YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 15 BY HARUNA USMANWww.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Sai dai kash, akwai wani abu da ke matukar damun su a tsibirin. Wato wani irin dodo ne, shi ba mutum ba shi kuma ba dabba ba. Kansa kawai ya kai girman akawalin doki, kuma yana da idanu hudu, daya a goshi, daya a keya, daya a kasan kunnensa na dama dayan kuma a saman kunnensa na hagu. Kowane kunne ya fi matsakaiciyar tabarma fadi kuma yana da bakuna guda biyu, daya a baya dayan kuma a gaba, kuma kowane baki zai iya hadiye Kato komai girmansa.

Wannan dodo dai yana da hannaye guda hudu wanda kowanne yana iya daukar babban dutse da shi, kafafuwansa kuwa kamar wasu manyan itatuwan rimi, cikin sa Kato wanda ko da wasa ba za a iya misaltawa da na toron giwa ba. Jikinsa kuma rabi da gashi daya rabin kuma babu, sannan yana wani irin doyi mai tsananin tayar da hankali. Ba kananan dabbobi irinsu kaji, talo-talo da awaki ba, kai hatta dawaki da rakuma in suka ji doyinsa ba duka ne suke rayuwa ba.
A dabi'a, a duk shekara wannan dodo kan fito daga cikin ruwan rataye da wani irin akurki mai girman katon gida, ya yi ta farautar mutane yana jefawa a ciki sai ya cika shi taf da mutane sannan zai juya ya nufi

ZAMU TASHI 

wani dutse da ke cikin tekun, kuma wani abin takaici ma shi ne tun daga wurin farautar ya ke fara cinye wasu, ka ji yana taunar mutum garas-garas kamar yana cin risga.

Ta yin la'akari da irin girmansa da aka bayyana ya sa kowa ya ke tsoron tunkarar sa ballantana a buga. An taba gayyatar jarumai misalin dubu daga garuruwa mabambanta don su halaka shi, amma Karshe dodon bai taba samun ganima irin ta wannan shekarar ba, don kuwa su ya kame kawai ya juya ya koma cikin ruwa abinsa. Wata shekarar kuma an taba hada wata wuta ganga-ganga da nufin in ya zo ya fada amma a banza, don kuwa komawa cikin ruwa ya yi ya guntso ruwa ya zo ya fesa mata ta bice. A Karshe dai mutanen yankin suka dukufa zuwa ga rokon Allah a kan Ya raba su da wannan fitina.
Yanzu shekarar dodon ta takwas ke nan da ya gane wannan tsibiri.

Amma in ba don wannan masifa ba, to ko kai wane ne ba za ka so tafiya daga wurin ba. Kuma da ma in kai bako ne da zarar mutanen tsibirin suka ga lokacin zuwan dodon ya karato, to za su yi KoKarin sallamar ka ko kuma gargadin ka gaggauta tafiya don kada dodo ya hada da kai. Lura da irin tasirin da ilmi ya yi a tsibirin da kuma

Www.bankinhausanovels.com.ng irin ni‘imar da ta linkime wurin ta sa Idrisu dan Hamidu yanke shawarar cewa zai yi wata uku don Karin neman ilmi da kuma hutawa kafin ya wuce.

Nan da nan aka isar da shi wurin wani dattijon malami wato Shehi Salim, wanda kuma shi ne Sarkin tsibirin. Ya karbe shi da mutuntawa kamar ya taba sanin sa. Idrisu ya roKe shi ko zai taimaka ya sanar da shi wani abu daga cikin ilmi na tsawon wata uku? Don shi matafiyi ne.

Sarki ya ce, “Kwarai da gaske kuwa, mu ai da ma abin da muke so ke nan. Ina amfanin kana da ilmi ka bar wa cikinka kai daya? In ba ka koyawa wani ba to kai yaya aka yi aka koya maka?”

Ba wata-wata Idrisu ya dukufa zuwa ga neman ilmi a wurin Shehin malami kuma Sarki Salim har sai da watanni ukun nan suka cika, kuma a cikin irin hirar da Idrisu kan yi da Sarki ya sami labarin wannan dodo da kuma irin sharrinsa tare da cewa yanzu sauran misalin watanni biyu ya zo ya debi na diba, mai rabon ganin badi kuma sai ya gani.

Sai Idrisu ya ce wa Sarki, “Ranka ya dade ina son zan zauna sai dodon ya zo in ga irin yadda ya ke.”

Sarki ya ce, “Kai dana rufa wa kanka asiri kada ka yi ganganci. Ka ga mu madon ba mu iya rayuwa a wata

Www.bankinhausanovels.com.ng Kasar ne in banda nan, ba don haka ba da ko kare ba za kasamu ba.”
Da Idrisu ya ji zancen Sarki sai ya ce, “Ranka ya dade ina rokon ka yafe mini in ga wannan maridi, kuma na yarda in Allah Ya Kaddara cewa a nan zan mutu babu yadda zan yi, kamar dai karatun da muka yi dazu da kai, Akaramakallahu.”

Sarki ya ce, “Tun da yadda kake so ke nan, to Allah Ya kiyaye mu baki daya.” Idrisu ya ce, “Amin Allah gafarta malam.”

A kwanaa tashi lokacin zuwan dodo ya yi, Sarki ya sa aka yi yekuwa cewa duk wanda ba dan gari ba, to ya gaggauta tafiya, duk kuma wanda ke rike da hakkin wani bako, to ya gaggauta sallamar sa tun kafin dodo ya iso. Baki suka yi ta shiga cikin jiragen ruwa, kuma kafin ka ce mene ne babu kowa sai mutanen tsibirin nan kadai sai kuma Idrisu da ke zaune gidan Sarki wanda mutane suka yi ta mamakin rashin gudunsa.

Bayan kowa ya shirya, masu neman wurin buya sun tanada sai can aka fara jin doyin dodon, wanda hakan ke tabbatar da cewa cikin kwanaki biyu zai iso. Mutane suka fara shigewa maboyarsu ta Karkashin kasa, dawaki da sauran dabbobi kuma tuni sun fara

mutuwa, amma shi Jagora dokin jarumi Idrisu sai

Www.bankinhausanovels.com.ng ‘harbin iska ya ke yi yana wata irin haniniya ta nishadi.

Can sai aka fara jin wani irin Rugi da Karaji mai Karfin gaske da ban tsoro. Ruwan ya dauki zafi kamar ana dafa shi, wanda hakan ya sa Kanana da matsakaitan halittun ruwa fara mutuwa.

Lura da haka sai Idrisu ya shiga kayansa na yaki, ya dora sirdi, ya rataya takobinsa, ya rike mashi. Ya yi tsalle ya haye Jagora, wanda shi kuma kamar jira ya ke yi. Idrisu ya nufi bakin ruwan ta bangaren da ya sami labarin cewa ta nan dodon ke fitowa ya tsaya abinsa.

Can sai ya ga wani abu yana dagowa daga cikin ruwan nan kamar tsauni, yana buga ruwa da hannayensa, yana furzar da wani abu mai kama da wuta daga bakunansa, yana matsowa yana wani irin Karaji. Idrisu ya tabbatar wa kansa cewa lallai wannan mugun maridi ne.

Ga akurkinsa nan rataye a kafadarsa, na jefa mutane in ya kama.

Lokacin da dodo ya kusa abin mamaki sai Jagora dokin Idrisu ya Kara tsawo da fadi. Idrisu ya zaro takobinsa, shi ma abin mamaki wurin fitowar takobin daga kubensa sai ka dauka Karar aradu ce, kuma kammala fitowar takobin ke da wuya sai ya
kara tsawo yana wani irin hayaki kamar an fito da shi Www.bankinhausanovels.com.ng daga cikin wuta.

Da dodo ya hango su sai ya yi wani irin Kumayji ya nufo su da cikakken tabbacin cewa ga wadanda zai fara somin tabi da su nan cikin sauki, amma Idrisu da dokinsa Jagora ko gezau, hasali ma lokacin da dodon ya zo gab-da-gab sai Idrisu ya riKka kewaya shi kasancewar shi dodon ba ya iya juyawa da sauri, sai dai kuma da ya ke yana da ido ta kowane Bangare yana ganin Idrisu din, ya rikKa daga manyan hannayensa yana kai bugu shi kuma dokin yana zamewa ba ya samun su, can ya dago hannaye biyu ya yarfo, shi kuma Idrisu sai ya sa takobi ya datse su, habawa! Jini kamar wasu manyan idanun ruwa ne suka Balle, ga hannayen dodo kuma kamar wasu manyan itatuwa a Kasa.

Dodo fa sai Karaji ya ke yana tsalle-tsalle don tsananin Zafi, itatuwa sai faduwa suke ta yi, ya fusata gaba daya ya nufo Idrisu, shi kuwa sai ya zame ya sa takobi ya sare masa cinya guda daya. Ya girgiza mashinsa ya auna tare da sakar masa a cikin idonsa na gaban goshi, nan take sai wuta ta kama baki daya, Idrisu kuma ya janye mashinsa ya koma gefe yana kallo.
Dodo ya yi ta Karaji yana motsawa ita kuma wuta tana ta cin sa har sai da ya kasa motsi ya Kone Kurmus.

Www.bankinhausanovels.com.ng ‘Tokarsa ma kawai kamar wani tsauni. To in ba ka sani ba bari ka ji yadda nauyin mashin nan na jarumi Idrisu dan Hamidu ya ke, wato matukar dai in ba shi Idrisu din ne da kansa ya girgiza shi ba, to nauyinsa kan koma kamar na wani babban tsauni ne, kuma babu mai iya daga shi sai jarumi Idrisu kadai, ko da yake shi a wurinsa yana jin nauyin ne kamar na kowane irin mashi.

Bayan yi wa dodo irin wannan kisa na wulaKanci sai ya koma cikin gari yana kiran mutane don su fito daga wuraren da suka boBboye, amma ‘yan kadan ne

kawai suka fito, su ma,a tsorace.

Da mutuwar dodo ta tabbata sai gari ya rude da sowa da murna, Sarki ya sa aka shirya biki irin na tseren kwale-kwale da sauran wasanni iri-iri cike da murna irin wadda ba su taba yi ba.

Aka zabi wasu Katti daga cikin matasa aka ba su alhakin daukar kwanduna da kwashe tokar dodo sannan kuma su kona hannayensa da Kafarsa wadanda Idrisu ya sare. Cikin sa'a uku suka kammala suka share wurin kamar babu abin da ya taba faruwa.

Da aka natsa Sarki ya sa aka tattara mutane ya gabatar da Idrisu ga wadanda ba su rigaya sun san shi ba, gaba daya aka yi masa godiya kuma suka roKe shi akan ya amince ya zauna tare da su.

Www.bankinhausanovels.com.ng A wurin ma Sarki ya ce ya ba shi ‘yarsa don ya aura.

Jarumi Idrisu ya mike ya yi musu godiya saboda karamcinsu, ya kuma sake yi wa Sarki da mutanensa godiya saboda yarinya da aka ce za a ba shi aure, ya ce shi yanzu ba shi da lokacin yin aure don irin babban aikin da ke gabansa wanda kuma bai san hakikanin ranar da zai kammala ba ma, in ma har ya yi tsawon rai zuwa ga kai wa ga nasara ke nan.

Ya ce musu daga nan yana nufin danganawa da bayan duniya ne don saduwa da Sarkin aljanu Sham'una, barawon ‘ya'yan mutane.

Suka ya gamsu da bayaninsa, suka kuma yi masa addu'a da fatan samun nasara. Wani dattijo a cikinsu ya yi wa Idrisu gargadi cewa a kan hanyarsa ya yi hankali don kuwa zai ratsa ta garin wata Sarauniya mayaudariya, sannan kuma ga ta jaruma, komai Karfin jarumi, to kuwa za ta iya kashe shi don ta kashe sun fi a Kirga. Ya kuma sanar da shi cewa dukkan fadawanta mata ne, jarumai na Kin Karawa. Sannan kuma tana da wasu macizai guda biyu da suke bauta wa, abincinsu shi ne mutane, kuma mazaje.
Dattijo dai ya ci gaba da bayanin cewa, “Su wadannan macizai tsawon kowannensu ya fi kamu hamsin, kaurin jikinsu kuwa kamar kaurin babban

Www.bankinhausanovels.com.ng jaki.ne Dafinsu kuma idan suka tsartawa mutum, to lallai ba zai kai rabin sa‘a daya ba zai zagwanye.

Ita wannan Sarauniya kuma dai tana da wani sihirtaccen ruwa mai dafi wanda in har ka sha shi, to za ka koma ba ka da sauran laka a jikinka sai yadda aka yi da kai. Ba a taba samun mahalukin da ya taba nasara a kanta ba, hasali ma an ce har aljanu shakkar ta suke don ana hasashen Shaidan ne ya daure mata gindi.

‘Tana da abubuwa uku wadanda take saurin samun rinjaye da su, na farko tana da wani irin doki da babu mai irinsa, na biyu akwai tsafaffen takobi, na uku kuma shi ne ba ta da na biyu a fannin kyau da cikar halitta. Kana ganin fuskarta sai jikinka ya mutu a kama ka kamar kaza. Kai sai kaza ma ta fi ka wahalar kamawa.”

Dattijo ya Kara da cewa, “Ya kai Idrisu tun da ka taimake mu har Allah Ya raba mu da wannan babbar masifa ta dodo, to mu ma za mu dan taimaka maka da irin abin da Allah Ya huwace mana. A duk fadin duniyar nan babu inda maganin dafi ya ke kamar wannan tsibiri namu, ni kuma wannan ilmi shi ne babban abin da nake tinkaho da shi na gadon gidanmu.” Dattijo ya sa hannu a cikin wata ‘yar jaka da ke Www.bankinhausanovels.com.ng
rataye a kafadarsa ya dauko wani Kullin magani ya ce wa Idrisu, “Ga wannan magani ka sha kai da dokinka, ba dai dafi ba, sauran kuma sai ka Boye saboda yiwuwar taimaka wa wani.”

Nan da nan aka miko masa Kwarya ya jika magani ya cika cikin sa ya kuma zuba ya mika wa Jagora ya sha sosai sannan sai ya sa sauran Kullin a cikin jaka.

Ba a tashi daga wannan gagarumin taro ba sai da aka sauya wa wannan tsibiri suna zuwa Tsibirin Idrisu. Daga nan kuma sai jarumin ya sanar da su cewa da ma shi a shirye ya ke, abin da ya dakatar da shi ke nan, wato yakar wannan mugun dodo. Ya yi musu godiya sannan ya ce zai wuce.

Sarki da kansa tare da mafi yawancin jama'ar - tsibirin aka shiga cikin jiragen ruwa aka nutsa cikin teku don yin rakiya ga wannan babban bako na su, bayan kamar tafiyar kwanaki biyar suka kawo bakin gaba, Idrisu ya sauka shi da dokinsa aka rabu ana kewar juna. IDRISU ya kama hanya ya ci gaba da tafiya har ya cim ma wata itaciya mai yalwatacciyar inuwa da kuma wani irin falali a Karkashinta, ya sauka daga dokinsa ya sauke masa kaya tare da kwance masa

Www.bankinhausanovels.com.ng sirdi ya sake shi zuwa cikin daji don kiwo, shi kuma sai ya je Karkashin bishiyar nan ya yi kwanciyarsa rigingine, kafin ka ce me har barci ya sace shi, can ya fara nisa cikin barcin sai ya ji wani abu ya fado masaa fuska, ya bude ido da gaggawa har da wata irin zamilya irin tasu ta manyan jarumai, amma sai ya ga ashe takarda ce, kuma har da rubutu a cikinta. Mamaki ya kama shi.

Yana budewa sai idanunsa suka tabbatar masa da ~ cewa lallai ya taba ganin irin wannan rubutun, hasali ma nan take ya gane daga inda takardar ta fito. “

Daga masoyiyarka mai begenka wadda tunaninka ya zama abincin ruhinta safe da maraice, ina fata kana cike da koshin lafiya kuma cike da taimakon Ubangiji.

Yaya ka ji da karo da mazaje da dodanni? Watakila ka yi mamakin yadda na san halin da kake ciki ko? To tun daga ranar da ka bar wurin malaminka wato mahaifina, ni kuma na dawo nan bayan duniya sai ya kasance halin da kake ciki shi ne babban abin tattaunawa da bibiyarmu a kowane lokaci. Hasali ma duk mako kawata aljana Dailanu kan kewayo ka, kuma wannan takarda ma ita ce ta kawo maka.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina samun labarin mahaifina kuma yana can lafiya lau a kullum yana yi maka addu'a da tambayar labarinka, don har yanzu Dailanu kan je wurinsa daukar karatu, kuma duk Asabar takan zo nan wurinmu.

Sauran 'yan matan da aljanin nan ya tsare mu tare kowacce tana nan lafiya sai dai tunanin iyaye da masoyansu kawai dake damun su.

Ina kuma sake sanar da kai cewa ka yi takatsantsan da Sarauniyar da za ka tarar a gabanka, don mayaudariya ce kuma tana da tsananin jarunta, sai dai kuma muna yi maka addu'ar Allah Ya ba kanasara,a kanta.

in har kana bukatar rubuta mini jawabi game da wannan wasika da aka ba ka yanzu, to Dailanu tana nan kusa da kai, in ka rubuta jefa takardar sama kawai, za ta kawo min. Ka huta lafiya. Ni ce masoyiyarka, Nur ‘yar Ibrahim.”

Murna ba sai an bayyana ba a wurin jarumi Idrisu, tun farkon karanta wasikar har zuwa kammalawa murmushi kawai ya ke yi wanda ke gab da kecewa da dariya. Yana kammala karantawa sai ya daga hannayensa sama yana mai roKon Allah a kan Ya

Www.bankinhausanovels.com.ng cika masa nufinsa. Ya dauko takarda da alkalami daga cikin burgaminsa ya fara rubutawa kamar haka,

Daga Idrisu dan Hamidu zuwa ga rabin rayuwata baki daya.

Da farko dai zan fara ne da ba ki labarin wani abu wanda ya faru a tsibirin dana kashe dodon nan, inda suka yi mini gargadi game da Sarauniyar da kike magana, wai a kan cewa in yi hankali da kyanta don wai yakan dimauta mazaje har kama su yafi sauki fiye da kama kaza.

A gaskiya wannan almara ta sa ni koyaushe na tuna sai in ta BabBaka dariya, lokacin da suke magana nake cewa a zuciyata da a ce gwanayen sanin kyau za su yi dacen ganin ki ko da sau daya ne, to da kuwa har abada sun daina zancen kyan wata mace adoron duniyar nan.

Ko da yake aka ce rashin sani ya fi dare duhu, don kuwa ba su san cewa a dalilinki ne Sarkin aljanu Sham‘una ya mayar da matan da suka tuke a fagen kyau suka zama masu debe miki kewa ba dalilin cewa ko kadan ba zaa misalta ki da su ba. Ni dai ganau ne ba jiyau ba, don kuwa na gan ki a cikinsu, yadda kike haskakawa kamar wata cikin taurari.

Ya ke wadda zakin muryarta babu zumar da ta kai
Www.bankinhausanovels.com.ng ta, wadda babu wani abu mai haske da na taba gani da ya kai farin idanunta, ina tabbatar miki da cewa soyayyarmu ta fi teku zurfi da fadi.

Saukin da kawai nake samu shi ne kullum da adikonki nake rufe fuskata sannan in sami lafiyayyen barci, kuma duk lokacin da kasala ta rufe ni shi nake ratayawa a wuyana sai in ji wani sabon Karfi ya lullube ni.

Ya ke Nur, ina ganin ya kamata in dakatar da rubutuna haka sai kin gan ni, in Allah Ya so. Sai dai kuma kafin nan, akwai taimako da nake so ki rokar mini Kawarki Dailanu ta yi min: ga wasikar gaisuwa nan zuwa ga dan‘ uwana Waziri Habu, Wazirin kasar Arewa. Shi ma akwai budurwarsa tana nan tare da ku.

Ki huta lafiya. Daga masoyinki har abada, Idrisu dan Hamidu.”

Idrisu na kammala rubuta wannan takarda sai ya dauko wata takardar ya rubuta sakon gaisuwa zuwa ga dan'uwansa Waziri Habu, wanda a ciki ya ke sanar da shi cewa yana lafiya kuma 'yan matansu duk suna lafiya sai dai begen masoyansu kawai da suke yi. Ya tambaye shi ko yana samun labarin iyayensu da sauran ‘yan'uwansu da suka fito karatu wato Yahaya

Www.bankinhausanovels.com.ng da Bashari, da sauran bayanai dai irin na ‘yan'uwa.


Da ya kammala sai ya daure wasikun biyu ya jefa sama, kamar wasa sai ya ga sun bace, wato aljana Dailanu ta cafe ta tafi da su.

Kasancewar faruwar haka a ranar Asabar ya sa yarinya Nur ta sami wasikarta da jarumi Idrisu ya rubuta mata ba tare ba wani Bata lokaci ba, 'yan mata suna kewaye da ita amma ta kasa Karanta takardar a gabansu saboda kada zuciyoyinsu su sosu irin yadda saurayinta ya fifita ta, tana karantawa tana murmushi, da suka tambaye ta sai ta ce musu, “Abin sirri ne, kuma sirrin irin na masoya biyu masu matukar begen juna.”

. Sai abin ya zame musu abin wasa da dariya, har maganar ta shiririce.

Can sai Nur ta ce wa aljana Dailanu, “Don Allah ko za ki taimaka, sako za mu ba ki zuwa Kasar Arewa.”

Ai kafin ta kammala sai Dailanu ta yi farat ta ce, “Haba Nur, ai ni yanzu tsakaninmu ya wuce ki roKe ni wani abu don ni ‘yar'uwarku ce, sai dai ko bambancin cewa ni ba'yar Adam ba ce kurum.”

Aljana ta Kara da cewa, “Wannan dan Karamin aiki, kin san kuwa in na ga dama yau cikin sa‘'a uku zan iya zagaye duniya sau biyarP”

Www.bankinhausanovels.com.ng
Nur ta ce, “to ranki ya dade, ai ban ce ina jayayya ba.” Suka yi dariya gaba daya.

Sai Nur ta ce, “Wannan takarda ta Wazirin Kasar Arewa ce, Waziri Habu, dan'uwan_ saurayina. Jarumin jarumai Idrisu dan Hamidu ne ke so a kai masa.”

Budurwar Waziri Habu tana jin an ambaci sunansa sai ta tambaya, “Wane Habun ne wai kuke ta magana ne? Ko wanda dai na sani ne Habu dan Hamidu?”

Nur ta amsa, “EF, shi fa. Af, Fa'izah ke ce budurwar tasa da aka ce muna tare?”

Ai fa sai yarinya ta mike tsaye tana ta Kwalla ihu, “Habuna ne, Habuna ne, ni zan tafitare da Dailanu.”

Ko kadan ba su yi fushi da ita ba, hasali ma sai suka shiga lallabar ta don sun san yadda so ya ke, suka nuna mata cewa ai su ma duk suna da masoya amma suke hakuri.

Wata daga cikin 'yan matan ta tambayi budurwar Waziri Habu, “Kina son tona wa Dailanu asiri ne, a halaka ta?”

A haka suka samu suka fara ciwo kanta kafin Bingyel 'yar Fulani matar Bashari ta yi wa Nur wata tambayar, “Ko kina nufin Habu dan Hamidu yana da yaya Idrisu da abokinsu Bashari>?”

a Www.bankinhausanovels.com.ng Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?”

Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.”
Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan'uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.”
Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk 'yan'uwa muke ba mu sani ba?”

"Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su.

Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.”

A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sama ta fado jikinsa.

Firgigit ya dan tsorata kadan kafin dai ya yanke
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...