YAKANA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAKANA BOOK 2  CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

- - Post a Comment

 YAKANA BOOK 2  CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

Www.bankinhausanovels.com.ng 
hammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta. Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta. Dago idon nan da za ta yi sai idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai tsokar zuciya a tare da ita. Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr. Hadizah...... ‘“‘Wannan yankar sai an yi dinki”. Ya fadawa Allti. Cikin sanyin murya ta ce, “Ai shi ya sa na ce muje asibitin’”’. 


Ya ce, “Ba damuwa bari in dinke mata”. 


Ya fara da yi mata allurar ‘anaesthesia’, sannan ya fara dinkewa. Idanunta a rufe ba ta bude ba har ya gama. 


Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama ko bai gama ba. 


Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din. Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya dinga hango rashin kyautatawar sa na tsanar jinin Hadiza da ba ta tsare mishi komai a rayuwa ba. Auren su da aka yi ya tabbata ita ma ba da son ranta a kai ba, soyayyar Hadiza da ta yi mishi yawa, ita tasa yake kin kowacce mace. Ita kuwa Fati ba zai ce ga dalili ba. 


Ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai, ina ruwan shi da tsarin rayuwar ta? Tunda ba a goshi zai lika ta ba? Ya soma kokarin goge muguwar kiyayyar da yake yi mata ta hanyar baiwa zuciyar shi uzuri iri daban-daban ga duk 

muguwar hujjar da ta kawo. 


Sai dai muhimmin abin da iyayensu suka hada wato AURE da mu’amalan auratayya, ba zai tava yin shi da wadda ta zamo kanwa ga Hadiza ba. Duk da ba haramun bane shi kam ya haramtawa kansa, an halicce shi kadai don Hadiza, kuma har ya koma inda Hadiza take ba zai kara mallakawa wata diya mace soyayyar shi ba, babu gurbin da zai iya jogana son wata. 


Sai dai shi kansa yana mai kalubalantar tunanin sa na cewa zai iya dauwama a haka ba tare da mace ba, kasancewar ta wani vangare na rayuwar dan adam, da kuma ganin tun ba a je ko ina ba ya fara kwana cikin halin ha’ula’i. Dole ya dau matakin da zai kawo karshen duk wannan, wato ya yi nisa da Fati, tun YAKANAR ta, kyautatawar ta, hakurin ta da juriyar ta basu ciwo galabar tattaurar zuciyar sa ba. 


Jin ya yi shiru ba ya dinkin kuma bai saki hannun ta ba, Fati tayi saurin bude idon ta, suka yi ido hudu da Sulaiman dan Sulaiman da Inna Halima. Ashe haka Baban Munib yake da kyau? Ban tava sani ba? Fati ta ce a zuciyarta. 


“Ina ma a ce yanda yake da kyan nan haka zuciyar shi take da kyau?’”. Zuciyar ta kara tambayarta. Ta samu kanta cikin wani sabon yanayi da ba ta tava tsintar kanta a ciki ba. 


A wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar kowannen su, daga Fati har Sulaiman babu wanda ya runtsa, soyayyar junan su ke neman samun muhalli a zuciyar kowannen su. 

Amma sun sa kafa suna fatali da ita da gan-gan, don a ganin kowannen su bai dace ba. Sannan ita Fati ta riga ta yiwa Dr. Sulaiman mummunar fassara Zuwa na makiyinta, mai nuna mata kiyayya karara, kiyayyar da babu wani mahaluki da ya tava nuna mata a rayuwar ta. 


Don haka a kan me za ta so shi in ban da sharrin zuciya, don haka take ta ciccijewa, ita lallai karya zuciyar ta take yi ba son shi take yi ba. 


Shi kuma a can nashi vangaren Sulaiman, ya kasa sukuni, ya kasa runtsawa ne a dalilin abubuwa da dama na yarinyar a yau da suka fizge shi. 


Ga dai kamannin Hadiza, sannan ga wasu (edtraordinary kualities) da ya lura dasu a dan zaman watannin da ya yi tare da yarinyar. Don haka ya kwana cikin yiwa kai da zuciya hisabi, don tantance al’amarin da ke shirin faruwa da shi a kan Fatima Ja’ afar Mai-Yadi. 


Sakamakon ba mai saukin fadi bane a gare shi, halayen ta da yakanar ta da juriyar ta wajen yin abubuwan ta don Allah ba don ya yabe ta ko ta burge shi ba, sun taimaka kwarai wajen sayo mata soyayyar dole, wanda ke nufin Fati ta yi nasara kenan a kansa? Shi kuma ya fadi game din da suke bugawa. (He is the loser, and she is the winner! 


Idan ya yi sake hakan ya bayyana gare ta shikenan za ta raina shi, GIRMA YA FADI! Ya manta cewa a magana ta aure babu raini tsakanin mace da mijinta. 


To amma ina zai kai jin kan? Na _ tunanin kankanuwar yarinyar da yake rainawa ta yi win

ning a kansa? Don haka tunanin sa na ya yi nisa da Fati, don gudun raini ya kara kamari a tare da shi. 


A kwanakin da suka biyo baya, duk hanyar da ya san za ta hada shi da Fati a gidan yana kauce mata. Ita ma Fatin hakan, tun daga ranar da ta yanke hannu, ga shi har ciwo ya kame. 


28 2K a su Kano ba su Abuja shi da wasu daga cikin likitoci ‘yan uwansa, suna fafutukar ‘visa’ zuwa jami’ar Chicago domin halartar wani kwas na shekaru biyu a kan dashen zuciya (heart transplantation) da ‘federal’ ta tura su. 


Ko Inna ba ta sani ba, sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa, shi lallai dole yana yaki ne da zama da Fati kada soyayyarta ta rinjaye shi, shi ya sanya ya sanya kanshi cikin ‘yan tafiyar, don da babu yadda shugaban su bai yi ba ya shiga cikin tawagar amma ya ce a’a, duk da matukar 

bukatar shi da kwas din da asibitin ke yi, don haka da ya zo da kansa ya ce zai tafi, ba karamin jin dadi shugaban su ya yi ba. 


Suka fara shirye-shirye, har zuwa yau da Allah ya nufa suka kammala, sai tafiya kwanaki uku masu zuwa. 


Ya cimma su ita da Alti a kicin don su nan ne ofishin su, suna ta suyar dambun nama. Ya hada giran nan sama da kasa lokacin da idanuwansa su kai arba da na Fati, ita ma ta hade tai murtuk kamar ta ga mala’ikan daukar ranta, wannan gigicewar da take yi in ta gan shi yau ba ta yi ba, sakamakon jimawa da ta yi ba ta sanya shi a idon ta ba. 


A can wani gefe daga karkashin zuciyar ta, wani sanyi ne ya sauka a zuciyar ta wanda ba ta san dalilin shi ba. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa a dan tsakanin, saboda yadda ganin sa ya zame mata SANYIN IDANITYA, yake gusar da duk wani vacin ranta, yake rage mata zugin rashin ‘yar uwarta da ke cin zuciyar ta, duk da rashin alherinsa gare ta kuwa. 


Babu ko tantama ta fada a soyayya, a inda take da yakinin cewa ba za a tava son ta ba, in haka ne zuciyar ta ta gingimo mata babban aikin da ba ta san ya za ta yi da shi ba. 


Yana duban sashin da Fati take kasa-kasa ya gaida Alti, sannan ya dauke kanshi a sashin Fatin, ganin yadda ta yi murtuk da fuska. Ya yi murmushi ya ce da Alti, 


“Ku yi shiri zan je in watsa ruwa mu wuce Bakori yanzun nan”. 

Alti ta ce, “Allah ya sa lafiya?” 


Ya yi murmushi ya ce, “Lafiya kalau Goggo Alti, yara sun kwana biyu basu ga Inna ba, suna ta tambaya ta”. 


Ta ce, “To bari mu yi sauri mu karasa”. 


Taso ta ce da shi, “Har da Fati?” Ta ga wannan ba abin da ya shafe ta bane sun fi kusa, wai harshe da hakori. 


Ita ma Fatin da ba a ce da ita ba kawai sai ta hau shiri, domin tana son ganin Inna ainun. Ta zuba Abaya kirar Kuwait, ta kawo katon hijabin ta har gwiwa ta zuba. 


Bayan ta shirya yaran dukkanin su, ta fi son ta goya Nana, maimakon ta yi ta rike ta a hannu ko a kafada. 


Har Sulaiman kan yi mamaki ya ce a ransa, ita wannan ba ta gajiya da goyo ne? An ce mai da wawa, kulawar da take yiwa ‘ya’yan shi ya taka rawa ba kadan ba, wajen sayo mata soyayya ta kwarai a zuciyar shi. 


Kafin wani dan lokaci sun kimtsa tsaf suna falo suna jiran shi, ya fito cikin wagambari shudiya mai hasken sararin samaniya, wato navy blue, hannun shi na hagu daure da agogon RADO na bakar fata, haka takalmin da ke kafar shi wanda ya kasance budadde na fatar damisa. 


Babu gilashi a idon shi sai fararen idanun shi ke sheki da daddadan kamshin ‘Chris Adams’ da ya baibaye su. 


Yaran suka nufi jikin shi, ya kama hannun kowannen su suka nufi harabar adana motoci, ita kuma ta koma kitchen ta juye dambun naman da 

suka yi gaba daya ta taho da shi don ta kai wa Inna. 


A wajen shiga mota ne ake dirama, yana son ganin in da za ta zava don zama don son sanin matsayin da ta aje shi, tunda ‘yar gaisuwar da ta ke mishi ma a darare ta hakura ta daina, tunda baya amsawa. 


Ta bude gidan gaba su Munib suka shiga, sannan ta sunto goyon ta shiga baya ita da Alti. 


Har suka hau titin Kabuga babu wanda ya yi magana, sai yaran da ke ta rigima a tsakanin su a kan jirgin sama mai batir na Munib da Muniba ta dage sai ta amsa. 


Ita dai Alti shiru ta yi tana nazarin su, ga dukkan alamu kowannen su ya sauya, ya yi sanyi, amma an rasa wanda zai sauke ya bi dan uwansa. Tana son ganin wanene zai yi jarumtakar tsaga billensa ya bi dan uwansa? 


Wadannan ma’aurata suna ba ta dariya, ganin har ta cikin mudubi satar kallon juna suke, amma in daya ya kama daya sai a yi maza a dauke fuska, wato babu shiri babu alaka. 


Tafiya ta yi nisa a kan kwalta, barci ya fara daukar Alti, yaran tuni sun yi barci har Nana, ya mika hannu ya rage musu karfin na’urar sanyaya mota. 


Kawai Sulaiman ya faka motar a tsakiyar daji, ya wani irin juyo ya dube ta, an yi sa’a ita ma a lokacin ta dago daga madara da take bai wa Nana, idanunsu cikin na juna, wani miracle ya yi aiki cikin ‘yan dakikai, ya haifar da wani al’ amari 

mai GIRMA a zuciyoyin su. 


Ji yake kamar yana yi mata kallon karshe ne, ya tuhumi kanshi da rashin sauke wani nauyi mai girma da Allah ya ce ya yi, ga shi har zai tafi, tafiyar da babu tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba, tunda rayuwar ba a hannunmu take ba. 


Ya samu kansa da son tausasa mata, ko babu komi yana son goge mugun tabon da ta yi mishi a zuciyar ta. Ya tabbata idan Inna ta san har zuwa yanzu bai kula ta ba, la shakka za ta dauki mataki, duk da ya san da wuya Fatin ta gaya mata, tunda ba ta da magana. 


Amma in Inna ba ta sani ba ai Allah ya sani, kuma ba zai kyale ba. 


Ya mika mata hannu, “Kawo ta in taya ki rainon”’. 


Ta galla mishi harara, sannan ta kara kankame ‘yar. Ya yi murmushi ya ce, “Ko ‘yar gaisuwar da kike min kin daina, why Fati?” 


Wannan karon ma ba ta yi mishi magana ba, amma ta tsuke baki ta juyar da kai. 


Ya yarfar da hannu, “Tunda kin ki mu yi hirar bari mu karasa gaban Inna, watakila ita za ki yi mata bayanin dalilin ki na daina gaishe ni a matsayina na mijin ki da kuke kwana gida daya ku wayi gari cikin gida daya, zan gaya mata ‘ya’yan ki kawai kika sani, amma ni kin daina shiga sabgata, kin mai dani saniyar ware, dan gyaran dakin da ake min tun daga ranar da kika yanke hannu kin daina. 


Haka nan zan iya tunawa cewa, tun daga ranar ne kika daina gaishe ni”. Nan ma shiru, kamar da 

dutse yake magana. Haushi ya ishe shi ya fizgi motar. Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan su cikin garin Bakori. 


Malam Sulaiman na alwala a kofar gida lokacin da suka isa, ya soma maraba da ‘yan jikokin shi. Suka dunguma suka shiga gidan tare, Inna na sallah lokacin da suka shiga falon ta, sai da ta idar ta shafa addu’a, sannan ne ta karvi Nana a hanun Fati, tana yi musu sannu da zuwa. 


Alti tana daga waje, yaran ma Khalid ya shigo sun bishi shagon sa, falon ya rage daga Inna sai Malam, Fati da Dr. Sulaiman, hira ce suke sosai a junan su, ba ta tsoma musu baki ba. 


Can anjima ya dubi sashen da take ya yi mata wani irin kallo da ya sanyaya gangar jikinta, ya ce, “Na kawo karar Fati Inna, ta daina gaishe ni, ga shi ban san laifin da na yi mata ba, na tambaye ta ta yi min banza”’. 


Kunya ta kama ta, ta mike za ta fita Inna na ganin yadda ya bita da kyawawan idanun shi kamar ya fasa kuka, ta yiwa Allah godiya cikin zuciyar ta, ta tabbata Sulaiman ya fara son matarsa, addu’ar da ta ke kwana da yini tana yi ba ta fadi a banza ba. 


Ta ce da Fati, “Koma ki zauna”. Ba musu ta koma ta zauna, amma ba ta kara hada ido da kowa ba, ji take dama kasar ta tsage ta shige saboda kunyar da Baban Munib ya ba ta. 


Inna ta ce, “Wai haka Fatima?” 


Malam kuma ya ce, “A’ah! Fatima ba za ta yi haka ba haka kawai, kai dai ka san laifin da ka yi mata”. 

Bai yi magana ba. Inna ta ce, “Me ya yi miki Fati? Na san ba shi da kirki”. 


Da kyar ta ce, “Ni bai yi min komai ba, bana ganin sa ne”, 


Inna ta ce, “Koma ya yi, ki yi hakuri kin ji Fati, komi na duniyar dan hakuri ne da yafiya (afuwa), kowa hakuri yake da abokin zaman sa, ta hakan ne Za a ci ribar zama amma ba ta kullaci da rashin afuwa ba”. 


Sai ta ga kamar Inna ta shiga zuciyar ta, da gaske ta kullaci Dr. Sulaiman kullata mai yawa a kan abin da ya yi mata, duk da ta fahimci shi ma ya sakko yana son a shirya, amma ba za ta yarda a shiryan haka (so easy) ba. 


Wanda ya riga ya ce ba ya son ka, daga baya ya dawo ya ce yana son ka akwai dalilin shi na yin hakan. 


Amma ba za ta iya yin musu da Inna ba, don haka ta ce, “Na yi hakuni Inna”. 


Ta ce, “To Allah ya yi muku albarka”’. 


Ya ce, “Inna na zo in yi muku sallama ne....”. Cikin mamaki ita da Malam suka hada baki suka ce, “Zuwa ina?” 


Fati kuwa zuciyar ta ce ta buga, irin bugun da ba ta tava yi ba. Ya soma yi musu bayanin course din da aka zave su su goma shi da abokan aikinsa na shekaru biyu a jami’ar Chicago din Amurka. ‘““Amma tare za ku tafi da iyalinka ko?” Malam ya tambaya. 


Ya ce a ransa, “An yi ba’a yi ba kenan? Fatin yake gudu kada ta rushe masa plan din rayuwa, in ya dauke ta suka tafi me aka yi ke nan? Duk da 

shi ma ya soma kalubalantar kansa da ganin wautar sa na tsallake abinda rai da zuciya ke so da gangan, wai don kada GIRMA YA FADI!”’. 


Ya ce, “A’a, za su zauna ita da Alti saboda yara suna zuwa makaranta’”’. 


Malam ya ce, “Kun yi shawara ne ta yarda za ta zauna?”’ 


Bai iya karya ba, ya ce, “A’a, bamu yi zancen ba”. 


Ya ce, “To sai ku yi shawara a tsakanin ku can, in ta yarda za ta zauna din shikenan, mu ‘yan sanya albarka ne”. 


Ba su taho ba sai yamma lis, kamin su iso gida har an yi kiran isha’i, kasancewar duk a koshe suke, Inna ta cika musu ciki da dambun shinkafar ta mai dadi, basu shiga kicin ba kowacce ta nemi makwancin ta, yaran ma sun nabba’a a dakin su, shi kuma ya juya asibiti. 


Fati tana shiga daki ta kwanta rub da ciki, da filo a karkashin ta cikin wani mawuyacin hali na soyayyar Baban Munib da ke cin zuciyarta. Ta kai hannu ta dafe kirjin ta wanda ke bugawa dasauri-da-sauri da sunan SU-LAJ-MAN a kowacce dakika, zai tafi ya barta, bayan ya gama da zuciyarta, ya kimsa mata soyayyar da ba ta san iyakacin ta a zuciyar ta ba. 


Ya warware duk wata nutsuwa da tunanin da ke tare da ita, ya mamaye 80% na zuciyarta. Ya haifar da wasu al’amura masu girma a gare ta da ba ta san ya ya za ta yi dasu ba. 


Jin tafiyar shi take har ruhi da vargon jikinta, 

maiyasa wasu maza suke haka ne? Idan sun san sun kimsa maka soyayyarsu, Sai su nemi gudu su barka da jibgin abar ka? 


Wasu hawaye suka zubo, maimakon ta share sai ta tara hannu tana tarar saukar su a kan tafukan ta. Ba ta ji motsin bude kofa ba sai alamar zaman mutum a gefen ta, kafadunsu suka gogi na juna, ta yi hanzarin juyawa, Dr. Sulaiman ke kallon ta da murmushi. 


Ya sanya hannu cikin aljihun bakin jeans da ke jikinsa, ya zaro hankicin sa ya mika mata, ta jima ba ta karva ba, daga karshe ta karva ta share ambaliyar hawayen ta. 


Ya mika mata hannu alamar ta ba shi abinsa, sai ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai ba ta bashi ba. 


Ya ce, “Bani mana? Ko kukan bai kare bane?” 


Ta tsuke fuska ta tsuke baki ta hade girar sama da ta kasa. 


Ya yi murmushi ya sa hannu cikin hannunta ya dauke hankicin sa, kadan ya rage ta sume da hucin sassanyan numfashin sa ya doki fuskar ta, kamshin turaren sa na fizgar ta, kamin ta farfado daga shidewar da ta yi na wucin gadi ya fice a dakin. 


Zuwa can kuma ya dawo da takardu a hannun sa, sai dai wannan karon ya janye murmushin da ke fuskar shi, ya zauna dab da ita cikin kakkausar murya ya ce, 


“Me ya sa ki kuka?” Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, zuciyarta na ci 

Post a Comment for "YAKANA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...