YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng 
A JIYA MUN TSAYA 

Yahaya ya ce mata, “A nawa zan nome miki ciyawar?” Gimbiya ta ce, “A matsayin Gimbiya ‘yar Sarki.” Yahaya ya ce, “Albarka.” Gimbiya Lubna ta ce masa, “To don soyayya.” Sai Yahaya ya kalle ta don tabbatar da cewa ita ce da kanta ta fadi abin da kunnuwansa suka ji, kuma tabbatar da hakan ya sa kawai ya ji zuciyarsa da bakinsa a lokaci daya suna amsa mata cewa, “An sayar. Saina Zo.” Ya juya zai tafi sai ta ce, “Mu je in raka ka.” Sai yace mata, “Haba yaya ‘yar Sarki za ta raka bawa mai lambu?” Gimbiya ta amsa masa, “Ba 'yar Sarki ce ke yi maka rakiya ba, masoyiya ce take yi wa masoyinta rakiya. Kuma ba na fata mai magana ya sake irin maganganun da suka wuce a baya, don da ace a yau mahaifina ba ya wannan duniya, kuma a ba ni damar zabo mai maye gurbinsa, to babu shakka zan ce mai lambu, don irin tsananin dimauta da na yi a kan rashin tsoronsa game da gaskiya.” Sai Yahaya ya ce, “Da ace mai magana ta san yadda


ZAMU TASHI 

mai lambu ke ji a zuciyarsa game da kyakkyawa abin son kowa, to lallai da kin tausaya mini, ni ma duk maganganun da na yi dole tasa ni, don ba na son raini, sannan kuma da irin zancen nan da masu iya magana ke cewa, “Abin da ba ka samu, to hada shi da bana so.” Lallai ni ina tsoron kada mu zurfafa cikin kogin soyayya, a karya mini zuciya daga baya kuma masu mulki su ki amincewa da talaka mai lambu.” Gimbiya ta yi murmushi sannan ta ce, “Kada mai magana ya karaya, ba a san namiji da tsoro ba. Kuma ina son mai lambu ya tuna cewa ita fa duk wanda zuciyarta ta amintu da son sa, to shi ne sarkinta. Amma in ka ga mace dukiya ko mulki su ne dalilan da take gina soyayya a kansu, to babu shakka mayaudariyar kanta ce.” Jin haka ya sa Yahaya yin murna da kuma tabbatarwa kansa cewa lallai wannan yarinya ta san abin da take yi. Sai ya ce, “Ya ke kyakkyawa, yanzu lokaci ya yi da zan koma lambu, don na tabbata Sarkin lambu zai damu in ya ga ban dawo da wuri ba. Kin san mutumin nan yana ji da ni kamar dan autansa.” Washegari bayan kammala aikin lambu, ma’aikata duk suna ta haramar komawa gidajensu, sai Sarkin lambu ya kira Yahaya yana jan sa da labari a hankali Www.bankinhausanovels.com.ng suna tafiya har sai da suka yi nisa da sauran jama‘a,

suka sami Karkashin wata itaciya mai yawan inuwa suka zauna. Sarkin lambu ya ce, “Ya kai Yahaya. Kai dai saurayi ne wanda babu shakka Allah Ya yi maka hankali da natsuwa. To abin da nake son shaida maka shi ne, ni — na aminta da kai wanda kuma har hakan ne ya sa nake shaida maka wannan sirri. Tun da Sarki ya amince da kai har ya yarda ka rika kai wa Sarauniya kaya marmari, to ina yi maka gargadin cewa ka yi hankali da ita wannan mata ta Sarki, don kuwa ba ta da mutunci ko kadan, sannan kuma ba ta da kamun kai. Ko kadan ba ta jin tsoron Allah. Sannan kuma wani babban abin takaici shi ne ko kara ta gifta a gaban Sarki, to ba zai Ketara ba saboda tsananin tsoron kada ya bata mata rai da ya ke yi. A yau da a ce Sarauniya za ta ce tana son kan Waziri, to babu shakka kuwa Sarki zai sa a saro mata.” Sarkin lambu ya Kara da cewa, “Ai ka gaa da nine Sarkin yaki na wannan kasa, kowa so ya ke yi ya ganni don tsananin jaruntar da Allah Ya ba ni, na shahara matuka da farin jini fiye da yadda kake zato. To wata rana an yi shiri tsaf za a tafi fagen fama, sai Sarauniyar nan ta ce da ita za aje, haka kuwa aka yi. Www.bankinhausanovels.com.ng Aka dauki mako biyu ana gwabzawa. Na yi budawar tawa irin ta jarumai, na zubar da kawunan mazaje, kowa ya ganni a wannan fili zai ce ni zaki ne. Kai kada in yi ta zuga kaina, amma dai ko babu komai, ka san cewa duk wanda aka kira da sunan Sarkin yaki na wannan makekiyar kasa, ka san lallai ba karamin jarumi ba ne. To ashe duk kaiwa da komowan can da nake yi a fagen fama Sarauniya hankalinta yana kaina ban sani ba. Bayan dawowarmu sai ta shiga farauta ta. Kai in takaice maka labari, wannan muguwar Sarauniya sau biyar tana KoKarin neman aikata alfasha da ni amma Allah da ikonSa Yana kiyaye ni. Lokacin da ta tabbatar da cewa ba za ta sami nasara game da bukatarta a kaina ba, sai ta kai mugun suka na a wurin Sarki wanda hakan ya yi sanadin raba ni da rawanina na Sarkin yaki. Ba don Sarki na shakkar askarawa da jarumai ba, to babu shakka da tsire ni zai sa ayi. Wannan shi ne dalilin mayar da ni Sarkin lambu don wulakanci. Shi ya sa ya kai Yahaya nake gargadin ka a kan cewa ka yi hankali don kada ta halaka ka kamar yadda ita ta halaka.” Ranar kai kayan lambu Yahaya ya cika Www.bankinhausanovels.com.ng kwandunansa guda biyu da kayan marmari, daya na Sarauniya, dayan kuma na Gimbiya. Sai ya fara zuwa gidan Sarki. Da zuwansa sai Sarauniya ta fara yi masa wasu ‘yan take-take irin na mace mara kamun kai, nan da nan cikin ladabi Yahaya ya juye kayan marmarin ya kama hanya zai fita sai ta kira shi. Ta kawo riga da wando da hula ta ba shi hade da takalma irin na alfarma, sannan kuma ta dauko kudi masu tsoka ta mika masa tana murmushi tana kallon sa. . Yahaya ya amshi kyauta ya yi godiya, ya dauki kwandonsa ya fice. Yana fita sai ta yi wata irin ajiyar zuciya saboda zakuwa da ta yi da shi. Ya tsaya wurin masu tsaron fada ya dauki daya kwandon kayan lambun da ya ajiye, bai zame ko ina ba sai Kofar gidan Gimbiya. 

Daya daga cikin masu tsaron Kofa ya shiga ya ce da Gimbiya, “Ranki ya dade ga mai kayan lambu ya zo.” 

Ai kamar wata zautacciya, zumbur sai ta mike ta nufi hanyar Kofar gida ta yadda har sai da kuyanginta suka tsorata suka tashi suka bi ta a guje. Ta yi sauri ta sauke kwandon da ke kan Yahaya ta dora a kanta cikin murna da farin ciki, ta dubi masu tsaron Kofa ta ce, “Daga yau duk ranar da mai lambu ya zo, to a rika barin sa yana shigowa babu iso.” Www.bankinhausanovels.com.ng suka amsa, “An gama ranki ya dade!” Ta juya ta nufi cikin gida, sai ‘yan mata masu yi mata hidima suka yi KoKarin karbar kwandon kayan ~ marmarin da ke kanta amma sai ta ce su yi hakuri wannan kaya nata ne. Da suka shiga ciki sai ta ce, “Yahaya da a ce zan iya yin fushi da kai, to lallai kuwa da na yi, sai dai kuma ba ni da karfin zuciyar da zan iya yin fushi da kai din ne, saboda son ka ya riga ya cika cunkus a cikin zuciyata.” Sai Yahaya ya ce, “Ko da ya ai wanda zaa yi fushin da shi bai riga ya san laifinsa ba, amma yana tuba. Tuban masoyi kuwa, tamkar taki née na soyayya.” Gimbiya ta ce, “Amma dai ai kyan masoyi in ya yi alkawari, to ya riKa cikawa. A kan alKawari tun da safe ya kamata ka zo amma ka bar ni cikin kogin tunani, ba na jin dadin ruwa ballantana abinci a dalilin rashin zuwan ka.” Shi kuma Yahaya sai ya ce, “Lubna lallai na yi kuskure, kuma ki yi mini hakuri a kan haka, kuma ina son in shaida miki kada ko kadan ki dauka cewa ni ma cikin jin dadi hakan ta faru gare ni, a'a, mai gidana ne ya shagaltar da ni da wani aiki. Amma lallai ne ki sani cewa tun daga ranar da na zo nan muka ga juna, to rabin dare kawai nake iya runtsawa, Www.bankinhausanovels.com.ng rabi kuwa na tafiya ne wurin tunanin ki.” Gimbiya ta sa aka kawo wa Yahaya abincin alfarma nau'i daban-daban, ya zauna ya ci ya sha, sannan ta zo ta same shi suka yi ta hirarsu ta masoya. Can sai idanunta suka kai kan daya kwandon wanda kayan kwalliya da Sarauniya ta bai wa Yahaya suke ciki. Gimbiya ta dube shi ta ce, “Yaya na gan ka da wani kwandon daban, kuma har da wasu suturar sawa a ciki?” Sai Yahaya ya ce, “Aina kai wa babarki kayan lambu ne can gidan Mai martaba, shi ne ta yi mini kyautar wadannan kaya, har da ‘yan kudi.” Tana jin wannan magana game da Sarauniya, sai ta sauya fuska, ta ce, “Ya kai masoyina, ka yi hankali da macijiya don kada ta sareka. Lallai na cuci kaina kuma na cuce ka in har ban sanar da kai cewa Sarauniya tana da mugun dafi ba, kuma in ba ka yi hankali ba, lallai za ka rufta don ta saba saran manyan mutane da Kanana. Saranta bai kyale na kusa ba ballantana na nesa, don ta sari manyan sarakunan duniya da 'ya'yansu kuma duk saran ya kai musu. Ni dai ina rokon ka ya kai masoyina, ka yi taka-tsantsan, in kuma ka Ki, to tabbas sunanka halakakke. Wata rana zan ba ka labarinta. Kuma ina roKon ka, matufar dai akwai soyayya tsakani na da kai, to don Www.bankinhausanovels.com.ng albarkacin soyayyar kada ka kuskura ko a mafarki ka taba sanar da Sarauniya cewa kana kawo mini kayan lambu.” Sai Yahaya ya yi murmushi ya ce, “Babu shakka kin yi gaskiya ya ke tauraruwa, labarin wannan macijiya da dafinta tuni ya riga ya sami masauki a kunnuwana, kuma in Allah Ya yarda zan rika kaffa-kaffa da ita.” 

Bayan wani lokaci Gimbiya ta raka Yahaya har Kofar gida kuma ta tsaya tana kallon sa har ya bace sannan ta koma ciki. Da ya koma lambu sai ya nunawa Sarkin lambu kyautar Sarauniya, shi kuma sai ya Kara ja masa kunne cewa,  Kai dai na gaya maka cewa ka kiyaye.” Aka dauki lokaci mai tsawo Yahaya na aikin lambu, yana ci gaba da zuwa gidan Sarki yana kai kayan marmari, kuma soyayya ta yi karfi tsakaninsa da Gimbiya har yadda abin ke nema ya zame musu kamar ciwo. Sarauniya Zizaratu a duniyarta kuwa, babu abin da tasa a gaba kuma take kwadayi kamar aikata masha‘a da saurayi Yahaya. Ta gwada shi kamar sau shida amma ko alamar gane abin da take nufi ba ta gani a wurinsa ba. Ran nan dai sai ta kasa hakuri ta ce masa, “Yahaya kana son rayuwarka kuwa? To wannan ita ce rana ta Karshe, in ka sake dawowa ba ka aikata abin Www.bankinhausanovels.com.ng da nake nufi ba, to babu shakka ka gama rayuwa.” Shi dai sai ya fita yana mai tunani tare da cewa, “Allah Ka yi mini tsari daga sharrin wannan halakakkiyar mace.” Ya koma ya sanar da Sarkin lambu abin da ya wakana tare da sanar da shi cewa, “Ni daga yau ba zan sake kai mata kayan lambu ba.” Sarkin lambu ya amince yana cewa, “Gaskiyarka, kuma na goyi bayan ka, in ranar ta zo sai mu aiki wani yakaimata. RANAR kai kayan lambu ta kewayo, aka tura wani ma’aikaci da na gidan Sarki, shi uma Yahaya ya dauki na gidan Gimbiya. Mai kai na gidan Sarki na zuwa sai Sarauniya ta -tambaye shi, “Yau ina Yahaya?” Shi kuwa sai ya ce, “Ranki ya dade ai an sauya shi  yanzu ni zan rika kawowa.” Sarauniya Zizaratu tace, “Af, to... shi ke nan.” Sai ta shiga tunani, “Wato yanzu matsiyacin yaron nan sun hada kai da Sarkin lambu suna son su tona mini asiri ko? To ai ba su isa ba, don kuwa wutsiyar 

rakumi ta yi nesa da Kasa. In sun san wata ai ba su san wata ba.” Ta ce a sanar da Sarki cewa lallai tana bukatar ganin sa a cikin gida, nan da nan Jakadiya ta cika aikinta. Ana tsakiyar fadanci Sarki ya yanke shari'ar da ke gabansa ya shigo cikin gida ya sami Sarauniya kace-kace cikin kuka da hawaye mai dumbin yawa, hankalinsa ya tashi har da durkusawa a gare ta yana Www.bankinhausanovels.com.ng 

tambayar abin da ya faru. Sarauniya ta dube shi ta ce, “Allah Ya taimake ka, ina tausaya maka ne, na ga irin yadda kake son mutane da tausaya musu, amma kuma kullum abin mamaki ba a kaunar ka. Ni ce kadai mai son ka tsakani da Allah wanda hakan ya sa ba na son in rika ganin ka cikin bacin rai, shi ya sa ba na fada maka wasu abubuwan.” Sarki ya ce, “E, lallai na san haka ya ke abar Kaunata. Amma don Allah mene ne dalilin kukan ki a halin yanzu>” Ya sa gefen alkyabbarsa yana goge mata hawaye. 

Sarauniya ta ce, “Allah Ya karya makiyanka, in banda raini da wulaKanci da kuma rashin ganin girman sarauta, ina mai aikin lambu ina Sarauniyar Sarki mai dumbin mulki da iko irin naka?” Ta Kara barkewa da kuka tana cewa, “A gaskiya in ba ka gama da Sarkin lambu ba, to watakila shi ne ajalin ka, don gabar da ke tsakanin ku tun daga lokacin da ka sauke shi daga Sarkin yaki Allah ne kadai Ya sani, Wai don ya ga saurayin nan Yahaya kyakkyawa ne, shi ne ya sa shi ya zo ya neme ni... kamar ni? Ko me ya mayar da ni oho? Kai wannan wulakanci da yawa ya ke. Sai ka ce kai ba Sarkin yanka ba ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng 

To fa da Sarki ya ji wannan zance sai hankalinsa ya tashi, ya yi fushi; fushi mai tsanani, idanunsa suka kada suka yi jajawur, ya tashi ya dunkule hannu yana ta bugun bango don bacin rai. Ita kuma Sarauniya sai ta mike tana rarrashin sa tare da sanar da shi cewa shawara kawai ita ce ba tare da shawartar kowa ba, ya zartar da hukunci. Ya tashi ya koma fada, ya tarar da shari'ar da ya fara tana jiran sa. Nan take ya ba da umurnin cewa a kai wanda ake Kara da shi kansa mai Karar gidan yari a kulle. Sun hadu da fushin Sarki. Sannan sai ya cewa ‘yan majalisarsa ba ya son ganin kowa, yana buKatar zama shi kadai. Can sai ya nisa ya kira Sarkin dogarai ya ce masa, “Ka je ka zo mini da Sarkin lambu da mataimakinsa Yahaya.” Sarkin dogarai ya ce, “An gama Allah huci zuciyarka.” 

Sarkin dogarai da tawagarsa suka nufi lambu — amma Yahaya kadai suka samu, domin shi Sarkin lambu ba ya nan, ya yi dan tattaki zuwa Kauye kuma zai yi ‘yan kwanaki. Ya sa aka yi wa Yahaya daurin goro, aka auna shi zuwa wurin Sarki. Ana isa wurin tun kafin a yi wani bayani, sai Sarki ya daka wa Sarkin dogarai tsawa, “Sarkin lambu fa?” Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin dogarai ya amsa, “Allah Ya ba ka nasara an ce ya je Kauye amma ‘yan kwanaki kawai zai yi ya dawo. Saboda haka na aike da dogarai gidansa, yana zuwa a taho da shi.” 

Sarki ya ba da umurnin cewa a kai Yahaya gidan kurkuku a rufe tare da horo mai tsanani, bayan kwana bakwai kuma a dandake shi ya zama baba, wato ya zama ba namiji ba. Kwanaki biyar da yin haka sai Sarkin lambu ya dawo gari, amma maimakon ya fara zuwa gidansa sai ya ratse ta wurin aiki tukuna, su kuma suka ba shi labarin cewa an zo an tafi da Yahaya, shi kuma ana can ana dakon zuwansa. 

Ya nufi gidansa a fusace, yana zuwa zai shige sai dogarai suka firfito suka nufo kan sa. Ya roKe su don Allah su bar shi ya shiga iyalinsa su gan shi tukuna, sannan ya fito su tafi. Wani dogari ya ce, “Mu Kyale ka ka shiga? Ai kai ma ka san ba zai yiwu ba, kamar ba Sarki ne ya aiko mu ba?” 

Nan suka nufo shi za su cafke, amma sai ya watsaf da su, dama su goma ne. Ya bi su ya fara daka musu kashi, suka watse. Ya shiga gida ya ga iyalinsa. Ya wuce dakinsa ya yi shiga irin ta yaki. Ya rataya takobinsa gaya wa-jini Www.bankinhausanovels.com.ng na-wuce, ya dauki garkuwarsa, ya sungumi mashi, sannan ya sauyawa dokinsa sirdi. Ya nufi gidan Sarki, mutane na kallonsa suna ta mamakin yau lafiya kuwa? Tsohon Sarkin yaki a cikin kayan yakir Sarkin lambu ya isa fada, ya shiga har gaban Sarki da dokinsa, babu wanda ya tare shi, don kowa ya san jaruntarsa. Ya dubi mutane ya ce, “Duk wanda ke son ransa ya fita, ina bukatar ganawa da Sarki, wanda kuma ya gaji da zaman duniya, sai ya zauna ko kuma ya yi wani mugun motsin da ban yarda da shi ba.” Cika-aiki suka zaburo za su nufo shi shi kuma sai ya zare takobi, Sarki ya yi musu tsawa ya ce su fita. Kowa ya tashi yana fita, har da malamin nan da ke koyar da Yahaya, amma sai Sarkin lambu ya ce, “Allah Ya gafarta malam banda kai, ka zauna.” Bayan duk sauran jama’a sun fice, wato sun rage su uku kadai, sai Sarkin lambu a kan dokinsa ya ce, “Na ji ka sa an kamo Yahaya babu gaira babu dalili, alhali yaro ya kiyaye mutuncinka, kasancewar shi ba mutumin banza ba ne. Yau zan sanar da kai gaskiya, matarka Zizaratu ita ce bakar makira don sau shida tana neman sa don aikata masha’‘a da ita, amma yana Ki, a kullum al'amarin ya faru, sai ya sanar da ni. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kuma ganin abin yayi yawa ne ya sa yaron ya ce shi ba zai sake zuwa gidanka ba, kuma na goyi bayansa, don kiyaye mutuncinka. Hasali ma tun farko ni na gargade shi a lokacin da na fara ganin alamu na tabbatar sai hakan ta faru. Ni kaina ba don tsoron Allah ba da kuma gudun kada in ci amanarka ni ma wani ya ci tawa, to da tuni na gama da ita. A Kalla sau biyar tana kai mini farmaki, kuma don na ki amincewa ta kai sukana wurinka, kuma ka amince har ka cire ni daga Bangaren yaki ka mayar da ni na kayan lambu don wulakanci, a dalilin makircin da Sarauniya ta Kulla. Ka riga ka yi nisa, babu wanda ya isa ya fada maka gaskiya don kana Sarki, sai dai daga baya a je ana ta zunden ka. Ranka ya dade, idan kana so a zauna lafiya a wannan gari, to kada a kuskura a taba Yahaya, in kuwa aka taba shi, to jini kuwa zai kwarara. Kar ka ga rannan ka sa an yi mini bulala a lambu ban ce komai ba, ka dauka ko jaruntata ta Kare ne, a‘a biyayya ce kawai. Ni da Yahaya in ba ka bukatar mu ne a Kasarka, sai mu tattara mu Kara gaba.” Da Sarki ya ji abin da Sarkin lambu ya ce, sai ya yi shiru, ya sunkuyar da kai cike da mamakin irin maganganun da Sarkin lambu ya farfada masa. Can bayan wasu ‘yan dakikoki, sai Sarki ya nisa ya daga kai, ya juya gefen malamin nan ya ce masa, “Ko mene malam ya gani game da jawabin Sarkin lambu?” Sai malam ya ce, “Allah Ya ba ka nasara ai abin da ka sani ne lallai kafin a yanke wa mai laifi hukunci, to ya kamata a bincika sosai, kasancewar in aka yanke hukunci ba tare da bincike ba, to lallai akwai zalunci ko kuma son kai. Saboda haka Allah Ya ba ka yawan rai, lallai a bincika al'amarin wannan yaro cikin natsuwa. Ni kaina na yi matukar mamakin a ce wannan yaro ya farar da wannan al'amari da ake magana don kuwa na dade ina lura da shi a matsayinsa na dalibina, duk da cewa ba a shaidar mutum gaba daya amma ni dai a iyakar fahimtata ban ga alamar yiwuwar samuwar irin wannan babban laifi daga gare shi ba. Ranka ya dade ya kamata a yi nazarin irin halayar wasu matan don kuwa su da shaidan duk tafiyarsu daya ce.” Sarki ya ce, “Lallai gaskiya ce Allah gafarta malam, to amma ni nasan abin dazan yi.” Ya dubi Sarkin lambu ya ce, “Na ji duk abin da ka ce amma ni zan bincika, sai dai akwai sharadi, in har na fahimci cewa akwai sharri a cikin zancenka Www.bankinhausanovels.com.ng 

tsakaninka da Sarauniya, to babu ko shakka zan saa tsire ka gaba daya kai da Yahaya. Amma in zancenka ya tabbata gaskiya, to lallai zan mayar da kai mukaminka na Sarkin yaKi. Sai dai kuma ko kadan ba na son kowa ya ji wannan magana har sai na gama bincikena, wato kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa yadda aka saba, ko da yake akwai dan bambanci kadan da za a samu, wato yanzu Yahaya zan dauke shi daga lambu zuwa inda zan iya samun saukin nazartar maganar da kyau.” Haladu Sarkin lambu ya ce, “naji davi, Allah Ya taimake ka!” 

Aka ba Sarkin dogarai umurnin fitowa da Yahaya daga kurkukun zuwa fada. Sarki ya ce masa, “Ya kai Yahaya an yi min bayani, kuma fushi ya sa na yi saurin yanke hukunci a game da kai ba tare da bincike ba. To yanzu wannan ya wuce, kuma daga yau na nada ka a matsayin mai kula da gidana na hutawa. Akwai dakuna biyu kusa da gidan, nan ne masaukinka.” 

Yahaya ya yi godiya ya tashi ya fita. Sarki ya sallami Sarkin lambu, shi maya yi gaisuwa ya fice. Bayan ficewar Yahaya da Sarkin lambu, sai Sarki ya fuskanci malam ya ce, “Malam Ahmadu ka ga wannan lamari mai bakanta rai dai? Ni kuwa in har Www.bankinhausanovels.com.ng 

wannan magana ta tabbata gaskiya, to zan zamo wanda ya fi kowa mamakin mata, don irin yadda na amincewa wannan mata, na sakar mata komai, na kori sauran matana saboda son da nake yi mata. Kuma Allah gafarta malam, saboda amincewar da na yi mata, ta sa na wulakanta 'yata har na sauya mata gida. Don ma a wancan lokacin na yi dacen daukar shawarar wasu mutanen kirki cewa kada in sa a sare wa ‘yar tawa kai. Malam in har wannan magana ta tabbata, to daga yanzu matan Kasata kaf za su riKa wahala kamar yadda mazaje suke yi, har yaki za su rika zuwa, kuma za mu sa su a gaba sai an fara kashe su tukuna kafin maza su shiga, kai har da 'yata duk za a hada, don ba zan kara saurarawa wata ‘ya mace ba.” Sai malamin ya ce, “Allah Ya huci zuciyarka, ai laifin wani ba ya shafar wani, don duk 'yan Adam ba su taru sun zama daya ba. Allah cikin hikimarSa Ya yi kowa daban-daban, kowa da irin halinsa da kuma irin fahimtarsa, don kuwa akwai matan da in ka gansu har zuciyarsu sai ka rantse cewa waliyai ne, kuma hakan suke. Saboda haka ina rokon Sarki ya huce kuma ya bi komai cikin natsuwa.” Sarki ya ce, “Haka ne malam.” Shigar Sarki cikin gida ke da wuya, sai ya sanar da 


HMMMM LABARI FA NATACI GABA DA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...