YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 11 BY HARUNA USMANWww.bankinhausanovels.com.ng 
A JIYA MUN TSAYA 

Komawar Sarki fada sai ya sa Sarkin dogarai a je - gidan hutawarsa a dauki gawar Sarauniya a tsaftace wurin. Ya ce, “Ina so a kai gangar jikin can Jakara a jefa cikin ramin da ake kai wadanda aka kashe, ungulai su ci. Kuma ina so a feke itace a soke kantaa kafa a Kofar fada don kowa ya gani.” Aka kafe kan Sarauniya a kofar fada, mutane suka yi ta zuwa birni da Kauye suna ta kallo da maganganu barkatai. Wasu na cewa Sarki ya yi zalunci, wasu kuma na ganin lallai akwai dalili. Bayan kwana biyu Sarki ya sa aka yi yekuwa birni da Kauye. Ya aike wa abokanansa manyan Sarakuna cewa su yi hakuri saboda irin wannan gayyata ta gaggawa da ya aike musu, wato gayyatar daurin auren 'yarsa ranar Jumaia. Aka Kawata gari da kayan kwalliya, manyan baki kuwa sai barkowa suke ta yi daga ko ina. Gari dai ya cika maKkil, babu masaka-tsinke. Ranar Juma'‘a kowa

ZAMU TASHI 

ya hallara aka daura auren Yahaya dan Hamidu da Lubna ‘yar Sarki Salahuddin. Bayan addu'o'i, sai Sarki ya mike ya yi godiya tare da bayanin kashe matarsa da kuma dalilin yin haka din, wato tsananin makirci da rashin amanarta. Ya ba da doka cewa duk wanda matarsa ta yi masa irin haka a fadin kasarsa gaba daya, to Sarki zai aike da ita lahira matuKar dai akwai hujja tabbatacciya ko kuma ingantattunshaidu. Daga nan kuma ya ba da sanarwar mayar da Sarkin yakinsa kan mukaminsa. Ya mayar da matansa uku da ya kora sannan kuma ya nada ango Yahaya a matsayin sabon Magajin gari, tare da mallaka masa gidan hutawa na Sarki wanda yanzu aka yi matukar Kawata shi fiye ma da gidan Sarki, don tarewar amarya. Sarki ya kammala jawabinsa da cewa, “Daga yau kuma na bude biki na kwana bakwai.” Shagali ya kankama babu kama hannun yaro, mawaka da maroka kowa sai washi ya ke yi.

Abinci da abin sha kuwa kamar ba sarrafa su ake yi ba. In aka ce za a ba da labarin duk abubuwan da suka faru a wurin sai kifin rijiya ya Karyata mutum a banza. A kwana a tashi ba wuya, kwanakin biki bakwai suka cika, wato za a kai amarya gidan mijinta don a sallami kowa ya kama gabansa. Aka dora ta a kan wani irin doki na alfarma, in ka ga irin yadda dokin nan ke sassarfa cikin takama, dole ne ko kai waye abin ya burge ka. Masu kadekade da raye-raye suna yi. Mata masu rakiyar amarya kuwa.a Kalla ba akasara ba a sami dari biyar. Abin bakin ciki, ana gab da isa gidan ango, wato Magajin gari Yahaya, sai kawai Sarkin aljanu Sham'una ya sure ta ya yi sama da ita. Mutane babu yadda za su yi su cece ta, sai dai daga kai sama kawai. Ita kuwa amarya sai ihu take ta kwallawa, tana kiran sunan mijinta Yahaya, har ta bace aka daina ganin ta.
Bakin ciki ba ya misaltuwa a wurin mahaifinta da mijinta a lokacin da kowannen su ya sami labarin abin da ya faru. Sarki fadowa ya yi daga karagar mulki, shi kuwa Yahaya nan take ya fadi sumamme. Aka yayyafawa ango ruwa ya farfado, ya nufi fada yana kuka, Sarki na ganin sa sai shi ma ya fashe da kuka, Sauran mutanen gari kuwa duk kowa sai ya yi zugun-zugun cikin Bacinraida jimami. Bayan 'yan kwanaki da faruwar wannan lamari, sai Sarki ya tara ‘yan majalisarsa ya ce musu, “Ina mafita?”
Malam Ahmadu, wato malamin Magajin gari Yahaya ya ce, “Allah Ya ba Sarki nasara, a kwanakin baya na yi wani baKon malami daga can Kasar Arewa, muna hira da shi ya ba ni labarin Sarkinsu, cewa wani aljani ya dauke masa tasa ‘yar. Sun sami labarin cewa akwai wani gida ne a kan daya daga cikin tsibiran nan na cikin tekun da ke bayan duniya, to a nan ya ke ajiye 'yan matan. An yi bayanin cewa ko a mafarki ba a taba samun dan Adam din da ya taba zuwa wurin ba. Na kuma ji labarin cewa wancan Sarki ya koma gida ya dakatar da fita neman ‘yar tasa. Sauran labarin ne ban sani ba.” Da Yahaya ya ji wannan bayani sai ya mike a gaban Sarki ya ce, “Yau rana ce ta farin ciki a wurina, tun da ya ke har za a iya samun wanda ya san inda matata ta ke. Ni dai ban ga ta zama ba, ina roKon Sarki ya yarda, gobe zan nufi Arewa don neman labarin wannan aljani. Kuma ba aljani daya ba, ni ina jin ko sun kai dubbai daruruwa ne, to zan tunkare su, kuma da Karfin Allah sai na gano matata ko kuma in mutu a kan haka.”
Sarki ya ce, “Ina yi maka addu'a da fatan samun nasara. Amma lallai in za ka tafi sai ka sami jarumai, ina ganin kamar guda dari su yi maka rakiya.” Sarki ya juya ya dubi Ma'aji ya ce masa, “Sai a shirya musu dinare dubu ashirin don yin guzuri.” Gari na wayewa Yahaya ya shiga gidan Sarki ya yi www.bankinhausanovels.com.ng sallama da shi da kuma mahaifiyar matarsa. Suka yi masa addu'o'in samun nasara da fatan alheri, suka rabu kowa na kuka. Shi da askarawansa suka hau suka rankaya.
Wannan shi ne labarin Yahaya dan Hamidu.
Bashari dan salihu kuwa wato saurayinnan makwabci kuma abokin da ya fito neman ilmi tare da yayan dan hamidu baiyi tafiyar data wuce ta kwanaki goma sha uku ba saiya tsinci kansa yana kutsawa cikin wani daji mai yawan duhu da itatuwa
Wahala da gajiya suka sashi fara tunanin juyawa da komawa gida amman kuma sai ya tuna da cewa aikata hakan zai iyq zame masa babban abin kunya nan gaba haka nan dai yayi haquri yayi ta kunna kai ciki har saida jikinsa yakai yanayin da bazai iya kara motsawa koda taku daya daga inda yake ba lallai yana buqatar hutu
Sbd haka saiya sami tsakanin wasu duwatsu biyu da sukayi makaifa da juna ya shige yayi rigingine
Bai dade da fara hutawa ba saiya hango wasu mutane suna tahowa wadanda kuma da ganinsu kasan cewa kowannensu akwai alamar kwarjini irinta sarauta tattare dashi sunsa shugabansu a tsakiya www.bankinhausanovels.com.ng gaba suna biye.
Kasancewar Bashari bai san abin da ke tafe da su ba, sai ya sake boyewa a tsakanin duwatsun yadda ba za su iya ganin sa ba, amma kuma shi yana hangen su. Suna wuce daidai inda ya ke kadan, sai ya ga daya daga cikin mahayan ya lababa ya sa kokara ya buge kan shugaban nasu da ke gaba, ya fado daga kan doki. Suka taru suka yi ta bugun sa har sai da ya daina motsi, ga alama dai ya mutu. Abin da ma ya sake dakatar da su shi ne, suna cikin wannan aiki sai kawai ga wani katon zaki ya fito daga cikin daji yana gunji, ya nufo su. Suka taru suka fafata har sai da suka kashe shi, kuma ga dukkan alamu sun yi matukar jin dadin fitowar zakin a daidai wannan lokaci. Dalili kuwa shi ne irin yadda suka tube wancan shugaba na su da suka kashe daga cikin tufafinsa, suka yayyaga sannan suka sa su face-face cikin jini. Suka ciccibi mataccen zakin suka daura a kan dokin marigayin. }
Suka dawo kan gawar mamacin suka dauke ta suka sa a cikin wani buhu na algarara suka daure bakin, suka yi kama-kama, suka jefa cikin wani rami mai . zurfi, sannan suka juya suka koma cikin daji. Duk fa abin da suke yi a kan idanun Bashari ne. Bayan tafiyar su sai ya fito daga inda ya ke boye a tsorace jikinsa na rawa, yana ta mamakin yadda hakan ta kasance. Ya fara tunanin ko zai bi mutanen nan ne don ganin yadda za su yi da rigar dan'uwansu, kuma ina za su je? Sai kuma ya tuna ai su akan dawaki suke, shi kuma yana kasa kuma in har suka gane yana bin su, to babu ko shakka halaka shi za su yi. Sai ya sauya shawara. Ya Kudiri aniyar cewa duk yadda za a yi, ya kamata ya shiga cikin ramin ya gwada ceto mutumin nan, mai yiwuwa yana da rai. In kuma ba shi da rai, to shi dai Bashari dan Salihu ya yi iyakacin abin da zai iya. Ya tube rigar jikinsa ya nufi rami da niyyar shiga, amma da ya leka ya hango zurmukeken zurfi mai duhu da ke wurin ai sai tsigar jikinsa ta tashi. Ya tabbatar da cewa ba zai iya ba. Ya zauna yana ta tunanin abubuwan da suka faru a cikin abin da bai kai sa'a daya ba da ta wuce, zuciyarsa ta rika fada masa cewa, “Babu yadda za a yi a jefa mutum cikin wannan rami sannan a ce zai rayu.” Sai ya yanke shawarar rabuwa da al'amarin wannan mutum wadda tasa ta Kare. Bai bar wurin ba sai ya ji nishi kamar na dan Adam, ya dudduba amma bai ga kowa ba. Can sai sautin nishin ya rika Karuwa, shi kuma sai ya saurara da kyau, ya kuma fahimci cewa lallai mutumin nan na
cikin rami na da sauran numfashi, wato bai mutu ba. A zuciyarsa sai ya ji cewa ko zai halaka ne wurin Kokarin ceto wannan bawan Allah, to shi kuwa zai gwada. Ya tashi ya dan kewaya cikin dajin, ya sami itacen kargo ya sara ya yi ta bare bayan yana tarawa har sai da ya sami wanda ya tukka igiya mai tsawo da kaurin gaske. Akwai wata itaciyar kirga kusa da ramin, a jikinta ya daure igiyar kamar dabaibayi. Ya zura cikin rami ya kama ya yi ta shiga har lokacin da ya ji cewa igiyar tana gab da Karewa, kuma ya sakankance cewa lallai akwai sauran tafiya. Wato dole ya koma ke nan. Ya laluba Kafarsa ta dama Kasa, sai ya ji ya tokari wani abu. Ashe an yi sa'a a lokacin da aka jefa buhun ya sarke a jikin irin itacen nan da kan fito a gefen rami ta ciki. Ai sai murna ta kama Bashari, ya lallaba da sauran igiyar da ta rage ya daure buhun tamau sannan ya saba a wuyansa ya rika kamo igiyar don kokarin fita. Hannayensa duk sun gaji, babu abin da suke fitarwa sai jini saboda sabulewar da suke yi, a dalilin nauyin shi kansa da kuma na mutumin da ke cikin buhu. Ashe matsala na nan waje tana jiran sa. Ya rage kadan ya fito, sai kawai ya ji wata murya daga bakin ramin tana cewa, “Yau kwananku sun Kare kai da shi. Ashe gara da aka ce in dawo, to yau a lahira za ku kwana.” Wannan mutumi daya ne daga cikin wadanda suka aikata aika-aikar nan ta dazu, kuma an umurce shi ne da dawowa don tabbatar da cewa ba su bar baya da Kura ba, amma da ya iso bakin ramin sai ya ga igiya a daure. Kuma ba tare da bata lokaci ba ya fahimci abin da ke faruwa, wato wanda suka halaka wani ke son ya ceta. Hasali ma babu mamaki ya gan su lokacin da suke aikatawar ke nan. Gaban Bashari ya rika duka uku-uku. Nan da nan bakinsa na rawa ya ce, “Ka yi wa Allah ka yi hakuri ka Kyale mu.” *
Mutumin ya ce, “In Kyale ku ka ce? Wato in rufa muku asiri mu kuma namu ya tonu ko? To ko da wasa haka ba za ta yiwu ba.” Da Bashari ya ji haka sai ya ce, “To yi yadda ka so, amma kada ka manta cewa rayuwarmu tana hannun Allah ne baa hannunka ba.”
Mutumin a fusace ya ce, “E lallai, wato kana bakin kabari amma kana fadar bakar magana ko?” Ya daidaici igiyar, ya daga takobi don sare ta a daidai lokacin da ya ke cewa Bashari, “Yi addu'arka ta Kar...”Www.bankinhausanovels.com.ng wata macijiya mesa da ke saman itacen ta duro masa a wuya. Da ma tuntuni take ganin kamar tsayuwar shi mahayin barazana ce a gare ta. Sai kuwa ga shi zatonta ya tabbata; don ta ga ya dago makami ya nuna inda take, alhali kuwa ba ta san cewa shi bai ma san tana wurin ba. Haka wannan Katuwar mesa ta murde mutumin suka fadi Kasa suna ta murkususu yana ihu. Shi kuma Bashari da ma hannayensa tuni sun gama yin tsami, yana gab da sakin igiyar ke nan ko kuma jin an sake ingiza su cikin ramin amma sai ya ji wancan mutumi na ihu. Haba ai sai ya ji wani sabon Karfi ya zo masa da kuma kwadayin ya fita ya ga abin da ke wakana. Saboda haka sai ya Kara yunkurawa yana fitowa har ya samu ya ingizo buhun da ke wuyansa bakin rami shi kuma ya sa hannayensa ya yiwo waje. Yana fitowa ya dan taka daya biyu sai ya zube saboda matsananciyar gajiya, amma duk da haka yana iya kallon abin da ke faruwa. Wancan mutumin da ke Kokarin kwatar kansa da kuma macijiyar da ke Kokarin halaka shi suka shiga wani irin artabu, kowa na ta kansa ba su san halin da suke ciki ba, har suka mirgina suka afka cikin mugun ramin nan. Bashari ya shiga tunani a zuciyarsa, “Da ma ana cewa in za ka gina ramin mugunta, to ka gina shi gajere don watakila kai za ka fada. To wannan ya gina wanda ya fi shi zurfi. Allah mun gode maKa da Ka kubutar da mu.” Bayan kuzarinsa ya dan dawo jikinsa, sai ya yunkura ya kwance bakin buhun. Ya ga ashe wani dattijo ne fari mai farin gemu da saje, duk ya daddauje ko ina jikinsa raunuka ne, ga su nan ba sa kirguwa, sai nunfarfashi ya ke ta yi sama-sama.
Bashari ya debo ruwa ya yi addu'a ciki, ya sa wa mutumin a baki. Aka yi sa‘a kuwa ya dan tsotsa, ya sa ruwan ya wanke masa jikinsa. Ya duba jikin dokin mutumin can da ya fada rami sai ya sami madara a cikin wata gora, ga kuma nama soyayye. Aka yi sa'a mara lafiyar ya dan kurbi madarar. Ya ciccibe shi ya dora kan doki. Ya sami igiya ya daure shi sakwa-sakwa yadda ba zai takura ba. Ya duba wurin don tabbatar da cewa bai bar wata alama da za ta nuna cewa wani abu ya faru ba, ko da mutanen nan sun yi tunanin sake biyo sawu. Ya shiga gaba ya kama linzamin doki yana ta tafiya don neman wani Kauye nan kusa wanda zai samu ya Yi jinyar sa yadda ya kamata. Wannan dattijo da aka lakadawa duka tare da neman halakawa ashe wani Kasaitaccen Sarki ne mai girman mulki, mai farin jini a wurin talakawansa. GaShi yana da dumbin sani ta yadda bayan kasancewar ‘sa limamin Juma’a na garinsa kuma shi ne malamin malamai. Da yammaci sai ka ga an cika makila kofar gidansa kamar ana fadanci, amma ba fadancin ake yi ba,a'a, manyan malamai ne ke Kara ilmi. Sarki Shahzad kuma,dai mutum ne wanda bai yarda da zalunci ba a,Kasarsa, Babu yadda za ka ga wata ;'yar--banza . karuwa: ko: ,kuma ;.dan, daudu ballanta wani shege barawo,; www.bankinhausanovels.com.ng Kasan mutane babu miai iya musu sai Allah. Ashe duk kyan halin wannan Sarki akwai wasu ‘yan tsiraru daga. cikin, mutanen; fada:wadanda ba sa jin dadin  yadda mulki ke-gudana. Babba daga,cikinsu shi, ne kanin Sarkin, wanda maganar.da ake ciki a lokacin ita ce Sarki ya fara shawara a.cikin zuciyarsa cewa ya kamata ya sauka daga.karagar mulki ya nada Kanin don shi ya fuskanci harkar karantarwarsa kadai, Shi,wannan kani na Sarki mai suna Rufaidu babu inda suka daidaita da Sarki ta bangaren hali, don, shi mutum ne,wanda yayi amanna da a Kyale kowa ya  Sakata ya wala, kowa ya yi nishadinsa da walwalarsa yadda ya ga dama matukar dai bai taba mulki ba, Mai bukatar karatu ya yi mara bukata ya bari. Karuwai da yan daudu in suna bubatar zama www.bankinhausanovels.com.ng a Kasar a Kyale su, in ba su bukata shi ke nan, amma fa a raayinsa. Ko da yake koyaushe yakan yi KoKarin Boye wa Sarki wannan ra’‘ayi tare da nuna masa cewa yana goyon bayansa dari bisa dari. Ya ci da zuci game da sarautar garin, musamman kasancewar Sarki bai taba haihuwa ba a rayuwarsa. Ya sha Kullawa Sarki tuggu da makirci iri dabandaban amma yana tsallakewa. Dole wani lokaci ya kan hakura da Kulla makircin in ya lura da irin yadda jama ar Kasar ke matuKar son Sarkinsu. To shi wannan adalin Sarki mutum ne da ya jarabtu da son fita farauta, kuma can cikin Kungurmin daji. In aka je sai a kafa tantuna a yi sansani, tantinsa a tsakiya, na sauran askarawa kewaye. al'adarsa kuma in za a shiga cikin daji, to yakan ce kowa ya kama gabansa ne ya je tasa farautar, duk abin da mutum ya kamo, to kansa ya kamawa. Sarkin kuma in zai shiga tasa farautar, to ba ya son kowa ya bi shi, sai dai wani lokaci wannan Kani nasa, don ya dauke shi ne kamar dan cikin sa. Karewa ma shi ya raine shi, ya ba shi ilmi da duk wani abu da da kan bukata daga majibintansa.
A ranar da lamarin ya faru an fito wata gagarumar
farauta ce ta kusa da gida, don Sarki ya ce ya tuna wani wuri da zakoki suke a cikin dajin, shi ne ya ke
son ya gwada ko zai yi sa'a ya samo ‘ya yansu don kiwatawa. Ya cewa wannan Kani nasa ya samo jarumai shida duk da shi na bakwai su tafi, su kuma samo buhu wanda in an sami ‘ya'yan zakin za a zubo a ciki. Jin haka sai murna ta kama Kanin Sarki, ya lissafta tare da kintata cewa yanzu dama ta zo wadda bukatarsa za ta biya cikin ruwan sanyi. Saboda haka sai ya je ya zabo irin mutanensa ya sanar da su abin da Sarki ya ce, sannan ya sanar da su shi kuma irin shirin dayayi.
Yace, “Kun dai riga kun san cewa irin wannan rana muke jira, to yau ga ta ta zo da kanta. Kun ga sarauta ta zama tawa ke nan, mu sheke ayarmu mu ci karenmu babu babbaka.” Ya shiga nuna su daya bayan daya yana cewa, “In mun yi nasara, kai zan nada ka Waziri babba, kai kuma Waziri karami. Kai Magajin gari zan yi maka, kai kuma Madaki, kai kuma kujerar Maji dadi na tanadar maka, kai kuma ta Sarkin fada.” Jarumai cikin murna suka ce, “Mun ji mun dauka.” Shi ne Bashari ya gan su suna zartar da wancan mugun nufi nasu. Bayan sun ga sun sami nasarar jefa shi cikin wannan mugun ramin ne, sai suka nufi sansani cike  da murna, amma da suka kusa sosai sai suka Bbarke da kuka, suna ihu. Da sauran askarawa suka gan su cikin irin wannan hali, sai suka zo suna tambayar su abin da ya faru da kuma yadda aka yi ba su ga Sarki ba. Shi kuwa gogan naka Rufaidu Kanin Sarki, sai kukan kawai ya ke ta zabgawa, ya kasa yin magana ma saboda nuna irin baKin cikin da ya ke ciki, yana ihu yana yayyaga rigar jikinsa tare da marin kansa. Sai daya daga cikin su ne ya iya ba da labarin cewa wai Sarki ya ce su Kyale shi zai kutsa cikin daji, shi ne aka sami wani Zaki ya fi Karfinsa ya halaka shi ya cinye shi bai bar komai ba sai kai da Kafafuwa kawai. Saboda haka suka haka rami suka bizne shi. Amma Allah Ya ba su ikon kashe zakin. Da mutane suka ji wannan mugun labari sai kowa ya barke da kuka, wani ba ya jin na wani. Kanin Sarki kuwa sai birgima ya ke ta yi a Kasa, ana rirriKe shi ana ba shi magana. Wasu kuma suna tausaya masa saboda rashin yayansa mai kama da mahaifi da ya yi.
Nan take masu busa Kaho suka yi ta busawa, wadanda suke cikin daji suka yi ta fitowa suna dawowa sansani don sun san babu lafiya. Bayan an kammala taruwa, sai aka dunguma zuwa gari kowa na hawaye. Kanin Sarki kuwa duk ya Kuje fuskarsa da faratansa wai shi bakin ciki. Lokacin da labari ya kai gari ai abin babu kyau, kuka yaro da babba, kuma ba mace ba namiji. Da ganin mutanen wannan gari lallai ka san suna cikin wani lamari mara dadi. Shi kuwa Kanin Sarki sai aka sa mutane kusa da shi don su lura da shi, wai kada a Kyale shi shi kada ya kashe kansa.
To yadda al'adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al'amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne 'yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda,
HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...