AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

- - Post a Comment

AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA

Rayuwar gidan Ambassador Hamza Atiku abar sha’awa ce abar koyi. Ba su da abin da ya fi tarbiyyar ‘ya’yansu da nema musu ilimi muhimmanci a gare su. Yaransu nitsattsu masu hankali da sanin yakamata. Uwar da uban kuma soyayya da shakuwa mai karfi ce a tare da su, ta yadda in ka lura za ka fahimci ba soyayyar aure ce kadai a tsakaninsu ba, akwai ta jini mai gudana a cikin jiki da jijiyoyi. Kaunar da suke yi wa yaran ba ta hanawa su ba su ingantacciyar tarbiyya, su kwabe su in sun yi ba daidai ba cikin nasiha da jansu a jiki. Sai dai fa kaunar Abdul’azeez daban ta ke da ta kowa a zuciyar Www.bankinhausanovels.com.ng Ambasada. Idan da abin da Abdul’azeez ya tsana shi ne a yi masa tsawa, ya fi son ko ya yi ba daidai ba ka fada masa a hankali shi ya sa ya fi son Daddy, ya fi sakin jiki da shi tunda Mammah tana yin tsawa. Rannan ya yi laifin yin kwallo (ball) da Magenta (qiddah) inji larabawa, sabida ta sa masa baki a abinci, Mammah ta yi tsawa. Yatsunsa biyu ya sa ya toshe kunnuwansa ya rufe ido jikinsa yana bari da karkarwa, cikin karkarwar jiki data murya ya ce.
‘“Mammah please... tell me what you want to me to do, but please don’t shout.......”. Sai ga

 ZAMU TASHI 


hawaye sun shimfido a guje. Jikin Mammah ya yi sanyi, daga ranar ba ta kara daga masa murya ba sai lallashi da nasiha, don Abdul’azeez ko dukansa aka yi ba ya hawaye. Amma in kayi masa tsawa zai yi abinda yafi kuka. Hutunsa ya kare ranar wata lahadi, suka kai shi airport ya daga Abuja, gidan karamin Kakansa Sanata Abdulkarim ya sauka. Washegari ya koma makaranta. Ya yi daidai da ranar da Mammah ta karbo baby daga asibiti, bayan likitoci sun tabbatar da koshin lafiyarta. Dr. Unaisa zaunar da Hajiya Maryam ta yi, ta yi mata lacca ta lokaci mai tsawo kan yadda ake kula da mai lalurar nimoniya, da shawarwari kan abincinta. Ta bada shawarar madarar da za a dinga ba ta (SMA) tana bugqatar dumi (heat) a kowanne lokaci, kasancewa cikin kaya masu kauri a lokacin zafi, kasancewa cikin kayan sanyi sosai a lokacin sanyi. Ta kasance jikin uwa a kodayaushe don samun dumin jikin uwa, kasancewa a daki mai dumi da shan madara mai dumi sosai. Wannan zai taimaka ta murmure sosai cikin watanni kalilan.

Hajiya Maryam ta yi wa Dr. Unaisa godiya sosai, ta karbi lambar wayarta ita ma ta karbi tata. Duka ‘bill’ din da asibitin ya caje su ta file din iyalin Ambasada aka biya.
Karfe shidda daidai na yamma Salah direba ya yi (parking) a cikin (gate) din gidan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyyah Professor Dr. Hamza Atiku Dakata, Hajiya Maryam ta fito rungume tsam da kyakkyawar bakwainin jaririyarta cikin
farin shawul mai tsananin taushi. Salah ya biyo ta da jakar ‘shopping’ din kayan jarirai da abubuwan bukatar su da ta yo a kasuwar (Baaba Sheriff), ta karasa cikin falon bayan ta ture kofar gilashin (sliding door) da ta raba harabar gidan da tangamemen falon wanda ya ji kayan alatu da ababen more rayuwa iri-iri.Www.bankinhausanovels.com.ng Daddy ne zaune a kan kilishi cikin ‘ya’yansa uku yana duba littattafansu na makaranta, don ganin halin da kwakwalwar kowannensu ke ciki. Halim yana kan cinyarsa da nashi (drawing book) din, a yadda ya fahimta Isma’el shi ne mai matsala, yana da rauni kwarai a kan darasin lissafi (mathematics). Nasiha yake masa sosai cikin hikima kan ya maida hankali ya iya lissafi domin shi ne kashin bayan ilimin boko. Mammah ta yi sallama suka mike da gudu suka yi kanta. Fadi ta ke, Ku yi a sannu kada ku kada kanwarku, kun ga ba ta da lafiya”.

A sannu Daddy ya daga ido ya dube su, ya soma dan yamutse fuska, suka hada ido da matar tasa. Ta fahimci ya canza fuska, gwiwoyinta suka yi sanyi, amma a haka ta karasa gare shi ta zauna dab da shi ta miqa masa jaririyar, kamar ba zai karba ba ko me ya tuna kuma ya karba, ganin Usman ya danne Isma’el duk a kokarinsu na kowanne so yake a bashi jaririyar ya dauka, sai ya karba don ya raba fadan, amma ba cikin dadin rai ba. Sama-sama ya kalli ‘yar sai kuma ya mika mata, ya tambaye ta,
To yanzu ya za ki yi da ita? Bana jin gidan marayu na Saudi-Arabia za su amshe ta, tunda mu ba ‘yan kasa ba ne”. Mammah cikin mamakin sauyin da ta gani a tare da Daddy farad daya, ta ce da shi cikin kwantaccen sauti. Wai da so nake ka yi min izini in sha magani in samu ruwan nono in shayar da ita”.
Girgiza kai ya shiga yi, “Wasa ne wannan, ki shayar da dan da ba nawa ba?” Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Daddy........ Ya dakatar da ita, “ Please don’t argue with me Maryama. Ki maida ita wajen dangin mahaifiyarta, ba zan iya rigon dan da ba nawa ba balle in kasa yin adalci tsakaninsa da ‘ya’yana Allah ya tuhume ni, musamman rikon maraya. Na yi miki alkawarin zan dauki nauyin iliminta har zuwa digiri na kololuwa idan tana so a ko’ina ta ke cikin duniya. Amma ba zan hada ta da ‘ya’yana in rike ba”.Www.bankinhausanovels.com.ng 
Hajiya maryam ta fashe da kuka, “Don Allah Daddy kada ka yi min haka... ina sonta, ina son uwarta ina son diya mace... Allah bai ba ni ba... don Allah Daddy ka yi min alfarma ka barni in rike ta koda wannan itace alfarma ta karshe da zaka yimin a rayuwa”.
Ta daga hannuwanta biyu gare shi tana kuka tana roko. Dukkan yaran ma kuka suka sa suna rokonsa har Halim, “Daddy ka bar mana don Allah, muna so, kada a kai ta wani waje ta mutu kamar yadda Mamanta ta mutu, do us a favour ”. Inji Usman.
Suka kama babyn duka suka kankame, ita kuma da ta ji matsa ta canyara kuka da muryarta kamar gyare don zaki. Su biyar din duka kuka da hawaye share-share. Sakin baki Ambasada ya yi yana kallonsu, kafin ya ce “Na shiga ukuna. Ku dakata, mu yi magana ta maslaha’”. Ya fada yana daga hannu irin na saranda. Duk suka dakata suna share hawaye suna hadiyar zucci. “Zan bi ra’ayinku tunda kun rinjaye ni, amma da sharadin ban yarda Mammah ta yi (breastfeeding) dinta ba, a nemi ‘alternative’.
Sai duk suka juya suna kallon Mammah don jin ta bakinta. Kowannensu fuskarsa na nuna “ Mammah ki yarda da hakan ”Hajiya Maryam ta sa habar zaninta ta goge fuska da majina, “Daddy ba ta da lafiya ne, tana da pneumonia , tana bukatar ruwan nono da dumin jikin uwa, in ban shayar da ita ba bani da kulawar da zan ba ta fiye da hakan’’.
Mikewa ya yi yana dakile fuska. Ya kakkabe rigarsa ya nufi matattakalar da za ta sada shi da dakinsa. Yana tafe yana fadin, “Shawara ta rage ga mai shiga rijiya, na ba ku daga yau zuwa gobe ku yi shawara, har madara zan dauki nauyin saye sadaqah fisabilillahi. Amma in ba haka ba gobe zan sa a buga mata fasfo ku kai ta inda ku ka dauko uwarta”’. Ya yi wucewarsa ya shige daki ya rufo kofar Www.bankinhausanovels.com.ng 
Usman ya matso sosai jikin mammanshi, idonsa a kan babyn da ta zuba fararen yatsunta cikin baki tana tsotso alamun yunwa.
“Mammah ki yarda don Allah mana? Tunda mun samu ya bar mana?”Isma’el ya ce, “Mammah don Allah ki yarda ta sha madaran, rayuwa da ciwo duka na Allah ne, idan mai tsawon rai ce sai ki ga Allah ya raya mana ita. Take heart Mammah... ”. Ya fada tare da kai hannu santar kirjinta yana shafawa alamun ta yi hakuri ta bi abin da Babansu ke so. Hajiya Maryam ta tsura wa ‘ya’yan nata ido, yara masu hankali da tunani tun a qananan shekaru irin nasu. Har sun fi ta tawakkali da hangen nesa . Da gaske Allah shi ne mai rayawa ba nonon uwa ba. Ta rungumo su gefe da gefenta, jaririyar na bisa cinyarta, ta sumbaci kowannensu a goshinsa, “Na amince. Gobe zan gaya wa Daddy. Yanzu zan fara ba ta madara kun ji ana kiran sallah, maza kowa ya je ya yi alwala yanzu Daddy zai sauko ku wuce masallaci”. Duk suka mike cike da murna har da tsalle suka nufi toilet don dauro alwalar. Ita kuma ta dauki ledar shopping dinta da babyn ta nufi dakinta.
A take ta tafasa ruwan zafi ta hada madarar ta soma ba ta. Wata irin kauna tana mamaye zuciyarta na ‘yar da ba ta san daga ina uwarta ta ke ba balle ubanta. Sai dai kaso 90% na zuciyarta ya amince yarinyar nan ba shegiya ba ce, da ubanta. Habiba ba ta yi kama da mutanen banza ba, sannan ba yarinya ba ce balle a ce shege ta yi ta gudu. Ta fi amincewa da cewa wani nau’i ne na kaddarar rayuwa ya rabo ta da gidan mijinta da iyaye da “yan uwanta. Ba ta yi gigin zuwa turakar Daddy a yau ba
kwata-kwata, shi ma bai neme ta ba. Duk abubuwan da ta saba yi masa kafin su kwanta da kansa ya yi, zuciyarsa fal haushin Maryam, tunda daga samun ‘ya har ta fara watsar da shi, da maa ce ita ta haifa da sauki ba zai damu ba. Ya yi tsaki yana shan ‘gahwah’ (coffee) ya fi sau shurin Www.bankinhausanovels.com.ng masaki. A haka ya kwana cikin bacin rai, ita kuma tana can tana ceton rayuwar ‘yar marainiyar Allah. Ta kashe A.C ta kunna (room heater), ta ciro kayan sanyi masu kyau cikin sayayyar da ta yi ta sunke ta a ciki, da pampers. Ta cika mata ciki da madarar da Dr. Unaisa ta yi umarni. Nan da nan ta hau baccinta cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne ta tuno da Daddy, ta yi ajiyar zuciya ta yi shirin bacci ta manna jaririyar a jikinta, ta rufe su ruf cikin lallausar bargo, suka yi bacci abinsu. Tun asuba kukan baby ya tashe ta, ta tashi zaune ta dauke ta ta yi toilet da ita. Wanka ta yi mata da ruwa mai dumi sosai, ta nado ta cikin shawul. Shafe ta ta yi da man zaitun ta canza mata (diaper), ta shirya ta cikin (overall) farare tas! Da hula mai kauri. Sannan ta hado madararta ta shiga ba ta. Ta kura mata ido ba ta ko kiftawa. Habiba ta ke tunawa da karamcinta, da yanzu ta fara jiyo sukurniyarta tana shara da goge-goge kafin ta fada kicin ta hada mata kayan girki kafin ta sauko. Hawaye suka ciko a idonta, me ya sa Habiba ta yaudare ta? Me ya sa ta boye mata asalinta da cikin da ta ke dauke da shi? Rayuwar yarinyar a gaba ta ke kokawa idan Allah ya raya ta ta fahimci ita din ba uwarta ce mahaifiya ba, ba a san kowa nata ba, ba a san daga inda ta fito ba.
Ta ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, ta share hawayen idanunta. A hankali ta sanya babyn cikin gadon da ta hada yanzu, sai bacci ta ke sadidan cikin koshin lafiya. Wanka ta yi, ta ci gayunta kamar yadda ta saba, kai ba za ka ce ta yi shekaru talatin da biyarba. Ta san sirrin gyara na diya mace kala-kala. Ta lakanci ado da kwalisa tun tana budurwa, haka yanzu da shekaru suka fara turawa ba abin da ya canza Maryam Dakata. Farar mace mai farar aniya, uwar gidan Professor kuma Ambassador Hamza Atiku Sakata.
Kicin ta fada ta soma hada wa iyalinta abin kari. Sosai ta yi latti, domin har gari ya waye. Sanin Daddyn a sama-sama yake da ita ta ce bari ta yi masa abincin da ya fi so, don ta dan faranta ransa. Kunun gyada ta hada ya ji madara yadda ya kamata. Ta hau suyar sinasir din da ta kwaba tun daren jiya. A gurguje ta ke yin komai, miyar ta ji ganyen alayyahu sosai da tsokar kaji. Sun dahu sun yi lugub. Yaran kuma (quaker oat) ta dama musu, ta soya musu ‘pancake’ ta shirya wa kowanne a sundukin abincinsa. Da hanzari ta shirya wa Daddy tebur jin baby ta fara kuka. Su Isma’el suka fito daga dakinsu cikin shirin makaranta kowanne goye da dirkekiyar (school bag) dinsa.Mammah sabahul khair’. Duk suka fadi a tare bayan sun shigo kichin din cikin russunawa. Kansu ta shafa daya bayan daya tana murmushi, “Sabahul khair, ‘yan albarka, kun tashi lafiya?’”’.Isma’el ya ce, “Karasa aikinki Mammah, I will help you with the baby ”Ta yi murmushi ta daga masa kanta. “Madararta na nan a kan (side drawer) ba ta ina zuwa’’Da hanzarinshi ya juya zuwa dakin nata. Tun a kan Halim Isma’el ya iya raino, shi ke taimaka mata da rainon Halim har ya yi wayau. Yanzun ma baby ya ciro daga Www.bankinhausanovels.com.ng gadonta ya aza a kafadunshi yana jijjiga ta har ta yi shiru. Ya zauna gefen gadon Mammah ya ba ta ruwan zamzam ta sha sosai, sannan ya sanya mata madarar a baki. A ranshi yana cewa, duk da dai an ce baa gane kamannin jariri, amma wannan da ganinta Habibah ce sak!
Mammah turakar Daddy ta nufa da saurinta, suka ci karo a matattakalar bene ya yo shirin office tsaf, rike da (briefcase) dinsa. Ta karba suka sauko tare, sai faman dauke mata kai yake yi. Ta yi murmushi a ranta ta ce, “Insha Allahu watarana sai ka yi alfahari da ‘yar da ba ka son rikewa din’Su Isma’el ya kwala wa kira yana kokarin ficewa daga falon ba tare da ya dubi (dining) din ba. Ba ta yi fushi ba, ta ce, “Daddy break fast fa?” yqce
Ya fada yana duba agogo. Ta ji ba dadi yadda mata ke ji in sun takarkare sun zabga wa maigida girki ya kici. Usman da Halim suka wuce tare da shi, Isma’el ya fito dauke da baby ya mika wa Mammah, sannan ya dau jakarsa da kwandon abincinsa ya bi bayansu da gudu. Ta yi ajiyar zuciya ta goya baby jikinta a sanyaye. Da gaske Hamzanta ya canza daga halin da ta sanshi da shi. Ta san shi mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa da shi, ba ta san me wannan yarinyar ta tare masa cikin gidan nan ba, da alama za ta fuskanci barazana mai yawa a rayuwar aurenta a kan rikon yarinyar daga mijinta, abin kaunarta. Ta kuma shirya karbar kowanne kalubale in har zai bari su rayu tare. Ba za ta kai ta Nigeria ba, inda ko sun je babu inda za ta kai ta a karba in ba gidan marayu ba.Www.bankinhausanovels.com.ng 
Ta shirya yin jihadin rikon ‘yar Habibah ko da Daddy zai kara aure ya kora ta Nigeria a dalilin haka. Ta watsar da tunanin ta shiga harkokinta. Islamiyyar ma ta daina zuwa sai ‘yarta ta isa bari a makarantar rainon yara (creche). Amma dole ta nemi ‘yar aiki don ayyukan gidan sun fi karfinta. Karshen ta dai Takarin da bata so.
A nan unguwarsu Albasaatin ta yi kawaye biyu ‘yan Nigeria matan ma’aikatan Embassy, daya matar mataimakin Daddy ce Safiyya sun fi su dadewa a Saudiyyah sosai, bayan ta gama girkin rana ta kira Anty Safiyya ta ce ta cigita mata mai aiki don Allah Takari, ta ce ta bari sai Juma’ah za ta shiga Misfalah in ta je Harami za ta taho mata da ita. Ta yi godiya suka aje wayan. A daren ranar, Hajiya Maryam ta yi shiri kamar yadda ta saba ta nufi turakar maigidanta, aiki yake yi a tsakiyar gadonsa cikin na’ura mai kwakwalwa. Ciki-ciki ya amsa sallamarta ba tare da ya dago daga abin da yake yi ba. Kokarin sauke baby ta ke daga bayanta don ta koma ta dauko gadonta. Da hanzari ya dago ido ya dubesu. Ya zare farin gilashin kara karfin gani da ke idanunsa, cikin kaushin murya yake magana. “Ban gane ba? Kina nufin tare zan kwana da yarinyar nan? Ta ya ya ki ke tunanin zan iya jure kukan jaririn da ba nawa ba? Excuse me please, Maryam! It’s enough wallahi, abin da ki ke min a kan yarinyar nan ya ishe ni. You are forcing me to be a father of your adopted daughter while 1’m not. To bari ki ji in gaya miki, wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Daga yau sai yau, kada ki kara kawo min ita dakin barcina. Ke kanki na hakura da ke in har za ki hada hidima ta da tata, ko za ki hada mana makwanci. Idan duk alfarmar da na yi mata ba ki gode min ba zan ba ki mamaki wallahi, don aure zan kara ki ji dadin kula
Tana kuka sosai ta juya da ‘yarta a kafada jikinta har rawa yake, domin Daddy fada yake sosai. Cikin babban sauti wanda ba ta taba sanin yana da shi ba. Tana fita ya banke kofarsa yana sakin tsaki. Haka suka kwana kamar jiya zukata babu dadi.
Washegari bayan yara sun tafi makaranta, shi kuma ya tafi office, kamar jiya yau ma bai kula abincin da ta bata lokaci ta shirya masa ba. Tun asuba ta tashi ta soya masa waina (masa) don ta san yana matukar sonta, haka ya tsallake ya bar mata kayanta kamar jiya ya sa ‘ya’yansa a gaba suka tafi. Su kansu yaran ba sa cikin walwala ganin halin da iyayensu ke ciki na rashin walwalar suma, yanayi ne da ba su taba ganinsu a ciki ba tun tashinsu. Daddy da Mammah suna matukar kaunar junansu, sun fahimci juna,Www.bankinhausanovels.com.ng 
ra’ayinsu daya kusan a kan komai na rayuwa, sai yau a kan ‘yar Habiba, kowanne gani yake shi ne a kan gaskiya. Shi Dr. Hamza ba muguwar zuciya ce da shi ba, ba rashin tausayi gare shi ba, ba kin taimako gare shi ba, a’ah, ra’ayi ne na rikau irin na Malam Bature, duk wani taimako da zai wa mutum ko jininsa ne ya fi yarda ya yi masa shi daga nesa komin girmansa, amma ban da ya dauko shi ya kawo cikin family dinsa. Ita kuma Hajiya Maryam tana matukar son Habibah, son ne ya shafi abin da ta haifa, sannan tana tunanin in ba ta rike yarinyar nan ba ina za ta kai ta? Ba ta san komai da ya dangaci Habibah ba ba ta san daga inda ta fito ba, sannan in ta kai ta gidan marayu tana tausayin rayuwar da za ta taso a ciki. Za ta taso ne a shegance, a shegantata bayan ita ta yarda yarinyar nan ba shegiya ba ce da ubanta, akwai abin da ya rabo Habiba da mahaifinta. Me ya sa Daddy ba zai yi mata alfarma ba?
Hantsi na dagawa ta samu wayar Anti Safiyyah ta daga suka gaisa da tambayar lafiyar yara. Anti Safiyya ta ce, “Mai aikin babba ki ke so ko yarinya, ko budurwa?” Babba dai, wadda ta san ciwon kanta. Ban da wadda ba ta kai shekaru hamsin ba”.
Safiyyah ta ce, “To alhamdu lillahi an samu. Sunanta Azumi, ‘yar Sakoto ce, zan kawo ta ranar juma’a insha Allahu. Za a dinga biyanta Riyal dari biyu duk wata, duk irin hidimar da ki ke so ta yi miki za ta yi miki, ku dai tattauna a tsakaninku”. “Na gode Safiyyah sosai. Na gode Allah ya kara zumunci’”. In ji Mammah. Da haka suka ajlye wayar.
A cikin wannan hali na zaman doya da manja, zuciya ba dadi, Hajiya Maryam ta ci gaba da zama da mijinta a dalilin ‘yar mai aikinta. Ana gobe za su cika kwana bakwai da baro asibiti tunanin ragon suna (haqiqa) ya dame ta. A yadda Daddy ke kumbure-kumburen nan za ta doshe shi da zancen yanka ragon suna? Ta yi tunanin ta bai wa Salah ya sayo da kudinta kamar yadda ta yi amfani da kudinta wajen siya mata suttura, madara kam ya saya katan-katan kamar yadda ya furta, sai dai Www.bankinhausanovels.com.ng wani (positive) tunani ya shige ta. Bai kamata tun yanzu ta soma yin gaban kanta a kan yarinyar ba, dole ta ba shi hakkin da yake cewa tana ‘forcing’ dinshi na zaman uban yarinyar yana so ko ba ya so, in ta sayi rago ta yanka mata ya tabbata ita ce uwarta, ita ce ubanta kenan, “You must be the father you don’t want to be Daddy! ”. Ta fada a fili A daren ranar ta cancada kwalliya, turare kalakala ta feshe jikinta da shi, a gobe ta ke sa ran za a kawo mata sabuwar mai aikin. Ba za ta iya barin Baby ita kadai ba, don haka ta kira Usman da Isma’eel da Halim ta jere su a gadonta ta ce su kwana a nan.
Isma’el ba ka da nauyin barci, ka kula da baby in ta motsa. Ga madararta, ga ruwan zam-zam dinta ka duba pampers akai-akai”. Dont worry Mammah, je ki lallasar mana


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...