ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dana gaza samarwa kaina wadannan amsoshin guda biyu, sai kawai na fita, ina juyowa muka hada ido yana kokarin fitowa daga nashi dakin janye da (travelling bag) mai matsakaicin girma 'troller' ruwan zuma.

Dammm! Naji kirjina ya buga, bugawar da ba'a kirjin kadai ta tsaya ba ta hudo ne har cikin zuciyata. Sanye yake da riga fara anyi rubutu da shudin zare 'TOMMY HILFIGER' da shudin wandon (jeans) turrare, sumar nan ta kwanta tayi luf a saman kansa sai sheki take, inda duk ya motsa sassanyan kamshin '212' ke tashi.. Ya saya kwayar idanunshi cikin gilashi 'porsche' mai duhu ainun, don haka kai tsaye ba zan iya cewa ga halin da kwayar idanunshi ke ciki ba.

Ya ajiye jakar a kusa dashi ya zauna a kujera sosai ya zage zip dinta, ya ciro katin ATM ya dago ido ya dubeni ina tsaye a inda nake ban ko motsa ba.

"Ko zaki iya zama?" Abinda ya ce dani kenan.

Tamkar wata rakuma da akala na bi umarnin furucin nasa, na zauna a kujerar dake fuskantarsa.

ATM card din ya aje mani gabana, ya yagi takarda yayi rubutu itama ya turo mini.

"Ga PIN dinsa nan na rubuta a jikin takardar na bankin UBA ne, in kina da bukatarsu sai ki kira Shu'aib a waya ki turashi ya debo miki adadin da kike bukata.

Anjima Surajo zai kawo miki waya ni na tafi ban san kuma ranar da zan dawo ba. In kina da matsala ki kira Mama ki gaya mata, Ya'u zai ke kawo miki (recharge-card) duk sati, ban yarda da fita ko bakin (gate) ba in ba lalura ta rashin lafiya ba tunda rayuwar da kika zaba kenan". Ya mike yana zuge jakarsa.

Idona ya cicciko da kwallah. Ba zan ce bai yi min dai-dai ba, kuma bazance yayi min dai-dai ba. Na san akwai hakkokin shi da yawa akaina, wadanda na sanya kafa na shure na take akan sanina, wadanda hujjojina babu ruwan Allah dasu. Auren Fa'iz dake kaina kadai ya sani dole in bude baki yau inyi magana saboda halin rai, yau yake da tabbatas gobe babu shi. Sannan sha'ani na tafiya wanda bana fatan hakan.

Muryata na rawa na ce, "Ga abincinka fa ka karya mana sai ka tafi".

Ya dubemu duka ni da abincin ya hararemu duk da ance aikin banza wai harara cikin duhu don kuwa bakin gilashi ne a idonsa, ya ce.

"Ki rike kayanki, na gode. Akanshi dai kike yi min tsaki in na saki, to insha-Allahu ba zan sake cewa ki dafa min wani abu ba, sai kin ganni ma balle ince ki bani abincin. Zan tafi inda ba sai nace a bani za'a bani ba, balle aje ga goranta min ko yi min tsaki".

"Kayi hakuri don Allah...". Na fadi cikin kuka.

Ya dubeni cikin mamaki, nasan bai zata ba. Ni kuma harga Allah banyi hakan ko fadi hakan don wata manufa ba, sai don kar ya tafi da fushina in kasance cikin fushin Ubangiji da tsinuwar Mala'iku har yaje ya dawo, wanda ban san ranar dawowar tasa ba.

Ya koma ya zauna, sannu a hankali yake zare gilashin idonshi, ni kuma ina ta sharbe. Ya kirani da wata irin kankanuwar murya.

"Fa'izah!".

Na cira jajayen idanuna na dube shi, ban amsa ba amma idanuna sun nuna ina sauraron sa ne.

"Komi ya wuce?"

Ya tambaya.

Na sunkuyar da kai ina jan zaren carpet bance komai ba, amma na daina kukan sai ajiyar zuciya. Ya baro kujerar shi ya iso gabana yayi zaman dirshan, ya kamo hannuna na dama ya sarke cikin nashi. Na dago kai na dubeshi kana  nayi sauri na maryar na sunkuyar. Ko da can bama iya hada ido da wadannan 'sexy' idanun balle yanzu? Da aka samu karin ilhamomi masu yawa a cikinsu?

Ya sumbaci goshina, idanuna, karan hanci da bakin da yakan ce rashin mutuncin dake cikinshi ya fishi girma, mun dade cikin wannan halin, da dukkannin mu bamu taba tsintar kanmu cikinsa ba, zuciyoyi da ruhinmu sun hade sun cure wuri guda, muka samu kanmu cikin mantawa da duk abubuwan da suka faru cikin rayuwarmu. Dai dai lokacin da kararrawar shigowa falon ta soma kara.

Mikewa nayi cikin sanyin jiki, don dama neman hanyar mikewar nake yi na rasa, saboda gangar jikina da zuciyata sun gaza karbar sababbin al’amura masu girma irin wadannan da Fa'iz ke bijirowa dasu a wannan lokacin,  wadanda bazan ce ban sani ba ko ban san sune suke wanzuwa a cikin aure ba. Sai dai ban taba yi ba ko kusantar yi ba a kulliyar rayuwata, daga yarinta har zuwa girma, sai ko yanzu da Fa'iz ke son tabbatar min da cewa, lokacin yin nasu ya zo. Goyon bayana da hadin kaina kadai yake jira, domin tabbatuwarsu, 'and I lack such a courage!' (Na rasa wannan kwarin gwiwar). A ganina ‘it’s not the hightime. ..... (lokaci bai yi ba).

Don haka wanda ya danna kararrawar nan in banyi masa addu'ar alheri ba hakika ya cancanci inyi masa fatan ALHERI. Na bude kofar ba tare da tambayar ko waye ba haka ba tare da waiwayar halin da Fa'iz ke ciki ba, Surajo ne.

Nayi murmushi na bashi hanya ya wuce amma kallo daya zai yi min ya tabbatar a rikice nake, kuma hankalina a tashe yake domin na tabbata ya zo ne domin ya dauki Fa'iz ya kaishi filin jirgi.

"Madam rikici, ke kika rike Pilot ko? Kina sane da cewa karfe goma sha daya zai tashi? Don Allah a ringa lura da lokacin aiki cikin lokutan ayyukan soyayyar kada a koro ko ku koma direban tashar da kuka saba".

Fa'iz ya harare shi yana gyara zaman gilashin sa a kyawawan idanunsa, bisa doron karan hancin sa. Ya kwalawa Ya'u kira, ya shigo da sauri, ya dauki jakar suka fita. Surajo ya aje min kwalin waya (Samsung-tablet) ya janyo kofar falon. Na bisu da kallo cikin shatatowar hawaye dana kasa maida su ko rage gudun zubarsu akan kundukukina. Ko hawayen menene? Bazan iya cewa ba.

                              *****
BAYAN TAFIYAR FA'IZ

Wani ikon Allah ko abin mamaki tun tafiyar Fa'iz sai naji sam bana jin dadin gidan. Kewa da kadaici suka yi min sallama. Da yana nan, ko banyi masa magana ba shi zai mani, zanji motsin dan Adam cikin gidan ta hanyar karakainarsa, a falo da (kitchen) da nasa dakin. Amma yanzu gidan ya zame min kamar makabarta ko motsin kyankyaso babu.

Kusan kullum ina baya wajen Dawisu ina jefa musu abinci, har kujera nake kafawa in zauna. Yanzu har sun saba dani har kofar falo suke biyoni in na haura lokacin da nake fitowa basu abinci. Sai suzo kofar falo su tsaya su bude bindinansu abin ban sha'awa suna juya su gabas da yamma, kudu da arewa cikin nuna baiwar kyan da Ubangiji Ya yi musu da bai yiwa wani tsuntsu a duniya ba.

Yaran gidanmu duka an hana su zuwar mana dagani har Ummi. Haka 'yan uwa ba mai zuwa don kamar yadda na fada a baya sunce sai ranar da suka ganni da ciki irin na Ummi ko 'ya'ya irin na Zaneerah. (In fact) ina kewar Fa'iz duk da bana so na yardarwa zuciyata cewa kewar tasa nake yi.

Duk da bamu dade tare ba, sati biyu kacal muka yi tare, abubuwan dake cikin sati biyun masu yawa ne (it seems like a journey of two year full of blissful adventures) da suka kasa goguwa a zuciya da kwakwalwata. Fadansa na bani dariya, haka kishinsa na babu gaira babu dalili.

In ka debe wadannan na fahimci wasu abubuwa wadanda ada ban sani ba, wato Fa'izu Abubakar, mutum ne mai saukin kai, barkwanci, dadin mu'amala da dadin zama amma fa ga wanda yake so kadai, shi yasa iyaye da dangi duka kowa ke sonsa. Idan baya yi da kai ko ya tsaneka zaka dauka ne cewa babu wanda ya kaishi rashin kirki da rashin dadin mu'amala a duniya.

Hakazalika yawan kiran sunana da yake yi cikin gidan Fa'izah-Fa'izah-Fa'izah kai kace shi ya rada min suna Fa'izah ko Aunty Fa'izah.

(I also missed his regular sayings) "O.K?" Wannan ban san me take nufi ba har ya zamanto nima ta zauna min a baki ko magana na yiwa Ya'u na gama sai na ce "o.k?"

A da kam nasan ba haka Fa'iz yake ba sam, magana ma wuya take masa balle mu'amala da mutane, ban san sanda bakinshi ya bude ba domin ada sai ya wuni baiyi magana ba.

Ina kewar Fa'iz ne a bisa dalilai da yawa dani kaina ban san adadinsu ba, ko ba komai ina jin motsinsa cikin gidan da maganganunshi ko a waya ne nasan dai ba ni kadai bace cikin gidan. To amma ya tafi, ya bar min kangon gidan da abin da ke cikinsa, gidan yayi shiru, yayi tsit sam babu dadi kamar babu mahalukin dake rayuwa a cikinsa.

Ina kwance tsakiyar kafet din falona na tada kai da filon kujera kwanaki uku da tafiyar Fa'iz, aka danna kararrawar son shigowa fallon. Daga nan inda nake kwance nake tambaya,

"Waye?"

"Ni ne Shu'aib".

Na bude ina dariya, "Yaya Shu'aib kaida wa?" Shima dariyar yake yi, ya shigo na bashi hanya ya wuce ya zauna a kujera muka soma gaisawa. Sannan ya ce.

"Yaya Fa'iz ya turo ni inzo in karbi ATM dinki in amso miki kudi a bankin UBA ko kina da bukatarsu, in kuma hada miki (tablet) dinki in sanya miki 'Interner data' in dora ki akan 'social networks' akwai 'group' na A.B family a (whatsapp) kowa yana ciki ki dinga hira da 'yan uwa madadin kiyi ta zama shiru".

Ban yi musu ba na mike na dauko masa 'Samsung tablet' din na kawo mishi ko ni zanso hakan. Amma jaganar karbo kudin a UBA na ce.

"Shu'aib bar kudin nan a muhallinsu, me zanyi dasu? Bana bukatar komi sai abinci gashi nan dankare nau'i-nau'i a 'store' da 'freezers, ga Ya'u na kawo katin waya. (I need nothing)".

Ya gyada kai cikin gamsuwa, hannunshi da idanunshi akan tablet din yana ta shiga 'applications' muna ci gaba da hirar mutanen gida da na Giwa.

Na mike na kawo masa lafiyayyen 'yoghurt' din 'L&Z Dairies' dake cike da (fridge) dina da sabon cup-cake din da nayi jiya.

Na ce, "Shu'aib, ina Hajjaty?" Sai bayan da na fada ne kunyar kaina da nadama suka zo suka rufe ni, muryata ma a lokacin tayi kasa sosai.

Dariya yayi, "Hajjah tana nan lafiya ko jiya na je Giwa sun tafi Umrah ita da Baba Na'ibi".

Ya cigaba da shan L&Z Dairy yana lumshe ido saboda gardin madarar ya aje gorar, ya ce.

"Wai kuwa don Allah Aunty Fa'iza yaya kike yi Yaya Fa'iz yayi miki magana?"

Shu'aib kusan sa'a na ne domin bai fi shekaru biyu ya bani ba, tsakaninsa da Fa'iz kuwa shekaru bakwai ne , mukan tattauna matsalolinmu da junanmu tun sanda muka fara hankali.

Nayi murmushi na ce, "Kamar Yaya Shu'aib?"

Ya ce, "Yo mutum ba fara'a kullum fuska kamar bindinga, babu alamar rahama sai muzurai. Duk inda yara suke ya tashe su. Shi ne nake mamakin yadda zai zauna da iyali yayi mu'amala ta dadin rai dasu. Don na tabbata in ba mace mai tsantsar hakuri ba, babu wadda zata iya daukar ginshirar Yaya Fa'iz ...".

Dariya nayi, "Baka da dama Shu'aib! Ni dai toh!! Ba zan ce baya magana ba, amma yafi yi a waya da abokansa!!!:.

Na jawo wata hirar don hirar Fa'iz da yake sani ya na sanyani cikin wani hali, da ni kaina ban san shi ba. Ban san irin shi ba, mai wuyar fassarawa ne.

Har la'asar muna tare da Shu'aib bayan ya hada min 'Whatsapp, wattpad, Facebook, Twitter da Instagram. Sannan ya zuba min duka numbobin 'yan uwa, muka yi sallama na juye duka 'cup cake' dinnan nace ya kaiwa Mama. A ranar na soma (chatting) dasu Ummi nima da (family group) dinmu ta watsapp.

Sati biyu bayan nan Mama ta sake aiko Yahya ya kawo min wasu jarkoki cike da magani mai zaki wai Mama ta ce in sanya a (fridge) in maida su ruwa sha na (tsumi). Da zuma iri-iri 'yan asali da abubuwa dai daban-daban wani ta ce asha da nono,. wani da peak-milk. Zuciyata tayi ta raya min meye nufin Mama na bani wadannan magunguna? Amma da nayi tunani mai zurfi Mama dai uwata ce wadda ba aurena da Fa'iz ne ya hadamu ba.

Mama uwata ce ta tun fil'azal ba zata bani abinda zai cutar dani ba, sai na dukufa shansu dare da rana yadda tayi 'prescribing' kowanne a rubuce a 'yar takarda har suka kare.

Satin ya kare ta sake aiko da wasu, haka muka yi tayi har watanni biyu.

Rannan a (chatting) nake tambayar Ummi ko tasan magungunan mene ne mama ke dirka min? Ta ce in fasalta mata su. Na fasalta har 'prescription' dinsu. Tayi alamar dariya ta hanyar turo 'emotions' na dariya ta ce.

"Mama nayi mana gatan da Hajjah, Aunty Hawwa da MOmin ABU suke kunyar yi amna. Ke dai kiyi ta sha Fa'izah ba zai cuce ki ba. Nima nan haka take aiko min dasu jarka-jarka kulli-kulli. Kiyi godiya kawai ga Allah da yayi mana baiwar uwar mazaje tagari mai kaunarmu tsakani da Allah.

Daga nan Mama ta koma aiko turaruku iri-iri 'yan Borno. Ni kam karba kawai nake ina faman turara daki. Amma sai Mama tayo waya ta ce.

"Fa'izah! Turarukan dana aiko miki fa ba na turara daki bane, jikinki zaki ke turarawa, kullum da yamma bayan kin fito wanka. Akwai abin turaren wuta na lantarki (burner) cikin lokas din (kitchen) dinki ki dauka kiyi amfani da ita, nasan hankalin ki bai kai wurin ba".

Na ce, "Akwai wata dana samu ne a falo da ita nake amfani, insha-Allah zanyi yadda kika ce. Mama Allah Ya kara girma".

Murmushi tayi ta aje wayar.

Tunda nayi nisa a sha da amfani da magungunan da Mama ke aikowa, sai na soma samun wani irin sauyi a jiki da zuciyata. Na nemi kiyayyar da nake yiwa Fa'iz na rasa tana (decreasing gradually) a kullum. Sai wani irin bege da son ganinsa. Da tsananin son kebewa dashi da son jin koda muryarsa ne amma babu. Tunda ya tafi ko sau daya bai kira ni ba har na soma zargin anya ba asiri Mama ke yi min ba, inso danta in kaunace shi? Nayi saurin kawar da wannan tunanin tare da yin istigfari a zuciyata.

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...