YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA 


lallai dakin ya kasance ma‘abucin fitilu masu haske a bayansa don ya rika haska musu wasanninsu. Yana so kuma a kammala wannan aiki ne a cikin kwanaki uku. Kartin aljanun nan suka ce an gama sannan suka bace. Wata rana suna zaune suna tsotson tatsattsun kayan marmari, shi kuma Sarkin aljanu yana kashingide a kan kilishi, wato kwana uku ke nan da ba da wancan umurni, sai suka ji wata irin rugumniya, aljanun nan sun dawo. Suka zo suka fadi suka yi gaisuwa tare da 


ZAMU TASHI 

cewa ga lambun nan ya shiryu. Sarkin aljanu ya cewa ‘yan mata su leKa ga lambunsu can an gama, suka tashi tare da shi suka je taga suna leKawa, sai ga lambu an ajiye shi a gefe shirim, kuma abin mamaki shi ne babu abin da babu irin na lambu a ciki. Shi wannan lambu dai da bakin Karfe aka yi shi, daga baya kuma aka cika shi da wani irin rairayi mai launi iri-iri. Itatuwa kuwa har da irin wadanda ba su sani ba akwai. Kai daga gani ka san aikin aljan sai dai kallo kawai. Suka yi ta mamaki don ba su taba ganin haka ba. Sarkin aljanu ya yi tambaya, “Ko wannan lambun ya yi” Nan da nan suka ce, “Kwarai kuwa ya yi, fiye da yadda muke zaton zai iya yiwuwa.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Ya umurci aljanu su dauki lambu tare da yarinya Nur a ciki don ta nuna musu inda take so a ajiye. Kafin Kiftawa suka yi sama har cikin sararin samaniya, suka iso wannan daji, suka yi ta zagayawa Kasa-kasa har sai da ta hango wadannan dakuna biyu sannan tace a ajiye mata lambun kusa da dakunan, amma Koramar ta raba tsakani.Shaihin malami Ibrahim ya ci gaba da yi wa saurayi Idrisu bayani cewa, “Ina daga nan ciki sai na ji diririm, in leKa sai ga lambu shirim, na komo cikin dakina cike da ta'ajjubi mara misaltuwa. Bayan an sauke lambu kuma ya zauna sosai, sai yarinya ta shige cikin dakin nan na tsakiyar lambu ta umurci cewa a dauke ta a cikin sa a maida ta wurin sauran 'yan‘uwanta, can inda Sarkin aljanu ya ke. Da komawarsu sai Sarkin aljanu ya umurci aljanu uku da umurnin cewa a kullum dare su riKa zuwa suna daukar ‘yan matan nan suna kai su, in sun gama wasanninsu sun shiga cikin daki a dauko su a dawo da su. Kuma kamar yadda ‘yan matan suka bukata, Sarki ya ba da umurnin cewa duk in an kai su, to aljanun su riKa nisantar su sai kamar bayan sa‘o'i biyu sannan su dawo inda suke, don su rika samun cikakkiyar damar sakewa da walawa ba tare da sa ido ba, a matsayin su na ‘yan mata. Haka aka ci gaba da yi, a kullum in dare ya fara shiga sai aljanun nan su zo su kawo su wannan lambu. Su yi wasanni da kade-kadensu, har sai in sun kusa kammalawa sai ‘yata Nur ta zo ta gaishe ni. Ka ji dalilin wannan lambu ke nan, wannan yarinya da kake gani tauraruwar cikin su kuma ita ce Nur din, wato ‘yata. Har yanzu suna nan a wancan gida da aljanin nan ya gina, kuma duk wannan shirye-shirye da muke yi har yanzu Sarkin aljanu bai sani ba.” Dattijo ya dauki ruwa ya kurba sannan ya ci gaba da , cewa, “Muna nan muna ta fatan Allah Ya kawo wani wanda zai iya fuskantar wannan Kalubale na ceto 'ya'yan jama'a, kwatsam sai ga ka, kuma wani abin sha'awa da burgewa na gan ka tare da wannan shahararren doki, kuma ga ka saurayi Kakkarfa kuma kyakkyawa, sannan kuma ga shi kana da son yin ilmi. Shi ya sa na hakiKancewa kaina cewa kai ne za ka karya wannan aljani barawon ‘ya'yan mutane. Da farko da ka zo idan ba ka manta ba na dan jarraba ka, na ce kada ka yarda ka makara, to dalili shi ne ba a son namiji ya cika barci da yawa. Haka nan kuma lokacin da kake jin waKoKin ‘yan matan nan, in ka tashi za ka tsallaka zuwa cikin wancan lambu amma ka ji haniniyar dokinka hankalinka kan dawo maka ka juyo, to da a ce ka biye wa zuciyarka ka tsallaka ba ka ji shawararsa ba, to da kuwa kai da shi dokin naka kun rabu ke nan, amma sai ka yi sa'a ka hankalta da ishararsa. Ya kai dana, yaki kuma da nake koya maka don ka san hiloli ne da dabaru irin na yakin tare da kuma juriya, kuma ga shi kana da doki wanda babu mai irin sa, kuma ga shi za ka sami takobi da mashi da kuma darduma, duk kayayyakin ban mamaki. Ya kai Idrisu, yau shekara daya ke nan kana zaune a wurina. A nan ka Karu da yawa na daga abin da ilmi mai yawa da sanin hikimomin rayuwa. Ina son in sanar da kai cewa gobe da Asuba, takobi da mashi da sirdi da darduma za su fito daga cikin wannan rijiya, kuma daga daren yau ‘yata ba za ta sake zuwa wannan wuri ba, ni kuma zan koma garinmu ba zan sake ganin ta ba sai lokacin da kamar yadda muke fata, ka sami nasara a kan Sarkin aljanu ka ceto su, sai dai kuma zan ci gaba da samun labarinta daga wurin dalibata aljana Dailanu, don kowace Asabar takan je wurinsu. Mai yiwuwa tambaya ko tunani ya iya zuwa maka a cikin zuciya cewa ni da na san duk wannan sirri me zai hana ni zuwa da kaina? To ya kai Idrisu lallai ya kamata ka san cewa wannan ba aikin tsoho iri na ba ne, a'a, wannan aikin yaro ne maijini ajika. Kuma ina kyautata zaton kai ne Allah Ya nufa da dacewa da wannan falalar. Saboda haka sai ka shirya, don kuwa gobe za mu rabu, sai kuma Allah Ya sake hada mu. Ka je ka kwanta don yanzu dare ya yi.” Saurayi Idrisu ya koma dakinsa yana mamakin irin wannan labari. |Www.bankinhausanovels.com.ng Ya yi rigingine, ya tsunduma cikin tunani, shi da ya fito neman ilmi amma kuma ga shi zai Kare masa da gwagwarmaya. Ya yi tunanin ko ya tafi abin sa ne kafin wayewar gari, sai kuma ya tuna da karamcin malaminsa dattijo Ibrahim, kuma ya tuna da yarinya Nur, ‘yar malaminsa da ke ciki Kangin Sarkin aljanu, ya kuma tuna irin kyau da cikar halittarta tare da tabbatar wa kansa cewa matuKar ya tafi ba ya ganin ta, to tabbas rayuwarsa za ta Kare ne cikin bege da da-na-sani. Yana cikin tunanin yadda zai fuskanci duniya, sai ya ji wakar yarinyar nan ta iso, ita da sauran tawagarta suna rera waka mai dadin ban mamaki. Idrisu ya fito waje ya zauna kusa da dokinsa Jagora yana wasa da gashin wuyansa. Yanzu kam Idrisu ya fahimci bakin zaren, saboda haka wakar da suka sa ta bankwana, nan da nan ya fahimci abin da take nufi, wato ba za su sake dawowa wurin ba daga wannan dare. Can sai yarinya Nur ta sauya salon wakar tana kiran sunan saurayi Idrisu tana yi masa sai wata rana, sai sun hadu. Ta dago hannunta tana yi masa sai wata rana shima yana mayar mata. Bayan duk sun kammala, sai ‘yan matan gaba daya suka shige cikin dakin lambu, shi ma Idrisu sai ya tashi ya shige cikin nasa dakin, ya haye gadonsa yana ci gaba da tunani. To ashe ‘yan matan ba tafiya za su yi ba, a'a, don kuwa bayan wani lokaci sai suka fito daga cikin wannan daki suka nufi dakin dattijo Ibrahim, suka gaishe shi kuma suka yi sallama da shi, suka rabu suna kuka. Malam ya yi musu du’a'‘i, kuma ya tabbatar musu cewa in Allah Ya so Zai bai wa Idrisu nasara a kan Sarkin aljanu. A haka suka yi sallama, ko da yake kafin nan sai da Nur ta bai wa mahaifinta takarda zuwa ga Idrisu. Lokacin da suka nufi lambu, sai dattijo Ibrahim ya fito ya tsaya yana kallon su har sai da suka isa cikin harabar lambun nasu sai suka tsaya, wato yau ba su shiga cikin dakin lambun ba, kuma kasancewar a daren akwai hasken wata sosai ana iya hangosu sosai. Idrisu yana cikin dakinsa sai ya ji ruagumniya, nan da nan ya fito don ganin ko mene ne, sai ya ga lambun su Nur a cikin sararin samaniya yana tafiya, kuma ga 'yan matan nan suna dago musu hannu shi da malaminsa, can kuma kafin ‘yan matan su Bace sai yarinya Nur ta sako wa Idrisu adikonta, nan da nan ya yi iyakacin KoKarinsa ya ruga kafin adikon ya fadi Kasa ya cafe shi ya dora a wuyansa, ya sake dubawa ko zai gan ta ko da sau daya ne amma ina! Bayan ‘yan mata sun bace tare da lambu, sai Idrisu da malaminsa suka ci gaba da kallon sama gefen da lambun ya yi, suna zubar da hawaye saboda irin wannan rabuwa, wato rabuwar da babu wanda ya san lokacin da za a sake haduwa sai Allah, in ma za a hadu din. Dattijo ya yi kuka kamar ransa zai fita ta yadda sai  da Idrisu ya tashi tsaye sosai wurin rarrashin sa tare da alkawarin cewa in Allah Ya yarda sai ya dawo masa da ‘yarsa ko da kuwa wurin Kokarin haka zai rasa ransa ne. Da gari ya waye, sai malam ya cewa Idrisu, Www.bankinhausanovels.com.ng “Zo mu je wurin rijiyar nan, ko sakonmu ya iso.” Ya wuce gaba Idrisu yana biye. Suna isa kuwa sai suka ga rijiya ta ciko har baki, ruwa ya dago sirdi da darduma da takobi da mashi. Suna ganin haka sai murna ta kama su tare da farin ciki mai yawa. Dattijo ya ce, “Je ka dauko, naka ne.” Nan da nan Idrisu ya nufi rijiya ya sa hannu ya kwashe wadannan kayayyaki, kuma wani abin mamaki shi ne yana dauke na Karshe sai kawai rijiyar nan ta hadiye ruwanta kamar baa taba yi ba. Suka koma dakin malam suna ta duba wadannan kayayyaki suna mamakin su. Ya cewa Idrisu, “Na yi farin ciki da Allah Ya sada mu da kai, bayan mun yi zama na shekara daya tare ga shi za mu rabu, kuma rabuwa ta mutunci. Ina so ka sani ya kai Idrisu cewa za ka yi tafiya mai nisa, za ka shiga gwagwarmaya mai yawa, to amma kada ka damu, in Allah Ya yarda kana tare da nasara. Kai dai ka ji tsoron Allah. Ina fata za ka zama namiji mai juriya da dauriya, kuma ka zama mai yawan gaskiya da riKon amana. Kada ka yi zalunci, kada ka yi girman kai, kada ka yarda a cuce ka, kai kuma kada ka cuci kowa. Ka zama kana mai neman ilmi har zuwa Karshen rayuwarka, kuma kada ka kuskura ka yi wasa da addininka.” Bayan ya gama yi wa Idrisu gargadi, sai ya mika masa wata takarda ya ce masa, “Nur ce tace in baka.” Nanda nan Idrisu ya sa hannu ya karba. Yana budewa sai idanunsa suka ci karo da rubutun yarinya ‘yar Shehin malaminsa, Www.bankinhausanovels.com.ng “Daga Nur ‘yar Ibrahim, zuwa ga kyakkyawan saurayl Idrisu, gaisuwa zuwa ga wanda raina ya ratayu da so da kauna da kuma bege. \na sanar da kai, ko da yake ba mu taba magana ba, cewa ina godewa Allah da kuma matukar murna da alfaharin cewa kana nan tsundum cikin kogin Soyayya musamman saboda abubuwan da na luradasu. Ni fa irin nawa imani da fahimtar ke nan. Ko ba haka ba ne? Ya kai wanda nake so tun ranar da na fara hango ka a wannan daji, duk lokacin da na yi tunanin ka sai in ji nishadi saboda tsananin so da nake yi maka. Kai ne kadai mutumin da a doron duniyar nan na taba jin cewa na kamu da son sa. Sai dai kash!... Jin dadin soyayyar tamu ba na yanzu ba ne, saboda mugun aljanin nan. Na san cewa malaminka, wato mahaifina, ya ba ka labarin komai, kuma babu wani dalili na maimatawa. Ya kai farin cikin ganina ina yi maka addu'a zuwa ga nasara, kuma ina so ka yi kokari matuka wurin karya wannan makiyi na Allah. Wannan fama za ka yi ne saboda abubuwa masu dama. Daga ciki na farko in ka sami nasara, to ka taimaki ‘ya'yan mutane da wannan aljani ya sace har mu hamsin da dori wanda har yanzu maganar nan da ake yi, akwai yiwuwar in ya ga wata mai kyau ya karo. Na biyu malaminka zai kara farin ciki da murna da kai har abada. Sannan kuma sai na uku, wato soyayyar da nake zato a tsakani. Ko da yake duk wadannan kadan ne in an auna da irin tasirin da wannan yunkuri naka zai iya samarwa dunbin al’umma. Ya kai Idrisu, zan yi maka wani alkawari, in Allah Ya ba ka nasara akan wannan aljani kuma ka ji cewa ba ka so na ko kuma ban yi maka ba, to na yi maka alwashin kowacce kake so daga cikin 'yan matan nan daga daya har hudu, in kuma duk ciki babu wadda ta yi maka, to zan ba ka kawata aljana Dailanu. Kai na tabbata dole ne maa cikin ‘yan matan nan ka sami wadda ta yi maka, don dukkan su zababbu ne a garuruwansu a fagen kyau da natsuwa ko kuma har da ilmi, shi ya sa ma na hada da ce maka ‘dole’. Amma kafin lokacin, za mu rika samun labarin juna a wurin Dailanu. Ka huta lafiya, ya wanda nake so Idrisu. Taka, har abada, Nur ‘yar (brahim." Bayan Idrisu ya kammala karanta wasika sai murna Www.bankinhausanovels.com.ng dadi suka lullube shi, ya yi kamar ya yi tsuntsu ya bi ta, kuma tun a wannan lokaci sai ya riKa jin cewa daace za su hadu da Sarkin aljanu Sham'una, to lallai da sun kara, can kuma sai Idrisu ya kanne fuska, zuciyarsa ta baci don a cikin wasiKar Nur ta ce wai in ya ji ba ya son ta za taba shi wata daga cikin Kawayenta. Sai ya cewa malaminsa Shaihi Ibrahim, “Allah Ya gafarta malam, duk irin abin da ka fada mini na dauka kuma na amince, tare da murna gami da godiya zuwa gare ka a game da duk abubuwan da ka yi mini. Ina rokon Allah Ya yi maka sakayya da alheri, kuma ina shaida maka ya malamin malamai cewa, ko da babu wani tallafi na kayan aiki wato makami da muka rika, to ina jin in na ga aljanin nan, zan iya taren sa gaba da gaba, kuma ko don wadda nake dimaucewa a kan ta,Www.bankinhausanovels.com.ng zan iya sadaukar da raina.” Malam ya amsa masa cewa, “Na gode, sai ka yi niyya, Allah Ya ba da sa‘a, kuma Ya yi maka albarka.” Idrisu ya nufi dakinsa, ya shirya litattafansa ya zuba su a cikin jaka, ya dauko sirdi ya dora wa Jagora, ya rataya takobi, ya riKe mashi, ya dora darduma a kan sirdi ya yi tsalle ya haye dokinsa. Yana hawa sai dokin ya yi wata irin haniniya, ya yi rimi, sannan ya koma ya tsaya cak kamar dai yana nuna ishara da yin murna. Shi kuwa Idrisu idan ka gan shia kan dokin, to ka san lallai akwai magana, da ganin sa ka ga jarumi, kyakkyawan jarumi kuwa. Ya nufo dakin dattijo a daidai lokacin da malamin ke fitowa. Shaihi yana ganin sa sai ya karkada kai. Idrisu zai sauko amma sai ya hana shi. Ya ce masa, “Ya kai dana Idrisu, in an yi niyya baa warwarewa, zauna a kan dokinka.” Suka yi addu'a da neman taimako daga wurin Ubangiji, Idrisu ya juya ya nufi Gabas yana hawaye shi ma malam yana yi.yA dan yi ‘yar tafiya kadan, amma gajen hakuri ya sa shi waiwayawa don kallon malam a karo na Karshe, amma ina, yana juyawa sai ya ga kamar baa taba yin komai a wurin ba, babu malam kuma duk dakunan nan guda biyu sun ace, ita ma rijiyar ta bace abin ta sai dai Koramar kadai. Ya nutsa cikin daji, ya ci gaba da kutsawa tsakanin duwatsu da kwazazzabai da namun daji. Wani lokaci ya yi kwana da kwanaki ruwan sama na dukan sa, wani lokaci mura ko zazzabi mai zafi su kama shi, bayan 'yan kwanaki ya warke. Haka ya yi ta tafiya cikin wannan bakin daji har na tsawon watanni uku inda a Karshe ya iso gefen wata teku baki Kirin, ga ta nan ta tafi Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, sai ruwa ne ke toroko yana gunji abin gwanin ban tsoro, babu wata hanya, saboda haka sai ya yanke shawarar zaunawa a wurin don sassaka danKaramin jirgin ruwa da zai iya daukar sa shi da dokinsa.Ya sami wuri ya hada 'yan bukkoki guda biyu, daya tasa daya ta Jagora. A kullum sai aikin sassaKar jirgi ya ke yi. A hankali bayan kamar makonni uku ya kammala. Ya debi kayan marmari mai yawan gaske da kuma ciyawa saboda dokinsa, suka shiga suka mika cikin teku. Yana ta tafiya bai san inda ya dosa ba saidai inda Allah Yakaishi. Kwanaki ashirin da biyar ke nan yana tafiya, can sai ya hango wani abu baki Kirin kamar dutse, amma da ya sake matsawa sai ya tarar ashe wata halitta ce ta cikin ruwa wadda bai taba mafarkin irin ta ba. Saboda haka sai ya karkata jirginsa ya nufi wani gefen. Ya ci gaba da nutsawa cikin teku ba dare ba rana, can kuma sai ya hango wani Katon jirgi, shi ma jirgin ya hango shi, saboda haka sai suka nufi juna har suka hadu. Wannan jirgi yana dauke da jarumai ne na wani shahararren Sarki su kimanin mutum dubu da dari biyu, kowane mutum daya da ke cikin wannan jirgi da zarar ka gan shi ba sai an yi maka wani dogon bayani ba, za ka gane cewa jarumi ne. Nan da nan jarmai din wancan jirgin ya ba da umurnin cewa a kai wa Idrisu tallafi shi da dokinsa, a saka su a cikin babban jirgi. Kafin ka ce haka har an cika aiki. Jarumai suka kewaye Idrisu a cikin jirgi suna mamakin kyan dokinsa, wasu kuma suna mamakin kyan shi kansa Idrisu din, wasu kuma mamakin kayan yakinsa suke yi tare da mamakin abin da wannan saurayi ke yi shi kadai a cikin teku. Jarmai ya tambayi Idrisu, ya ce, “Ya kai wannan yaro mene ne labarinka, kuma mene ne labarin abubuwan da kake tare da su na mamaki?” Idrisu ya amsa masa cewa, “Ya kai wannan shugaba, sunana Idrisu dan Hamidu, kuma labarina yana da wuyar fada, to amma idan kun fada mini naku labarin, to zan dan gutsura muku nawa. Saboda haka ina son ganin shugabanku baki daya.” Jin wannan kalami na Idrisu sai jarmai ya hasala, ya daka wa Idrisu tsawa, “Kai yaro ka san da wanda kake magana kuwa? Kada ka kuskura in yi fushi da kai.” Sai Idrisu ya ce, “Ya kai wannan shugaba ai babba ba ya saurin fushi.” Kafin ya rufe bakinsa har wani jarumi kusa da shi ya wanke shi da mari, ya Kara dagawa zai Kara sai Idrisu ya yi wuf ya rike hannun. Jarumin ya yi iyaka KoKarinsa don fisgewa amma ya kasa, sai da Idrisu ya ga ya wahala matuka sannan ya sake shi. Mamaki ya kama jarumin kasancewar tun da ya ke babu namijin da ya taba yi masa abin da wannan yaro ya yl masa yanzu. Jarmai ya ba da umurnin a cafke Idrisu don a kai shi wurin Sarki. Sai Idrisu din ya ce, “Ya ku jarumai ku ~ dakata, ni ba fada ne ya kawo ni ba, saboda haka kada ku ce za ku kama ni da Karfi. Mu je wurin Sarkin naku.” Dukkan su suka dunguma, suna gaba yana biye da su shi kuma dokinsa Jagora na biye. Suna isa sai aka ce ya dakata, aka shiga aka sanar da Sarki cewa ga wani saurayi jarumi amma mai girman kai. Nan da nan ya ba da umurnin a shiga da shi, sai Idrisu ya rike ragamar dokinsa, ya jawo shi suka shiga harabar tare. Sarki ya yi mamakin yadda ya shigo wurinsa da doki, Idrisu ya zauna a gabansa ya yi gaisuwa har yadda Sarkin ya yi mamakin ladabinsa, kuma ya yi mamakin kyan dokin da sirdinsa. Sarki da kansa ya tashi yana kallo. Bayan ya koma ya zauna, sai ya cewa Idrisu, “Ya kai wannan saurayi an ce kana da girman kai, amma kuma ni ban ga haka ba.” Sai Idrisu ya amsawa Sarki cewa, “Ranka ya dade ai da ma an ce ba a mugun Sarki sai mugun bafade.” Sai Sarki ya ce, “Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, kana da abin da nake mamaki, na farko ka yi kama da Wazirina, na biyu kuma dokin nan naka da sirdi da takobi da mashinka ban taba ganin irin su ba. Babu shakka akwai wani lamari game da su. Ya kai wannan saurayi mene ne sunanka? Mene ne labarinka da yadda muka tsince ka a cikin teku?” Wurin amsa wadannan tambayoyi sai Idrisu ya ce, “Allah Ya ba ka nasara sunana Idrisu dan Hamidu, kuma labarina ba ya faduwa a gaban jamaa haka.” Nan da nan Sarki ya ba da umurnin cewa kowa ya fita. Www.bankinhausanovels.com.ng Lokacin da suka zama su biyu sai Idrisu ya gutsura wa Sarki wani bangare daga cikin labarinsa, ya ce, “Ya kai wannan Sarki ni matafiyi ne, ina so zan je wurin wasu tsibirai ne can a bayan duniya. Dalili kuwa shi ne don in yaki wani mugun aljani wanda ya sace ‘yan mata 'ya'yan mutane ya tara su a can, su kamar hamsin da doriya. A can ya yi musu gida, kuma su wadannan duwatsu suna cikin wata babbar teku ce. Wannan wuri yana da wahalar zuwa.” Da Sarki ya ji zancen Idrisu sai ya yi wuf ya rungume shi yana zub da hawaye. Ya ce, “Ya kai Idrisu ina maka fatan nasara. Ka gan mu nan mu ma mun fito neman 'yata ne. Ita ke nan guda daya a wurina, na karantar da ita fanni daban-daban na ilmi, ina alfahari da ita, ina sonta so mai yawa saboda hankalinta. Muna cikin shirye-shiryen yi mata aure da wani saurayi wanda shi ma bako ne, sai abin da ya HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATA KAYA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...