ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1  by Sumayyah Abdul-kadir 


Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mai taxin ya gaji da gaya min gamu cikin Zaria, ina zamu dosa? Na zama kamar mutum-mutuma, kurma, makauniya don tunani, saida ya bubbuga kujerar danake zaune nace masa gida mai lamba tamanin cikin gidajen malamai na jami'ar Ahmadu Bello. Gidan da ya zamto mahaifata, dandalin quruciyar rarrafe da tata-ta ta, kafin in gu

jeshi zuwa inda nake ganin ya fishi farin ciki da walwala, a yau gani na dawo da qafafuna, na kuma gwammace in qarashe sauran rayuwata cikinsa ko da ace yafi kurkuku rashin daxi da taqaita farin ciki. 


Wata irin doguwar ajiyar zuciya na saki, na ciro kuxin da suka rage min kaf ko girgawa banyi ba na baiwa mai tasi, ya fitar min da jakata daga bayan motar sa, ya yi min godiya mai yawa ya ja motarsa ya bar harabar wajen. 


Zan iya kimanta lokacin da garfe takwas na dare sanda nake tsaye qofar gidanmu, domin ina iya hangen tangareren agogon falonmu wanda hasken qwan lantarki ya wadata, kuma an xage labulen wawakekiyar tagar falon. Rashin motar Baba ya tabbatar mini bai shigo cikin gida ba, ya shiga cikin (city) kamar yadda ya saba duk bayan sallar isha'i. Don haka naji xan sanyi da qwarin gwiwar cira qafa da tura jakata. 


Sai dai a take wani irin tsoro da shakka suka lulJube ni, idan Momi ta yarda ta kyaleni in zauna Baban ABU zai kyaleni ne bai gayawa iyaye da ‘yan uwansa ba? Kuma wane mataki zai dauka a kaina tunda ga dukkan alamu bai dauki al'amarin nan da sauki ba?

Hakan dai nayi shahadar quda da yin garfin halin danna qararrawar gofar shiga falon (door-bell), sai da na danna sau uku kafin a bude. 


Walida ce, zata yi magana nayi hanzarin kai hannu na rufe bakinta, muryata na rawa na ce. 


"Ki rufa min asiri Walida, shin Baba na gida?" 


Ta girgiza kai. 

"Momi fa?" Ta nuna min (kitchen). Na ce, "To don allah Walida kar ki gayawa kowa ina cikin gidan nan, zan zauna dakin Abdallah, ai yana makarantar kwana ko?" Ta gyada kai tare da lekawa ciki ta tabbatar momi firar doya take, tayi min alamar in shiga. A hankali ta murda gofar dakin Abdallah na shige wanda ke daga can gefen tafkeken falon, ta mayar ta rufe kenan Momi ta qwala mata kira. "Walidaa!”. Ta ruga a guje tana faxin. "Yes Mom". Momi ta ce, "Ke da wane a waje ku ke magana?" Ta xan diririce na rashin sabo da yin qarya, kafin ta ce. "Joseph ne yake neman Cinyere na ce bata zo ba". Ba tare da ta juyo ta dubeta ba ta ce. "Ga abincin ku can kan leda ki ta da Walid ku ci, ya yi bacci ko?" Ta ce, "Kai Momi, ki kyale shi ya fa sha kunun tsamiya mai yawa kafin ya yi baccin”. Ta juya don ta kira Kausar ta tarar tayi bacci akan litattafanta itama, ta gayawa Momi kana ta xauki plate din ta buxe qofar a hankali ta shigo. Nayi tagumi ne a gefen gadon Abdallah na zubawa kayana ido, da ‘yar muryarta mai sanyi ta ce. "Yaya Fa'izah". Tare da zama a kusa dani, ta xdora hannunta bisa cinyoyina. "Wai shin me ke faruwa ne? Duk akan auren ki 

da Ya Fa'iz ne?" 


Na share hawayen da suka cika mini ido, na ce. "Shin Walida kin mance sanda Fa'iz ke azabtar ne Fa'iz bai min ba, bai kuma gana min ba? Qiyayyar duniya wacce iri ce Fa'iz bai min ba? Amma ki ga don zalinci ya zo ya kalallame Hajja da su Baba suka daura mana aure...". 


Wasu azababbun hawaye suka mirgino akan kundukukina. 


"Don haka ni kam Walida anan zan ci gaba da boyewa har zuwa sanda suka gaji da nemana suka warware auren nan, ko kuma su kai gawata idan bagin ciki ya qarasa ni, da dai in zauna ayi bikin nan jibi...”. 


Na ci gaba da share hawaye ina fyace majinar dake ambaliya daga hanci na. 


Walida tayi zuru tana kallona. Da alamun tayi nisa a tunani. Ni na san Walida yarinya ce mai kaifin basira duk da kasancewarta mai qarancin shekaru, kwata-kwata bana ji ta cika shekaru goma sha huxu. Wala’Allah abinda take saqawa ya zam mai amfani a gareni. 


Ta ce, "Yaya Fa'izah, ban zauna a Giwa ba ko kadan balle in san halin Ya Fa'iz a da can, ko rayuwar da ku ka yi tare, bana ma kuma marmarin zaman, sai dai nakan ji ana labarin a cikin ‘yan uwa ko in munje gidan Baban Kaduna ko yaro ne ya takurawa daya sai kiji manya na fadin, "Kada ku zama Fa'iz da Fa'izah mana, kuyi riqo da ZUMUNTAR ku”. Sai dai wallahi a yadda Baba ke son auren nan naku ya kuma dage ya 

tsaya wajen ganin wanzuwar sa na rantse duk inda ki ke sai ya nemo ki, balle cikin gidansa. 


Ni kam banga abin ta da hankali da gin Ya Fa’'iz ba, da kin dora idonki bisan Pilot Fa'iz Giwa a akwatin talabijin sanda aka nuno shi a tashar CNN, ranar da wani jirgi ya fadi a Mozambique da kinyi alfahari da kasancewar shi miji a gare ki. Wanda ba isarki ko cancantar ki ce ta baki shi ba, cikin ‘yammatan A.B bakidaya face darajar Zumuncin da kasancewar ku JINI DAYA. Miji ne na liqawa a goshi, kuma abin tinqahon kowacce xiya macen da ta san ciwon kanta. Da kinyi nadamar wannan azabtar da kankin da tada hagargarin da kike yi kan wai ba kya son sa. 


Ko kin san Ya Fa'iz na yanzu bai yi kama da Fa'izun gidan Baban Kaduna ba na da can da kika sani a baya? Wallahi in banda Fa'iz ke son ki, da na ce yafi garfinki a halin yanzu kam! 


Umm!! Ni dai ina baki shawarar ki haqura ki fauwalawa Allah al'amarinsa da yinsa, kada ki zamo mai shisshigi cikin iyakar Ubangiji, wato yarda da qaddara mai dadi ko mara dadi. 


Wallahi Yaya Fa'izah ni shaqiqiyar ki ce, don haka ba fata nake miki ba, muddin yaya Fa'iz ya barki ba za ki samu ko da wanda ya kama qafarsa ba...". 


"Ni kam na shiga uku!!!". 


Abinda na fadi kenan a fili kamar in dora hannuwa aka in fasa kururuwa. 


Me yasa kowa ba ya ganin hujjata da qima, girma da muhimmanci? Me yasa kowa ke son Fa'iz? Me yasa kowa ya bude baki yabon Fa'iz yake yi? Sun 

manta cewa maqiyinka baya taba dawowa ya zama masoyinka? Wanda ya ce bai son ka jiya, gobe ya ce yana sonka to tabbata wani abin ya hango. 


Na dubi Walida cikin matsanancin bacin rai a ido da zuciyata, na ce. 


"Yau na amince kina daga cikin maqiyana Walida! Kin nuna min ba ki qaunata Fa'iz kike so kamar sauran dangi, kema kina cikin sahun su Ummi, Hajja da Zaneera... Yaya Aliyu kaxai ke sona har gobe cikin A.B, kin kuma nuna min ke


ma...... . "| ,.Walidaaa!”. 


Momi ke kwala mata kira. 


Walida ta mike a razane, a kidime muryarta na rawa ta ce. 


"Wallahi-wallahi daga yau ina bayanki Yaya Fa'iza... tunda har baki son Yaya Fa'iz har haka, nima daga yau na tsane shi... na tsane shi!!!". Wani irin murmushin qaunar 'yar uwata ya subuce a fuskata irin wanda ke fitowa tun daga qarqashin zuciya, itama murmushin tayi mini. 


"Daure ki ci abinci Ya Fa'iza, zan ke kawo miki abinci ko yaushe. Don Allah ki daina kuka. In kinga ban shigo ba to ina makaranta ne boko ko Islamiyya. (Toilet) din Abdallah a bude yake, kuma famfo yana zuwa". 


Ta fice da sauri ta ja gofar ta tadda Momi, ina jiyo Momi na faxin. 


"Me kike a dakin Abdallah tun dazu ina ta kira?" Ta ce, "Momi littafina da ya ara nake nema "An African Night Entertainment” nake jin ma ya tafi 

da shi". Shigowar Baba ya katse su. 


Na dauki kwanon abincin da Walida ta kawo mini nayi loma guda na sakwara da miyar Ugu. Tamkar nayi loma da curarren madaci duk da zaqin nama da na mai tauraro da miyar tayi cau. Yadda zuciyata take baqiqqirin haka bakina yake daci dau. Na runtse ido na a hankali na kishingida bisa gadon Abdallah tare da jan bargo har kaina, sakamakon wani irin sanyi da naji yana ratsa qasusuwana, yana son shiga har cikin bargo na alamar shigar zazzabi. 


Zuciyata na wani irin tuqugi, maqaqi da azalzalar baqin-cikin da ba zan iya kwatantawa ba. 


KK KK 


A GIWA A can Gida babu wanda ya farga da rashina a gidan har garin Allah Ya waye, duk jama’ar gidan bagi da 'yan gidan kowa harkar gabansa yake yi, ana ta shirye-shirye. Musamman kasancewar ranar ta 

Alhamis a matsayin ranar budar kai. 


Aliyu ne ya shigo falon Hajjah tare da dan uwanshi kuma babban abokinshi, wato Muftahun Yaya Rabi da ya zo a lokacin don su gaisa da Hajja, isowar shi Giwa kenan. 


A babban falon dake shage da A.B family maza da mata, Muftahu ya zo ne da labarin rasuwar Dr. Nazir Sani Galadanci, manemin auren Fa’'izah. 


In banda Salati babu abinda Yaya Aliyu keyi yana mai qara jinjina wannan mummunan labarin, tare da gqara tsinkewa da_ al'amarin Ubangiji. 


Muftahu ya nemi ganina don yi min bayani, Ummi dake kokawa mutuwar Naziru haigan har kamar ta shide ta yarfe hawaye da majina, ta ce. "A wannan halin da Fa'iza ke ciki ne zaka ba ta Jabarin rasuwar Dr. Nazir Yaya Muftahu? Ka rufawa kanka asiri, idan Fa'izah bata ce kai ka kashe mata Nazir ba, la-shakka zata ce hada baki ku kayi aka kashe Naziru don ta yarda da auren Ya Fa'iz". 


Muftahu ya ce, " amman dole ne ta ji?" 


Ummi ta ce, "Ji kam ya zama dole ko ba jima ko ba dade, amma ba yanzu ba, kuma ba daga bakin kowa ba sai na wanda zai iya ma haukar Fa'izah tamkar Yaya Aliyu ko Ya Rabi, amma ba kai ba". Da sauri Aliyu Na‘ibi ya ce, "Wallahi babu ruwana, ba a bakina ba nima, indai har ka dage sai ka fadan Muftahu ga hanya, tana uwar dakinsu tana neman kashe kanta don bala'i da qin auren Fa'iz ko falo ba ta fitowa". 


Muftahu ya ce, "Bari inje, inji dai ba zata bugeni 

ko ta zage ni ba?" Suka ce a tare, "Uhm!”. 


Hajja ta ce, "Muftahu ka qyale Fa'izah don Allah, shin Fa'izar da ta rufe ido ta zageni tas kan Naziru kai waye da bazata zage ka ba, zaka je mata da labarin mutuwar Nazirun?" 


Muftahu bai tsaya ba a yayin da ya danna kanshi a dakin bakinsa dauke da qatuwar sallama. 


Ya yi dube-dubenshi ya fito, ya ce. 


"Au, ai ma bata nan”. 


Ummi ta ce, "Ko dai ta shiga bayan gida?" 


Ya ce, "Ga bayan gidan nan a hangame, ai babu kowa a ciki". 


Ta ce, "Duba sosai dai can qarshen gado ko ta nade cikin bargo". 


Muftahu ya yi dube-dubensa har da duba qasan gado ya kuma hada da kira. 


"Yar Zaria a Kano!!!". 


Shiru ta ziyarce su, sai ma amsa kuwwar muryarsa da ta dawo cikin kunnensa. 


Ya ce, "To, wataqila dai idona ne, Aliyu zo ka duba”. 


Baki dayansu suka mike suka shiga dakin inda Fa'izah ta ce daukar ni inda ku ka ajeni. 


Zaneera Sai da ta qara shiga (toilet) ta duba bayan qyaure da cikin baho, ta ce. 


"Kai! Tikisa!! Da qyar fa idan Fa'izah na cikin dakin nan”. 


Lega nan leqa can cikin A. B Estate baki xaya babu Fa'izah. 


Hajja ta tuna kalaman Fa’'izah. 


"Daga yau ba za ki sake ganina cikin gidanki ba balle ki yi iko da ni...". 

Hajja ta fashe da kuka tana fadin. 


"Ni Dijah na shiga uku, wace irin zuciya ke da yarinyar nan wadda babu ahuwa da rangwame a cikinta? Tabbas Fa'izah ta gudu ne, ba ta gidan nan, ba ta garin nan”. 


Zaneerah ta ce, "Ina! Babu inda Fa'izah za ta iya zuwa da ya wuce Kaduna, Kano ko Zaria. Bayan wadannan wurare na tabbata Fa'izah ba zata yawon banza ba, kuma ba zata kai kanta mahalaka ba duk rintsi duk kuwa abinda ke damunta". Aliyu ya zaro waya daga aljihunshi, haka Muftahu. 


Muftahu Aunty Rabi ya kira, ya ce. 


"Maman Abdul 'yarki wurin ki ta iso ko?" 


Ta ce, "Wacce 'yar tawa Mufty? Kasan ‘ya'yan nawa yawa ne da su". 


"Y ar rigima mana matar Fa'izu!”. 


Da fari Rabi kam dafe qirji tayi kafin ta ce. 


"Ni Rabi'atu, rabona da Fa'izah tun ranar da suka haura qafa suka bar Kano, amma gani nan tafe. Nima shirin kayana nake yi yanzu haka". 


A sanyaye Muftahu ya zura wayarsa a aljihun gaban rigarshi, ya ce. 


"Fa'iza ba ta Kano fa". 


Zanira ta fashe da kuka, "Ni kam wannan aure dole ne? Me ya yi zafi nquide haka da ba za a haqura ba? Wallahi ni nasan Fa'izah da kafiya da taurin zuciya, tunda ta ce bata auren nan wallahi bata yi xin ne, babu wanda ya isa ya tanqwasa ta”. 


Cikin alhini Aliyu ya ce, "Haka Fa'iz Giwa, tunda ya ce bai sakin auren Fa'izah yanzu ya saka xamba a aurenta, na tabbata ko duniya zata taru 

akansa ba zai saketa ba, sai dai mutuwa ta raba su A wannan gava ni na saduda Hajjah, dabarata da tunanina sun qare wajen tanqwasa Fa'izah tunda har anzo gejin da Fa'izah ta soma zartarwa rayuwarta hukunci ba tare da shawara dani ba, ya tabbata cewa nima ta sanya ni a rukunin sikelin da ta xora kowa. Sai ki yanke hukunci na qarshe, in har bata Kaduna ko Zaria". 


Yana faxi yana kiran Maman Kaduna. 


Ita xin ce ta xaga suka gaisa cikin matsananciyar girmamawa ta 'ya'yan A.B ga iyayensu maza da mata, Aliyu nauyin Mama ya dabaibaye shi, shin yaya Zai yi ya tambayeta yarinyar da ta bar gida domin giyayyar xanta? Jikinshi na bashi yaqinin ba yadda za ayi Fa'izah taje Kaduna, shin giyar wake ta sha ma? 


Ya yi ta maza jin shiru ta ratsa a tsakaninsu, ya ce. 


"Shin Mama ina Pilot ne?" 


Ta ce, "Yana vangarensa yana shirya kayansa, wai shirye-shiryen tafiya yake yi jibi can Russia, anyi masa kiran gaggawa kan wani muhimmin aiki. Yaya Fa'izar? Ince ko ta ware?" 


Gaban Aliyu ya bada damm! cikinsa ya ba da sauti, ya ce. 


"Don Allah Mama yi min magana da shi yanzun nan ko Yaya Bashir". 


Mama ta ce, "Na ce lafiya dai? Bashir yana kan hanyar tahowa na san ma ya kusa isowa yanzun, ka gaya mini mene ne? Me ya faru Aliyu?" Tausayin Mama ya kama Aliyu, daga jin muryarta kasan ta daxe bata cikin nutsuwa da kwan

ciyar hankali duk akan Fa’iza. Aliyu ya rasa yadda zai yi don ta wuce ya yi mata qarya, ya ce. "Wallahi Mama Fa'izah ce bata kwana gidan ba, gamu nan a Giwa kowa hankalinsa a tashe". Mama tayi murmushi mai fitar da sauti, ta ce. "Ina da kyakkyawan zato da shaida akan xiyata, ba zata iya wuce Zaria zuwa Kano ba duk nisan da zata yi". 


Ya ce, "Wallahi bata Kano, yanzu Ya Rabi ke faxa”. 


Mama ta ce, "Ka jarraba Zaria mana. Yanzu kam bai kamata mu faxawa Fa'izu ba tunda Zariyan yake shirin zuwa gaida Maimuna wataqila ya tadda ta can". 


Aliyu ya sake neman gidan baban ABU, momi ce ta xauka suka gaisa tana tambayar Little F. Aliyu kam duk gaisuwar ta gundire shi, ya ce. 


"Shin momin Walida, please Fa'izah Zaria ta kwana?" 


Da farko Momi Maimunatu shiru tayi sakamakon mugun faxuwar gaban da ya dirar mata. Ta samu ta haxa sauti wanda zai ba da ma'ana, ta ce. 


"Ko da zancen nan bai shafeni ba Aliyu da Fa'izah ta zo gidan nan da tuni na sanar daku ko don gudun tashin hankalin ku. Rabona da ganinta tun zuwansu daga Kano da suka zo suka kwana biyu nan ita da Ummi". 


Aliyu ya ce, "Ya Salam!!". 


Tare da tura wayarsa a aljihun bagin wandon (jeans) mai matugar qwari dake jikinsa. 


Ummi ke tambayar, "Bata je ba ko?" 


Sai kuka, kazalika sauran ‘yan uwa da ‘yan buxar 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...