YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN


Www.bankinhausanovels.com.ng 


A JIYA MUN TSAYA 

Sarki ya fuskanci malam ya ce, “Malam Ahmadu ka ga wannan lamari mai bakanta rai dai? Ni kuwa in har Www.bankinhausanovels.com.ng 

wannan magana ta tabbata gaskiya, to zan zamo wanda ya fi kowa mamakin mata, don irin yadda na amincewa wannan mata, na sakar mata komai, na kori sauran matana saboda son da nake yi mata. Kuma Allah gafarta malam, saboda amincewar da na yi mata, ta sa na wulakanta 'yata har na sauya mata gida. Don ma a wancan lokacin na yi dacen daukar shawarar wasu mutanen kirki cewa kada in sa a sare wa ‘yar tawa kai. Malam in har wannan magana ta tabbata, to daga yanzu matan Kasata kaf za su riKa wahala kamar yadda mazaje suke yi, har yaki za su rika zuwa, kuma za mu sa su a gaba sai an fara kashe su tukuna kafin maza su shiga, kai har da 'yata duk za a hada, don ba zan kara saurarawa wata ‘ya mace ba.” Sai malamin ya ce, “Allah Ya huci zuciyarka, ai laifin wani ba ya shafar wani, don duk 'yan Adam ba su taru sun zama daya ba. Allah cikin hikimarSa Ya yi kowa daban-daban, kowa da irin halinsa da kuma irin fahimtarsa, don kuwa akwai matan da in ka gansu har zuciyarsu sai ka rantse cewa waliyai ne, kuma hakan suke. Saboda haka ina rokon Sarki ya huce kuma ya bi komai cikin natsuwa.” Sarki ya ce, “Haka ne malam.” Shigar Sarki cikin gida ke da wuya, sai ya sanar da 

ZAMU TASHI 

Sarauniya cewa ya sa an kama Yahaya har ya daure shi na tsawon kwanaki biyar yana jiran a yanke masa hukunci, amma da ya ke jama’a ba su san laifin da ya yi ba, sai suka yi ta ba da hakuri, ni kuma don kada a ga kamar kan zalunci ne na daure shi, sai na nuna musu cewa ke ce ya yi wa rashin biyayya. Amma da roKo ya yi yawa a gaban mutane da aka zo da shi, sai na yi masa gargadi mai Karfi cewa ke uwargijiyarsa ce kuma daga yanzu duk abin da ki ka umurce shi, to lallai ya aikata. Kuma kada ya sake yin kuskure irin wanda ya yi da. Kuma don in nuna wa jama'a cewa na huce da kuma irin adalcina, sai na nada shi matsayin mai kula da gidan hutawana, kin san tun da yaron nan Sallau mai kula da wurin ya koma Kauyensu don lura da tsohuwarsa ban sake daukar wani a wurin na dindindin ba. Sai dai dogarai su je su share su rufe kawai. Sannan kuma sai na ga gaskiyar masu ba ni shawara ne, bai kamata a kashe yaro saurayi kuma kyakkyawa kamar Yahaya ba. Gara dai a tsawatar masa.” Murna ta lullube Sarauniya a Boye don jin cewa Sarki ya umurci Yahaya da yi mata biyayya a game da duk abin data umurce shi. Nan take kuma ta ji wani ‘shaufi mai tsananin gaske na kadaituwa da Yahaya in din ya zo mata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kuwa Yahaya sai ya mayar da hankalinsa wurin ci gaba da kulawa da gidan hutawar Sarki. A kullum in ba aiki ya ke yi ba, to yana tare da Sarkin lambu ko kuma yana makaranta wurin malaminsa don kuwa akwai mai tsaro a gidan hutawar kuma a dabi'a Sarki ba ya zuwa sai ya aiko cewa yana nan tafe. Wadancan abubuwa da suka yi ta faruwa wadanda kuma suka sa tsoro a cikin zuciyar Yahaya da kuma tunanin cewa yanzu ba shi ne ke kai kayan lambu gidan ‘yar Sarki ba, sai suka sa aka dauki kwanaki Yahaya bai je wurinta ba. Ran nan dai ya kasa hakuri yace a cikin ransa, “Bari dai in je in gai da Gimbiya.” Ya je ya same ta cike da bakin ciki kuma har ta fara fita hayyacinta. Yahaya ya yi maganar duniyar nan amma Gimbiya ta ki amsawa, can sai ga hawaye shar-shar suna gangarowa daga cikin idanunta. Ta bude bakinta tana magana, “Babu shakka ku maza kuna da wuyar rike al'amarin soyayya, bayan mace ta amince tare da sallamawa ta ba ku amana, amma ga shi ko ina ba a kai ba har ka soma biri-biri. To ina
kuma ga ka aure ni na koma Karkashin ikonka? Saboda haka ina roKon ka ya kai masoyina, don Allah kada ka ci amanata.” Yahaya ya duKar da kai, ya ce, “Ni dai hakuri kawai
zan ba ki saboda rashin zuwana tsawon kwanaki masu yawa haka.” Gimbiya ta ce, “Yo mene ne dalilin rashin zuwan naka har kwana goma sha daya?” Yahaya ya amsa mata da cewa, “Masoyinki yana can kwana biyar a gidan yari cikin tsutsotsi da sauro da Kwari da sauran wahalhalu, amma fa ki sani cewa wadannan ba su suka fi damuna ba fiye da Kaunar ki da kuma tunanin ki. Babbar sa'ar da na yi kasancewar zobenki yana hannuna, da na kalle shi sai in sami natsuwa har in sami damar yin barci. Kuma lokacin da na fito, sai tsoro ya lulluBe ni da kuma kasancewar duk hankalina ba ya jikina, kuma in na zo a wancan lokaci kika gan ni, to hankalinki na iya tashi. Shi ne na je na sarara tare da fuskantar sabon aikina, a haka har hankalina ya dawo jikina. Wannan shi ne dalilin rashin gani na tsawon wadancan kwanaki. Amma kuma yanzu ina fatan komai ya wuce don ga ni a wurinki ya ke Sarauniyar raina.” Tausayin sa ya kama Gimbiya, ta ce, “Ya kai inuwar raina, kai kuwa mene ne dalilin da ya sa aka kai ka wancan mugun gida>?” Yahaya ya ce, “In kin tuna kwanaki kin yi mini gargadi a kan cewa in kula da macijiya kada ta sare ni ko? To zancenki ya tabbata gaskiya don kuwa ta kawo mini sarar, amma cikin ikon Allah ba ta yi nasara ba.” Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da Sarauniya ya labarta mata, sannan ya ce, “Sarki ya yarda da zancen matarsa, ya sa aka kama ni aka kai ni gidan yari tare da umurnin cewa a dandake ni bayan kwana bakwai.
Allah Ya taimake ni Sarkin lambu ya je ya fanshe ni, amma ba don haka ba, ai da tuni na gama yawo.”
Wani gaurayen tausayi da kuma murna ya kama Gimbiya, sai ta ce, “Ai dama na gaya maka. Ita wannan mata gara saran gamsheka da saranta. Ni dai babu abin da zan ce sai dai in sake ba ka hakuri, kuma in yaba maka don ka isa da, don da a ce kai mutumin banza ne irin ta, to lallai da ka biya mata buKatarta kun halaka tare.” Suka dai ci gaba da hirarsu irin ta masoya har zuwa lokacin komawar Yahaya gida ta raka shi. Aka dauki lokaci kamar baa taba yin wata magana irin wadda ta shafi Yahaya da Sarauniya ba. Ran nan sai Sarki ya shirya tafiya zagaye na kwana bakwai, amma ya ce ba ya son tafiya da mutane da Www.bankinhausanovels.com.ng
yawa don yana son wannan ta kasance ziyarar bazata ce a wurin hakiman da zai ziyarta din. Saboda haka sai ya debi mutane goma kacal, ya bar Waziri tsaron gari. Aka yi masa rakiya kamar yadda aka saba, shi kuma ya ci gaba. Ya iso yankin wani Hakimi, sai ya sanar da shi cewa yana son zai yi 'yan kwanaki a nan don hutawa, amma ba ya son kowa ya sani. Aka kai jama'arsa masaukai, ya ce su je su huta har sai lokacin da ya neme su.
Ba tare da sanin kowa ba, ya debi amintattu guda biyu daga cikin su, tare da Sarki suka sauya kamanni kamar masu fatauci suka juya suka koma cikin gari. Akwai wani gida wanda ba shi da nisa da gidan hutawar Sarki wanda kuma mallakinsa ne, a nan ya sauka. Ya umurci wadannan amintattu nasa cewa su je kusa da fada su yi ta karakainarsu cikin sirri, su lura da kyau, matuKar Sarauniya ta fito, komai: dare komai rana, duk inda ta sa Kafa ko kuma ta je, to su rugo su sanar da shi. Suka ce, “An gama.” Washegari tun safe har dare babu abin da ya faru.
A rana ta uku da tafiyar Sarki, can bayan dagawar hantsi, sai ga Sarauniya ta fito tare da wasu yardaddun bayinta su biyar, uku maza biyu mata. Ta nufi gidan hutawar Sarki, ta shige tare da kuyangi, ta bar mazan a Kofar gida KarKashin wata itaciya suna hutawa. Duk a idanun wadancan amintattun bayi na Sarki haka ta faru. Suka shiga wurin Sarki suka ce yanzu dai ba ta da nisa da shi don kuwa tana cikin gidan hutawarsa. Ya fito cikin sauyin kamanni da umurnin cewa kada kowa ya bi shi. Akwai wata ‘yar hanya da ta bi ta bayan gidan, ta nan Sarki ya kewaya ya kama katanga ya haye. Ya sadada ta baya har sai da ya gane dakin da Yahaya ya ke, kuma ga alama yana aiki ne a daya daga cikin dakunan Sarki, kuma ga alama ya riga ya gaida da Sarauniya kafin ya koma bakin aikinsa. Sarki ya hango Sarauniya can tsakar gida tare da kuyanginta tana ta shawagi cikin iko da isa. Sarki ya yi Kokari ya ja jikinsa zuwa Karkashin wasu furanni da ke bayan tagar dakin hutawarsa. Ya labe a daidai lokacin da ya ke jiyo maganar Sarauniya tana cewa kuyangin, “Sai ku koma can babban gida, ni ina tahowa can an jima, don ba na son yawan damun mutane ne nake tunanin in Zo nan kawai in dan huta kadan.” Ba su dade da tafiya ba, sai ta yi wuf ta shiga ainihin dakin da Sarki ke hutawa, ta kama tagar dakin ta bude, Sarki da ke labe bai ankara ba kawai sai ga shi yana kallon Sarauniya Karara, ya dukar da kansa, ita kuma ta kalli inda ya ke labe. Www.bankinhausanovels.com.ng
Amma ikon Allah hankalinta ashe ba a wurin ya ke ba. ‘Ta rafkawa Yahaya kira, shi kuma ya shigo yana zaton ko za ta ce an yi wani abin ne ba daidai ba.
Ta dube shi ta ce, “Ya kai kyakkyawan saurayi Yahaya, na lura dai kai yaro ne, ba ka san mai son ka ba, kuma ba don ina matukKar son ka ba, da tuni ka zama dan gida a lahira. To dai ka ga yanzu daga ni sai kai, kuma lallai ne yau ka biya mini buKatata, ko na samu Kwalamata ta koma, kuma kai ma in Kyale ka ka huta, ba zan sake damun ka ba. In kuma har ka amince cewa bayan wannan karon za ka ci gaba da biya mini buKatata a duk lokacin da na buKace ka, to lallai ka sani cewa babu wanda zai fi ka jin dadi a garin nan, don duk tsananin mulkin wannan tsohon idan na gifta masa kara, ba ya tsallakewa don tsananin so na da ya ke yi. Bai taba yi mini musu ba.
In kuma har kana tsoronsa ne, to ka sani cewa yana can ya tafi gewaya.” Sarki da ke labe da yaji irin butulcin matarsa, ransa ya yi matukar baci, hankalinsa ya tashi duniya ta yi masa baki Kirin. Ya tuna irin yadda ya sakar mata komai, iko da mulki duk a hannunta. Ya tuna yadda ta yi sanadi da makirci ya kori sauran matansa uku, ya Www.bankinhausanovels.com.ng tuna yadda ta sa ya wulakanta Sarkin yakinsa wanda ya ke matukar ji da shi ba tare da hakKinsa ba, da kuma yadda wannan makirar mata ta sa ya wulakanta ‘yarsa da sauran wasu abubuwa marasa kyau ga jama‘arsa. Ya ciji dan yatsarsa da Karfi har jini ya rika diga amma Zafin bai dame shi ba, don yana so sai ya ga kwal-uwar-daka. Sai Yahaya ya ce, “To amma ya kamata ki ji tsoron Allah, ki sani cewa abin da kike nema na da shi haramun ne, sannan kuma akwai wani hakki na aure a kanki, kin zama maci amana. Kuma in shi mai martaba ba ya kallon mu, to ai Allah ba Ya gyangyadi, Yana kallon abin da muke ciki. Don Allah ina rokon ki ki Kyale ni kuma ni a wurina zan dauka cewa wannan bai taba faruwa ba kuma ba zan fadawa kowa ba cewa kin zo nan.” Sarauniya Zizaratu tace, “To shin ko ka manta cewa Allah din da kake magana Mai gafara ne, kuma kullum neman gafararSa muke yi? Sannan kuma da kake maganar cin amanar mijina shin ka san ko kuyangi nawa shi Sarkin ya ke kebewa da su wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ko kuwa ni kadai ya tsayawa?”
Yahaya ya ce, “Watakila in ba ki manta ba kin ce Www.bankinhausanovels.com.ng kuyanginsa, kuma kin sani cewa halas ne su a wurinsa ya keBe da su ko?”
Sarauniya ta sake cewa, “Yaro yaro ne, shin ka manta da ni da shi ai duk abu daya ne, duk ba sha'awa ake yi wa ba? Kai dakata, kada ka tsaya ka nemi kawo mini wani Kabli da ba'‘adi, idan kana son ranka, to ka biya mini bukatata kawai ka huta. In ba haka ba kuwa, to lallai zan yi maka sharri fiye da wanda na yi wa Sarkin yaKi, na san wataKila ko ya taba ba ka labari ko Tana yin wannan magana sai ta yi wuf ta rufe dakin ' da suke ciki, ta riKe mabudin a hannunta. Kafin Kiftawa da bismillah sai ga ta tinbirbir huntu. Yahaya na ganin haka sai ya sa tafukan hannayensa biyu ya rufe idanunsa ya ce a zuciyarsa “Allah ka tsare ni daga sharrin wannan shaidaniya.” Sai ya ce mata, “Babu shakka ke mayaudariya ce. Kin cuci kanki kin cuci mijinki, kuma kin ci amana, kuma ga shi kin yi rashin sa'a bukatarki ba za ta taba biya ba a kaina, ba iri na ake tunkara da wannan sharri ba. Na yi rantsuwa da wanda raina ke hannunSa, da in biya miki bukatarki ta irin wannan hanya, gara in fada wuta ta cinye ni da raina. Allah dai wadaranki!” Duk maganar nan da ya ke yi idanunsa na rufe, ita kuwa tana tsaye tinbirbir, zuciyarta ta hasala saboda Www.bankinhausanovels.com.ng bakaken maganganun da yaro karami ke dankara mata, tana tunanin wai har zagin ta ya ke yi, abin da ko Sarkin garin bai isa ba. Sai ta fara zagin Yahaya zagi mai tsanani, ta matsa jikin ragaya ta dauko wata wuka da ke wurin ta nufo shi. Ganin haka Sarki da ke labe bai san lokacin da ya yi kundumbala ya kama taga ya duro cikin dakin a daidai lokacin da ta daga wukar za ta dabawa Yahaya wanda har yanzu idanunsa ke rufe bai san abin da ake ciki ba. Da gaggawa kafin ta san abin da ya duro cikin dakin Sarki ya ture ta ta fadi Kasa wuKar ta fadi gefe daya. Jin irin wannan motsi sai Yahaya ya bude idanunsa, suka yi ido hudu da Sarki, ai nan da nan sai jikinsa ya fara rawa yana cewa, “Na rantse da Allah yallabai ita ce ta ke so ta yaudare ni, wallahi tallahi ba ruwana ranka ya dade.” Sai Sarki ya ce, “Aminci a gare ka ya kai dan Hamidu, lallai kana daga cikin samari masu mutunci, gaisuwata ta girmamawaa gare ka ya kai dan halas.”
Da Sarauniya ta ji abin da Sarki ya ce da Yahaya sai ta fashe da kuka ta ce, “Wato ka yarda da maci amanarka? Lallai na san ba ka so na, saboda haka yau ba zan kwana a wannan gari ba.” Sarki ya juya gare ta cikin fushi ya ce, “Yi mini shiru, Www.bankinhausanovels.com.ng yau dai asirinki ya tonu algunguma, maci amana! Yau makircinki ya Kare, yaudararki ta fallasu. Na godewa Allah da ba ki kawo mini mugun da gidana ba. Muguwa, bakar shaidaniya. Allah dai wadaran irin ki.” Yana gama magana sai ya sa takobi ya dauke mata kai, nan ta yi ‘yan shure-shurenta ta mace babu mutunci babu lada. Ta yi shahadar bunsuru. Sarki ya juya ga Yahaya wanda a yanzu ya ke ta kaduwa da kyarma, ya matsa kusa da shi, ya dafa kafadarsa ya ce, “Ya kai dana Yahaya, babu shakka kana daga cikin mutane amintattu, duk yadda aka yi daga babban gida ka fito wato gidan tarbiyya. Daga yanzu ni na dauke ka dana. Mahaifinka ya haife ka ne kawai amma ni ina ji a raina yadda ya ke Kaunar ka ni ma haka nake Kaunar ka. Na gode yadda ka kare mutuncina, ba ka yarda ka biya wa wannan shaidaniya buKatarta ba, don duk mutumin da ya san matarka, to babu shakka ya gama da kai. Da a ce ta hadu da irin ‘yan banzan samarin nan ne, da tuni ya gama da ita, ya riga ganina sororo wai ina mulki, alhali ga wanda ya fi ni mulki can gefe guda. Yanzu ma Allah ne kadai Ya san wadanda ke ganina ahaka.” Ya ci gaba da yi wa Yahaya jawabi, “Tun lokacin Www.bankinhausanovels.com.ng haduwar mu ta farko da kai a lambu na amincewa raina cewa kana da natsuwa da hankali. Ni dai ina yi maka addu'a da fatan gamawa da rayuwarka ta duniya lafiya.” Yahaya ya yi godiya saboda girmama shi da Sarki yayi. Sarki ya ce masa, “Akwai sauran magana ya kai dana, ina son ka yi mini alKawarin amincewa da abin da nake so in fada maka.” Yahaya ya ce, “Allah Ya ba ka nasara, in abin da zan iya ne, to zan amince tare da alKawari. Amma in wanda ba zan iya ba ne, to yallabai don Allah sai ka yafe mini.” Sarki ya ce, “To ya kai Yahaya da ma ina da wata ‘ya guda daya wadda ta yi ilmi mai yawa kuma fannifanni, tana da hankali da natsuwa, kuma ga kamun kai. Allah kuma da ikonSa Ya yi mata kyau kamar ‘yar aljanu. Ko da yake 'yata ce amma na tabbata cikin abin da na fada maka babu Kari. Ya kai Yahaya ita ce nake so in hadaku aure, don ina son in hada zuriya da kai.” Wani irin gauraye na tsananin murna da mamaki suka kama Yahaya, sai ya riKa jin kamar ya mutu ne an yi masa albishir da Aljanna don tsananin dadi da farin ciki. Ya rasa yadda zai yi wa Sarki godiya, sai dai Www.bankinhausanovels.com.ng wani natsatstsen murmushi kawai da ya like a fuskarsa. Sarki ya ce masa, “Biyo ni.” Yahaya ya bi shi a baya, ba su zame ko ina ba sai gidan Gimbiya. Sarki ya cewa Yahaya, “Dakata mini a wannan zauren.” Ya shiga wurin ‘yarsa ya tarar suna ta hirarsu da dariya ita da masu mata hidima, sai ya yi gyaran murya. Suna ganin sa duk sai suka tashi suka yi gaisuwa. Ita kuwa Gimbiya mamaki ne ya lullube ta, kasancewar tun dawowarta wannan gida, Sarki bai taba zuwa ba, kuma ya hana ta je ta gaishe shi don matarsa ta rigaya ta shiga tsakanin su. Ta Kura masa ido Kurui kamar wanda ba ta sani ba, Kwalla na ta kwararowa daga idanunta tana gudana a kumatunta. Ganin ta a cikin wannan hali shi ma Sarki sai da Kwallar ta riKa gangarowa daya bayan daya, abin dai gwanin ban tausayi. Ya matsa kusa ya rungume ta yana ta tausarta da cewa ta yi hakuri da wasu abubuwa da ya yi mata a kan kuskure. Ya yi mata alKawarin hakan ba za ta sake faruwa ba, tare kuma da albishir cewa zai mayar da mahaifiyarta gidansa. Suka dan yi hirarsu irin ta mahaifi da'ya. Sarki ya dube ta ya ce, “Ya ke gudan jinin zuciyata, Www.bankinhausanovels.com.ng na zo ne don in sanar da ke cewa na yi miki miji kuma ranar Juma'a zan daura miki aure da shi.” Yarinya tana jin abin da mahaifinta ya ce sai gabanta ya, fadi, hankalinta ya tashi. Ta tuna soyayyarsu da Yahaya da kuma irin alkawarin da ta yi masa. Sai kawai ta sunkuyar da kai Kasa tana zubar da wata wala, Ganin haka sai Sarki ya ce mata, “Ya ke’ yata, kin san dai cewa ba. zan zabar miki abin da bai cancanta ba, ko ba: komai a kan  da abubuwan da suka gabata, ina ganin bai kamata in sake Kokarin sa ki ko kuma yi miki sanadin abin da zai cutar da ke ba. Ina so ki share mini hawayena ki, auri wannan saurayi da nake SO, hadaki dashi Yarinya ta sunkuyar da kai Kasa tana mai cewa, “Ya kai babana mai girma, ai ba sai ka roKe ni ba, don kuwa ni kayanka ce, kuma dole ne in bi abin da kake so. Amma a gaskiya abin ne ya yi mini nauyi, na ji kamar an dora wani gungumen dutse a zuciyata. Don a duniya in ba ka zauna da wanda kake so ba, to babu shakka akwai damuwa.
Akwai wani alKawari ne da na dauka wanda ya sa  nake jin dama a ce mutuwa na yi maimakon saba shi. Amma Baba na amince, don duk dan kirki dole ya share wa mahaifansa hawaye in yana neman Www.bankinhausanovels.com.ng albarka.” Da Sarki ya ga hankalin 'yarsa ya yi matukar tashi ‘Sai ya ce mata, © Ya ke ‘yata, na ga hankalinki ya tashi, kuma daga yau na kudiri aniyar cewa ba zan sake yin wani abu wanda zai tayar miki da hankali ko kuma jefa ki cikin damuwa ba, matukar dai ba kya so.” Sai ya mike ya fuskanci hanyar zaure ya yi kiran Yahaya yana mai nufin cewa ya shigo cikin gida, shi kuma Yahaya ya amsa ya shiga. Ita dai Gimbiya kanta na sunkuye kasa ko bukatar ganin kowane ne sai ya ce, “Ya kai dana Yahaya, ka yi hakuri kan alkawarin da na yi maka, don kuwa ‘yata ta ce ba ta son ka, amma kada ka damu, ni zan auro maka wata.” Jin mahaifinta ya ambaci sunan Yahaya, ai sai yarinya taji kamar wata aradu ce ta sauka, firgigi ta dago kanta suka yi ido hudu sai ta ga ashe Yahayanta ne. Sai ta bude baki cike da mamaki ta rika muttsuke idanunta, tana tunanin ko dukkan abubuwan da ke faruwa mafarki take yi ne ko kuwa ta tsunduma ne cikin kogin tunani? Da Sarki ya lura da abin da ke faruwa, sai wata irin murna ta sirri ta lullube zuciyarsa. Ya shuri takalmansa ya kama hanyar fita yana mai cewa, “To nina koma fada, bari in bar ku ku dan zanta ko?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan fitarsa sai suka yi ta mamakin irin wannan al'amari mai ban mamaki. Yahaya kuwa cewaya ke yi, “Tsarki ya tabbata ga wanda ke hada abin da Ya ke sO. Ta tambayi Yahaya labarin yadda abin ya wakana haka, shi kuma ya kwashe kaf ya fada mata har da yadda Sarki ya sare kan Sarauniya da takobi.
Komawar Sarki fada sai ya sa Sarkin dogarai a je - gidan hutawarsa a dauki gawar Sarauniya a tsaftace wurin. Ya ce, “Ina so a kai gangar jikin can Jakara a jefa cikin ramin da ake kai wadanda aka kashe, ungulai su ci. Kuma ina so a feke itace a soke kantaa kafa a Kofar fada don kowa ya gani.” Aka kafe kan Sarauniya a kofar fada, mutane suka yi ta zuwa birni da Kauye suna ta kallo da maganganu barkatai. Wasu na cewa Sarki ya yi zalunci, wasu kuma na ganin lallai akwai dalili. Bayan kwana biyu Sarki ya sa aka yi yekuwa birni da Kauye. Ya aike wa abokanansa manyan Sarakuna cewa su yi hakuri saboda irin wannan gayyata ta gaggawa da ya aike musu, wato gayyatar daurin auren 'yarsa ranar Jumaia. Aka Kawata gari da kayan kwalliya, manyan baki kuwa sai barkowa suke ta yi daga ko ina. Gari dai ya cika maKkil, babu masaka-tsinke. Ranar Juma'‘a kowa
HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...