita tareda taimaka Mata ta zauna sosae...tana kallonta tace"sannu kinji..bari a hada maki tea Kisha sai kiji da yarinyar nn..tun dazu take rabka mana uban kuka a dakin nn da kyar idan ba kukanki ta gada ba"...itadai Layla batace komai ba sai hawaye dake sintiri kan face dinta...ummi ta juya da sauri jin kmr tana shehshekar kuka tace"La'ilaha illallahu..ke meya faru kike kuka kuma...kodai wani waje na maki ciwo?.."a hankali Layla ta shiga girgiza Kai alaman ba inda ke mata ciwo...ummi ta danyi kasa da murya tace"to kiyi hakuri idan sbd nace tayi gadon kukanki ne..wasa nake maki wlh...in kukane ma ai Taheer yafiki..lokacinda yana karami yini yake yana kuka in fada maki ko gajiya ma bayayi..kuma gashi da murya don duk ya fara kukan nn ko Kiran sallah banaji"...itadai Layla batai mgn ba kuma hawaye bai dena zubiwa kan fuskanta ba...a rikice ummi tace"yau na shiga uku to meyake damunki Kuma..meya faru dn Allah ki sanar dani..keda kika haihu maimakon ki godema Allah sai ki farka da kuka Kuma..haba Layla idan kikayi haka kin godewa Allah knn"...har yanxu dai Layla shiru ba mgn...ummi tayi shiru kawai ta zuba mata ido don bata san me zatace ba Kuma..ita tsoronta kar wani abun ne ya faru ne da ita...daidai lokacin umma da Taheer suka shigo dakin a tare...da sauri Taheer ya karasa gareta ganin yanda hawaye ke ambaliya a face dinta...ya kamo ha nunta ya rike sosae idanunshi har sun canza launi yace mata"baby lfy..meya sameki..meyasa kike kuka..akwai inda ke maki ciwo ne"...shima batace mishi komai ba sai ma zame hannunta da tayi cikin nashi tareda juya mai baya ta kwanta...umma itama tayi tsaye tana kallon ikon Allah...sai Kuma taja tsaki tareda ficewa daga dakin...itama ummi mikewa tayi ta shiga bathroom don dama su take jira su taho Mata da kayanta sai tayi wanka...ummi na shiga bathroom din Taheer ya sake kamo hannunta ya rike cikin nashi..Yana murza hanun a hankali yace"baby am sorry plss..kiyi hakuri ki dena kukan nn dn Allah..idan ma wani abu nayi maki just tell me ni Kuma zan baki hakuri..I don't want you to suffer by crying like this plss..am sorry"...a hankali ta mike zaune sai kawai ji yayi ta fada jikinshi gaba daya...ta rungumeshi gam tana girgiza kanta tace"daddy saura kadan in mutu wlh..ban taba tunanin zanci gaba da rayuwa ba..tun da nake ban tabajin ciwo irin Wanda naji jiyaba daddy nidai bazan kara haihuwa ba dn Allah"...a hankali Taheer yasa hannayenshi tareda sake rungumeta ga jikinshi...yana kokarin danne dariyan dake son kufce mai ya shiga bubbuga bayanta yana cewa"I agree with you my baby..nima bazan yadda ki kara haihuwaba sbd wahalan da kikasha..so ki dena wnn kukan kinji..ko babyn namu ma bakice a baki ki ganiba"...lokaci daya ta dago taga jikinshi tana goge hawayenta...sai Kuma idonta ya sauka kan cradle da babyn ke kwance a ciki...a hankali Taheer ya mike zuwa inda babyn take..ya daukota snn ya dawo inda take..Saida ya zauna ya dora babyn kan cinyanshi snn ya janyota ta dora kanta kan shoulder dinshi...ta kurama babyn ido tana kallo lokaci daya kuma tanajin wani irin feeling da bata tabajin irinshi ba na shiganta...bata san lokacinda ta Kai hannu tareda amsan yarinyan daga hanunshi ba...tacigaba da kallonta kmr ta samu mirror..sai Kuma ta lumshe ido tareda sunkuyawa tayi ma babyn kiss a goshinta..lokaci daya yarinyan tayi motsi hadda dan yatsine fuska..Layla ta saki dariyan da bata shiryaba ganin yanda tayi da face dinta..sai ta koma Mata kmr Taheer din itama..shima haka yakeyi da face dinshi...Taheer dake kallonsu full of love and happiness yace"baby ya kikaga babyn tamu"...a hankali ta kalleshi still tana murmushi tace"she's cute"...shi Kuma ya matso tareda sa hannu ya zagayesu daga ita har babyn gaba daya...murya can kasa ya sake cewa"did you like her"...da sauri ta daga mishi kai snn tace"I love her"...Taheer ya manna Mata kiss a goshi snn yayima babyn ma haka yace"nima I love you both..you are my everything"..sai ya sakesu tareda amsan babyn ya maidata inda take..ya nufi inda kayan tea suke yana cewa"Bari in hada maki tea Kisha..idan kin gama itama sai ki bata nata tea din tasha tun dazu take nemanshi"...itadai Layla batayi mgn ba as har yanxu jikinta ba wani kwari sosae gareshi ba...nan da nan ya hado tea din mai kauri sosae ya kawo Mata..ba musu ta amsa ta fara sha don dama yunwa takeji...ya sake zaunawa kusa daita yana kallonta smilingly yace"baby thank you so much..na gode sosae da wnn cute baby da kika haifomin..I love you alot..ki fadi duk abinda kikeso ni Kuma I promise zan yi maki..zan iya maki komai baby don ban isa in biyaki wnn kyautan da kikaimin ba.. thank you so much..muaaahh"..ya karasa mgnr tareda kissing din hanunta...a hankali Layla tace"nidai kawai so nake ka yadda bazan kara haihuwa ba daddy..mutuwa zanyi Allah"...tana rufe baki yace"an gama baby..yanda kikeso haka zaayi"...daidai nn Kuma ummi ta fito daga bathroom...Kai tsaye Inda babyn ke kwance ta nufa tareda daukota..ta dorata cinyan Layla tana cewa"yi maza ki bata nono tasha dn Allah"...a hankali Layla tasa hannunta ta riko babyn...Saida ummi ta daidaita mata yanda zata rike babyn snn ta ciro nonon da kanta tasama babyn a baki aikam ta kamashi da kyau kmr abinda take jira knn...wani uban qara da Layla ta fasa Saida ummi ta toshe kunnenta da duk hannayenta...hawaye na sauka kan face dinta take cewa"wayyo Allah na ummi zafi wlh..cizona takeyi fa"...da sauri Taheer ya amsa babyn da saura kadan Layla ta yar da ita a kasa itama kuwa ta fashe da kuka...ya rungumeta a chest dinshi yana jijjigata amma kukan bai tsayaba...ummi tace"yanxu Layla wane irin iskanci ne wnn zaki kurma Mana ihu haka sai kace mahaukaciya...idan baki bata nonon ba ya kikeso muyi da ita"...Layla na girgiza kai tace"Allah ummi inaga cizona takeyi..bakiji zafin da najiba"...tsaki ummi taja tareda ficewa daga dakin...a hankali Taheer ya matso inda take...ya dora Mata babyn a cinyanta snn a nutse ya fara cewa"baby dn Allah kiyi hakuri ki bata ko kadan ne kinji...kinga yunwa takeji tunda aka haifeta bataci komai ba sai zamzam kadai...dn Allah ki daure ki bata idan kika saba Zaki denajin zafin"...wahaye na sake wanke Mata fuska tasa hannu ta dago babyn sosae...tana kallonshi tace"ni tsoro nakeji daddy"...da kanshi ya zaro nonon tareda daidatashi da bakin babyn...tana sake kamawa Layla ta Kara sakin ihu wnn karon dai bata cire bakinba...Taheer na zaune yana taimaka Mata don ko rike babyn bata iya sosae ba...Saida ya tabbatar ta Dan samu tasha dukda ruwan nonon baizo sosae ba snn ya kyaleta...

Yinin ranar mutane sukaita zuwa dubiya sosae don baa sallamesu ba...Taheer da kanshi yace su bari zuwa gobe idan yaga yanayin jikinta dana babyn ba matsala sai su tafi...haka  akaita fama da Layla  wajen bama baby nono..duk ta kama nonon sai tasa kuka wai ita zafi takeji...Saida umma ta kusan dukanta snn aka samu tayi shiru...

Abbansu ya Kira ta wayan ummi yayi barka snn ya hadata dasu Al'ameen suma sun dade suna hira hadda kira video call aka nuna musu babyn suka gani...Taheer kam bayan anyima baby wanka an shiryata tsaf cikin kayanta yayita snapping dinta pictures kala kala hadda su video sai kace mace...haka yabi almost duk contacts dinshi yayi musu sending yana cewa Allah ya albarkaceshi da samun diya mace...Friedns dinshi da yawa sunzo sunga baby a ranan cikinsu hadda Yusuf... Alhamdulillah Kuma daga baby har mamanta suna cikin koshin lfy..

Washegari da safe aka sallamesu bayan an tabbatar da baby da mamanta suna cikin koshin lfy...Taheer ya kwashesu sukayi gida...suna zuwa ummi tasa mama hauwa ta dora ruwan zafi wai zasuyi wankan jego...ita Kuma umma ta karba babyn itama ta fara yi Mata wanka...+


Ruwa na tafasa ummi ta hada ruwan wanka ta kaishi bathroom din dakinta...Layla da ido ya raina fata taji kmr ta kurma ihu don ba son wankan nn take ba...haka ummi tasata agaba suka shiga bayi...ana fara zuba ruwan a jikinta ta saki wani razanannen ihu da har Taheer dake part dinshi sai da ya jiyo ihun...ya fito daga wanka da sauri ko gama wankan baiyi ba ya dauraye jikinshi ya fito daure da towel..jallabiya kadai ya iya zurawa snn ya fita daga part din nashi da sauri...yana shiga nasu part din yaci karo da Mama hauwa a parlor...da sauri yace Mata"lfy mama hauwa nakejin kukan baby..tana Ina?.."Saida hauwa tayi dariya snn tace"ba wani wlh..wanka ne kawai ake Mata shine take wnn kukan"...Taheer ya zare idanu kafin yace"wane irin wanka Kuma mama hauwa"...a takaice tace mishi"wankan jego"...bai sake tsayawa yin mgn da itaba ya nufi dakin ummi inda nan ne yakejiyo sautin kukan nata...umma na zaune dakin tanayima baby wanka...Taheer ko bi ta kansu baiyi ba kawai ya karasa tareda tura kofan bayin...Saida ya shiga ciki sosae snn kmr zaiyi kuka yace"ummi dn Allah kiyi hakuri a bar wankan nn haka tunda bataso plss...tun daga part dina fa na jiyo kukanta"...a fusace ummi ta dago hannunta rikeda towel da takema Layla wanka dashi tace"fita daga bayin nn tun kafin inci ubanka wlh..wane irin iskanci ne wnn inama yarinya wanka kawai zaka fado mana cikin bayi..wane irin rashin kunya ne wnn"...Taheer ya sake rausaya kanshi yana kallon Layla dake sheshshekan kuka a hankali yace"ummi dan girman Allah kiyi hakuri ki bar wankan nn haka..kinga fa dinki ne a jikinta and wnn ihun da takeyi yana iya sawa dinkin ya warware Kuma baa son haka..nidai dn Allah kiyi hakuri ki kyaleta ko wani maganin ne sai a nemo a bata a madadin wankan jeg"...kafin ya karasa mgnr ummi ta jefeshi da wani mini bucket dake ajiye kusada Layla...tana huci tace"bazaka fita ba koh"...sum sum ya juya tareda ficewa daga bathroom din..duk ranshi a jagule...cikin dakin ya koma ya samu wuri ya zauna Yana kallon umma data gama yima babyn wanka tana Sanya Mata kaya yace"umma kiyima ummi mgn plss...wankan nn fa ba dole ne sai anyishi ba...tunda bataso sai a rabu da ita..ni bazan iya gani tana Shan wahala hakaba dn Umma kiyi wani abu kinji...kinga dai wahalan da tasha umma bai kamata Kuma a sake bata wani wahalan ba yanxu"...umma Kam dariya ta saki sosae don maganganun nashi ba karamin dariya suka bata ba...dama tunda taga ya shiga bayin tasan abinda zai biyo baya knn...Saida ta gama shirya baby ta Mika mashi ita ya amsa snn ta shiga kwashe kayan da tayi amfai dasu..duk ta maidasu inda ya dace...tana kokarin fita daga dakin Taheer yace"umma bakice komai bafa"...sai juyo tareda komawa ta zauna kusa dashi...har yanxu face dinta da murmushi tace mishi"ai ban San me zance maka bane Taheer...bazan iya da rigiman nn naka ba wlh"...tana rufe baki yace"umma kawai fa mgn zakiyi da ummi kice a hakura a wankan jegon tunda baby bataso..nasan idan ke kika fada zata saurareki"...umma na dubanshi tace"nidai bazanyi mgn kan a fasa yi Mata wankan jego ba gsky..sbd wankan ba karamin taimaka Mata zaiyi ba..Kuma ai ba ruwan zafi sosae ake Mata wankan dashi ba..sai da aka sirkashi sosae..ai munsan tanada dinkin a jikinta don haka bazaayi sakacin da har dinkin zai warware ba...so ka kwantar da hankalinka"...Taheer ya bude baki zai sake yin mgn umma tace"ya isa da Allah..kar Kuma in sakejin kayi mgn kan wankan jego..idan ba hakaba kuma zakaga bacin raina wlh..tunda nema kake ka maida kanka lusari sai abinda mace takeso zakayi Mata"...bata jira ko zaiyi mgn ta juya tareda ficewa daga dakin..shi Kuma ya sauke ajiyar zuciya cikin ranshi yasan tunda ta fadi haka to da gaske takeyi..shi bawai wankan ne baiso na..wnn kukan da takeyi ne baisonji...bayason abinda zai daga Mata hankali kwata kwata...ya maida idanu kan 'yarshi daketa wutsil wutsil da kafafu tana yatsine fuska kmr zata fara kuka...bai San lokacinda ya saki murmushi tareda kissing goshin yarinyar ba..."Hello Sweetheart"..ya fada kmr yana mgn da babba...ya dagota ya mannata da chest dinshi..sai ya shiga sauke ajiyan zuciya a jere a jere..wato Allah ne kadai yasan irin soyayyan dake tsakanin 'da da iyayenshi...bai taba tunanin haka iyaye keji akan 'ya'yansu ba...wani irin pure love ne tsakanin iyaye da 'ya'ya...duk yanda zaa kaiga yima mutum bayani bazai taba ganewa ba har rananda ya haifi nashi na kanshi...ubangiji da kanshi yace 'ya'ya sanyin idaniya ne ga iyayensu...babu shakka wnn mgn haka take don yanda yakejin son yarinyar nn is beyond expectation...shiyasa ubangiji yace yanajin kunyar duk wanda ya mutu bai taba haihuwa ba...sbd bazai taba experiencing wnn bond dake tsakanin 'ya'ya da iyaye ba(Allah ka azurtamu da zuri'a dayyiba🙏🏻)

Yana nn rungume da ita su ummi suka fito daga bathroom...da mamaki sosae ummin ke binshi da kallo don bata yi zaton Yana dakin ba...ta karasa inda yake kawai sai ji yayi ta karbe babyn dake hannunshi...ya bude idonshi da sauri sai Kuma ya sauke ajiyar zuciya ganin ummi ce ta karbeta...a fuska a daure ummi ta nuna mishi kofa tace"tashi ka bar min daki..kuma kar ka kuskura ka sake tako kafa ka shigo min nn don ranka zaiyi mummunan baci wlh"...baice Mata komai ba ya mike tareda kama towel dinshi dake cikin jallabiya ya rikeshi gam..snn ya fita daga dakin..shi Sam ya manta Ashe ko wankan bai gamaba ya fito...ya saki murmushi Yana shafa lallausan gashin kanshi daya tuno da yarinyarshi...kallonta ne duk ya mantar dashi damuwan da ya shiga...a hankali ya furta"I love you sweetheart..Allah ya raya min ke ya maki Albarka"...

STORY CONTINUES BELOW

Yinin yau ma dai sunata Shan baki yan barka...Ramla ma tun safe tazo gidan...da yawa daga cikin Friedns din ummi dana umma Wanda suke kusa duk sunzo barka suma...Haka iyalan Yusuf ma yau yini sukayi a gidan hadda yaransu.


Bayan kwana uku...


Yau kwana hudu cif da haihuwar Layla...yau ne Kuma Nafeesa da Mijinta Awwal suka zo ganin baby..shi zai koma yau sbd yara itakuma Nafee sai bayan suna zata tafi...

Tun dazu Taheer ya tafi airport daukosu...bai dade da zuwa ba jirginsu yayi landing...suna fitowa suka hangoshi don haka suka nufi inda yake..tun daga gaisuwa Taheer sai ya kasa sakewa dasu...bai san meyasa yakejin wani hadadden kunyarsu ba yanxu...duk sai yajishi a takure...suma da suka ga kmr nauyinsu yakeji sai suka barshi...a haka suke tafe in silence har suka karasa gida... Taheer ya dauki uban kayan da Nafee ta zo dasu ya shiga ciki...suma duk cikin suka shiga...sun samu su ummi a parlor..ita Kuma Layla na daki don har yanxu ko daman fitowa parlor ummi bata bata ba wai don jikinta ya dahu...wai tanada danyen jiki bazata na fitowa tanashan iska sosae ba...a parlon suka zauna bayan sun gaisa umma ta kwance babyn dake goye a bayanta ta fara mikama Awwal...cikeda farin ciki sosae ya amsa yarinyar hannu bibbiyu...ya Kira mata ido yana kallonta with so much love...yayi Mata addu'a snn ya mikama Nafee da takeji kmr ta kwace babyn daga hanunshi sbd kaguwan da tayi ta dauketa...Yana murmushi yace"ubangiji Allah ya rayata..yayi mata albarka..Allah yasa cikon addini ce"...gabaki dayansu suka hada baki wajen cewa Ameeenn....ita ma Nafee  ido ta kurama babyn sosae tana kallonta...tun a kallon farko ta gano tsantsar kamannin da takeyi da babanta...bata dauko komai na Layla ba sai haskenta...hakan yasan babyn take kyakyakyawa da ita tubarakallah...Saida tayi Mata kiss itama ta Mata addu'a snn tace"kullum su Al'ameen sai sunyi zancen yarinyar nn...kullum sai ance anaso azo aga babyn Ya Layla da daddy"...sukasa dariya...Awwal ne ya tambayi Layla...ummi ta mike tana cewa"Bari in kirata..kasan mai danyen jiki Saida zaman daki"...daga haka ta shiga dakinta jimm kadan sai gata ta fito hanunta rikeda na Layla dake sanye cikin dogon riga na atampa...suka karaso parlon ummi ta zaunar da ita kusa da ita snn itama ta zauna...Layla dake cikeda farin cikin ganin iyayenta tace"Abba sannunku da zuwa..Ina yini"..Yana murmushi yace"lfy qlou Layla..ya jikin naki"..tace"naji sauki Abba..Ina su Ramadhan"...yace"su Ramadhan na gida Layla sbd school..amma ana gobe suna zasuzo InshaAllah dasu zaayi suna"...tana murmushi tace"Allah ya kaimu"...sai ta kalli Nafee itama ta gaisheta...bayan sun gama gaisawan ummi na duban tace"to Taheer sai muji wanne suna kakeson sama yarinyar..idan Kuma ka bamu zabi sai mu zaba Mata"...Taheer dake murmushi at thesame time Yana shafa kanshi yace"dama yau nakeso inyi Mata huduba ummi..a kawota inyi yanxu sai in fada maku sunan dana sa Mata"...ummi tace"aah ka fara fada Mana sunan dai muji koh..duk nn waye bakinka..ai duk mune sbd haka ka fada munaji"...shiru Taheer yayi yana kallonta don Allah ya sani yafiso sai yayi Mata huduba snn yace sunanta wance...Awwal ne yace"Ummi tunda yace yanada zabi a barshi ya sa Mata duk sunan da yakeso...ai shine mahaifinta"...yana gama mgn ya kalli Nafee dake rikeda yarinyar har yanxu yace Mata"bashi ita yayi Mata huduba"...ba musu Nafee ta mike tareda mikamai yarinyan...Taheer ya amsheta da hannaye biyu...Saida ya fara yi Mata Kiran sallah a kunnenta duk biyun snn yayi Mata huduba da sunan daya dade da zabar Mata...su ummi duk suna kallonshi...bayan ya gama ya dago tareda mikama Nafee Yarinyar...face dinshi daukeda murmushi yace"nayi Mata huduba da sunan Ummata..Aisha.."gaba dayansu tsitt sukai suna kallon kallo don ba Wanda ya kawo sunan da zai sa Mata knn...shi Kuma cikeda tabbatarwa yace"yeah..she means the world to me..na tabbata ba don umma ba aurena da baby bazai taba yiwuwa ba..dama tun tana ciki nasama raina indai mace aka Haifa sunan umma ne da ita"...yana rufe baki umma da hawayen farin ciki ya wanke Mata fuska..ta bude mai hannayenta tana cewa"zo nan"..ba musu Taheer ya mike tareda fadawa jikinta...ta rungumeshi gam tana shafa kanshi tace"thank you so much son..I really appreciate..Allah ya maka albarka kaji"...Taheer na gyada Kai yace"Ameen Ummata..I love you so much"...umma tace"I love you more my son..I love you"...duk kallonsu kawai sukeyi kowa yana dariya...bayan sunyi breaking hug din ummi ma tace"Nima zo indan rungumeka ba don halinka ba".. da sauri Taheer ya fada jikinta itama tayi hugging nashi gam..tana bubbuga bayanshi tace"Allah ya maka albarka..Allah Kuma ya raya mai sunan kanwata..Allah ya raya Aisha"...Saida ya dago daga jikinta snn yace"Ameen Ummi..Nawal...Nawal nakeso ana kiranta dashi"...ummi ta kama haba tace"Oh Taheer yanxu ko nickname din bazaka bari uwarta ta zabar Mata ba"...yace"ummi nasan itama bazata qi zabina ba..and Nawal mean gift shiyasa nakeso ana kiranta dashi tunda she's a gift from Allah"...gabaki dayansu da suke cikin parlon ba Wanda baiyi murna da wnn suna da aka sama yarinya ba.. especially Nafeesa da takejin kmr anyi Mata albishir da aljannah...bata da burin da ya wuce taga zumunchinsu ya Kara karfi ta dalilin wnn hadin Kuma Alhamdulillah Yana Karfi din....

Da dare Taheer ya maida Awwal airport ya tafi bayan ya cika Layla da baby da Kaya kala kala..banda uban kudi daya basu...a Daren Kuma Taheer keta kokarin yaga sun kebe da Layla don yaji ra'ayinta akan sunan daya sama baby Amma ko keyarta bai ganiba...ganin ba ganin nata zaiyi ba sai ya hakura tareda komawa part dinshi ya kiranta a waya...tana zaune tana feeding Nawal Kiran nashi ya shigo...Saida ta kalli Su ummi dake gefe suna duba uban kayan da Awwal da Nafee suka kawo ma baby da Layla..Kaya ne masu yawan gaske...Saida taga hankalinsu bai kanta snn tayi picking Kiran...a hankali Taheer dake kwance kan gadonshi yace"babyna"...Layla ta lumshe idanu ta bude itama a hankali tace mishi"yes daddyna"...Taheer ya saki dariya before yace"baby ya kikaji sunan dana sama babynmu..sorry banyi shawara dakeba..I hope you like it"...yana rufe baki Layla tace"of course I like it daddy..sunane mai daraja da Kuma Ma'ana...sunan Amaryar fiyayyen halitta Muhammad SWA...itace mafi soyuwa a cikin matan Manzon Allah SWA...ita kadaice matar da ya aura a matsayin budurwa..itace akema lakabi da ummul mu'uminoom...itace ubangiji ya saukar da wasu ayoyi akanta don ya wanketa daga zargin da ake Mata..itace aka tambayi manzo SAW duk duniya wa yafi so..a Mata yace Aisha..a maza Kuma yace Mahaifinta wato Sayyadina Abubakar RA...daddy duk duniya nasan babu sunan daya dace da babynmu idan ba Aisha ba...snn sunan Umma ne..Wanda ba don umma ba da bazan taba auranka ba daddy...Ina alfahari da kasancewarka mijina Kuma uban 'yata..inason sunan da kasa Mata har cikin zuciyata..infact ko Maryam da yake sunana banjin ina sonshi kmr yanda nakeson Aisha..Allah ya raya mana Aysha Nawal"...tunda ta fara mgn Taheer ya lumshe ido yanajin wani farin ciki na sake mamaye shi...Saida ta gama mgn snn yace mata"Thank you..thank you so much my baby...I love you..Allah ya maki Albarka kinji"...a hankali tace"Ameen"...shi Kuma yaci gaba da fadin"baby am missing you so much..tun dazu nakeson ganinki amma ban ganki ba..where is my sweetheart"...Layla da har yanxu ke smiling ta kalli Nawal dake bacci kan cinyanta tace mishi"she's sleeping"...yace"ke yaushe zakiyi baccin"...a hankali ta sake cewa"Nima yanxu xan kwanta"...ya rausayar da kai kmr tana ganinshi snn yace mata"shi knn baby Saida safe..kiyi bacci mai dadi kinji...ki shafa min kan sweetheart snn kice mata Papa yana sonta sosae sosae...am missing you two like crazy"...kmr zai fashe da kuka ya karasa mgnr...Layla Kuma dake ta aikin dariya tace"to Saida safe daddy..we are missing you too"...daga haka sukayi sallama...ita kanta Layla sai taji duk ba dadi don ba karamin missing dinshi takeyi ba...tayi nisa cikin tunani kawai sai ji tayi Nafee ta dauke Nawal daga kan cinyanta tana cewa"so kike ki yar da itane Layla..wane irin iskanci ne wnn"...da sauri hankalinta ya dawo jikinta sai taga Nafee ta kwantar da ita...Ashe tayi nisa cikin tunani har Nawal din ta kusa faduwa kasa bata sani ba...

Washegari saiga Hanna tazo barka...da yarinyarta Hanan tayi girma sosae...baya ta gaisa dasu ummi a parlor ummin tace ta shiga daki Laylan ma ciki...haka kuwa ta nufi dakinda ummin ta nuna Mata...Layla na zaune suna waya da Taheer sai ga Hanna ta shigo...tayi mishi sallama snn ta mike da sauri tareda hugging din Hanna...itama hugging nata back tayi tana dariya...Saida suka gama cacime cacimensu snn suka karasa gefen gado suka zauna...Hanna na kallon Layla tace"oh wai Jakada kece kika haihu...ikon Allah knn kinganmu yanxu duk mun xama mamas"...Layla na dariya tace"bakida kirki wlh...ni sauko min Hanan din in ganta"...ba musu Hanna ta sauko Hanan dake gobe bayanta...Layla ta dauketa tana dariya tace"Tubarakallah Hanan din badai girma ba Hanna"...Hanna tace"umh wlh shegen girma gareta..ga fitina"...sai ta matsa inda Nawal ke kwance tana bacci...tana kallonta yace"wow mashaAllah...gata nn mai kamada babanta futuk..Allah ya raya mana"...a hankali Layla tace"Ameen"...ita kuma komawa tayi ta zauna snn tace"tafiya mukayi fa shiyasa kikaga shiru ban zoba...Muna Kano sai jiya muka dawo"...Layla tace"ba komai wlh..ai nasan dama kinada reason"...Hanna na gyada Kai tace"to ya sunan babyn tamu..ko baa da suna ba"...Layla tace"an sa Mata sunan Umma...Aisha amma zaana kiranta Nawal"...Hanna na zare idanu tace"Kai jama'a kin ga mun zama iyayen Aishoshi dagani har ke.. MashaAllah to Allah ya raya mana baby Nawal"..Layla ta amsa Mata da Ameen...ranar dai yini sukai suna hira da Hanna...har hiran makaranta Saida sukayi...Layla tace itama so take bayan suna ta lallaba ummi ta barta ta koma makaranta...Hanna bata bar gidan ba sai dare Habibinta yazo ya dauketa...tayi ma su ummi sallama tareda alkawarin zata dawo ranar suna..

Ana gobe suna su Al'ameen suka iso Abuja...murna a wurinsu baa mgn da sukaga baby..har rigima akeyi wnn yana shi zai dauka wnn Yana shi zai dauka...a ranar Kuma da yawa daga cikin family dinsu na kano sun iso...mutanen Dutse ma mota kusan biyar sukayi suka taho suna...Ta ko Ina Yan iwa da abokan arziki sai zuwa sukeyi..+


Shirye shirye sukeyi sosae sai kace taron biki ne ba na suna ba...umma ce ta dauki nauyin komai na suna hatta hall da zaayi taron a ciki ita ta kama..babu yanda ummi dashi kanshi Taheer din basuyi da ita kan ta bari ba amma Sam tace wnn taron nata ne tunda ita akayima takwara...har mawaki ta gayyato all the way from Kano..ga kuma cards da aketa bi ana rabawa mutane sai kace biki...

Washegari...

Tun safe dama aka yanka raguna kmr yanda al'ada ta tanadar...duk inda ka kalla a gidan zakaga cike yake da jama'a...tun safen Kuma masu kidan kwarya sukazo suketa faman kidi suna wakokinsu..sai wake Aysha Nawal suke mutane nata musu liki...umma Kam har rawa Saida ta taka itada Ramla..su ummi ma sun fito sunata likin kudi...mai jego kuwa tana ciki itada babyn da sauran mates dinta...taci kwalliya har ta gaji da haduwa itada baby Nawal.


Karfe biyu daidai make up artist ta iso gidan don yima mai jego kwalliya...a part din mahaifin Taheer aka sauketa don nan ne ba jama'a..basu bata lokaci na Kuma suna fara..suna tareda Hanna dake gidan itama tun safe...


Acan cikin gidan kuwa su ummi ankon lace sukayi Sea green..gaba daya sunyi dinkin bou bou iri daya...Ummi..Umma..Ramla..Nafee da Kuma Hibba..sunyi kyau MashaAllah har baa mgn...bayan sallahn asr aka fara diban mutane ana kaiwa hall din da zaayi sunan...Su ummi sune kusan na karshe a tafiya..

5:30 daidai aka gama ma Layla make up dinta...tana sanye cikin Lace dinta Blue Black..mayafi da Kuma head dinta suma blue black...sai diamond necklace dinta silver..purse da takalminta ma duk silver ne...Ni kaina dana kalleta sai dana furta Tubarakallah MashaAllah sbd tsabar kyan da tayi...Aysha Nawal kuwa tana sanye cikin dan gown dinta blue black da fari...ansa mata dan band dinta mai kyau a Kai shima white..sai showel da aka nadeta ciki shima white...kallo daya zakayi musu kaji sun shiga ranka matuka sbd tsabar haduwan da sukayi...Saida aka gama ma Hanna light make up dinta snn suka fito don tafiya wurin taron...

Angon karni kuwa tun safe ya wuce gidan Yusuf...Yusuf din nata tsokanarshi wai baban baby da baby amma kobi ta kanshi baiyi ba...sai karfe hudu snn shima ya shirya cikin Shadda sky blue snn suka nufi hall din shida Yusuf da some of friends dinshi...Allah ya sani da anbi ta nashi ba wani party da zaayi organising..shi ba son wnn harkan yakeba kwata kwata..don dai babu yanda zaiyi da Umma ne shiyasa zaije amma shi baa son ranshi zaa sa matarshi taci uban kwalliya ta shiga cikin Arrijaalu kowa ya kalle mai itaba...


Isowansu wurin yayi daidai da isowan su Layla ma...tunda ya dora idanunshi a kansu yaji tamkar ya Dora hannu bisa kai yace wayyo Allah sbd tsabar kyawun da yaga sunyi..they look absolutely breathtaking...wani irin so da kaunar su na sake mamaye ilahirin jinin jikinshi...kawai sai ya lumshe ido tareda jingina jikin mota yana dafe saitin heart dinshi da hannu...shi kadai yasan abinda yakeji cikin zuciyarshi...shi har yanxu bai yadda da ake cewa wai idan anyi aure soyayya na raguwa ba..coz kullum son baby karuwa yake cikin zuciyarshi bai tabajin ya ragu ba..ga kuma little Umma da yakejin sonta itama har cikin jininshi...yana sonta fiyeda komai...Yusuf ne ya jashi suka karasa inda suke...umma ta fito daga cikin hall din ta amsa Nawal dake hanun Layla snn suka jera tareda few mutanen da aka jera zasu shiga dasu ciki..


DJ najin zasu shigo ya sakar musu waqar Gimbiya Aisha ta Ali Jita...wai ya sadaukar da ita ga hajia Aisha uwar taro..da Kuma takawararta Aisha Nawal..

STORY CONTINUES BELOW

🎼🎼Gimbiya Aisha...Sarauniya ce Aisha...Aisha kixo ki dauki kidan girma...Aisha kinada babbar alfarma...Indo Indo da Aisha...gata abokin mu Aisha... Sarauniya ce Aisha...gamai kwalliya Ina Aisha...ga mace ta gari taho Aisha...yi sarauta Aisha...ke kwanta cikin kilishi huta...Aisha zauna a miki fifita...Aisha zana so ganin angon ta... Sarauniya ce Gimbiya... kyakykyawa ku tambaya...mai hakuri ce farar diya...mai nutsuwace 'yar hajiya...an kirata zinariya...Aisha Aisha...Aisha Aisha...Aisha dole ne na danyi miki take...masu sarewa kui tayi gobeda safe...ai hakuri baa fita ba... kwalliya baa fita ba...ilimi baa fita ba...nutsuwa baa fitaba...Yar babban gidace Aisha...Yar manyan mutane Aisha🎼🎼🎼🎼(Bari in bar ku haka kar kuce na cika son kai😜)

Tunda suka shigo wurin sai kallo ya koma kansu...sunyi kyaune na bugawa a jarida...duk Wanda ya kallesu sai yace mashaAllah...bayan sun karasa sun zauna akayi opening prayer tareda yima Aysha Nawal addu'an Allah yayi Mata albarka..sai Kuma taro ya cigaba kafin karasowar babban mawaki Ado Isa Gwanja...(kunsan tsakaninmu da gwanja akwai Amana😉)


Su Ramla sai raba suveniers suke...kowanne na daukeda picture din babyn an rubuta welcome to the world Aisha Taheer Jakada(Nawal)...kusan duk mutanen dake wurin ba Wanda bai samu ba...

Anci ansha an kumayi rawa sosae snn anyi barin kudi kmr baa san ciwonsu ba...Layla dai lallaba jikinta take don ko rawan ma kasawa tayi...dukda dinkin jikinta ya warke amma gani take motsi kadan zai iya warwareshi...shiko Taheer dama haka yakeso..bai son tace zatayi rawa at all...and he's happy yau da mayafi a jikinta unlike lokacin bikinsu da ko mayafin babu...dukda hakan kuma tayi mishi kyau sosae kmr ya rungumeta yakeji...baby Nawal kuwa duk wnn hidiman da ake tana hanun Namesake dinta wato umma..suk Wanda zai ganta saidai ya ganta a hanunta..dukda hidiman dake gabanta bata yadda ta bama kowa itaba wai don kar a jagwalgwalata😹


Bayan anyi sallahn magrib an dawo mawaki Ado Gwanja na Mata ya iso cikin hall din...Saida yaranshi suka gama kafa kayan kidinsu snn suka fara kida..shi Kuma ya sakar mana wakarshi mai taken Mamar Mamar...lokaci daya nida jama'ata da mukazo suna tare muka shiga filin rawa😜


🎼🎼🎼Ayye lube...Ahayye lube gumbar Dutse...naga gidanka ya cike ya batse...dan wnn kidan na mai kayane duk wcce babu sai ta koma gefe..Mamar Mamar...ai wnn kidan kidan Mata ne..Mamar Mamar...Naga Kuna rawa Kuna wani juyi..Mamar Mamar...wnn kidan kidan matane..maar Mamar...Dan kuji wnn kidan kidan matane..Mamar Mamar...Naga Mata kunyi dumur dumur Kuna wani jumping..Mamar mamar...sai na biyoku baya zam mini baitin..Mamar Mamar...sai ku tayani inji dadin sautin..Mamar Mamar...Mata a kiraku ran gida daidai ne..Mamar Mamar...dn matar wane tafi matar wane..Mamar Mamar...Mata kune na bara kune na bana..Kuma kune na shekarar basasa..Mamar Mamar...ai kowa ya ganku ya San kune..Mamar Mamar...saidai tambayar rashin albarka🎼🎼🎼

Ado gwanja na fara wakar nn Mata suka fara tashi..masu rawa nayi masu yi mishi liki ma nayi...Ni kaina da naji waqar nn Saida nadan taka rawana snn naci gaba da dauko muku bayani...shima bai gama performance din nashi ba sai after ishaa...daga nn Kuma mutane suka fara raguwa a hankali a hankali...su ummi Kam basu bar wurin nn ba sai around 9..lokacin kowa ya watse..Kuma taro yayi tsari yayi kyau saidai ace Alhamdulillah..Allah ya raya Aysha Nawal...


Layla kuwa dama tun dazu Taheer da kanshi ya dauketa suka tafi..bayan sun karbi Nawal da har yanxu ke hannun umma..


Yarinya tayi goshi sosae don sun samu Kaya fiyeda ma yanda sukayi tunani...ba na Nawal dinba...ba Kuma na Layla ba...Ummi kanta saida tayi musu Kaya masu yawa Banda nasu Nafee ga Kuma umma da akaima takwara...ga sauran family da friends dinsu suma sunyi kokari sosae...ga Kuma uban Wanda Taheer yayi musu kmr Wanda ke hada lefe..Layla har mamakin inda zasu Kai wnn uban kayan takeyi...sai takega kmr sunyi musu yawa..

Wanna kenan


Bayan kwana biyu da suna Taheer ya shigo gidan da dare...tun jiya yake son a bari yaga matarshi Amma ummi ta Hana...daya tambayi Layla zatasa a kawo mishi Nawal shi Kuma ba ita kadai yakeson ganiba...he wants to see his wife too...direct ya wuce dakin ummi don baiga kowa a parlor ba...su Al'ameen da zasu koma gobe suna zaune Kan gado shida Ramadhan...sunsa Nawal dake bacci a tsakiya sai musu suke wnn yace tana kamada Layla wnn yace no da Taheer take kama...ita Kuma Layla na zaune gefe tana kallonsu...Taheer ya rungume hannayenshi a kirji Yana kallonsu with a smile kan face dinshi yace"Hey musun me kukeyi haka"...da sauri Al'ameen yace"daddy dn Allah Nawal ba dakai take kamaba"...shima Ramadhan yace"daddy ai da Ya Layla take kama koh"...Taheer yasa dariya kafin ya sunkuyo tareda daukan yarinyar dake kwance...ya Kura mata ido shima kmr yanason gano dawa take kaman snn yace"yeah duk kunada gsky...eyes dinta da nose dinta da Kuma lips dinta duk irin nawa ne...skin dinta Kuma irin na mamanta ne"... Al'ameen ya mike yana dariya yace"dama na fada maka yaro..da daddy take kama"...shima Ramadhan ya mike yace shi bada daddy take kama ba..a haka suka fice daga dakin...Taheer ya rakasu da ido kafin ya dawo da dubanshi kan Layla da itama ke binshi da kallo...ya saki murmushi tareda karasawa ya zauna kusada ita..a hankali ta matsa jikinshi sosae tareda rungume hannunshi a chest dinta..ta dora kanta akan shoulder dinshi suna kallon Nawal dake baccinta peacefully...a hankali shika Taheer din ya kwanto da kanshi kan nata..muryanshi can kasa yace"my cute babies"...Layla ta dan turo baki tace"ai na fada maka bazaka na kiranta baby ba wlh..itama Kuma bazata na ce maka daddy ba"...Taheer na dariya yace"ki kwantar da hankalinki dama ba sunanku daya ba..ita kinsan mene sunanta?.."banza tayi dashi tana cigaba da turo  baki..Saida yayi kissing goshin Nawal din snn yace"sweetheart..she is my sweetheart..my blood and she is my mom"..da sauri Layla ta matsa daga jikinshi tareda juyawa mishi baya...shi Kuma ya ajiye Nawal a gefe snn ya dagata cak ya dora akan laps dinshi...tana hararanshi tace"idan ummi ta shigo nidai ba ruwana"..yaja kumatunta Yana kokarin yin mgn aka bude kofar dakin...a razane suka daga kawunansu suna kallon kofan...umma ce tsaye..ta kama kugu tana kallonsu da mamaki sosae a fuskarta...da sauri Layla ta mike daga jikinshi tana marairaicewa tace"Allah umma bani na kirashi ba..kuma ni bance ya dorani a cinyanshi ba Allah"...umma batabi takan abun da Laylan ke fada ba..tana duban Taheer tace mishi"tashi ka fita"..ba musu ya mike inda yake Yana sosa Kai..shi sai yaji sauki daba ummi ce ta shigo ba..yasan da yanxu tana nn ta inda take bata nn take fita ba...maimakon ya fitan saiya tsaya kusada umman yace"umma shigowana knn wlh..ki tambayeta k"bai karasa mgnr ba umma ta sake cewa"nace ka fita kabar dakin nn Taheer..idan Kuma so kake Yaya ta shigo ta sameka Bismillahi"..bai sake mgn ba ya kama hanya kmr zai fita daga dakin sai Kuma ya dawo da sauri zuwa inda Nawal ke kwance tayi kissing goshinta yace"I love you sweetheart"...yayima Layla ma kiss din yace"I love you baby"..sai ya karasa inda umma take itama yayi kissing forehead dinta snn yace"I love you umma"...daga haka ya fice daga dakin...umma ta bishi da kallo tana girgiza Kai..wato ko kunyarta baiji yake wnn iskancin hadda wani kissing dinta..ko dayake batayi mamaki ba..indai Taheer ne akan Layla ba abinda bazai iyayi ba..ga Kuma 'yarshi itama da ba kunyan me dashi a kanta ba...haka ta juya ta bar dakin tana murmusawa ita kadai...alamrin Dan nata dariya yake bata wlh.."Allah ya shirya mana"

A gurguje plss..

Bayan Sati 3...

Yau tun safe Layla ke zuba idon ganin Taheer tanason yimai mgnr komawanta school amma shiru bata ganshi...tun last week take so tayi resuming amma datayi mgn da ummi sai tace wai sai sunyi arba'in..ita harga Allah ta gaji dayin missing karatunta...yanxu satinta hudu knn da haihuwa..Kuma Alhamdulillah daga ita har Nawal din basu da wani matsala...ita ta maida jikinta tayi kyau tayi fresh abunta..kana ganinta zakasan batada wani problem..ta Dan Kara kiba da yayi suiting dinta...itama Baby Nawal tayi kiba ta Kuma Kara haske sosae...in ka gantasai kayi tunanin takai 2 months..gashi tayi wayo ga Kuma kyanta dake Kara fitowa..kowa ya ganta sai yayi sha'awanta...haka uban ke sata a gaba yayita Mata wasanni kala kala..tun tana kukan bata so har tazo ta saba..idan kaji yanda yake mgn da ita zakayi tunanin da babban mutum yake mgn...ummi tayita fada wai so yake ya lalata ta kmr yanda ya lalata mata Layla...


Tana cikin daki ta gama shirinta tun dazu..tana zaune da wayanta a hannu tana tunanin ko kiranshi zatayi ta fada mishi mgnr komawa school din..sai Kuma taga it's better suyi mgn face to face...tana nn zaune tana tunane tunane tajiyo kmr muryanshi a parlor...da sauri ta ajiye wayan nata ta fita...yana zaune parlon shida umma..Yana sanye cikin kananun Kaya sai taga ya koma yaro sosae a idonta..gaba daya hankalinshi na kan Nawal da yake wasa daita..ita Kuma sai babbaka dariya dake har dimples dinta suna lotsawa...umma na gefe tana kallonsu tana dariya..dawowanshi knn daga Clinic ko abinci baici ba ya fara wasa daita...ta kuma San tunda suka fara wasan nn yanxu cin abincin ma sai illah MashaAllahu...

Karasowan Layla yayi daidai da shigowan ummi parlon itama...Layla ta zauna opposite to him snn a hankali ta Kira sunanshi don hankalinshi na kan Nawal bai ma ga shigowanta ba...a hankali Taheer ya dago idanunshi tareda saukesu a kanta...wani irin difff yaji cikin brain dinshi kmr irin an kawo wuta am dauke...ya zuba Mata idanun nashi sosae yana binta da wani kallo mai wahalan fassarawa... zuciyarshi yaji tana wani fat fat fat..gashi kuma ta koma bugu da sauri sauri..idanunshi sun kada sunyi jajir...ya Kuma kasa dauke idanun nashi daga gareta..it's like akwai wani force of attraction dake Jan idanun nashi zuwa gareta...lokaci daya komai da komai nashi ya tsaya cak kmr ansa musu brake...ita Kuma Layla kallon da taga yana Mata ne ya haifar Mata da abubuwa da dama a cikin heart dinta..gaba daya sai taji ta kasa fadan maganan da yake bakinta...yawun bakinta taji ya kafe kaff ba tareda sanin musababbin hakan ba...ummi Kam zuba musu ido tayi tana kallon ikon Allah...ta kalli wnn ta kalli wancan ta rasa kallon me akeyi ne haka..ita Kuma umma dama tun da taga yanda Taheer ya kafeta da ido tasan karshen zancen...Kamar kiftawa da bismillah kawai sukaga Taheer ya mike ya kama hanyar fita daga dakin...da sauri ummi tace"Kai Ina zakaje da jaririya bakada hankali ne"...a hankali ya juyo tareda mikama umma Nawal snn ya fice daga dakin..shi gaba daya ma ya manta tana hannunshi Saida ummin tayi mgn...duk suka rasashi da kallo bayan ya fita ummi na tabe baki tace"yaro sai kace mai iskokai..iskanci iri iri ya iyashi...yanxu dubi yanda ya wani mike a zabure sai kace bashi ya cika mana kunne yana wasa da 'yarsa ba dazu"...daga umma har Layla baby Wanda yace kala..ita Layla ta mike tareda komawa daki tanajin gaba daya jikinta a sanyaye..bata yadda da kallon nn da taga Yana Mata ba Sam...tasan for sure something is fishy..da akwai abinda ke damunshi...ita Kuma umma gaba daya sai taji ya bata tausayi...tasan yanda Taheer yake son Layla Allah ya sani yamayi kokari da aka kawo har yanzu bai gaza ba...tun kafin ta haihu fa take gida Kuma bai taba cewa komai ba..ko ganinta ma watarana ummi hanashi takeyi..batasan meyasa ummin kemai haka ba wlh..ko don ta lura Yana matukar son Laylan ne oho...ta maida idanunta kan Nawal data fara yan koke koke..ta dan saci kallon ummi taga hankalinta ma na kan tv..a hankali ta mike zuwa dakinda Layla ta shiga..ya kamata tayi wani abu..bai kamata tasa ido tana kallon danta yana kokarin zaucewa kan abinda is his ba..bazata zuba ido ba gsky..she really must do something idan ba haka zasu shiga hakkin yaran nn... especially ma Taheer da tasan bashida hakuri ko kadan akanta..saukin abun ma yanzu shine Nawal...ko ya yake cikin bacin rai yana fara wasa daita sai ya mance..amma dukda haka zata duba taga abunda zatayi..


A kwance ta samu Layla tayi daidai kan gado..ta rufe face dinta da hannayenta so bata ganin face dinta...umma ta zauna gefen gadon snn tace"tashi muyi mgn"...da sauri Layla ta mike zaune don bata ji shigowan umman ba...umma ta Mika Mata Nawal tace"fara bata tasha naga zata fara rigima"...ba musu Layla ta amsa Nawal da umma ke miko Mata snn ta fara feeding dinta...Umma na nn zaune tana jiran Layla ta gama feeding Nawal suyi mgn kawai sai ga ummi ta shigo dakin...ba don umma taso ba ta mike tareda fita daga ciki...tanata ayyana yanda zaayi ta tura Layla part din Taheer ba tareda ummi tayi noticing ba...wnn shine kadai hanyan da tasan zai dan samu sauki cikin ranshi...ta San Yana bukatar kebewa da matarshi tunda ta dade a gidan..ba kuma abinda yake shiga tsakaninsu...snn itama Laylan ta lura akwai maganan da take sonyi dashi don haka wnn ne kadai solution...+


Saida ta daidaici ummi tayi bacci snn ta sake komawa dakin...kmr yanda tayi zato ummi tana kwance kan gado tana bacci...ita Kuma Layla ta gama Shirin kwanciya itama zata kwanta sai ga umma ta shigo...zatayi mgn umma ta dora hannu kan bakinta tace"shhsshs"...ba musu Layla taja bakinta ta tsuke...ita Kuma umma ta kama hanunta a hankali suka fita daga dakin...Saida suka shiga parlor snn umma ta sake hannun Laylan...tayi kasa muryarta tace mata"kina jina..so nake kije ki dauki abincin ki kaima Taheer yana bangarenshi.. duk yau ya kasa cin abinci ban San meke damunshi ba"...a hankali Layla tace"umma ko dai bashi da lfy ne"...umma tace"ke da kike matarshi ai ke ya kamata ki sani Layla..haka nn kike biyema Yaya kuna azabtar da yaron nn..ko gaisheshi fa baki zuwa har can part din nashi kiyi..kullum kina daki bayan Kuma kinsan yanada bukar ganinki amma kike iskanci..ki cigaba da biye mata duk ya gaji da wulakancinki yace zai Kara aure bazan hanashi ba wlh.. instead ma zanyi supporting dinshi tunda ke kina nuna baki damu dashi ba"...da sauri Layla da idanunta har sun raina fata jin maganan da umma ta fada tace"Kai umma dn Allah...Ni wlh ba Wulakanci nake mishi ba ummi ce..kinsan halinta bazata na barina Ina kulashi ba..wai sai na gama jego"...umma ta saki tsaki kafin tace"ai sai Kita yi...kici gaba da biyema Yaya kina banzatar da mijinki..shi namiji kulawa yake so kuma idan bai samu wurin matarshi ba yana iya zuwa koma inane ya samu..idan kinga zakiyi hankali sai kiyi"...tana gama ta nuna kofa tana cewa"yi sauri kije ki dawo kar Yaya ta tashi taga bakya nn"...da sauri kuwa Layla da kayan bacci kadai ne a jikinta sai hula ta fita daga dakin...Kai tsaye part dinshi taje..a hankali ta tura kofan parlonshi luckily tajishi a bude...duhu sosae ta gani a dakin don ya kashe bulbs din ko Ina...a haka ta karasa bedroom dinshi...nan ma tana tura kofan tajishi a bude ba bata lokaci ta bude ta shiga...Saida tayi switching light din dakin snn ta shiga bin dakin da kallo tana so taga a inda zata ganshi...ta wara ido sosae tana waige waige ganin baya cikin dakin...a hankali tace"to Ina ya shiga a Daren nn Kuma"...zuciyanta ya buga da karfi data tuna mgnr da umma ta fada Mata yanxu..."shi namiji kulawa yakeso Kuma idan bai samu a wurin matarshi ba yana iya zuwa koma inane ya samu"... innalillahi badai daddy fita yayi cikin Daren nn ba...to Ina zaije..wajen wa zaije at this time of the night...gaba daya ta gigice har bataji time din da ya fito daga bayi ba...abinda taji kawai shine an rungumota ta baya...ta lumshe ido lokaci guda kuma ta sauke ajiyar zuciya mai karfi...koda bataga face dinshi ba tasan shine...taji kamshin perfum dinshi and taji yanda hug din nashi yayi affecting duk body systems dinta..a hankali ta juyo tana facing dinshi...zatayi mgn ya sake hugging dinta gam yana cewa"baby I missed you...am about going crazy..baby dn Allah stop all this drama..ki dena biyema ummi kizo mu koma gidanmu dn Allah..wlh na gaji..na gaji da boye mn Mata da akeyi sai kace wanda bashida gata..duk ummi ta maidani gwauro ta karfi da yaji"...Yana gama mgn sai ya jata suka zauna kan gado yana kallonta da kyau yace"Yama akai kikazo nan..ummi ta sani?.."da sauri Layla na girgiza mishi kai tace"bata saniba..umma ce tace inzo..wai ko abinci bakaci ba"...Taheer na murmushi yace"Allah yaja zamanin ummata..she is one in a million..I love her so much"...sai Kuma ya kwabe fuska yace"baby am starving..yunwa nakeji sosae wlh"...da sauri Layla ta mike tana cewa"let me get you something..idan kaci sai muyi mgn"...tana kokarin barin inda yake yasa hannu ya jawota ta fada jikinshi..ya kwanta kan gadon tareda dorata itama ta kwanta a samanshi...murya can kasa yake cewa"Ina Kuma zakije"..tace"zanje in kawo maka abinci mana daddy"...ya dan bata rai snn yace"Ni ba abinci nake bukata ba..I want you"...Layla ta zaro idanu sosae tana kokarin mikewa daga jikinshi tace"Aa daddy kar kayi haka plss..wlh ummi zata gane nidai ka kyaleni in tafi dn Allah..Kuma Nawal zata iya tashi daga bacci bana nan"...a hankali taji ya saketa daga rikon da yayi Mata..lokaci daya jikinshi yayi sanyi jin ta kira Nawal..ya sani tabbas zata iya tashi daga baccin idan bata kusa Kuma zatayi kuka..shi kuma baison kukanta..dn haka zai hakura ko dan sbd ita..amma indan ta ummi ne bazai damu ba..tunda yasan kota tashi baza tace zata biyo Layla har part dinshi ta dauketa ba..iyakaci dai da safe idan sun hadu ta sauke masu kwando kwando wnn Kuma sun riga sun saba dashi so bazai dameshi ba..amma Nawal kam yasan definitely zata iya tashi daga bacci and babu wanda keda nonon da zai bata sai Layla so wnn shine kadai dalilin da zai sa ya hakura komai matsuwar da yayi kuwa..bazai taba dora bukatarshi kan ta yarinyarshi ba..no.. Never..yana yi mata sonda ko yaya yaji kukanta hankalinshi na matukar tashi so bazai so ya zama source of yin kukan nata ba...a hankali ya koma tareda kwanciya kan gadon ya juya ma Layla da tayi tsai tana kallonshi baya...murya can kasa yace mata"kije..Saida safe"...kmr zatayi kuka tace"daddy"...ya juyo yana kallonta ba tareda yayi mgn ba...ita Kuma ta sake langabe Kai tace" daddy am sorr"...bata karasa ba ya mike zaune tareda dora hannunshi kan bakinta...yana girgiza kai yace"u don't have to apologise ay ba laifi kikayi ba..kawai nace ki tafi ne because I don't want sweetheart ta tashi daga bacci Kuma baki koma ba..so kiyi sauri ki tafi kar ta tashi baki kusa"...a hankali ta sake cewa"but daddy I want to talk to you"...a takaice yace Mata"umhumm inaji"...tace"mgnr komawa school ne dama...ya kamata in koma daddy inata missing abubuwa masu muhimmanci"...Taheer ya shiga girgiza kanshi yace"No baby..ba yanxu ba"...kmr zatai kuka tace"but daddy why"...yace"sbd Sweetheart bata yi kwari sosae ba..ban so kije kina wahalar min da ita a school so it's better ki bari ta dan Kara girma"...lokaci daya Layla ta fara hawaye tace"ai dama ni yanzu nasan baka Sona..Allah daddy nasan yanzu kafi son Nawal a kaina"..dafa goshi Taheer yayi yanajin yanda take sake dama mishi lissafi da wnn kukan da takeyi...tanaso ta sake hargitsa mashi 'yar ragowan nutsuwar da yai saura a tare dashi...har ya Kai hannu zai kama nata sai kuma ya fasa..murya a hankali yace Mata"baby mene abun kuka dn Allah..to kiyi hakuri ki bari idan kuka karasa 40 days sai ki koma..and stop saying na dena sonki okay?..yanxu ki tashi ki koma kar ta tashi a bacci baki nn"..Layla na share hawayenta tace"gashi nn har wani korana kakeyi sbd ita"...Taheer ya sake dafa goshi before yace"to naji am sorry..bazan Kara koranki ba..are we good now?.."ta murguda baki tareda dauke kanta gefe..shi Kuma ya saki murmushi snn ya sake komawa ya kwanta..shi kadai yasan what he's feeling right now..yasan idan taci gaba da zama a nan komai na iya faruwa..shi Kuma baison abinda zai sa sweetheart dinshi kuka..ya tabbata ba dan Nawal ba yau da Layla bata isa tabar dakinshi batareda ya aikata wani abun ba...ita Kuma Layla a hankali ta mike ta kama hanyan ficewa daga dakin...har takai bakin kofa sai Kuma ta tsaya tana tunani...anya kuwa ya kamata ta tafi ta barshi bayan tasan ko abinci baici ba..sai taga kmr bata kyauta ba idan tayi hakan..tasan for sure yana cikin damuwa...sai ta juya a hankali tareda komawa cikin dakin...ta zauna kusa dashi tana bubbuga bayanshi da hannunta tace"daddy"...Taheer yayi Mata banza bai amsa ba..ta sake cewa"daddy"...nan ma baiyi mgn ba...sai tasa duk hannayenta tana kokarin juyo dashi tace"daddy mana..I want.."tun kafin ta karasa mgnr Taheer ya mike zaune yana kallonta da idanunshi da sukai jajir yace mata"ki dena tabani baby indai baso kike ki karar min da dan hakurin dayai min saura a tareda ni ba..na fada maki ki tafi..banason Nawal ta farka baki koma ba"...ta rausayar da Kai snn tace"daddy to in kawo maka abinci"...ya girgiza Mata kai..ta sake cewa"amma daddy kace min bakaci abinci ba"...yace"am not hungry any more"...ta mike zata fita tace"nidai bari in kawo maka ko tea ne kasha"..tana rufe baki yace"ko kin kawo ma baby ba iya cin komai zanyi ba..I lost my appetite so dn Allah kije ki kwanta nima I want to sleep"...Layla bata sake cewa komai ba ta juya tareda ficewa daga dakin...zuciyarta taji na Mata wni irin zafi..wato ma ita yake Kora daga inda yake..kawai sbd Nawal shine yake Mata wnn Koran Karen...tana tafe tanata tunani ita kadai har ta karasa part dinsu ta shiga...bata samu umma parlor ba don haka ta wuce dakin ummi...suna kwance suna baccinsu daga ita har Nawal kmr dai yanda ta tafi ta barsu..a hankali ta haura kan gadon itama ta kwanta tareda lumshe idanunta..har yanxu idanunta basu bar gano Mata shi cikin yanayin da ta baro shi ba..duk sai taji ta gagara sukuni..duk haushin ummi taji ya kamata don ita ke hanata zuwa inda yake wai kar ya lallaba ya sake dirka Mata wani cikin..ita Kuma Allah ya sani tsoron haihuwa take..tunda tayi bataji dadinta ba..gani takeyi har abada bazata sake haihuwa ba sbd tunda take bata tabajin ciwon da yakai nakuda azaba ba a duniya..ta wahala ne fiyeda tunaninta..ta dade tana tunane tunane sai juyi takeyi kan gado baccin yaki daukanta..sai can dare sosae snn wani barawo ya lallaba yayi gaba da ita..

STORY CONTINUES BELOW

Washegari ma haka ta tashi sukuku kmr mara lfy...bayan tayi wanka ta shirya kanta cikin skirt da riga na material daya amshi jikinta sosae..sai ta fita parlor sakamakon Kira da ummi keta kwala Mata tun dazu wai Nawal na kuka taje ta bata nono..baki a tunzure ta karasa parlon ta zauna tana cewa"ummi nidai gsky na gaji da halin Nawal wlh..shegen ci gareta..kullum nono kullum nono ko gajiya ma batayi..Muna komawa gida zan fara bata baby formulas don bazan yadda ta karar dani a banza ba"...ta karasa mgnr hadda su murguda baki kmr Nawal din tasan me take fada... ummi Kuma tsaki taja kafin tace"kedai zanga ranar da zakiyi hankali wlh"...daidai nn Kuma sukaji sallamar Taheer a cikin parlon...ya karaso ciki ya gaisa da ummi..umma ta shigo parlon tana dubanshi tace"wuce muje kayi breakfast kafin ka fita"..yace"umma na koshi"...umma na hararanshi tace"ban gane ka koshi ba..ko kaci abinci ne a wani wurin"...a hankali yace"aah"..tace"to wuce muje bana son gardama..naga jiyama haka ka kwana bakaci abincin ba shine yanxu ma kakeso ka tafi aiki ba tareda kaci ba..to da raina da lfyta bazan bari yunwa ya hallaka ka ba wlh..wuce muje"..Taheer ba yanda ya iya haka ya wuce gaba umma na binshi a baya har zuwa dinning..Layla ta bishi da kallo ganin yanda yayi kmr bai San da zamanta a wurin ba...umma taja mai kujera ya zauna snn tayi serving dinshi..ta samu wuri itama ta zauna Saida ta tabbatar da yaci abinci da yawa snn ta kyaleshi..ya mike Yana goge bakinshi da tissue ya koma parlon umma na bayanshi...ya dauki brief case dinshi daya ajiye snn ya kama hanyan fita daga parlon..Saida yakai bakin kofa snn ya juyo ya wani marairaice yana kallon umma fuska a kwabe kmr zaisa kuka..ita Kuma umma ta saki murmushi tana girgiza kai tace"ai ban manta ba" sai kuma ta karasa inda Layla ke zaune ta dauki Nawal dake hannunta ta mikama Taheer ita..da sauri ya amsheta lokaci daya yana Dora murmushi kan fuskan nashi..Saida ya lumshe ido snn yayi kissing forehead din Nawal din..da cheeks dinta snn ya dorata a chest dinshi ya dan matse for almost 2 mins kafin ya mikama umma ita yana cewa"I love you"...umma dake kallonshi tana dariya ta karbi Nawal din tace"an gama sallamar"..Yana murmushi shima yace"an gama ummata"..umma tace"to shknn Allah ya tsare"..yace"Ameen"snn ya juya ya fita daga parlon...kawai Layla saita kifa kanta kan cinyanta ta fashe da kuka...ummi na kallonta tace"ke lafiya"...Layla dake kuka wiwi tace"ummi kalli fa yanda yayi banza dani sai kace bai sanni ba..kawai sbd ya samu 'ya yanxu shine yake wulakanta ni"...ummi tace"to Kuma shine abun kuka sbd bakida hankali..ba sai ki barshi yaje yayita iskancinshi ba me zai dameki..qanin ubanki ne shi da zaki cika mana kunne da kuka wani wai yayi kmr bai ganki ba..kin haihu amma har yanzu baza kiyi hankali ba...

idan kika barni dashi ai zai dawo har cikin gidan nn ya sameni"...itadai Layla kukanta taci gaba dayi bil haqqi...umma Kuma ta karasa ta zauna snn tace"aah fa Yaya ni Banga laifin Taheer ba a nan"...ummi tace"ai dama bazaki ganiba Aisha..ai har abada bazaki taba ganin laifinshi ba"...umma tace"wlh mgnr gsky ne Yaya..itama da take matarshi take banzatar dashi toshi meye laifi idan yayi Mata abinda takeyi"...ummi tace"kmr ya take banzatar dashi wai..me takeyi mai ne"..dariya umma ta saki kafin tace"nidai banga laifinshi ba gsky..kuma ke dama ya zaayi ki hada son da yake maki da Kuma Wanda yakema diyarshi"...umma ta karasa mgnr referring to Layla...ita Kuma sai ta mike da gudu ta shiga daki tana cigaba da kukanta..ummi ta bita da kallo har ta shige dakin kafin tayi kwafa tace"zaka dawo ka sameni wlh..sai naji dalilinda yasa zaka wulakanta Matarka kawai sbd ka samu 'ya...sai kace ba ita ta shiga labour room ta haifo maka 'yar ba"...umma na jinta amma sai tayi kmr bata jiba ta shiga yima Nawal wasa suna dariya abinsu..

Shiko Taheer yana sane yayi mata duk abinda yayi..yaji tana cewa zata fara hadama Nawal da baby formulas and yasan idan ba bacin rai ya nuna mata sosae ba bazata hakura ba..yasan halin kayarshi Sarai..tana komawa school zata iya fara bata formulas din kmr yanda ta fada..shi Kuma bazai taba yadda ta fara bata wani abu ba har sai ta kai 6 months..yasan Kuma hakan da yayi shine kadai maganinta..


Karfe hudu daida ya dawo gidan..bayan ya shiga part dinshi yayi wanka yayi changing sai ya nufi part din ummi...bai samu kowa parlor ba sai tv dake aiki..direct ya wuce dakin umma..ya sameta zaune kan sallaya..idar da sallahnta knn tana addu'a ya shigo..sai ya hau kan gadonta ya kwanta tareda lumshe ido..ita Kuma umma ta mike bayan ta gama addu'an ta cire hijab din jikinta ta hada da sallayan ta ajiyesu inda ya dace snn ta zauna kusa dashi kafin tace"are you alright?.."da sauri Taheer ya mike zaune yana dubanta yace"am fine umma..gajiya ne kawai"...umma tace"to muje kaci abinci sai ka samu ka huta"...har zata tashi daga wurin Taheer yayi saurin kamo hannunta yace"umma Ina baby..nasan tayi maku kuka bayan tafiyana koh"...dariya umma ta saki before saying"wlh kuwa kmr ka sani..kuka sosae wai ka dena sonta yanzu sbd Nawal"...shima dariyan yayi yana girgiza kanshi yace"umma babyn ce batajin mgn wlh..ji nayi fa tana cewa wai muna komawa gida zata fara bama Nawal baby formulas..wai ta fita tsotso da yawa"...umma ta kalleshi snn tace"kaji rashin hankali koh..jariryar zaa fara bama wani abu sbd iskanci"...Taheer yace"abinda na gani knn umma shiyasa nayi kmr ban ganta ba..nasan idan ba da gaske nayi Mata ba zata iya yin abindata fada din"...cikeda gamsuwa umma tace"kayi daidai wlh..ao gara da Kai mata hakan sai ka zama namiji kaima..ba wai ka ringa biye Mata tana iskanci ba"..dariya kawai ya saki jin mgnr da umma ta fada..umma ta kama hanunshi zasu fita daga dakin saiga Layla ta shigo dakin..tana ganinshi Kuma ta juya da sauri zata fita yayi azaman rikota ya dawo da ita ciki..itadai umma ta fice abinta don tasan Taheer ba kunyane ya isheshi ba...shi Kuma Saida ya zauna gefen gado itama tana zaune jikinshi yace"baby am sorry"..ta turo baki tanata kokawan kwatan kanta amma ta kasa..Taheer ya sake cewa"ay mgn zakiyi"...tace"shine daxu hadda yin banza dani..kawai sbd kayi 'ya yanxu shine kake min Wulakanci"..ya sake rungumeta yana dora kanta a chest dinshi yace"ai kece kika janyo baby..don me zakice zaki fara bata baby formulas"...Layla ta rausayar da Kai kmr zatasa kuka tace"nifa da wasa nake"...mgnr da yake sonyi ya makale sbd bugun da sukaji anama kofan..Layla ta matsa daga jikinshi da sauri tana zazzare ido..shima Taheer din mikewa yayi Yana dariya..muryan umma suka jiyo daga waje tana cewa"bazaka fito daga dakin nn ba ko Taheer"..da sauri ya bude kofan ya fita..itama Laylan mikewa tayi ta fita tana addu'an Allah sa ummi bata tambayeta ba..tasan idan umma tace mata tana tare dashi sai tayi Mata fada wlh.Post a Comment for "DR TAHEER CHAPTER 11 BY UMMU ASHRAF"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...