YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN


Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Dailanu tana fita sai ta yi wa jama’arta nuni, ai nan da nan suka sungumi gida, tana gaba suna biye har tsakiyar dumbin aljanun nan da ke fagen fama sannan aka sauke shi. Aljana Dailanu ta shiga ciki,

Www.bankinhausanovels.com.ng can bayan wani dan lokaci sai ga 'yan matan nan gaba daya suna biye da ita.

Wannan al'amari ya yi matukar bai wa jama'ar aljanu mamaki, suka Kara tantance cewa wato a banza ke nan Sham'una ke daukarsu tun da har ba zai iya soyayya da ‘ya'yansu mata ba sai dai na mutane. Ai nan fa suka yi ta tsine masa, kuma zaluncinsa ya Kara bayyana a gare su.

Wasu daga cikin jama’ar da ke wurin sai suka yi ta cewa, “A fito mana da azzalumi, a fito mana da mugu.”

Aka kuwa fito da shi daga cikin battar Karfe, daure cikin sarka. Wasu daga cikin ‘yan matan nan suna kuka haka suka rika tashi suna bayyana irin yadda Sham'una ya rabo su da gidajensu da masoyansu ya mayar da su Karkashinsa don fin Karfi. Bayan sun kammala, sai aljana Dailanu ta mike ta yi bayanin irin yadda ta hadu da wadannan ‘yan mata mutane, yadda ta taimaka musu da kuma sanar da taron nan cewa ita ce ta dauki bakin littafin da asirin rayuwar Sham'una da kakarsa Bakayalu ke ciki har zuwa dai irin wannan gagarumar nasara da aka samu.

Sham'una da ke daure duk yana jin abubuwan da ke faruwa kuma yana kallo da idanunsa. Zuciyarsa ta Kuntata matuka, hankalinsa ya tashi musamman

ZAMU TASHI 


lokacin da suka hada ido da Dailanu, ya tuna irin, karfinsa da yadda ya karya mazaje da kumajnin yadda ake tsoron sa, sai ga shi wai shi ne yau  kaskance ake tozartawa a gaban talakawansa da kuma yarinyar da ya fi so a rayuwarsa gaba daya, wato Nur, kuma sai ya tuna cewa wai duk wannan ‘yar'uwar tasa ce Dailanu sanadin wannan tozarci, ai sai ya yi wani irin kukan kura ya yunkura ya tsinka sarkar da aka,daure shi din ya nufo aljana Dailanu gadan-gadan da nufin daga yanzu ko bai sake samun nasarar komai ba, a rayuwarsa, to aKalla dai ya sami damar salwantar da ita.  Ya kuwa yi nasarar kawowa har inda take, amma ya hadu da rashin sa'a, jarumi Idrisu ne ya girgiza mashi ya sakar masa a baya, wanda ya sa shi yin wata irin Kara mai ban tsoro, ya yi sama, kuma kafin ya fado. Idrisu ya sa takobi ya datse shi, shi kuma Sarki Ifritu yasa gwalminsa yabaramasakai, Irin wannan mummunan kisa da Sham'una ya samu ya sa jikin kowa a wurin ya sake yin sanyi. Aka yayyanka gawarsa gunduwa-gunduwa don samun saukin Konawa, aka kwashe tokar aka yi ta watsawa. a cikin teku ruwa na tafiya da ita. Aka dunguma gaba daya aka shiga cikin gari, jama’ar birnin cike da murna don duk da cewa an
Www.bankinhausanovels.com.ng zo da yaqi an kuma shigo cikin garinsu, to amma kuma kamar ba a yi ba, don babu wanda zai hadu da wani kaskanci da a al,adance aka saba in irin hakan ta faru. Ko ba komai dai sun ci albarkacin 'yar’uwarsu aljana Dailanu * Bayan komai ya natsa sai jarumi Idrisu ya ba jama’ar wannan birni shawara a kan cewa, ba zai yiwu su zauna haka babu shugaba ba, saboda haka wajib? ne su zabi wanda zdi jagorance su, amma wannan karon lallai ne su'zabi wanda suke jin zayyi musu adalci,ai sai duk taron ‘da ke wurin kamar sun hada baki suka ce su ba su da wanda ya wuce Dailanu, don kowa ya santa da adalci da mutunci da tausayi da kyauta da son jama‘a ko da wancan mulkin, saboda haka ita’ suka zaba' a‘ matsayin Sarauniyarsu-,  wannan abu yayi marukar faranta wa duk masoyan Dailanye rai, don Kawayenra mutane ma Barkewa da ‘wake-wake da rafka  Bayan waurin yayi shiru sai Dailanu ta miqe don yin jawabi,-ta farada bismillah da kuma salati; abin da mutanenta basu. sani ba, sannan sai taci gaba da cewa“Yaku *yan‘uwana, na yi farin ciki da godiya da kuka nuna irin wannan Kauna da soyayya gare ni, ta yadda har kuke ganin cewa na cancanci in


Www.bankinhausanovels.com.ng shugabance ku, sai dai kuma dole ne in ba ku hakuri don a zahirin gaskiya ba zan iya ba...”
Ai ba ta kammala fadin abin da take nufi ba sai wurin ya yamutse da hayaniya kamar ana fada, suka harzuka a kan cewa sai dai in za ta tozarta su ne, amma abin da suka zartar ke nan.

Dailanu ta ce, “To ku saurara.” Wuri kuwa yayi tsit. Sai ta ci gaba da cewa, “Ya ku jama’ata, ina da dalilai guda biyu masu Karfi da suka sa ni cewa ba zan karbi sarautarku ba. Na farko dai shi ne addinina da naku ba daya ba ne, yanzu ni Musulma ce, ku kuma kuna bauta wa rana da wuta, to yaya za a yi in mulke ku kuji dadi nima in ji dadi?”

Sai wani aljani mai matsakaicin shekaru ya yi wuf ya mike, ya ce, “Ya ke Dailanu, ke din nan kin fi mu sanin wasu Ka'idoji na bautar rana da wuta, amma kuma kika yi watsi da addinin, kuma ke kanki kin san cewa ina daya daga cikin shugabannin bautar tamu, amma a zahirin gaskiya yanzu ni kaina na fahimci cewa bautar da muke ta banza ce mara tushe, saboda haka ni dai na yi amanna da addinin da kike kai.”

Ai nan take dumbin jama'ar aljanun da ke wurin suka yi ta cewa sun yi imani da Musulunci kamar

yadda Dailanu ta yi. Dailanu fa cike da murna da walwala ta ci gaba da

Www.bankinhausanovels.com.ng jawabinta na murnar fitarsu daga kafirci, ta ce, “Sai dai kuma ba shiga cikin Musuluncin ba ne kawai, a'a akwai sauran aiki a gabanmu.

Aikin kuwa shi ne, shi addinin Musulunci ba a yin sa da jahilci, kuma a Ka'idarsa ba a yin sa da cewa wai haka na ga wane yana yi, ko kuma haka ya dace da al'adarmu, ko kuma haka ya fi dacewa ayi, a'a. A Ka‘ida mutum ba shi da wata kirKira tasa sai dai abin da Allah da Ma'‘aikinSa suka koyar a yi ne kawai addini. Wato ba kamar tsohon addininmu ba da a kan Kirkiro sababbin dokoki ko kuma a yi musu gyaran fuska daga lokaci zuwa lokaci.

Abin da nake nufi shi ne dole ne kowannenmu ya tashi ya nemi ilmi don da shi ne ake tauna gardin addinin tare da fahimtar inda aka sa gaba, kuma babu wanda zai taba zuwa ya iya sa ku musanya addininku, don za ku sami hujjojin da suka gagari dukkan wani abin halitta wanda kuma hakan ke nuna cewa ku ne ke kan hanya ta Kwarai, wato hanyar da Allah Mahaliccin komai Yake so.

Amma fa matukKar kuka zauna babu ilmi, to shi ne zaayi ta muku yawo da hankali, ko a cikin addinin Musuluncin ma wancan ya ce muku kaza yau, gobe wancan ya ce ba haka ba.”

Nan take wani dattijon aljani ya mike ya ce, “To

Www.bankinhausanovels.com.ng Dailanu duk mun yarda, yaya za mu yi mu sami shi wannan ilmi?”

Nan take Sarki Ifritu ya mike tsaye ya fuskanci wannan dattijo, sannan ya juya ya fuskanci sauran jama’a ya ce, “Ni, a maimakon jama’‘ata na ba ku gudummawar malamai dubu goma don su fara imantar da ku.”

Aljana Dailanu kamar za ta daka tsalle don murna, ta kalli Sarki Ifritu ta ce, “Na gode, na gode, mun gode.”

Kasancewar wancan dattijon aljani bai riga ya zauna ba sai shi ma ya ce, “A gaskiya mun gode Kwarai ya kai mai alfarma Sarki Ifritu. Sai dai kuma akwai wani abu da tun tuni ya dan dame mu game da ke ya ke shugabarmu Dailanu. A zahirin gaskiya muna ganin ba zai yiwu a ce Sarauniyarmu ba ta da miji ba.”

Idrisu kuwa sai murmushi ya ke yi, Dailanu ta dukar da kai Kasa sannan ta dago ta ci gaba da bayani, “To da ma dalilai biyu ne na ce za su hana ni shugabantarku, na kawo na farko sai lamarin farin cikin Musuluntarku ya dauke mana hankali. Dalili na biyu shi ne, a dai dan karatun da na yi na addinin Islama ina fahimtar cewa Shari'a ta fi son shugabancin da namiji a kan jama'ar kasa fiye da

shugabancin mace. Saboda haka abu daya zan iya yi, kamar yadda kuke so ni kuma yanzun nan zan fitar da miji, in har ya amince ya aure ni, to ni na yarda in zama Sarauniyarsa mai ba shi shawara, shi kuma ya zama Sarkinmu, amma fa in kun amince.”

Jama'‘a suka ce sun amince don sun san ba Za ta cuce su ba.

Dailanu ta waiwaya ta kalli Idrisu ta ce masa, “Ya kai jarumin jarumai, in ba ka manta ba lokacin da ka shigo cikin koriyar ciyawar nan, wato lokacin da ka shigo ‘yankin aljanu har kuka hadu da masoyiyarka Nur, na roke ka cewa ina son in Allah Ya ba mu nasafa akwai abin da nake so daga wurinka.”

idrisu ya ce, “E Kwarai kuwa an yi haka.” Ya dubi yarinya Nur ya ce mata, “Ai ke ma kin tuna ko?”

Nur ta amsa musu cewa, “Tabbas an yi haka. Amma dan dakata Kawata, kin san fa ba irin haka tsakaninmu, kada kuma ki ce shi kike so! Ko a ranar ma ina ce wasa kike yi.”

Dailanu ta yi murmushi sannan ta ci gaba, “Ya kai Idrisu ba wani abu ne nake bukata ba face wannan doki naka ya zama mijina.”

Mamaki ya rufe Idrisu, ya ce, “Dailanu ko ban ji abin da kika ce da kyau ba ne?”

‘Tace, “Kwarai kuwa ka ji da kyau, dokinka Jagora

Www.bankinhausanovels.com.ng ne nake so ya zama mijin aurena, sai dai in ba ya so na.”

Jama’a fa suka yi haja-haja ana neman karin bayani daga wurinta, ta yadda a matsayinta na Sarauniya take bukatar doki ya zama mijinta. Hatta kawayenta su Nur abin ya yi matukar kulle tunaninsu.

Dailanu ta nuna Jagora dokin Idrisu da dan yatsanta ta ce, “Don Allah Jagora koma siffarka ta asali, yau ba ranar boye-boye ba ce, in ma kowa bai sani ba, to ninasani.”

Abin mamaki sai ga Jagora ya rikide ya koma asalin siffarsa. Kuma ma babban abin mamaki sai kowa ya ga ashe kyakkyawan saurayin jarumin nan ne wanda ke ta taimakon su jarumi Idrisu da Sarki Ifritu tun daga birni na goma lokacin da Jagora ya fara rashin lafiya. Ashe dai shi ne Jagora, kuma duk lokacin da ba ya kusa da Idrisun rikidewa ya ke ya koma siffarsa ta asali.

Kuma shi ne wanda ya zo da gudummawar dumbin jama’arsa lokacin da yaki ya yi Kamari sosai, kuma aka yi ta dauki-ba-dadi da shi har zuwa yanzu da aka yi nasara.

Mutane da aljanun da ke wurin kowa ya yi shiru ana ta mamaki, shi kuwa Idrisu bude baki ya yi ya kasa cewa komai yana tunanin yadda hakan ta Www.bankinhausanovels.com.ng kasance.

Jagora ya bude baki ya yi magana, ya ce, “Ya shugabana ina roKon kafin in shaida muku labarina, Dailanu ta fada mini yadda aka yi ta san sirrina yadda har ta gane cewa ni ba doki ba ne.”

Kowa fa ya juya ya kalli Dailanu, ita kuwa sai ta ce masa, “Ka tuna ranar da na kai Kawata suka hadu da jarumi Idrisu a cikin gonakin Ifritu? To in ba ka

manta ba kai kana can waje kana kiwo ni kuma da muka gama gaisawa sai na fito waje don in bar su su dan zanta, to ina cikin wasu ciyayi ina shakar Kanshinsu alhalin kai ba ka gani na, sai ka koma cikin siffarka ka je ka yi Sallar Azahar da La’'asar sannan ka sake komawa doki. Ni kuma tun daga ranar na ji babu namijin da nake so a duniya kamar ka.”

Sai Idrisu ya kalli Jagora cikin murmushi ya ce, “To yallabai, kai muke saurara, ba mu labarin dalilin komawarka doki, domin dai ‘yar budurwar nan ta farke maka laya, ta bayyana maka yadda aka yi ta san ka.”

Jagora ya gyara murya sannan ya ce, “Ya shugabana ka gafarce ni kafin in fara bayani, dole ne in yi wa Allah godiya da Ya sa na sami amsuwa a wurin wannan yarinya kyakkyawa mai hankali da tausayi da kulawa da addini. Wato tun lokacin da muke cikin
Www.bankinhausanovels.com.ng
dajin nan wurin malam mahaifin Nur kana daukar karatu, to ita ce kan zo ta kawo wa malam abinci, kuma takan zo daukar karatu duk ina ganin ta, kuma a duniyar nan na ji babu wadda nake bukatar aure kamarta. Ashe ita ma za ta kamu da so na.”

Jarumi Idrisu ya katse shi, “Malam tun da dai ka sami karbuwa kar ka yi ta jan mu da nisa, mu dai ba mu labarin dalilin kasancewarka doki.”

Jagora ya ce, “To, ya shugabana.

Ni dai asalin sunana shi ne Ramalanu dan Rayalanu. Ni dan Sarkin aljanu ne na can Kasar Yamma, mu Musulmi ne, kuma dalilin zamana doki shi ne don in taimaka wa Idrisu ya sami saukin tafiyarsa zuwa nan ya yaki azzalumi Sham'una.

Dalili kuwa shi ne, Sarkin aljanu Sham'una da ‘yan  kanzaginsa sun daden gaske suna zaluntar mu kuma babu yadda za mu yi da su kasancewar sun fi mu Karfi nesa ba kusa ba. Haka kawai yakan shiga cikin Kasarmu ya kakkamo matasanmu ya tura su fagen fama su yi masa yaki, ko kuma a wasu lokuta su shiga shi da jama’arsa su sami ‘yan matanmu, kai wani lokaci ma har da matan aure su aikata mummunan aikin fyade da su. Irin wadannan ayyuka na zalunci da makamantansu sun dade suna aukuwa a cikinmu

ta bangaren Sham'una.

Www.bankinhausanovels.com.ng Maimakon abubuwa su yi sauki sai wani lamari ya faru wanda a wancan lokaci ya zama mummuna a garemu. Duk aljanin da ke bautar tsafin su Sham‘una a wancan lokaci ya san akwai wani aljani na hannun daman tsohuwa Bakayalu wanda ta amince wa Kwarai mai suna Ziri-muzi. To shi Allah Ya kaddara masa shiriya, saboda haka sai ya gudo kasarmu a matsayin hijira.

To duk ba wannan ya fi dugunzuma wa aljana Bakayalu rai game da shi ba face lokacin da tsafinta ya nuna mata a wancan lokaci ta ga surar fuskarsa a jikin bakin littafin nan da sirrin rayuwarsu ke ciki, ta tabbarar cewa ya yi mata leKen asiri. Ta bugo tsafinta sai ta fahimci yana wurinmu, saboda haka ta umurci jikanta Sham’una ba tare da wani Kwakkwaran dalili ba ya je ya halaka shi kawai.

Mahaifina shi ne Sarki, a lokacin da Sham'una ya shigo bai zame ko ina ba sai fadar garinmu, ya yi ta kisan aljanu, wanda hakan ya sa dole mahaifina ya ba da umurnin kariyar kai, shi ma ya fito aka gwabza wanda kuma ba a dauki wani lokaci mai tsawon gaske ba, musamman irin yadda suka duro mana babu shiri, suka sami galaba a kanmu.

Sham’una ya sa hannu ya kashe mini mahaifi, sannan ya kashe duk wanda ke gidanmu. Ni kadai ne

Karami Kwarai, watakila kuma bai lura da ni ba ne,

amma a yanzu ma ina kallon lokacin, sannan sai

lauma wani Kanin mahaifiyata da ba ya gari a lokacin da abin ya faru.

A karshe dai suka ga wanda suka zo nema, a nan wurin Sham‘una ya tsire shi tare da fada masa cewa duk da cewa yana son sa, to amma babu makawa zai kashe shi don haka kakarsa Bakayalu ta ce a aikata. Sham‘una ya yanke kan ya je ya kai mata.

Shi wancan aljani Ziri-muzi wanda Sham‘una ya kashe, a lokacin zaman da ya yi a garinmu ba shi da wani amini da malamin da ya wuce wancan kawu nawa da ba ya gari lokacin da Sham’una ya shigo ya yi kisan gillarsa. Lokacin da ya dawo sai ya dauke ni na girma a wurinsa yana koyar da ni ilmi da dabarun yeki.

A kallum cikin zuciyata in na tuna lokacin da Sham‘una ya kashe mini mahaifi da *yan‘uwa da jama’‘a sai in ji babu abin da nake bukata ko da zan rasa raina ne face daukar fansa.

Lokacin da na girma sai kawuna ya ce mini, “Yaro tun da yanzu ka kawo Karfi to abin da kake jira na daukar fansa ina ganin kamar ya kusa, don kuwa zaman da muka yi da Ziri-muzi ya taba bayyana mini

sirrin kashe wannan mugun maKiyi namu Sham'una, wato abin da ya karanta a bakin littafin, kuma tun daga wancan lokaci na wajabta wa kaina gano inda ke da Korama da rijiya kusa da ita a cikin duniyar mutane. Na kuma dace, ko da yake wurin yana can cikin wani kungurmin daji ne mai wuyar shiga ga mutane, kuma wani abin mamaki shi ne ina kyautata zaton akwai wanda ke da irin wannan buri namu, don kuwa jiya da na kewaya na tarar da wasu dakuna guda biyu an kafa su a wurin, kuma na ga wani dattijo dan Adam, malami, wanda kuma ina kyautata zaton zai yi Kokarin tafiya ne shi kansa, saboda haka nake son ka zama doki mu san yadda za a yi tafiyar nan da kai, kasancewar irin wannan tafiya ba za ta yiwu ba sai a kan dokin aljanu. Ni kuma zan ta yi maka addu'a yadda zai yi wuyar gaske aljanu ma su iya tantance cewa kai ba doki ba ne.”

Jagora ya ci gaba da ba da labarinsa cewa, “Sai nida kawuna muka mayar da wancan daji wurin zamanmu, muna lura da malamin nan mahaifin Nur, wani lokaci in zama doki din in rika zuwa kusa da shi ko zai yi kokarin mallakata amma shi sam sai na lura babu ruwansa da ni, saboda haka sai muka sake lura cewa ai ba ya zuba ruwa a cikin rijyar wanda hakan ya tabbatar mana cewa ba shi ne Zai yi tafiyar ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shaihi Ibrahim ya sha kallon irin artabun da nakan yi da manyan jaruman da wani lokaci hanya kan ratso da su ta dajin. Musamman in suka zo gadan-gadan suna son kama ni.

Wata rana muna kan wata bishiya zaune sai muka hango maigidana Idrisu yana tafe shi kadai, sai kawuna ya ce min, “Ka kuwa san wani ikon Allah? Wancan saurayin ne nake ta gani a cikin mafarki cewa zai kashe Sham'‘una, kuma kai ne dokinsa, saboda haka yanzu sai ka yi sauri ka zama doki ka tare shi.”

Shi ne na sauko na je na sa Kafata cikin wata sarkakiya har ma na ji rauni, shi kuma Idrisu ya zo ya taimaka mini ya yi jiyyata, ya sa mini sunan da na yi matukar Kauna, wato Jagora.

Babu shakka Idrisu saurayi ne mai mutunci da tausayi, don tun daga wancan lokaci har zuwa yau din nan bai taba daga bulala ya buge niba.

Wannan shi ne takaitaccen labarina.” AKA fara hada-hadar daurin aure tsakanin Jagora dokin Idrisu, wato Ramalanu dan Rayalanu da kuma Dailanu ‘yar Kailanu. Idrisu ne waliyin ango, shi kama Sarki Ifritu waliyin amarya, bisa amincewar

Www.bankinhausanovels.com.ng sauran dangin ango da amarya da ke wurin.

Jarumi Idrisu ya ce, “A matsayina na aboki kuma uban ango ina son don Allah a dan saurare ni don yanzu zan je in taho da sadakin wannan tsaleliyar budurwa da abokina ya samu.”

Ya debi aljanu ya ce su biyo shi, shi kuma ya haye dardumarsa, bai zame ko ina ba sai cikin kogon nan da ya kashe Bakayalu, ya ce su ciccibo masa Katon gadon nan nata na alfarma, sannan duk wani abu mai daraja da ke wurin shi ma su dauko shi. Haka ko aka yi.

Jama’‘a a filin daura aure kawai sai aka ga abu gingiringin haka tun daga cikin sama yana ta Kyalkyali. Idrisu ya ce, “Ga sadaki nan.”

Murna wurin amarya da Kawayenta in aka ce zaa misalta sai abin ya zama Kauyanci. Aka dai daura aure, sannan aka tabbatar wa Jagora da sarautar wannan babban birni. Jama'‘ar garinsa suka ce su ma suna bukatar don Allah a je garinsu don tabbatar masa da sarautar mahaifinsa, wato a takaice dai Ramalanu Jagora ya zama Sarki a manyan Kasashe biyu na aljanu. Gaskiya an ragargaji buki da shagali yadda ya kamata.

Www.bankinhausanovels.com.ng
BAYAN an natsu sosai sai hankalin kowa ya koma zuwa garinsu. Aka yi shiri mai kyau na mayar da kowa gidansa tare da ya da zango a wasu muhimman wurare. An fara ne da garin Sarki Ifritu, sannan sai birnin Idris inda Sarki Abdurrahman ke mulki, wato tsohon garin Sarauniya Zinkadaziyya mai macizai, wanda a lokacin da aka je suka ji irin rugugin da ke sauka daga sama na jama‘ar aljanu da mutane da ke cikin tawagar sai suka rufe birninsu suka je masallaci suna ta neman kariyar Allah.

Daya ke a bayan gari aka sauka sai Idrisu ya sa wani aljani ya dauke shi ya sauke shi cikin gari, ya same su a masallaci ya yi musu sallama, suna ganin sa farin ciki ya lulluBe su, ya tambaye su lafiya, suka ba shi labari, sai ya yi dariya ya ce wa Sarki Abdurrahman, “Ai baa san jarumi da tsoro ba.” ;

Suka mika masa budurwarsa suka tashi suka Kara gaba, haka nan suka yi ta sauke ‘yan matan nan daya bayan daya a garuruwansu bayan an shiga an yi wa jama’‘arta bayanin yadda abubuwa suka faru.

Duk tafiyar nan da ake yi ‘yan matan nan suna cikin wancan gida ne da Sham'‘una ya gina musu, a ciki ake ta karakaina da su. Duk yarinyar da aka sauke a garinsu sai a kawo dumbin dukiya ta zinare da lu’u'lu'u da yakutu da zabarjadi da sauransu a bata.
Daga Karshe aka je aka sauke wa jarumi Idrisu wannan Kankararren gida a garinsu bayan daurin aurensa shi da masoyiyarsa Nur ‘yar babban Shehi Ibrahim. Murna wurin duk wadanda abin ya shafa ba ya misaltawa musamman ma iyayensu da sauran ‘yan'uwa da abokan arziki.

Babban abin sha'awa game da wadannan ‘yan'uwa da abokai da Kawaye shi ne yau wannan na garin wancan gobe wancan na wurin wannan. Babu yadda za a yi Dailanu da mijinta Ramalanu su yi wata uku ba su kai wa Idrisu da Nur ziyara ba, ko kuma wani gari inda Kawayensu suke. Ita kama Nur da mijintaa kai-a kai ba su yanke ziyara zuwa garin Bashari, Yahaya, Habu ko Abdurrahman ba.

Haka suka kasance cikin jin dadi da farin ciki da Kauna har mai raba jin dadi kuma mai raba masoya ta zakke musu.


MASHA ALLAH TO JAMA,A NAN MUKA KARKARE WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN NA YAKI MAI SUNA YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

PLEASE IDAN HAR KA KARANTA KIN KARANTA WANNAN LITTAFI KUMA KUNJI DADINSA KUYI COMMENTS A KASA HAKANNE ZAI BANI KARFIN GWIWAR SAKE NEMO MUKU WANI LITTAFIN NA YAKI MAI DAN KAREN DADI INAMA KOWA FATAN ALKHAIRI ❤

Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...