YAKANA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAKANA BOOK 2  CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

- - Post a Comment

 YAKANA BOOK 2  CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

sauran wani mahaluki in ka dauke Malam Ilu dake can bakin ‘gate’ yana gadi, an bar ta daga ita sai halinta. Ji ta yi kamar an kawo ta kabarin ta, ta yi kuka ta yi kuka har ta gode Allah. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah, ta jawo kular da Inna ta ajiye mata ta debi abinci tana ci. Ai ba ta tashi jin tsoro ba, sai da karfe tara na dare ya yi, Fati ba ta tava kwana a gidan da babu mutane ba, ta tabbatar ita kadai za ta kwana a wannan katon gida, don tuni ta san Dr. Sulaiman ya saba aikin kwana. 

Jikinta ya soma mazari kamar ana kada mata gangi, ta daddage ta takure a can karshen katifa ta kudundune cikin bargo tana dakacen ina ma ita ce ta tafi, Hadiza ta zauna, ko babu komai Hadiza ta fita bukatar rayuwar. 

Na farko tana aikin lada, ta hanyar ceton rayuwar mata ‘yan uwanta. Na biyu tana da ‘ya'ya tana kula da tarbiyyar su da rayuwar su, na uku tana da mijin da ke son ta suke rayuwa cikin so da kaunar juna. 

To amma ita fa? Babu sidi babu sadada. Ba ta kai karshen tunanin ta ba ta ji karar fashewar tangaran a kitchen, wannan ya tabbatar mata ba ita kadai ce a gidan ba, to wane ne? Ta san dai ba maigidan bane, don shi in ya dawo karfe shida ba ya kara fita sai takwas, ba kuma zai dawo ba sai past ten sai dai in yana da aikin kwana. 

Ta ji dan tsoron ya ragu, ko ba komi tana da confidence na cewa akwai mutum cikin gidan ba ita kadai ba ce. Ta mike ta fito ta nufi kitchen, wanda ba ta zata ba shi din ta gani, ya tara hannu cikin 

famfon sink yana wanke jinin da ke vulvula daga hannun sa, ga kuma kwai yana ta kauri a kan cooker. 

Ta karasa da sauri ta sauke, ta kashe gass din. Ta dauki tsintsiyar laushi ta soma tattare fasashshen tangaran din, kafin ta farga ya fice a kitchen din yana ta disar da jini a kan tiles. 

A take ta hada wani kwan ta soya masa, ta juye a farantin tangaran ta debi ‘cake’ samosa da spring roll cikin firji ta dumama a karamin oven, ta tafasa ruwa nan da nan ta juye a karamin tea flask ta kwasa ta yo falo don ta ba shi. 

Ya tada kai da karamin filo yana kwance a tsakiyar kilishi, sanye da fararen riga da wando na barci marasa nauyi, har yanzu dan yatsansa bulbular da jinni yake, amma bai damu ba, kamar ba jikinsa ba, ta zo gaban shi ta russuna ta aje mishi, sannan ta sanyaya murya ta ce, "I'm sorry!". 

Bai kalle ta ba, haka bai amsa ba kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a gun ba. Kai vangaren data ke ma bai kalla ba. Ta mike za ta koma daki cike da tunanin hannun shi da ke ta kwararar da jini, amma matsayin shi na likita bai yi wani kokari ba ko yaya ne don dakatar da gudun jinin ba. 

Ta san da Hadiza tana nan Allah kadai ya san irin gigicewar da za ta yi, sannan za ta sa mishi magani ne ta daure, sannan ta yi ta jinyar ciwon har sai ya warke. 

Hakan ya tava faruwa da ya sharce babban dan yatsan sa garin ferar tuffaha, irin wannan kulawar kenan Hadiza ke nufi ta yiwa mijinta? Da kamar 

Ya yi mata addu’a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi. Da yardar Allah watarana za ta tashi da riba. 

Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta. Ta kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba. Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al’amarin shi kamar yadda ya bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah. 

Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa’a rufe kofar kawai ya yi amma bai sa key ba. 

Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau. Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a toilet fal cikin kwando. 

A jikin bed side ta yi tozali da ‘yar uwarta tana murmushi. Ta karasa ta dauki ‘frame’ din hoton tana shafawa a hankali tana murmushi, hawaye fal idanun ta. 

Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet ta canza wani. Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi. 

Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun 

tsaftace ko ina kamin su tafi. 

Zuwa la’asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr. Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa turaren gidan (Chris Adams). 

Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa. 

Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din ba na dazu ba. 

‘“Wato yarinyar nan ba ta jin magana”. Ya fadi a zuci. 

Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni’ima ta musamman dake fita, wanda ya gauraye da ravar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da gangar jiki. 

Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya ga sakon Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ya girgiza kai ya ce, “Na san maganin ki tunda baki da zuciya”’. Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining. Yau ma girgiza kai ya yi ya wuce, “Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!”’. ‘Surely’ yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi. In ya ci girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu duk daya. Babu wani amfani da mace za ta yi 

masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so? Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda. Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta hanyar danna kararrawa. 

Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja’afar ne rungume da Baby Nanah, Munib da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su. 

Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe. Suka karasa cikin falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karve ta ya rungume yana sunsunar ta. Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa. 

Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar su. “Ina Fatin ne? Ko barci take?” 

Cikin dauriya ya ce, “Bari in duba”. 

Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike. Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI? Kallon second biyu ya yi mata y dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya ya ce, “Mukhtar ke kiran ki’. 

Ta zubo doguwar rigar shadda ‘dark-blue’senegalese ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su a 

falon. 

Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita. Itama ta rungume su, suka soma jero mata tambayoyi. 

“Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu? Ina kika tafi muka daina ganin ki? Nana tana ta kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu.....”. 

Ta ce, “Ba zan kara ba”. Ta kamo hannun Muniba, “Ba inda zan je muna tare kun ji my kids?” Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi Iemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai rangwamen sanyl. 

Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi. Bayan ya karvi lambar Fati. Tana so ta karvi Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba. 

Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka sake gogar juna. Wasu irin hannuwa gareta masu bala’in taushi, wadanda suka tada_ tsigogin jikinsa. Ita kuma suka haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa. 

A hanzarce ya mike, “Oya kids! Muje mu sha (Ice-cream)”. 

Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce, “Amma har da Anti Fati za mu je?” 

Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta. Ya sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu suka yi 

waje. 

Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma baiwa Nana bayan ta sha iska. 

eK 

Kayan cefanen su sun kare, ba ta san ya za tai ta gaya mishi ba, saboda irin yadda yake bi ya daure fuska kamar wani soja idan ya ganta. 

Fati na mamakin wannan wace irin kiyayya ce Sulaiman yake mata ta babu gaira babu dalili? Kamar ita ce ta kashe Hadiza? 

Yana da wata kima a idon ta kasancewar shi wanda ya auri ‘yar uwarta da ba ta da ya ita a duniya, ya zauna da ita, ya rayu da ita cikin so da kauna har ta koma ga mahaliccin ta, ba ta tava fadan laifin sa ba ko aibunsa ba, ko wani abu da ya yi mata na rashin dadi. 

Sannan da kasancewar shi Baban ‘ya’yan da take so sama da komi a duniya. Idan ba zai so ta ba ai ta ci albarkacin Hadiza. 

Amma yadda yake nunawa kamar ko a hanya basu tava hada wata alaka ba, idan ta biyewa wulakancin da yake mata ta ce za ta dinga vata ranta a banza, ita ce za ta cutu, ta dorawa kanta ciwon zuciya da hawan jinin da ko duba ta ba zai yi ba, balle ya rubuta mata magani. 

Don haka ta debe tsoro da shakku, bayan sun dawo yana kwance a falo yaran shi sun baibaye shi suna ta yi mishi tadi, shit kuma yana aiki cikin kwamfutar da ke bisa ruwan cikin sa. 

Ta lallavo ta fito uwa munafuka, tana goye da 

Nana ta rave a gefe, Muniba ta taho ta zauna a cinyar ta. Sai a lokacin ya ankara da shigowar ta falon, ya juyo da sauri kamin ta yi magana ya mike, ya aje computer a fusace. 

Ta runtse ido tana jiran saukar mari a lallausan kumatun ta, ya ce, “ Don’t I warned you? Idan ban neme ki ba ki daina zuwa inda nake?” 

Cikin makyarkyatar murya da gigicewa ta ce, “Ka yi hakuri, kayan cefane ne suka kare, sannan babu kayan abincin makarantar su Munib”. 

Ya yi tsaki “Tsuuu!” Kamar ya tsinke harshen sa, ya ce, “Na ji shiskenan ko?” Ta mike a saluve gwiwa babu karfi ta koma daki, don ita ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata tsawa. 

Su kansu yaran sun tsorata da tsawar da Baban su ya yiwa Antin su, sun yi Zuru-zuru, suma ya nuna musu hanya ya ce su bita. Da gudu suka tafi har suna faduwa, ya kashe komai ya fice daga gidan. 

Washegari Alti ta dawo, ba karamin jin dadin dawowar ta Fati da yara suka yi ba, ko ba komai ta samu mai taimaka mata da debe mata kewa, don Goggo Alti mutum ce mai barkwanci da ban dariya. 

Sai ga Malam Ilu yana shigowa da kayan abinci nau’i-nau’i. Suka zaun ita da Alti suka gyara komai suka adana na adanawa a firij, suka markada na markadawa suka adana a ‘freezer’ 

Washegari ta tashi da wuri da taimakon Alti suka kammala komi da wuri, suka shirya yaran da abincin su, karfe bakwai da rabi Babansu ya kwashe su ya wuce dasu, sannan ya dangana ga 

ofishinsa. 

Kuma ranar ne su Yaya Haulatu kanwar Yaya da wasu daga aminan arzikin ta suka zo suka yi mata jeren kayan gado dai-dai karfin iyayen ta da dan uwanta Mukhtar. 

Falon ba ya bukatar komi, masu gidan sun riga sun tsara abin su dai-dai da rayuwar su ta masu murza tsinin biro, sai ba’a tava komi ba, iyakacin su dakinta. 

A kwanaki bakwai da Alti ta yi tare dasu, ta fahimci irin zaman kare da kyanwar da ake tsakanin Fati da maigidanta Dr. Sulaiman. A ranta ta ce, “Yarinya kyakkyawa kamar Hadiza, ga hankali da addini, ko meye nakasunta da Dr. Sulaiman ya kasa son ta?” 

Ta ce, “Ko da yake so ba’a nan yake ba, abune wanda ke faruwa kawai a duk sanda ya so, ga duk wanda ya so, cikin iko da kudurar Allah. 

A yau suna yankar alayyahu ita da Alti, domin yin miyar wainar masar dare. Suka jiyo motsin shi yana shigowa kitchen din, tuni Fati ta soma makyarkyatar jiki, kan ka ce meye wannan wuka kakkaifa ta shiga cikin naman hannun ta. 

Don ita ko gyaran muryar shi ta ji gigicewa take ta fita hayyacinta kada ya yi mata tsawar nan tashi mai dimauta ta. 

Jini ya soma vulvula a dai-dai lokacin da ya idasa shigowa kitchen din. Alti ta ce, “Ya salam! Kin gani kin yanke, na yi na yi ki daina amfani da wannan wukar kin ki, ta fiye kaifi da yawa, san

nan gaki da saurin gigicewa”. 

Ya ji hankalinsa ya tashi ganin yadda jini ke gudu amma ba ta dago ba. Ya basar Ya ce, “Babu sauran ruwan roba ne Alti? Firjina babu komai, sannan ina jin kishi’”. 

Ta mike zuwa store ta dauko mishi katon na FARO ta dawo, ta kama hannun Fati ta ce, “Babu kananzir balle in sanya miki, bari a daure da tsumma”’. 

Ta tsaga zanin ta tana kokarin daure mata. Ya kalle ta a kaikaice ta kasan ido ya fita, zuciyar shi babu dadi, don ya tuno yadda ta nuna damuwa ranar da ya yanke nashi hannun. 

Mamaki ya kama Alti, ashe Baban Munib ba shi da kirki? Matarka ta yi irin wannan yanka amma ko kallo ba ta ishe ka ba? 

Tana daure mata Fati ta fara kuka yankar ta fi karfin daurewa da tsumma. Alti ta biyo shi, ba ya falon yana dakin sa. Ta tura Munib wanda ke ta wasan game cikin computer ta ce ya kirawo Baban shi. 

Jim kadan suka fito tare shi da Munib, yana rike da gorar ruwan yana sha. Cikin takaici ta ce, “Zan kai Fati asibiti ne”. 

Ya sunkuyar da kai duk jikin shi ya yi sanyi, ganin vacin rai kwance a fuskar tsohuwar da bai tava ganin vacin ran ta ba tsayin shekaru shida da suka yi tare da ita, ya dukar da kai sosai ya ce, “Bari in diba ciwon nata”’. 

Ya koma daki ya dauko first aid bod ya same su a kitchen din, jinin na ta zuba har yanzu. 

Sanye yake da brown getzner ta sha dinkin ko

Post a Comment for "YAKANA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...