YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN                    Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Da suka ga haka, sai suka fara rikidewa suna komawa wasu irin macizai, iri-iri, launi dabandaban, jajaye da farare, algashi da masu dabbaredabbare, kai wasu ma har da dan kunne. Wasu manya kamar girman giwaye, wasu kuma Kanana. Wasu na kukan jaki wasu suna haniniyar doki, kai wasu har tashi sama suke yi suna sauka.

Lura da haka sai Idrisu ya zaro takobinsa daga kubensa, kuma wani abin mamaki shi ne takobin na fitowa sai kawai bakunansa suka koma goma sha biyu, kuma dogaye masu tsawon gaske.

Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka fara kai masa hari, amma da zarar ya kai sara sai ka ga aljanun macizan nan suna ta fadowa kasa kamar fari, kafin wani dan lokaci ya kashe duk macizan da ke shawagi a kansa da kuma wani kaso mai yawa daga cikin wadanda ke Kasa. Sauran sai suka raba junansu kashi-kashi, koraye daban, jajaye daban, tika-tiKka daban, haka nan sirara, ga su nan dai kowanne sun ware gefe. A haka kungiya-kungiya suka shiga kai wa Idrisu da dokinsa farmaki. Tsartuwar dafi kake ji babu KakkKautawa har sai da suka jike su shi da dokinsa sharkaf, amma wannan babu tasirin da ya yi musu don tun a tsibirin dodo jikin Idrisu da dokinsa sun zama babu dafin da zai iya tasiri a kansu.

Cikin wani dan KanKanin lokaci sai ga Idrisu ya gama da wani kashi da ya fado masa. Ganin haka sai wadannan aljanu suka tunzura suka koma cikin mummunar siffa irin tasu ta aljanu suka nufo shi gaba daya, shi ma sai ya yi fushi ya kara kaimi wurin sara da suka. Babu ko tsoro ko razana haka ya ke ta yi, sai dai ka ga ya matsa gaba, ya ja baya ya buda Kafafuwa ya yi wani irin juyi ya tunkari wadanda suka nufo bayansa kafin sauran su gyagije ya sake juyowa kansu, kai fada da dan Hamidu ba dai gaba da gaba ba, kai ko ta bayan ma sai an shirya.

ZAMU TASHI 

Yaki ya yi yaki, ba ka jin komai sai Karajin aljanu, wuta kuwa sai faman tashi take ta yi kamar walkiya, aljanun nan idan suka buga suka buga sai su kara tsawo don su bai wa Idrisu tsoro, amma ina? Ba ruwan jarumi da tsoro, duk lokacin da suka Kara tsawo suka kere shi sai shi ma dokinsa Jagora ya Kara wani irin tsayi da fadi don daidaita da sabon matsayinsu yadda za a ji dadin bugawa.

Kwana biyu ana gwabzawa kafin jarumi Idrisu ya sami nasara a kan wannan jama’a ta aljanu, ya karkashe su ya yi musu fata-fata da runduna. 'Yan sauran wadanda suka rage; ba su wuce ashirin ba, da suka ga ba za su iya ba, sai suka tashi fir kamar tsuntsaye suka fantsama cikin duniya.

Idrisu ya yi wa Allah godiya sannan ya karasa zuwa wurin wani karamin kogi ya wanke dokinsa Jagora, shi ma ya wanke jikinsa, ya yi alwala ya gabatar da ibada sannan ya zauna yana cin abinci tare da hutawa yana mai kara yi wa Allah godiya. -

Cikin wannan hutun da ya ke yi ne sai kuma tunanin soyayya ya shige shi. Ya rika tuna yarinya mai dumbin kyau da hankali, wato Nur ‘yar Ibrahim, yana tuna irin cikar halittarta, muryarta da irin kalamanta masu cike da hikima. Nan da nan ya sa hannu a cikin burgamensa ya janyo taswirar da ta ba

Www.bankinhausanovels.com.ng shi ya shiga kallo yana Kara tsunduma cikin kogin so. Idrisu ya shiga tunani a cikin zuciyarsa cewa, “Lallai hutu bai gan ni ba, akwai aiki a gaban maza.” Zumbur ya tashi ya dora wa Jagora sirdi yana mai yi masa magana cewa, “Jagora ba mu ga ta zama ba.”
yA ci gaba da tafiyarsa, har dai ya iso Kofar wani babban gari, shi ma na aljanu. Bai tsaya wani Bata lokaci ba ya kutsa kai.

Abin da ya ba shi mamaki shi ne shigarsa ke da wuya sai ya fahimci cewa mafi yawan aljanun da ke garin suna da wata irin kyakkyawar siffa, kuma mafi yawancinsu suna sanye da fararen tufafi ne, wasu har da rawuna a kawunansu, sun kuma yi gungu a gefe daya suna ta gabatar da Sallar jam'i. Wannan, babu shakka ya yi matukar burge jarumi Idrisu tare kuma da cika shi da farin ciki.

Bayan sun idar sai ya yi musu sallama, suka amsa masa.

Ya ce, “Don Allah jama'a ni bako ne, matafiyi, ina so ne in kun amince in dan huta a wannan gari naku kafin in wuce.”

Suka ce, “A'a ko kadan babu matsala, ai kamar ka zo gida ne, amma don Allah mu tambaye ka kai mutum ne ko kuwa aljani>”
Idrisu ya amsa, “Babu shakka ni mutum ne dan Adam.”

Sai mamaki ya rufe su, yadda za a ce wai mutum ne ya biyo ta wannan hanya ya shigo garinsu lafiya. Hanyar da ko aljani ya biyo ta, to lallai ya isa a nuna shi a matsayin mai tsananin tsawon kwana. Abu na biyu shi ne irin yadda da kuma wanda ya wanke idanunsa ta yadda rangadadau yake iya ganin aljanu, ba su iya Boye masa.

Aljanun nan suka ce, “Ya kai bawan Allah, abin da zaa yi shi ne yanzu za mu je mu gabatar da kai zuwa ga shugabanmu, kuma abin da ya ce da shi za a yi aiki.”

Idrisu ya amsa musu cewa, “Wannan kuma daidai ne.”

Suka wuce gaba yana biye har tsakiyar gari, suka umurce shi da ya jira.

Suka shiga wurin shugabansu, suka sanar da shi cewa ga wani matafiyi nan dan Adam, Musulmi, kuma ya shigo cikin aminci ne ba sharri ba, yana bukatar masauki kafin ya wuce.

Aka ba da umurnin shiga da shi.

Shigar Idrisu sai mamaki ya kama shi, don tun daga Kofa har zuwa inda kujerar Sarki take askarawa ne aka jera dama da hagu sun tafi reras gwanin ban

Www.bankinhausanovels.com.ng a. Sai da ya yi tafiya mai dan tsayi kafin ya iso wurin shugaban.

Akwai manyan kujerun alfarma, daya babba daya kuma Karama. Shi wannan shugaba da Idrisu ya tarar yana zaune ne a kan Karamar kujerar.

Idrisu ya yi sallama aka amsa, aka ba shi umurnin zama a kan wata kujera ta azurfa da ke nan gefe. Ya gai da wannan shugaba na aljanu da gaisuwa irin wadda ake yi wa manyan sarakunan duniya, shi

kuma ya amsa cike da murmushi, farin ciki da jin dadi, kuma ya fahimci cewa lallai Idrisu saurayi ne mai mutunci wanda ya san darajar na gaba. Dattijon aljani ya ce, “Ya kai wannan saurayi dan Adam mene ne labarinka? Mene ne labarin tafiyarka? ‘Wane aljani ya zo da kai nan? Don kuwa in ba dauko ka aka yi aka tashi da kai sama ba, to babu yadda zaa yi ka biyo wannan hanya guda daya tilo da muke da ita ta wannan fuskar. Dalili kuwa shi ne akwai wasu bakaken aljanu masu zama macizai, miyagu ne wadanda duk Kasashen aljanu an san irin muguntarsu da yadda ba su barin ko kuda ya ratsa ta inda suke face sai sun halaka shi, ballantana dan Adam. Kai ko Sarkin aljanu Sham'una yana sane da irin sharrinsu. Ya kai saurayi, da a ce ta wannan hanya ka biyo, to

Www.bankinhausanovels.com.ng babu shakka zan ce ka shigo ta cikin wani kogo wanda shi ne kamar katanga da ke tsakanin Kasashenku na mutane da namu na aljanu. Ko kuma tsakanin cikin duniya da wajenta.

Kuma dai ya kai wannan saurayi, da a ce ta wannan hanya da nake magana ka biyo, to babu makawa ka ga wata babbar gona wadda ciyawa ta tafi Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, to asali gonarmu ce, kuma duk yankin wurin garinmu ne wanda muka gada shekaru dubbai da suka wuce amma wadancan bakaken aljanu suka yi mana fin Karfi suka kwace. Kuma saboda yawan zalunci da kisan da suke yi mana ne muka lallaba muka matso nan muka kafa wannan gari.

Yanzu ma da ka gan mu nan albarkacin addu'o'i ne muke ci, Allah Ya shafa mana lafiya Ya kiyaye mu, ba don haka ba da tuni wadancan miyagu kuma bakaken aljanu ko kuma wannan la'anannen Sarkin aljanu Sham'una sun gama da mu.”

Da Idrisu ya ji jawabin wannan dattijo sai murna ta fara kama shi don ya fara shiga wurin da ya ji ana ambaton sunan Sarkin aljanu Sham'una sosai, wato ya fara kusantar Kasarsa ke nan. Sai ya ce, “Ya kai wannan dattijo mai daraja, ni sunana Idrisu dan Hamidu. Wannan hanya kuma da kake magana ta

Www.bankinhausanovels.com.ng cikinta na biyo, hasali ma ita wannan gona taku sai da na share kusan sa‘o'i bakwai cikinta kafin na ci gaba da tafiyata.

Babu shakka wadancan miyagun aljanu da kake magana na ci karo dasu, kuma daga yau din nan kada ku sake tayar wa da kanku hankali don kuwa Allah cikin ikonSa Ya ba ni nasara a kansu, duk na halaka su, in banda in ban manta ba...  na kirga su lokacin da suke guduwa, su goma sha takwas kawai. Suka rage wadanda suka gudu

Kuma kamar yadda aka sanar da kai ne cewa ni matafiyi ne. Babban burina ko kuma ince abin da ya biyo da ni nan shi ne don in je in yaki wannan azzalumin Sarkin aljanun da ka ambaci sunansa yanzu, wato Sham'‘una, in Allah Ya yarda, kuma ina fata Allah Zai ba ni nasaraa kan haka.” .

Da dattijon aljanu ya ji bayanin Idrisu ko kadan bai Karyata ba, sai ya ce masa, “Yo .fa Sai dai kuma tsugune ba ta Kare ba tsakaninka da wadancan bakaken aljanu da ka kashe, don kuwa jikoki ne da tattaba-kunne na wasu bakaken kafiran aljanu marasa imani wadanda ba su da wani abinci sai jini da naman dan Adam, kai hasali ma wannan dalili ne ya sa suka Ki zama cikin aljanu ‘yan'’uwansu suka koma garin wata Sarauniya 'yar Adam suka hada guiwa da ita don cin ma burinsu. Ina tabbatar maka

Www.bankinhausanovels.com.ng ko kadan ba za su Kyale wannan ya tafi a banza ba, wato sai ka daura damarar karawa da su, kuma duk aljanin da ka san ya kwana duniya ya san cewa su ba kanwar-lasa ba ne wurin jarunta.

Ka ga yanzu zuwan ka nan ka shafa mana kashin kaji ke nan, don na tabbata yanzu suna nan suna shirin neman ka, in ma ba su fito din ba ke nan. Sai dai kuma Allah Ya kiyaye mu da kariyarSa!

Da Idrisu ya ji zancen dattijo sai ya ce, “Ya shugabana, ina so ka kwantar da hankalinka, kuma ka saki jikinka. Dalilina kuwa shi ne, su wadancan miyagun aljanu, wato kakannin bakaken da aka kashe, to ta kansu na fara, yanzu maganar da ake yi ko tokar su babu. Su ma Allah Ya sa mun yi nasara a kansu har ita Sarauniyar. Su ne suka cinye ta, ni kuma takobina ya cinye su.”

Dattijon aljani ya bude baki yana mamaki, “Yanzu takobinka ya kama jikinsu?”

Idrisu ya ce, “Kwarai kuwa Allah Ya taimake ka.”

Sai aljani ya ce, “Lallai akwai mamaki cikin lamarinka, ina kyautata zaton addu'o'in da ake ta yi ne Allah Ya amsa a kanka. Saboda haka muna fata Allah Ya taimake ka, Ya kuma ci gaba da kiyaye ka. Allah Ya dora kaa kan Sham'una.”

Idrisu ya amsa, “Amin.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Dattijo shugaban aljanu ya ci gaba da bayanin cewa,

“Ya kai Idrisu, na tabbata tun da ka biyo ta cikin

kogon dutsen nan ka fito lafiya, kuma har ka kashe

aljanun nan biyu su da jikokinsu kuma ko kwarzane

ba ka yi ba, to babu shakka za ka iya karawa da Sham'una.

Ina son sanar da-kai labarinmu ya kai jarumi. Ka ga wannan babbar kujera wadda ta fi wadda nake kai girma? To ita ce ta Sarkinmu.

Shi wannan Sarki namu na ifritai yana da mulki, kuma ga shi jarumi mai yawan dabarun yaki, sau da yawa aljanu kan kawo masa hari amma sai ya tarwatsa su.

Mu aljanun wannan gari muna da wata al'ada, ba mu da sarautar da ake kira Waziri, a'a Limamin gari shi ne Waziri kuma Alkalin gari. In Sarki ba ya nan kuma shi ne a matsayin Sarki kamar yadda ka gan ni yanzu haka nan. Sunana Abdallah, kuma sunan wannan daula ta mu Yaminul-Ausad.

Sai Idrisu ya tambaya, “To shi Sarkin naku ina ya ke?”

Sai Limamin aljanu Abdallah ya amsa da cewa, “Abin da ya faru ya kai Idrisu shi ne, mu dai aljanun wannan gari muna matukar son zaman lafiya, babu abin da muka fi so fiye da shiga cikin duniya neman

Www.bankinhausanovels.com.ng abinci, sai kuma neman ilmi da bautar Allah da yabon shugabanmu Annabi Muhammadu tsira da amincisu tabbata a gare shi.

Sauran aljanu makwabtanmu babu abin da ya fi bakanta musu rai game da mu sai don tafarkin da muke bi na addinin Islama, su bukatarsu ita ce mu zama kafirai kamar su mu rika bauta wa tarkace kamar yadda suke yi, amma kuma a kowane lokaci sai mu riKa nuna musu cewa haka ba zai taba yiwuwa bain Allah Ya so.

Bangarori biyu ne suka fi tsananta mana, Bangaren farko shi ne na wadancan macizan aljanu, har ma suka kore mu daga garinmu na ainihi, sai kuma daya sashen wanda Sarki Sham'una ke yi wa mulki, wato daular Jarirul Waki-waki wadda take da manyan birane har guda goma sha biyu.

Bayan wadancan aljanu sun kore mu daga birninmu mun dawo nan, sai jama'ar Sham'‘una suka shiga tsananta mana, kullum sai kashe mana jama’‘a suke yi suna yi wa’ya'yanmu mata fyade.

Da tura ta kai bango sai shugabanmu Sarki Ifritu ya tara jama'a aka tsayar da shawara a kan cewa dole ne mu yaki Sarki Sham'‘una don mu kare kanmu, in kuwa ba haka ba, to da dai-dai da dai-dai za su yi ta halaka mu.

Www.bankinhausanovels.com.ng Muka yi shirin yaki tsaf muna jiran zuwan dalili. Can kuwa bayan wasu ‘yan kwanaki sai ga wasu katti daga bangaren Sham'una su ashirin sun shigo har cikin gari suka kama mana ‘yan mata goma suka lalata. To da labari ya zo, ai ba mu bari sun bar garin ba, aka tare su aka yi musu lugude, aka yi kaca-kaca da su, da Kyar biyu suka kai labari.

Ashe shi maSham'una Kiris ya ke jira, saboda haka sai ya turo runduna, amma ko labari ba su kai ba, mun aika da su inda ba a dawowa, ya sake turo wasu mayakan su ma ba su kai ba. A haka sai da ya turo rundunoni biyar muna halaka su.

Dalilin haka shi da kansa Sarki Sham'unan ya shiryo gagarumin yaki ya tunkaro mu, muka fita aka fara gwabzawa.

An dauki tsawon kwanaki ana karawa, kuma a kullum sai Sham'una da shugabanmu sun buga. Babu shakka a tarihin yakukuwan aljanu, Sham'una bai taba samun jarumin Sarki kamar Sarki Ifritu ba; Sarkinmu.

Kuma yawan jarumai da dakarun Sarkin aljanu Sham‘'una dubban daruruwa ne kan dubban daruruwa in ka misalta da yawan jama'armu, saboda haka nan da nan suka ci Karfinmu, suka kashe mana jama‘a da yawa kuma suka kama da yawa. Mu sauran

Www.bankinhausanovels.com.ng da muka rage sai Sarkinmu ya umurce mu da janyewa zuwa cikin gari. A Ka'ida ba ma jayayya da Sarki, saboda haka sai muka fara Kokarin janyewa din, a gajiye.

Sarki Sham‘una ya ba da umurnin cewa a bi mua kashe na kashewa a kama na kamawa, amma sai Sarki Ifritu ya yi wata irin tsawa mai tsananin firgitarwa, wuri ya yi tsit. Ya ce shi ya ba da kansa don a Kyale jama'arsa kada a bi su, ya zubar da makamansa, aka kuwa zuba masa ankwa shi da jama'ar da ke tare da shi a lokacin, su dubu saba'in da uku.

Shi Sarkinmu sai aka saka shi a cikin wata Katuwar batta ta bakin karfe. Akwai wani dutse a can cikin tekun Tsagirgi, shi ne Sham'una ya tsaga shi biyu ya sa wannan batta ya mayar da dutsen ya hade. Wannan bayani mun same shi ne daga majiya mai tushe, hasali ma har izgili mutanen Sham'una ke yi mana in suna fada mana inda Sarkinmu ya ke.

Su kuma sauran jama'armu da aka kama sai aka kai su saman wani babban dutse da ke gefen tekun aka kulle aka ba Sham'‘una makullan yana rike da su a hannunsa.

Da wancan dutse da aka saka Sarkinmu da kuma sarkokin da aka daure ‘'yan'uwanmu ba wanda zai iya

Www.bankinhausanovels.com.ng bude su sai Sarki Sham'una.

Kuma ya kai Idrisu, shi wannan dutse da 'yan‘uwanmu ke daure a kai ta nan ne ma hanyarka, za ka gan su da idanunka.”

Liman ya ci gaba da labarta cewa, “Shi wannan dutse ya kai Idrisu ya tafi a kwance ne, in ka fara hawa a hankali za ka ga kamar kana hawa sama ne. Kafin ka kai Karshen samansa za ka dauki misalin watanni masu yawa a tafiya irin taku ta mutane, amma in aljani ne, kakkarfan saurayi zai kai cikin kwana bakwai.

Babban abin da nake son jawo hankalinka a nan shi ne ita tafiya a cikin Kasashenmu na aljanu, to ko a wurin aljanin ma ba ta da sauri sabanin yadda muke da tsananin sauri a cikin Kasashenku na mutane, sai dai ko in aljani na da waniirin shiri ne na musamman, shi ne za ka ga ko a cikin Kasashen namu yana sauri kamar walkiya, wanda kuma samun irin wannan sai an tona.”

Limamin aljanu Abdallah ya ci gaba da yi wa jarumi Idrisu bayani cewa, “In ka Kure saman dutsen, to za ka ga fadinsa ya tafi ta kowane bangare, har ma ka dauka cewa ba a kan dutse kake ba. In kana son Ketare shi da sauri, to ka bi ta fuskar Gabas, wanda akan yi tafiyar kwana bakwai kawai.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Karshen wannan dutse ne za ka ga wani ruwa baki Kirin ya tafi iyaka ganinka, to a ciki ne Sham'una ya tsaga dutsen da ke cikin sa ya sa Sarkinmu.

Wannan shi ne labarinmu ya kai Idrisu.”
Bayan Idrisu ya kammala jin wannan labari daga bakin Limamin aljanu har ma da taimako a game da siffanta masa irin hanyar da zai bi sai murna da farin ciki suka kama shi, musamman ma da ya ji cewa yana wurin da labarin Sham'una sananne ne, wato yanzu ya Kara tabbatar da cewa lallai ya kama hanyar haduwa da shi.

Sai Idrisu ya ce wa Liman, “Ya kai wannan dattijo mai dumbin daraja, ina so ka kwantar da hankalinka, kuma ka sani cewa in Allah Ya yarda shekarar jin kunyar Sham'una ta tsaya, tura ta kusa kaiwa bango, kuma da yardar Allah Sarkinku ya kusa fitowa daga Kangi.”

Dattijo ya ce, “Ya kai Idrisu abin da nake yi maka tunani shi ne hawa dutsen nan, kuma bayan hawa dutse sai maganar shiga cikin kasar Sham'una, wanda ba abu ne mai sauki ba ko da ga aljanun da ke tashi, balle dan Adam. Da ma ace Sarki Ifritu na nan ne, to babu shakka da ya taimaka maka.”

Idrisu ya amsa masa da cewa, “Baba wannan kada ka damu kanka, don in Allah Ya so matuKar dokina

Www.bankinhausanovels.com.ng Jagora yana tare da ni, to ba na tsoron nisan tafiya ko kuma wahalarta, kuma ma ina tabbatar maka da cewa in Allah Ya so tare da Sarkinku za mu yaki azzalumi Sham'una.”

Aka shirya gagarumar walima, aka ci aka sha, suka yi ta murna da raye-raye irin nasu na aljanu. Babu shakka Idrisu ya ji dadin wannan karramawa da aka yi masa.

Aka nuna masa dakin da zai sauka, saboda girman dakin gaba daya shi da Jagora suka shige, ko da yake zuwa yanzu ya fara daina mamaki game da irin aikin aljanu.

A haka, kuma cikin matukar jin dadi da farin ciki sai da ya kwana bakwai yana hutawa, jikinsa ya warware.

Daga nan sai ya sanar da Shehi Abdallah Limamin aljanu cewa shi fa yanzu ya yi harama yana bukatar wucewa, kuma ya gode game da dukkan irin tarba da kyautatawa da aka yi masa. Liman ya yi gayyar dumbin jama‘ar aljanu don yin rakiya ga wannan babban bako nasu.

Kwana uku suna tafiya tare da Idrisu, daga nan aka tsaya aka yi addu'o'in dacewa da nasara gare shi sannan suka yi sallama suka juya don komawa gida.

Yanzu aikin da ke gabansa shi ne hawa dutsen daHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...