DA KAMAR WUYA CHAPTER 8 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DA KAMAR WUYA CHAPTER 8 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

DA KAMAR WUYA CHAPTER 8 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

- - Post a Comment

DA KAMAR WUYA CHAPTER 8 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU


                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kallonta yakeyi fuskarsa dauke da smacking, Ticket din ta ajiye a gabansa. Tare da zuba masa harara, baki ya tabe ya dauki ticket din yana kara dubawa.+


" gobe zamu tafi, pack your bag and get ready." Ya fada in husky voice dinsa


" sai ka dawo!! Ba inda zani." Ta fada tana tura baki.

" kar muyi haka dake! Kefa kika ban wannan shawarar to meye laifi don kin tayani na gyara kuskiren da kike ganin nayi?"


" Allah kama gama rainamin hankali. Gotai gotai dani, zan rakaka zance? Bama a nan ba har Egypt, saboda bani da aikin yi? Ko ce maka akayi cewa tayi inje na gani?"

Murmushi yayi mai sauti, " we shall see to it." mikewa yayi ya dau ticket dinsa, sama ya haura cikin gudu -gudu, sauri -sauri.


Da harara ta rakashi, kafin tayi kwafa.


               *******************

Yau gaba daya gidan bai mata dadi ba, daga ita sai Mariya, yau ko bakin ma da suka saba zuwa yau babu. Hayder kam tunda ya fita da safe har zuwa lokacin to 5 bai shigo ba. Dole haka hubby ta sallami Mariya ta tafi gida, don lokacin tafiyarta yayi.


Tana kwance a kan sallayarta data idar da sallar isha'i. Tunani ne fal zuciyarta na rayuwa, sai lokacin ta fara tunanin magan ganun Asiya. Tabbas gaskiya ta fada mata. Don tasan ada ba wacce tafita kin kishiya. Tunowa da kishinta kan Yusuf, wanda ko kallon mace wadda ba muharramarsa ba, bata kauna taga yayi, balle magana. Yan matansa na family da wanda ta sani, gaba daya bata Shiga shirginsu, bata basu fuskama balle su kawo mata wargi.

Tsaki taja, tunowa da yadda hayder ya dage maganar zuwa Egypt. Ita bawai kishin Nasrin takeyi ba, don tare ta gansu. Amma ta yaya don ya raina mata wayau, wadda bata san abinda  takeyi ba, ta rakashi zance. Ita a tarihima bata taba ganin inda mata take raka miji zance ba, ba kuma zaa fara a kanta ba.


Lokaci yayi da zata kama mutuncinta. Tabbas ko bata sonsa, mijinta ne, uban yayanta. Duk wadda zai auro, ko tanason ko bata so, dole ya shafeta, ya kumayi tasiri a rayuwarta data yaranta. Sai ma tafi tasiri a kanta sama da yadda zatayi akansa shida ya aurota. Ya zama wajibinta ta sa su a adduarta, in alkhairi ne shigowarta rayuwarsu Allah ya tabbatar in ba alkhairi Allah ya masu canji na alkhairi.

Cikinta ta shafo, da har lokacin ba alamar tasowarsa, sai tauri da wurin yayi. Wani dadi da natsuwa taji suna ratsata for the fist time.


Tunowa da yadda Yusuf ya kwallafa ransa don ganin kwansa, A duniya. Kana naka Allah na nashi.wane irin farin ciki zaiyi in da ta samu ciki dashi? Wane irin so da tattali zata gani? Ta tabbata ko sarauniyar England bazata fita samun kulawa da tattaliba.

Hakika soyayya wani jigone, a rayuwar aure, duk auren da babu soyayya, dole zaka samu akwai tawaya a tattare dashi. Duk jin dadi da kulawar dake cikinsa.

Yanzu take jin son cikin jikinta, koba komai ta samu abunda zai sata farin ciki, da debe kewar masoyinta. Allah yasa namiji zata Haifa, ta nemi alfarmar koda hayder beyi niyya ba, yasa mata sunan masoyinta, balle a yadda shakuwar dake tsakaninsu ta San zai yi wuya ya kasa sa sunan."


Kuka sosai yazo mata,. Bataji shigowarsa ba, sai kamshin turarensa. A hankali ya tako zuwa inda take kwance saman daddumar sallah tana kuka, don gaba daya zuciyarta ta karye. Zama yayi kan lallausan carpet din dakin, tare da daddagota, ya daurata a kan cinyarsa, yana tare da rungumota jikinsa. Kara shigewa jikinsa tayi. A hankali ya dinga lallashinta, cike dajin tausayinta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana lafe a jikinsa.


Sai da ya tabbatar ta samu natsuwa tukun.

" are u OK." Ya fada cike da kulawa. Kai ta kada masa.


Dagata yayi suka shiga toilet. Dayake shigowarsa kenan yaji zuciyarsa ta kasa natsuwa, yayi dakinta, sabanin da da bedroom dinsa direct yake wucewa. A tare sukayi wanka, shiya taimaka mata ta shirya cikin kayan baccinta, masu kyau da laushi. Dakinsa ya wuce daure da towel dinta don ya shirya.


Kitchen ya nufa don samawa cikinsa wani Abu don yunwa yakeji. Da yake bata cika ajiye masa abincin dare ba, saboda baya dawowa dawuri, in ma ya dawo baya bin takan abinci. Sau da yawa a main house yake cin abincin darensa, kafin ya wuce daukan karatu.


Dakinta ya nufa da trey dinsa. Tana kwance a kan bed, still fuskarta akwai damuwa, da rashin walwala.


Kujera ya jawo ya daura trey din a kai, ya zauna kusa da ita.


chicken salad, sai natural fruits juice, Kallonta yayi, da yanayin data kasa fassarashi. Dagota yayi, ta zauna sosai, salad din ya diba, yakai bakinta. Kauda kanta tayi, tare da kada masa kai.


Murmushin gefen baki yayi " ki ci, basai kin biya ba, tunda da kaina na baki."


Kada kai tayi " na koshi." Ta fada


" na dauka tsoro kikeji, kar ince sai kin biyani." Ya fada still da murmushi a fuskarsa.


" da can ma da naci ban biya ba, balle yanzu!! In ina so ci zanyi, ba yadda ka iya dani." Ta fada tana gyara kwanciyarta.


" kin dai manta, anma ba abincina da kikaci da baki biya ba." Ya fada yana cin salad din.


" sai ka tunamin ai!!"

" na school, kin biya da chocolate da sweet dinki. Food dinki dana friends dinki." Ya fada yana daga mata gira daya " right. ". Harararsa tayi. " ka biyani chocolate dina ai!! Tunda gasu nan a kitchen sai wanda nakeso in sha." Ta fada tana murmushi


" kifina da kika ci, da chips, suma kin biya With high price. " ya fada yana smacking


" ni ban biya ba! In don girkin da nake maka ne, bawai don in biyaka nakeyi ba malan." Ta fada cikin shagwabarta

" really!!!! Ke adole kin dauka bulus kika ci? I keep it they intentionally. Its a trap!" Ya fada


Tashi tayi ta zauna, Kallonsa take tana mamakin maganarsa. " why do u say that?" Ta fada tana rike habarta tare da daga masa gira duka biyu.


Sagensa ya shafa yana Kallonta, smacking yayi " Allah ne ya soki, da mage ta koromin ke!! Amma da trap dina ya kamaki?" Kada kai yayi tare da hadiye sauran maganar yana dari ya kasa -kasa.

Ido ta zaro cike da mamakin maganarsa. " hayder wane muguntar ka shirya min?" Ta fada tana tsareshi da ido.


Tabe baki yayi " ki dauka dama kazar da kowanne ango ke kaiwa amaryasa ranar da zai tare da ita, Kikaci. Koda mage bata koroki ba, nayi niyyar amsar hakkina a ranar, Your under my plan, Allah ya kwaceki. Kika kawo kanki cikin salama."


Rasa abinda zatace masa tayi, har ya gama ya fita da kayan binsatake da kallo.


Dakinsa ya wuce, ya tsaftace bakinsa tare da kara fesa turare, na baki dana jiki. Ya nufi dakinta. Har lokacin tana inda ya barta.


" please hayder me ka shirya yimin a ranar?" Ta fada


" forget about it," ya fada yana yarfe hannu daya.


"Amma kace ba kai ka turo min mage ba?"

" yes!"" Ya fada yana kallon kwayar idonta.


" ki gode ma Allah magen taimakonki tayi." Ya fada yana kwanciya kusa da ita. Hannu yasa zai rungumota ta bige hannun.


" uchh!!! " ya fada yana yarfe hannu. " don't u dare touch me, again." Ta fada cikin fushi.


" OK." Ya fada yana smacking tare da gyara kwanciyarsa sosai, kanshi na kallon sama, hannayensa duka biyu a hade kansa na tsakiyarsu.


Kallonsa tayi, tana jin kamar ta mari fuskarsa, saboda haushin murmushi rainin hankalin dake kan fuskarsa. Kwanciya tayi ta juya masa baya. "Amma kinsan ba kyau juyawa miji baya ko?" Ya fada in husky voice banza tayi dashi.


Tafiyar tsutsa ya fara mata a bayan. Hannunta tasa ta buge hannun again.


" gobe flight din  rana zamubi ki tabbatar kin shirya kafin 11, don ta abuja zamubi.


" sau nawa zan gaya maka, bazan jeba."


" yes u tell me. But look!!! Bana son gardama do as i say." Ya fada in high tone.


Shiru tayi, tana jin hawaye na kara cika mata idonta.


" kar dai maganar tafiyan ce ta saki kuka dazu?" Ya fada still in high tone


"Na tuno da masoyina ne, mai son farin cikina." Ta fada cike da takaici.


" good for u!! Amma ki Sani kin aikata haram, da aurenki, kike tunani fast love life Dinki?" Ya fada in his husky voice


" har kanada bakin da zaka fadi haka? Kai yanzu abinda kake shirinyi, a ina ka taba ganin anyi haka? Ina matarka ka rasa wanda zai rakaka neman aure sai ni? A ina ka taba jin anyi haka?" Ta fada still tana kallon gefe, ba tare data juyo ba.


" its not a big deal!! Zaa fara a kanmu."


" sai ka nemo Janeway ka jani ai!!!" Ta fada


" no need for that, da kafarki biyu zamu tafi. A u jealous of her ? "


" never." Ta fada


"U love me, bakya son ganina da wata, zuciyarki zata buga, bazata iya dauka ba. Is that your reason?" Juyowa tayi tana harararsa " Allah ya kiyaye, in tsaya ina kishinka! Kawai I don't want to go with u."


Tabe baki yayi, yana Kallonta. Murmushi ne ya kufce masa ganin yadda ta daure fuska, wai ita ranta ya baci.


" just sleep! I don't want your trouble, bayan ina cikin farin cikin ganin sweet heart tomorrow. "


Ya fada yana jawota jikinsa, tare da lushe idonsa. Kokari take ta kwace daga jikinsa ta kasa, dole ta hakura. Hannunsa na kan cikinta yana shafawa a hankali, har bacci yayi awan gaba dasu.

             *********************


Duk yadda hubby taso kaucewa binsa Egypt abin ya ki yiyuwa. Hayder akwai naci da tsayawa kan maganarsa. Dole tana ji tana gani suka nufi Abuja daga nan jirginsu ya daga zuwa Egypt. Su mommy Hauwa sai a waya ta musu sallama, don daga gidan Hajiya direct suka wuce abuja.


Da mamakin hubby tunda suka isa Egypt, yana tare da ita, in basa room dinsu a hotel din da suka sauka, to sun fita ganin wuraren tarihine, ko shopping. Shiru shiru taji ya mata maganar zuwa wurin nasrin taji shiru. Har ta kasa yin shiru, ta tambayeshi.


Bai ce mata komai ba, in banda murmushi da yayi mata, ya share zancen


Iya murzuwa hubby ta murzu a wurin hayder cikin kwanaki 14 da sukayi. In ka gansu gwanin shaawa baka taba cewa ba soyayya a tsakaninsu. Don wani kulawa da tattali suke ba juna na musamman.

Satinsu biyu suka tattaro zuwa kasa Nigeria, kowa yabar gida - gida ta barshi. A dade anayi sai naija...........

Sai karfe 4:45pm suka iso international airport Abuja. Kara marai raicewa hubby tayi ma hayder. Tun a jirgi take lallabashi ya bari su kwana a abuja, Tana son ziyarar Aisha da Ummul khair. Bai ce mata komai ba. ashir ne yazo ya dauke su.

Direct gidansu Alhaji Jamil suka wuce dake gwarampa, Gidane madai daici mai kyau da tsari. A second falo suka sami Hajiya maryam zune tana kallon zee world.+


Cikin fara'a ta fara musu sannu da zuwa 

Cike da girmamawa suka gaisheta. Kusa da ita ta nunawa hubby ta zauna. Hajiya Maryam mata ce, wadda ilmin zamani, da gayu ya ratsa. Bata Faye son hayaniya ba, shi yasa yawancin dangi ma basu damu da zuwa gidanta ba, in ba da wani dalili mai karfi ba. Dadin dadawa yaranta duk mazane, ko wanne yana wurin aikinsa, sai ashir da suka gama dasu hayder, da karaminsu Abdul alim, wanda shima yake shirin dawowa daga Malaysia, inda ya kammala nashi karatun. Kullun gidan shiru, sai masu aiki, in Hajiya Maryam ta tafi aiki shima Alhaji Jamil ya fita, sai yamma sosai suke dawowa gidan.


Yauma saa sukaci, ta tashi aiki da wuri. Table tasa aka shirya musu. Gaba daya hubby ta kasa sakewa don dama can bawai ta saba da ita bane sosai. Sai ta iya cewa ma baifi sau 3 zuwa 4 ta taba takowa gidan ba.

Sun gama cin abincin Hajiya maryam taja hubby zuwa dakinta don ta huta. Hayder ya fita da ashir.


Kwanciya hubby tayi a luntsimemen gadon Hajiya Maryam. Ga fruit da Hajiyan tasa mai akinta ta yankowa hubby. Wayarta ta janyo ta fara neman number din Aisha.  " mai ciki, wallahi bani son sunan nan." Aisha ta fada tana dariya bayan ta daga wayar. Tsaki hubby tayi " Allah ya shiryeki."

" yan honey moon an dawo kenan?" Ta fada still tana dariya


" shi kenan, tunda abin naki iskanci ne sai anjima." Hubby ta fada tana kwafa


Da sauri Aisha tace " afwan!! Amaryar agric chicken. " kashe kiran hubby tayi tana tsaki.

Kwanciya ta gyara, tana jin Aisha nata kiranta taki dauka. Sai ma wayar data sa a salent.

Text Aisha ta tura mata tana bata hakuri.

Sai magrib Hajiya Maryam ta shigo dinta tasheta tayi sallah da mamakinta idon hubby biyu, har ta dauro alwala. " na dauka baki iya tashi ba." Ta fada tana murmushi


" ban ma yi baccin ba, nadai kwanta ne kawai." Hubby ta fada cike dajin nauyinta.


" hakane, wani baya iya bacci bayan la'asar." Ta fada tana wucewa toilet din dake dakinta.


Sai 7 Alhaji Jamil ya shigo gidan. Yaji dadin ganinsu hayder. Sun dade tare kafin Hajiya ta rako hubby ta gaisheshi.


Karfe 10 dai dai, ashir ya shigo ya shaidawa hubby ta fito su tafi. Ba haka Hajiya Maryam taso ba, don haka kurun taji hubby na burgeta. amma kasan cewar gobe ranar aiki ne, dole ta fita gida tun 7, yasa ta hakura. Har mota suka rako hubby.


             ********************


Shi yake driving, hubby na zaune a gefensa tana kallon gari. Duk da darene, bai hanaka kallon tsaruwar garin.


Hilton taga sun nufa, Kallonsa tayi, taga gaba daya hankalinsa na kan get man dake scanning duk motar da zata shiga.


A hankali ta zuro kafarta, tana karewa wurin kallo. Wannan ne karonta na biyu data kwana a cikin hotel din.


Sun shigo harabar  cikin hotel din, suka  wuce  reception don karbar key.

Kusan a Jere suka shigo, in ka gansu zasu matukar burgeka, da daukar hankalinka. Dayawa basa iya musu kallo daya, sai an sake juyowa an kallesu.

Ganin hakan yasa jikin hubby sanyi, hayder ya lura da hakan, hannunsa ya sa ya riko nata hannun cikin nasa. Kallonta yayi, yana kashe mata ido daya.


Kauda kanta tayi gefe. Sun karbi key din dakinsu dake plow na 5, juyowar da zasuyi taji an ce" wa nake gani kamar Habiba? " da sauri suka kai idonsu kan mai maganar. Doctor Hashim ne, tsaye sanye cikin cot bakake, da farin shirt. Cike da kunya  hubby ta gaisheshi, koba komai akwai zumunci sosai a tsakaninsu. Amma da gaske taji kunyar haduwa dashi.


Hannu ya mikawa hayder cike da faraa. Shima hannun ya mika masa. Ba yabo ba fallasa suka gaisa. Don hayder ya sanshi, tun suna zuwa shida junaid, ya kuma samu labarin zamowa daya daga cikin maneman auren hubby.


" yaushe kuka shigo garin?" Ya tambaya yana kallon hubby, mamakin kyau da cikan data kara.  Wanda ya kara famo masa wani ciwo dake kasan zuciyarsa. Har lokacin bai gama warwarewa daga zafin rashin samunta a rayuwarsa ba.


" dazu." Ta fada a takaice. Su mommy ya tambayeta ta amsa shi cike dajin nauyinsa.


Ganin yana son Jan hirar da tsawo, yasa hayder cikin husky voice dinsa " ya ce nice to met u! Let go." Ya ja hannun hubby suka yi gaba. Da ido doctor Hashim ya bisu. In ya cire son zuciya tabbas bai taba ganin couples din da suka dace, suka burgeshi irin su hubby ba. Gashi da gani harda rabo, tabbas Matar mutun kabarinsa, wani baya haihuwar dan wani. Fatan alkhairi ya musu a zuciyarsa ya nufi wurin da motarsa take, dama meeting ne ya kawoshi wurin.


Da kallo hubby ta bi hayder, cike da mamakinta. ta kasa karanta yanayin dake kan fuskarsa har suka hau lifter zuwa 6 plow. Gingina yayi da jikin lifer din, hannunsa duka biyu a rungume a kirjinsa, ya harde kafafunsa. Gira ya daga mata, ganin yadda take ta binsa da kallo. " kallon fah? Ko don na hanaki hira da bazawarinki.?" Ya fada in husky voice dinsa


Baki ta sake cike da mamakin kalamansa. Kauda kanta tayi " kasan dai ko ba komai his like brother to me."


Tabe baki yayi " I  have no idea, yadda akayi ya zama brother Dinki?"

Ya fada yana smacking


Harararsa tayi " dama ya za'ayi ka sani." Ta fada tana kallonsa kasa- kasa.


" kalan dangi." Ya fada in Hausa. Da sauri ta dago tana kallonsa cikin mamaki, har yaushe yaji hausan da yasan kalan dangi?


Gira ya daga mata " ko ba haka bane?"


Rasa me zata ce masa tayi. Taja bakinta tayi shiru.


" this is the fist and last time da zaki tsaya kina washewa zawarawanki baki a gabana, in kuma kika sake a wurin zan rugurguza bakinki., sannan in hada masa jini da magina" Ya fada in warning tone. Kanta ta nuna da yatsanta manuni. " ni zaka ruguzawa bakin?"  Hannunsa daya yasa yana Sosa sumarsa da key din hannunsa. Idonsa na kanta, wanda ba komai sai kallon gargadi. " ki maimaita ki gani, shi kuma banza sai wani washe baki yake yana kare miki kallo." Ya fada yana kwafa.


Cike da kaduwa hubby ke binsa da kallo. " are u jealous? " ta fada muryarta tana rawa


Key din yasa yana Sosa kunnensa. " u are my property, so be care full."

" I'm not your property! naga ni a gabana ma kiran budurwarka kake yi, amma ban taba cewa komai ba why me." Ta fada cikin sanyin jiki


Smacking yayi, tare da gyara tsawuyarsa. " banda ke ina da space din 3, amma ke u are only belong to me, so don't compared yourself with me. Duk abunda na mallaka, to nawa ne kawai, bana sharing dinsa da kowa, koda ban son abun. Abunda kika sani ne."  Bude baki tayi ta bashi amsa dai dai dashi. Lifter din ya tsaya tare da budewa.


Hannunta ya kamo cikin nasa suka fito, batada zabin da yafi ta bishi. Don gaba daya magan ganunsa sun sata a wani tunani daban.


Dakin ya burgeta, ya kayatu matuka, gashi ta samu kayanta already ya shigo dasu. Hannunta ta zame daga nashi, ta wuce kofar da take tunanin toilet ne. Komai tsaf sai kamshin air freshener mai dadi. Ruwa ta tara a baf din, sannan ta fara cire kayanta. Don jin jikinta take har yana wani danko danko, rabonta da wanka tun da safiyar ranar. Wanda da a gidane da tayi na uku, zuwa hudu, zuwa yanzu.


Bobble soap mai matukar kamshi ta zuba, bayan ruwan ya mata dai dai, yadda take so. Shiga tayi ta zauna. Lokaci daya ta sauke ajiyar zuciya.


She is not his shoes da in wani yasa, sai dai yayi kyauta dashi, ko chocolate da zaka gutsurar masa, ya bar maka, ko wani abun anfaninsa da muddin wani ya taba, ko yayi anfani dashi ko sau daya ne, ya hakura dashi kenan. Kamar yadda in ta ci masa abinci, kota rage sai dai ya zubar, ko abokansa sukarasa sauran. After all ita kanta a second yasa meta, kuma yayi hakurin zama da ita. To me maganarsa ke nufi. Kar dai kishinta ya fara? Kai no ba haka bane! Don bata ga wani alamar hakan ba.  "Kawai fitina ce da neman magana." Ways zuciyar ta fada, duk da bata amince da hakan ba.


Fuskarta da ya shafa yasa tai saurin bude idonta." Tunanin me kikeyi?" Ya fada yana zagaye fuskar da yatsunsa biyu. Shiru ta masa, ta dau sabulu ta fara wankanta.


" kar dai maganar dazu ce, bata wuce ba." Ya fada yana zaune yana Kallonta.


Tabe baki tayi ta ci gaba da abinda takeyi.


" uhimm!!!! Yau da Nasrin ne, hakan ta faru? Da kinga yadda zamu kwashe. Don gaskiya zan gaya miki ina da matukar kishi, fiye da yadda baki tsammani." Ya fada yana shafa sajensa.


" amma kasan yadda Muke dashi ko?"


Tabe baki yayi " sanin hakan shi yasa na fada miki, don ki kiyaye."


" sai ka bari in ta shigo, ka tsara mata, amma ni baka isa ka hanani gaisawa da abokan arziki ba."


Murmushi yayi mai sauti. " Allah ya baki saa, karki fasa, amma duk abinda ya biyo baya ki kuka da kanki."


Fitowa take kokarin yi, don ta kammala, Rike hannunta yayi, " not so fast." 

             *******************


Shirye shirye sun kammala na bikin su Abdul Karim. Saura sati biyu ya rage, wanda yayi dai dai da wata daya, daya wuce da akayi bikin jafar mai bin hubby.


Cikin hubby ya shiga wata na biyar, yanzu kam kallo daya zaka mata kasan tana dauke dashi, saboda dan turowar da yayi, ya kara mata kyau da cika.


Kulawa sosai take samu daga hayder da Hajiya. Haka mommy ma baa barta a baya ba. Gwaggo kusan kullun sai ta kira hubby don jin lafiyarta. Tun bikin jafar da tasan da ciki a jikin hubby. Murna baa magana, don ranar har rawa saida gwaggo ta taka. Har aka gama biki hubby na takure, don hankalin kowa kusan kanta ya dawo.1


               ********************

Kayan dinkin data amso ta baje akan gadonta tana dubawa. Cike da yaba dinkunan a ranta. Sunyi kyau, kuma yayi dai dai da abunda tace ya mata.


Hayder ne ya shigo, sanye cikin black jeans da light ash T-shirt mai gajeren hannu. Hannunsa rike da gasashshiyar masara da aka shafeta da butter.

Miyau hubby ta hadiye, idonta a kan masarar ko kaftawa batayi, ayyana dadin da zatayi, take a ranta. Gira ya daga mata, tare da kai masarar bakinsa, ya lumshe ido. Yana taunawa a hankali.


Kasa hakuri hubby tayi, ta nufoshi gadan gadan. Don yanzu wani dan banzan kwadayi ne, ya tasata a gaba. Sau da yawa in ta rasa abin ci haka zata kwaba yaji da magi tayi ta lasa. Duk wani kayan kwalama yanzu tana wurin.


Daga masarar yayi sama, dage ta fara don ta kamo hannun ta kasa. Dariya yayi yana daura hannunsa a tsakiyar kanta. " da wane tsawon zaki kamo." Shagwabe fuska tayi tana tura baki.

Still tana kokarin kamo hannun, ta kasa. " please bani mana!! Miyauna ya gama tsinkewa." Kara daga hannun yayi sama.  Tsalle tayi tana son kamo hannun. Da sauri ya tareta, tare da mika mata masarar yana zabga mata harara. " karki jamin asara."


Tura baki ta danyi, tare da kai masarar bakinta, bakin gadonta ta koma tana ci tana lumshe ido, da wani sauti na nuna dadin da masarar ke mata.


Smacking yayi, ya fara daga dunkunan dake kan gadon. " waannan fah!" Kallon material din daya daga tayi " dunkunan biki ne." Tabe baki yayi, yana ci gaba da dagawa daya bayan daya.


" baa saminba, amma zaa sa aje gidan biki?" Ya fada in husky voice


Kallon kayan tayi, ta kalleshi. " wane kwalliya ne banayi a gidan nan? Wan nan wani yajika zai dauka da gaske kake!" Ta fada cikin sanyin muryarta


Girarsa yadan Sosa kadan kafin ya kalleta. " ban yadda kisa suba gaskiya." Da mamaki take kallonsa. Da kyar ta hada kalmomin bakinta " yaushe ka fara zabamin kayan da xansa in fita, da wanda bazan saba? I don't understand u, kwana biyun nanfa!."


" do as I say." Ya fada in high tone


Baki bude take kallonsa cike da mamaki da kaduwa.......in kikayi wasa, bikin ma gaba daya sai in hanaki zuwa, muga yadda zakiyi." Ya fada yana tattare kayan.+


Shiru tayi, don tasan karamin aikinsa ne. " to yanzu wane kaya kake so in sa don Allah?" Ta fada cike da shagwaba


Tabe baki yayi. " meye ma, sunan wa'annan zunbula- zunbulan rigun nan naku?" Ya tambaya

" ban son suba." Ta fada tana tura baki


" fine. Baki kara sa kaya masu shelf ki fita gidan nan. Da naga ai su kike saw a, amma da yake yanzu kin raina ni, zaki dinga samin wadan nan yan iskan kayan, daya kamata ace ni aka sa mawa, in gani in more, ki samu lada. Amma zaki sa ki fita, duk inda kika wuce ana binki da kallo ko?" Ya fada in husky voice dinsa


" Allah ka fara takura min." Hubby ta fada cikin sanyin muryarta


" au takurawa ne ma? Daga fadar gaskiya? To aje na takura mikin kar a kara saminsu a fita. In sababbi kike so, gobe zan kaiki ki zaba, muje kibada Dinki ko express ne."


" aa, na gode! Kayan can ma ni ko tabasu ban yiba, zan dauka a ciki." Ta fada tana nuna masa akwatunan ta na lefe.


" na dauka ai taru kike min? Kinga na huta in lokacin yayi, sai dai kawai a dauka a kai." Ya fada yana fadawa saman bed din.


Dariya hubby tayi, cikin dariya tace " amma dai taci baya wallahi."

Smacking yayi tare da daura kansa a kan duka hannunsa biyu. Yana kallon saman dakin.


Kallonsa tayi still tana dariya " ka rasa mai zaka kai mata sai old modern, old fashion? "


" in da so, ai bazata damu da wannan ba." Ya fada Idonsa a rufe still fuskarsa dauke da smirk.


Tabe baki hubby tayi, ta ci gaba da cin masararta.

Har tayi brush ta dawo yana nan inda ta barshi. A gogo ta kalla already 3oclock.

Har takai Kofa zata fita, taji miryarsa " kin min assignment dina?" Dawowa tayi, shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka. " sai fa anjima zanyi."


Still Idonsa a rufe " good for u!! Yau zan dawo da wuri, in baki yiba, bada biro zanyi punishment ba."


Harararsa hubby tayi ba karamin takurata yake yiba, kan karatun da yake koya mata. Da farko ta dauka abin zai shiririce kamar yadda sukeyi da Yusuf. Amma ina. In lokacin karatu yayi, hayder zama yake  tamkar zaki, ba ko digon rahama a tare dashi. Tanayin wani shirme ya fara bubbuga kanta da biron hannunsa kenan yana " zero head " abinda tafi tsana kenan ya kirata da " zero head. " dole yanzu take maida hankali. Kuma alhamdulillah tana ganewa sosai. Don ya lura she is slow learned. So yana binta a hankali komai dalla -dallah yanda zata fi fahimta. Physics, chemistry, biology, mathematics. Ta fannin Islam yafi bada karfi wurin koya mata, tajweed, fighu, hadith's. Suna break fast zai sa ta dauko takardunta,a  kowacce rana subject biyu  Ba yadda ta iya. A cewarta " karatu by fuse!"


Suna zaune a falonta na kasa, ita da Mariya. Suna kallon TV arewa 24. Ya sakko daga sama, like always gudu- gudu, sauri- sauri. Yana sanye da riga da wando na farar shadda. Dinkin half jamfa, yasha surfani new design na farin zare.


" dogo dan Hajiya"  ta fada a kasan ranta tana dauke idonta daga kallonsa. Harga Allah ya mata kyau, da kwarjini a idonta. Shi kanshi kamar yasan fararen kaya na masa masifar kyau, yasa mafi yawan traditional autfit dinsa farare ne.


Gaba daya wurin ya dauki kamshin turarensa duk da kamshin turaren wutan da ya wadaci gidan.


Da sauri, Mariya ta gaisheshi ta fita. Don tun ranar daya gargadeta a kan aike take tsananin tsoronsa.

Kiss ya manna mata a goshi, da saman lips dinta. Tare da zura hannunsa yana shafo dan matashin cikinta. " I'm going out." Ya fada bayan ya janye daga gareta.


" a dawo lafiya." Ta fada tana kare masa kallo ba tare da ita kanta ta shirya hakan ba. Gira ya daga mata tare da smirk akan fuskarsa. " na burgekine?" Ya fada in husky voice


Tabe baki tayi tare da dauke kanta zuwa kallon TV " kayan sunyi kyau." Ta fada da daddadar muryarta


Lumshe ido yayi. " thanks, kice in ta ganni rudewa zatayi gaba daya." Ya fada in husky voice dinsa yana smirk


" bakai nace kayi kyan ba! Kayan nace sunyi kyau." Ta fada tana tabe baki


" nasan ita dani da kayan duka zamu burgeta." Ya fada yana kokarin fita, har yakai Kofa ya juyo, ido hudu sukayi tayi saurin dauke idonta tana dan tura baki.


" ba matsala dai ko?" Ya tambaya


" ka taho min da kullisuwa, kwakumeti da tuwon madara!!"

Gira daya ya daga mata, tare da mata alama da hannu " ina zan samo miki duk waannan. "


" a Habib yeghout."


Kada kai yayi ya fita, yana jin jina ciye -ciyen data tsura yanzu. Shi Allah dai yasa ba zasu cutar masa da beby din saba. Duk da Hajiya tace duk abin da take jin ci, ya barta taci, shi hankalinsa bai kwanta ba. Musamman ranar daya dawo ya sameta tana cin wani abu kamar kasa, 'unxu, ko uzuu" shi yama manta sunan. Haka ya kwasa yayi wurin doctor sabir dashi, don ya tabbatar bazai cutar dasuba. Sai da ya tabbatar masa zata iya sha amma bada yawa ba, Tukun hankalinsa ya kwanta.


                ****************


Tana jin karar bike dinsa, gabanta ya fadi, sai lokacin ta tuno batayi masa assignment dinsa ba.

Wata dabara ce ta fado mata, murmushi tayi tare da furta " yes!!" A saman labbanta. Taji dadi da taji ya wuce dakinsa, hakan zai bata damar gudanar da plan din da take tunanin zai kubutar da ita.


Jikinsa sanye da pajamas na kampanin NICK light blue. Ya shigo daga bakin kofar bedroom din ya ce mata "ki dauko takardunki ki sameni a falo." Cikin muryar da ba wargi balle wasa a cikinta, ya juya ya fita.


Kirjinta ta dafe, tare da sauke a jiyar zuciya. Juriya ta aro ta saka a zuciyarta. Hijab din jikinta ta cire ta ninke, ta mai dashi maajiyarsa. Tana adduar Allah ya dorata a kanshi. Mirror taje tana kara kallon kanta. Sanye take da kayan bacci na kampanin ARAKS SHEBY, top ne da boxer short, kayan silk ne, pusher pink color, sunyi mata matukar kyau, komai ya fito masha Allah, musamman dan matashin cikinta, da rabin  kirjinta dake waje, ko Brazee babu suna tsaye kam kamar sa tsone maka ido, sun kara cika abun baa cewa komai.


Humranta ta kara shashshafawa tare da jefa alewar chupa chups, mai tsinke a bakinta. Murmushi tayi, tare da daukar littatafan ta nufi falonta dake sama, cikin takun daukar hankali.


Hannunsa rike da remote yana rage volume na TV, Kamshinta ya fara masa sallama. " innalillahi wa inna ilaihir rajiun." Ya fada a saman labbansa. Kasa dauke Idonsa yayi a kanta, hakika ta tafi dashi, musamman takunta, da yadda take tsotson sweet din. Shi bai taba ganin wadda ciki ya mata kyau ba, kamar hubby, idonsa ya sauke a kan kirjinta da suke kallonsa kamar sa shiga idonsa, wani shock tare  da wani filling da ya fara bin jinin jikinsa.


Ganin irin kallon da yake mata, ta yi murmushin don tarkonta da take tunanin it work. A hankali take takowa tana rausaya kamar wata reshe, lokacin damuna, komai sai juyawa yake in Beautiful  and sexy way. Books din ta ajiye kan center table.


Hannunsa ta kamo, wanda duk kansu sai da sukaji waji shock daya ratsa jikinsu. Kirjinta ta kai kan nasa, duk da yafita tsayi sosai, haka tayi dage, ta manna masa kirjinta a nashi, hannayenta duka biyu ta sarkafo wuyansa dashi, hancinsu ta hada tana sauke numfashi a hankali.


Wani wawan ajiyar zuciya hayder ya sauke. Jikinsa da zuciyarsa sun fara rawa, tare da daukar sakon ninta. Kamar wanda ya farka daga bacci, lokacin da take kokarin hada bakinta da nashi. Da sauri ya janyeta a jikinsa, yana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya.


Fuska ya daure. Da kallo ta bishi, ganin yadda ya hade rai jikinta yayi sanyi an ma she never give up. Kara matsowa tayi. Da sauri ya dakatar da ita " ware is the assignment? " shagwabe fuska tayi, tare da fadawa jikinsa. Hannunta daya tasa tana shafo faffadan kirjinsa.


Hannunta ya rike, tare da janta zuwa kan kujera ya zaunar da ita. " i say ware is my assignment?"


Tura baki tayi, tana mar mar da ido, kamar zatayi kuka.


Kallon daya zabga mata yasa ta sungumi book din ta mika masa jikinta na rawa.


Amsa yayi, ya zauna a kujerar kusa da ita. Don tsaf ya gano so take tayi seduce dinsa, a manta da maganar assignment, But he isn't give up, in ya bari tayi winning ta gaba daya karatun shirme zai koma, don ta samu hanyar zillewa kenan.


Cikin daure fuska ya kalleta yana daga book din.  " meya hanaki yi, bayan koda zan fita sai da na tuna miki.?" Tura baki tayi, a shagwabe tana kallon book din " sorry!! Dama dama!!" Ta rasa excuse din da zata bayar sai ta hau sosa hanta. Data sakeshi har kan kirjinta.


Smirking yayi, ya mika mata book din " oya!!! Stat it right now"


Kamar zatayi kuka ta kalleshi, da niyyar ta bashi hakuri, sai gobe tayi. Hararar daya zabga mata yasa jikinta  rawa ta karba, Tana tura baki.


Ledar din kusa dashi ya dauko, kwakumeti irin mulmulallun nan, da tuwan madara, gullisuwa, eloka. A cikin transparent robber, sun kai 20 ya fito dasu ya jera mata a kan center table. Murmushi tayi cike da jin dadi tana hadiyar yawu. Da sauri takai hannu zata dau eloka, ya rike hannun. " please. " ta fada


Kada kai yayi, da tabe baki. Book dinta ya nuna mata, ya gyara zamansa sosai. Yana smirk, ganin yadda take kallon robobin kamar mayun waciyar zakanya.


Kamar zatayi kuka ta kalleshi " calculator dina, yana daki, inje in dauko?"


Wayarsa ya danna ya fito mata da calculator din, ya mika mata.


Yana kallon yadda lokaci zuwa lokaci take kallon robobin, tare da satar kallonsa. Wani lokacin kuma takai hannu zata dauka, ya buge hannun da pen. A haka har ta gama.


Mika masa tayi, taja robar eloka, wanda shi yafi komai daukar idonta a lokacin. Tunowa yayi da yadda sukayi da yaron shagon Habib yeghout. Sai da ya gaya masa da abunda akeyi, daga wurin gidan doctor sabir ya wuce, don ranar bashi da duty, sai da ya tabbatar masa ba matsala tukun ya nufo gida, doctor sabir na masa dariya.


Ba laifi tayi kokari. Idonsa yakai kanta, har ta ajiye eloka ta dauki gwakumeti. Kallonta kawai ya tsaya yanayi. Cike da tausayawa.


Jingina tayi da jikin kujerar tana maida numfashi a hankali. " thanks. " ta fada tana murmushi


Shima murmushin yayi. Ya Mike, hannunsa ya mika mata, ta kama ya dagata. Rungume ta yayi a jikinsa suka sauke ajiyar zuciya a tare.


" u want to seduce me right? " ya rada mata a kunne in his husky voice ya dagata bridal style zuwa bedroom dinsa. " bafa seducing dinka zan yiba" ta fada a shagwabe


" really. " ya fada yana shinshina wuyanta. Yau hubby ta tsokano mayun wacin zaki. Dama ya lafiyar giwa? Ranar kam ta gwammace kidi da karatu, a hannun hayder.


             ***************"*****

Biki ya rage 5 days. Ranar hubby ta shirya zuwa main house. Su Aisha da sauran yan matan duk sun iso.


Tana sawo kan motarta, cikin gidan, Anty samira na sawo nata hancin motar.............

Inuwa ta samu ta parka motarta. Sanye take cikin wani dakakken less mai matukar kyau da tsada. White and pink, doguwar riga, wadda ta bude sosai, sai kashka pink mai adon duwatsu masu daukar ido. Takalmi da jakarta pink. Batayi wani make up ba, in banda pawder, sai kwalli, da wetlips. Tayi matukar kyau, ga kanshi na musamman na tashi a jikinta.+


A hankali ta ziro kafarta, ta fito, dai dai lokacin da Anty samira ma ke kokarin fitowa. Kallon -kallo sukawa juna.


Dan murmushi hubby tayi " Anty samira ina wuni?" Ta fada cikin muryarta mai dadin sauraro.


" kina  lafiya." Anty samira ta fada ba yabo ba fallasa, tana karewa hubby kallo


Da murmushi akan fuskar hubby tace " alhamdulillah! Ya su ilham?"


" suna gida." Ta fada tana wucewa ciki.


Su Abdul Karim ne da abokansa suka fito daga parts din su Hajiya, dai dai lokacin ta tunkaro shiga. Matsawa tayi ta basu hanya. Tare da musu " Salamu alaikum." Dukansu idonsu a kanta. " waalaikumus salam." Wasu daga ciki suka amsa. Ganin ta samu hanya ta shige ciki, ba tare data kara furta komai ba.


" kai classy guy! Wannan ma kanwar ka ce." Daya ya fada bayan shigewar hubby yana kallon Abdul Karim


Ajiyar zuciya Abdul Karim ya sauke. Cike da takaici yace " ita ce yarinyar da nake baku labari, da zan aura, kafin wannan yar bakin cikin ta ruguza komai." Baki suka rike.


" Amma gaskiya an cuceka!! Zuki!!!" Daya ya fada yana jinjina rashin rabo irin na abokinsa.


Ka fadarsa dayan ya dafa. " sorry guy!! Tabbas kayi missing duk da dai ban ganta sosai ba, amma gaskiya ta gama hadewa karshe. Kaninka ya more mata wallahi."


Tsaki Abdul Karim yaja tare da wucewa part dinsu.


Suma binsa sukayi, suna jin jina lamarin.


Sai da ta shiga part din sauran matan gidan, sannan ta wuce part din Hajiya. Rungumeta Hajiya yayi cike da jin dadi. Bayan sun gaisa, tare da tambayar lafiyarta. Cike da jin nauyinta take amsa ta. Don tun bulowar cikin jikinta ta tsinci kanta dajin nauyi da kunyar Hajiya. A wurin Hajiya kam sayayyar hubby karuwa tayi akan ta da. Soyayyar autan Hajiya ya kara shafanta, da kuma soyayyar abinda ke cikinta. Ita kanta hubby har tunanin tsakanin Hajiya, gwaggo da hayder wayafi son cikin.

" su ummu sulaim fah!" Hubby ta tambaya


" suna falonsu, da munanan dasu, sun cikamin kunne na korasu can." Hajiya ta fada tana murmushi


Tashi hubby tayi,. Hajiya ta kalleta cike da kulawa. " ga mutuminki nan akan dinning, kici tukun kafin kije wurin waannan surutattun."


" to." Ta fada tana nufar dinning din.

Danwake ne, mai rai da lafiya. Ai tuni miyanta ya tsinke, cike dajin dadi, taja kujera ta zuba, yadda zai isheta, tare da lafta uban yaji. Tana ci tana Jan yaji, saboda azaban fadansa. Amma haka ta tada dan waken. Don tunda ta tashi, kunu kawai tasha, sai kwakumeti data nadawa cikinta.


Kallonta Hajiya keyi, cike dajin dadi. Wani farin ciki takeji a duk lokacin data ga hubby. ( Matar auta)


" kai jakar daki kafin ki fita." Hajiya ta fada. Dawowa tayi ta dau hand bag din takai bedroom din Hajiya kafin ta fice zuwa falon dasu ummu suke.


Fatar hubby daga part din Mmn Yusuf, innani ta kalli Maman Yusuf tare da rike haba " ikon Allah, kiga rabo!" Murmushi Mmn Yusuf tayi

" wallahi kuwa, gashi nan dai."


" yarinya anata kiranta juya, gashi daga yin aure Allah ya bata nata rabon, don wannan daga gani ba karamin ciki bane." Innani ta fada


" ikon Allah kenan. Don shi yakeba wanda yaso, ya hana wanda yaso. Mune mutane bama ganewa, irinsu tausayawa da jin kai da kyakyawan muamala ya kamata muyi musu, amma sai mu dinga anfani da wannan muna tozartasu da cin mutuncinsu. Alhali basu zasu ba Kansu ba." Daya Matar ta fada


" yarinya mai hakuri da juriya, wallahi kinyi rashin suruka, naji miki haushin rashin ta." Innani ta fada cikin takaici


" yo!! Haushin me zaki ji mata? Bayan ita ta zabi hakan da kanta. Kuskure kam tayishi sai zuwa gabama in ba Allah ya shige mata gaba ba, zata koka. In dai rafaatuce." In ji Matar


" shawara ce bata ji, data dauki shawarata da duk haka bata faruba. Ni nake zama kusa dasu, nasan halin kowa, rafaatu, ba kamar nafisa bace. Ita halinta daban da Nasu, gaba daya batayi, halin yayaba, haka bata dauko halin a'i ba. Gashi sun dau son duniya sun daura mata, sai abinda taga dama takeyi, ba Wanda ya isa ya taka mata burki. Kahlil kawai take dan shakka duk gidan, amma kika ce kinji kin gani, bakya laakari da yanayin aikin Abdul fatta, na tafiye tafiye, zaki dauko masa irin wannan mata, da ba natsuwa da kamun kai a tare da ita. Gashi gaba daya iyayen basa son laifinta. Dan uwanane, amma nasan akan yarsa zaku samu matsala."


Shiru Mmn Yusuf tayi tana jin jina maganar. Ajiyar zuciya ta sauke. " wallahi nayi nadama, batun yauba. Nasan nayi rashin suruka. Ni yanzu kunyartama nake ji. Ki duba yadda yanzu dukiya ta rufe idon al'umma, mata nawa ke fatan miji ya mutu suci gado? Mata nawa ke kashe mazan don suci gadonsu? Amma yarinyar nan duk abunda ta samu na gadon Yusuf, gaba daya ta tattara ta bayar aka gina masallaci dashi, sadakatul jariyya ga Yusuf. Harda kwala kwalanta ta hada, da kudin bai kai ba. Sai kunga masallacin, kato dashi, gashi fuskar jamaa. Ni da nake uwarda ta tsugunna ta haifeshi, nake tutiyar nafi kowa sonsa, ban taba wannan tunanin ba. Niko mai zan cewa wannan yarinya? Iyakar kauna da soyayya ta nunawa Yusuf, taso dana, be sake dani taso ba. Duk abinda na mata bata taba kullataba ba, bata taba canza girmamawar da take min ba. Basai kowa ya gayamin ba nasan nayi rashi, mai wuyar mayarwa. Gashi da bata da hakkinmu, Allah ya mata canji na alkhairi, bani na haifi hayder ba amma ni kaina nasan haider mutun ne, nagartacce samun irinsa sai an tona."


" yaro dan albarka, Allah dai ya masa albarka. " Innani ta fada


" amen!! Ai ni ba abinda zan ce ma yaran nan biyu, sai fatan alkhairi. Shekara biyu, ina fama da takaicin auren abida, amma kika daga dawowarshi, ya fuskanci halin da take ciki. Ya kasa zaune ya kasa tsaye, har saida ya tabbatar su Alhaji babba sun shiga maganar. Cikin yardar Allah gashi komai ya dai daita. Wai ni jiya mijin abida yazo har gidan nan gaisheni! Mitumin da ko kallon arziki bana samu a wurinsa, balle sauran yan uwanta." Mmn Yusuf ta fada cikin alhini


" shi yasa akace da da da dukiya, baa musu mugunta, don baka san mai anfanarka ba. Allah yasa mufi karfin zuciyarmu." Inji Matar


" me nake gani, kamar ciki a jikin yarinyar nan." Hajiya kaka ta tambaya tana kallon anty samira


Murmushi Anty Samira tayi " aikuwa dai gashi, har ya fito abinsa."


Baki Hajiya kaka ta rike " topahh!!! Iko sai Allah."


            

Yau hubby tasha tsiya da tsokana a wurin yan matan gidan. Gaba daya ba sauki, sai gudu dakin Hajiya tayi, ta kwanta.


                 ******************

Haka hidimomin biki sukayi ta tafiya cikin kwanciyar hankali. Wannan karon gaba daya Hajiya komawa gefe tayi, ta sa musu ido, sabanin da da take uwa tayi makarbiya. Biyu maxa suka kasu, wasu sukayi abuja daurin auren Abdul Karim, wasu kuma Niger na Abdul fatta, wanda ya kasan ce harda hayder cikin masu tafiya Niger.


Anyi biki lafiya an watse lafiya, kowa ya koma gidansa.


Hubby ta ci gaba da rainon cikinta cikin kulawa da tattalin miji dana iyayensu. Cikinta na wata 7 suka tafi Dubai ita da Hajiya da Ummul khair siyayyar haihuwa. Kwanansu 10 suka dawo.


Ta fannin karatunta, har lokacin sunayi da hayder, kuma alhamdulillah tana maida hankali yadda ya kamata.


Haka ta bangaren kasuwancinsu hayder, sun kara bunkasa, yanzu duk wani babban dan kasuwa yasan da zamansu. Don suma yanzu online business sosai sukeyi, kamar jumia, a Nigeria da aliexpress China. Sun inganta nasu fiye da hakan, don in kayi oder din kaya cikin 1week, zaka samu a ko ina kake a duniya. Kuma kaya masu inganci da nagarta. A gefe daya kuma suna ci gaba da zurfafa ilminsu na software development, shida junaid shima ba karamin alkhairi suke samu daga gareshiba.

Kampanoni da masana antu da yawa da suke basu contract na kirkirar musu application dazai saukaka musu ayyukansu na yau da kullun.


Hajiya taso Kwarai hubby ta koma gidanta, tunda cikinta ya shiga cikin wata na tara. Amma hayder yaki, akan a bari ta haihu tukun. Dole gwaggo tazo tana zama dasu, hakan yama hubby da hayder dadi.


Duk kansu yanzu suna jin juna a ransu. Tunanin hayder taya zai iya rayuwa a cikin gidan shi daya?, ba hubby. Ya saba yanzu da kasancewarta tare dashi. Baya iya bacci sai ya jita a jikinsa, hannunsa na shafar ajiyarshi.


Yau tun safe hubby ke fama da ciwon baya, sai mararta dake kullewa lokaci zuwa lokaci. Daurewa tayi tayi, ba tare data iya furtawa kowa ba. Gwaggo dai sai binta da kallo take, in ta tambayeta tace ba komai. Kai kawai gwaggo kan kada, don ta lura kamar nakuda ta fara. " zaki maganu ne yarinya."  Gwaggo ta fada, lokacin da hubby ta shige kitchen da niyyar dafa black tea, ko daurewar marar zai saketa.


Sakkowar hayder ya samu gwaggo zaune a falo, zama yayi kusa da ita " matar ya akayi ne? Ke kadai!?" Murmushi tayi tana tabe baki. " ina ga takwara fa! Nakuda ta fara."


Ido ya zaro " tana inah!" Kitchen ta nuna masa da yatsa


" Ku tashi mu tafi hospital, bai kamata a zauna a gida." Ya fada yana nufan kitchen din


Dafe da baya ya ganta, tana faman cije lips. Da sauri ya iso tare da rungumota jikinsa.


Numfashi take saukewa a hankali. " bayana!! " ta fada cikin wahalalliyar murya. Kashe gas din yayi. Cak ya daukota zuwa falon ya ajiyeta ya haura sama da sauri.


Already gwaggo ta fito da akwatin da suka shirya na zuwa haihuwa. Hijab dinta ya dauko mata da key din mota.


Daukarta yayi zuwa mota, malan idi ne ya bude masa kofar motar jiki na rawa, yana jerama hubby sannu, da fatan sauka lafiya.

Komawa yayi ya kinkimo akwatin. Kusada hubby gwaggo ta zauna, kan hubby nakan cinyarta, sai faman yarfe hannu take da rike kwankwaso.


Doctor sabir ya kira, cewar gasu nan a kan hanya, ya tada motar suka tafi.


Already nurses 2 ke jiransu da abin daukar Mara lafiya, a harabar hospital din. Cikin sauri suka sata a kai sukayi ciki da ita.


Waya yayiwa Hajiya ya shaida mata suna hospital.


Cikin mintin da basufi 15 ba Hajiya ta iso. Hayder na tare da hubby duk yadda doctors din suka so yabasu wuri suyi aikinsu, kin fita yayi. Suna rike da hannun juna, yana jero mata adduai, da share mata zufa dataki yankewa.


Mommy Hauwa kasa hakuri tayi, ta dauko mota zuwa hospital ita da junaid, isowarta kenan sai ga Mmn Yusuf. Suna tsaye sai safa da marwa suke. Aka gunguro hubby zuwa ainihin dakin haihuwa. Hayder na rike da hannunta.


A bakin kofar suka tsaya, suna rokonsa ya tsaya daga waje. Its not allowed ya shiga dakin haihuwa.


Tsawa ya daka mata kamar zai bugeta. Doctor sabir ne ya mata alama ta wuce, kafadar  hayder ya dafa " take it easy! " rigar hannunsa ya mikawa hayder. Doctor biyu ne a kanta mata. Duk abunda ake hayder na rike da hubby sai cakumarsa take any how. Bai damu ba, sai share mata zufa yake, tare da mata addua. ........

Hajiya taji dadin zuwan Mmn Yusuf, duk da bata nuna hakan akan fuskarta ba. Tare suke safa da marwar da addua, gwaggo kam tana zaune sai rarraba ido take. Mommy Hauwa ma zama tayi, tare da daura kanta kan hannun kujerar, motsi kadan ta dago takai dubanta zuwa dakin da hubby take.+


Ahmad da junaid, reception suyi zugum- zugum.


A dakin haihuwa,hubby ce rike da hayder, sai faman salati take, tana jujjuya kai. Hayder kam saboda tsananin tausayi, hawaye ke bin fuskarsa. Lokaci zuwa lokaci ya sumbaci goshinta, tare da share mata zufa.


Sai bayan kusan 1 hour 32min sannan hubby ta sunkuto katuwar yarta. Wani ajiyar zuciya ta sauke tana maida numfashi. " alhamdulillah. " hayder ya fada, lokacin da yarinyar ta fado. Doctor din ta dagota, cikin ikon Allah harda mabiyyar gaba daya.


Cikin lokaci kadan aka gyara hubby da bebynta. Duk abunda suke hayder na kallonsu, sai faman sannu yakewa hubby.

Beby nurse din ta mika masa, hannu na rawa ya karbeta. Wani sanyi yaji a ransa, tare da tsananin soyayyar yarinyar. Sai wuntsila hannu take, tana motsa baki. Dabino( ajwa) ya Ciro a aljihun wandonsa ya tauna dan karamin bakinta yakai bakinsa, ya zuba mata ruwan dabinon. Tsaf ta tande abunta. Ya mata kiransallah a kunnenta na dama, tare da hudba.  Lokacin sun gama gyara hubby zasu fita da ita zuwa dakin Hutu.


Bebyn ya jingina mata, yanda zata iya ganinta sosai. " see your agric chicken beby!!! Look just like him." Ya fada yana murmushi.


Murmushi tayi tare da kauda kanta cike da kunya.

Shiya fara fitowa dauke da bebyn a hannunsa. Da Mmn Yusuf suka fara cin karo. Cikin rawar jiki, ta karasa tana tambayarsa hubby. Ganin beby a hannunsa yasa tai saurin mika hannunta ya bata beby. " she's a girl." Ya fada cike da faraa.


Gaba daya su gwaggo duka taso, fitowa da hubby yasa hankalinsu ya koma kanta. Dakin Hutu suka rufawa su hubby baya, Mmn Yusuf na dauke da beby, sai kallonta take, cike da jindadi, tare da wani abu daya tsaya a ranta.


Doctor sabir ne ya fito daga office dinsa. Rungume hayder yayi, yana masa congratulation. " thanks ahehhh!!!." Ya fada cike da faraa


Su junaid suka iso, da sauri hayder ya rungume Ahmad " I'm a father. " ya fada cikin matukar farin ciki. Dariya su Ahmad sukayi, yana dan buga bayansa a hankali. " welcome to the father hood aheeh!!". Ahmad ya fada yana dariya. Juyawa yayi ya rungume junaid da bakinsa yaki rufuwa, Allah Allah yake ya karasa yaga sweet beby dinsu, da hubby.


Dakin dasu hubby suke, suna nufa gaba daya harda doctor.


Gwaggo Mmn Yusuf ta mikawa bebyn. Hannu na rawa, baki har hunne gwaggo ta amsheta. " masha Allah, tubarkallah. Allah na gode maka daka nunamin jinin takwara, kafin kasa ta rufe idona, yau ina zankai wannan farin cikin." Sai ga hawaye.


" rawa ya kamata ki taka ba kuka ba." Junaid ya fada.


" barni inyi kuka, rawar ma zan taka!!"


Wurin hubby da aka gama daura mata drip suka nufa, suna mata sannu da jiki. Cike da kunya da nauyinsu take amsawa. Duk da muryar bata fita sosai, gaba daya kunyar kowa takeji. Kasan zuciyarta farin ciki da soyayyar yarinyar ne dankare,.


" madam ba matsala dai ko?" Doctor sabir ya fada kai hubby ta kada masa

" masha Allah," ya fada tare da juyawa wurin hayder " in akwai wani abu let me know."  Ya fada yana shafa kan bebyn dake hannun gwaggo, tare da manna mata kiss a goshi. Ya fita a dakin. Bayan su gwaggo sun masa godiya sosai, bisa tsayawa ya tabbatar sun sami kulawar data dace.


Beby junaid ya amsa a hannun gwaggo data rike kamar bazata ba kowaba. Addua ya mata, ya mikawa Ahmad, shima adduar ya mata ya mikawa mommy Hauwa, murmushi tayi, ta mikawa Hajiya cike da jin nauyi da kunya. Dariya Hajiya tayi. Ki tsaya ki kalli kishiyar taki da kyau. Ni kam muna tare.


Cike da kunya mommy Hauwa ta ke kallon bebyn tare da jin wani kaunar yarinyar na shiganta. So cute, so beautiful. Wai wannan kyakyawar yar jikarta ce? Jinin imminta. " masha Allah LA kuwwata illa billah." Ta furta saman lebbanta. Tare da mikawa Mmn Yusuf ita. Dariya Mmn Yusuf tayi. Ta amsa ta mikawa Hajiya


" masha Allah. Wannan ta gidan Alhaji Munir ce!! Nasan yana ganin wannan zai rude." Hajiya ta fada cike da faraa da jin dadin yau itace da yar auta a hannunta.


Hayder ne ya rungume Hajiya yana leko da kansa yana kallon bebyn. Cikin murya mai kama da rada " she look like me ko?" Murmushi Hajiya tayi. " aa auta!! Wannan tafika kyau." Bata rai yayi cike da shagwaba " tun yanzu zaki, fara son kai? Kallenifa dakyau." Gaba daya dakin dariya sukasa.


" naga alama Hajiya bata kishi, tunda ta fadi gaskiya. " Ahmad ya fada yana dariya


Harararsa hayder yayi " kaima ka yadda tafini kyau kenan.?"


Kada kai Ahmad yayi. Tabe baki hayder yayi " its OK."

" ina ita ina samun kyan yarona? Kawai farin ka, data dauko ne, yake kashe musu ido." Inji Mmn Yusuf

Gwaggo cike da farin ciki tace " dani tai kama, shiyasa daga kai har takwara, tafiku kyau."

Dariya junaid yayi " kar kima yarinyarmu baki, muga tana komawa kamanki." Duka gwaggo ta kai masa "kai ma kasan in dai kyau ne, akwai shi."


" a rashin kyawawa ba." Junaid ya fada.


Wurin hubby da take jinsu sama - sama bacci na kwasarta, saboda cikin drip din sun sa maganin bacci, don ta samu isashshen bacci. Kiss ya mata a goshi, yana shafa kanta a hankali. Sunkuyowa yayi dai dai kunnenta, in his husky voice " thank u so much, Allah ya miki albarka, ya saka miki da alkhairi, ya raya mana bebynmu cikin musulunci, ya baki lafiya, next year by this time mu sake haduwa a labour room. " duk da baccin dake idon hubby bai hanata harararsa ba. Smirk ya mata, tare da kiss a kumatunta, Sannan ya dago, yana kallon junaid. " muje ka kaini gida, in canza waannan kayan."

Kallon gwaggo yayi " ba abunda zan taho muku dashi?" " babu." Gwaggo ta fada


Bebyn yama kiss a goshi, sannan ya fita.


A harabar hospital din, suka hadu da Alhaji Munir da abokinsa, suna shigowa. Cike da girmamawa suka gaishesu, tare da musu jagora zuwa dakin da hubby take, kafin suka tafi.


" oh!!! Ni Habiba!! Yaran yanzu ina zaku kai rashin karane ne? Haihuwar yar fari, amma gaba daya kun kasa nuna kawaici." Gwaggo ta fada tana hararar Alhaji Munir, murmushi yayi, ya wuce wurin hubby daketa faman bacci hankali kwance.


" mata fah!! Ai dole ki ganshi, irin wannan zukekiyar mata haka." Mmn Yusuf ta fada tana mikawa abokin beby din.


" rashin kunya dai." Gwaggo ta fada tana tabe baki.


Ko da su Alhaji Munir zasu tafi, mommy Hauwa ma mikewa tayi, tabi bayansu. Don gaba dayan su gwaggo ta hada, tana harara. Dama tasan zaayi haka, dazun ma hankalinta ba a kwance yake ba, shi yasa bata mata tijara ba.


Hajiya ma jakarta ta dauka, zataje gida, saboda abincin da zaa kawowa hubby inta farka, gasu gwaggo dake wurin. Mmn Yusuf cewa Hajiya tayi, taje zasu zauna da gwaggo.

Kafin dare gaba daya asibitin sun san yar dangi ta haihu, saboda tururuwan yan zuwa dubiya da ganin beby.Sai wurin 10 suka samu sakat na yan barka. Ya rage daga gwaggo sai hayder. Yana zaune a kujerar dake facing din hubby tana ba beby nono, sai ciza lips take saboda xafin da take complain.


Yana rike da hannun bebyn yana wasa dashi. Ji yake kamar ya daukesu ya saka a tsagen jikinsa, yadda yakejin sonsu na ratsa zuciyarsa. " balarabe zo ka tafi, ka bamu wuri mu kwanta. Tun azahar ana abu daya." Gwaggo ta fada


Kallonta yayi yana murmushi " korata fa kikeyi?" Ya fada cikin gurbatacciyar hausarsa


" hyo!!! Na koreka din!! Kaima ai ya kamata kaje ka huta. Tunda haihuwar nan dakai aka yita."


A gogonsa ya kalla, kafin ya mike. Kiss yama bebyn sannan yama hubby a saman lips dinta. " good night, and sleep well."  " oh!!! Ni Habiba!!! Ina ganin fitsarar yaran zamani." Gwaggo ta fada tana rike baki.


Sallama ya mata ya fice a dakin.

Shiru dakin, sai sautin numfashin gwaggo dake nuna tayi nisa a cikin baccinta. Hubby ta tashi ta zauna. Hannu tasa ta dauko beby tare da kunna touch light din wayarta, ta na kallon bebyn cike da so da kauna. Wai yau ita ce ta mallaki yarta ta kanta? Yanzu wannan cute beby tatace, meyafi wannan dadi? Me yafi wannan farin ciki? Yarinyar kamar tasan ana son Kallonta a lokacin, ta bude idonta a kan hubby, tana cilla hannaye da kafafuwanta. Murmushi hubby tayi tare da mata kiss a goshi, kumatunta duka biyu. Sai mui mui take da baki, alamar tana neman abincinta.


Rungumeta tayi, akan kirjinta. Tana jin wani sonta da kaunarta na kara ratsata. Kukan da beby ta fara, yasa ta gyara mata rikon, ta fara shayar da ita, fuskarta dauke da murmushi. " she look like him. " ta fada a saman labbanta.


Washe gari, aka sallamesu, direct main house suka wuce.


Dakinsu Ummul khair aka gyara mata. Ba abunda ya burgeta irin gadon bebyn. Ana sata a ciki ta fara wuntsila, kafafu da hannayenta." lallai rashida, saukowa zakiyi, wannan gadon dani ya dace." Hajiya Fatima ta fada tana nadota cikin shawls. " kishi dai kike, Alhaji haruna tuni ya canza da ita. " gwaggo ta fada


Dariya sukayi " ina!!! da tsohuwar Zuma ake magani. Wannan Jan duk nunan rana ne, baki yafi karko."

" shidai ya gani yana so, ko nunan inuwane." Inji gwaggo


" shi yasa Mmn Yusuf keta nan nan da ita, kar Alhaji Jamal yace in ba ita ba sai rijiya." Daya daga cikin yan barka ta fada.


Dariya gwaggo tayi " ta makaro, yana ganinta yace in ba ita ba sai rigiya, rigiyarma mai kwalabe."

" wane ita!!! Ta dai tsaya gidan Alhaji Munir ko Alhaji haruna, sune masu dai dai." Mmn Yusuf ta fada tana murmushi.


Hubby na daga zaune a bakin gado tana jinsu. Gaba daya ta kasa sakewa, kasancewar Mmn Yusuf a wurin. Tana mamakin saukowarta.


Gwaggo ba karamin kula take ba hubby ba, da bebynsu. Haka Hajiya da Mmn Yusuf ke kula da ita. Mmn samira ma ba laifi tana nata kokarin. Duk da har yanzu basa wani shiri sosai da Hajiya.


Angon karni, kam dole daga Hajiya har gwaggo, sun dau dangana saboda yadda ya kasa ya tsare. Wani lokacin sai Hajiya ta koreshi. Don shi ba ruwansa da yan barka. Duk lokacin da yaji son ganin matarsa da bebynsu kai tsaye zai shiga, cikin sallama. Ya gama abinda yake ya fita.

Hakan ba karamin kunya yakesa hubby ba.

Kallon bebyn yake, ya kalli hayder. " I may dreaming? " Hafiz omer ya fada yana murmushi


Mintsini Hafiz ya masa. " wayyoh!!!" Ya fada yana zabura.


" da gaske ba dreaming nake ba." Ya fada yana rungume beby da kyau a jikinsa. Yana mata kiss a kumatunta.


Kallon hayder yayi dake tsaye, yana musu murmushi. " da gaske yarinyar ka ce da Anty hubby? " harararsa hayder yayi  " of course. " ya fada yana daga masa gira


" ka gama burgeni wallahi, da na dauka ko giyar wake kasha bazaka tunkari Anty hubby ba. Ashe!! Ashe!!." Hafiz omer ya fada yana murmushi


" kaifa wallahi baka da mutunci." Hafiz ya fada


" kai ya ka gani, ai maganata akan hanya take." Hafiz ya fada idonsa akan bebyn


" she's so cute!!! Dani tayi kama."

Hafiz ya mika hannu ya dauke ta makaleta Hafiz omer yayi. " barta ta gama jin dumin ubanta tukun." Ya fada yana kara rungume a kirjinsa.


" Allah ya shiryeka." Hayder ya fada


" me yafi wannan dadi? Mune da ya." Hafiz ya fada


" abu namu, maganin a kwabemu." Hafiz omer ya fada yana mikawa Hafiz bebyn.


                * ******************

Ana gobe suna, su aisha, ummu sulaim, ummu aiman da ummul khulsum, suka iso garin kaduna. Ummul khair ce kawai bata samu halattaba, saboda cikinta, haihuwa yau ko gobe. Hubby taga gata na karshe, mutane wannan ya shiga, wannan ya fita.

Ranar suna beby ta amsa Amatullah............

Post a Comment for "DA KAMAR WUYA CHAPTER 8 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...