YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?”

Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.”
Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan'uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.”
Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk 'yan'uwa muke ba mu sani ba?”

"Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su.

Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.”

A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sama ta fado jikinsa.

Firgigit ya dan tsorata kadan kafin dai ya yanke

ZAMU TASHI 

shawarar daukar takardar yana mai cike da tararrabi. Ya bude a hankali bayan zuciyarsa ta natsu kuma ya tabbatar cewa shi ake nufi ya duba takardar, duk da cewa bai ga mai kawowa ba.

Yana budewa sai fuskarsa ta cika da murmushi tun da ya fahimci rubutun dan'uwansa.

JARUMI Idrisu ya mika kamar yadda ya saba ba dare ba rana har sai da ya sami kwana sittin da hudu yana kutsawa cikin daji, kuma duk cikin anakin nan bai hadu da dan Adam ba ko daya. In dai ya ji motsi, to babu shakka manya ko kuma miyagun namun daji ne.

Ya iso wata mararraba wadda ta rabu gida uku, tsakiya, dama da hagu. Bai yi wata-wata ba sai ya mike sanbal.

Wannan hanya ita ce ta zuwa birnin Salsala, wato garin Sarauniya Zinkadaziyya, kuma matukar mutum zai nufi bayan duniya, to dole sai ya bi ta nan.

Sai da ya yi kwana biyar yana tafiya cikin wani irin mugun sanyi da ke zubowa fari sal daga sama kamar KanKara sannan ya hango garin.

Ganuwar garin kamar an gina ta da azurfa ne saboda wani irin sheki da take yi. Shi kansa Idrisu sai da mamakin irin wannan katanga ya rufe shi. Fitilu

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG kuwa a kowace kusurwa ta wannan gari ko allurarka

ce ta fadi da dare, to za ka dauka ba tare da wahalarwa . ba, ko kadan ba abin mamaki ba ne in aka ce wannan

gari aljanu ne suka gina shi. Sai dai kuma mutane ne
ke zaune a cikin sa ba aljanun ba.

Ga wasu itatuwa da furanni iri-iri masu matukar ban sha'awa da Kanshi. Abubuwan bukata na yau da kullum dai babu abin da mutum zai buKata ya rasa, komai suna da shi.

Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne duk garin babu namiji ko daya sai dai mata. In kuwa har ka ga namiji, to an kamo shi ne kawai don ya zama abincin macizan da mutanen garin ke bauta wa. Musamman sukan fita farauta don kamo mazaje, ballantana kuma wanda ya kawo kansa.

Ba su ba macizan nasu ramammen namiji, a'a sai sun kiwata mutum ya yi Bulbul tukuna.

Wadannan mata sun Kware matuka wurin jarunta, suna da wata irin tarbiyya wadda mace daya ko kadan ba ta tsoron tunkarar jarumai arba'in, ita kuwa Sarauniyarsu saboda irin siddabarunta da _ sanin lagon yaki sai an tara jarumai dari sannan ta kan fafata dasu.

‘Ta Bangaren kyau kuma mutanen wannan gari baa magana, ballantana Sarauniya Zinkadaziyya wadda

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG duk Karfin halinka in har kuka yi ido hudu da ita kuma ka ga zahirin fuskarta, to sai jikinka ya yi sanyi saboda irin cikar halittar da Aah Ya yi wa fuskar tata da jikinta.

Yadda suke jin dadinsu kuma shi ne su sha giya, su yi kida da raye-raye sannan su bauta wa macizai. ‘Tsakanin su da maza kuma sai kisa.

Da Idrisu ya kusa da garin sai masu tsaro da ke kan husumiya suka hango shi, nan take suka sanar, kafin ka ce mene ne wannan mata goma sun yiwo masa dauki a kan dawakansu dauke da makamai. Da suka Karaso sai suka daka masa tsawa, suka ce, “Kai tsaya, dakata a nan, wane ne kai? Daga ina kake? Me ya biyo da kai nan? Ba ka san ka biyo hanyar mutuwarka ba ne sannan kuma ba damar juyawa baya? To, yi maza ka sauka daga dokinka ka kawo takobi da mashinka. Ko kana so ko ba ka so ka zama abincin macizan da muke bauta wa.”

Da ya ji jawabin jaruman ‘yan matan nan sai ya ce, “Haba, ku ba ku kyautata wa bako ne? Shin ba ku san cewa mutumin da ba ya kyautata wa bako ya yi hasara ba? Shin ku ba ku zuwa wani gari ne ku ga yadda ake karramawa tare da mutunta baki? Kuma idan kun ga cewa ba za ku iya sauke ni ba ne, to ku Kyale ni mana

in yi wucewata zuwa inda na yi niyya. Don Allah ku

Www.bankinhausanovels.com.ng yi hakuri ni ba rikici nake nema ba.”

"Yan matan suka ce, “Kai ba doguwar magana muke so ba. Yaya mu da musamman mukan fita farautar mazaje, kuma ga shi ka zo har gida sannan ka ce mu Kyale ka? Ai sai dai wani ba kai ba. Shi kuma wannan kyakkyawan doki naka Sarauniyarmu ce ta fi cancanta da hawan sa... ko da yake kai ma ba baya ba ne a fagen kyau din.”

Suka fara zagaye shi da dawakansu, shi kuma yana tsakiya, suka zazzare takubba, ai sai Idrisu ya yi wa dokinsa Kaimi. Jagora ya buga wani irin tsalle na Kwararren doki ya tsallake 'yan matan nan ya koma gefe a daidai lokacin da Idrisu ke jawo takobinsa ya saro wani babban reshe na bishiyar da ke kusa dainda dokin ya dira. Jarumin ya rike reshen ya mayar da takobinsa cikin kube.

"Yan matan nan suka yiwo kansa. Idan sun kawo sara sai ya goce, har sai da ya fahimci cewa da gaske suke yi sannan ya fusata ya sa wannan reshe na itace ya yi ta bugun su yana kauce wa saran takubbansu har sai da ya yi musu tilis. Da Kyar suka koma cikin gari.

Kai, ‘yan matan nan sun sha wuya.

Jina-jina suka je suka sami Sarauniya, abin ya yi matukar ba ta mamaki, amma duk da haka saida tasa aka kama su aka daure don sun kasa kamo mutum

Www.bankinhausanovels.com.ng daya tak, ta riKa fada cewa sun cika da mayen giya ne har aka yi musu haka, amma za ta koya musu darasi. Ta sa wasu jarumai wadanda an tabbatar da jaruntarsu a kan cewa abin da take so shi ne azo mata da wannan mutumi da ransa don a azabtar da shi kafin a ciyar da macizai namansa.

"Yan mata suka je suka yi shirin yaki, daga ganin su ba sai an fada ba cewa jarumai ne, suka nufi bayan gari inda Idrisu ya ke. Suka hango shi zaune Karkashin wata itaciya kashingide, ga alama ba abin da ke damun sa. Shugabarsu ta ba da umurnin cewa ashirin su je su kamo shi, amma fa kada a kashe shi.

Idrisu dai ya fahimci sun nufo shi gadan-gadan, sai ya yi wuf ya suri itacensa na dazu ya haye doki. Bai Bata lokaci ba wurin fara jibgar su alhali shi ko rigarsa ba su iya tabawa ba.

Duk ta hanyar da suka Bullo sai su tarar ashe ya fi su sanin ta. Tun da suke ba su taba ganin jarumi kamarsa ba wanda hakan ya ba su mamaki.

Fada ya yi fada, ‘yan matan Sarauniya suka ga dai in aka ci gaba a haka, to babu shakka wannan mutumi zai halaka su, don a halin da ake ciki ma akwai guda goma kwance, saboda haka sai sauran suka juya linzami suka rufa a guje sai cikin birni.

Idrisu ya koma ya daure wadannan jikkatattu guda

Www.bankinhausanovels.com.ng goman tamau kamar ya daure goro.

Sauran talatin da suka sha da kyar suka sami Sarauniya suka tabbatar mata da cewa babu shakka lamarin ba na wasa ba ne, don su dai wannan mutum ba su taba samun jarumi kamarsa ba. Sarauniya ta fusata ta yi musu bulala sannan ta ba da umurnin cewa su maaje a kulle.

Sai suka ce, “Ranki ya dade, mun yarda ma a kashe mu ba daurewa ba kawai, matukar dai aka samu wanda ya je ya kamo shi.”

Jin hakan sai hankalin Sarauniya ya dawo jikinta tace a Kyale su, sannan ta ce, “Lallai babban al'amari ya zo mana.”

‘Tunanin Sarauniya na gaba shi ne a sako wa wannan jarumi zakoki.

Su wadannan zakoki Kwararru ne wadanda aka yi wa kyakkyawan horo na komai jaruntarka sai sun gama da kai. Guda daya kawai daga cikinsu kan karya jarumai fiye da dari biyu. Babban abin da sukan yi kuwa shi ne da sun iso wurin jarumai sai su yi wani irin ruri mai tsananin Karfin gaske, wanda kuma suna yi sai dawaki su rude su yi ta karo suna kayar da mahayansu suna gudu, shi ke nan sai zakokin su bi su karkashe jaruman. Dasun kammala wannan aiki sai su koma cikin gari a guje su shige inda ake killace su.

Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya ta ba da umurnin a sako wa jarumi Idrisu su. Cikin kanKanin lokaci suka nufo bayan gari suna ruri da gunji

Da ya hango su sai ya yi tunani a ransa ko dokinsa zai firgita, shin zai iya fuskantar wadannan girdagirdan zakoki kuwa? Sai ya shafa wuyan Jagora ya dan bubbuga, wato alamar yana Karfafa masa guiwa tare da tausar sa a game da irin Kalubalen da ke tunkarar su. Jagora ya fahimci abin da ake nufi sai ya yi haniniya wadda ta tabbatar wa Idrisu cewa babu fargaba.

Nan da nan sai tunanin Jarumin ya hararo masa dodon da ya taba artabu da shi, irin girmansa, ban tsoronsa da mummunar kamarsa amma ba su sa Jagora ya tsorata ba, ballantana zakoki, saboda haka sai ya sami cikakkiyar natsuwa. Da suka kusa karasowa sai Jagora ya yi ta harbin iska abinsa yana wani irin rimi yana kewayawa.

Cikin murna Idrisu ya sake gode wa Allah da Ya ba shi irin wannan jarumin doki.

Zakokin nan goma da suka Karaso kusa da Idrisu sai suka fara, mai Karaji yana yi, mai ruri yana nasa amma Idrisu ko gezau, su kuwa wadancan 'yan mata da ke daure sun zuba ido ne suna jiran ganin abin mamaki yadda zakokin nan za su yi watandar naman

Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu da dokinsa a tsakanin su.

Bai yi wata-wata ba ya zare takobinsa, Kara kamar aradu. Wasu irin shimfidaddu kuma dogayen sararraki guda biyu kawai ya kai ta gefen dama da hagu amma ya raba zakoki hudu kowanne da gangan jikinsa. Ko shurawa ba su yi ba.

Sauran shida suka ja baya suna jiran su yi masa dirar mikiya, amma kuma sun makara don kuwa ya rigaya ya gane nufinsu. Kafin su iso ya daga takobinsa sama, sai kuwa baki dayansu suka diro masa, amma kafin su gama sauka har yasara sau uku kamar walkiya.

Sai dai wasu ba su ba. Duk Idrisu ya halakar da su.

Daurarrun ‘yan mata dai sun rigaya sun yanke tsammani da duk wata tantama ko shakka game da jaruntar Idrisu. Tunaninsu ma yanzu ya karkata zuwa ga cewa lallai shi ba mutum ba ne, a'a sai dai wani jarumi ne daga cikin manyan jaruman aljanu, dalilinsu kuwa shi ne, su dai ba su taba ganin mutumin da ya yi nasara a kansu ba ballantana a ce kuma ya yi nasara a kan zakokinsu. Ga shi kuma kyansa ya kai ace dan aljanu.

Idrisu ya karasa wurin wani tafki da ke nan kusa ya wanke jinin zakokin da ya fantsamar musu a jiki shi da dokinsa, sannan suka sha ruwa ya kuma debo ya zo ya bai wa 'yan matan nan wadanda tuni da ma

Www.bankinhausanovels.com.ng kishirwa ta rigaya ta dame su. Yanzu kam sun tabbatar cewa tun farko ya Ki kashe su ne saboda tausayi.

Suka ce, “Mun gode saboda ruwa da ka ba mu.”

Ya amsa musu cewa, “Af, ashe kuna da saukin kan da za ku iya yin godiya? Don ni ina fahimtar ku ne a matsayin masu girman kai da jin mugunta a rai. Ga alama kuma a fuskarku duk wanda ya gan ku ya ga kyawawa amma a zuciyoyinku za ku iya cinye mutum danye saboda tsabagen rashin imani da kumia rashin tausayi.”

Suka ce masa, “E, lallai ba ka yi Karya ba ya kai wannan jarumi, amma kafin mu ce maka komai, me yasa baka kashe mu ba bayan ka yi nasaraa kanmu?”

Ya ce, “Babu shakka kun yi tambaya, idan za ku iya tunawa dazun nan nace ba ku da tausayi, kuma duk mutumin kirki dole ne ya zamo mai tausayi. Kamar yadda kuke jin zafin jikinku haka ma wani ya ke jin zafin nasa jikin.”

Da 'yan mata suka ji jawabin Idrisu sai suka ji a zuciyarsu sun natsu da shi, sai suka ce masa, “Lallai mun yarda da abin da ka fada mana, kuma yanzu za mu gutsura maka labarinmu.

Mu dai yadda ka gan mu din nan ba mu jin tausayin kowa. Babu soyayya tsakaninmu da sauran mutane

Www.bankinhausanovels.com.ng don muna ji a jikinmu cewa mun fi kowa, kuma daga cikin mutane wadanda muka fi ki da tsana su ne mazaje. Mu din nan da ka gan mu da yawanmu tun da suke ba su taba sha'awar wani da namiji ba, ballantana har su san shi. Wasu kuma bacin ran da da namiji ya Cusa musu a rayuwa ne da kuma tunanin  daukar fansa a kan dukkan jininsa ya sa suka gudo suka zo nan suka zauna. Duk wadda ta kuskura aka ' gan ta tana magana ma kawai da wani namiji, to kuwa ranar ba da ranta za ta kwana ba.

; A yanzu haka akwai mazaje sun fi dubu goma suna ‘ nan a kulle a gidaje daban-daban ana kiwon su, don mu tsakaninmu da maza sai dai kawai mu kama, mu ; kiwata mu bai wa macizan da muke bauta wa su ci.”

Sai Idrisu ya tambaye su, “Macizai kuke bauta wa?” Suka ce, “K:warai kuwa, abin mamaki ne? Ai bayan bauta musu ma akwai irin macizan da har dafinsu mukan rika sha don mun yi imanin cewa zai riqa sa mana tsattsaura kuma mugun hali irin na rashin tausayi.” Da jarumi Idrisu ya ji zancen wadannan 'yan mata sai ya tambaye su, “To yanzu mene ne abin yi?” Suka ce, “Abin yi shi ne kawai mu gudu, don mu daga yau mun yarda da kai.” Idrisu ya ce, “A'a ba za mu gudu ba, don kuwa tun

Www.bankinhausanovels.com.ng da har hanya ta biyo da ni ta nan, to ya zama dole a kaina in hana zalunci in ceci duk wanda ke cikin garin nin da kuma duk wanda hanya za ta biyo da shi nan gaba. Saboda haka ina zaton abin yi kawai shi ne yanzu bari in sake ku ku koma cikin gari, ni ma ba da dadewa ba ina nan shigowa.”

"Yan mata suka ce, “Wai! Ai babu yiwuwar haka. Dalili kuwa shi ne yanzu in ka sake mu muka koma, to Sarauniya tana da matsanancin wayon da za ta iya gane cewa mun yi wani shiri ko kuma wata magana da kai, kuma ko shakka babu da ranmu za a dafa mu. Kasancewar ita a irin nata tunanin babu yadda zaa yi ka yi nasara a kan mutumin da ke son kashe ka amma kai kaqi kashe shi.”
Sai suka ce, “Abin da zai fi dai shi ne ka sa mu a gaba a daure, mu nufi cikin gari, in ta ga haka, to ba za ta yi wani zato ba. Kuma da ya ke mun ga akwai amana tattare da kai, to za mu fada maka wani sirri don kada ka cutu. In kuma ka kuskure, to kuwa ba

shakka za ta halaka ka.

Lallai ka yi matukar taka-tsantsan da kyau, kasancewar mun san a irin abubuwan da ka aikata babu shakka yanzu za ta bukaci halaka ka da kanta ne. Na farko dai tana da wani tsafaffen takobi, ko da yake mun ga naka takobin ya fi nata ban mamaki.

Www.bankinhausanovels.com.ng Tana da wani irin doki, wanda ya yi matukar horuwa, kai hasali ma wani lokaci ya fi dan Adam dabara. Ita wannan Sarauniya tamu tana da wani irin kyau wanda in har ka kalli fuskarta kuma kuka hada ido, to dole ka ji ka yi sororo ka kasa tabuka komai har kama ka ya fi sauki fiye da kama kaza, har in ta ga dama tana iya sa takobi ta buge wuyanka ba tare da ka ankara ba.

In kuma har ta ba ka ruwa ko kuwa waniabin  sha, to shi ke nan ka gama yawo, don akwai wani irin dafi da kan lalata kuzarin jiki a ciki. Tana kuma dai da wata kujera ta zinare wadda za ka dauka ta alfarma ce, amma matukar ka zauna a kai, to Sarauniya tana iya sa kujerar ta zame da kai kuma bazakazameko ina ba sai ramin macizanta. Ko kuma duk in ba ta Bullo maka ta nan ba, to tana iya neman aikata masha'a da kai, wanda kuma matukar ka amince, to sai wani ba kai ba.”

Da Idrisu ya ji zancensu sai ya tabbatar da cewa lallai gaskiya suke fada masa, saboda haka sai ya yi musu alkawarin lallai zai yi iyaka Kokarinsa wurin kare su daga sharrinta.

Bayan wannan tattaunawa sai ya sa su a gaba, shia saman doki su kuma a Kasa daure tamau da juna, suna tafiya Kafafuwansu na sarsarkewa ya nufi cikin

Www.bankinhausanovels.com.ng gari yana yi musu hargowar da ke nuna kamar ba ya tausayin su. Da aka hango su nan da nan ‘yan kar-takwana dake kusa da kofar gari suka sanar da Sarauniya ita kuma ta ba da umurnin cewa a bude Kofar gari. Idrisu bai zame ko ina da su ba sai Kofar fada.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye a zaurenta na shiga, tana cikin kaiwa da komowa aka sanar da ita isowar jarumi da ‘yan matan da ya daure. Ta ce a sanar da shi tun da ya shigo cikin garinta, to ya sako mata mutanenta. Shi kuma sai ya amince don kokarin tabbatar mata da cewa ba tashin hankali ya kawo shi ba. Wadannan daurarrun mata suka sami Sarauniya suka zube suka yi gaisuwa. Ta tambaye su dalilin da suka kasa samun nasaraa kan wannan mutum. ;

Suka ce mata, “Ran shugabar duniya ya dade, mun yi iyakacin kokarinmu amma ya fi karfinmu. Kumaa gaskiya mu mun tabbata cewa in ba ke da kanki ba wannan mutum samun wanda zai iya masa sai an tona. Zakokin nan ma fa kashe su ya rika yi kamar , yana kashe ‘ya'yan kyanwa.”

Da Sarauniya ta ji an yabe ta a kan cewa ita ce za ta iya maganin abin da ya gagara sai ta ji dadi a cikin

ranta, ta umurce su da su je su yi wanka su ci abinci su Www.bankinhausanovels.com.ng huta su kuma kasa kunne tare da zura idanu su ga yadda za ta yi da wannan dan tahaliki.

Idrisu kuwa yana can tsaye a inda aka umurce shi a Kofar fada yana ta mamakin irin kyan garin yana kuma sauraren abin da zai je ya zo a daidai lokacin da Sarauniya ta zagaye ta je gidan sarkar da ake ajiye manyan gagararrun jaruman da aka kama ana kiwonsu don bai wa macizai, ta same su ta fitar da wadanda suka fi gogewa guda dari ta kawo kayan yaki ta basu.

Ta fara yi musu jawabi, “Ya ku wadannan jarumai, ga rana ta zo wadda kowannenku zai nuna tare da tabbatar da jaruntarsa har in yi farin ciki da shi. A da na jarraba ku ne na sakaya ku anan don in ga wanda a zahiri zai zauna a garin nan saboda ni, kuma yanzu duk na tabbatar ku masu Kaunata ne, sai dai kun san kuma dole daga cikin gwanaye a fitar da gwani guda daya.

Akwai wani jarumi yana can a Kofar fada, kashe shi ko kuma kamo mana shi a hannu shi ne sadakina, saboda haka daga cikinku duk wanda ya sami nasara

zai zama mijina, kuma in har hakan ta kasance, to kun ga dole ke nan in sauka daga karagar mulki mijin da na aura ya hau.”

Nan fa suka shiga Karaji wai su manyan jarumai,

Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai dai kash, akwai wani babban abin da ke damun su, wato rashin Karfin jiki a dalilin dafin da Sarauniya ta taba shayar da su.

Ita ta san cewa a irin wannan halin da suke ciki sai dai kururuwar kawai, don ko bera ba za su iya kamawa ba, saboda haka sai ta dauko wata katuwar gora ta fuskanci jaruman nan, kuma tana sane ta yi kamar ba ta sani ba ta kyale lullubin fuskarta ya yaye, ta yadda dumbin kyan da ke dankare a fuskarta ya bayyana har jaruman suka gani sau daya sannan ta yi sauri ta rufe. Ai fa wannan sai ya Kara tunzura tare da haukata su wurin hankoron fita don cinye wancan jarumi.

Babu ko tantama sun isa jarumai, ballantana kuma ga shi sun huta, an kiwata su sun yi bulbul.

Kafin wani lokaci ta sa duk an dora wa dawaki sirada, kuma kafin kowane jarumi ya hau sai ya amshi moda daya ta magani ya sha tukuna.

Wannan maganin shi ne makarin dafin da ke jikinsu wanda ke hana su katabus. Yanzu sai suka ji kamar an cire musu kaya, kuma Karfinsu ya dawo jikinsu.

Duk abin nan da Sarauniya ke yi akwai wani saurayi daga cikin jaruman nan da ke ji kamar ya kashe ta don irin wulaKancin da ta yi musu a baya,HMMM LABARU FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...