YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN


                  Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Idrisu ya amsa masa da cewa, “Baba wannan kada ka damu kanka, don in Allah Ya so matuKar dokina

Www.bankinhausanovels.com.ng Jagora yana tare da ni, to ba na tsoron nisan tafiya ko kuma wahalarta, kuma ma ina tabbatar maka da cewa in Allah Ya so tare da Sarkinku za mu yaki azzalumi Sham'una.”

Aka shirya gagarumar walima, aka ci aka sha, suka yi ta murna da raye-raye irin nasu na aljanu. Babu shakka Idrisu ya ji dadin wannan karramawa da aka yi masa.

Aka nuna masa dakin da zai sauka, saboda girman dakin gaba daya shi da Jagora suka shige, ko da yake zuwa yanzu ya fara daina mamaki game da irin aikin aljanu.

A haka, kuma cikin matukar jin dadi da farin ciki sai da ya kwana bakwai yana hutawa, jikinsa ya warware.

Daga nan sai ya sanar da Shehi Abdallah Limamin aljanu cewa shi fa yanzu ya yi harama yana bukatar wucewa, kuma ya gode game da dukkan irin tarba da kyautatawa da aka yi masa. Liman ya yi gayyar dumbin jama‘ar aljanu don yin rakiya ga wannan babban bako nasu.

Kwana uku suna tafiya tare da Idrisu, daga nan aka tsaya aka yi addu'o'in dacewa da nasara gare shi sannan suka yi sallama suka juya don komawa gida.

Yanzu aikin da ke gabansa shi ne hawa dutsen da


ZAMU TASHI 


aljanu suka rako shi karkashinsa, dutsen da ‘yan'uwansu ke daure a kai, wanda kuma aka ba shi labarin cewa ita ce kadai hanyar bi.

KWANA uku, ba dare ba rana, tafiya suke suna hawa kan wannan dutse har suka Kure hawansa. Babu shakka wannan doki Jagora ba irin sauran dawaki ba ne, kuma wannan ya Kara tabbatar da cewa yana tare da wasu martabobi na daban, don kuwa ya yi tafiyar da kakkarfan saurayin aljani zai yi a kwana bakwai cikin kwanaki uku kacal. Tabbas abin a yaba masa ne.

A kololuwar saman dutsen nan kuwa sai Idrisu ya ga abin da aka ba shi labari, ga aljanu nan fululu daddaure cikin wata irin muguwar sarka mai hakora wadda ba don aljanu ba ne, to dai ko babbar giwa ce aka yi mata dabaibayi da ita to sai dai wata ba ita ba.

Idrisu ya yi matukar tausaya musu irin ganiyar azabar da suke ciki, ga su nan daddaure tamau, ba su samun sararawa, sannan kuma suna cikin irin wannan hali tsawon shekaru masu yawa kamar yadda ya sami labari, kai lallai Sham'una ya isa babban mugu, kuma irin wannan ukuba ba don aljanu suna da tsawon rai ba ai da tuni sun dade da zama ‘yan gida a lahira.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Fushi nan take ya kama Idrisu, ya zare takobinsa, ya dubi wata mahada a jikin wannan Katuwar sarka ya yi mata wata irin sara wadda ta sa ta warwarewa tun daga farkonta har Karshe. Aljanun nan suka kubuta, cike da mamakin irin wannan baiwa ta Idrisu dan Hamidu.

Jarumi Idrisu ya ce musu, “Assalamu alaikum. Sannunku da juriya.”

Murna ta lulluBbe wadannan aljanu jin tabbacin cewa wannan dan Adam da ya zama sanadiyyar kuButarsu Musulmi ne. Nan da nan suka amsa.

Suka ce, “Da a ce dai mu ba Musulmi ba ne, to a irin abin da ka yi mana sai dai kawai mu fadi mu yi maka sujada, don hakan ne nuna makurar godiya, to amma Allah Ya san mun gode, kuma sai dai kawai mu yi maka addu'ar Allah Ya saka maka da alheri.”

Idrisu ya amsa cike da farin ciki, “Amin.”

Suka tambaye shi, “Kai kuwa a matsayinka na dan Adam, mene ne labarin zuwanka har wannan wuri?”

Idrisu ya amsa musu cewa, “Labarina akwai dan tsawo wanda ba zan iya faro muku daga farko ba, sai dai kawai abin sani ta garinku na biyo, kuma na sami labarinku ne a wurin shugabanku; Liman Abdallah.”

Dole Idrisu ya ya da zango a saman wannan dutse don wadannan aljanu su samu su dan warware. Www.bankinhausanovels.com.ng

cikin wadannan ‘yan kwanaki uku da suka yi suna hutawa ne ya ba su labarin dalilin fitowarsa da kuma inda ya nufa.

Idrisu ya tambaye su, “Shin za a iya samun wasu daga cikinku kuwa da za su iya kai ni karkashin teku, inda Sham'una ya tsare Sarki Ifritu?”

Ai nan fa wuri ya rude, kowa yana cewa shi ne zai kai shi.

Jarumi Idrisu ya ce, “To ku saurara, ina ganin abin da ya fi kamata yanzu shi ne sai a sami manyan jarumanku guda ashirin da biyar kawai, da su za mu yi wannan aiki, saura kuma duk sai a yi harama a lallaba a sauka Kasan dutse don ya fi rashin zafi, a jira mu can, a ci gaba da warwarewa tare da yi mana addu'ar nasara.”

A haka shawara ta daidaitu.

Sauran jama’ar aljanu suka fara haramar gangarawa, shi kuma Idrisu da wadannan jarumai ashirin da biyar sai suka nufi gabashin dutsen suka fara tafiya, a haka sai da suka kwana takwas kafin su kawo Karshe, a dalilin rashin cikakken kuzarin da ke tattare da aljanun.

Idrisu ya leKa ya ga ruwan nan ya tafi, ya kere sasannin samaniya ta kowace fuska. Abin dai gwanin ban al'ajabi.

Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka ce wa Idrisu, “Ya _ kai shugabanmu, a nahiyar nan kaf babu ruwan da ya kai wannan girma da zurfi, babu wanda ya san hakikanin iyakansa sai wanda Ya halitta shi wato Allah. A karkashinsa ne wancan katafaren dutse mai tsananin girma ya ke, wanda Sham‘'‘una ya tsaga tsakaninsa da wani tsafi irin na zamanin farko ya sa shugabanmu a ciki. Ko aljanu sun kai dubu nawa ba za su iya tsaga shi ba.”

Da Idrisu ya ji wannan bayani nasu sai ya ce, “In Allah Ya yarda mu ne za mu bude shi.”

Jin wannan sai wani masanin ilmin kimiyya daga cikin aljanun ya shiga dudduba saman dutsen da suke har sai da ya dace da wani wuri, ya kuwa je ya kama wurin ya hau shi da latsaww da Karfin tsiya har sai da wani irin abu mai kumfa da launin niwa ya rika fitowa, to wannan abu ne ya tattara ya gaggauraya da hannunsa ya fitar da wasu abubuwa ai sai ga abin ya koma kamar wani mayafi. Da ya kammala sai aljanun suka ce wa jarumi Idrisu ya rufe fuskarsa da kansa da shi. Shi wannan abu amfaninsa shi ne ko kwana nawa zai yi a cikin teku to ba zai rasa iskar

shaka ba, ruwa ba zai shiga cikin kunne ko hancinsa ba, kuma tangararan zai riKa ganin komai. Suka ce, “In ka shirya yanzun nan za mu yi

Www.bankinhausanovels.com.ng Kundumbala da kai cikin ruwa.”

Kafin nan sai da jarumin ya bukaci aljanu biyu su tsaya a waje tare da dokinsa, aka sami wani KakKarfa daga cikinsu ya goya Idrisu a bayansa ya afka cikin tekun nan, sauran ashirin da biyu suna biye.

Tun hantsi suke buga nutso, amma ba su isa tsororuwar dutsen ba sai misalin La‘asar sakaliya, sa'ar da suka ci ba Karkashinsa za su tafi ba, don duk saurinsu da sai sun yi kwana biyar ba dare ba rana kafin su kai.

Ganin irin wannan dutse ya sa Idrisu Kara ganin girman Ubangiji Mabuwayi Mai halitta tare da aikata yadda Ya so. Idrisu ya yi duba da kyau zuwa ga Kololuwar dutsen sai ko ya ga alamar kamar an taba tsaga shi biyu an mayar an hade. Ya tabbatar cewa lallai abin da suka fito nema ke nan.

Ya ce wa aljanun da ke biye da shi su dan ja baya. Shi kuma sai ya janyo mashinsa ya auna mahadar dutsen, sai ga mashin ya Kara tsawo da kauri, abin mamaki da ya tura ya danna kadan sai ga dutsen yana budawa. Sai ya umurci aljanun cewa su matso kusa don tallafar battar Karfen da Sarkinsu ke ciki, su kinkimo ta. Hakan kuwa aka yi.

Bayan kamar sa'a bakwai sai ga su a saman ruwa, daga nan sai suka tashi sama kamar tsuntsaye, suka
Www.bankinhausanovels.com.ng dire battar a saman dutsen da jarumi Idrisu ya bar dokinsa Jagora da aljanu biyu suna jira.

A jikin battar sai suka tarar da kwaduna guda goma sha biyu wadanda Sarki Sham'‘una ya kulle ta da su ya rike makullan a hannunsa. Idrisu ya sa takobinsa ya sassare kwadunan daya bayan daya, sannan ya kama bakin battar ya bude murfin.

Budewarsa ke da wuya sai ga wani irin hayaki launi biyu, ja da baki yana fita, ya yi sama can da nisa, har sai da ya kammnala fita gaba daya, daga nan kuma sai ya shiga saukowa Kasa, yana gama sauka sai ya Bace, can sai ga wani irin zabgegen Ifritu, gangarangan da shi cikin siffar aljanu a Kasa. Kai sai ka dauka wani tsauni ne. Yana fitowa sai ya ce, “Alhamdulillahi.”

Aljanun nan ashirin da biyar gaba dayansu suka yi masa wata irin gaisuwa wanda sai su suka san abin da take nufi, shi kuma Idrisu sai ya daga masa hannu da nufin gaisuwa. Sarki Ifritu ya tambayi mutanensa abin da ke faruwa har ya sami kubuta, su kuma cikin wani irin harshe nasu suka dan labarta masa labarin jarumi Idrisu.

Nan take sai Sarki Ifritu ya yi wata irin girgiza sai ga shi ya koma cikin siffar mutane, babu shakka daga ganin sa da irin kyakkyawan farin gemunsa ka ga alamar aljanin kirki, kuma duk da cewa ya yi sama da

Www.bankinhausanovels.com.ng shekara dari biyu a daure amma kuma fuskarsa cike take da annuri.

Ya kebe Idrisu suka yi wata irin ‘yar ganawa tare da tambayar sa labarinsa bayan ya yi masa godiya mai dumbin yawa irin yadda har ya yi tunanin taimaka masa haka, shi da jama'arsa.

Sarki Ifritu ya ce, “Ya kai Idrisu, yanzu ba zai yiwu ka wuce ba. Komawa za mu yi zuwa garina mu dan huta sannan mu yi shiri mu tunkari azzalumi Sham'una, kuma in Allah Ya so wannan karon sai buzun makiyin Allah.”

Da jarumi Idrisu ya ji abin da Sarki Ifritu ya ce sai bai yi musu ba, ya amince a kan su tafi din. Suka kama hanya suka sauka daga kan dutse, haba aljanun da ke jira a karkashin dutse sai murna da shewa ganin cewa Sarkinsu ya sami kubuta. Aka zabi aljanu guda dari suka zabura suka nufi gari don sanar da cewa ga su nan su dubu saba'in da dorin nan har da Sarki duk sun sami kubuta.

Lokacin da jarumi Idrisu da Sarki Ifritu da sauran jama’a suka isa kusa da gari sai suka tarar da jama'a babba da yaro, mace da namiji kai har da marasa lafiya duk an fito tarba. Aka dunguma cike da murna ana farin ciki da annashuwa har aka isa cikin gari.

"Yan'uwa suka ga ‘yan'uwansu, ‘ya'ya suka sadu da

Www.bankinhausanovels.com.ng iyayensu, haka nan mata suka ga mazajensu. In an ce za a misalta irin farin cikin da wadannan aljanu ke ciki, to wanda bai gani ba sai ya nemi karyata mutum kawai a banza.

Zangonsu na farko shi ne babban masallacin garin inda aka yi sallolin nafila don godiya ga Ubangiji, sannan Sarki ya wuce fada ya shiga wurin iyalinsa, shi kuma Idrisu da ma ya san masaukinsa.

Sai da aka yi mako uku ana zuwa gai da Sarki Ifritu.

Bayan an dan shakata, duk daurarrun da aka kwanto har ma da shi kansa Sarki kowa ya mayar da jikinsa ya murmure sai Sarki Ifritu ya sa aka yi yekuwa cewa yana son ganin mayaKansa gaba daya, suka taru a fada yana da jawabi.

Aka yi cincirindo, Sarki ya fara jawabi kamar haka, “Ya ku jama'‘ata, kun san cewa mun dade muna shan bakar wahalar azzalumin nan Sarki Sham'‘una, kuma mun dade muna bugawa da shi, har ma wasu lokuta kamar za mu sami alamar nasara a kansa, amma kuma alhamdulillahi, duk abin nan bai taba samun nasarar Karar da mu Karkaf ba, to wannan karon za mu fita, ko a mutu ne gaba daya ko kumaayi rai.

Ya ku jama'‘a, wannan shaidanin aljani, wato

Sham'una ya cika babban azzalumi. Zaluncin nasa

ma har ya wuce kan mu aljanu ya kai kan bil-Adama,

Www.bankinhausanovels.com.ng duk ya kame musu 'ya'ya mata ya kai can bayan duniya ya kulle. Don Allah ina zaluncin da ya fi wannan? Ko kuwa don ya ga ba su da Karfi ne kamar nasa?

Ko da yake mu ma aljanun in kun tuna shin wane Sham'una ya Kyale ne? Kuma ina Kara tambayarku, shin wane jinsi ko Kasa ta aljanu ne Sham'una bai yi wa barnaba? To da ma kamar yadda kuka sani mu kadai ne da kuma macizan aljanu muke tsone masa ido, muka zame masa alakakai, su kuma yanzu macizan aljanu ta su ta Kare, Allah Ya kawo halakarsu ta hannun wannan saurayin jarumi, dan Adam, Idrisu dan Hamidu. Wannan babu shakka ya yi musu daidai, don da ma su ma mugayen ne da suka dade suna zaluntar mutane da aljanu.”

Sarki Ifritu ya ci gaba da bayani cewa, “In har wani dan Adam daga can cikin duniya zai taso, ya fuskanci tare da shan wahalhalu iri-iri ba don komai ba sai don yakar azzalumin aljani, to mu kuwa me zai hana wannan ya zama Karin Karfafa guiwa a garemu na fuskanta tare da ragargaza wannan azzalumi?”

Jama'ar aljanu suka yi wata irin kabbara gaba daya wadda ke nuna sun yi matukar tsuma da jawabin da Sarki ke yi, har ma wasunsu cewa suke, “A fita yanzu kawai.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Sarki Ifritu ya ce, “Saboda haka ya ku jama’‘ata,

daga yau na ba ku wata shida a je a shirya sosai, a sake horo a game da batun dabarun yaki, saboda za mu je mu yi ta ta kare tsakanin mu da Sarki Sham'una. Ko mu, ko shi.

Ina kuma fata, kamar yadda muka saba rike sirri da amana, kada wani wanda ba cikinmu ya ke ba ya san cewa na kubuta ni da sauran jama'‘a daga Kangin da Sham'una ya saka mu, don kun san cewa hakan zai iya wargaza mana tsari.”

Bayan jawabin Sarki sai kowa ya koma nasa wuri, jarumai suka shiga tayar da Kwanji ana ta motsa jiki da sake sanin dabarun yaki, ko da yake da ma can ba ragwaye ba ne.

Sarki Ifritu kuma sai ya shiga tausar Idrisu a kan cewa lallai ya hakura har zuwa watanni shida tukuna ta yadda za a hadu gaba daya a tunkari Sarki Sham'una. Bayan doguwar tattaunawa da kuma girma da Idrisu ya ke gani na Sarki Ifritu dole ya amince cewa zai zauna din, ammaa kan sharadi daya, wato maganar Kara ilmi.

Sarki Ifritu ya ce, “Wannan ai mai sauki ne. Ga Limaminmu nan Shehi Abdallah, shahararren malami ne daga masana addinin Islama, saboda haka sai ka ci gaba da daukar karatu kawai. Ni ma da ma Www.bankinhausanovels.com.ng wurinsa nake dauka.”
Haka Idrisu ya ci gaba da daukar darasi, kuma lallai ya yi mamakin irin dumbin sani da kuma bayanin da ake ganewa da sauri na wannan Shehi na aljanu.

Duk yammaci Idrisu da Sarki Ifritu sukan fita wajen gari don ci gaba da gwajin yaki. In ka gan su suna gwabzawa sai ka rantse da Allah cewa fadan gaske ne. Idrisu ya Karu da wasu dabarun yaki masu yawan gaske musamman a irin karawa ta aljanu daga wurin Sarki Ifritu, shi kuma Sarki Ifritu ya Karu da wasu dabarun masu yawa wadanda a da bai sani ba a wurin jarumi Idrisu dan Hamidu.

Bayan sun gama nasu gwajin kuma sukan kewaya

filayen da aljanu ke samun horo suna Kara nuna musu wasu dabarun da kuma gyara a wuraren da ke da kuskure. WATANNI shida da aka diba sun cika. Kowa ya shirya, an tanadi duk abin da ake bukata don wannan karawa, jama'‘ar Sarki Ifritu wannan karon gaba daya suka fito, ba a bar kowa ba sai Kananan yara, mata da tsofaffi, aka tunkari babbar daular Jarirul Waki-waki ta Sarki Sham'‘una.

‘Ta waccan hanya da Idrisu ya kubuto da Sarki Ifritu dai suka sake komawa, wato kan dutse, don ita

Www.bankinhausanovels.com.ng kadai ce hanyar da za a iya bi in za a shiga yankin Sarki Sham'una. Haka suka yi ta tafiya kwana da kwanaki har suka iso Karshensa.

Sarki Itritu ya ba da shawara a kan cewa lallai ya kamata a tsaya a huta kwana biyu tukuna, a shawarta abin yi kafin a ci gaba da tafiya. Babu ko gardama aka yi hakan.

Bayan cikar kwanaki biyun sai aka yi addu'o'i masu dumbin yawa don neman dacewa da nasara, kowa ya sake dubawa da tabbatar da ingancin makaminsa. Shi Sarki Ifritu wani irin gwalmi gare shi na wani irin katafaren bakin Karfe, kai da ganin sa ka san daga shi sai aljanin da ya isa don irin girmansa. Shi wannan makami yana da wasu irin kusassari masu tsawo da tsini.

Ga dukkan alama kuma Sarki Ifritu ya yarda da gwalmin kuma yana matukar alfahari da shi. Har ma ya ke ba jarumi Idrisu labarin cewa, “Wato Idrisu shi wannan gwalmi nawa da kake gani, gadonsa na yi wurin mahaifina Sarkin aljanu Nagujungu, shi kuma ya gada a wurin nasa mahaifin, wato Sarkin aljanu Wourkilili. Sannan kuma ka san wani abu? Babu mai iya daga shi sai wanda ya gaje shi, wato kakana, mahaifina da kuma ni, kuma mu a wurinmu nauyinsa kamar na kowane makami ne kawai. In

Www.bankinhausanovels.com.ng kuwa har ba mu ba, kuma ana son daga shi, to akalla

sai an samo Karatan aljanu majiya Karfi guda ashirin sannan za su iya dauka, shi ma cikin tsananin wahalar nauyi.”

Idrisu ya ce masa, “Ka ga kuwa in na sa mashina zan iya daga shi.”

Jin haka sai Sarki Ifritu ya yi murmushi sannan ya ce masa, “To kai banda abinka Idrisu ai ba a gardama in abin da ake gardama a kansa yana kusa, bismillah, jarraba mu gani.”

Idrisu ya ciro mashinsa ya sa a Karkashin wannan gwalmi na Sarki Ifritu, tsakanin wasu kusassari, cak ya daga shi babu ko nishi. Mamaki ya rufe Sarki Ifritu don bai taba zaton yiwuwar haka ba, ya bude baki kawai yana kallo.

Daga karshe dai zancen da ya fito bakinsa shi ne, “Babu shakka akwai abin mamaki cikin lamarinka. Ya zama dole a rubuta labarinka ko don nan gaba masu sha'awar labarai su rika karantawa don hira, kuma abin da ya sa na ce don hira shi ne in zamani ya tsawaita wani sai ya yi zaton labarinka almara ce kawai don abubuwan da kake yi mamakinsu ya isa.”

Caraf Sarki Ifritu ya kai wa mashin Idrisu cafka don daga shi da kuma jinjinawa ya ji irin nauyinsa, amma ina, sai ya ji kamar ya shafa tsauni don

Www.bankinhausanovels.com.ng tsananin nauyi Sarki Ifritu ya ce, “Kai, Idrisu lallai al'amarinka sai dai a bar ka.”

Jarumi dan Hamidu ya ce, “Ranka ya dade yanzu ba lokacin a yabe ni ba ne, ka tuna fa cewa muna da babban aikia gabanmu.”

Sai Sarki Ifritu ya amsa masa da cewa, “Ai ina ganin kamar duk mun gama nazarin dabarun yaki. Karin bayani kawai shi ne yanzu a Kokarin tafiyar da muke yi zuwa daular Sham'una, za mu tashi sama dukkanmu kamar tsuntsaye. Wannan tafiya ta kai misalin kwanaki arba'in kafin mu shiga cikin Kasar Sarki Sham'una, amma ina fata ka fahimta a nan, da nace maka shiga cikin kasarsa ba wai ina nufin za mu je ainihin garin da ya ke zaune ba ne, a'a, ina nufin za mu tarar da gari na farko ne da ke karkashin mulkinsa, a takaice za mu yaki garuruwa akalla goma sha wani abu kafin mu riske shi.

Sai dai kuma babbar matsalar da nake zaton za ta kawo mana cikas in mun isa wurin nasa ita ce wata gunkinsu, wato wata kakar Sham'una din wadda ita

ce shugabar tsafinsu. Tsawon shekaru dubbai babu wanda ya taba ko iya yi mata rauni ballantana maganar samun nasaraa kanta da yaki.”

Da Idrisu ya ji maganar Sarki Ifritu sai ya ce, “Ya

Www.bankinhausanovels.com.ng kai wannan Sarki mai daraja, in dai don wannan tsohuwar mushrika ce, to ka bar ni da ita, ni ne zan kashe Bakayalu in Allah Ya yarda.”

Sarki Ifritu jin Idrisu ya ambaci har sunan wadda ya ke nufi ma sai ya dada tsinkewa da lamarinsa. Ya ce, “Ya kai Idrisu, yanzu zan sa aljanu biyar su dauke ka kai da Jagora mu tafi.”

Suna wannan magana sai Jagora ya yi wata ‘yar haniniya, ya kwanta a Kasa ya mike Kafafuwa. Idrisu ya fahimci cewa ishara ce wadda ke da dangantaka da ainihin abin da ke faruwa ko kuma maganar da ake yi a lokacin, saboda haka sai ya ce wa Sarki Ifritu, “Ran Sarki ya dade, ni da dokina ba mu bukatar a dauke mu, shi zan hau mu tafi.”

Sarki Ifritu ya ce, “Wannan daidai ne.”

Nan da nan jarumi Idrisu ya dora wa Jagora sirdi, shi kuma Sarki Ifritu ya umurci jarumansa, su misalin dubu dari biyar a kan cewa kowa ya yi haramar tashi sama. Idrisu da Sarki a gaba, sauran aljanu suna biye, aka tashi sama, Jagora yana taka iska kamar yana taka tsandaurin kasa, har ya fi sauran aljanu sauri, shi kansa Idrisu sai ya fara tunanin shin ko wannan doki nasa dokin aljanu ne? Haka shi ma Sarki Ifritu ya ke tunani.

Tafiyar wannan gagarumar runduna ta su Sarkin

Www.bankinhausanovels.com.ng aljanu Ifritu da jarumi Idrisu a sararin samaniya, da a ce mutum zai ji rurinsu, to babu shakka zai hakikance cewa duniya ce za ta tashi.

Wannan runduna ba ta bata wani lokaci ko kuma wani hutawa ba saukarsu gari na farko sai suka yi fata-fata da shi. A irin wannan karon ma ko damuwa da kama aljanu ba su yi ba, kisa kawai suka yi ta aiwatarwa, kuma ba su kyale duk wani kakkarfan aljani ba. “Yan kadan da suka tsira suka ruga zuwa gari na biyu suka sanar da su irin bala’in da ke tafe.

Aljanun gari na biyu suka shirya cikin gaggawa suka fito don tunkarar abokan gaba. Kwana biyu kawai ana gwabzawa aka ragargaji wannan gari, masu tserewa suka tsere.

Abin da kawai wannan runduna ta Idrisu da Sarki Ifritu ba sa tabawa shi ne basa kashe Kananan yara da tsofaffin aljanu, wato sabanin Sarki Sham'una wanda in yana yakar wata kasa, shi har jarirai ya ke halakawa.

Kai kafin dai wasu kwanaki an lankwame garuruwan Sarki Sham'una har guda tara, wanda hakan ya sa babu makawa Sarki Sham'una ya sami labari, don a Ka'ida, masu kwatankwacin mukamin hakimai da dagatan da Sham'una ya nada don jagoranci a wadannan garuruwa dole ne sai sun yi


HMMM ASHA RUWA A KOMA AIKI LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...