AFUWA BOOK 1 CHAPTER 1 BY JAMILA HALLIRU G/DUTSE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

AFUWA BOOK 1 CHAPTER 1 BY JAMILA HALLIRU G/DUTSE

AFUWA BOOK 1 CHAPTER 1 BY JAMILA HALLIRU G/DUTSE

- - Post a Comment

AFUWA BOOK 1 CHAPTER 1 BY JAMILA HALLIRU G/DUTSE                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
Tsananin gudun da take yi shi zai ba ka mamakin ganin mai jaye da motar mace ce, sanye take da . bakin tabarau tana sanye da hijabi wanda - hausawa suka yi masa lakabi da makabuliya, wato dai duk wanda suka gani da wannan hijabin mafi yawa tsaraba aka ba su. Har ta shigo layin ba ta rage gudun ba, da ta zo daf da makeken get din da ya lullube gidan sannan ta tsaya ba tare da ta dannan horn din da zai ankarar da masu gadin ba. Ta kusa minti biyu a zaune a cikin motar dan iko da mulki batayi hon ba. , ; Cikin isa ta bude motar ta fito fuskar nan tata murtuk wai dole an bata mata rai.
Duk su ukun suka miqe dan nuna girmamawarsu gare ta, suna yi mata, “Sannu da zuwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta tsaya tare da cire gilashin da ke fuskarta ta kalle su sama da Kasa ta yi Kwafa ta maida gilashin ta manne idonta, ta yi gaba domin sam ba ta ga laifinsu ba, laifin mai gidan ne ai yau lahadi, kuma ya fi kowa sanin ta fita, aiko shi ta yi isar da zai taso ya bude mata Kofa, amma yayi banza da ita.


Kai tsaye falonta ta nufa wanda ya sha kayan alatu, wanda-in zaka tsaya lissafa su da wahala ka iya lissafe su a lokaci guda. Tana shiga ta yi jifa da jakarta har ma da hijabin dan dama da wahala ka ganta da dankwali dan ta tsane shi tun fil’azal ta fi ganewa ta sanya hijabi, shi ma kuma ba dogo ba, wanda iyakarsa kafadan ko kuma rabin baya. Wato dai iyakarsa ya rufe mata gashinta da ya sami masauki a bayanta.

BILKISU kenan, yarinya mai ji da kanta ~ ‘duk da ba ‘yar kowa ba ce, amma tsananin kyawun da Allah ya ba ta shi yasa mata girman kai da dagawa, domin Bilkisu yarinya ce mai shekaru ashirin da haihuwa. .
Bilki fara ce sol, kamar tsada. Doguwa ce amama ba wai tsayi mara misali ba, tana. da jiki wanda ba za a Www.bankinhausanovels.com.ng iya kiranta lukuta ba, kuma ba za a iya kiranta da siririya ba. Wato dai duma-duma za a iya kiranta. Idonta ya yi matuKar dacewa da fuskarta, dan yadda yake dara-dara kamar dauka aka yi aka ajiye su, ga su farare sol kamar farin wata. . .
Hancinta har baka bakinta Karami mai dauke da kyawawan hakora. A takaice dai yarinyar sai a tara mata dubu ba a sami wadda suka yi kunnen doki ba, balle kuna a sami wadda zata fita kuma ko da a cikin indiya ne. Wannan ni’ima da Allah ya yi mata ne yasa ta ke murza mijinta yadda taso dama duk " “wanda zai rabe ta, kuma komai girmansa ko kuma Kankantarsa.  Abin da ta keyi a cikin gidanta shi yasa mafi yawan jama’a suke daukar cewa, kawai asirce mijin nata tayi, kuma alifun bata taba yi. wai dan mallakarshi ba, asalima tana ganin- fadowa ne kamar ita a ce wai da namiji ba zata - miallake shi da kyawun surar da Allah Yayi mata ba har sai ta hada da malamai, wallahi ta shige wannan Karnin dan haka mace bora ita ke mallakar miji da asiri. Ta jima a zaune sannan ta miqe ta shige  bandakin da ke manne Ga frlon, tayi wanka ta. sake caba ado tare da fitowa ta nufi lafiyayyan ' kicin dinta da shi ma ba zan iya zayyana muku ’ irin dukiyar da aka jibga a cikinsa ba Ta dan leKa nan da. Nan Kuma ta Sata rai, ta soma kwadawa Yahane kira. Yahane ta taho da saurinta domin amsa kiran uwargijiyarta. Ta sake bata rai tare da yiwa _ Yshane wani kallo, ta ce.
Yahane ya ya yau ba a goge kicin ba, kalli duk yadda ya yi datti”Yahane ta yi saurin kallon Bilkisu, tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wallahi Hajiya na goge shi sosai, sai dai ko idonki ne yaga kamar ban yi ba”. “Yahane ya ya zaki yi min musu bayan na fiki ganin kasancewata Kuruciya, ke kuma ba ama jika ba kin yi tattaba kunne dani? Dan haka in dai lalaci ne zai hana ki yi min aiki na gari babu dole, sai ki yi gaba dan ni dama kin ishe ni. Yahane ta durkusa tana bawa Bilkisu hakuri.
Bilki ta juya ko kallon tsiya ba ta Kara yi mata ba, balle kuma har ta sami na arziKi, ta juya ta koma falonta tana taku kamar ita kadai ce mace a cikin duniya ta rage. Ta yaye labulen falon ta shiga, da sauri ta tsaya tare da yi masa wani kallo, kawai ta dauke kanta.Shi ma ya daure ya ce.“Bilkisu na shigo dazu na iske baki nan nayi mamaki domin ganin baki tambaye ba fita, shi yasa yanzu nake son in gane inda ko in san inda kika je Ta saki wani numfashi-tare da bude firij . din‘dake gabanta ta dauko lemo kwali ta soma , kwadawa Safiya kira.  Safiya ta shigo jikinta ko’ina yana bari, ta zube a gaban Bilkisu ta ce “Anti gani”. Bilki ta kauda kai, sannan ta mikawa Safiya lemon,tace “Dan Allah Safiya bude min lemon nan”Safiya ta sa hannu biyu ta karba ta bude ta. mika mata. Bilki tace. “Haba Safiya yanzu kin budé? Ai kamata ya yi ki Karasa ladanki”Cikin sauri Safiya ta mike taje kicin ta dauko kofi ta tsiyaya mata, ta miqa mata. Bilki ta karba ta dan kurba ta ajiye, ta kalli Safiya tace. Jeki abinki kinji”. , Kafin Bilki ta Karasa maganarta tuni har Safiya tayi waje, dan ta san halin uwar dakin nata, yanzun nan ta Kare mata tanadi.
Ta Karaso cikin rausaya ta zauna daf da shi, tare da dora Itannu akan fadadarsa ta kashe murya ta ce.
“Yanzu dan Allah in zan fita sai na gaya - maka, shin wai har yanzu ban yi isar da za a sakar min mulkin kaina ba, ko kuma har yanzu kana daukar zugar ‘yana uwanka akainane?”
Anas da ya yi Kuri yana kallonta, duk sonta ya kuma dabaibaye shi har yana jin zai iya rabuwa da kowa a kanta, ya ce.“Haba Bilkisu ni ba wai ina nufin haka ba
Ne a kanki, ina so in san abin da ya fitar da ke, inji na lafiya ne Ko kuma ba na lafiya ba”, _. Tatsuke fuska tare da mikewa tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ka yi haKuri domin ba zaka taba sanin wannan ba , nasamn ana zuga ka a kaina domin kaf danginka sun tsane ni, har ma da mahaifiyarka da shi kansa mahaifinka. A yanzu kai ma na ga ka fara neman rusa katangar farin cikina, ni kuwa duk wanda yace zai rusa min katangar farin ciki wallahi ba zan taba barinsa ba”Ta juyo ta kalle shi ido cikin ido,tace. Anas in kaga ba zaka iya bin ra’ayina ba ka iya haKura da rayuwa da ni inyaso sai in sami wanda zai iya faranta min zuciya, tunda ni dama baka taba jin nace sai na mutu da kai ba”. Tana gama wannan maganer ta sanya kai ta fita ta bar masa falon.  Anas ya bita da kallo cikin damuwa da kuma nadamar yi mata wanna magana dan yadda Bilkisu ta ke da taurin kai zai wahala kafin ta huce, dan haka shi ma ya tashi ya bi bayanta yana ta lalubo abubuwan da zai gaya mata dan ya ga ta huce, kuma har ta saki ji. da shi domin dama_jiya suka shirya ‘sannan kuma yau tana " neman janyo wani? Bazaiyiwuba.

************

Gida ya cika da ‘yan uwa da abokan arziki saboda Karuwar da suka samu ta haihuwar diya mace da Biba tayi, wato Kanwar Anas Kenan. In ka shigo-sai ka yi zaton yau ne suna, tare suka danno kai cikin gidan domin in dai za a , je sabga danginsu to dole shi-zai kai ta, kuma ya dawo ya dauke ta, idan kuwa ba haka ba babu inda  zata.Suna ta hira suna dariya kai ba zaka ce a cikin surukai take ba, domin har da tafawa su kuma kowa sakin baki ya yi yana kallon ikon Allah.
Babu wanda ta gaishe saboda bakin girman kai da izza. Hakan ya sosawa Anas rai, amma ya kasa yi mata magana dan yana tsoron wane hukuncin zata yanke idan suka koma gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suka shiga falon da yake cike da iyaye da kakanni, nan ma Anas ne kawai ya gaishe su, amma Kememe Bilkisu ta yi wa kowa banza har ma da mahaifiyar Anas din. Momy ta yi Kwafa tare da cewa.“Bilkisu ina yini?” Bilki ta ji kamar zata nutse dan kunya, amma dan girman kai sai ta matse ta yi wa Momy wani kallo tace.lafiya, an sami Karuwa Allah Ya raya”.
Momy ba ta sake kallonta ba ta dauke kai ‘tana jira a kuskure ta yi mata tsiya. Biba ta fita Ke da yarinyar ta ce. A’a manyan baki sannunku da zuwa, ai ni da har na yi fushi na yi zaton ba za a zo a yi min sannu ba”. Tana fade tana Kokarin miKawa Anas. baby. “Ke” Momy ta yi mata tsawa da fadin haka, hakan yasa da sauri Biba ta tsaya tana kallon Momy, yayin da Momy ta mika hannu ta — karbi jaririyar ta ce. “Haba Biba, ai wanda ya san darajar haihuwa shi ake ba wa da yanzu kin ba Anas  yarinya bayan bai san radadinsu ba? Ai sai ya iya cutar da ita, gara dai ki bari nan gaba in ya auro ‘yar mutumci kuma mai haihuwa sai ki ba shi, idan ma duka kika ba shi ba zan hana ki ba”Da sauri Anas ya kalli Momy, sannan ya kalli Bilkisu. wadda fuskarta babu alamun damuwa, dan ita a nata haukan ko yanzu ta ga , damar haihuwa zata haihu. Anas ya runtse ido yana jin zafin abin da  mahaifiyarsa ta gaya masa, duk da ya san ba laifin kowa bane laifinsa ne da tun wuri ya nunawa mace so wanda har zata raina shi.  Amina ta shigo ta yi mata kallon banza ta dauke kai ta ce.
“Banzar bazara iskar damuna, ai ni da kuke ganina iyayena talakawa ne a tausaya a ba su tsumma, amma na sami daular gidan miji sai iko da mulki nake zubawa, kuma kun san wani abu wallahi a yau in ya ce in bar gidansa shi kenan Karyata ta Kare sai in hakura in koma gidan Kasa in ci gaba da rayuwa, kin ga a wann.... Www.bankinhausanovels.com.ng
Ke Amina! Ya ishe ki domin kowa yayi zagi a kasuwa to babu wai ya san da wanda yake, dan haka bar ganin kina gidanku, wallahi sai in nada miki dukan tsiya”Amina tayi dariya tace. “Ai ni wallahi na wuce ki hada jiki da ni, domin ni na san kaina, ke kuwa banza ‘yar matsiyata maimakon ki zo ki ci arziki ki bar arziki a mazauninsa kin kasa, wallahi ki gama ° iskancinki duk lokacin da Allah Ya karya alKadarinki sai kin koma banza a gidan, kuma a kawo wadda ba ta kai ki ba ta zo ta juya gaba dayanmu, har ma da ke ta hanyar ladabi da biyayya, ko kuma kina ji kina gani ki koma bora kowa kuma ya taka ki”.Bilkisu ranta ya gama baci, dan ta manta matsayin Amina a wajen Anas, don haka tana’ mikewa ta dage hannu da niyyar ta mare ta, amma Anas ya yi saurin rikewa cikin dakewar zuciya ya wanka mata mari, yaso Kara mata _ sannan ya nunata da yatsa, yace. .
“Bilkisu iskancinki ya soma isa ta wallahi ni zan yi maganinki tunda abin naki ya soma shige kaina ya dawo kan yayata, in na zura miki ido wata rana ma Momy zaki yiwa”. Bilkisu da kunya duk ta rufe ta da bakin . ciki, ta dubi Anas tace. “Yanzu Anas ni ka mara saboda yayarka?” Anas nan da nan ya ji Www.bankinhausanovels.com.ng nadama ta sauka a ' cikin ransa, domin yadda yaga abin da bai taba gani a idon Bilkisu ba, wato hawaye.
“Kiyi hakuri Bilkisu, wallahi bana so ki raina min ‘yan uwana shi yasa na ke nuna miki hanya, amma...”
“Anas ka rufe min baki, ba na son jin wata magana daga bakinka”. Ta miqe ta rataya jakarta ta yi waje cikin . fushi, shi ma kuma Anas da sari ya mike ya bi ta yana kiranta, amma kota juyo. Momy da ta bi su da kallo cikin fushi ta mike ta kalli Hajiya Ummi ta ce.
“Hajiya Ummi a yanzu na yarda da shawarar da kika ba ni a'baya, don haka Anas zai gamu da ni, wallahi sai yabi ra’ayina dan nice na haife shi”. Zaune take q dakin mahaifiyarta ta hade kai da gwiwa tana ta sharbar kuka ita yanzu bakin ciki goma da ashirin ne ya hadar mata da farko dai abinda anas yayi mata na biyu kuma tunanin kwana a cikin wannan gida na ubanta wanda ko fanka babu ciku balle kuma ayi maganar inji
Ta dago kai ta kalli innarta tana kokarin tuka tuwo ta sake jin wani kunci a cikin ranta shin wai mai yasa ta yanke hukuncin tahowa gida ne? Mai yasa ba zata zauna ta gasa shi ba, gaskia ba zata iya kwana cikin sauro ba don inma ta haqura ta kwana babu yaddah za,ayi ta runtsa kunji fa masu karatu kamar ba gidan ubanta ba ko kuma ba a cikin gidan tayi rayuwa ba tayi saurin mikewa don bin umarnin zuciyarta inna ta dago daga tukin tuwon tace ya naga kin miqe ba cewa yayi zaizo ya daukeki ba
Eh haka yace amman naga dare ya soma yi wata kila wani uxurin yake don haka gara na tafi

Post a Comment for "AFUWA BOOK 1 CHAPTER 1 BY JAMILA HALLIRU G/DUTSE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...