ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7  by Sumayyah Abdul-kadir
             Www.bankinhausanovels.com.ng 
kin gane?" 


Ummi ta tafa hannu tayi dan fitoo, ta ce. 


"Yeho! Yarinya wallahi kinci a baki kyautar amsarki. Indai wannan shi ne hauka, don Allah a nada min sarautar mahaukatan duniya akan umarnin iyayena nake ba kuma zan taba ganin ba dai-dai ba, tunda na bisu, su nakewa biyayya. 


Ke kuma mai hankalin da yafi na kowa da kika tasarma kisan kai fa? Waima tukunna ina hankali ga matar da ta titsiye mijinta da duka da zagi ya saketa? Matar da ta dauki kwalba ta rotsawa mijinta ai ta tabbata tsinanniya”. 


(Baki kasan me zaka fada baka san me za'a mayar maka ba-TAKORI). 


Zaneerah ma aka cire mayafi aka jefo min. Eh naji kamshin (212) din yaya Aliyu kam babu shakka amma itama ta cancanci a tanka ta duk dai da ban san ita din dame zata mayar min ba. 


"An dai ji kunya wallahi, tsofai-tsofai ga goyo ga tirtsetsen ciki amma ba'‘a fasa jaraba ba, shima Yaya Aliyun...”. 


Daga labulen dakin yayi yana fadin. 


“Zaneerah ina wayata da na baki ki sa min caji?" Dif! Kake ji na dauke wuta, kamar ba ni ce mai magana ba. Ya dube mu suna ta sheka dariya kamar sun samu motsatstsiya ya ce. 


"Me take cewa ne?" 


Na mike gaba-gadi na dauki dankwalina na daura na bar musu dakin. Ina jinta tana cewa dashi. "Zaginmu take yi". 


Ya ce, "Baya tsiro ai, da tuni jikin nata mijin ba masaka tsinke". 


KK 


WwW 


ashegari tun safe su Ummi ke shirin wucewa Kaduna liyafa, sai shirya kaya ake ana zuge (troller). Motocin da za su kwashe su zuwa Jabi Road basu zo ba sai bayan azahar suka shiga suka tafi da kawayenmu duka daga can ne za su shirya zuwa wajen da aka tanada don yin liyafar. 


Ina kwance a doguwar kujera ban ko motsa ba ina kallon fitarsu daya bayan daya. Yaya Aliyu ya shigo yana balle ‘links' din hannun rigarshi ya ce da Zanirah. 


"Madam, muje ko?" 


Ta tashi wata tikisa da ita kamar alkubus, shi kuma aka sakalo hannu kugunta aka tallafeta, a haka suka fice ko kallona basu yi ba, suka fice. Inda ya bude mata gaban ‘Porsche’ dinsa ta shiga, ya rufe ya zagaya shima ya shige. Bashir aka kama hannun amarya mai kama da Princess Diana don kyau da daukar ado suka fice. Har sun kai kofa ya juyo yana ce da ni. 


"Af, gwauruwa, mijin robarki fa yana jiranki a waje Yaya Sa'idu, an baki kaya don kidifiri kin ki amsa. No worries, na jikinki ma inaga ba laifi, kya samu waje ko tebirin iyaye da su". 


Wani gululu yazo ya tokare ni yaki wucewa, ya tsaya min a makoshi, amma Fa’'izah (is always) Fa'izah, ina da ‘ki-fadi' sai na ce. 


"Allah Sarki Yaya Bashir ka sallami mijin robar Fa'izah ko babu shi Fa'izah (can survive), kasan mace Allah Ya yi mata juriyar iya rayuwa ba tare da namiji ba, namijin ne bai iya rayuwa mai dadi 


sai da mace. I.e namiji zai saki mace, ta zauna gidan iyayenta ba tare da ta yi wani auren ba kuma ta zauna lafiya. Amma shi namiji a ranar da yayi sakin ma zai iya kawo wata, ka gane?" 


Ya ce, "Ohonki kuma! Tsoron shan kunya ya hanaki zuwa (party) baki da sauran bakin surutu”. Da haka ya fice. 


Na mike tsam bayan fitarsu nayi wanka, na dauko lesi na na sanya, na saki dogon gashina a gadon bayana, na karkata goggoro na tsayar dashi dai dai goshi na. Na janyo takalmi da jaka na cikin kwalinsu mai tudun dunduniya siririya da siririyar igiyar daurewa na fitar na sanya, na rike ‘purse’ din mahadinsa wadda kudin mota kawai na zube a ciki. Nan da nan na hau walkiya kamar wata dan daren goma sha hudu. 


Na kawo (fashion earing) kalar adon lesin na daura (shimmering pearls) hannu, wuya, kunne da idon sawu sai walainiya nake duk motsin da nayi. Ni kaina yau nayi mamakin yadda nake, ban taba tunanin haka Allah Ya kyautata surata ba sai yau. 


Na fito harabar gidan Baba Na'ibi babu kowa don haka na tura wani almajiri yayo min hayar taxi kafin minti goma sai gashi ya dawo cikin motar tare da mai taxin. 


Na ce da mai taxin ya yi duk iya gudun da zai iya ya kaini (Indoor-sport hall) na garin Kaduna cikin awa daya, ko nawa ne zan biya shi. Nan da nan ya ce in shigo mu tafi. 


Dakin taron ya cika ya batse babu masaka tsinke da kyawawan iyalin A.B tabbacin a yau 


—_ 


mallawan na biki kasurgumi da basu taba yin kwatankwacinsa ba. A cikin tafiyar nutsuwa na shiga ratsa taron jama'ar suna kallona tabbacin basu tsammaci zuwana ba ma balle wannan shiga ta firgitarwa. Ashe wajen cike yake da abokan Fa'eez na Kad-Poly irin su Surajo Nuhu wanda a halin yanzu ma’aikaci ne a Central Bank da wasu daga cikin abokan su da yawa suka mike suka tarboni muka jero tare sai tafi suke yi da dariyar farin ciki, yayin da Sa'adu Bori dake cin kasuwarsa a wajen ya karkatar da akalar wakarsa gareni ya kyale su Ummi, cewa yake. "TAKAWARKI LAFIYA GIMBIYAR ABUBAKAR FA'TIZU GIWA... AMARYA FA'TIZA AMANAR FA'IZ GIWA...". 


Suraj tunda na tako kafata cikin (hall) din yake min (spraying) da dollers madadin Fa'izun su kenan. 


Ni kam ko a jikina, a raina fadi nake wahala ce bata ishe ku ba, ko kallo basu isheni ba. 


Wajen ya hautsine da kirarin abokan Fa'iz masu video da masu camera suka juyo da akalarsu kanmu gaba daya abokan Fa'iz daukana suke hotuna wasu vedio da wayoyinsu. Ina kallon bakin su Yaya Aliyu dake (high-table) yaki rufuwa, haka Mama da tarin hamshakan matan Kaduna da ta gayyato. 


Anan Yaya Rabi, Aunty Hauwa da Mama da kanta suka taso suka tarbeni suka hana ni isa ga mazaunin su Ummi. 


Girgiza kai nake cikin son kecewa da kuka ina yi musu nuni da ka su barni in wuce, amma sunki 


—_ 


hakan. Mama ta rikeni gam-gam, haka Ummi da Bashir, Zanirah da Yaya Aliyu tasowa suka yi daga mazauninsu ya saura babu kowa a gaban Sa'adu bori cikin filin sai mu ‘ya'ya da jikokin Hajjah da kawayen Maman Kaduna sai ko Surajo da ya rufa min asiri suka shiga yi mana "spraying” ni da Surajo sai ka rantse da Allah shi ne angon nawa, kazalika Ummi da Bashir, Zanira da tirtsetsen cikinta da Yaya Aliyu rungume da ita, duk suka bude bakin jaka suka shiga yi mana ‘spray’ tako'ina. Dadi ne ko mene ne ya yi min yawa, sai gani kuka ya kece mani. 


Tausayin Mama har kokon raina da jinjina kaunar da take mani na kasa jurewa nima ban san dalilin tausayin nata da ya rufeni ba, na zame da gudu na karasa mazaunin su Ummi na zauna na kifa kaina a tebirin na shiga kuka mai yawan gaske wanda ni kaina bansan dalilinsa ba. 


Suraj ne yazo ya zauna a kujerar Yaya Bashir ya ce. 


“Fa'izah, Fa'iz bai kyauta ba na sani, don me ya yi mana haka? Rana irin wannan mai dumbin tarihi ka tsallake ka tafi wani aiki kai kafi kowa aiki?" Haushinsa ya kara kamani da shisshigin da yake ta yi mini tunda na sako kafata a filin wajen nan shi bai yadda ba asiri ya rufawa abokinsa, kuma abin kirki yayi. 


Na dago idanuna jike jagab da hawaye, 


"Kada ka kuma yi min zancen wani Fa'iz, nazo (partyn) nan ne don Ummi da Bashir, don me zaka zo kana tambaya ta wani Fa'iz bayan mun rabu tuntuni?" Dariya Surajo ya yi, "Aradu 


— = 


bonono Fa'iz yayi miki wai rufe kofa da barawo, waye ya ce miki Fa'iz zai iya sakin ki? Ko jiya shi ya kirani daga England ya ce in taimake shi inzo in tsaya tare da ke, bai yarda da kowa ba cikin abokanmu sai ni. Wane irin saki babu ko dadin ji? Kina hauka ne?" 


Wani irin rugugi naji cikin kwanyar kaina, da kyar in ba motsin kwakwalwa bane. Na zazzaro ido ina duban Surajo ina auna abinda yake fadi cikin hankali da tunani. Nasan Surajo mutum ne mara wasa, na sanshi da can don ya so Ummi aka nuna ba za’a bashi ba ya hakura. 


Abubuwan da suka faru suka shiga dawo min sabbi kar, wato yanayin Fa'iz bai nuna damuwa ko bacin rai ba a sanda yake min rubutun cikin takarda, babu wata alama ta nuna damuwa a fuskarshi. Me ya hana Baba bai lallasa ni ba, kuma su Aunty Rabi babu wanda ya yi fushi dani a lokacin? Sai ma cewa da tayi in taso mu tafi bikin Ummi Giwa? Me ya hana ni karanta takardar da kaina abin kamar tsafi?" 


Raina ya yi mugun baci, hankalina ya jirkice, idanuna suka kada suka yi jawur suka wani irin cicciko da kwalla. 


Suraj Nuhu, ya yi danasanin karambaninsa, ya tabbatar ya yi babban kwafsi, kuma abinda ba'a aike shi ba don son ya burge. Ya shiga in-ina yana fadin. 


"Fa'izah da gangan nake, na rantse miki bamu yi maganar komi da Fa'iz ba, ni na kawo kaina...". Ina! Surajo ya barota domin kuwa mikewa nayi gaba dayana tsam nayi hanyar fita, yayin da ya 


—_= 


biyoni yana magiyar in saurare shi, amma kurar da ta debo shi ban kalla ba. 


Su Ummi suka dakata da abinda suke yi suka biyo mu da idanu. Aliyu ya saki hannun matar shi ya biyo bayanmu, ya rigo hannun Suraj ya ce ya rabu dani, kana ya haushi da fadan. 


"Don me yasa ka gaya mata Surajo? Wa ya aike ka yi mata zancen Fa'iz? Ka san haukar Fa'iza kuwa? Muna zaman zamanmu lafiya ka sayo mana tashin hankali". 


Surajo cikin matsananciyar nadama ya ce. 


"Ni ina na sani? Na gaya mata ne kawai Fa'iz ne ya yi min waya cewar yana Wales inzo in tsaya da ita, shi kenan abinda na fada”. 


Yaya Aliyu ya dafe kai yana fadin, "Shi kenan Surajo ka baro mana likin, sai gyaran Allah. Wallahi ko lallashi ba zan je ba ta je can duk inda zata je zata dawo da kafafunta, ai ba yau ta fara ba”. 


Da daren washegari aka raka Ummi gidanta a Kabala Custain. Washegari Zanirah da Aliyu da ‘yarsu Fa'izah suka wuce Lagos, na Giwa suka nufi Giwa, na Zaria ma haka, haka na Kaduna. Miftahu da Ya Rabi suma suka dauki hanyar Kano da yaransu biyu, amma Ya Rabi ta ce da Yaya Mufty su tsaya Zaria su ga halin da nake ciki. 


Hajja kam ta ce da su don Allah kowa ya kyale ni inyi kida na da rawata ni kadai, kada wanda yaje inda nake balle ya wani lallasheni in bata masa rai a banza. Amma Ya Rabi ta kasa jurewa. Ko cikin 'ya'ya Fa'iza ta daban ce a wurinta, tana da 


matsayin da babu mai shi cikin tarin 'ya'yan nata. 


38 OK OK a na baro Indoor Sport Hall Zaria na nufa a taxi bana ko ganin abinda yake gabana don tsananin takaici da tashin hankali. Fatana inga takardar sakin nan nawa da idanuna in karanta abinda ke ciki. Har aka zo kofar gidanmu ban sani ba ina sharar hawaye da dankwalin leshi na, sai da mai taxi ya ce. 


"Hajiya, ba nan ne gidan ba?" 


Na bude na fita na fiddo kudin da ban tsaya kirgawa ba na dai tabbatar yafi abinda zai nema na zube mishi a kujerar gaba nayi ciki. 


Na danna kararrawa (door bell) Momi ta zo ta bude duka hannuwanta cude da fulawa ina jin alkubus take yi. Ganina haka hajaran majaran fuska babu alamun rahama ta tabbatar cikin ranta da kyar in ba (bomb) din ne ya tashi ba. Ta matsa min hanya na shige, ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. 


Gidan babu kowa sai Walid autan Momi, duk suna Kaduna cin biki. Na fadi nan bisa carpet na shiga kururuwa kamar na rasa iyayena biyu a lokaci daya. 


Momi bata ce min cikanki ba, haka ko lekowa bata yi ba. Wannan ya kara kunna ni, na mike na shiga tamaula da kayan falon su filillikan kujera, flower rose. Ganin ina shirin yi mata ta'adi da kayan kallonta ta fito a fusace ta nuna ni da yatsa. “Wallahi-wallahi ki kiyayeni cikin gidan nan, 


kinga dai babu kowa, babu mai kwatar ki don haka sai inyi miki dukan tsiyan da zai taimaka ya dawo dake cikin hankalinki, don da alama Fa'izah ke dabba ce, dabbar ma ta daji wadda bata san ciwon kanta ba. Allah Yasa Fa'izu yankan kai yake yi, ya yanke naki kowa ya huta wannan bala’in". Na hade kaina cikin gwiwa bayan nayi fatali da goggoron. 


"Momi bai kamata kice min haka ba, duk abin nan da nake yi saboda in kare mutunci da martabar ki ne daga idanun wanda bai san kina da su ba, don ni ta tawa mai sauki ce ban dauki kaina a bakin komai ba balle in dauki wulakancin da Fa'iz ya shekara yi mini abinda zai hana ni shakar numfashi a duniya. 


Ba zan taba son shi ba Momi, ba zan taba ganin farinshi ba tunda ya wareki daga cikin iyayensa. Duk abinda yayi min a baya kin manta Momi...". "...Na manta don ubanki, sai ki sani in tuna! Wallahi ki ka sake yi min kururuwa a gida sai na kakkarya ki, kin kuma koma inda ki ka fito kinji na gaya miki". 


Sai na tura kai cikin kafafuna nayi ta rasgas kuka a hankali, babu mai lallashi balle wanda zan yiwa in huce. A kuma yanayin Momi na na tabbata zata aikata abinda ta fadi na sake na sake daga mata sauti. 


A haka Babana ya taddani, ya zauna cikin kujera yana fadar. 


"Kiyi kukanki mai dalili, yi kukanki da babbar murya Fa'izu bai sake ki ba! Da yake shi ya haifu cikin uwa da ubanshi ya san darajar iyayenshi da 


—_ 


karfin ikon su a kansa. Allah Ya dawo dashi lafiya kafarki kafarsa, inda duk ya sanya kafa na rantse da wanda raina yake hannunsa". 


3K KK wana biyu aikina kenan ina abinda naga shine rangwame a gareni wato (kuka) duk na koma jemammiyata ta baya a dakin Abdallah. A haka ne Ya Rabi da Ya Mufty, kan hanyarsu ta komawa Kano sai gasu a Zaria, Aunty Rabi ta shigo ta iskeni dakin Abdallah, ta aje mayafinta da babynta akan gadon Abdallah, ta ce. 


"Kai! Fa'izah bakya gajiya, zuciyarki bata gajiya da kuntatawa kanta a banza a wofi alhalin hakan ba zai sa ba, kuma ba zai hana ba! Shin duka wannan na kiyayyar ne, ko na haushin Fa'iz dan albarka bai yi saki ba?" 


Nayi banza da ita, can kuma na ce. 


"Ki bani takardar in gani da idanuna”. 


Da murmushi fal a fuskarta ta ciro takardar a jakarta ta ce. 


"Gata". 


"Don haka in zaki hutar da kanki da zuciyarki to ki hutar, in kuma kina ganin kukan ki da tayar da hakarkari da hankalin ki shi zai sa Fa'eez ya yi saki to anan kam kinyi kuskure. Haka in ma duka da kwalba ne shima aikin banza za kiyi tayi don kuwa Fa'iz jinin Hajjah ne, rabin zuciyarta, magajinta. Idan ya ce ‘eh’ baya taba dawowa ya ce, 'a'ah’. 


Shin don Allah in tambaye ki, meye abin ki ga 


Fa'iz?" 


Na dago sharkaf da zufa, kashirban da hawaye da majina bayan na karanta takardar. 


"Ai ba zaku taba gano aibunshi dani nake hangowa ba tunda danku ne, ba kuma ka taba ganin aibun danka komin muninshi ko munin halinshi. To tunda ba zaku gani ba da duk hujjar da na kawo to ni na tsane shi ne, bana sonsa, fakat! Da inyi zaman aure dashi gara min zama a dokar daji da bakin-kumurci. Allah da Ya halicce ni Shi Ya daura min kiyayyarsa da duk wani mai irin halayyarshi. 


Yadda kuma ake ikirarin shi jinin Hajja ne baya magana biyu sai a gaya min in ni tawa uwar shege na tayi ta kawo muku". 


Ya Rabi ta jinjina kai cikin kidima tana fadin. "Babbar magana. Ni na kawo kaina, dama ba yadda Hajja bata yi dani ba kar nazo ke mahaukaciya ce amma banji maganar uwata ba dole naji wohoho! Sai ki mutu kuwa! Muddin Fa'iz ya dawo kafarki-kafarshi zuwa Russia, wallahi nima na daina lallaminki, mu zuba mu dake aga wanda ya haifi wani. Dabba kawai, shashasha, mara hankali". 


Na ce, "Ko uwar Rasha ne ba zani ba, wallahi ba zani ba ko gunduwa-gunduwa za’ayi dani". 


Rabi tayi dariya, "Ai har uwar Rashar ma zaki, tunda matukin jirgi kike aure ina ne ba za'a saka ki a jirgi a kaiki ba?" 


Na ce, "Koda na rasa bawan Allah Dr. Nazir, mai ilimin da ya amsa sunan ilimi, banga me zanyi da direba ba Ya Rabi. Kamar ni in kare a mutumin 


da bai da ilimin komai sai na tuki? Direban tasha, wallahi na yi asara!!!". 


Rabi ta ce, "Kin kuwa yi asarar. Yanzu ke ko babur zaki iya tukawa ne balle aje ga mota zuwa jirgi? Ke kinga shegen bakin ki baya mutuwa, ni na gaji da magana don ba malamar jami'a bace. Ranar da ki ka bi Fa'iz daga ke sai shi na tabbata murus bakin zai mutu mu don kin raina mu ne ki ka cika mana kunne da babatu. Don haka sai anjima, mijina yana jirana. Sai mun zo rakiya filin jirgi...”. 


Tamkar ta soka min mashi a kirji haka naji. 


"Ko kuma an aiko muku da sakon mutuwar danku kunzo zaman makoki ba? Ki sani, ranar da duk Fa'izu ya yi gigin sake sako kafarshi cikin gidanmu kamar yadda na dauke kafata daga nasu gidan, wallahi sai buzunsa Ya Rabi!". 


Ta ce, "Ko? Lallai kin fitsare, inama ina nan za‘ayi wannan (BOXING)? Kai da na kadawa (Winner) tuta. In kuma kanwar ta kar tsamin ne sai kiyo min waya inzo jinyarki”. 


2K KOK aman Zaria fa yayi min zafi, Walida, Abdallah duk suna makarantar kwana. Kausar da Walid makaranta suke zuwa safe da yamma. Babu Ummi babu Zanirah balle tsohuwa Hajjah mai samu farin ciki. Ko da yake Hajjah ni na gujeta don a ganina ita ce ummul-haba'isin sanya rayuwata cikin halin kuncin da take ciki bayan shafa min bakin jini da hakan ya yi a idanun 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...