ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5  by Sumayyah Abdul-kadir                Www.bankinhausanovels.com.ng anyita ba dadi da Fa'izah. Hasashen shi ya hasaso mishi ita ce ta yiwa Fa'iz wannan raunin. 


Fa’iz ya ja numfashi ya sauke, da gasken-gaske cikin damuwa yake mai yawa, wadda ta kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskar shi. 


Maajid ya bubbugi kafadunshi, ya yi murmushi ya ce. 


"WO-MAN! Inka fahimci kalmar ko? Tana nufin Wo! MAN ka shiga uku kenan!”". 


Duk halin da Fa’iz yake ciki sai da Maajid yasa shi dariya, ya yi mai isarsa kafin ya ce. 


"Maajid! Maajid!! Ya aka yi kasan cewa Fa'izah ce ta rotsa ni?" 


Ya ce, "Oho maka wannan kuma! Ni dai na san kai ba makaho bane balle ince faduwa kayi ka ci da baka ka fasa goshi ka fasa kai, na kuma san ba dambe kayi ba aka fi karfinka da (giantness) din nan naka Fa'iz. Na kuma tabbata ba gidan giya kaje wani yasha ya bugu ku kayi rigima ya rotsa maka kwalbar ba". 


Sai ya sake tintsirewa da dariya, ya ce. 


"To amma saboda Allah me yasa ka kirani adaidai lokacin da kasan ina tsakiyar yakin neman soyayya a tsakiyar rikici da Fa'izah? Shin ko kasan wannan kadan ne da ace ban yi mata karyar saki ba da ta kwankwatse ni gaba daya da gilasai?’ 


Majid ya yi tsaki ya ce, "Kai ka so duka wannan shirme na Fa'izah. Ni kam yana daga cikin abinda ya hanani aure yanzu, wato fargabar irin macen da zan debo ma kaina, don ni dai ba zan auri matar da bata so na ba wallahi. Idan wani ya ki ka 


da wuni, wani da kwana zai soka. Ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare, don haka mu bamu fara cin tuwon ba ma balle miyar ta kare, yanzu ne muka fara laluben har sai mun lalubo mai son mu. 


Mu matuka jirgin sama, muna bukatar mata masu matukar son mu, wadanda kullum muka fita sai sun kai goshinsu kasa sun roka mana kariyar Ubangiji saboda kullum rayuwarmu_ cikin sadaukarwa take, za'a dawo ko ba za'‘a dawo ba. In zamu fita su faranta mana, hakazalika in mun dawo. Sannan ba nymphos ba (masu yawan bukatar Da namiji) ka gane? Don haka ne naga wautarka da rashin azancin ka wurin nemo auren yarinyar da tun fil'azal kai tafi tsana sama da komai a rayuwarta wai a matsayin (life-time partner) dinka. Kada ma kayi gigin kawo mana Fa'izah a yanzu, ta hada maka zafin da zaka tura rayukan al'umma cikin (solar-system). Ka barta tukun, zuwa wani dan lokaci har ta sauke zafin kanta". 


Ya yi murmushi mai hade da sautin dariya. 


"Yau Majid so kake ka kasheni da dariya. Da alama kana da (good experience) akan WOMEN din nan. To ga tambaya, shin ya za‘ayi Fa'izah ta so ni? Ni dai (I can't do without her no matter what). Ko kasan duk haukan kiyayyar da Fa'izah ke yi a kaina bana jin ciwo? Ka san cewa har iyayena Fa'izah ta zage su tas akan idona ban ji komai ba, me yasa?" 


Da sauri Majid ya amsa. 


"Don kana sonta mana, so irin na halaka ga maza, wanda ya zarce halastaccen so ya hada da ribatar zuciya, so na fiye da kima don iyaye ba'a hada su da wata abar banza (mace). Duk da ance so hana ganin laifi to amma banda iyaye. (They made us what we are today! They are, therefore, incomparable to any worldly material). Ka farka daga gigin son nan Fa'iz ka zama jarumi akan Fa'izah kamar yadda kake jarumi akan komai. Sai dai in kiyayyar Fa'izah ta ci gaba wata rana zaka kita kaima. 


Kiyayyar Fa'izah a gareka ta yi yawa, tafi wadda ka ce kayi mata. Ni dai in ni Maajid ne bazan jure ba, mace ta fasa min kai... ta zagar min iyaye, mace! Mace!! Mace!!! Woman, Imra'ah! Ana maa Adhry!!! Macen ma wata karamar yarinya Fa'izah da ta tashi a kauye irin Nigeria? Ba zan dauka ba". 


"Baka taba fadawa a son Woman din da ka rainawa kura bane Maajid shi yasa kake duk wannan cika bakin da kake yi. Nima da irinka ne, haka nake da wannan akidar. Ban taba zaton akwai macen da zata sani zub da kaina ba sai da Allah Ya dora min lalurar ciwon son Fa’izah. Ko kasan har kasa na dire gwiwoyina ga Fa'izah? Maajid SO BA KARYA BANE. 


Sai dai ta wani bangaren ina cizawa ina hurawa. Iyaye duka iyaye ne a zuciyar kowanne Da na halak Maajid. Na zagi uwar Fa'izah yafi sau shurin masaki akan idonta a kunnenta kawai don bata fito daga family dinmu ba, ban taba tunanin yaya take ji a ranta ba, duk da yarinyar ce a lokacin. Kuma kasan saboda mene? Ba wani abu bane 


— = 


kawai Maman nata (we are not bloodly related). Babanta yaje bautar kasa yayo (secret marriage) da ita daga Taraba da yake na gaya maka a zuri'armu ba‘a auren (outsider). 


Bayan wannan Aunty Maimuna bata yi min laifin komi ba, baya ga ALHERI. Ko kallon banza nayi mata murmushi take mayar min a da can tana fadin yarinta ce, idan na girma zan gane wani baya auren matar wani, itama bata taba zaton zata auri bazazzagi ba tana cikakkiyar bafulatana. Da Allah Ya tashi saka mata Maajid rana daya sai Allah Ya yiwa al'amarin nawa juyin waina da kaunar abinda ta haifa tun ranar da aka haifeta....... ", 


Labarin mai tsaho ne Maajid, (just bear in mind I have reason to love and respect Fa'izah and her mother to such an extent, and I'm ready to do everything to undo the hurt I caused to them). In kuma ci gaba da jajircewa ga rike igiyoyin auren Fa'izah da duk iya karfin da Allah Ya halicceni da shi har sai na dinke ZUMUNCIN A.B family ya koma yadda ABUBAKAR BAMALLI ke son ganinsa, hakan kuma zai ci gaba ko babu tsohuwa Hajjah (to the last journey) insha-Allah, ni na lalata ni zan gyara, duk da ance ba'a bari a kwashe dai-dai, jikina na bani ni zan kwashe daidai Maajid, sai Fa'izah ta so ni fiye da sonda nake mata in Allah Ya bamu tsawon rai da lafiya”. 


Jinjina kai Maajid yayi, ta wani bangaren ya yarda ta wani bangaren bai yarda ba. 


"To da ka dire mata gwiwoyin a kasa, ka roketa me? Ta so ka?" 


Ya yi dariya ya ce, "Ina! Karewa ma kwarjini tayi min na kasa fadin abinda nayi niyya". 


Maajid bai san sanda ya fashe da dariya ba. "Amma ka ba da maza Pilot. Zan so ganin wace ce Fa'izar nan da zata ki namiji kamar ka ko yankar naman jikinta yake yi kullum, sai dai in ba mace bace. Tukunna ma cewa nake shekarun yarinyar basu fi ashirin ba? In har kana da tsokar zuciya a jikinka Abubakar, kuma kana son in yarda kai namiji ne mai mazakuta a jikinsa ba bonono kake mana ba mata-maza ne, ka share Fa'izah kayi kamar ka manta da al'amarinta kada ka koma inda take sai nan da (atleast) watanni uku. A kalla Fa'izah tayi haukarta ta gama ko da bata bari duka ba to 80% zai ragu tunda ta zame maka mutu-ka-raba daga kai har iyayenku. Sannan ne zaka neman sulhu cike da juriya da kai zuciya nesa, ka hadiye duk wani borenta so zallah zaka yi ta (portraying) ka zama kalar tausayi ka nuna baka da katabus sai yadda aka yi da kai, ka kwanta kace “in takani za kiyi to ga bayan taka”. Amma yanzu abinda yafi haka ma Fa'izah zata yi maka indai labarin da ka bani can baya da yanzu gaskiya ne, UWA ba abin wasa bace, ai na dauka ita kadai kayi ta yiwa shakiyancin. Tunda kace ita Maman (have reason with you) baka da matsala da ita kun fahimci juna tuntuni. 


Wacece Fa'izah? Me take takama dashi da zata ce bata son ka Fa'iz baya ga kyawun da take da shi? Me aka yi aka yi ta? Sai dai in muna-mata ce ba mace ba wadda tasan me ake so a namiji. 


— = 


Takamar diya mace kowacce iri ce kafin a daura mata aure ne, amma yanzu Fa'izah ta zama nama, bata da sauran abin tinkaho. Duk yawan kiyayyar ta fa muddin ta dauki ciki Fa'iz ta kare, domin a lokacin ne zata shiga fargabar ba zata so danta ya yi maraici ba, kuma ba zata so a kirata bazawara ba, ko kada ku rabu ta rabu da ‘ya'yanta, Zata shiga tunanin yanzu fa ta zama (second-hand) ba zata je gidan da babu mace ba, kuma kasan ba son kishiyar nan suke yi ba, kuma idan ta fita, ba zata samo yaro kamar ka ba ko da ta samu mara mata din. Zata shiga fargabar me zata je ta tarar gidan mutumin nan dama ta zauna da wanda bata so din ita azo a tadda ita tunda ku zama da mace fiye da daya al'adarku ne. 


Kiyayyar diya mace tana da wasu magunguna guda uku wadanda in kana dasu, wallahi sunan kowacce diya mace "sorry" ko ko ince (finished product). 


Na farko mace na son yawan kyauta na abinda tafi so daga hannun mijinta, kyauta wadda zata ratsa mata zuciya ba gayan kudi ba. Sannan mace Allah ya yi ta da son a nuna an damu da ita, duk inda kake, ka nuna mata tana ranka kana tuna ta da so da kauna. Tana kuma son a darajja ta (kada ka nuna mata danginka sun fita, suna kuma kada ka nuna musu ta fisu) ka barwa kanka wani sirrin na zuciyar ka. 


Tana so ka kwantar da kai ka bata hakuri in ka bata mata rai. Da fari zata nuna shariya ne, amma zuciyarta sanyi take, tana hucewa a hankali. Idan ka matso ‘yar kwalla zaka ji ta ce, "Shi kenan, ya 


— = 


wuce”, 


In ka kawo kyautar nan in ranta yana bace zata ce, "Ni bai dameni ba" ko "bana so ka bar abinka” amma a cikin zuciyarta sonka karuwa yake yana fidda rassa. Haka kayi kokarin ka fahimci duk wani (likes and dislikes) dinta shima ka dage da gujewa/aikatawa. Ka rike amanarta, kada ka dinga zancenta da kowa ko da ‘yan uwanka. Duk inda kake, ya zamanto kana yawan nemanta tare da nuna mata ita kadai ce a gabanka saurin mata basa burgeka ko da ba hakan bane (in reality) a zuciyarka. In kayi riko da wadannan Fa'iz kiyayyar Fa'iza komin girmanta babu inda zata je. 


Fa'eez ya dube shi cikin mamaki. 


"Who taught you all these?” 


Maajid ya yi murmushi. 


"Matar Yayana (psychologist) ce muna dasawa da ita sosai. Tana yawan bani ‘theory’ akan mata da abinda suke so. Ko baya ga haka ni ba irinka bane da inji kadai kasa gaba. (All work without play make jack dull boy) ina karance-karancen Novels domin samun nishadi (mostly authorized by women). Kuma ina soyayya da mata kala-kala a kasar mu. 


Ina zaunawa da kanne na mata ina jin hirarrakinsu da damuwoyin da suke ciki da mazajen su, ina sakar musu fuska ni ba (terror brother) bane irinka”. 


Fa'iz ya kyabe baki ya ce, "In ka gama surutunka don Allah tashi muje mu samu (hotel) in kwanta in huta. Zazzabi ke neman rufeni sabida jinin 


dana zubar. An gaya ma Fa'izah na kamar sauran matan da ka fahimta ne? An gaya ma Fa'izah zata tsaya ta saurari mutum har yayi mata wani dogon sharhi in ta tsane shi? Koko an gaya maka Fa'izah abin hannun maza ya dameta da zan bata abu, ta amsa bata kwada mini ba? (Above all) ma ta yaya kake tunanin ni Abubakar Mukhtar zan yiwa mace kuka har in tsaya lallashinta ta samu kafar wulakanta ne?" 


Maajid ya kunna sigari ya dasa ma lebbansa, ya ce cikin murmushi. 


"Meye kuma ya rage baka yi ba? Yanzun nan fa ka gama ce min ka durkusa da gwiwoyinka a gaban Fa'izah ba matse maka baki nayi ba". “Tsugunno daban, kuka daban. Ko da na tsugunnawa Fa'izah bance mata komi ba balle inyi mata kwallah. Da in yiwa Fa'izah kwallah don ta so ni wallahi gara mun dauwama a haka. In na sami sararin aiki inje gidansu ko ta taga ne in leka in ganta in dawo bakin aiki na kada Allah Yasa ta biyonin, an gaya maka a matse nake da mace kamar ka?" 


Maajid ya fashe da dariya, ya ce. 


"Ba’'a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Amma da ka tabbata sakarai, haka kawai Allah Ya halatta maka abu ka haramtawa kanka? Fa'izah dai mace ce dake shekarun shekarunta na (teenager) ba abinda tafi bukata a yanzu irin kasancewa da namiji da zama gidan mijinta, musamman da kace duk tsararrakinta an kaisu dakin aure. Ka zauna nan kayi ta rikon aure, ta yi saurayi mai debe mata kewa koda da hira ne asarar wa?" 


—_ 


Ya kai mishi wani mugun kutufo a kwibi, ya ja jakarsa keey...! Ya taka da gudu ya shige (lifter) ya barshi a baya. 


Fa'iz yayi tsaye kafafunshi harde da juna yana bin (lifter) da ta dauki Maajid zuwa sama da kallo har ya daina hango farar fatar Maajid da fararen kayansa da kwantaccen bakin gashin kansa na Larabawan Syria, yana mai auna maganganun da suka fito daga bakin Maajid din cikin ma’auni na hankali da tunani. 


Ya tabbata duk abinda Maajid ya fadi gaskiya ne, to amma ta yaya zai bullowa Fa'izah su kasance tare? Bama a gida Nigeria ba a duk inda ya sanya kafa? Barma (bomb) din da ya taho ya barota dashi ya fashe me zai je ya tarar bayan fashewar (bomb) din? 


Dole ya bi shawarar Maajid na tilasta kansa kin ganin Fa'izah da dosarta har bayan watanni uku kamar yadda Maajid ya ce. 


"Kai to kuma har wata uku! Wata uku fa ba kwana uku ba!! Fa'izah zata iya yin saurayi a tsayin lokacin. Yadda take kin shi din nan zata iya yin saurayin da zai debe mata kewar mataccen nata. 


Ya rike kanshi da hannunshi biyu yana girgizawa da sauri... 


"No! Babu mai barinta, iyayensu ba zasu bari wani abu ya taba mishi aure ba tunda tana tsakiyarsu. To itama bata da hankali ne? Ai aure yafi gaban wasa". 


A wannan karon hawayen kawai yake ganin idan ya yi (shading) zai samu sassaucin kishin da ya 


tokare shi ya hana shi hadiyar miyau. In kuma ya sake ya bari suka zubo ya tabbata Fa'izah ta maida shi kamar sauran maza da Maajid yake misali masu yiwa mace kuka don ta so su. Kada 


Allah Ya nuna masa wannan ranar. ok OK 


A ZARIYA N a fito falo fes dani cikin doguwar rigar Momi, 


baki na kamar gonar auduga, ban zauna a ko daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya ba sai a tsakinin Momi da Ya Rabi, suka dan matsa gefe suka bani fili a darare duk da ita Momi babu alamun jin tsorona a fuskarta, ta bani filin ne kada in dire akan cinyarta. Duk sai suka bani dariya, ga Aunty Rabi mai yi min kallon hauka sabon kamu. Na tsugunna gaban Momi da gwiwoyina biyu, na ce. 


"Don Allah Momi kiyi hakurdi ki yafe ni, duk bacin ran da na sanya ki da kashin kajin da na shafa miki na zama cikin gidanki ba tare da saninki ba. Wallahi ni kaina wani abin idan ina yi ban san sanda nake yinsa ba, ji nake kamar ana kitsa min shi a tsakar ka, bana cikin hayyaci na. Ya Rabi kema don Allah kiyi hakuri, kuma wallahi Momi bata san ina gidan nan ba". 


Nan suka dubeni baki bude kamar sunga wadda ta warke daga cuta. Yaya Rabi ta muskuta ta ce. "Yanzun kin kyauta kenan da abinda ki ka yiwa Yayanki da yazo miki sallama zai yi tafiya? Fa'izah kisan kai za kiyi? Kisan ma na mijinki dan uwanki, rabin jikinki? Fa'izah kina son gamawa da duniya lafiya da kike ta da hankulan rayukan iyaye da masu kaunarki akan sanin kanki?" 


Na kara kwantar da kai da kaskantar da murya sai ka rantse duk duniya ba za'a samu mai kirki na ba. 


"Kiyi hakuri Ya Rabi, komi ya wuce bi'izinillah. Tsakanina da Ya Fa'iz yanzu sai gaisuwar mutunci da mutuntawa, na bashi hakurin ciwon da 


—_= 


na ji masa tunda YA SAKENI!”. 


Rabi ta shiga salati tana sallallami tare da tafa hannuwa, kafin ta kai karshen salatinta take direwa ta dauko sabo. 


Kafin ta fashe da kuka ta ce. 


"Kin cuci kanki kin cuce mu Fa’'izah, hakkin iyayenki da na Hajjah ba zai taba barinki zama lafiya ba. Kin bata wayonki, kin fita zakka cikin A.B, kin zame mana bakin bunu bata baibaya. Bace min da gani tun ban lallasaki ko na tattaka ki ba...”. 


Ko a jikina wai an tsikari kakkausa. Sai na sa hannu biyu na mika mata takardar, Rabi ta mike tsaye kamar an fisgota ta fisgi takardar daga hannuna, na tabbata in na tsaya tabbas zata tattakanin, sai na mike tsam koma daki na murza key. 


Na shige cikin bargon Abdallah tunani dubu dari da hamsin ya aureni 70% na Dr. Nazir ne. Mutuwar shi ta dawo min danya, inama ana mutuwa a dawo! Ga damar da nake nema kwana da kwanaki ta samu, amma wanda nayi ta hakilon akansa mai sawa da hanawa ya yi ikonsa akansa. Na rufe ido ina kuka, tunanin kyakkyawar soyayyar mu cikin Jami'ar Bayero da wajenta ke gifta min filla-filla. Na yiwa Allah godiya da na zamo silar kimtsuwar Nazir Sani, ya kuma mutu akan niyyar AURE. Babu abinda zanyi domin nuna soyayyata a gareshi bayan nema masa rahma da gafarar Ubangiji a halin yanzu. 


Momi dai ban san halin da take ciki ba don bata yi magana ba, sunkuyar da kai tayi, sai Ya Rabi 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...