ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 6  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 6  by Sumayyah Abdul-kadir


              Www.bankinhausanovels.com.ng ke ta fadace-fadacenta wanda ko a kwala ta. Kukan rashin Nazir nake baka da zuci, na jiyo muryar Ya Rabi na cewa. 


"Shima Fa'iz ya yi karamin tunani, ba'a biyewa mace, da maza na biyewa mata da cikinmu babu wadda ba bazawara ba. Idan hankali ya bata shi ake sawa ya nemo shi, haka nan komai aka yi shi cikin fushi, sai anyi nadamar aikata shi". 


Ashe Momi na hawaye take yi, can na jiyo tata muryar tana fadin. 


"Yo ai shi kenan, sai ta yi ta zama idan zaman gidan iyaye dadi ne ga baligar mace. Duka sa’o'inta babu wanda ya ba da kunya sai Fa'izah Bakin Buni Bata Baibaya a cikin A.B. 


Fa'izah bata dauko zuciyata ba sam, zuciyata mai tsafta ce da ban taba kwana da wani a cikinta ba balle in tashi da shi tsayin shekaru a cikinta. Duk wanda yayi min ba dai-dai ba ko nice da gaskiya uzuri nake yi masa da ajizanci irin na dan Adam. Dukkanmu masu kuskure ne da gazawa a wani bangaren, balle Fa'iz akan Fa'izah ne kawai za'a ce bashi da kirki. Na kuma yi mishi uziri tun a wancan lokacin da rashin haxuwar jini ne kawai, ko cikin 'ya'yanka ba ma 'yan uwanka ba sai kaji wani yafi kwanta maka. 


Da babanta ya ce min Fa'iz ya ce Fa'izah yake so da aure jikina ya bani akwai wani al'amari mai girma tsakanin Fa'iz da Fa'izah da babu wanda ya sani sai Allah. Nayi addu'ar Allah Ya hadasu da alherin dake tare da junansu, Ya rabasu da sharrin juna Ya kuma sanya albarka a cikin aurensu. Amma ga abinda Fa'izah taga ya fiye mata, titsiye 


— = 


miji ya saketa. Ba zan yi mata baki ba sai dai duniya kanta makaranta ce mai azuzuwa kalakala. Kuma na roke ki Rabi, kada ki sanya sunana cikin sha'anin nan, har gobe ni ‘yar kallo ce a cikin al'amuran ku, ki bar iyayenta suyi hukuncin da ya dace da ita”. 


Momi ta share hawaye. 


"Babu wadda ta baiwa uwarta kunya a cikin A.B sai Fa'izah don ta tabbatar muku da gaske ni bare ce a cikin ku...”. 


"Ki bar fadin haka Aunty Maimuna". 


Rabi ta katseta cikin jin tausayi. 


"Dole ince haka Rabi, shin da me zan doshi babanta da shi yau ya yarda ban san da zaman Fa'izah cikin gidana ba? Duk muna zaune aka yi saki akan idonmu, wallahi duk mu za su dorawa laifi...". 


Bata idasa maganarta ba tayi shiru saboda sallamar Baba. 


Prof. Ahmadu A.B, ya shigo da sallama, duk ya rame yayi duhu saboda tashin hankalin rashin sanin halin da nake ciki, da kuma ina na shiga. Ya samu kujera gefen Momi na ya zauna, ya ce. "Wash Allah! Taimaka mini da ruwa mai sanyi Mainmunatu". 


Momi ta mike tayi (kitchen) don ta kawo masa ruwan, sai a lokacin ne ya lura da autar Hajja a gefe, ya ce. 


"A'ah! Rabi yaushe a garin? Kin zo kuma kin tadda tashin hankalin da diyarki ta saka mu ciki ko? Fa'izah ta bani kunya, ta bada min kasa a ido. Ban taba zaton tana da wannan halin ba na kafiya 


da kekasasshiyar zuciya wanda ba’a taba samun irinshi a zuri'ar A'B ba. Sai dai ta wani bangaren na yi mata uzuri tunda ance Barewa bata yi gudu danta ya yi rarrafe ba, kuma duk abinda ka yiwa iyayenka ko bajima ko ba dade naka 'ya'yan za suyi maka (auren Momi da yayi ba tare da yardar nashi iyayen ba). Allah Ka bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya, ameen. 


Rabi ta ce, "Ai tana nan cikin gidan dakin Abdallah, ba wani waje taje ba. Sai dai Fa'iz din yazo ya saketa har nan”. 


Baba ya zabura ya mike, "What! Shi Fa'izun ne ya yi mana haka? Duk ta da hakarkarin da nake yi akan auren nan, tunda aka fara maganar auren nan bamu ci abinci ni da ubansa ya fada mana ba, shi ne ya biyewa shirmenta?" 


Momi ta karaso da gorar ruwan 'Rogolis' da tambulan din karau a hannunta da gorar lemon (Salive) ta aje a gefe don tasan bacin ran da Baba ya samu kansa a ciki ba zai barshi ya sha ruwannan da yake son sha ba. Bacin ran ya kashe kishirwar. 


Ta ce, "Kada kaga laifinsa Baban Abdallah, ta nemi rabashi da ransa in bai saketan ba me zai yi mata ya ceci kansa? Rotsa masa kwalba tayi aka fa?" 


Baba ya mike yana salati, ya kara da. 


"Innalillahi wa inna ilaihi raji‘un! Tana ina tambadaddiya ku gani in babballata itama jikinta ya gaya mata, kisan kai zata yi? Shi kuma ya tsaya yana kallonta?" 


Rabi ta tabbatar muddin na shiga hannun Baba a 


wannan lokacin sai tarihina yadda komi nashi yake tsima kamar ana kada mishi gangi, don haka ta tare kofar dakin Abdallah tana fadin. 


"Yo Yaya in ka daki Fa'izah a yanzu aikin me aka yi? Wacce riba za'a ci? Baka huce ba tunda aikin gama ya gama, bakin alkalami ya bushe. Mu duba takardar idan ya yi na Musulunci ayi kokarin gyarawa". 


Ta shiga wurga ido neman inda ta cilla takardar saboda tashin hankali, kafin ta ganota a tsakanin kujerar da take zaune. Baba da kyar ya zauna a kujerar da ya mike sai wata irin zufa yake yi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, duk ilahirin jikinshi rawa yake. Ya karbi takarda daga hannun Rabi ya warware, ga abinda dansa Fa'izu Abubakar ya rubuta cikin takardar. 


Baban Giwa ko Baban A.B.U. 


Fa'izah ta takura min in saketa alhalin ban iya hakan ko giyar wake na sha. Igiyar aure dai kowa ya sani uku ce, to ni Fa'izu Mukhtar Abubakar na ninka (ribanya) igiyoyin aurenmu da matata Fa'izah Ahmad Abubakar ukku sau uku =(9) kenan. 


A kara tausar Fa'izah don Allah kada wanda ya kara dukanta indai akaina ne, domin nayi mata laifin da na cancanci horo daga gareta fiye da wannan da take mani. Ko kun manta baya? 


Na tafi kasar Ingila saina dawo a san abin yi. Danku, mai neman albarkar ku. 


Fa'eez Giwa. 


Nan da nan Baba ya washe baki yana dariya, ya kuma mikawa Rabi takarda. Cikin zumudi ta karbi takardar tun kan ta gama taya yayanta dariyar farin-cikin da yake yi, tun kafin ta kare karantawa take dariya har ta gama. Kana ta mikawa Momina itama ta karanta duk suka sa dariya. 


Rabi ta ce, "Aje a hakan, kada wanda ya ce mata ba haka ba. In ya dawo ya fada mata da kansa ". Baba ya yi dariya a zuciyarsa hamdala kawai yake yi. Ya dauki ruwansa da Momi ta aje masa wanda ya kasa sha ya shanye tas, ya dau mukullin motarsa ya fice zuwa masallaci. 


Ya Rabi ta kalmashe takarda cikin jakarta ta shigo dakin da nake tana yatsina fuska. 


"To Gimbiyar bala'i, in kin ga dama ki taso mu wuce Giwa tare ko hankalin gyatumar bayin Allah Ya kwanta, jininta da ya hau ya sauka saboda kaunar ki alhalin ke din ba kya son kowa sai kanki, har kuwa da iyayen da suka yi nakudar ki suka haife ki. Gobe ake yinin Ummi bai kamata ace babu ke ake yi ba koda yake ke zakka ce". 


Na yunkura ina fadin, "Zuwa kai kamar da kasa, sai dai wallahi ba zan kwana gidan Hajjah ba sai dai gidan Baba Na’ibi?". 


Ta ce, “Yanda kike so ai haka za'ayi miki don 


kam kinfi karfin kowa". a KK 


A GIWA 


WwW 


ashegarin ranar ya kama yinin bikin Ummi. Ni, amaryar kanta da Zanirah da sauran kawayen amarya duka gidan Baba Na'ibi muka kwana. Babu wanda ya nuna min wani canji ko a fuska ko a mu'amala kamar komi bai faru ba, ashe Ya Rabi ta bi ta bayan gida ne ta yiwa kowa bayanin yadda abin yake. Duk da babu wanda ya nuna min wani abu ko alamar jin haushi ko ta da abinda ya gabata ni din akan kaina jina nake wani irin sukuku! Duk jina nake kamar bare a cikinsu, kuma kenan ashe abinda nayi din ban kyauta ba kenan tunda nake jin kaina matsayin mai laifi a garesu da babu wanda ya budi baki ya ce nayi laifin. Gani nake kamar dukkansu A.B kallon tsana da kyama suke min tunda na ki dan uwansu na kawo sauyin al'amari cikin zuri'ar su wanda tun Ahmadu A.B shekaru ashirin da uku a baya ba'a samu kwatankwacin sa ba. 


Ummi sai faman ja na take a jiki, dinkuna ma duk iri daya tayi mana, wanda duk tasa nima shi take takura min in sanya, dai-dai da kalar agogo bata bambanta ba. 


Zanirah kam wani baya-baya take dani tare da yi min wani gani-gani, ni dai naki yarda in biye mata tunda ta samu labarin cin zarafin da na yiwa Yayanta ta koma min haka. Ba na yarda in nuna nasan tana yi ma duk da raina baya yi min dadi. 


Allah wadaran surutun Ya Rabi. 


"Yan uwa da abokan arziki kowa yazo yadda yake kiran Ummi da "Amarya" haka nima suke kirana, amsawa nake da karfin gwiwata tunda nasan ina da ‘guarantee’. 


Su Walida, Hanifa, Maryam manyan kanne kirazan biki sun kasa zaune sun kasa tsaye, sunyi ankon shadda ruwan zuma da bakin gwaggwaro sunyi kyau matuka. Walida idan muka hadu da ita ta takarkare tana rabon abinci sai ka rantse da Allah bikinta ne ko nawa, saboda rawar kai da rawar kafa. 


Ashe Walida tasan komai, ni ina mata dariya itama a ranta ni take yiwa. Ummi ce ta gargadeta kada ta sake aji mutuwar sarki a bakinta. 


Da yamma can goshin magariba muna sanye da wani (swiss-lace) mara nauyi ni da Ummi (turquise blue). 


Jama'‘a sun fara bajewa don gab ake da kiran sallar magariba a falon Aunty Zainab, Ummi zaune a gefe tare da sauran kawayenmu, hatta Haulatu ta halarci bikin Ummi, Naja'atu da Zubaida duk suna falon ana ta zuba hira. Ni ina gefe kwance a doguwar kujera, Fa'izah ce akan ruwan cikina diyar Yaya Aliyu ina mata wasa tana ta dariya. Yayin da Zanirah tana zaune da zungureren cikinta a gaba tana faman zuba (souvenirs) a leda ita da su Haulatu, kowacce da abinda take zubawa a leda wata kek, wata meat pie, wata cincin, wata soyayyen nama suna dai yin kullin nasu cikin tsari mai burgewa. 


Walida ta shigo ta ce wai muje inji Yaya Bashir 


—_= 


duk mu ukun yana dakinsu na da na gidan Hajjah. Gaba daya muka mike, Ummi aka sake gyara goggoro aka duba madubi aka dauki (spray) aka feshe jiki, tuni dakin ya dume da kamshi mai dadi. Aka sa hoda aka fente fuska, nan da nan ta hau sheki. 


Nayi dariya na ce, "Iyen ba! Kaga amaren babban Yaya, haduwar ba sauki". 


Ta kyabe baki ta ce, "Ohon miki! Kece gwauruwa, sai ki zuba mana ido in munyi ‘ya'ya kunyi kai daya sai ku ci naku zamanin tare dasu ko?" Na ce, "Ina! Ta Allah ba taki ba. Allah Ya kiyaye insha Allah nima bazan kara shekara gidan iyayena ba Allah Zai kawo min nagari na kowa, kuma zabin zuciyata". 


Da hirarrakin da muka karasa dakin su Yaya Bashir kenan. Ummi ta faki idona tayi min gwalo. 


A tare muka yi sallama Yaya Bashir ya amsa, kowaccenmu ta samu kujera ta zauna. Yaya Bashir na fadin. 


“Ummi tawa dawo nan mana". Yana nuna kusa dashi. 


Tayi murmushi tana sunkui da kai, bata amsa tayin nashi ba ta zauna a gefena, shi da Yaya Aliyu ne, wanda tsam ya taso daga inda yake zaune ya zauna a masangalin da Zanirah ke zaune ya zauna cike da kulawa yake tambayarta. 


"How is my baby kicking?" 


Cikin murmushi ta amsa, "Gashi nan yana ta yi kamar zai kwance min zani”. 


Murmushi yayi suka ci gaba da hirarsu. Bashir ya 


taso daga inda yake ya nuna min kujerar da ya mike. 


"Ke gwauruwa, ja jiki ki bani wurin zama kusa da mata ta mana”. 


Sum-sum-sum na mike na bashi kusa da matarshi, a zuciyata ina da na sanin biyo su don kamar da gayya suke yi, don su ci min fuska. Sai dai tun can ina girmama Yaya Bashir, saboda yadda baya nuna bambanci tsakaninmu da Zanirah da kowa cikin gidan Hajjah. Na hada hannuwana biyu na tallabe haba ina kallon su suna barkwancinsu suna dariya, babu wanda ya damu da ni, kamar ma sun manta da ni a dakin. 


Takaici ya isheni, na mike zan fita, Aliyu ya ja gefen zani na zan gifta su. Na juyo amma ban yi magana ba. 


"Dama ba wani abu yasa aka yi kiran tare da ke ba, maganar liyafar Kaduna ce ta gobe, mu zamu sa ankon shadda (hilton) da su Ummi, ke kuma tunda kin saki naki auren (don bana ce an sake ki ba) sai kisa wannan". 


Ya nuna min leda bacco shake taf da kaya. 


"A wajen Maman Kaduna na amso miki cikin kayan da tsohon mijinki yayi niyyar baki tsiya ta hanaki kwantar da kai ki ci arziki, ya tattara ya barki bayan ya dankara miki sakin wulakanci tara rigis! Wai 3x3 =9. In basu yi miki ba ki fada aje a buda a canjo miki don babu abinda zai yi da su, in zai yi sabon aure na tabbata sababbi zai yiwa sabuwar matar duk da nasan ko zai yi ba nan kusa ba, don kinsan matuka jirgi mata ba damunsu suka yi ba, kullum a tsaye suke kwana cikin iska, 


—_= 


ba lallai ya damu da yin aure nan kusa ba". 


Suka kwashe da dariya baki daya. 


Kallon Yaya Aliyu kawai nake yi ina lissafa shi cikin sahun boyayyun makiyana wadanda ke sanye da fatar damisa suna (pretending) ta akuya ce. Yaushe Yaya Aliyu ya koma haka? Yaushe ya zabi Fa'iz ya barni? 


Hawaye suka zubo min wadanda duk kokarina na kasa maida su. Naso insa kai in wuce ba tare da na ce dasu komai ba, amma zuciyata ta ki amincewa ko da ban iya na rama ba, bazan nuna karaya ba. 


"Koda bani da wanda zan aura a halin yanzu, nafi karfin suturar da zan sanya a jikina. Allah Ya hore min abinda zan dinka ma kaina inyi fitar bikin Ummi ko da bai kai nasu tsada ba a kalla dai ba za‘a ce an ganni tsirara ba. 


Don haka ba sai na daura na Fa'izun ba, ko a sanda yake mijina bai yi arzikin da zai dinka min sutura ba, ya baro yi min sutura a sanda nake da bukatarta balle yanzu da igiyar ta tsitstsinke, alakar ta bi rariya. Don haka Yaya Aliyu, ina ganin ku nemo wanda za kuyiwa gorin sutura ba dai ni Fa'izar ba”. 


Suka sake kwashewa da dariya alamar ‘game’ din nayi masu dadi dukkansu. 


"Sai Hajiya Fa'izah!!!". 


Suka ajiye jinjina da hannayensu. 


Ganin sun mai da ni mahaukaciya na fito na barsu ina matsar hawaye zuwa falon Aunty Zainab. Fa'izah baby ke ja min zani, ban san sanda na tureta ta fadi gefe tana kuka ba. 


Aunty Zainab Maman Yaya Aliyu ta tare ni tana tambayar me ya faru nake kuka? Ina kuka na zayyane mata wulakancin da suka yi mani dukkansu. 


Ta ce, "Fa'izah duk ke kika jawowa kanki. Da kin kwantar da hankalinki da Fa'izu da duk hakan bata faru ba. Kin san dai duk cikinsu Fa'iz ya fisu komai har shi yayan kobon (Aliyun). Amma ki ka rufe ido ki ka badawa idonki toka da bala'i da rashin arziki har ya gaji ya tafi ya barki. Don haka baki da hujjar jin haushin su Ummi ko mazajensu anan”. 


Kokari nake in danne tasirin maganganun Aunty Zainab a zuciyata ta hanyar turawa gidan Hajjah a dauko min wani tsalelen leshi na (pitch colour) asalin shi marigayi N.S ya dinka mani kudinshi sun kai Naira dubu tamanin da biyar, ya dinka min shi ne wai inyi fitar fatin bikin shekarar haihuwar wani abokinsa da aka yi a Kano mai suna Dr. Gadanya. To a lokacin a ranar sai na tashi da zazzabi, dalilin rashin zuwana kenan na linke na goge leshin na boye can kasan kayana. 


Ina da takalmi da jaka ‘yan (Thailand) suma mahadin leshin duk ban taba sanyawa ba. Abinda yayi mani cikas inda zan samu goggoro ba tare da na kula wadanda muka yi amfani dasu a yau ba. A take na dau mayafi na fita, naje saloon aka gyara min kai da (setting) na burgewa na kuma je aka nado min goggoron yadda nake son shi (light pitch) aka yi min gyaran akaifa da wankin kafa nayi sumul da ni. Na dawo gida na kulle kaina cikin kallabi kai ba zaka ce an taba shi ba na hada 


— = 


kayan da goggoron na boye a sif din Aunty Zainab. 


Wurin sha biyun dare barci ya soma fizgata sannan su Ummi suka shigo ina kwance a gado, ta cire goggoronta ta kwado min, shi kansa goggoron kamshin turaren Bashir yake yi. 


Na ja wani wawan tsaki na ture goggoron daga kusa dani, ko me zan jiwa haushin oho! Tana so ta gaya min ne ta hada jiki da namiji, ko me zan jiwa haushin oho! 


Banza an bata sidin turawa shi ne zata zo ta yiwa mutane fiffika, har warin tabar da aka ce yaya Bashir yana sha take yi. 


"Banza mahaukaciya". 


Ban san sanda furucin ya amayo daga cikina ba. Tayi dariya ta ce, "Duk haukana ai ban kai ki ba. Yaya Bash ya ce a gaya miki kada ki samu damuwar rashin (partner) gobe don ‘couple evening’ ne za'ayi miki mijin roba da yaya Sa‘id Ibrahim Bamalli". 


Ashariya naso danno mata, amma sai na fasa. Ta cancanci bakar magana itama, don haka nayi gyaran murya daga kwance. 


"Babban hauka ya wuce ka kaiwa miji kanka a soron gidan iyaye? Don haka ban fiki hauka ba, ke naki salon na zamani ne, nawa kuwa (oldfashioned) ne. Ni kam ku bar mijin robar ku na yafe ba a matse nake da namiji ba da har sai nayi riga malam masallaci. Party ba don kowa zani ba, sai don kar ku dauka wulakancin ku da cin fuskar ku ya hana ni sakewa ne ko ina bakin cikin rashin miji har hakan ya hana ni shiga mutane, ina fatan 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...