UMM ADIYYAH CHAPTER 5 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 5 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 5 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 5 BY AZIZA IDRIS GOMBE                      Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Nan da nan ta seta tunaninta, saboda kar ma ya gane komai, ta Karasa inda yake tsaye jikin motarsa, a wurin Parking din motoci a gaban Complex. "Yaya Zaid yaya aka yi ka san inda za ka sameni?" 

Murmushi ya yi, bai ba ta amsa ba, sai da ya mikawa su Idris hannu, wadanda suka fara gaishe shi. "Ina wuni Yallabai?" "Assalamu-Alaikum, yaya karatun dai ana ta fama?" Ya fada fuska a sake. "Eh, Wallahi." Muhammad ya ce. "To ya yi kyau. Allah ya taimaka." "Ameen-Ameen.” Dukansu suka amsa. Sai da suka wuce ne, ya bi su da kallo ya dubi Umm Adiyya, "Ke kuma 'yan maza ne Kawayenki?" Yaso ya ba ta dariya, amma yanayin da ta ke ciki ya hanata wannan daman. "Test muka fito." Muna tare da Saadik ne, amma ya tsaya can wai za su gaisa da wata Saudat ce ko WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

waye?" Ajiyar zuciya ta yi, shi ya sa mana Saudat ta isheta da tambayar labarin ‘yan gidansu, wato daman Yaya Saadik ne ya dan zagayo. Cikin karfin hali tace, "Yaya hanya?" "Lafiya Kalau. Mu Karasa ko ba hostel za ki koma ba?" Ba tare da ta amsa ba, ta zagaya ta zauna a daya gefen. Yana shigowa ta ce. "Congratulations." Juyowa ya yi ya kalleta, sannan ya Karasa saka seat belt dinsa "Na gode duk da ban san na meye bane wannan." Ta gefen idonta ta dube shi, idan ma ya zo ne ya Kara juya mata tunani ko lissafi ba za ta taba barin hakan su faru da ita ba, don ta gama da wannan bangaren na 

rayuwarta. A hankali suke tafe, har suka Karasa (NANA KHADIJA HOSTEL). Nan suka gaisa da 

Yaya Saadik, ita dai Allah-Allah ma take yi su tafi, a wani Nangaren don ta gamu da Saudat, a daya bangaren kuma ba ta son ko ganin Yaya Zaid. 

Cikin ikon Allah, bai wuce minti goma ba, suka ce za su wuce don suna kan hanya, 


saboda Yaya SaadiK zai koma Gombe ne, yayin da Yaya Zaid kuwa wani aikin ne ya kawo su Bauchi. Don haka suna tafiya ta sauke numfashi. 


Bayan sun koma daki ne ta dubi Saudat ta ce, "Asirinki ke ma ya tonu, wato daman abin kenan, shi ne kina Kus abinki. To Dangin miji mode activated, bari na fada miki, zan zuga shi ya fasa, tunda ba a ban kula na musamman ina matsayin Kanwar miji guda.” Saudat na dariya ta ce, "Ai yayankin nan abin tsoro ne, don haka na bar maku kayanku, ke daga zuwa sau biyu, yana min maganar zuwa gida. Haka daman ‘yan Nafadan nan ku ke ne?" "Ke kin samu an bi ta kanki ma? Kar ki mana yanga, dama ki bada go ahead, ehem." 


Ta fada, ta na zaro mata idanu. Su Takiyya suka sa masu dariya. 

ZAMU TASHI 


Yau ga shi watanni biyu da gama Service cinta inda ta yi a Jigawa State, dole ta sa

ta koma gida gaba daya. Banda TJ. Babu wanda take bawa fuska, shi din ma kullum

sai ya sha fama take saurarensa. Shekarar su kusan uku tare, amma kullum idan

yana son zaman lafiya, to kar ya dago mata maganar aure.

Wannan ya sa ya daga mata Kafa. "Ina ga Umm Adiyya, ki na buKatar lokaci, ki yi

nazarin abin da yake tsakanin mu. Kin ga dama ba kusa muke da juna ba, so zai fi Www.bankinhausanovels.com.ng 

kyau ki fuskanci me ki ke so daya, duk abinda ki ka yanke nan da watanni biyu, ina

saurarenki."Ita kanta ta san ta Kure TJ. Amma ta tabbata ba don ta wurin Adda Zubaida ya fito ba, da bai samu hakan ba ma.

********,,,,

Tana karanta wani magazine ne, suka shigo falon suna dariya, "Yanzu da gaske ba

za ka zaba ba?"

"Ni kuma me na sani kan wannan? Yawwa ga Ummu nan ta taya ki." Asma’ tana murmushi ta isa inda take zaune ta hau bude mata catalog. "Ummu A.

kin ga Yaya Zaid ya ki ya tayani zaba, wanne ki ka ga ya fi dacewa?” Fiddo idanu ta yi cikin razana, tana duban su dukan su biyu. Tashin hankali! Yanzu haka za ta zauna a gidan nan tana ganin abin da ya fi Karfinta? Yaya za ta fara zaba masu kujerun da za su yi amfani da shi a gidansu? Murmushi kawai ta yi ta ce, "Adda Asma’ ku da gidanku, ai za ku fi ni sanin me zai dace da gidan da wanda ranku ya fi so, duk da dai wannan gray din ya yi kyau sosai." Ta fada hade da rufe littafin hannunta, ta miKe daga falon. Asma’u ta dubi Zaid, ta samu shi ma kallonta yake yi, ta daga masa hannaye alamun ba ta san amsar ba ita
ma. Tun da ta shige kuwa, take aikin kuka, a nan ta yi zamanta har sallar Issha, sai da Abba ya kirata, sannan ta fita ta ci abinci, ce masu ta yi idanunta ke ciwo. "Na ga alama kin zama sauran Likita, za mu kai ki asibiti mu bar ki a can ko ba haka ba Mamana?" Abba ya fada cikin zolaya. "Fa’iz ga wannan ka samo mata eye drop, mai kyau ko idon zai wartsake." Abba ya fada. Fa’iz yana jin ya cika saurayi har saurayi, ya sosa kai ya ce, "Ah, Abba bar shi kawai akwai kudi a jiki na." FaruK ne ya ce, "Da kyau, Don! Ni ma ka sayo min iPhone charger, nawa ya Kone." Harararsa ya yi ya ce, "Don Allah gafara Malam, Maami ki sa FaruK a hanya. Wallahi son banzan shi ya fiye yawa." Dariya suka yi kawai, don muddin suka hadu wuri guda, to ba za ka ji kunnenka shiru ba, tsabar fada, amma fa ba a taba dayansu a share. Kafin gari ya waye kuwa Asma’ ta tsinci Ummu Adiyya cikin zazzabi mai zafi. Www.bankinhausanovels.com.ng 

**********

A Kudundune take a lungun gado, kan sallayah, banda kakkarwa, babu abinda take

yi, ba ko tantama ta san zazzabi ne ya saukar mata, sai dai ko hobbasan neman magani Umm Adiyya ba ta yi ba, don ta san ciwonta bai da magani. Sai dai sauKi
kawai daga wurin Ubangiji, wanda yanzu haka ta gama kai kukanta ne, zafin zazzabi ya hana mata tsayuwar sallan daren ma da ta tashi, domin yi, shi ya sa ta koma yin tasbihi. Jin shessheKar kukanta ne ya sa ‘yar-uwarta Asma’ ta farka daga barci, ta kunna wutar dakin, saboda daga ji kukan ba na lafiya bane. "Ummu A? Me ya sameki ki ke kuka haka?" Ta fada daidai lokacin da ta durKusa a gefenta tana shafa kanta, saboda yadda ta ga tana kakkarwa.
A hankali ta bude idanunta, wadanda suka yi jazur! Kamar jan gauta, ga kuma azabar ciwon kan da hasken dakin ya Kara mata. "Babu... Ki kwanta Adda Asma’u.” "Yaya za ki ce min babu? Kin ga yadda ki ka koma kuwa, bari na samo miki magani ki sha. Zazzahi fa ki ke yi mai zafi. Amma kamar farilla, sai kin yi wannan tashin daren naki, ki huta mana, don na yau kawai, ai jiki ma yana da haKKi kan ‘Dan Adam." Www.bankinhausanovels.com.ng 
Da sauri ta miKe ta nufi durowar jikin madubi, ta fito da robar adana magunguna (first aid box). Panadol Advance ta balla ta ba ta, ta miKa mata kofin ruwa. Karba ki sha, don Allah Ummu A. Ki sa wa kanki sa'ida, haka nan, na kula kin fi sati biyu a wannan halin da ki ke ciki na damuwa, kuma na san shi ya sanya miki zazzabi. To ki sani idan ba ki daina damuwa ba, zan fadawa su Maami halin da ki ke
ciki, kuma kin san taron dangi za ayi a kanki, sai kin fadi matsalarki. Ko ba ki fada min ba, ki daure ki cire damuwar a ranki, ki barwa Allah komai kin ji?" Murmushi ta yi na Karfin hali da kuma yaba yadda 'yar-uwarta take matuKar Kaunarta. "Adda Asma’ ni ba ni da wata damuwa, kawai dai jikin nawa ne ya Ki dadi. shi ya sa. Amma tunda na sha magani. Inshaa Allah shi kenan." Asma’u ta zura mata idanu, tamkar tana so ta karanto Karyar da ta sharara mata.
Don dukkansu sun san juna ciki da bai, yadda ba yadda za ayi daya na cikin wani hali daya bai sani ba. Hakan ne ma ya sa Umm Adiyya ta san cewa lallai ta iya zurfin ciki, tunda ko 'yar-uwarta ta kasa gane yaudarar da zuciyarta take son tayi mata na cin amanar Kaunar da ke tsakaninsu. Eh, mana lallai zuciyarta ta yanko mata wani danyen aiki ja, wanda ba ko tantama zai jefa ta a halaka ne kawai, ya kuma raba dangantakarta da 'yar-uwarta, wannan
ya sa ta gwammace ta zauna, koda ciwo zai kasheta ne, gara ya kashe, amma ba za ta bawa zuciyarta abinda take so ba. Domin abinda take so haramtacce ne a gareta.

Lokacin ne ta Kara hadiye hawayenta, ta kuma sa hannu ta goge fuskarta, hade da miKewa cikin jiri-jiri, ta isa bandaki, domin wanko fuskarta. Saboda yanzu kam ta yanke wa kanta shawara, komai zai faru da ita, sai dai ya faru, amma ko shi ne autan maza, wajibi ta haKura da shi. Ba za ta taba yarda soyayyarsa ta raba tsakanin su ba.

***********

2010 RANA TA YAU.

Tana riKe da wayarta tana karanta wani shafi a yanar gizo ne a falon Abba ta ji alamar shigowar mutum, wannan ya sa ta daga idanu ta dubi mai shigowar, sallamarsa ce ya sa ta yi saurin miKewa a zabure da nufin barin falon, sai kuma ta tattara natsuwarta ta daure ta gaishe shi.
"Yauwa lafiya Ummu, yaya Maami, tana kusa ne ki mata magana?" Murya a sarKafe ta ce, "Eh... Bari na fada mata.” Gabaki daya haibarsa rudata yake yi, yana da wani abu a tare da shi wanda muddin yana wurin, dole ka ji a jikinka, ga wata natsuwa ta musamman da hatta kalamansa a natse suke fita. Idanunsa kuma.... Kafin ta ida fasalta shi a zuciyarta, ta shiga firgici, a dalilin ji da ta yi ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Ummu.” Ya Kira sunanta a cikin dakewa kamar yadda ya saba, tana juyowa ya ce, "Ki taho min da ruwan sanyi." A hankali ta gyada masa kai ta wuce cikin gida, na daKiKa daya ta mayar wani abin zai fada mata wanda take matuKar son ji daga gare shi, sai dai wannan kam sai dai a mafarki, domin ita ba komai bace a gare shi, face Kanwarsa da kuma Kanwar matar da zai aura! Hannunta na rawa, duk da fadan da ta yi wa kanta tana nanatawa cewa babu ruwanta da shi. Babu ke, babu shi, babu abinda zai shiga tsakaninku, ba ki san shi ba baicin shi yayanki ne kawai. Amma wannan bai hana hannunta rawa ba, a yayin da take zuba masa ruwan sanyinsa. "Ummu, lafiyarki Kalau kuwa?" Ya tambaya saboda shi kansa ya santa da natsuwa, amma sai zuba ruwa take yi, yana zuba ba tare da ta sani ba. Shigowar Justice Khadija falon ne, ya sa duka hankulansu ya koma kanta, tana murmushi ta ce. "Hmm! Kai ma dai Zaid ka tambayeta, haka nan ta rikide mana mun kasa gane kanta." Asma’ ce ta shigo ta Kofar da Zaid ya biyo, wanda hakan ba sabon abu bane, domin a office dinsu take aiki, mafiya lokuta tare suke zuwa aikin ma su dawo tare. "Kun sa min 'yar-uwa a gaba, zazzahi ta kwana da shi, shi ya sa amma da sauKi."
Zaid ya dauki glass din ruwan ya zauna, sannan ya ce, "Sweetheart, Yaya za ki ce da sauKi, bayan hannunta rawa yake yi da take zuba min ruwa?" Ya fada idanunsa a kafe kan Umm Adiiyya, wannan ya sa ta kasa tsayuwa a wurin, ta wuce ciki da sauri, zuciyarta na bada wani Dalli-Dalli tsabar kishin yadda ya kira 'yar-uwarta. Domin ba abinda kunnuwanta suke rattabo mata illa kiran Asma’u, sweetheart da yake yi. "Maami ki dai bincike ta sosai, akwai wani abin, ko kuwa ku kai ta asibiti." Rabu da Ummu da shirmenta. Banda abin ta yaya tana zazzafi sai ta yi shiru? Ciwon bai ci ta bane, shi yasa. Ta ce ka na nemana.” Ajiyar zuciya ya yi, sannan ya ce, "Yawwa Maami, daman shawara na ke so mu yi."
Murmushi ta yi ta zauna, sannan ta ce, "Ina jinka.”
Haka nan zuciyarta cike fal! Da dadi, saboda yadda Zaid ya daukesu daga ita har mijinta tamkar su suka haife shi, sam baya wani ja da baya ko ya nuna shi ba dan gidan bane a kodayaushe, kai tsaye yake samunsu da matsalolinsa, ko shawarwari, ko yanzu ma kan maganar auren Asma’, shi ne kan gaba a komai. Asma’ kam wuri ta ba su da ta ji za su yi shawara, can daki ta koma ta samu ‘yar uwarta, sai dai duk labarin da take mata, banda uhm da uhm-uhm, ba abinda take
cewa koman shiru shirunta dai, wasu lokutan ta kan tanka. Musamman yau da ta ba ta labari mai ban dariya, ta kula ko murmushi ba ta yi ba.
"Haba Ummu A, tun dazu kin maida ni kamar mahaukaciya, sai surutu na ke yi ni kadai? Ke Wallahi ba ki da dadin yin hira sam!" "Na yi magana da Adda Zubaida, Energy commission sun neme mu Intabiyu, ran Asabar zan tafi Inshaa Allah, don litinin ne Intabiyu din." Ta fada cikin kawar da Korafin ‘yar-uwarta. Da gudu Asma’ ta rungumota tamkar ta ce mata aikin ta samu. "Kai nayi miki murna
Kwarai. Allah ya ba ku sa‘a, ya sa a dace, hinyau za ki zama ‘yar Bauchi kenan." Adda Asma’ ba ki ga dai na samu ba tukun." Are you kidding me? (Ki na wasa dai), ta yaya za ki fadi wannan Interview din?
Kanwata mai nasara ce kuma za ki ci Inshaa Allah."
Murmushi ta yi kawai, domin ba komai ya sa ta zabi ta nemi aikin ba tun farko, illa Www.bankinhausanovels.com.ng 

saboda ta gujewa Yaya Zaid, domin muddin tana ganin sa zuciyarta ba za ta bar ta ba, son shi ba zai bar ta ba. Amma idan ta yi nesa da shi, ta san dole ta yi haKuri ta mance da shi. Shiru ta yi kawai ta shiga tunanin tun farko me ya jefata cikin wannan abu mai wuyan fitan?

**************

Ta gama shirinta tsaf! Ta hada jakarta, ta dauki duk wasu takardun da za ta buKata, domin Intabiyun da za ta jeyi a Bauchi. Don haka dakin Maami ta haura a sama, ta samu tana karatun AlKur'ani, "Ummu,
har kin shirya ne?" Ta tambaya bayan ta kai aya.
Eh, Ke da Abba kawai na ke jira daman. Har ma an sa min kaya a mota.” "To bari na yi masa magana. Allah dai ya taimaka ya sa a dace." "Ameen Maami, ki tayamu addu'a." Mai shari'a na nade hijabinta ta ce, "Addu'a kam ai kullum ana kai, sai fatan Allah ya
kawo alkhairi cikin rayuwarku gaba daya. Kasa ta sauKa inda take jiran fitowar Abba, shigowar Yaya Zaid ne, ya sa ta dago kanta, sama-sama ta gaishe shi. Mal. Bala ke fada min wai zai kai ki Bauchi Interview?" "Eh. " Ina ne suka neme ki?" Nan dai ta fada masa wurin da kuma aikin da take neman ta yi masu. Shigowar Abba ya katse masa tambayar da ya so ya yi mata, sai da suka gaisa duka sannan ya ce, "Abba, yanzu Ummu ke fada min za ta je Bauchi Interview, amma idan ba wani abu ba, me zai hana ta nema kawai a nan wurin mu? Tunda yanzu an Kara offices wurin ya Kara girma kuma muna buKatar iliminta a nan." Abba ya yi shiru yana jinsa, sannan ya ce, "Tabbas ka kawo shawara mai kyau, amma tunda sun riga sun yi short listing dinta, ina ga ba laifi ta je ta yi a can cin, idan ya so sai ku gama duk wani abin da ya dace, kafin nan ta nema a wurin naku, duk inda aka yi dace shi kenan." Murmushi ya yi ya ce, "Abba, fa mu ne da wurin, ai ko ba Interview ni mai daukar Ummu ne, bare kuma na santa da Kwazo so Sai"To shi kenan, idan ta dawo sai ku yi maganar. Ita kam tana zaune a Kasan kafet din falon Abba kamar ta kurma ihu ta ce allamfir ba inda za ta, ta yi aiki, sai kuma ta ga tunda ga Abba ya tare mata fadan, za ta ja bakinta har zuwa ta ga abinda hali zai yi. Fatan ta daya Allah ya sa ta lashe gwajin da za ayi masu. Domin idan akwai inda tafi kwadayin nisanta, to yana bayan duk inda Zaid Abdur-Rahman Nafada yake. Ta shiga mota ne. Asma’ ta zo daf kunnenta ta windo tana fara'a, "Allah ya bada sa'a Ummu A. Sai kin dawo ki sha gist yau Dee zai zo." Cikin tsantsar rudani Umm Adiyya ta dago ta dubi 'yar-uwarta. Dee kamar yadda take kiran wanda za ta aura zai zo kuma? Bayanta ta duba inda Yaya Zaid ke tsaye tare da Abba suna jiran ganin tafiyarsu. Daman Dee din ba Yaya Zaid bane? To idan
ba shi bane waye ne? Me yake shirin faruwa? Haka ta yi wannan tafiyar cikin ruda ni tsantsa. Har zuwa safiyar Litinin ba ta da natsuwa, don haka ba ta yi tsammanin ma Za ta tabuka wani abin arziKi ba a wurin gwajin. Koda za ta tafi. Adda Zubaida sai Kara mata Karfin gwiwa take yi, haka su Maami duka, sai da suka kira suna mata fatan Samun nasara. Duk gidan kowa ya kirata, banda wanda ta fi tsammanin kiransa, koda yake me zai sa ya kira? Tunda fatansa ta fadi, ta je ta yi aiki a kamfaninsa, inda zai fi jin dadiin ganinta cikin wuya. Duk da Adda Asma’ ta Ki ta yi mata bayanin komai a waya, wannan bai sa ta sauke tunanin cewa Yaya Zaid na son Adda Asma’ ba. Rubutaccen gwaji aka soma yi masu, sannan akai masu na baki, ta san dai a na
rubutun ne kawai, ta yi abin arziKi, amma na bakin kam sai a hankali, don banda "Pardon" ba abinda take ce masu, saboda hankalinta baya jikinta, daga baya suka ce ta matso da kujerarta gaba saboda ta rinKa jinsu da kyau. Har ta ji kunya, sai lokacin ne ta maida hankalinta garesu. Suna fitowa ta saki ajiyar zuciya, duk da ba ta san meye sakamakonta ba, amma ta sauke mai wuyan. Gidan Adda Zubaida ta koma tana ba su labarin yadda Interview din ya gudana. Suna zaune Asma’u ta kira, wannan ya sa Umm Adiyya ta yi wuf ta koma daki ta ce, "Don Allah Adda Asma’ yau kam ki fada min sunan Dee na gaskiya."HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 5 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...