YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Wani irin farin ciki da murna suka lullube jarumi Idrisu, ganin cewa dokinsa da ya dade babu lafiya ga shi yau ya ji sauki kuma ma kamar ya fi shi zakuwar haduwa da abokan gaba, ai nan take Idrisu ya dauke sirdin dokin da ke kan dardumar da ya ke ta yaki a kanta ya dora wa doki abinsa, ya nade dardumar tashin ya saKala a kurciyar sirdi. Doki yana jin an hau "shi sai ya yi wani irin rimi ya dire, ya daga kafafuwan baya ya harbi iska sannan ya zabura ya nufi inda su Bakayalu suke. Aka hade a tsakiya, su biyu kadai, jarumi Idrisu dan > Hamidu da tsohuwar aljana Bakayalu.

ALJANA Bakayalu ta ce masa, “Kai dan Adam! Me kake bukata ne haka kake ta kashe mana jama’a babu dalili?”

Jarumi Idrisu ya amsa mata cewa, “Ranki kawai nake son dauka, ke da azzalumin jikanki Sham'‘una saboda irin mugun zalunci da kuka dade kuna yi.” Cikin fushi sai ta ce masa, “Kai Karamin alhaki! Ka san da wadda kake magana kuwa? Nice kakar aljanu, nice sharri, ni ce mugunta gaba daya, na kashe aljanu da mutanen da babu wanda ya san adadinsu, wadanda suka fi ka jarunta da tsageranci. Ba a taba nasara a kaina ba kuma ba zaa taba yi ba...”

Idrisu ya katseta, “Ke dakata! Yi gaggawar janye wadannan kalmomin cewa ba za a taba ba, don ina yi miki albishir din cewa lokacin ne ma ya zo yanzu. La'ananniyar tsohuwa kawai wadda rayuwarta ba ta da wani amfani sai cutarwa.”

Da Bakayalu ta ji irin wannan magana da mutum

ZAMU TASHI dan Adam ya danKara mata, a cikin Kasarta, sai ta yi fushi ta dunkule, ta yi wata irin tsawa sannan tazama wata irin Katuwa mai kiba, daga nan kuma sai ta zama yarinya, can kuma sai ta tuna cewa an ce wai jarumin yana da karfi, saboda haka sai ta sake rikidewa zuwa wanijarumin namijin aljani.

Kawai sai ga wani irin doki jajawur da shi a wurin wanda ba a san daga inda ya zo ba, kuma sai kawai aka gan ta a kansa ba tare da ganin lokacin da ta hau ba, ta daga hannuwanta sama sai ga makamai, ta dumfari Idrisu, fada ya kaure tsakanin su abin sai wanda ya gani. Idan ta bullo masa ta nan sai dokinsa Jagora ya baude da shi, ta yi ta yi amma ya gagare ta, suka buga matukar bugawa, abin dai ya zama turnuku. Babu ko tantama wannan tsohuwa ta isa jarumar gaske, don tun fitowar Idrisu har zuwa yanzu bai taba cin karo da jarumin da ya sha wahalar gaske wurin neman nasara da kariyar kai kamar yadda a yanzu suke gwagwatawa da aljana Bakayalu ba.

Da fada ya yi fada sai aljanar ta fahimci cewa dole ne ta sake salo, saboda haka sai ta shiga dabaru irin nasu na aljanu, sai ta shiga fesa wa jarumi Idrisu wani irin dafi a jikinsa don ya zagwanye gaba daya, amma saboda makarin dafin da ke jikinsa sai ya rika jin
kamar ruwa take fesa masa. Da ta ga wannan bai yi masa komai ba sai ta shiga jifan sa da mulmulen garwashin wuta, shi ma dai hakan babu nasara.

Kafin Kiftawar idanu sai ga hannayen aljanar sun koma guda ashirin, kowane hannu rike da mugun makami yana kai wa Idrisu sara, bugu ko suka, amma ko taba shi ba ta sami damar yi ba. Shi kuma duk Kokarin kai sara da dan Hamidu ke yi ko ya sari hannayen nata sai ya ga babu abin da ya faru kasancewar tsafaffun ne ba na hakika ba. Irin wannan yawo da hankali da jarumar tsohuwar ke ta yi masa da wadannan hannaye nata da kuma neman rikita shi da take neman yi ya sa Idrisu tunzura, ya girgiza takobinsa, sai ga takobin ya kara tsawo, girma da nauyi, ya tattakura ya auna tsakiyar jikinta ya kai sara.

Aljana Bakayalu ta kauce, takobin Idrisu ya sari Kasa ta yadda saboda nauyi da kuma irin kaifin sarar sai da wurin ya zama wani dan madaidaicin rami da sai Kato ya tattakura sannan zai iya tsallakawa. Ita kuwa aljana sai ta rikide zuwa wata irin dabba mai tsananin ban tsoro, baka kuma Katuwa, kai ko a mafarki gama-garin mutum ya ga irin wannan dabba, to babu shakka zai zautu in ma bai bakunci lahira ba. Ta zaro harshenta wanda girmansa ya kai na wata

Www.bankinhausanovels.com.ng babbar bishiya ta rika fyadawa tana kai wa Idrisu duka da shi, amma dokinsa Jagora ya rikKa zamewa da shi. Da a ce harshen nan ya taba shi, to babu ko tantama zai yi mugun jin jiki, in bai mutu ba ke nan. Da ta fahimci cewa Jagora yana ba da gagarumar gudummawa wurin ceton uban gidansa, sai ta nufe *“ shi, ta yarfo harshenta daidai Kafafuwansa da nufin sarKafesu, amma saboda kwarewarsa da kuma gane nufinta sai Jagora ya yi sama shi kuma harshen nata ya sauka a Rasa, kafin ta janye har ya dira Kasa, shi kuma Idrisu ya sa takobi ya datse harshen.

Aljjana Bakayalu ta yi wata irin Kara, alamar cewata ~ ji zafi a jikinta, ai nan da nan ta rikide ta koma aljana sosai sai ga jini irin nasu na aljanu yana ta zuba daga bakinta, da Sarki Sham'una ya ga haka sai zuciyarsa ta harzuka ya yi kukan kura don fada wa Idrisu, amma kafin ya Karasa tuni Sarki Ifritu ya zabura ya tare shi, da suka hadu suka bangaji juna sai da kowannensu ya zube a Kasa saboda tsananin Karfinsu, sauran jarumai kuwa sai yaKi ya sake Barkewa.

Karajin mazaje kake ji kamar aradu na fada wa manyan itatuwa da duwatsu, hayaki da wuta kuwa ba a magana, da ma yaKin aljanu sai su.

Aljana Bakayalu wankin hula na nema ya kai ta

dare game da al'amarin karonta da jarumi Idrisu dan

Www.bankinhausanovels.com.ng hamidu. Yanzu kam ta fara tsorata da shi, saboda haka sai ta sake dabara, ta koma wata irin iskar goguwa mai tsananin Karfi ta yi ta zagaye shi, shi kuma Idrisu sai ya yi ta kai wa iskar sara ta duk inda ya ke zaton za ta ji a jikinta. Da dai ta ga wannan shawara ma ba za ta fitar da ita ba sai ta koma kamanninta na asali suka ci gaba da karawa.

Da dai ta ji cewa lallai ta wahala sai ta tattakure da nufin yin wata irin rikida ta ko dai a mutu ko kuma a yi rai, wato rikidar da a zuciyarta ta tabbatar cewa ta karshe ke nan wadda kuma tana jin cewa ko birni ta yi wa wannan rikida tana iya halaka shi ballantana mutum daya.

Wurin wannan rikida irin Karar da ta yi sai da kowa ya razana. Hankalin kowa ya koma kanta, wurin ya gauraye da wani irin hayaki mai kauri kuma jajawur, bayan hayakin ya wanye sai ga wani abu gangaram kamar tsauni, ga shi baki Kirin gwanin ban tsoro, sannan kuma ga shi yana ta motsawa, kai a wannan lokaci hatta Jagora sai da ya fara ja da baya saboda razana; abin da bai taba yi ba.

Wadannan tsauni mai kama da dutse gadan-gadan ya daga sama ya nufo Idrisu da nufin murKushe shi. Jagora dai yana ta ja da baya shi kuma Idrisu yana zungurinsa da nufin Karfafa guiwa. Shi dai jarumin

Www.bankinhausanovels.com.ng tun da wannan abu mai kamar dutse ya nufo shi babu abin da ya ke lura da shi sai wani abu dan madaidaici mai launin ja dake ta dan harbawa yana motsi a jikin tsaunin, saboda haka sai Idrisu ya yi zaton ko idon Bakayalun ke nan, saboda haka sai nan take ya warware mashinsa ya girgiza, ya auna shi ya saki. Ashe ba idonta ba ne, shi ya sa ma ba ta lura ta baude ba, zuciyarta ce! Mashi sai dada shiga ya ke yi yana Kara tsawo da fadi, ita kuwa sai mirginawa take tana ihu da kururuwa ta yadda har Idrisu sai da ya tsorata a lokacin, shi dai murnarsa yanzu kam ya tabbatar da cewa ya same ta a makasa.

A Bangaren Sarki Sham'una kuwa a daidai wannan lokaci ga alama an sami gangara a kansa, don kuwa ga shi can yana ta kurmususu Sarki Ifritu ya kayar da shi kasa yana ta tiKkarsa da gwalmi. -

‘Tuni Bakayalu ta koma ainihin siffarta, ta faditana Karaji, sai ta yi yunKuri ta tashi da mashi a jikinta ta nufo Idrisu gadan-gadan tana kawo masa raruma da nufin a yi mutuwar kasko, shi kuma Idrisu ya fahimci nufinta, saboda haka sai ya kauce ya ba ta wuri, sannan ya sa takobinsa ya sare mata kafada, nan take ta durKushe, kuma kafin ta kai Kasa ya yi sauri ya sa hannu ya zare mashinsa daga jikinta.

Zare mashin nan kawai irin Karar da ta yi kada ma

Www.bankinhausanovels.com.ng mutum ya taba fatan jin makamancinsa, don ana iya kurumcewa. Tana fadowa Kasa sai ta kama da wuta, tana karaji da kururuwa har dai ta kammala Konewa.

Sai ga tarin toka him.

Wasu da yawa fa sai yaki ya dakata aka koma ana kallo, musamman wadanda suka fi kusa da wurin da abin ke faruwa. Wannan toka ta aljana Bakayalu sai ta shiga rikidewa tana musanya launi zuwa wata Katuwar macijiya baka, ga tsawo ga kauri, kanta jajawur, girmansa kamar kan jaki. Kunnuwan macijiyar har da wasu ‘yan kunne, jelarta kuma fari

: fat.

Wannan macijiya sai ta yi wani irin kuka kamar na dan jariri, sannan ta tashi sama ta fuskanci hanyar wasu manyan duwatsu guda uku da ke nan bayan duniya, ai nan take sai jarumi Idrisu dan Hamidu ya tuna jawabin da malaminsa Shaihi Ibrahim dan Yahaya ya taba yi masa a lokacin da ya ke bayani game da abin da da aka samu a cikin baKin littafin da ke dauke da sirrin rayuwar Sham'‘una da kakarsa, wato inda Shaihin ke cewa,

“Ya kai Idrisu, ina so in jawo hankalinka game da wasu muhimman kalmomi wadanda ko ni yanzu ban san hakiKanin abin da suke nufi ba, sai dai in Allah Ya yi maka tsawon kwana ka kai lokaci da kuma

Www.bankinhausanovels.com.ng yanayin, to za ka fi kowa fahimtar abin da ake nufi, wato wannan wurin da ke cewa, “Muddin ana so a kashe Sham'‘una, to sai an kashe kakarsa mai rayuka biyu, wato sai an kashe ta a gangar jiki sannan’a kashe ta a ruhi. Ruhin nata kuma 'wata tirin hatsabibiyar macijiya ce mai mazauni a wani kogon dutsen da ke cikin manyan duwatsun bayan duniya. Kuskure ne

babba a kashe ta ba acikin kogon dutsen ba. Da Idrisu ya kammala wannan tunanisai ya yi sauri ya sauka daga kan Jagora,. ya shimfida darduma ya haye ya tashi sama abinsa ya nufi wurin:da macijiyar nan ta fuskanta, ya ba ta ‘yar tazara yadda ma ba ta san yana biye da ita ba, suka'yi ta tafiya'a haka: "Tana isa wurin babban dutsen sai ta:shige cikin’ kogonsa abinta, shi ma bai yi wata-wata ba wurin aukawa, Shigarsa sai ya fahimci:cewa ashe cikin: wannan kogon dutse a nan wurin hutawar Bakayalu ya ke, nan ne kuma turken tsafinta ya ke, abin da‘ke cikin.sa na alatu::sai wanda ya gani,:‘kuma banda ita babu wanda ya taba shiga cikin sa, har shi Kansa Sham!'‘una din.  Yana shiga sai ya ga wani-Katon gado ‘na zinare wanda aka yi wa ado da lu'ulu‘u;: babu: shakka. in banda aljani irinta babu wanda ya isa ya.mallaki irin wannan gado. A kan -wannan gado kuma ga

Www.bankinhausanovels.com.ng macijiyar nan ta yi gammo ta fito da kanta sama tana kallon sa.

Irin dadewar da Idrisu ya yi zaton za su yi suna marKabu da ita abin bai kai haka ba, watakila ko don ta rigaya ta gaji ne oho, don kuwa yana shiga zare da takobinsa a hannu daya, mashinsa kuma a daya hannun sai ya riKka nufar gadon a hankali.

Macijiya ta yi masa dirar mikiya bakinta bude da nufin halaka shi, shi kuwa sai ya yi sauri ya cilla mashinsa cikin bakinta, a daidai lokacin da ya baude gefe guda, kuma kamar walKiya ya sa takobi ya raba tsakiyarta gida biyu. Nan take ta fadi ta yi wani irin ihu tana mai cewa, “Shi ke nan ka kashe ni.”

Tana zubewa Kasa sai ga shi ta koma cikin cikakkiyar siffarta ta tsohuwar aljana Bakayalu. Ga ta nan an rabata biyu.

Idrisu ya yi wa Allah godiya. Ya tattara gawarta ya zuba a kan dardumarsa ya yunkura ya koma can fagen fama inda ya bar mazaje suna fafatawa. Ya kuwa je a kan lokaci, wataKila ba don Allah Ya kawo shi a daidai lokacin ba, to da labari ya sha bamban. Abin nufi kuwa shi ne irin markabun da ya bar Sarki Sham'una da Ifritu suna yi, to yanzu sa'ar ta koma wurin Sham'una, yanzu har ya buga Sarki Ifritu da Kasa ya daga tasa kokarar zai kwankwatse masa kai.

Www.bankinhausanovels.com.ng Shi dai Sham'‘una ya ji an buge shi ne kawai ya fadi gefe. Jarumi Idrisu ne ya yi amfani da gindin mashi ya bazar da shi, kuma kafin ya kammala mikewa sai ga gawar kakarsa an watsa masa a jiki, Idrisu ya ce masa, “Ga mushen kakarka nan, Allah Ya Kara mata azabar lahira, saura kai.”

Rayuwa ta yi wa Sarkin aljanu Sham'‘una Kunci, zuciyarsa ta kumbura kamar za ta fashe, idanunsa suka firfito suka yi jajawur fiye da garwashin wuta, ya sake kallon gawar kakarsa, shugabar tsafinsu, sannan ya kalli talakawansa, ya tabbatar gara ya fafata ko da kuwa zai mutu ne da ya zauna cikin KasKanci, ya bude baki da Kakkarfar murya ya bai wa jarumansa umurni cewa, “Me kuke jira ne? ayi ta ta Kare, ko dai rai ko kuma mutuwa.”

Yaki ya sake rincabewa, shi kuma Sham'una a tunzure ya nufo Idrisu kamar zai cinye shi danye. Ji kake tim, tititim. Fada tsakanin su ya kai wani yanayi da babu kyan gani.

Bayan kamar kwana uku suna gwabzawa sai bege ya taso wa Idrisu, ya tuna da masoyiyarsa, ya kuma tuna cewa wannan aljani da suke bugawa yanzu shi ne babbar katangar da ke tsakaninsa da ganin ta ai sai wani irin Karfi ya sake shigar sa, ya sa gindin mashi ya banke Sham'‘una har Kasa, ya yi sauri ya sa takobi ya

Www.bankinhausanovels.com.ng  sare masa Kafa daya sannan ya ba da umurni ga Sarki Ifrita da wancan jarumin da a ba san shi ba a kan cewa su ma su ZO su more.

Habawa, haka suka rufa suka yi ta jibga tare da tumurmusa Sham'una har sai da ya yi lilis, kai karshe dai ya some. Sarki Ifritu ya sa aka daure shi tamau da sarka suka sa shi cikin battar Karfen nan da ya taba kulle Ifritu a ciki. Ashe da ma suna tafiye da ita don tunanin yiwuwar samun irin wannan damar.

Sauran mayakan Sham'una ganin yadda aka yi da shugabansu sai jikinsu ya yi sanyi, kuma ashe da ma su a al'adarsu in an kama shugaba, to fa babu sauran yaki, saboda haka duk sai suka watsar da makamansu danufin mikawuya.

Abin da ya ba su mamaki sai suka ga bangaren su jarumi Idrisu ba Kokarin tozarta su suke yi ba, don kuwa ba a bi su an ci gaba da kisa ba irin yadda su suke yi, a'a sai suka ji an ce kowa ya dauki makaminsa atattaru wuri daya jarumi Idrisu zai yi jawabi.

Dan Hamidu ya fara gode wa Allah da yin salati ga Manzon tsira, sannan sai ya yi wani dan takaitaccen jawabi yana mai cewa, “Ya ku taron jama’ar aljanu, yanzu dai yaki ya Kare, Sarki Sham'una yana hannu, kuma tsohuwar azzaluma Bakayalu tuni ta bakunci lahira, duk wannan ba don komai ba sai don tsananin

Www.bankinhausanovels.com.ng zaluncinsu. . ‘Su ne suka jawo muku wahala. Suka gayyato muku yaki, suka jefa ku cikin hadari da kisa duk ba don wani abu da ya shafi kiyaye mutuncinku ba, a‘a sai dai don tsananin son zuciyarsu kawai Mun sani cewa biyayya ce da‘kuma cewa babu ‘yadda za ku yi don an fi Karfinku suka'sa kuka sallama musu rayukanku duk da cewa'ba wai sun Kyale ku ba ne da zalunci’da cutarwarsu.'Saboda‘haka ya ku *jama'ar wannan kasa ina bukatar‘ku sani cewa ba “ zalunci ya kawo mu ba, a'a adalci ne da kuma Kwatar ‘yancin wadanda aka dade ana zalunta,; wato a''yantar ‘da mutane da aljanu’’daga~ mulkin ‘kama-Karyar wadannan ‘yan tsiraru guda biyu.  ‘ Sarkinku shi da"yan kanzaginsa sun‘dade'suna yi “wa matanku“da ‘matan ‘mutane«fyade; '‘suna’ ‘cin " karensu babu’ babbaka.‘ Sham'una’ ya kamo ‘yaran + mutane mata-ya kai-su ‘can ‘Saman ‘tsibiti ‘ya kange. Saboda‘ me? : Ina’ sake’ ‘tambaya, ‘wai ‘shin da‘ wane dalili? Idrisu‘yana cikin wannan jawabi sai suka ji muryar ‘wata mace ‘tana ‘cewa, “Tabbas Wannan’ gaskiya‘ne, kuma babi karya cikin jawabin wannan saurayi dan -‘A'dam.” Sai ga'aljana Dailariu ta bayyana. Ganin ta sai jama'ar garinta gaba daya suka gaishe ta don da

Www.bankinhausanovels.com.ng ma ita suna matukar kaunar ta, har zuci. Dailanu ta ce, “Ni ma shaida ce game da bayanan da wannan jarumi ke yi.” Ko gaisawa ba ta tsaya an yi ba ta umurci jaruman aljanu guda dari cewa su bi ta. Ba ta zame ko ina da su ba sai can tsibirin da su yarinya Nur suke, ta ce su jira ta za ta shiga ta fito, gidan take so za a dauka a kai can fagen da aka kammala yaki. Tun kafin ta shiga cikin gidan take ta rafka sallama, Kawayenta suka amsa mata cike da farin cikin sake ganin ta bayan tsawon lokacin da ta dauka rabuwarta dasu., Nur tace, “Ke kuwa baiwar Allah ai alkawari bai ce haka ba, yaya za’a yi tun da kika bar nan sai yanzu muke sake ganin fuskarki? Don Allah yau kwana nawa? Ko kuma dai’yi hakuri in tambaye ki, shin lafiya dai ko? Meke faruwa?”..dailanu  ta'cé, “Ke rufa mini‘asiri, gudu na yi can “wani'wuri ina Boye wa‘kakata Bakayalu, don ta hakifance cewa tana gani na sai'kisa. Yanzu dai ba wannan labarin ba, maganar da ake ciki akwai aljanu dari a waje suna jiranmu, saboda haka sai ku shirya da Sauri zan-sa su dauke wannan gida mu gudu abinmu.” Jin wannan zance sai hankalin Nur ya tashi matuka,

ta yi sauri ta tambaya, “Don Allah Dailanu babu Boye-Boye tsakanina da ke, fada mini me ya faru da masoyina Idrisu?”

Dailanu ta ce, “Ke kwantar da hankalinki, zolayar ku nake yi, kuma babu wani abu mai muni da ya faru da shi sai alheri. A taKaice dai sai in ce albishirinku.”

Gaba daya suka ce, “Goro, fari sal kuwa.”

Sai Dailanu ta ce, “To a yau dai Allah Ya ba jarumin jarumai Idrisu dan Hamidu nasara a kan muguwar tsohuwa Bakayalu, yanzu ma maganar da ake yi tuni ta zama ‘yar gida a lahira, shi kuma wancan karen saurayin naku Sham'una yana can a hannu daure cikin sarKa.”

Ai fa ‘yan mata sai rungume juna saboda irin wannan labari mai faranta zuciya, suka ciccibi Dailanu suka daga ta sama suna rera wata irin waka mai tausasa zuciya.

Da suka sauke ta sai ta ce, “to yanzu ai sai mu yi harama, ni zan tafi, kuma aljanun da na ce muku yanzu za su dauki wannan gida don mu isa wurinsu Idrisu din.”

Dailanu tana fita sai ta yi wa jama’arta nuni, ai nan da nan suka sungumi gida, tana gaba suna biye har tsakiyar dumbin aljanun nan da ke fagen fama sannan aka sauke shi. Aljana Dailanu ta shiga ciki,

Www.bankinhausanovels.com.ng can bayan wani dan lokaci sai ga 'yan matan nan gaba daya suna biye da ita.

Wannan al'amari ya yi matukar bai wa jama'ar aljanu mamaki, suka Kara tantance cewa wato a banza ke nan Sham'una ke daukarsu tun da har ba zai iya soyayya da ‘ya'yansu mata ba sai dai na mutane. Ai nan fa suka yi ta tsine masa, kuma zaluncinsa ya Kara bayyana a gare su.

Wasu daga cikin jama’ar da ke wurin sai suka yi ta cewa, “A fito mana da azzalumi, a fito mana da mugu.”

Aka kuwa fito da shi daga cikin battar Karfe, daure cikin sarka. Wasu daga cikin ‘yan matan nan suna kuka haka suka rika tashi suna bayyana irin yadda Sham'una ya rabo su da gidajensu da masoyansu ya mayar da su Karkashinsa don fin Karfi. Bayan sun kammala, sai aljana Dailanu ta mike ta yi bayanin irin yadda ta hadu da wadannan ‘yan mata mutane, yadda ta taimaka musu da kuma sanar da taron nan cewa ita ce ta dauki bakin littafin da asirin rayuwar Sham'una da kakarsa Bakayalu ke ciki har zuwa dai irin wannan gagarumar nasara da aka samu.

Sham'una da ke daure duk yana jin abubuwan da ke faruwa kuma yana kallo da idanunsa. Zuciyarsa ta Kuntata matuka, hankalinsa ya tashi musamman


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...