YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN                Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Shi dai bai ga mai magana ba, alhali kuwa ga dadin maganar ya daki dodon kunnensa, sannan kuma ga Kanshin turare yana ta zagaye hancinsa yana kaiwa zuwa ga zuciya da kwakwalwarsa, sai ya ce, “Ya mai wannan magana mai dadi, na dai san cewa mace ce,

Www.bankinhausanovels.com.ng kuma na san na taba jin muryar, saboda haka in dai babu yaudara, to ya kamata a fito fili. In kuma an Ki, to babu ko shakka ni zan ci gaba da tafiyata don na zaku da ganin abin da ya fito da ni.”

Shiru kake ji.

Idrisu ya mike zai tafi, sai ya ga an dan daga labule, sai ga wata yarinya wadda duk wanda ya ce zai siffanta hakikanin kyanta, to babu ko shakka zai zalunce ta ta hanyar rage ambaton wani abin.

Suna hada ido sai gaban Idrisu ya fadi, kuma babu abin da ya fado masa a cikin zuciya sai kamannin yarinya Nur da ya taba hangowa daga nesa. Yana Kokarin tantancewa shin ashe a duniyar nan akwai kyakkyawar da za a iya hadawa da Nur su yi daidai? Ko kuwa yarinya Nur tagwaye ne? A'‘a ai malaminsa bai taba fada masa haka ba.

‘To idan ko wannan yarinya da ke tsaye a gabansa Nur ce, to ya aka yi ta zo nan? Kuma me ya faru da Sarkin aljanu Sham'una? Ko kuwa wani tarkon ne aka dana masa?

Idrisu ya ce,  ke kuwa yarinya don Allah ke aljana ce ko kuwa mutum? Mene ne labarinki? Yaya aka yi kamarki ta yi daidai da Nur? Kuma yaya turarenki ya yi daidai da nata? Yaya aka yi kika san sunana? Abin da ya sa nake yin wadannan tambayoyi

ZAMU TASHI 


shi ne don yanzu yaudara ta yi yawa.”

Bayan kyakkyawar yarinya ta ji zancen Idrisu sai ta yi murmushi, kyanta ya Kara bayyana, hasken hakoranta ya fizgi wani sashe na hankalinsa, sannan ta ce, “Haba, ya kai masoyina Idrisu dan Hamidu, babu shakka na yi matukar murna da jin dadin cewa har yanzu kana nan kan bakanka na soyayyar Nur.

Ya kai Idrisu babu yaudara, Nur ‘yar Ibrahim ce a gabanka.

Na san za ka yi mamakin yadda ka gan ni yanzu a wannan daji, sai dai kuma in ba ka manta labarin da mahaifina malaminka ya ba ka ba cewa yau Asabar ranar bauta ce a wurin su Sarkin aljanu Sham'una, wanda kuma ba ya zuwa ko ina a ranar. Kuma ai ka san labarin aljana Dailanu wadda ke ta koKarin kaiwa da komowa tsakaninmu ko?

To wai ma in tambaye ka, ina adikona da na taba jefo maka? Ko kuwa in rera maka wakar da na taba shirya maka ne lokacin kana wancan Kungurmin dajin kana daukar karatu?”

Ai nan da nan sai ta rero wasu baituka guda biyu, za ta fara na uku ke nan sai Idrisu ya daka wani irin tsalle cike da murna, don yanzu ya sakankance babu yaudara cewa wannan yarinya da ke gabansa masoyiyarsa ce; yarinya Nur ‘yar babban Shehi

Www.bankinhausanovels.com.ng Ibrahim.

A rayuwar Idrisu wannan ne karo na farko da ya taba magana da ita fuska da fuska, baki da baki, kunne da kunne. Duk sadarwar da ke tsakanin su gabani a takarda ce kawai, sai dai kuma kallon ta da ya taba yi daga nesa.

Idrisu ya ce, “Har yanzu dai ina da bukatar sanin labarin zuwanki nan.”

Nur ta amsa masa cewa, “Ya kai rabin rayuwata, kamar yadda na fada maka ne cewa yau Asabar, wato ranar bautar su Sham'una, a duk irin wannan rana ba ya zuwa wurinmu, shi ya sa na saci fage kawata Dailanu ta dauko ni.

Mun kintata isowarka nan cikin wannan dan tsakanin, shi ya sa muka tareka. Kuma ka san wani abu? Tun ranar da Sarkin aljanu ya sace ni ban taba irin wannan fitowa ba sai yau.

Kuma a yau ya kamata ka san Kawata aljana Dailanu. Ka dai san irin kokarin da take ta yi, kuma duk inda kake, to takan kewayo ka har muke samun labarinka. Na manta ma ban tambaye ka labarin gwagwarmayarka da Sarauniya ba.”

Idrisu ya ce, “Ke! Ai wannan Sarauniya shaidaniya ce; babba kuwa, amma mun gode wa Allah tun da har aka sami nasara a kanta da abubuwan bautarta.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Sai yarinya Nur ta yi kira, “Dailanu... Dailanu, yau dai ya kamata ki zo ku gaisa da mutumin don shi ma ya san fuskarki a zahiri.”

Dailanu ashe tun bayan rabuwarsu da Nur a wannan tanti sai ta nufi waje tana ta sunsunar wata irin ciyawa. Jin kiran Kawarta sai ta fahimci abin da ake nufi, wato ta zo a gaisa, saboda haka nan da nan sai ta koma cikin siffar mutane ta nufi tantin, ta yi sallama, jarumi Idrisu ya amsa, ta shiga.

Yana ganin ta ya gane cewa aljana ce, don irin hasken jikinta da kyanta sai dai wanda ya gani. Ba don yarinya Nur kyanta ya kai a ce lahaula wala Kuwwata ba, to da saiace Dailanu ta fi ta, amma ina? Wane ita da kyan Nur.

Ta gai da Idrisu cikin girmamawa, fara'a da walwala. Bayan ya amsa sai ya ce, “Ya ke Dailanu, na san labarinki daidai gwargwado, da kuma irin taimakon da kike ta yi wa wannan baiwar Allah.” Ya nuna yarinya Nur da hannunsa.

Dailanu ta ce, “Ai ranka ya dade ni ce da godiya, don dalilinta ne Allah Ya qaddara na fita daga cikin bakin duhun bautar abin da ba Allah ba. Yanzu kullum cikin farin ciki nake.”

Cikin dabara Dailanu ta fice abinta don ba su wuri su zanta, ta koma can cikin ciyayin da take sunsuna.

Www.bankinhausanovels.com.ng Hira fa ta barke tsakanin Nur da Idrisu, ta ba shi

labarin mahaifinta, wato malaminsa dattijo Shaihi

Ibrahim, da irin zaman da suke yi ita da sauran 'yan mata a can bayan duniya.

Cikin hirarsu ne take shaida masa cewa, “tun ranar da muka rabu da mahaifina a lambun nan ba mu sake haduwa ba, sai dai kowane lokaci ina jin labarinsa in Dailanu ta je daukar karatu.

Kuma ka san wani taimakon Allah? Har yanzu wadannan shaidanun 'yan'uwan nata ba su san ta musulunta ba, ballantana har su gane cewa tana zuwa wurinmu, ai da tuni sun halaka ta.”

Labari fa ya yi dadi, har lokacin tafiya ya Karato. In sun tuna cewa za su rabu sai su yi ta fata da addu'ar Allah Ya hada su haduwar da babu rabuwa sai dai ko mutuwa. Ita ma mutuwar ba su Ki ta dauke su tare ba; a irin yadda suke ji dai, saboda tsananin son juna.

Yarinya Nur ta ce, “Labari ya yi dadi, na manta ban fada maka ba cewa, cikin 'yan matan da muke tare da su akwai guda uku. Akwai ta dan'uwanka Waziri Habu, da ta Yahaya, da kuma ta Bashari dan Salihu,

suna nan lafiya in dai banda matsalar begen masoyansu da ke ci musu tuwo a Kwarya.”

Ta ci gaba da yi wa Idrisu bayani, “Miu dai kullum babbar addu'armu ba ta wuce Allah Ya ba ka nasaraa

Www.bankinhausanovels.com.ng kan halaka wannan bakin maridi Sham'una.

Babu shakka wannan mugu ya zalunce mu, ko da yake zaluncin nasa ne sanadin haduwata da kai amma dai irin su Sham'una ne ke haifar da dacin soyayya...”

Idrisu ya katse ta, “To, kafin ki yi nisa, shi kuma mene ne dacin soyayya?”

Sai yarinya Nur ta yi wani irin murmushi mai dauke hankalin wanda ya ga wushiryar daidaitattun hakoranta, ta ce, “Ya kai namijin mazaje, idan ba ka san dacin soyayya ba, to saurara, dacin soyayya shi ne masoya biyu suna matuKar son juna amma ba su tare da juna, kuma da zarar sun tuna juna sai bakin ciki ya lullube zukatansu don babu yadda za su yi su hadu. Abu daya ne kuma kawai kan kawo irin wannan daci. Shi ne takobin soyayya.

In ba ka san takobin soyayya ba ya kai hasken masu haske, to shi ne hassadar mahassada, suna bakin cikin su ga masoya biyu cikin jirgin ruwan so, duk yadda za su yi don huda jirgin ya nutse sai sun yi, don bakin ciki. Kamar dai yadda la'anannen aljanin nan ya hana ‘ya'yan mutane shan inuwar zuciya.”

Ai kafin ta kai jawabinta duk Idrisu ya tsuma da irin yadda ya ji bayani na fita filla-filla daga bakinta, sai ya ce, “Babu shakka kina da gaskiya, iya magana,

Www.bankinhausanovels.com.ng kuma babu shakka duk ranar da Allah Ya ba mu nasara a kan wannan azzalumi na mayar da ke wurin malam aka daura mana aure, to na yi alwashin yin raka'a ashirin don godiya ga Allah da Ya ba ni wayayya irinki.”

Da yarinya Nur ta ji abin da masoyinta ya ce sai ta dukar da kanta Kasa, irin 'yar kunyar nan sannan tace, “Ni kuma na yi alwashin in Allah Ya so ba kai kadai za ka yi ba. Tare za mu yi raka'o'in godiya ashirin din.”

Lokaci ya yi nisa, Magriba ta yi gab matuka, sai yarinya Nur ta ce wa saurayinta Idrisu, “Yanzu lokacin komawa ya yi, ka yi hakuri ka kwantar da hankalinka, sai mun sake saduwa ranar da ka tumurmusa hancin tsinanne.”

Masoyan nan biyu suka dubi junansu sai dukkan su hawaye ya yi ta kwaranyaa kan kumatunsu. Nur ta sa hannu a cikin wata jaka wadda aka yi wa bakinta

; kwalliya da danyen zinare ta zaro wani kyalle fari sal wanda a jiki akwai taswirar da aka yi Kokarin debo kamanninta, ga ta nan ta sa wasu tufafi masu ruwan dorawa, da mayafinsu wanda ya rufe rabin gefen kanta. A cikin taswirar ta yi wani irin dan sunkuyar da kai kamar tana kallon kasa. An daje kyallen da taswirar ke jiki da dusar zinare. Ta mika masa.

Www.bankinhausanovels.com.ng

Ya karba ya bude, ai sai murna ta lullube shi, ya ji kamar ba rabuwa za su yi yanzu ba. Can kuma sai ya daure tare da murtuke fuska, ya mayar mata da kyallen yana mai cewa, “Na rantse in dai har Sham'una ne ya sa aka zana wannan taswira taki, to ba na bukata.”

Nur ta yi dariya tana mai cewa, “To sarkin kishi, kai in banda abinka ai Sham'una ma bai san da wannan ba. Matar dan'uwanka Yahaya, gwana ce wurin zane da dinka taswira, ita ce ta dinka mini shi, saboda haka ka kwantar da hankalinka, babu wani a fadin duniyar nan sai kai.” Tana kammala fadin haka cike da murmushin da ke tabbatar da abin da bakinta ke furtawa. Wannan jawabi kuma shi ne abin da ya warware sakar kishin da ta dabaibaye zuciyar Idrisu.

Yarinya Nur ta yi kiran Kawarta don su tafi, Dailanu ta zo don yin sallama da Idrisu, ta ce masa, “Akwai wani abu da nake so wanda kuma naka ne, amma kuma ba zan fada maka ko mene ne ba yanzu, sai ranar da Allah Ya ba mu nasara tukuna. Sirri ne wanda in na fada maka yanzu za ka yi matukar mamaki, saboda haka don Allah kada ka tambaye ni.”

Jin haka sai Idrisu bai matsa don jin labarin ba, sai ya ce, “Ya ke shugabar matan aljanu, kwantar da

Www.bankinhausanovels.com.ng hankalinki, raina ne kawai ba zan iya ba ki ba, wadda kawai zan iya ba raina sai dai Kawarki Nur.”

* Sai Nur ta yi mata irin wasan nan na Kawa da kawa ta ce, “Kada dai ki Kwace mini miji, kin gan shi dan kyakkyawan saurayi.”

Dailanu ta ce, “Kamar kuwa kin san shi nake so in kwace.”

Nur ta amsa mata tare da murguda baki, “Mhm, wai ma.”

Sai dukkan su suka yi 'yar shewa irin tasu ta mata in suna nishadi.

Nur ta dafa kafadar kawarta Dailanu sai kawai ya ga sun tashi sama suna dago masa hannu, shi ma bai Bata lokaci ba wurin daga musu. Tun yana iya hango su har dai suka bace a cikin sararin samaniya.

Sauke idanunsa sai ya ga babu komai a wurin da tantin nan ya ke sai ciyawa koriya shar. Bai yi mamaki ba, don ya san aikin aljanu ya fi da haka. IDRISU ya ci gaba da tafiya har ya iso Karshen filin nan mai koriyar ciyawa.

Dole ya ja linzami ya tsaya.

Yanzu abin da ke fuskantarsa fuska da fuska wani

irin hayaki ne jajawur kamar wuta, wanda kuma ya

Www.bankinhausanovels.com.ng zama kamar wata katanga mai shiga tsakanin wannan kyakkyawar ciyawa da ya fito daga ciki da kuma inda yanzu ya ke nufin shiga.

Sai ya fara addu'a yana cewa, “Allah ina rokon kiyayewarKa daga sharrin wannan hayaki da ban taba ganin irinsa ba.”

Bai yi wata-wata ba ya kutsa kai cikin hayakin, ba ya ganin komai sai dai inda Jagora ya bi da shi kawai, wani lokaci ya ji Jagora ya karkata da shi, wani lokaci ya ji kamar ya tsallake wani abu, a haka sai da suka yi misalin kwana uku suna tafiya.

Bayan Karewar mugun hayaki sai kawai Idrisu ya tsinci kansa gab da wani babban birni. Kofar garin kuma a bude, saboda haka sai suka shiga.

Babu shakka birnin na da matukar kyan gine-gine, dogaye wadanda suka wuce tunanin dan Adam.

Sai dai kuma wani abin mamaki, babu kowa a garin.

Ya shiga tunani cikin zuciyarsa, “Aljanu ke nan, kun gina gari amma kun Ki ku zauna a ciki.”

Bai zame ko ina ba sai gindin wata Katuwar bishiya mai kauri da wasu ganyaye masu fadi lif-lif gwanin ban sha'awa, ya kwance sirdi KarKashinta. Da ma kuma gajiya da rashin barci tun tuni sun rigaya sun yi wuji-wuji da shi. Ya dora kansa a kan sirdin da ya kwanto ya bar Jagora nan tsaye ya san nayi.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Barci da minshari ya ke ta yi har sai da dare ya fara tsalawa. Can sai ya rika jin motsi ana ta kaiwa da komowa, kamar dai ana cin kasuwa.

Ya bude ido sai ya ga wasu irin halittu, su ba mutane ba, su ba dabbobi ba, su kuma ba tsuntsaye ba. Idanunsu jajawur kuma jikinsu da wani irin gashi kamar na rago. Wannan birni cike yake makil da irin

- wadannan halittu kowa yana ta harkar gabansa amma babu mai magana da wani.

Ga kuma wani gungu nan sun taru suna kallon sa.

Idrisu ya daga hannu ya yi musu sallama, “Assalamu alaikum.”

Babu wanda yaamsa.

Sai ya tambaye su, “Don Allah in ku mutane ne, to wadanne iri ne? In kuma ba mutane ba ne shin ku aljanu ne ko kuwa tsuntsaye?” .

Babu dai wanda yace masa uffan-kanzil.

Ya ce, “To ni dai na fita hakKinku. Kuma in ku masu sharri ne, to ina neman tsarin Allah daga gareku.”

Ya juya ya sake dora kansa a kan sirdi ya rungumi takobinsa da mashi ya ci gaba da barci, Jagora kuma yana tsaye kusa da shi. A takaice dai jarumin bai farka basai Asubahi.

Farkawarsa abin mamaki sai ga wannan birni ya

Www.bankinhausanovels.com.ng

Bace babu ko alamarsa, filin babu komai sai wannan itaciya da ya ke Karkashinta kawai, ganin haka sai Idrisu ya ce, “Na san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Wane mutum da aikin aljanu.”

Ya tashi ya gabatar da ibada da addu’o'insa na neman samun nasara sannan ya dora wa Jagora sirdi suka ci gaba da tafiya.

Bayan kamar kwana goma sai ya iso wani fili fari fat wanda babu ko digon baki a cikin sa, abin da kawai ya hanawa jarumin sukuni a wurin babu kamar tsananin zafin rana. Can a gefe sai ya hango wasu mazaje su goma, Karfafa, ba tare da wani bata lokaci ba sai ya nufe su ya yi sallama, “Assalamu alaikum.”

Suka ce, “Wannan kuma kai ka san abin da kake nufi, mu ba shi ya dame mu ba, ba ruwanmu da shi, mu yau ranka kawai muke bukata.”

Idrisu ya ce, “Ban ki ba, amma shin ko kuna da wani dalili na bukatar raina?”

Abin mamaki gaba dayansu suke magana, a lokaci daya kuma da kalamai iri daya kamar sun haddace, sai dai kuma shi Idrisu wannan bai rudar da shi ba don ya san ba karamin aikinsu ba ne. Wadannan halittu suka ci gaba da mayar masa da martanin cewa, “Mu kuwa ke da kwakkwaran dalilin kashe ka. Ka ga birnin da ka wuto wanda babu wanda ya yi maka

Www.bankinhausanovels.com.ng magana a cikin sa? To birninmu ne, ka gan shi can.” Suka yi nuni da hannayensu, yana dubawa sai kuwa a gefe shirim ya hango birnin da ya wuto misalin kwana gona da suka gabata.

Jarumi Idrisu ya tambaye su, “Amma ku kuwa mene ne labarinku, kuma mene ne labarin wannan birni da ya bace ya dawo nan?”

Suka amsa masa cewa, “E lallai za mu sanar da kai, akalla kafin mu kashe ka mu shanye jininka, mu cinye namanka, kuma mun yi maka alkawari cewa ko digo na jini ko tsoka ko kuma wani bangare na kashi

ko sashe daga jikinka ba za mu rage ba.

Ka ga wannan gari garinmu ne wanda yau ya kai kimanin shekaru dubu tara da dari tara da kafuwa. Duk kuma da ka gan mu cikin wannan siffa ba mutane ne ba ne; aljanu ne. Tun farko abin da ya sa ba mu zartar maka ba shi ne dalilin kwanciyar da ka yi a karkashin waccan itaciya da ka wuto kwanakin baya.

Ko kiyashi ba mu iya kashewa Karkashin waccan itaciya saboda girmama ta da muke yi, don duk aljanin da ka gani a yau yana rayuwa, to ya tarar da wannan bishiya ne, kuma duk wani aljani da ya shahara, to in ka bi diddigi da tarihi za ka tarar yana da wata dangantaka da bishiyar. Kai ko Sarkin aljanu

Www.bankinhausanovels.com.ng Sham'una ma lokacin da ya ke Karami sai da ya taba kwana a kanta.

Daga cikin darajar wannan itaciya da kuma irin yadda muke girmama ta shi ne babu wani aljani da ya isa ya yi magana a lokacin da ya ke kusa da ita, shi ya sa ka ga ko amsa maganarka ba mu yi ba.”

Wadannan aljanu dai suka ci gaba da yi wa Idrisu bayani, “Mu aljanun wannan birni muna iya daukarsa mu kai shi inda muka ga dama. Kuma mun kawo shi nan ne don mu tare ka.”

Idrisu ya ce, “Duk na ji wannan, to amma mene ne dalilin bukatar kashe ni? Ko kuwa za ku kama mutum ne da laifin da bai sani ba? Ina kyautata zaton

cewa yanzu laifina shi ne hutawa da kuma yin barci a Karkashin itaciya ko? To a gaskiya da ace na san haka kuka dauki itaciyar to babu abin da zai hana ni sare ta kowa ya huta.”

Suka ce masa, “To ai mu in mun kashe ka ma bakin cikinmu raguwa kawai zai yi, amma ba zai kare duka ba, sai dai kuma akwai dan sauki in mun tuna cewa ba ka numfashi, don ka zalunce mu, ka cuce mu, ka halaka mana kakanninmu ta hanyar kashe su kisan gilla ba tare da wani laifi ba.”

Idrisu ya tambaya, “Su wane ne kakannin naku da na kashe? Yanzu dai dole sai kun Kakaba mini laifi da

Www.bankinhausanovels.com.ng karfin tsiya don ku zalunce ni?”

Suka ce, “Af, har ka manta, macizai biyu da ka kashe a birnin Sarauniya mai macizai, to ai wadannan macizan ne kakannin namu. Su ne ke da wannan birni namu da ka gani, duk wanda ka gania cikinmu daga 'ya'ya ne sai jikoki da tattaba-kunne nasu, kuma dukkanmu mun yi alkawarin cewa sai mun shayar da kai modar mutuwa a duk inda kake a duniyar nan ko wajenta.”

Da Idrisu dan Hamidu ya ji jawabin wadannan aljanu sai ya ce musu, “E, lallai kam babu shakka ni ne na kashe wadancan tsinannun kakanni naku, kuma muna rokon Allah Ya gaggauta rayukansu zuwa cikin wuta, Ya kuma dandana musu azaba. To ku ai wadannan kakanni naku ai ko Sarkin aljanu Sham‘una ba na zaton ya kai su zalunci.

A kullum fa sai sun kashe mutane, sun shanye jininsu sun cinye namansu, ana kuma bauta musu alhali su ba Ubangiji ba, saboda haka Allah Ya tsine musu, da ku ma baki daya don kuwa kun ki gaskiya.

Saboda haka tun wuri ku bace mini da gani, ku ba ni wuri in wuce, don ni ba don ku na fito ba.” Sai wadannan aljanu suka ce, “Lallai ka isa azzalumi, ka kashe mana kakanni, sannan ka bi su da mugun zagi da mummunar addu'a, ko kunyarmu ba

Www.bankinhausanovels.com.ng ka ji ba. Kuma maimakon ka roke mu arziki mu Kyale

ka amma mu kanmu sai da ka zage mu tare da raini.” Idrisu ya tambaya, “In roke ku? Ai wannan zancen

banza ne irin naku na 'ya'yan azzalumai. Bayan zagin

ma ingiza ku lahira zan yi don ku je ku tarar da su

can.”

Saboda irin tunzura da suka yi sai wani daga cikinsu ya yi wata irin magana wadda Idrisu bai san abin da take nufi ba, sai ga aljanu kamar su dubu biyar sun kewaye shi sun yi masa zobe, dukkan su kumaa cikin siffarsu ta aljanu don su tsorata shi kafin su yi watanda da namansa wadanda suka samu sun samu wadanda kuma ba su samu ba su yi hakuri.

Amma kuma shi Idrisu ko gezau.

Da suka ga haka, sai suka fara rikidewa suna komawa wasu irin macizai, iri-iri, launi dabandaban, jajaye da farare, algashi da masu dabbaredabbare, kai wasu ma har da dan kunne. Wasu manya kamar girman giwaye, wasu kuma Kanana. Wasu na kukan jaki wasu suna haniniyar doki, kai wasu har tashi sama suke yi suna sauka.

Lura da haka sai Idrisu ya zaro takobinsa daga kubensa, kuma wani abin mamaki shi ne takobin na fitowa sai kawai bakunansa suka koma goma sha biyu, kuma dogaye masu tsawon gaske.

Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka fara kai masa hari, amma da zarar ya kai sara sai ka ga aljanun macizan nan suna ta fadowa kasa kamar fari, kafin wani dan lokaci ya kashe duk macizan da ke shawagi a kansa da kuma wani kaso mai yawa daga cikin wadanda ke Kasa. Sauran sai suka raba junansu kashi-kashi, koraye daban, jajaye daban, tika-tiKka daban, haka nan sirara, ga su nan dai kowanne sun ware gefe. A haka kungiya-kungiya suka shiga kai wa Idrisu da dokinsa farmaki. Tsartuwar dafi kake ji babu KakkKautawa har sai da suka jike su shi da dokinsa sharkaf, amma wannan babu tasirin da ya yi musu don tun a tsibirin dodo jikin Idrisu da dokinsa sun zama babu dafin da zai iya tasiri a kansu.

Cikin wani dan KanKanin lokaci sai ga Idrisu ya gama da wani kashi da ya fado masa. Ganin haka sai wadannan aljanu suka tunzura suka koma cikin mummunar siffa irin tasu ta aljanu suka nufo shi gaba daya, shi ma sai ya yi fushi ya kara kaimi wurin sara da suka. Babu ko tsoro ko razana haka ya ke ta yi, sai dai ka ga ya matsa gaba, ya ja baya ya buda Kafafuwa ya yi wani irin juyi ya tunkari wadanda suka nufo bayansa kafin sauran su gyagije ya sake juyowa kansu, kai fada da dan Hamidu ba dai gaba da gaba ba, kai ko ta bayan ma sai an shirya.HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...