ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND  by Sumayyah Abdul-kadir                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

nake jira.

Na zauna na ci son raina na koshi, har da kara tea bayan na shanye kofi guda. Naji ni dai-dai, nayi hamdala ga Allah. Na kwance daurin da nayi na dankwalin atamfata na yafa da yake dankwalin babba ne sai ya rufeni ruf. Na nufi kofa na tsaya. Ya mike ya fito falon ya jingina da kofar da ta raba uwar dakin da falon, ya ce.

"Au, baki ji abinda na ce ba ko? Tunda kunya kike ji dauki biro da takarda ki rubuta min kinji sabuwar kurma?"

Ban musa ba, sai dai a raina na ce, "Inji kunyar ka? Amma da nayi asara. Kunyar maras kunya al asara ce!".

Na dawo na dau takarda da biro na jingina da bango na soma rubutu.

Da na kammala na aje nan, na sake komawa bakin kofa na lafe. Ya dauki takardar ba tare da ya bude ba ya sanya a aljihu ya taho yana fadin. "Kin manta da guzurinki". (Yana nufin sanitary pard).

Ban bashi amsa ba ya shiga (toilet) din ya kullo duka kayan a ledar da ya shigo dasu ya fito ina ta manna masa harara kamar kwayan idanuna sa fado. Ya yi murmushin sa (broad smile) ya ce cikin rada.

“Wannan hararar, wata rana kallon so zai koma, wannan hararan, wata rana in wata tayi min Fa'izah dukan tsiya zata yi mata, sai inda karfinta ya kare akan duk wanda yayi min ita. Wannan hararan, ni a ganina ‘I love you ne, I can't do without you ne’. Ba abinda lokaci baya magani".

Ni dai bance komai ba, kulawa ma yabawa ce koko Hausawa sunce sai an kula kashi yake doyi. "Saura ki sake batawa Baba mota, wannan karon Shu'aib zansa ya wanke. In yaso in ya tambayi na mene ne? Sai in turo miki shi kiyi masa bayani”. Kokari yake mu hada ido, na ki. Na koma na sanyo (slippers) din bandakin don bai sayo da takalmi ba. Muka sauka kasa ya basu mukullin su muka wuce, ‘parking lot’.

Nayi-nayi in bude kofar gidan baya, na kasa ban sani ba ko kulleta yayi, dole na hakura na shiga gaba, shima ya shiga mazauninsa ganin naki rufe kofar daga inda yake ya sunkuyo har muna gugar juna ya rufo kofar ruf. Maimakon ya ja motar, sai ya bude takarda ta ya soma karantawa a fili.

"I hate you. And I would never love you forever... In mafarki kake, ka farka...!!!"

Ya zuba min shanyayyun idanunshi masu cike da wata irin fitina, maimakon kalamaina suyi tasiri mara dadi a kansa. Sai naga kamar dadi sukai masa. Na juyar da kai domin ba zan iya jure kalon abubuwan da ke cikin idanunshi ba masu kama da (magnet) mai jan zuciya tamkar jan wutar lantarki, wadanda a fakaice wasu irin sakonni ne suke bayyanawa masu nuna matukar bukatar miji Zzuwa ga matarsa ta sunnah. Sai naji wasu bangarori na jikina suna kokarin karbar wannan sako, idan har banyi da gaske na zama jajirtacciyata ba kamar yadda nake wannan mutumin zaiyi saurin cin galabata dole in kara jajircewa. Wanda ba komi bane illa kokarin ganin ban yarda mun sake kadaicewa ba. Domin nima din ‘adolscent'

— >

ce mai bukatar mahadin rayuwa, don dai auren ya zo ba a yadda na so ya kasance bane. Ya kasance ya ZO min tareda wani mutum da ba abinda zai yi ya burgeni a rayuwata, ko ya wanke dattinsa dake raina.

Ya yi murmushin da yafi kama da takaici ya tada motar. Bai sake magana ba har muka fita garin Minna. Yayin da ni kuma na tsayar da idanuna gefen da bishiyoyi suke zuciyata cike da farin cikin ko yaya ne dai kalamaina sunyi tasiri.

28 OK ok

Wajejen karfe uku sai gamu cikin garin Kaduna. Ya karya kan motar ya dauki hanyar anguwar Kabala Custain. Ni sam bam ma san nan gidan Ummi yake ba. Yayi (parking) bayan maigadin gidan ya bude get din gaba daya. Su Yahya ne suka fito ashe duk suna gidan sunzo musu wuni, abin mamaki har da su Walida, Abdallah, Kausar da Walid autanmu. Nan gidan ya rude da sowar kannen mu kamar zasu hadiye mu.

A sannan ne na gane gidan Ummi da Yaya Bashir ne ganin tangamemen hoton su (window size) ranar (cocktail) din (Indoor sport hall) kafe a kayataccen falon.

Sai na wuce kai tsaye zuwa uwar dakin matar gidan babu wanda na kula a cikinsu sai cika nake ina batsewa. Na zauna a gefen gadonta ina kallon dakin kallon kurilla, na jiyo alamar tana (toilet) ne wanda ke makale da dakin nata tana wanka. Ummi tunda taji ana oyoyo Yaya Fa'izah, oyoyo Yaya Fa'iz tayiwa wankan baja-baja ta fito a guje

duk rabin jikinta kumfa ta fado mini.

Na ture ta na ce, "Ke baki da hankali ne za ki jikani? Don kawai nazo gidanki? Ba tambayar mutum ya yake? Ko wane hali yake ciki?"

Ta daga ni tana dariya, ta rasa inda zata sa kanta don farin ciki. Na bita da kallo har cikin ta ya tasa. Na kama baki cikin tsananin mamaki domin na dauka da da wasa take kamar a bakin kofa ake tuntube da cikin?

Ta sunkuya ta zauna a gefena hannuwanta duka biyu tallabe da fuskarta tana murmushi, ta ce. "Faizah matar Yaya Fa'iz! Sai kyallin amarci kuke don na hango shi ta taga, daga ina kuke haka? Naji labarin Baba ya kore ku, tsammanin mu kun bar kasar babu sallama ga kowa".

Na hade girar sama da na kasa, na ce.

"Kin san Allah ki fita daga harkata, wane irin an kore ni kamar wata shegiya? Maras kunya fitsararriya, kyallin amarcin uban wa? Amarcin yaci ta kaza-kazan sa". Na mirgino ashariya.

Ummi ta dafe baki, sai kuma ta fashe da dariya. "Oho dai! Mun gane kiyayya taci uwatar, Pilot yayi fari yayi kiba, Fa'izah ta rame saboda amarci amma ta zama kyakkyawa. Shin wai a ina aka yada zango ne?"

Ganin tana neman maishe ni mahaukaciya na mike nayi (toilet) don inyi wanka in sauya kunzugu na ko naji dadin jikina. Na fito daure da tawul tana make-up a (dressing mirrow) fuska kamar jikakken kwaki don turbunewa na ce.

"Bani kaya in sauya, ko ba hali?”

Tayi dariya kawai, ta dauko min atamfa Vlisko

—_=

mai ruwan ganye mai karamin dinki na karba na saka nayi kwalliyata sosai nayi sharr, tuni kuma tausayin ‘yar uwata ya kamani ganin yadda take ta rawar jiki dani cike da kauna. Sai na ware nima muka shiga hirar arziki.

Duk sanda ta sako zancen Fa'iz cikin hirarmu bana yarda ince mata komai, dolenta ta kyale, muka koma hirar makaranta da dakace iri-iri na cewa yanzu an shiga zangon karatu na farko na sabuwar shekara babu mu, Haulatu na can tana ta (missing).

Ko da wasa Ummi bata yi zancen marigayi N.S ba, nima banyi ba. Na ce.

“Wai ina Yaya Bashir ne?"

Ta ce, "Ya koma Russia zai harhado kan takardunshi don na ce ni ban yarda yayi aiki a can ba, sai dai ya je, ni in zauna anan duk sanda ya samu dama ya neme ni, dalilin komawar shi amso takardun kenan ya dawo nan ya nemi aiki".

Nayi dariya na ce, "Kin hadu, wai kema mai tsarawa miji rayuwa ko?"

Ta ce, "Ba wani tsarin rayuwa ko dai gaskiya. Na rantse miki shashanci yake a can ba aikin da yake yi. Ya jima da gama karatu babu yadda Mama bata yi ba ya dawo yaki, wai jiran Yaya Fa’'iz yake ya kammala da yake karatun Fa'iz yafi nashi nisa. Gara Fa'iz idan ya ce zai yi aiki a waje yana da hujja a Nigeria bamu da wasu Airlines na arziki, kuma ba zaki hada albashinsu da nagartarsu da ‘Internationals’ ba.

Shi kuwa Yaya Bashir su Nigeria ke bukata suzo su amfanar da al'ummar su yafi, (Global; secu

—_

rity) ya karanta.

Na samu da dabara da taimakon Allah da na addu'a na tsayar da hankalin Yaya Bashir a kaina, anan bai fita ko’ina sai tare da ni, don kar in zarge shi. Firinji kuwa (fridge) duk gidan daya ne na (kitchen) don kar ince yana boye (gulder) wani wuri. Don haka ko ya dawo ya samu aiki zan ci gaba da sa masa ido sosai duk da cewa na tabbata a yanzu yaya Bashir ya bar shashanci 90%".

Na jinjinawa Ummi a fili da zuci, kaga mace duk gabuntarta a fannin mu'amala da miji kada ka rainata. Ban taba zaton Ummi na da hankalin da yau na sameta da shi ba.

Na ce, "Bani abinci Ummi, yunwa nake ji, tun karin kumallon safe rabona da abinci, kin san kuma ba iya jure yunwa nake ba".

Ummi ta dafe kirji, kai Fa'izah, amma kin iya rashin mutunci, kin shagaltar dani ko ki tuna mani da dan uwa na dake waje cikin yara ko ruwa ban bashi ba, kanki kawai kika sani, (selfish!)". Ummi ta fita falo da fara'arta sai taga wayam! "Ku! Ina Yaya Fa'iz?"

Ta tambayi Walida.

"Ai tun dazu ya debi Shu'aib, Junior da Yahya suka wuce wai Zaria za su raka shi.

Haushi ya kashe Ummi ta harari Walida.

"Shi ne baku gaya min ba? Ban bashi ruwa ba, ban bashi abinci ba". Ta fada kamar ta fashe da kuka.

Abdallah ya ce, "Shi ne ya ce mu kyale ki hira ku ke, kun jima baku hadu ba. In ya dawo daukan Yaya Fa'izah gobe ko jibi kun gaisa”.

Ba haka ta so ba, sai dai tayi farin cikin jin cewa ya bar mata 'yar uwarta barin rayuwarta su kwana su hantse tare, wani abu da suka rabu da samu tun barowar su Kano gidan Yaya Rabi.

Da kuzarinta ta fada (kitchen) don dora sanwar dare. Ta dawo ta ci gaba da yi min sababi, ta gaji ta koma wa'azi na hakkin miji akan matarsa da girmama shi da kula da cin shi da shansa da shimfidarsa. Amma ga mamakina na kasa tanka mata duk da nasan gaskiya take fada ban dai furta komai ba mai nuni da na amshi wa'azinta ko a'ah? Ba zata gane ba, ba zan iya bane, da zata gane ta adana yawun bakinta a gaba zai yi mata amfani, ta barni yadda ta ganni, rayuwata da tata ba zata taba zama daya ba.

MU HADU A LITTAFI NA HUDU WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...