ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7  by Sumayyah Abdul-kadir

ran Fa’izah ba. Da na san haka abin zai zama tun farko da ban saurare ka ba..... Surutun Hajiya kara kular da shi yake. A kufule ya ce, “To na ji Hajjah, in ta farfado din sannan ki san abin yi ko ba yanzu ba da lafiyarta ake nema ba komai ba”. 


Hajjah ta wuce tana fadace-fadacen ta da mita wanda Fa’izu bai saurari ko daya daga cikinsu ba. Pilot Fa’iz Giwa babu abin da ya gama shi da asibiti. Amma tsabar kishin kada Aliyu ya daukar mishi mata ya gwammace kada a kaita asibitin. Shi kam yanzu ya fara son Fa’izah ma da damarar rayuwa da ita. Sai dai ta mutu su je lahira suyi aure su zauna tare, amma Hajjah ta canza masa farat daya kamar ba Hajjar shi ba wadda ta fi kowa son shi a duniya including iyayenshi, ta fi shi son duk abinda yake so, ta fi kowa farin ciki da ya ce a aura mishi Fa’izah ba. Ta yi murna, ta sa mishi albarka har da kukan farin cikinta. Amma da ya dubi halin rai kwakwai mutu kwakwai da Fa’izar ke ciki sai ya yi mata uzri. 


Firjin dake gefe ya bude ya fiddo ruwa mai sanyi ya zuba a kofi ya tsugunna ya karanto AyatulKursiyyu, Falaqi, Nasi da Ikhlas. Ya karanto karshen Suratul Al-Imran wato daga (Rabbana faghfirl lana wa af-anna) ya karanto ayoyin karshe na suratul Hashri tare da addu’ar Yusuf (A.S) a lokacin da ya shiga kunci a kurkuku, da addu’ar Yunusa (A.S) duka ya tofa a cikin ruwan, duk wata addu’ar yayewar kuncin zuciya da ta zo bakinshi ya tofa a ciki. 


Ya shafe min fuska da ruwan har cikin kirjina 

dai-dai santar zuciyata. Na lumshe ido a hankali amma ban motsa daga yadda nake ba, Fa’iz ya samu kanshi cikin tsananin rudewa da firgita, bai san sanda ya kwalawa Ummi da Zanirah kira ba. Dama suna falo suna ta tsuma. Zanira a guje Ummi da sassarfa suka fado dakin. Ya ce, “Shi kenan da gaske ne ta mutu, ku ce da su Baba su zo su _ binneta....” Fa’iz kuka yake sosai da hawaye da zuciyarsa. Haka Ummi da Zaneerah. Ko kusa da Fa’ izar sun kasa karasawa. 


Aunty Hauwa ta shigo dakin da saurinta, da alama zuwan ta gidan kenan. Tana ta fada kamar ta ari baki, ‘““Wane irin hauka ne wannan Fa’iz? In ka hana Aliyu kai Fa’izah asibiti me kenan ka yi? Ko meye ribar ka cikin hakan? Wai ma tukunna Fa’iz da na sani ne kuwa? Crying for the sake of Fa’izah’s unconsciousness?” 


Ta yi murmushi, duk ita daya ta ciccibeni gaba daya ta yi waje. Fa’iz bai ce komi ba, illa rakamu da kyawawan idanunsa dake cike da hawaye sun kuma kada sunyi jair. Sai kuma ya tashi da hanzari ya bita. Aliyu ya yi dariya ya aje little Fa’izah ya bisu ya ja motar zuwa asibitinsu wanda ke bayan gidan duka cikin A.B Estate wato A.B Clinic and Maternity. 


Likitoci biyu ne suka rufu a kaina suna kokarin ceto numfashina. Fa’iz ya shiga kai kawo tsakanin gabas da yamma, kudu da arewa. Ya yin da Aliyu ya jingina da kofar (Emergency Room) da nake ciki yana hango fuskata cikin (oxygen) da aka makala mini. 


Aunty Hauwa ta yi tagumi a kan kujera ta rasa 

abin da yake mata dadi. A haka jama’ar gidanmu da ‘yan daurin aure duka suka taddamu wannan ya harari Fa’iz wannan ya tausaya mishi, babu wanda ya iya ce masa ko da sannu da zuwa bayan shekaru masu dama da suka kwashe basu sanya shi a idanunsu ba. Shi kam Babana kujera ya samu ya kame yana kallon kowa daya bayan daya. 


A lokacin Baban Kaduna wato Alh. Mukhtar ya iso asibitin. Da Dr. Habib ya fito ya nemi son ganin daya daga cikinsu Baban Kaduna ne ya shiga. 


Ya ce, “Muddin Fa’izah ba ta farfado ba nan da awanni uku, to zai yi wuya in ba coma bane ta shiga. Sannan jininta ya hau, mugun hawa kuwa, zuciyarta ta tabu. Kokarin da muke yi yanzu shine na jininta ya sauka, numfashinta da bugun zuciyarta su dawo dai-dai. Na roke ku idan an samu Fa’izah ta farfado ku guji gaya mata awkward incidence ba ta hanyar da ta dace ba. Domin sudden unpleasant shock ya kan harbi kwakwalwa har ya haifar da depression’. 


Baba Muntari ya shiga sharar zufa, babu shakka ya shiga tashin hankali. Ya ce, “Ba komi likita, shi kenan ai in an samu ta farfado din shi kenan. Kuma ni ban san abin da aka gaya mata na tashin hankali ba, aurenta kawai aka daura da dan’uwanta yanzu-yanzun nan, bayan wannan ban san komai ba, dama can tana da makamancin ciwon hawan jini ko (something associate) ne bamu sani ba?” 


Dr. Habib ya ce, “Lafiyarta kalau. Sudden shock 

ne wanda zuciyarta ta kasa karba kawai. To ko auren ne ba ta so?” 


Baban Kaduna ya ce, “Mai yiwuwa. Biri ya yi kama da mutum, domin wasu daban sun zo neman auren ta. Bari in je in same su in ji”. Ya mike ya firto fuskarshi babu annuri sam. 


Barau ya kira gefe suka yi magana don da shi ya fara cin karo, ya kuwa gaya masa komai a gurguje cewa, Fa’izah ba ta son Fa’iz tun tana kankanuwa, Fa’iz ya tsani Fa’izah, tunda aka haifeta basu taba zama a inuwa daya ba dai-dai da sakan daya. Aliyu ta so ta aura kuma da bata samu ba ta dangana saboda Zaneerah. Tun sanda Hajjah ta fara fito da zancen ya same ta cikin sirri ya ce kar a soma wannan kada gyara zumunci ya zama bata zumunci. 


Su da aka yi musu haka suka zauna lafiya, to fa in babu soyayya a tsakani haka babu kiyayya, kuma su na jiya ne ba na yau ba, zamani kullum canzawa yake yi. Zai fi kyau a dinga karbar canjin da ya zo da shi idan babu sabon Ubangiji ko halaka a cikinsa’’. 


Jikin Baba Muntari sanyi kalau kuma ransa ya baci domin shi ba haka Fa’iz da Hajjah suka gaya mishi ba kafin ya karbi waliccin auren nan. Ya dauka cewa ko da hakan (doctrine) din su ne kuma umarnin Hajjah ne, to babu wani abu makamancin wannan tsakanin Fa’izu da Fa’izah. Ofishin Dr. Habibu ya koma ya dauko takarda da biro ya fito ya doshi Fa’iz wanda ke tsaye gefe yana kallon su cikin dimuwa, don ya amince ba ALHERI Baba Barau ke gayawa Baban Kaduna 

ba, ganin yadda fuskarsa ma’abociyar kamala ke tattarewa tana yamutsewa. 


Don haka ganin ya nufo shi da takarda da biro fuskarshi babu alamun rahama, sai ya ji hanjin cikinsa suna dunkulewa wuri guda. 


Fa’iz ya daga dara-daran idanunshi da suka kada suka yi jawur ya dubi Baba kallon rashin fahimta, ya motsa baki zai yi magana amma ya rasa me zai ce ne. 


Baba ya ce, “Karbi ka rubuta min saki uku yanzun nan Fa’izu”’. 


Fa’iz ya ja da baya ya soma hawaye ya ce, “Baba Fa’izah za ta farfado ne, amma ni ba zan yi saki ba...” 


Baba ya ce, “Fa’iz har ka yi kaurin wuyan in fadi ka musa min? In ka kashe ta za ka auri gawarta?” Fa’iz ya shiga girgiza kai ya ce, “Shin Baba a kan me za ka yanke wannan danyen hukuncin gare ni? Ka sani muddin ka takurani na rubuta takardar nan shi kenan, in na tafi ba zan kara dawowa kasar nan ba, kuma ba zan.....” 


Wani irin mari Baba ya share shi da shi, sai ga habo ta hancinsa. Ya kai hannu zai sake sharara mishi Babana ya rike hannun tamau. 


Suka juyo suka fuskanci juna su biyun, kowanne zuciyarshi na tafasa, inda Baban Kaduna ya yi amfani da gadarar shekaru biyu da ya tserewa Baban ABU da su ya ce, “Ni sa’anka ne Ahmadu? Ko ko akwai irin wannan wasan tsakaninmu?” Babana ya ce, “Babu ko daya, amma a nan kam ka yi zalunci in ka takurawa daya don amfanin daya. Aure kuma Fa’iz ba zai saki ba in dai a kan 

don kar wannan yarinyar ta mutu ne. Mutuwa lokaci ne kuma tana kan kowa, sannan lazim ce baka isa ka kara mata dakika daya daga wanda Ubangiji ya riga ya rubuta mata ba. 


Ni dai ni na haifi Fa’izah in kuwa ni din ne to in ta mutu na yafe, zan dawwama da farin cikin cewa da igiyar auren Fa’iz ta mutu cikin cika burin mahaifinmu Abubakar Bamalli. 


Sai dai fa abin bai kai da duka ba, Fa’iz ya wuce duka! Sai dai in Fa’izah ta kashe kanta a kan shirmen banza ta mutu kafira ba ruwana, amma aure ko ka kunce sai na sake daurawa. Ba a haifi dan da ya isa ya ki bin umarnin A.B Family ba, ba a haifa ba in dai ina da rai, ba kuma za a haifan ba. Fa’izu jeka abinka sai na neme ka, kada ka kara wahalar da kanka zuwa asibitin nan’. 


Fa’iz ya juya da sauri ya fita duk gaban rigarsa ya baci da jinin dake fita daga hancinsa. Ya dauki motar Aliyu da suka zo a ciki ko rufewa bai yi ba ya yi ribas da gudu ya fita daga estate din baki daya ya bar garin Giwa baki daya ya nufo Kaduna. 


Yadda ya shigowa Mama falo ya firgitata, sai dai kuma ba ta yi mamaki ba sam, habon ne da bacin da rigarsa ta yi da jini ya daga mata hankali, amma ba ta nuna ba. 


Tozali na farko da Abubakar Fa’iz dinta bayan shekaru takwas. Amma ta ganshi cikin wannan halin mara dadi da kyawun gani. Ta yi tagumi ta zuba mashi ido sai zufa yake. 

Daga bisani ya mike ya ware karfin A.C falon gaba daya da fanka, ya yi kwance rashe-rashe a tsakiyar falon yana lumshe ido yana budewa a hankali, shi kadai ya san abin da ke cin zuciyarsa, sai ko Ubangijin da ya halicci zuciyar ya sirrantata ya sanya mata hijabi don ta zama sirrin dan Adam da Ubangijinsa. 


Ita Mama zato take ma Fa’iza ce ta fasa masa hanci, ta ce cikin ranta, ai tayi da sauki da ba kan duka ta rotsa maka ba. Ta shige kitchen ta sakar masa labule ta janyo masa kofa. 


oe 2K 2k 


Karfe biyar na yamma agogon dake dakin asibitin ya nuna, wanda ya yi dai-dai da lokacin da na ja dogon numfashi tare da ware dukkanin idanuwana kan likitoci biyu dake kaina. Dr. Habib da Dr. Imoh suka dubi juna suka yi murmushi tare da zare na’urar da suka makala mini. Kwata-kwata na mance komi, ban san abin da ya faru dani ba da har ya kawoni gadon asibiti. Dr. Imoh ya ce, “Ya ya dai Fa’ ya?’ 


Na yi murmushi na ce, “Bani da lafiya ne na ganni a clinic?” 


Dr. Habibu ya ce, “Of course Fa’izah! Za ki dinga fama da migraine (ciwon kan barin kai guda) lokaci zuwa lokaci. A duk lokacin da kika ji ya tashi, akwai kwayoyin da zan baki ki dinga hadiya kin ji ko?” 


Na gyada kai. Suka juya suka fita suka jawo min kofar. Nurse ta shigo ta gyara min kwanciya ta fita. 

“Yan’uwa da iyayena suka shiga shigowa mutum uku-uku suna duba ni suna fita. Shigowar Ummi da Zaneerah daga karshe ya tariyo min abin da ya faru awanni shida da suka gabata. 


eeeees An daura aurena da FA’EEZ, FA’EEZ BAMALLI.!..... Fa’izun gidan Baban Kaduna...... Fa’iz Yayan Zaneerah, Fa’iz mugu, azzalumi, makaryaci, maketaci mai cin amanar ZUMUNCI da tozarta shi a gaban ko a bayan idon kowa... Munafuki, masharranci.... Fa’iz da na_ sani? Fa’izun Hajjah? Fa’iz da na tsana tamkar mutuwata...... Fa’izun da ya nuna min tsanar da a duniya babu wanda ya nuna min kwatankacinta, mai cin mutuncin mahaifiyata! Fa’iz! Fa’iz!! Fa’iz Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa......!!!” Na mike zaune sannu a hankali ina bin Ummi da Zanirah da kallo, wadanda bayan kalmar sannu da jiki basu kara ko tari ba. Na kai hannuwana duka biyu na rike kaina dake juyawa yana sarawa tamkar ya tsage. Idanuwana suka kada suka yi jajawur suka kankace, na dubi Ummi, Zanira, Yaya Aliyu da Babana da suka shigo daga baya. A lokacin ne hawaye suka soma zuba min tarara! Na bude baki zan yi magana na kasa. Wani kunci da bakin cikin da ba zan iya fassarawa ba ke azaIzalar tsakiyar kirjina, na kai hannuna na dafe kirjin na ce cikin rishin kuka, “Baba anya kana sona kuwa? Da hadin bakinka aka yi min haka? Da saninka aka daura min aure da Ya Fa’iz? In kun hanani Nazir ku rasa wanda za ku lika min duk cikin zuri’armu sai Hafizin Hajjah? Baba 

kana sane da tsakanina da Fa’iz tun tali-talin kuruciya har girma! Baba Fa’iz fa ya tsaneni nima haka!! Makiyinka baya taba rikidewa ya zama masoyinka, har abada Baba. 


Don me baku hada shi da Ummi dake son shi yake son ta ba? Ya ya kuke so na yi da nauyin so, kunya da alkawarin da na yiwa Dr. Naziru?” 


Na shiga rurin kuka mai tsima zuciyar duk mai imani, balle MAHAIFI. Amma Baba bai ce komi ba, karewa ma fita ya yi daga dakin baki daya. 


Su Aunty Hauwa duk suka sake shigowa, ashe suna kofar dakin basu tafi ba. Yaya Aliyu ya dubi Aunty Hauwa cikin bacin rai ya ce, “Gaskiyagaskiya ba a kyauta ba”. 


Aunty Hauwa ta harare shi ta ce, “Saboda me baka gayawa wanda ya fita ba? Ko kuma kana so ka kara da ta biyu ne?” 


Ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce, “Ki bar maganar wasa Aunty Hauwa, ko kadan babu wannan tsohuwar ajiyar a zuciyata, illa gaskiya duk inda take dole in fade ta, ba a kyautawa Fa’izah ba! Ko babu komi yanzu Fa’izah matar Fa’izu ce, kinga kuwa ai babu sauran zance”. 


Aunty Hauwa ta yi murmushi, ban ga alamar ba a kyauta min din ba a fuskarta. Yaya Aliyu ya ce, “Fa’izah bani da ilimin (psychology) amma ina da tabbacin yadda kika ki auren nan haka Fa’iz yake kin shi ko ma fiye. Haka na dauka kafin ya dawo tun sanda iyayenmu suka fito da zancen. Amma Fa’iz ya zo da wani sauyi mai ban mamaki da na kasa fassarawa, he’s completely a changed person, unpredictable. Hajjah kanta 

yanzu ba ta son zancen auren ganin halin da kike ciki, haka Baban Kaduna da Baba Barau. 


Baban ABU da Baba Na’ ibi da sauran hadin sune kawai, kuma su kadai ke son abin a yanzu. Yanzu Baban Kaduna ya gama fada da Baban ABU a kan a raba auren tunda yanzu ya fahimta abin da babu wanda ya fahimtar da shi a baya. 


Don haka ki kwantar da hankalinki ki saki ranki ki koma cikin nutsuwa da walwalarki, babu inda auren nan zai je tunda kaso mafi rinjaye kuma (most powerful) yanzu basu so. Ki bisu da duk abin da suka umarceki da dadin rai, ki kwantar da kai ki roki Fa’iz in har baya sonki ya baki takardar saki, na rantse miki in har yanzun baya sonki zai baki ko don maslahar kansa, ni kuma idan har ya baki, ni kuma na yi alkawarin duk yadda zan yi zan yi in ga kin auri zabin ranki, wa ma kika ce yake da suna?” 


Maimakon kalaman Yaya Aliyu su faranta mini ji na yi sun bakanta mini kamar akwai rainin hankali a cikinsu, musamman da na ga Aunty Hauwa ta bamu baya tana danna waya, ba shakka dariya take. 


Na dubi Yaya Aliyu a hankali da rinannun idanuna jage-jage da hawaye. Akwai wani irin yanayi a tattare cikin kwayar idonsa wanda ban saba gani ba in yana magana. A duk sanda Yaya Aliyu ke magana, kwayar idanunsa kan nuna gesture wanda ke tabbatar da abin da yake fadi. Amma a yau, ina shakka, Ali Na’ibi ya ki mu hada ido in hango wancan gesture din dake cikin kwayar idanunsa, ya juya wani bangaren ne da

ban baya kallon idanuna, kuma fuskarshi ta yi jawur abinki da farin mutum, farin Bafillace, Bamalle. Tsagin Mallacin ya fito rada-rada a gefen fuskarsa, kamar wanzamin A.B ya tisa. 


Idona a kanshi bana ko kiftawa na ce, “Yaya Aliyu ka rantse min da Allah ba da yawun Fa’iz aka daura mana aure ba”. 


Yaya Aliyu ya dan rikice kafin ya ce, “To Fa’izah me ya kawo rantsuwa, baki yarda dani ba kenan? Za ki dora min kaffara a kan abin da bani da tabbacinsa”. 


Na ce, “Duk ba haka bane Yaya Aliyu.....” 


Aliyu ya dubi su Ummi da su Aunty Hauwa kowacce sai ta sunkuyar da kai aka rasa mai yi min rantsuwar da nake so ya yi min din, duk da na san basu da masaniya a kan komai, musamman Ummi. 


Aunty Hauwa ta ce, “Fa’izah ki saurare ni, duk kin bi kin ta da hankalinki a kan abin da bai kai ya kawo ba. Fa’izu dan’uwanki ne ko babu aure tsakaninku ba zai cutar dake ba, ko baya son naki aure Ibada ne ba don biyan bukatar rai ake yinsa ba ko soyayya kadai. 


Ki dubi girman zumunci da nonon da iyayenku suka tsotsa tare ki kwantar da hankalinki ki manta da kuruciya..... daban take da GIRMA! Dukkaninku jiya ba yau ba!! Babu wanda bai mallaki hankalinsa ba, abin da kuke yi a da duk kuruciya ce..... Wani irin kallo na yiwa Aunty Hauwa wanda ita kanta ya tsoratata. Ya kuma ba ta mamaki a yadda dai matsayinta yake a gare ni da yadda 

muke girmama su. 


Na ce, “Uhm! An daura fa! Nima shaida ce a kan hakan. Sai dai wallahi yadda aka daura haka za a sunce. Wallahi-wallahi in har ina numfshi babu inda auren nan Zai je daga kaina ba zaku sake ba A.B. Da in yi zaman aure da Fa’iz na gwammace in kare rayuwata haka nan single! Da in zauna da Fa’iz gara min zamana a kabarina, gara na ga mutuwata, gara min zama da bakin kumurci.... gara na rasa rayuwata dungurugum!!!” 


Wani irin juyi da barin kaina ya shiga yi ya tabbatar min (migraine) da likita yake magana ya tabbata. Na dafe kaina na shiga kuka sosai. Na ci gaba da fadi cikin gunjin kuka. 


“Ya ya ma hakan zai taba faruwa? Wallahi ba zai yiwu ba!” Ni kadai kamar mahaukaciya nake ta wannan sambatun sun yi min shiru. Wannan ya kara tunzura zuciyata. 


Tunanin halin da bawan Allah. Dr. N zai kasance a ciki idan ya tsinkayi wannan labarin ya kara Sanya ni tsandara kuka da kara duka a tare. 


28K KK 


Kwana biyu kacal duk na rame fiyet na zabge na fita a hayyacina. Sai ka rantse na yi shekara ne a kwance. Likita ya bamu sallama tare da kashedi iri-iri ga su Babana. Baban Kaduna ya ce, “Af! Ai aure ba makawa za a kwance shi me ya yi zafi?’ 


Wata sabuwa in ji ‘yan caca! Hajjah ta dawo ta girgije ta sanya ranar biki kwanaki bakwai masu zuwa, kasancewar ana jiran Basheer da zai dawo 

kwanaki uku da zuwan Fa’iz. Ashe daman rudewar ganin halin da na shiga ya sanyata canza alqibla a baya? Uhm! Zan ga wanda za su yiwa bikin kuwa. 


Babban rangwame ga zuciyata ban sa fuskar azzalumin ko sau daya a idanuna ba balle keyarshi. Wannan ya tabbatar mani lallai ne shima yana tsoron haduwar mu which I believe must be the most dangerous approach bayan gushewar shekaru masu dama. 


Ummi kam ta rungumi kaddara, ta bi umarnin iyayenta, a cewarta, ilyayenmu ba za su taba zaba mana abin da zai zama cuta garemu ba. Ba za su taba kaimu mahalaka ba (Ummi fa ba ni ba). Karfe tara na dare na kadaice kaina cikin (store) kuka nake kamar raina zai fita. Irin shirye-shiryen da na ga A.B baki daya na yi ya tabbatar mani biki babu fashi za su yi shi. Ba ruawan kowa dani, ba mai shiga sabgata don da alama basu ma dauke ni a cikakkiyar mai hankali ba. 


Da na yi na gaji, babu mai rarrashi, babu kuma abin da kukan zai tsinana mini, sai na daura dukka hannuwana biyu a ka na shiga kwarara ihu tun karfina, ina bubbuga hannuwana jikin buhunhunan masara da shinkafa dake lode a store din. Jama’ar gidan duk suka baro abin da suke yi suka taru a kaina ban ga alamar akwai mai shirin lallashi na ba ko tambayar ba’asin ihun da nake yi. Kallo na suka tsaya yi tamkar masu kallon talabijin. 


Ummi ta yi tsaki ta ce, “Allah wadaran rashin tawakkali da rashin hankali da sakarci wallahi! 

Shin cikinmu don wa kike wannan haukan Fa’izah? Aure dai baya wurinmu kuma bamu muka daura ba balle mu warware miki, don haka ki kyale mana kunnuwanmu su huta’”’. 


Hajjah ta fito daga kitchen ta ce, “Don son Annabi wanda duk ke son gamawa da duniya lafiya ya tafi a wurin nan ya kyale Fa’izah!” 


Na sake sheko ihun tun karfina, na ce, “Hajja kun cuce ni, ku doke ni ku hanani kuka? Ku kulla min igiyar aure da mutumin da na ki jini a duniya fiye da mutuwa ta, bayan kin raba ni da wanda nake so da farko da na karshe, sannan ki ce ba zan yi kuka ba? Shin in ban yi kuka ba ya rage min radadin da zuciyata ke yi kashe kaina kike so in yi don bakin ciki ko me?” 


Baban Giwa ya ratso mutane bayan ya karyo reshen dalbejiya ya ce, “Uwar waye ta cuce ki ba dai uwarmun ba ko? Ja’irar yarinya har nake daga hakarkari nake son ayi miki son ranki don a zauna lafiya, ashe baki da mutunci baki da da’a? Hajjah kike cewa ta cuce ki?” 


Ya zuge ganyen baki daya ya shiga dankara min dukan da ake kira dukan mutuwa, wanda tunda nake a rayuwata ko makamancinsa ba a taba kwatanta min ba, amma bakina bai mutu ba, bai huta ba da fadin “Hajjah kin cuce ni.... kin raba ni da burin da na ciwa rayuwata.... ba zan taba yafewa ba muddin rayuwata.....” 


Hajjah ta soma kuka da idonta a yayin da ta kama hannun Barau ta ce, “Kyale ta haka nan, Fa’izah ba ta cikin hankalinta, ka kyaleta na ce kada ka yi abin da za ka zo kana nadama, in kuma baka bari 

to ka sauke zuciyarka a kaina ka karasa min dukan”’. 


Baba Barau ya yar da tsumagiyar ya yi waje fuuuu! Kamar kububuwa, jikinsa har tsuma yake. Na tabbatar da Babana ne yau sai dai a dauki gawata in ya so shima a kashe shi. 


Hajjah ba ta yi fushi ba ta kama ni za ta mikar dani, cikin kurarin kuka na ce, “Kada ki kuskura ki taba ni..... Daga yau ba zaki sake ganina ba balle ki yi iko dani. Ki tuna Ubana kika haifa ba ni ba, don haka ko kashe ni aka yi babu ruwanki......” 


Zaneerah da Ummi suka saki kuka, “Fa’izah kina da hankali?”’ 


Na ce, “Kwarai, Baba Muntari da Aunty Hauwa ke rabon ciwon hauka har na je Kaduna na samo. Ko me za ku ce ku ce wallahi banni zaman aure da Fa’izou...... Jini ke bulbula ta hancina yana shiga bakina inda Baban Giwa ya shauda min dalbejiyarshi a kan hanci. Na kai hannu na share a yayin da na zaro jajayen idanuna suka kumbure suka suntume suka yi luhu-luhu jajir. Na ce, “Ku bace min da gani ko in kakkarya ku na rantse yanzun nan, manyan munafukai algungumai, ai daku aka kulla komai amma babu wadda ta gaya mini. Tsakanina daku sai Allah ya isa!” 


Ai kamin in rufe bakina na nemi kowaccensu daga yaran har manyan na rasa. Na ci gaba da gunza kuka ban ko damu da radadi da zugin da jikina ke yi mani ta ko ina ba. 

Muryar Yaya Aliyu daga tskar gida ya tabbatar mani ya shigo gidan. A yayin da Ummi ke fadi mashi cikin kuka........ “YAYA ALIYU FA’IZA TA HAUKACE!” 


Wadannan sune kalamai mafi firgitarwa da Aliyu Na ’ibi ya taba ji a tsayin rayuwarsa. Baya ga dogon salati da ya ja ya dire ya tsarkake Ubangiji ya yiwa Annabi salati, sai ya sanya hannu ya zare hularsa da takalmi ya ce, “Tana ina?” 


Hajjah dake sharbar kuka zaune a kofar kicin ta yi mashi nuni da hanyar store. Aliyu ya shigo a hankali ya kunna fitilar da na kashe ya zauna gefena a hankali, ya dubi yadda na yi jina-jina, face-face cikin hawaye, jini da majina, ya matso kwallar da ta tarar masa cikin ido. 


“Shin wane ne da wannan danyen aikin haka Fa’izah?” 


Na ja shesshekar kuka cikin dusasshiyar muryar da ta dushe gaba daya, “Kadan kenan tun yanzu kan DAN DA KOWA KE SO. Nan gaba in na batawa Fa’iz mai yiwuwa a nakastani ko a hura wuta a babbaka ni Aliyu? Ba dukan kawo wuka ba, ko yankani A.B za ku yi gunduwa-gunduwa ba ni auren nan. Na gwammace in bi yawon dandi, da dai in yi karashen rayuwata a matsayin matar FA’EEZ BAMALLI!” 


Aliyu ya kaskantar da murya ya ce, “Fa’izah! Abin bai yi zafin haka ba ai. Kash! Ki bar furta kalmar nan ta “DANDI’ ba don ni ba, ba don halina ba, ba don halinsu ba su duka iyayenmu. Sai don darajar da Allah ya yi miki ta ‘ya mace mai cikar mutunci ‘yar manyan mutane, kuma 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...