ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6  by Sumayyah Abdul-kadir


Idona ya cicciko da kwalla kadan ya rage su shimfido a kundukukina, na ce, “Yaya Aliyu ka taimake ni ina son Naziru, ina tsoron halin da zan shiga in na rasa shi. Fadar A.B ba fadar Allah ba! Bani da wanda zai taimaka min ya shige min gaba idan ba kai ba. I cannot afford losing him...” Yaya Aliyu ya zuba min ido na san mamakin halinmu na mata yake yi, a raina na ce, “Har an fika Aliyu Haydar?’ 


Ya saukar da kai bisa yatsun Fa’izah karama dake bisa cinyarsa, ya ce, “To ni dai Fa’izah babu abin da zan iya a kan wannan rigima da kika je kika jajibo. Zan yi dai iya kokarina in ga cewa ba a yiwa dangin Nazir wulakancin da za su tafi damu a baki ba idan sun zo. That is all. Ki jira hukuncin Hajjah a gobe”. 


Tun daga nan jikina ya kara yin la’asar. Na tashi na bar Yaya Aliyu don a ganina ba shi da abin da zai iya yi min din da gaske kamar yadda ya ce. Karfe tara na dare na kira Maman Kaduna nake sanar da ita zuwan dangin Nazir a gobe, don na manta ban sanar da ita a Kaduna ba. 


Na kare da cewa (cikin murya mai ban tausayi) “Mama na san ko da kowa bai goyi da bayan in auri Dr. Nazir ba, to ban da ke don ke uwa ce mai son duk abin da ‘ya’yanta ke so. A ganina lokaci ya yi da za a kawo CANJI a kan auren zumunci da ake tilasta mu yi, domin ZAMANI YA CANZA. 


A duk lokacin da zamani ya canza, dolen al’umma ne ta tafi tare da canjinsa in har tana so ta ci gaba. Auren zumunci ba laifi bane amma 

idan akwai son ran ma’auratan, in ko babu na daya daga cikinsu ya zama auren MUGUNTA, domin dole za a zalinci daya. 


Ke kadai kika rage min da zan kawowa kukana ki share min hawaye...... ki taimake ni Mama su amshi maganar Dr. Naziru da muhimmaci da karramawa. Wallahi ina sonshi Mama ba zan iya hakura haka in barshi ba a kan tsarin Hajjah... Ki taimake ni Mama don Allah, he’s the stranger that I’m always praying for!” 


Mama shiru ta yi na lokaci mai tsawo, kamin ta aje wani gwauron numfashi wanda ya kara samun suspence ya sagar da gwiwoyina. Domin numfashin da Mama ta sauke na nufin ba za ki taba cin nasara a soyayya ba Fa’izah. Ba za ki cimma ko daya cikin burarrakinki a rayuwa ba. 


A karshe ta yi tashin gwauron zabi ta murje jin nauyi da kawaici ta ce, “Fa’izah! Sai dai ki yi hakuri kam. Amma wannan yaron BA ZA KI AURE SHI BA! An riga an yi muku mazaje ba tun yau ba”. 


Da maganganun Mama na kwana zuciyata jagule ta kasa sukuni. Wadanne irin mazaje Mama ke ikirarin an mana? Mu bamu sansu ba? Mama na nufin ba zan auri Nazir ba? Mama na nufin ba zan taba cimma burirrikan rayuwata ba? Ya ALLAH ka sa kada shima in rasa shi kamar yadda na rasa Aliyu-Haydar. Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar..... ranar da za a ce shima Dr. N na rasa shi. 


Ni sai yanzu ne ma na san ina son Dr. N, hankalina ya yi matukar tashi da al’amarin dake 

shirin faruwa dani. Ya ya zan yi iyayena su amshi Dr. N? Na yi tunani iyaka tunani bani da mai mara min baya cikin dangina kakaf, kowa tsoro yake kada in shafa mishi kashin kaji. 


Na yi kuka na yi kuka har na ji babu dadi, idanuwana suka shiga yin wani yaji-yaji saboda kuka. Tunanin halin da Dr. N zai kasance in ya tsinci labarin ba za a bashi ni ba, da wanda nima zan kasance da abin da iyayena ke nufina da shi, shine babbar damuwata. Shin me ya mantar dani matsalar gidanmu tunda fari? Na yi zurfi a son Naziru? Me ya mantar dani rigimar gyatumar mu mai ran karfe? Babu ko tantama SO ne, SON NAZIRU ne. 


Ya makantar dani ya kurmantar dani har bana iya tunanin me zai je ya zo, har bana tuna baya balle abin da gobe za ta haifar. A wannan rana na yi fatan a ce ina ma ban fito daga A.B family ba! Ina ma ban kasance cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa ba. 


a8 OK eK 


Karfe goma na safe su Ummi suka yi shirin tafiya taren su Bashir a filin jirgi. Tun asuba da na yi sallah fuskata babu walwala, kallon kowa kawai nake zuciyata a cunkushe da bakin ciki da bacin rai maras dalili. 


Hajjah yau ko gaishe ta ban yi ba, babu wanda na yiwa magana. Na zubawa allon talabijin ido kuri kai ka ce program din nake saurara, amma ina! Zuciyata ba ta tare da gangar jikina, abubuwa masu ban al’ajabi da ban tsoro kawai take was

safa min masu shirin faruwa dani. 


Kafin karfe goma na safe gidanmu ya cika ya batse da dan Adam, sai busa algaita ake “yan daurin aure suka fara layin shigowa gai da Hajjah suna fita, “yan’uwa ne da abokan arziki. Kafin Babanninmu su shigo sun sha ankon farar shadda (getzner) sai sheki suke. 


Suka zube a falon Hajjah suka kwashi gaisuwa suka fita. Ina daga uwar daki ina hango ficewarsu ta taga daya bayan daya. Mintina talatin bayan fitarsu na ji gabana YA FADI! A dai-dai lokacin da dakikar agogo ya nuna karfe goma sha daya na rana, a lokacin ne aka daura aurarrakin masu ban mamaki, da suka ajiye kundin tarihi da wani aure bai aje ba cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa. Wani maroki mai zakin muryar tsiya yake fadi da murya mai karsashi da kwarzantawa cikin babatun magana “ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!!” Sai da ya fada har sau uku. “An daura auren FA’?IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA da FA’?IZU MUKHTAR ABUBAKAR GIWA. HADIZA da MUHAMMADU BASHIR, a kan sadaki lakadan ba ajalan ba. Allah yasa anyi a sa’a, yaSa anyi sai bakin rai, Allah ya sanya alkhairi ameen.....”°da sauran babatu irin na maroka. 


Maimakon in kira yi sunan Allah sai na kwarara ihu da iyakacin muryata na zube a wajen a sume. 


Ban kara sanin me ke faruwa a duniyar ba. 2k ok 

Jirgin Boeng 708 ya sauka a filin jirgin saman Mal. Aminu Kano da misalin karfe daya na ranar da ta kasance Asabar, wato awanni biyu da daura auren. Jirgi ne da ya taso daga Ukrain zuwa Nigeria bayan shafe awanni masu yawa yana keta hazo, kafin ya wulwulo kasa ya tsaya a cyprus ya sha mai sannan ya keto kasarmu mai dimbin albarka. 


Sai da passengers kaf suka gama fita kafin Pilots din su fito cikin fararen uniform dinsu. Shine na karshe a saukowa. Fari sol! Mai madaidaicin jiki, zai fi kyau ka ce ba shi da kauri sai fadin kirji wanda da ka kalla za ka san gym ya samar da shi. Ma’abocin wasu ilhamomi da nasibobi da dama da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. 


Ya saya fararen idanunshi cikin gilashi mai duhu ainun samfurin ‘KAREN MILLEN. Sajen da ya zagaye gefe da gefen fuskarsa baki sidik kwantacce wanda a da baya da shi bai boye tsagin mallacinsa ba. Sai ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa ya fiddo cikakken Bamallen sa, kuma Bafillace. Dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ya dama, ya kutsa cikin ilmummukan zamani daban-daban. 


Dogon hanci gare shi kamar ruler aka sa aka ja shi aka daidaita shi a tsakanin idanunsa. Idanunsa 

dara-dara wadanda suka dan shige loko kadan farare tar masu sheki da maiko (oily eyes) wadanda duk cikin zuri’arsu maza da mata shi kadai aka ya yiwa wannan ilhamar. Idan lissafin da yake yi dai-dai ne yau shekarunsa takwas da barin gida ba tare da ya sake ko da waiwayarta da sunan hutu ba. 


A zubin halitta da kirar jiki ya fi kama da Ahmadu A.B, a halayya kacokan Abubakar Giwa ya kwaso ba wani cikin zuriyarsa ba. 


Don haka, ka ce ga hakikanin halayyar FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA, abu ne mai matukar wuya. Za ka san halinsa ne kadai idan ka zauna da shi, zaman ba na kwanaki ko watanni ba, sai dai shekaru. 


Shekarun ma sai idan kwana kake tare da shi daki daya ka kuma tashi tare da shi, halin da ake kira halin MAZAN JIYA ba na YAU ba, and difficult to be studied by sociologists and psychologists. Idan aka ce su karanci irin pilot Fa’iz za su yi placing dinsa ne kawai (upon hypothesis) but not a dependent variable. 


Daga fitowar shi daga jirgi har shigewar shi wani ofishi (pilots changing room) idanun KhadijaUmmi na kansa, tana mai yiwa Allah tasbihi da godiya mara iyaka da wannan miji da Allah ya ba ta wanda ke ninkaya cikin zuciya da mafarkinta, ba ta taba tsammanin akwai ranar zahirantar mafarkin nata ba. A hankali ta ji danshi a kan fuskarta, wanda ba ta ko tantama hawayen farin ciki ne. 


Har zuwa lokacin da ya gama shige da ficensa a 

(airport) din tare da abokan aikinsa, ya canza kaya zuwa kaftan na farar lallausar shadda (Hilton) da ruwan kasar hula a kansa, takalmin fata dake kafarshi shima ruwan kasar ne. Ya janyo trolley dinsa zuwa inda ya hango fuskokin masu kama da tasa fuskar, wanda komai daren dadewa suna gilmawa cikin idanunsa, wato fuskar zuri’ar Abubakar Bamalli, wanda ya fi so da gani shi ya fara ganin, wato Aliyu Na’ibi. 


Da sassarfa Aliyu ya karaso suka rungume juna shi da Fa’iz, rayuwarsu ta baya ta dinga dawo masa tar-tar kamar a majigi. Abubuwa da yawa ba zai manta dasu ba. Cikin taron nan kaf na mata da mazan Bamalli, manya da yara, wadanda ya sani da wadanda bai sani ba, musamman kananan yara, ya hanga ya duba bai ga Zahrar cikin taurarin ba. 


Ya ga Zanirah, ya ga Ummi, Mus’ab, Junior Yahya, Shu’aib, Walida, Abdallah da wata karamar yarinya mai tsananin kama da Fa’izah (Khausar), da sauran kannensa ‘ya’ yan Baba Barau, Sadi, Salisu, Sani da Na’ ibi. 


Mutum daya ce kawai babu, wato KANWAR kuma abokiyar fadan da a yau ta juye ta rikide zuwa matarsa ta sunnah. 


Ko da wacce irin fuska za ta karbi al’amarin? Ko da wace irin fassara za ta fassara shi? Ko da wanne irin hannu Za ta karbe shi? Abin da ya sani ya kuma kwana da da sani ne cewa, Fa’izah! Ba ta da makiyi a duntya irin sa!!! 


To amma ai shi sonta yake yi tun can din ma. Har kuma gobe son ninkuwa yake yi irin kaunar da 

bai taba yiwa kowa a duniya ba, in ka dauke Mama da Baban Kaduna wato iyayensa. This is his own style of love! 


To amma da wane language (yaren) zai yiwa Fa’izah bayanin hakan har ta yarda ta fahimce shi, ta karbe shi a matsayin miji a gareta? Ya kuma wanke wancan dattin da ya dade yana yabawa kansa a idanunta? 


Don haka kallo daya za ka yiwa pilot Fa’eez ka karanto matsananciyar damuwa cikin fararen kwayar idanunsa. Duk da yaken da yake yiwa Aliyu da sauran ‘yan’ uwansa. 


Yasa hannu ya karbi little Fa’izah hannun Zanirah ya dora a kafadunsa yana murmushi, kallo daya ya yiwa Ummi ya bude baki yana mamaki, ganin yadda kibarta ta zaizaye gaba daya, abin da babu wanda ya taba tsammani. 


Shi da ita murmushi suka yiwa juna, wanda ga Pilot Fa’iz murmushin ‘yan’ uwantaka ne. Kuma ba annuri a fuskarsa har suka shisshiga motocinsu, yana motar Aliyu ne, Aliyun na tuki shi yana gidan gaba, Ummi da Zanirah da ‘yarta a baya. 


Sai dai tunda suka hau titin Zaria Road dodar wanda zai sada su da garin Zaria, kowa ya fahimci Pilot Fa’iz Bamalli cikin matsananciyar damuwa yake. Ya sanya fuskarsa cikin tafukansa Allah kadai ya san me yake tunani a zuciyarsa. Ummi ta yi tagumi a kujerar owner side da take zane. Wane irin mutum Fa’iz ya koma? Wane irin ango ne wannan babu wani alamar kulawa ko kwayar murmushi ga amaryarshi da aka daura 

musu aure yanzu-yanzun nan? Wane irin mutum ne shi da zai bar kasar haihuwarshi shekaru har shida da wani abu ya dawo babu alamun farin ciki a fuskarshi? Me ke damun shi? Anya Fa’iz na farin ciki da dawowar sa cikin ‘yan’ uwansa? Anya Fa’iz lafiyarshi kalau? Anya Fa’iz na murna da auren su kamar yadda take tsammani? Ta jerowa kanta duka wadannan tambayoyin lokaci guda, ba ta da amsar ko daya, don haka ta sunne kanta cikin cinyoyinta ta soma kuka a hankali. 


Daga Aliyu, Zanirah da sauran kannensu dake cikin motar zuwa uban gayyar, babu wanda ya tambayi Ummi dalilin kukanta. Ga Aliyu shi kam abin ne ya zo mishi wani irin banbarakwai cikin sarkakiya. Bai san irin bayanin da zai ma kowannensu ba. Babbar fargabarshi yadda Fa’izah za ta karbi zancen aurenta da Fa’ iz. 


A karo na farko ya ji haushin kansa kan munafuntarta da ya yi jiya, don me bai gaya mata gaskiya ba? Don me ya rufe mata? In kowa ya rufe mata shi bai dace da hakan ba. 


Ita kuma Ummi tunaninta da Fa’iz aka daura mata aure amma ganin halin ko in kula da ya nuna mata ya sanyata kuka. Shin da wane yare zal yi mata bayanin cewa da Bashir ne? Ya ya Ummi za ta tallafi maganar bayan yana da masaniyar cewar ta tsani halayyar Basheer fiye da kowa? Ta ya ya nitsattsiyar yarinya ‘yar kauyen Giwa ta cancanci tantirin dan duniya irin Yaya Basheer? 


Kaico da tunanin Hajjah! Kaico da bahagon tu

nanin iyayensu wurin hada irin wannan rikitacciyar auratayyar zumunci ko bata zumunci? Su kam sun haye! Yanzu na ‘yan bayansu yake ji. 


A zuciyar Zanirah cewa take yi, “Ina ma ban zo garin ba kwata-kwata balle in ga wannan rikitacciyar rana......! A dai-dai lokacin da Aliyu ya karya kan motar cikin tafkeken (gate) din ABUBAKAR BAMALLI HOUSE.....” 


36 6 Ok ok 


WANE NE NAZIRU GALADANCHI? 


Major General Sani Galadanchi shine mahaifin Dr. Nazir. Da na farko wurin iyayenshi, kamin haihuwar shi sun kwashe shekaru masu tsaho basu samu haihuwa ba. Da Allah ya kawo Naziru sai hakan ya zamo musabbabin nuna mishi tsantsar gata wanda babu kwaba ko tsawatarwa a cikin sa. 


Nazir ya tashi yaro dan hutu tun yana sakandire, sune samarin da ake kira ‘yan (high life) a lokacinsu. Haka nan bayan haihuwar Nazir sai da suka kwashe shekaru takwas zuwa tara kafin su samu haihuwar Haulatu. Daga Haulatu yara ne maza uku daya na bin daya duk bayan shekaru uku. 

Duk da jin dadi da sakewar da Nazir ke samu bai sa shi yin wasa da karatu ba, domin ya ga amfanin ilimin wurin mahaifinshi. Ya so ya tafi soja don ya gaji ubansa amma Baban ya dage kan harshen Larabci yake son ya karanta, baya son shi da aikin soja, babu kwanciyar hankali a cikinsa. 


Su shan sigari wannan duk a wurin Larabawa ya koya, sai dai sam in ya zo hutu baya sha a gida sai ya koma. Bai fara neman mata ba sai da ya kammala degree ya fara masters a zuwan shi bautar kasa garin Lagos, inda ya yi wani aboki Tim ya koyar da shi mu’amala da mata, don haka da ya koma Taiwan sai idonshi ya bude da hakan. 


A can ya kammala PHD ya dawo Kano ya fara aikin da yake yi a Bayero. Rasuwar Tim ta hanyar muguwar cutar (SIDA) Aids bai sanya Nazir Sani kintsuwa ba sai haduwar shi da Fa’izah A.A Giwa. 


Bai taba neman kowacce diya mace da niyar aure ba sai a kan Fa’iza, kamar yadda bai taba son wata diya mace tsakani da Allah ba baya ga Fa’izah. Bai taba tunanin zai bar yaudarar mata ba sai a kan Fa’izah. Daga ranar da ya dora ido a kanta, bai kara kula wata yarinya da sunan iskanci ko yaudara ba, domin yana ganin kintsattsiyar yarinya kamar Fa’izah ba ta dace da watsattsen miji kamar shi ba. 


Don haka ya kimtsa kansa, tun hakan bai zamo dalilin da za a hanashi Fa’izah ba. Tunda ya tabbatarwa kansa aurenta zai yi domin Allah da soy


ayya. 

Ya yarda ya amince da duk zargin da ake masa na cewa shi din dan iska ne, ya yarda ya kuma amince bai taba musantawa ba, kamar yadda bai taba cewa yana da wani hali na kirki ba. To amma wanda duk yake tarayya ta jiki da Naziru Sani, zai yi shaidar cewa mutum ne wanda baya wasa da sallah, kuma zuciyarsa daya ce da ita yake zaune da kowa, sannan ba shi da tsoro. Baya tsoron uban kowa, sannan abin hannunshi bai rufe mishi ido ba sam. 


Daga ranar da suka yi magana da Abdullahin Haulatu, ranar ba ta zagayo ba sai da Dr. Nazir ya gabatar da maganar Fa’izah ga iyayenshi, ya kuma roke su da aje mishi neman auren ta sati mai kamawa. 


Hajiyar su Haulatu ta yi matukar farin ciki da Allah ya nuna mata ranar da Nazir ya kawo mata zancen aure da bakinsa da ranta kafin mutuwar ta. “Yammata iri-iri ta sha nemawa Naziru yana fitittikewa, shi aure ba yanzu ba sai ya ci lokacinsa matarshi ma ba a haife ta ba. 


Da farin cikinta da rawar jikinta ta isar da sakon Nazir ga General, shima ya yi farin ciki sosai, suka yi ta yiwa Allah godiya. Tabbas addu’ar iyaye ba ta faduwa kasa banza a kan ‘ya’yansu, ko ba jima ko ba dade. 


A washegari ya tura kanin mahaifinsa da kanensa biyu da wan Hajiyarsu wurin iyayen Fa’izah. Haulatu ce ta ce dasu Kaduna za su wurin Alh. Muntari don shine madaurin auren su, ta karbi address wurin Aunty Rabi. 


Tarba ta girma da mutunci Mama ta yiwa iyayen 

Nazir ita da Baban Kaduna da suka ce daga Kano suke neman auren Fa’iza wa dansu Naziru, malami a inda Fa’izar take karatu. Sai mama ta kalli Baban Kaduna shima ya kalle ta aka rasa mai yin magana. 


Tun daga nan jikin dattijan ya fara sanyi. Da kyar Baban Kaduna ya ce, “Na yi mamaki da kuka zo neman aure ba tare da kun yi bincike a kan gidan su yarinyar ba. Ban da haka duk wanda ya san zuri’ar Abubakar Giwa, ya san basa auren bare. Ban fadi haka don yaron wajena ne mijin Fa’izah ba, sai don cewa ka’idar gidanmu kenan da muke bi tun iyaye da kakanni. Ina mai bai ma Naziru hakuri, ya yi hakuri, ya yi hakuri Fa’izah TA YI AURE!!!” 


Da wannan bakin labari Hajiyar Dr. N ta tare shi a dawowarsa daga wajen aiki. Labarin da ya yi masa bugun da wani labari bai taba yi masa ba. Ya dauki mukullin motarshi ya nufi kofa Hajiyarsa na kira, bai juyo ba yake fadin “Barni in je Hajiya, Giwan za ni in tambayi Fa’izah dalilin da yasa ni ban yaudareta ba ita ta yaudare ni...... ta san auren gida ake musu amma ta yi min haka.... me na yiwa Fa’izah da za ta zabi ta yi min wannan yankan kaunar ta yi dai-dai da zuciya da farin ciki na?” 


Gudun da yake shararawa a kan titin da zai kai shi garin Giwa ya fi kama da na ‘yan sumogal. Zagin duniya ya sha shi daga motocin gaban shi da bayanshi. A dai-dai kwanar da zai karya ya shiga Giwa suka yi arangama da motar shanu ta bi ta kan motarsa ta murkusheta irin murjewar da 

sai wani babban ikon Allah za a fidda mai rai a cikinta. 


a i ok 


GIWA 


Ban motsa daga inda nake ba, tun daga lokacin da na fadi na suma. Karar da na yi ya janyo hankalin Hajjah da sauran mazan dake zarya a tsakar gidan. A guje Hajjah ta shigo har tana tuntube da kofar daki tare da su Baba Barau da suka shigo a lokacin da ‘yan kanzaginta su Inna Kubra. 


Hajjah ta tsugunna da hannuwanta biyu ta girgiza ni tana kirana “Fa’izah...... Fa’izah!!” Baban Giwa (Barau) shi ya fita ya zo da ruwa a kofi ya shiga yayyafa min amma ban motsa ba, ga idanuna a bude ina kallon su tarrr! 


Hajjah ta shafi fuskata zuwa idanuna shima ban motsa ba, ta kama hannuna ta ji shi sanyi kalau, jijiyar ta saki. Ta dubi fuskata babu alamun rai a tare dani sai ta rushe da kuka. 


Inna Kubra ta soma karanto addu’a tana tofa min a fuska. Ya yin da Baban Giwa ke tofawa cikin kofi, ya kammala ya shara mini duka a kaina, sai na kwanto sharaf jikin Hajjah kamar matacciya. Ko dan yatsana na kasa dagawa, babu wata gaba dake motsi a jikina. Wannan ya tabbatar musu da cewa dogon suma na yi, irin wanda shock ke sanyawa, mai wuyar farfadowa. 


Hajjah ta rungume ni tana kuka ta ce, “Na shiga 

uku ni Hadiza, me ya yi zafi Fa’izah? Muddin kika mike Hafizi na isowa za a warware auren nan, ba zai yiwu garin neman gira a rasa ido ba. Wayyo ni Hadiza, wallahi na manta shaf da kiyayyar Fa’izah da Fa’izu da ba a yi auren nan ba”. 


Baban Giwa ya zauna gefe ya zuba min ido duk sunyi tsuru-tsuru, ya ce, “Uhm! Ai na fada Hajjah babu wanda ya saurare ni, yanzu in ta mace ai shi kenan hankalinki ya kwanta. Tun lokacin na Aliyu na gaya miki kada a kara aurarrakin nan kin ki ji. Yanzu ai an dau darasi ko?” 


Baban ABU wato mahaifina ya daga labule ya shigo yana cewa, ““Zancen banza kake Barau, ba suma ba, ko mutuwa Fa’izah ta yi babu mai karya dokar Abubakar Giwa ko bayan ran Hajjah, mu zamu tsaya a kan wannan principle har karshen rayuwarmu. Tashi ka fita ka baiwa mutane wuri sakarai matsoraci girman wofi tun ranka bai baci ba wallahi’. 


Baba Barau ya kwantar da murya ya ce, “Nima ban ki hakan ba, amma a dinga duba soyayya tsakanin yaran nan kafin a kara kulla kowanne aure tsakaninsu. Fa’izah da Fa’izu basa ga amciji tun tali-tali har zuwa girmansu. Baban ABU rai! Yana gaba da komai, sai da shi ake komai”. Fa’izun ne ya bankado labulen dakin ya shigo a sukwane kamar an jefo shi tare da Yaya Aliyu, don tun fitowarsu mota Khalid yaron Baban Giwa ya ce dasu wai Fa’izah ta yi kara ta mutu! 


Bai iya ya ce komai ba duk da ya ji kadan daga abin da suke tattaunawa, illa bin Fa’izar da ke 

yashe a kasa mushe ko mai rai da kallo. Manyan fararen idanuwanshi gaba daya sun fito waje sun yi jawur, har wani brown-brown suka koma. Jikinsa sai mazari yake bakinshi na motsi, amma ya kasa magana. 


Aliyu ya ce “Shin Baba me kuke yi haka dukkanku tun dazu da aka rasa mai kaita asibiti? Fa’izah ba mutuwa ta yi ba!” 


Sai ya sunkuya ya ciccibe ta gaba daya, Fa’iz ya hade girar sama da na kasa ya ce, “Ko da ban karanta ba na san maganin wannan suman...” 


Da sauri Yaya Aliyu ya dire ni gefen gado ya yi baya, ya ce, “To likita mai mata Bismillah” 


Ya yi waje abinshi. A ranshi kam dariya ma abin ya ba shi yana ta yin ta ciki-ciki, wai matar dake tsakanin rai da ajali ake ma kishi? Bai san gara ta dauwama a suman ba da ta farfado ta ganshi. Ya karbi diyarshi da ke ta tsala ihu hannun Ummi a falo ya yi waje. 


A hankali su Baban ma suka shiga ficewa daya bayan daya ba tare da kowannensu ya sake tofawa ba. 


Hajjah ta share hawaye ta ce, “Yanzu Hafizi ya za ayi Fa’izan ta farfado?’ Fa’iz cikin jin haushinsu duka ya ce, “Ban sani ba Hajjah’”. Ita ma a fusace ta ce, “Amma ka hana a kaita asibitin?” 


Ya fiddo ido ya ce, “Hajjah bakya gani daukarta ya yi ne?” 


Hajja ta hasala ta ce, ““Zancen banza zancen wofi, yau ga sakaran kawai. Sannu mai mata, hala gawa za ka aura? To in gaya maka gaskiya auren nan kunce shi za ayi ba zai zama sanadiyyar rasa 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...