YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN
                   Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

. A wadancan shekaru na farkon hada tsafin, ni da Kaina na rika zuwa dajin da makaman suke ina tsaron
rijiyar, amma da na ga alamar babu komai sai na , daina zuwa, don akwai wahala ko da a mafarki wani mahaluki ya taba sanin irin sarkakiyar matakin da za - a taka wurin.halaka mu, shi,ya sa na ce babu shakka ; wani ya munafunce mu ya fita da wancan bakin littafi.A gaggauce tsohuwa Bakayalu ta nufi dakinta cikin taskar da take ajiye kayayyakinta mafi muhimmanci ta. bankada .inda-:ta ajiye littafin sai kuwa ta gan shi ‘kamar ba,a;taba.motsa shi daga, wurin ba, saboda - haka sai ta dauko shi.ta fito ta sami Sarkin aljanu Sham ‘una a inda ta bar,shi tun dazu a durKushe. Ta . Nuna tare da ce masa, “Ashe.muna neman tayar da hankalinmu, bakin littafi dai yana nan a inda na bar shi, kuma ina zaton babu wanda ya taba shi. Sai ta gabatar da waniirin sihiri, ai nan take sai ga taswirar fuskar Dailanu a jikin littafi,,, . . Bakayalu ta ce, “Babu shakkayari yarnan Dailanu
ce ta taba littafin nan.” Saboda haka sai ta fita ta sa aka kamo Dailanu aka fara azabtar da ita da wata irin ukuba mai tsananin gaske.

Bakayalu ta zo tana tuhumar Dailanu a game da fita da littafi, ta ce, “Ke ce ki ka fita da wannan littafi, don ga taswirar fuskarki nan a jikinsa.”

Aljana Dailanu ta yi wani irin marairaicewa ta ce, “Ya ke kakata, kin sa ana ta azabtar da ni alhali ban san maganar fita da littafi daga cikin dakinki ba. Kuma maganar ganin fuskata kada ki manta ni kadai ce ke shiga ko'ina a dakinki. Kuma fa ba a dade ba da ki ka umurce ni a kan cewa in share tare da goge ko ina a dakin, to yaya za a yi in share ko kuma goge wani abu ba tare da na taba shi ba?”

Aljana Dailanu ta ci gaba da bayani ga kakarta Bakayalu cewa, “Littafi dai yana nan, duk da cewa ba a fada min abin da aka Boye a cikinsa wanda ya Bace ba. To ko ma dai mene ne kada fa mu manta cewa masifar yaki ne ta tunkaro mu gaba daya, kuma a matsayina na jinin gidan nan ina ganin wannan ba lokacin da za a tsaya zargi ba ne, don wannan masifa in aka yi sakaci za ta yi wa gidan sarautar nan muguwar Barna gaba daya.”

Jin wannan zance fa sai tsohuwa Bakayalu ta sa aka

ZAMU TASHI 

kwance ta duk da cewa jikinta bai ba ta da bayanan ba, har ma take ce mata, “Akwai sharadi guda, yanzu ba lokacin bincike ba ne, lokacin yaki ne, amma babu shakka bayan an kammala zan yi cikakken bincike, kuma duk wanda muka samu cewa ya taba fita da wannan littafi, to babu shakka za mu Kona shi da ransa. Ko wane ne.” Aljana Dailanu ta doddogara ta nufi bangarenta

don fara jiyyar raunukan da ta samu a lokacin azaba. ‘Tsohuwa Bakayalu ta juya ta fuskanci jikanta Sham'‘una tana mai tambayar sa, “Ka ce mene ne  sunayen jagororin yakin?”

Sham‘una ya ce, “Sunan dan Adam din Idrisu dan Hamidu, sannan sai Sarki Ifritu wanda muka taba yaki da shi har na sa shi a cikin battar Karfe, sannan na sa shi a tsakanin dutse. Na yi mamakin yadda aka yi ya kubuta shi da jama'‘arsa da ke daure a cikin sarKka.”

Bakayalu ta ce, “Sarki Ifritu dai da na sani kake magana?”

Sham‘una ya amsa, “EF, shi kaka.”

Sai Bakayalu ta nisa sannan ta ce, “Sarki Ifritu kuwa ka san in ba mu ba babu wanda ke ja da shi ya kwana lafiya a duk cikin aljanu, amma wannan karon

zan bayyana masa sharrina baki daya. Abin da nake —

Www.bankinhausanovels.com.ng so da kai yanzu shi ne ka je ka shirya dukkan mayakanka, ni kuma zan fara girka nawa.”

To yadda lamarin ya ke shi ne, ita wannan makirar tsohuwar aljana Bakayalu har rundunonin mayaka take da su na musamman, kuma wadannan zaratan mayaKan aljany ba sa aikin kowa babe sai nata, ta tsaface su da wani irin tsafi mai ban al'ajabi. Ga su nan launi daban-daban, akwai wasu mayu daga _ cikinsu wadanda ba su da abinci sai dai shan jinin aljanu, wasu kuma ga su nan bakake, wasu koraye, algashi, jajaye da sauran launuka gwargwadon abin da ita Bakayalun ta san dalilin da ya sa ta juyar da su haka. Miyagu ne, wanda daya daga cikinsu kawai in rana ta Baci zai iya karawa da jaruman aljanu dari biyar.

Shirin yaki ya kankama a bangaren Sarkin aljanu Sham'una, jarumai da dakaru dubban daruruwa kowanne sai Karaji ya ke yi don za a kara da abokan gaba, sannan kuma duk da haka sai da Sham'una ya sa masu yekuwa cewa su kewaya cikin duniya da wajenta, duk inda wani bakin aljani dan asalin yankin ya ke, to ya koma don kare gida.

Aljana Bakayalu kuma tuni ta shiga don fara girka wadancan mayun aljanu nata.

Amma lamarin aljana Dailanu kuwa bayan an kwance ta don yin jinya, kuma kasancewar ranar

Www.bankinhausanovels.com.ng Juma'a ce, washegari Asabar sai ta zame jikinta ta sulale ta nufi wurin kawayenta su Nur. Ta yi musu sallama suka amsa, suka rungume ta suna tambayar lafiya yau mako biyu ba su gan ta ba? Shi kuma Sarki Sham'una yau kwana takwas ke nan ba su gan shi ba?

Sai aljana Dailanu ta ce musu, “Ina fa lafiya, Idrisu dan Hamidu ya tunkaro, ya tayar wa da matsafa hankali, ai nesa ta zo kusa don kuwa a halin yanzu ya cinye birni na sha daya, yanzu saura birni na sha biyu wanda azzalumin karen aljanu Sham'una da muguwar kakarmu Bakayalu ke ciki.”

Ta Kara da ce musu, “Ai ni ma Allah ne Ya sa kwanana yana gaba, ba don haka ba da tuni shaidaniyar kakata ta babbaka ni.” Saitakware musu jikinta suka ga irin yadda aka tsattsaga shi a lokacin azaba.

Tace, “A kan littafin nan ne dana taba kawo muku, in ba ku manta ba har a wancan lokacin na ce kar ku kuskura ku taba shi da hannunku, har na rika bude muku shafukan da hannuna lokacin da kuke juyewa. To na yi haka ne don tsoron kada bincike ya tashi su ga fuskokinku, to binciken kuma ya taso, an ga tawa fuskar, ko da yake taimakon Allah Mai girma zuwa yanzu ba ta gama tantancewa ba tukuna, lallai da ba ku sake gani na ba, don da a ce ta gane da kuwa

Www.bankinhausanovels.com.ng ni za ta yi kamar yadda ta halaka mahaifina. Ba ni kadai ba, ku ma kanku da tuni muna can lahira tare. Amma in Allah Ya so kafin Bakayalu ta mutu sai na mayar mata da jawabi, muguwar kafira!” Ai fa nan ‘yan matan nan suka jajanta mata da kuma Kara karfafa mata guiwa, kafin su Balle da labaransu yadda suka saba, sai dai yau babu wasanni don ba ta jin dadin jikin. Cikin labaran da suke yi ne har take sanar da su cewa an yi karen batta a karon farko tsakanin jarumi Idrisu da Sarki Sham'una, har shi Sarkin aljanun ya dafe keya ya ranta~a-na-kare. Jin wannan labari sai murna da farin ciki suka cika , zukatan 'yan matan nan, suka fara tuna dangi da masoyansu tare da addu’o'in Allah Ya bai wa jarumi | Idrisu cikakkiya kuma tabbatacciyar nasara a kan Sarki Sham'una da kakarsa Bakayalu. Aljana Dailanu yau ba ta bari yamma ta yi ba sai ta  mike don sallama da Kawayenta. : Nur ta tambaya, “Yau da wuri za ki tafi haka?” Dailanu ta ce, “Kawata na san za ki fahimta, kin san  Kasa babu lafiya, kuma kin san akwai dan zargi a kaina, saboda haka ma dai ni ba za ku sake gani na ba sai abubuwa sun lafa tukuna, in Allah Ya so.”

ZUWA yanzu babu abin da ya fi damun jarumi Idrisu fiye da rashin lafiyar dokinsa Jagora. Kuma a dalilin halin da dokin ke

ciki ne tafiyarsu zuwa birni na sha biyu ba ta yi saurin gaske ba.

Tun da suka dunfaro wannan birni, shi kansa Idrisu da kuma wasu da yawa daga cikin aljanun da ke tawagarsu suka tabbatar da cewa ba su taba ganin birnin da ya fina Sham‘una kyau ba.

Tun daga nesa  cikin sararin samaniya za ka hango taswirar Sarki Sham‘una shi da kakarsa, wato masu gidan mulki. Kana kallon fuskar Bakayalu da ke cikin taswirar ka san sharri ya zauna daram da gindinsa a wurin. Dole ne ma gabanka ya fadi.

Akalla akwai aljanu dubu dari sau dari a cikin wannan birni na goma sha biyu na Sham‘una.

Kafin su jarumi Idrisu su kammala karasowa tuni labari ya isa, ashe da ma jirace ake da su, kuma da ma tsarin da aka shirya ke nan, ai sai kawai aka bude
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kofar birnin jarumai suka shiga fitowa kamar ba za su taba Karewa ba, tun daga nesa Sarki Ifritu ya lura da haka amma babu abin da ya ke shelantawa a cikin rundunarsa sai, “Kada gabanku ya fadi, Karfi da nasara suna wurin Allah ne ba yawa da Karfin jiki ba, kowaya natsar da hankalinsa.”

A haka har suka Karaso inda suka yi sansani don fuskantar Sham'una da jama'arsa wanda akalla wadanda suka fito zuwa yanzu ‘sun nunnunka yawansu kuma ci gaba da fitowa suke. ' anan

Jarumi Idrisu ya ba Sarki Ifritu shawara a kan cewa kada a jira sai sun gama fitowa don ba a ‘san irin shirinsu ba, ya ce, ‘Mu afka musu kawai, tun kafin jikin mayakanmu yayi ganyi.”

Haka kuwa aka yi, aka rufar wa mayakan Sarki Sham'una da sara da suka. Masu harbi na yi karfafa kuwa ba abin da suke yi sai karya wuyaye. -

Jarumi Idrisu, Sarkin aljanu ‘Tfritu da wancan saurayin jarumin kowanne ‘nasa gefe ya ja yana ta Ta  yankan aljanu kamar kubewa.  Sarkin aljanu Sham'una sai ya ga abin kamar a . mafarki a lokacin da ya fito fagen fama, zuciyarsa ta hasala matuka. A kan wata irin katuwar giwar aljanu ya ke, ya juya ya kealli irin yadda Idrisu mai takobi ke masa Barna, sannan sai ya waiwaya wancan bangaren

Www.bankinhausanovels.com.ng ai sai suka yi ido da ido shi da Sarki Ifritu yana ta kwankwatsa masa kan aljanu da gwalminsa, ai nan take ya nufi wurin Sarki Ifritu din da nufin bari ya fara da shi su yi ta ta Kare.

Suka fa fuskanci juna, Sarki Sham'una a kan giwa shi kuma Sarki Ifritu a kan doki. Abin da Sarki Ifritu ya fara yi kafin ma giwar Sarki Sham'una ta gama tsayawa sai ya dubi Kwaurinta ya buge da gwalmi, ai sai ta durkushe, kafin ta kai Kasa sai ya sake daga gwalmin ya dankara mata a kanta, nan ta fadi a mace, amma abinka da aljani kafin giwar ta kai Kasa

. Sham'una ya tashisama abinsa kamar tsuntsu.

Shi ma Sarki Ifritu sai ya tashi fir ya bi shi suka hade can sama. Ko kadan fadan nasu babu kyan gani, sai Kara kake ji kamar aradu ce ke faduwa, wannan shi ake cewa turnuku fadan iblisai, yaro bai gani ba balle ya raba. Can kuma sai suka dawo kasa aka ci gaba da fafatawa. Da ma Sarki Ifritu ya san karonsu da Sham‘una, shi ma kuma Sham'una ya san shi.

Wani irin mummunan bugu da Sarki Ifritu ya kai wa Sarki Sham'una da gwalminsa wannan karon an sami tangarda bai iya kaucewa ba, ai sai ga shia Kasa, amma abin mamaki ko a jikinsa, hasali ma sai ga shi ya mike yana dariya tare da kakkabe Kura.

Da Sarki Ifritu ya ga haka sai ya sake kai masa hari,

amma ina, ai da ma kowa ya san cewa Sarki Sham'una ba Karamin jarumi ba ne, ai nan take ya zame tare da yin wata irin tsawa mai tsananin firgitarwa, sai ga wata irin sarka mai tsananin tsawo da kauri caf kamar kiftawa da bismillah ta nannade  Sarki Ifritu ta yi sama da shi.

Tsawar da Sham'una ya yi ne ta janyo hankalin Idrisu da ke can yana zabge kan abokan gaba, Dubawar da zai yi sai ya ga Sarki Ifritu a daure ana yin sama da shi, kafin ka ce yaya aka yi haka jarumi Idrisu ya nufi Sham'una da sara, amma kasancewar tuni Sarkin aljanun ya rigaya ya tsorata da wannan takobi na Idrisu sai ya janye cikin dabara ya koma cikin mayaka yana mai ci gaba da fada.

Sham'una ya kamo wani farin aljani da hannunsa, ya dunkula hannunsa ya yi masa dundu, tafiyar wancan aljanin ke nan zuwa barzahu. Ya finciko wasu biyu ya gwara musu kai, ai sai ga kwakwalensua waje! Ashe haka kwakwalwar aljanu take?

Cikin wata dabarar kuma Sham'una ya zame daga wurin yakin ya nufi cikin gari ba tare da mayakansa sun fahimci ba ya fagen ba.
Shi kuwa jarumi Idrisu abin da ya yi shi ne sai ya

daga takobinsa ya sari gefen sarkar da ta daure Sarki  Ifritu, nan take ta warware, Ifritu ya tashi rike da —_

Www.bankinhausanovels.com.ng gwalminsa ya yi wa Idrisu wata irin jinjina irin tasu ta manyan mayaka, daga nan ko kallon juna ba su sake yi ba kowannensu ya juya ya rufar wa abokan gaba, abin dai babu kyan gani.

Shigar Sarki Sham'una cikin gari bai zame ko ina ba sai wurin kakarsa Bakayalu, yana zuwa sai ya zube a gabanta yana mai cewa, “Ni fa jarumin dan Adam din nan ina jin tsoron takobinsa, ina ganin kamar in aka yi rashin sa'a ya sauka a jikina zai iya yi mini Jahani.”

Jin wannan jawabi ya sa idanun Bakayalu suka yi jajawur kamar garwashin wuta, tana mayar da nunfashi da sauri-sauri, kuma da ta mayar da nunfashin sai ka ga ga wani irin hayaki mai dan karen doyi ya fito daga cikin hancinta. Ta ce, “Ya kai dana, ina zaton mugun takobin nan ne da shi kadai zai iya yi mana illa. Amma in tambaye ka, shin shi wannan jarumi yana rike da wani mashi?”

Sham'una ya ce, “A'a babu mashi a hannunsa. Ni dai ban gani ba.”

Bakayalu ta yi shiru ta tsunduma cikin kogin tunanin irin yadda wannan lamari ke nema ya shige mata duhu. Dalilin da ya sa dai Sham'una bai ga mashin Idrisu ba shi ne, shi wannan mashi yana da wani abin al'ajabi tattare da shi, wato jarumin kan iya

Www.bankinhausanovels.com.ng nade shi kamar damara ya daure a Kugunsa. In ba ka san yana da shi ba, to ba za ka taba cewa akwai ba.

Da aljana Bakayalu ta kammala tunaninta sai ta ce, “Wannan lamari bai kamata mu dauke shi da wasa ba, ya zama dole mu gaggauta halaka su don kada dan hakin da ka raina ya zo ya tsone maka idanu. Tashi ka koma filin yaki, ni kuma zan shiryo maka babban dauki nan da wasu kwanaki in na kammala girka dakaruna.”

Ta fara shirya sahu-sahu na mayaka. A jerin korayen aljanu akwai dubu dari biyu, Haka nan na bakake suduf, su ma akwai jarumai dubu dari biyu, Haka nan algashi da shudaye, kowanne dubu dari biyu ne, sai jerin karshe mai dauke da aljanu dari biyu, jajaye kamar jini. ,

Su wadannan aljanu jajaye mayu ne, duk aljaninda ka sani ba ya son ko haduwa da su. Miyagu ne masu tsananin Keta da ketare iyaka da kuma kasancewar babu wani makami da aka taba samun cewa ya taba kama su. Kai ita ma kanta Bakayalu ba don ita kanta shaidaniyar ba ce, to da wadannan jajayen aljanu sun gagare ta.

A fagen fama kuma ana can ana ta karawa, can sai aka nemi saurayin jarumin nan da ke cikin tawagar su Idrisu aka rasa, amma kasancewar yaki ake yi babu

Www.bankinhausanovels.com.ng damar dubawa ko bincikawa sai dai kawai Kakkarfan tunanin cewa watakila shi tasa ta Kare.

Yaki ya yi yaki, can sai aka ji wani irin diri wanda dole sai da aka dan tsahirta da yaki don ganin ko mene ne haka, ai sai aka ga saurayin jarumin nan da ba a san kowane ne ba tare da dubban daruruwa na aljanu tare da shi sun dira a fagen faman, suna zuwa sai jarumin nan ya yi wa jarumi Idrisu da Sarki Ifritu jinjina, su ma suka mayar masa, ai kafin a ankara sun auka wa abokan gaba da sara da suka, sai girbe musu kawuna kawai suke yi, abin sai wanda ya gani.

Labari ya riski Sarki Sham'una a daidai lokacin da ya dawo fagen fama, cewa abokan gaba fa sun sami tallafin mayaka masu yawa, ai sai hankalinsa ya sake tashi tare da ba da umurni ga jama’'arsa cewa a auka tare da yin yaki gaba daya.

Yanzu al'amari fa ya sake Kazancewa, Sarkin aljanu Sham'una a nasa bangaren sai murmushe aljanu ya ke yi kamar yana murmusar soyayyar gyada, babu ko Shakka ya isa Kasaitaccen jarumi, saboda sadaukantakarsa duk inda ya fuskanta sai a dare a ba shi wuri. Shi ne da kansa ya ke bi da gudu yana kamowa yana kashewa, amma ba dai a tarbe shi ba. A’a, Sarkin aljanu Sham'una ya wuce haka a wurin gama-garin aljanu.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Ran nan sai Karajin mazaje kake ji da hargowa, da ma ko fadan mutane ne yaya, ballantana kuma na aljanu har ma da manyan jaruman sarakuna irin Sham'una da Ifritu?

A takaice dai kwanaki ashirin da daya da aka yi ana ta gwabzawa kafin a rabu don hutawa da kuma sake shiri, kumaa cikin kwanakin nan daidai da rana daya Bangaren Sarkin aljanu Sham'una bai taba samun nasara baa kan daya bangaren. Tsananin yawansu ne kawai ya sa ba a saurin gane irin nasarar da ake samu a kansu, sai dai ko in an kwatanta yawan gawarwakin kowane bangare tukuna.

Bayan an dan natsa ana hutawa sai shi jarumin aljanin nan wanda har yanzu ba a san kowane ne ba ya zo wa Idrisu da wata irin riga da wando da takalmi ya ce masa, “Ya kai Idrisu amshi wadannan kaya ka saka a jikinka kafin a ci gaba da yaki.”

Jarumi Idrisu ya karba tare da tambaya, “To su kuma wadannan kaya mene ne labarinsu da kuma hikimar sanya su? Kai hasali ma kai kanka mene ne labarinka?”

Jarumin saurayi ya ce, “Ya kai Idrisu, labarina dai ka bar shi sai in Allah Ya taimake mu mun kammala yaki, amma labarin sutura da na ba ka shi ne, kaya ne na kare tartsatsi da kuma zafin wuta, don mu aljanuHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...