YAKANA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAKANA BOOK 2  CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

- - Post a Comment

 YAKANA BOOK 2  CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIRWww.bankinhausanovels.com.ng 
gaba da azalzala da azabar soyayya, wadda ke linkuwa a bayan kowacce dakika. Jikinta ya soma rawa, tana son cewa ya tashi ya ba ta waje ta samu iska amma ta kasa. Kallon ta yake yana (observing) da ido, da zuciya. Gaba daya yanayin ta ya sauya, ya nuna wata mace da ke azabtuwa da soyayya da sha’awa mai yawa. 


Amma kawaici da kau da kai ya rinjayi komi, ya tabbata idan ya tafi ya bar ta cikin wannan halin, Allah ba zai yafe mishi ba, amma tunanin Hadiza ya danne komi. Tattalin girmansa da mutuncinsa a idanun yarinyar ba zai bar shi ya aiwatar da abinda zuciyoyin su da gangar jikin su ke so ba, idanun shi a juye yake kallon ta, gangar jikin shi babu inda bai kadawa. Ya soma kokarin saisaita kansa, in azabar soyayya ce ai ya fita dandana, ba tun yau ba. 


Ya janyo brief case ya fiddo daurin kudi masu tudu ‘yan awolawo ya ajiye a gefen ta, sannan ya mika mata form din JAMB Online. 


Ta dan ware ido tana kallon sa da alamar jin dadin hakan sosai a kwayan idanun ta, ya kawar da fuskar shi gefe ya ce, 


“Zan bude maku account da Afri Bank in Allah ya kai mu gobe, in na wajen ki sun kare kuna da bukata sai ku je ku diba. Akwai sabon direba na aje muku duk inda kuke son zuwa ki kira shi a waya ki gaya masa, ni zan tafi jibi insha Allahu sai Allah ya nufe mu da dawowa. 


To amma Fati, ba zan samu ko da kalmar Allah kiyaye hanya ba, daga Fatin da ba zan kara gani ba, sai bayan wasu shekaru har guda biyu?” 


— = 


Hawayen ya kara zubo mata, ta yi saurin sharewa da bayan hannun ta. Ya ce, “Girl, ina so in san damuwar ki....., a kalla ko ban yi miki maganin ta ba, ina da shekarun da zan ba ki shawara a kanta. Ta vangare na dai duk hanyar da nasan zan bi in gyara kuskure na nabi, amma kin ki bani hadin kai. You are a darling! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi!!” 


Ta yi hanzarin dagowa ta dube shi, kallon ta yake cikin kwayar idon shi, da wani lallausar murmushi makale a gefen bakin shi. 


“Gaya min mene ne damuwar ki?” 


A hankali ta ce, “Babu”. 


“Ba kya bukatar komai?” 


Nan ma ta ce, “Eh, Allah ya kai ku lafiya!’”. 


Ya ji dadin addu’ar da ta yi mishi, sai dai ba irin wannan rabuwar yake so su yi ba, ta rashin dadin zuciya. 


Ya kama tafin hannun ta cikin nashi, “Ba za ki gaya min abin da ke sanya ki kukan ba?” 


Ta ce a ranta, “Za ka yi min magani ne?” 


Magana ta yi a zuci, ba ta san ta fito, ta shiga kunnuwan sa ba. 


“Idan ina da shi me zai hana in yi miki?” 


Ta ce, “Bani da damuwa, ba sai mutum yana da damuwa yake yin kuka ba, wani zubin mutum yana yin kukan don ya ji dadin ransa”. 


Ya yi murmushi a kaikaice ya lakaci kuncin ta da dan alinsa, “Mu kwana lafiya, amma ina rokon ki 


duk wasu inconveniences ki yafe min su”. 


Ta ce, “Babu wani inconvenience game da kai a tare dani, kada ka manta ka ce ni kanwar ka ce. Idan Yaya Mukhtar ya yi min laifi zan kullace shi ne, ko zan kasa yafe mishi?” 


Ya yi kirr! Da ido yana duban ta da wani irin sassanyan kallo. Tattausar muryar ta da nutsuwar ta na burge shi har bai son a daina hirar, ita kuma so take a gama, saboda yadda yake kara ruruta wutar son shi a zuciyarta 


Nana ta yi motsi za ta soma kuka, dukkan su suka juya gare ta, suka mika hannu a tare don su dauke ta, nata hannun ya riga sauka a kan Nana, don haka nashin sai ya sauka a kan nata. Dukkan su babu wanda bai ji a jikin shi ba. Ta yi saurin sakar mishi Babyn, ta dunkule hannun ta. 


Ya dauke ta ya kai kafadun shi ya mike tsaye yana safa da marwa da ita a dakin don ta koma barci, ya kasa fita a dakin Fati, mai wani irin sihirtaccen kamshi da ba zai ce na kowanne turare ne ba, haka nan gauraye da ravar A.C mai kwantar da hankali. Dakinta ko tsinke babu saboda masifar tsafta. Bai ki ba su kwana a hakan, yana jin sassanyan sautin ta mai motsa zuciya, ta yl mata rahma ko da ba da son ran mutum ba. 


Ya kwantar da Nana cikin dan gadon ta dake kan gadon Fati, ya mika mata hannun daman shi, cikin sigar son a yi hannu ya ce, “Can we be friends?” 


Murmushi ta yi, ta sarke hannuwan ta a baya, ‘““A’a, ai ka ce ni kanwar ka ce wadda take zaman 


lalata kuruciya........ ” 


Daga yadda take furta maganar za ka karanci (bitterness) wato dacin da maganar ta yi mata a kan harshen ta. 


Ya ce a ransa, “Baki shi ke yanka wuya....”. Yana da tabo mai yawa a zuciyar ta, wanda ke dakusar da karfin soyayyar sa da ta soma shigar ta. Dole ya wanke kanshi, domin karfi da yaji Fati na neman zamowa wani vangare na zuciyar sa cikin dan kankanin lokaci. 


Ya ce, “Mun yi magana a kan all the inconveniences, kin ce kin yafe su, amma why kike maida hannun agogo baya?” 


Sai ta yi murmushi, ita ma ta mika mishi tattausan hannun daman ta, suka sarke su cikin na juna. Kowanne siririyar fatar bakin shi dauke da murmushi. 


Dai-dai lokacin da suka ji kiran sallar asubahi a cikin kunnuwan su, a sannan ne suka mike domin haramar sallah cike da mamakin tsayin lokacin da suka vata suna hira. 


Washegari ma bai samu zama ba, suna ta zirgazirga a airport na booking jirgin tashin su. Bai dawo ba sai dare, lokacin kafatanin mutanen gidan sun yi barci. 


Bai nemi kowa ba shi ma ya ci abincin da suka aje masa ya yi wanka ya shirya ya kwanta, amma tunanin Fati ya hana zuciyar shi sukuni, yana so ya san halin da take ciki, yana so ya sake jin sassanyar muryarta da ke yi mishi yawo a kwanya, yana so ya sake jin taushin hannun ta, yana SO....44. yana so...... Kai yana son komi nata! She is indeed a _ blessing cikin gidansa da 


rayuwarsa.... She is also a DARLING farin cikin kowanne da namijin da ya san ciwon kansa. Amma ba za a gane hakan ba farat daya, sai wanda ya yi zama da ita na tsayin lokaci ya nazarce ta, amma a fuska za a fassara ta da mutum mara son magana, kidahuma mai takurawa rayuwarta. Sai an fahimce ta a hankali za a fuskanci halitta ce, wato nature. 


Ya So ya je gare ta a wannan daren da ya zamo na karshe da zai dade bai ganta ba, su raya shi da hira ta fahimta kamar yadda suka raya shi jiya. Wata zuciyar ta ce, “A kul! Kama girman ka ka rike tsam-tsam kada ta ga weakness din ka”. 


To kamun girman har yaushe ne? Shi ma ya tambayi zuciyar tasa. Tunda dai ba za a dauwama a haka ba, kuma ba zai tava sakin Fati ko ya yi mata kishiya ba, don bai da ra’ayin zama da mace sama da guda daya. 


In haka ne dole watarana za’a aje girman a gefe a ranar da Allah ya nufa. Ta riga ta kama zuciyar shi fiye da yadda biro zai iya rubutawa. 


Tana shirya masa kalaci a dining ya fito, cikin shirin tafiya, duk ta yi sanyi ta zama cool. Kodayake dama haka halittar ta take, komai cikin sanyi take yin sa, amma na yau ya fi na kullum. Ya tokare hannun shi jikin kofar dakin shi, dayan na zube cikin aljihu, ya langavar da kai yana kallon ta. Jikinta ne ya ba ta ana kallon ta, don haka ta dago kai ta dube shi, sai ta yi murmushi ta sunkuyar da kanta, 


“.,.Morning friend!!” 


Ya fada. Tare da miko mata hannu, tana murmushi ta mika masa nata. Ji take kamar in ya tafi shikenan ba za ta kara ganin shi ba. 


Daga gaisuwar bai cika ta ba ya janyo ta a hankali ya rungume ta, ya sumbaci goshinta sannan ya cika ta. 


Ta lumshe ido a hankali tana daidaita tunanin ta. Wani abu na zarya a dukkan ilahirin jikinta. Ya iso ga tebir ta karaso da sauri ta yi serving din sa, ya kama kasan hijabinta ya cire ya ajiye a kan daya daga cikin kujerun, ya ce, “A dinga ajiye shi a cikin gida, don a sha iska”’. 


Wata muhimmiyar kunya ta kama ta, saboda ‘yan kananan kayan da ke jikinta. Kukan Nana ne ya cece ta daga kaifafan idon Sulaiman, don haka ta garzaya shi kuma ya fara cin abincin kamar bai tava cin abinci mai dadi irin shi ba. 


Har karfe goma ya kasa fita, yana tare da ‘ya’ yan shi da Nana a cinyar shi suna ta bashi sautun abin da zai sayo musu yana murmushi yana rubutawa. 


Abokan tafiyar shi sun yi waya har sun gaji, yana cewa, “I am coming..... (gani nan)”. Sai da Dr. Khalil ya biyo bayan shi sannan ya mike, ya mika wa Fati Nana wadda kanta ke sunkuye. 


Ya dago havarta da hannun sa, ta lumshe ido sai hawaye ya valle. Ba sai ta fada ba ya san ko na mene ne, Fati ta kamu da ciwon da shi ma yake fama da shi, amma kawaici da alkunyar ta ya sa take voyewa. 


Yatsun shi biyu ya sa yana goge mata hawayen, kararrawar da Dr. Khalil ke dannawa ta sa dole ya amshi brief case din shi a hannun ta. Da sas


—_= 


sarfa ya juya ba tare da ya kara waiwayowa ba, da sanyin ido ta bishi har ya fice a falon. Nana da ke hannun ta na ta kuka amma ba ta san tana yi ba, yara na ta yi mata magana, suma ba ta ji me suke cewa ba, ta tafi cikin duniyar soyayya...... mai wuyar fassarawa. 


Idan wannan ita ce soyayya da Sulaiman ya dandana ta Hadiza, sai ba ta ga laifin shi ba na wulakanta ta a farko, don ba ta jin in ita ce ya mutu a yanzu za ta yarda ta kara yin wani aure a rayuwar ta, ko zata kara son wani, kwatankwacin wannan son na Sulaiman da take ji a zuciyarta, ruhi da vargon jikinta. 


Ta kara tausaya mishi kwarai game da yadda ya jure da rashin Hadiza. Idan haka rabuwa da masoyi yake, tana addu’ar Allah ya sa ita ma ya so ta ko da rabin-rabin yadda yake son Hadiza ne”. 


3K OK KK 


BAYAN TAFIYAR SULAIMAN ayuwa ta yi zafi ga Fati, komi na yanayin rayuwarta ya sauya, ta zama calm mai yin komi cikin kokari, juriya, karfin zuciya da dauriya. Soyayyar mijinta ta hana ta sukuni, hatta ‘ya’yanta sun san Auntyn su ta sauya, ta rage zama da su, ta rage walwala, sai dai Nana kullum tana jikinta. 


Ta sakar ma Alti ragamar komi na gidan, ta fiya kwanciya tsakiyar gado, rigingine da Nana a kan ruwan cikinta. Ta rasa walwala da kazarniyar ta, 


komi ya fice mata a rai, mijinta kawai take so, wanda kuma ya yi mata nisan da ba za ta kamo shi a nan kusa ba. 


Ita Alti sai ta yi zaton ciki ne, don haka take bata kulawa ta musamman. Misali da yake ta rage cin abincin gidan, sai lemu da ruwa, sai take tambayar ta ko da wani abu da kike marmari in yi miki? A lokuta da dama cewa take babu, in kuma akwai sai ta fada mata. 


A daddafe ta zana jarrabawar JAMB. Ba jimawa ta sake samun admission inda za ta karanci fannin da take so, wato Islamic Studies. 


Idan direban yara ya kai su da motar da Dr. Sulaiman ya bar musu, sai itama ya sauke ta a makaranta. 


Kullum cikin zumbulelen hijabin ta har kasa, Alti kan zauna a kofar aji ta rike mata Nana, ko su zauna masallacin Ramat su jira ta ta fito lacca. Karatun na taimakawa dari bisa dari wajen debe mata kewa da rage mata tunanin Dr. Sulaiman din da take zaton zuwa lokacin ya manta da ita. Don har yau da ya cika watanni biyar da tafiya, ko sau daya bai kira ta ba. Kai tana jin ma ba shi da nomba din ta. 


Duk sanda suka yi waya da Inna tana tambayar ta lafiyar ta da ta ‘yan jikokin ta, ba ta yin zancen Sulaiman, tana so ta tambayi Inna ko yana yi musu waya, tana kuma tsoron kada su yana yi musu ita ce ba ya nema, Inna ta yi mishi magana ya ce ta kai karar shi. Don haka ta ci gaba da jurewa ba ta yiwa Inna zancen ba. 


Shekarar farko ta kare cike da dimbin nasarori a 


gare ta, domin duk jarrabawar da ta zana ba ta faduwa. Ta kare shekarar da maki mai daraja. Nana ta yi vul tana gudun ta ko ina, ba ta tava sanin ba Fati ce mahaifiyar ta ba. Ta shiga 200 level cike da karfin gwiwa, tun Alti na zuba idon ganin ciki ya vullo mata har ta gaji ta gane ba ciki bane. 


A yau da suka tashi Karkasara suka wuce domin duba jikin Baban su da bai ji dadi ba. Yaya ta ji dadin ganin su, fes dasu cikin koshin lafiya, wanda ke nuni da cewa babu abin da suka nema suka rasa. Dr. Sulaiman ya tsaya musu a kan komi. 


Alti na tsakar gida, ita da Yaya suna daki suna hira irin ta da da mahaifi, ta ce, “Dazun nan nake ce da Sulaiman kun kwana biyu baku zo ba, ya ce karatu ne ya yi miki zafi ashe kuna tafe’’. 


Mamaki da haushi suka kama ta, wato yana kiran kowa har ‘ya’yan shi yana kira a makaranta ofishin malaman su su yi hira ya ji lafiyar su, ita ce dai ba ya kira don har yanzu yana kin ta, don rannan Munib yake gaya mata wai Daddy yana gaishe ta. 


Ta ce, “A ina ka ganshi?” Ya ce, “Waya muka yi a school”. 


Sannan ga shi yau Yaya ma ta ce yana yi musu waya. Duk inda ranta yake in ya yi dubu to ya vaci, har Yaya ta lura kamar ta yi shiru tana tunani. 


Ta ce, “Lafiya ko?’ Ta yi saurin girgiza kai, “Babu komi”. 


A dakin Baban su bayan sun gaisa, ta tambaye shi jiki ya ce ya ji sauki alhamdulillahi. 


Sannan ya ce, “Fati har gobe ba zan daina sanya miki albarka ba, saboda yadda ki kai mana biyayya kika zauna lafiya a dakin mijin ki, duk da na san ba da son ranki aka yi auren nan ba. Biyayyar ki da YAKANAH.... ni na gaya miki ba za su tashi a banza ba! 


Allah ya baki ‘ya’yan da za su yi miki biyayya fiye da yadda ki kai mana”. 


Idanun ta suka cicciko, kamar ta gaya mishi cewa har yanzu Sulaiman ba ya son ta, da yana son ta da ya damu da lafiyar ta. Amma ko ya take tsayin shekara guda bai tava cewa ba. 


Idan kuma ta yi tunanin sauyikan da ta gani a tare da shi kafin ya tafi, sai ta samu kanta cikin rudu a kan al’amuran Dr. Sulaiman, ta kasa tantance cewa yanzun yana son ta ko ba ya son ta? 


“You are darling! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi’. 


Ta tuno kalaman shi ana i gobe zai tafi. Gaba daya maganganun da suka yi a ranar take tunawa filla-filla, wadanda in aka auna su a ma’auni na hankali da tunani suna nufin Dr. Sulaiman ya sauya muguwar fahimta da akidar shi a kanta. 


To amma why yake kin neman ta a waya ko common gaisuwa ce su yi? Me hakan ke nufi? Babu wanda zai amsa mata tambayoyin ta sai shi. To ina za ta gan shi? Ta MAIRON HURE da ta ce, 


“He is far away.....” (Ya yl nisa). oe oe gE a la’asar sakaliya suka yi shiri suka nufi Bakori dukkannin su, za su yiwa Inna week end (hutun karshen sati). 


Direba Malam Habu ne ke jan su, zuwa karfe shida na yamma suna cikin garin Bakori. An yi sa’a Saude, Ruma da Anti Ramatu kannen Sulaiman duk suna gidan sun je biki sun dawo suka zarto wajen Inna. 


Don haka falon Inna yau ya yi albarka, ya kauraye da hira. Ita dai Fati ba ta magana illa in anyi abin dariya ta yi murmushi, suna son yarinyar sosai saboda sanyin ranta. 


Anti Ramatu da yake sarkin barkwanci ce, ta ce, “Fati sai yaushe za mu zo suna ne? Mun kosa fa Nana ta samu kani ko kanwa”. 


Kunya ta kama ta, musamman da yake Inna tana wurin. Ta rufe fuska da mayafinta, haka suka yi 


ta tsokanar ta su lallai suna jiran baby da Yayansu ya dawo. 


Wayar Inna ta yi kidi tana neman agaji, Inna ta amsa cikin nutsuwa don ta gane lambar ta Sulaiman ce. 


Bayan sun gaisa ya ce, “Hirarrakin me nake ta ji haka?” 


Ta ce, “Su Ruma mana, sun sanya Fati gaba duk sun hanata sukuni, gasu nan sun zo dukkannin su baka ga yadda Nana ta yi wayo ba”. 


Ya lumshe ido yana sauraron Inna, amma bai ce ta ba shi Fati ba sai ‘ya’yansa. Sun dade suna ta shirmen su kamar ba kudi suke narkarwa ba, har gwalantun Nana an sanya mishi ya ji, sannan suka shiga gaisawa da kannen shi. 


Ya ce, “Ina Khalid?” 


Inna ta ce ya je Malumfashi ta aike shi wajen Inna Atika kanwar ta. 


Cike da kewa ya yi sallama da su, ya koma ya kwanta ya ta da kai da hannayen shi a rest chair irin kujerar nan da turawa ke sakawa da zaren roba da katako. 


Ya mika hannu ga zungureriyar robar coca-cola ya daga, ya tashi zaune yana daddaka. Sanyin lemon da karfin ‘gass’ din shi na soya mishi makoshi, amma bai kula ba. 


Ga wanda duk ya san Dr. Sulaiman-Sulaiman a da, lokacin Hadiza, ya kuma gan shi a yanzu, to ba zai gane shi ba. 


Gaba daya ya rame, ya kara yin duhu, sai dai hakan bai voye zahirin kyawun halittar sa ba. Ba abin da ya sa gaba sai abin da ya kawo shi, sai dai 


Post a Comment for "YAKANA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...