UMM ADIYYAH CHAPTER 1 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 1 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 1 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 1 BY AZIZA IDRIS GOMBE 

                      Www.bankinhausanovels.com.ng Ya fi sau goma tana Karewa takardun da ke gabanta kallo, saboda ta gano inda ta yi kuskure, amma sam! Ta gaza samo wuri koda daya ne, ita kanta ta san ta Kona

lokacinta wajen tsara wannan rahoton, domin ta bi komai daki-daki cikin tsari,

sannan ta yi rubutun.

Agogonta ta kalla, domin kuwa lokacin da ya dibar mata ya cika, ga shi an kusa Www.bankinhausanovels.com.ng

tashi, saboda haka dole ta san abin fada masa. Kodayake ta riga ta san

lokacinta ma take yi, domin kuwa tunda ya rantse, sai ya ga kasawarta a duk abinda

ta yi, ba abinda za tayi masa ta burge.

Wannan ya sa ta hada kan takardun ta jera su, sannan ta shigar da abin da ya

kamata ta shigar a na'ura mai Kwakwalwa cikin shafin kamfanin. "Ai idan ka san

wata, ba ka san wata ba." Ta furta Kasa-Kasa gudun kar su Oga Akim su ji ta.

Kasancewar su uku suka rage a cikin ofishin nasu, sauran ma’aikata ukun yau sun

fita aikin fili, (Field work).

Jakarta ta daga ta kimtsa komanta a ciki, cikin shirin tafiya gida saboda ta kula

lokacin tashi ya gabato, sai a lokacin ta mulke hannunta man kariya daga Kwayoyin

cuta, (Sanitizer) da ke cikin Jakarta, wanda kadan daga cikin dabi'un Oga Musa da

ta dauka kenan a iya fara aikinta da su watanni uku da suka gabata.

Umm Adiyya Zubair, Umm A. Kamar yadda kowa yake kiranta ko kuwa Ummu

"Yan gargajiya ko manyan cikin dangi. Ta mika duka aikinta na ranar ga shugabanta

wanda yake duba ayyukanta kafin a mika su ga Oga kwata-kwata. Sai dai yau a

maimakon ya yi mata fara'a hade da sai da safe. Alama ya yi mata da ta zauna, bari

ya duba, idan ba matsala, sai ta wuce.

Shiru ta yi tana kallon mutumin da _tsakar kansa yake sheKi, tsabar yadda yake tal!

Ba ko burbudin gashi, ga wasu gilasai rau a idanunsa masu Karin Rarfin idanu. A

ganin farko, ba za ka ce Oga Akimu yare bane, saboda yadda kullum za ka gan shi

cikin shiga na hausawa, sannan fuskarsa tamkar wani bafulatani, sai ya budi baki zai

yi magana, za ka fahimci tsantsar bayarabe ne, na Karshe, don ko turanci yake yi za

ka fahimci haka.

Bayan shi kuwa teburin Jamila ce a gefensa, wacce a halin yanzu ba ta nan sun fita

tare da Oga Musa, wanda yake kusan matsayinsu daya da Oga Akimu a ofishin. Ba

laifi, daga fara aikinta tare da su, sun saba Kwarai, idan ka debe rashin sukuni da

take samu daga wurin mugun murdadden shugaban kamfanin, ko ma menene

dalilinsa na ba ta aikin, tunda ya tsaneta, har haka oho?

Ita ma maganinta kenan, da har ta mika takardar neman aikin a nan. (Application), Www.bankinhausanovels.com.ng

da ace ta fahimci asalin shi mai kamfanin da tuni ta tsere, tunda kaf garin ba shi

bane mutum na Karshe da za ta iya aiki da ma’aikatansa.

Koda yake ita ta dorawa kanta wannan masifar, da ta nace ita sai NGO ko kuma

kamfani mai zaman kansa za ta yi aiki. Idan banda haka, ayyuka nawa ta tsallake ta

yiwo nan, da har za a zazzare mata idanu ana sha mata Kamshi?

Hannu ta sa ta karbi takardar da Oga Akim ke mika mata, "Ga wannan mabudin,

shiga shafinmu na yanar gizonki, ya samu (Password), wanda aka fitar bayan

gyagije shafin kamfani.

Ga naki nan da aka bude miki, saboda haka ko daga gida za ki iya Karasa wasu

ayyukan." Ya fada cikin turancinsa mai cike da harshen yarabanci.

Murmushi ta Kago masa, ta yi godiya hade da saba jakarta ta yiwa Ayo (Ayodele)

ban-kwana, wanda bai cika magana ba, duk ofis din, sai ku wuni bai ce maku komai

ba, dama da shi da Oga Musa ne, shiru-shiru, dan surutu kam sai Hasan, ita ma

Ummu A. din haka ta fi so, don sam ita ba ta ra'ayin ta zage tana ta shewa tana

surutu da ma’aikatan ofis dinsu.

Sai da ta faki Kayataccen babban falon da ya hada Kofofin ofis-ofis na kamfanin, ta tabbatar ba za ta hadu da damuwa ba, sannan ta danna kai, cikin dan falon wanda

aka Kayata da kujerun silba masu sulbi suna sheKi, ko ina shimfide da marbles, ga

Kamshi ga sanyin iyakwandishin da ke ratsa ko ina, saboda duk baKon da ya zo ya ji

dadin tarbar da aka yi masa.

Ganin ta wuce sumul ba tare da wani abin daga hankali ba, ya sa ta kawo ajiyar
zuciya ta sauke hade da lumshe idanu, ai kuwa kan ta bude su ta ji ta hadu da wani

abu mai tauri da Kamshi da dumi, da sauri ta bude idanunta, gudun ko ta ji ciwo.

Ko me take tunani, ba ta ga abu a gabanta ba... Nan ta yi turus! Domin kuwa ba abu

bane wanda dai take ta Kokarin gujewa, shi din ne ta fada kuma rigimarsa, domin ko Www.bankinhausanovels.com.ng

ba ta fadi ba, wannan kallon na tsantsar rigima ce a tare da shi, hakan ya sa ta kauce masa cikin sauri.

"Yi hakuri!" Kawai ta iya fadi, domin ba za ta

ma iya ce masa Yallabai (Sir) din ba, saboda dalilai masu dama.

"Idanun naki dama ba su gama warkewa bane, ki ka cire tabarau din?” Ta san

magana ya fadia mata, amma ba ta nemi tanka masa ba, kafin ma ta ce wani abu ya

ce, “Sannan, meye dalilinki na tauye min lokacina?"

A razane ta dago idanu aka yi rashin sa‘a idanunsa tsab! A kanta suke, "Ko kuwa

Karfe hudu da rabi ki ka ji an fada miki shi ne lokacin tashi a aiki?"

A hankali ta sauke numfashi sannan ta ce, "Ayi min uzuri, ina da abu mai

muhimmanci ne da ya taso min, shi ya sa."

Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya hade ran nan, uwar hadewa, sannan ya sa
kai cikin falon hace da saKala hannunsa daya a aljihun wandon suit dinsa na Hugo Boss, yayin da ta samu daman shigewa, amma ba tare da ta gagara jin tasirin

Kamshin turarensa a cikin ranta ba, domin kuwa Kamshinsa kadai ke sawa ta

haukace idan ta tuno abubuwa da dama, bare aje ga idanunsa masu rigima.

Da Kyar ta samu hannunta ya bar rawa har ta iya tada motar, ba wai tsoron Oganta

ne ya haddasa mata wannan halin da ta fada ba, tsoron abinda Ogan nata zai iya yi

game da ita, shi ya fi daga mata hankali.

A gaggauce ta wuce cikin gida, sai da ta yi wanka ta shirya, sannan ta nemi Maami

wacce ta baro a Kasa, ita ma dawowanta kenan daga kotu inda take aiki a (Court of Appeal).

Ta fi minti goma a zaune a falon ba tare da sanin abin da ke gewaye da ita ba, har

sai da Fa’iz Kaninta ya yi mata ihu a saman kai, ya sa ta firgita za ta hau shi da fada

ne. Fa’iz ya ce, "Adda Ummu, dole ya yi miki ihu ai, don kin yi nisa. Maami ke

tambayarki ko kin bada saKonta kan ki dawo?" Sai lokacin ta kula da Maamin ma a falon.

"Wai meke damuna ne?" Ta fada a Kasan

ranta, gaya zuciyarta ce ta ba ta amsa da,

"Me yake damunki kuwa? Banda tunanin Zaid Abdur-Rahman?" Take ta ture

wannan tunanin, "Allah ya sawwaka na yi tunaninsa, akan wane dalili? Mutumin da ya haramta gareni?

Ko bai haramta ba, da ni da tunanina mun yi masa fintiKau, babu abinda zai sa

tunaninsa ya zama halastacce a gareni. Saboda babu wanda na tsana duk duniya, irin sa."

"Umm Adiyya lafiya ki ke kuwa?" Jin muryar Maami ya sa ta yi saurin yake baki,

cikin murmushin kawar da damuwar da take ciki ta ce, "Maami lafiya Kalau, kawai Www.bankinhausanovels.com.ng

dai na gaji ne. " "Sannu, ki huta mana sannan mu ci abinci."

Shafa dan shafal din cikinta ta yi, cikin yatsina fuska ta ce, "Maami ku fara kawai, a

Koshe na ke."

Kallon tsab! Mahaifiyarta ta bita da shi sannan ta ce, "Kin tabbata ba wani abu ko?

Ba dai Za..." Da sauri ta kada kanta ta ce, "Ba komai Maami. Ku ci bari na yi shirin

sallah na ga maghrib, ya gabato."

Ta dade tana azkaar, bayan ta idar da sallah, sannan ta sauko falon daga dakinta

da ke sama, sai dai turus! Ta yi ganin mutanen falon, wani irin abu ne ta ji ya taso ya

turniKe mata zuciya yana yi mata ciwo. Daidai lokacin da abin tuhumar nata ya juyo

suka hada idanu.

Tunda take, ba ta taba ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdur-Rahman ba. Ta so ta juya, amma ganin su Maami ya sa ta fasa, ta shigo falon ta gaishe su

sama-sama, don tare suke da Yayanta SaadiK

Har ma yana tambayarta, "Umm A. Da fatan dai wadannan ba su ba ki wahala a wurin aikin?"

Murmushi ta yi har sai da kumatunta ya loba, sannan ta ce, "Mutanen da suka bi ni

har da roKo, saboda na yi masu aiki ba sau daya ba ba sau biyu ba, ai ka ga ba za

su yi garajen ba ni wahala ba, don haka ina aiki na cikin kwanciyar hankali, with full

amenities. Ko ba haka ba?" Ta fada cikin dan murmushinta hade da harde

hannayenta saman Kirjinta.

Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yake yi,

"Saadik, dole mu kula da Adiyya, saboda ko ba komai ta san yadda take amfani da

Kwakwalwarta, she's very smart." Ya Kare maganarsa cikin murmushi.

Tsumewa ta yi hade da aika masa kallon banza. Dole ka ce ku na kula da Adiyya, Www.bankinhausanovels.com.ng

banda dan karan wuyar da ku ke ba ni, me ku ke yi? Kullum na yi aiki, sai an

Kwakulo kuskure a ciki, ko me ya kai shi dauka na aikin ma tun farko, oho? Barin

falon ta yi zuwa kicin, inda ta yi zamanta a can ta ci abincinta.

Bata sake bi ta kan falon ba, bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado

sai aikin saKe-saKe take yi, abu daya ke yawo a Kwakwalwarta, kuma hanya daya

ce da za ta bi don magance wannan damuwar, ita ce ta bar aiki a AZ IT Consultants.

A karo na uku!

Ko su kadai suke daukar ma'aikatan da suka karanta fagenta, ta yafe wannan aikin

da irin uKubar da take shiga kullum wayewar gari. "To ma wai aikin dole ne?" Umm

Adiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba, ta samu kanta tana tsiyayar

hawaye. "Duk har da laifin Abba ma, yaya za ayi bayan na fada masa komai kuma yace naci-gaba da aiki da su?"

***********

Babbar yatsar hannunsa na dama yake kadawa kan sitiyarin motar, yana tafe yana

tunanin abubuwa da dama. Kwarai ya san cewa ba Karamin kuskure ya yi ba da ya

sake barin Umm Adiyya ta shiga rayuwarsa.

Koda kuwa ta fuskar aiki ne, duk da kasancewar ba yadda za ayi ya yakice ta daga Www.bankinhausanovels.com.ng

rayuwarsa, saboda abin da ya hada su ba Karamin abu bane da zai warware a dare

Daya, abin da ya hada su dangataka ce da ba ta rabewa ba, a tunaninsa ya mance

da ita, ya sa ta a gefe, ba za ta taba tayar masa da abubuwan da ya zaci ya

adanasu ya boyesu a wani lungu a can cikin Kirjinsa ba, sai dai yau abin da ya gani

a tare da Adiyya, sun motsa masa abubuwa da dama masu dadii da masu daci.

Amma ya zama dole ya dubi Dangaren daya dace ya yi aiki da shi, saboda hakan zai

fi fishe su, daga shi har ita. Har rana mai kamar ta yau ba zai taba mance abinda ya

faru ba. Birki ya ja da Karfi, a dalilin wata motar da suka kusa yin karo, ashe tsabar

tunani, ta sa ya bar kan hanyarsa ya hau wata daban.

“Zaid Abdur-Rahman ka wuce haka!" Ya fada a bayyane, yayin da ya yanki kwanar

(Darussalam Close da ke Wuse 2), inda shiryayyen gidansa yake.

##########

Zaid Abdur-Rahman Nafada da na uku a cikin yara goma sha bakwai wurin

mahaifinsa, mutum ne da ya taso cikin gatansa dai-dai gwargwado, mutum ne kuma

da ya saba samun duk abin da ya nema, ko ya yi burin samu, saboda hazaKarsa da Www.bankinhausanovels.com.ng

kuma jajircewansa.

A garin Gombe ya yi Karamar makarantarsa kafin ya wuce zuwa sakandirensa a

birnin tarayya Abuja, a Kwali. Wannan ya yi mafarin zamansa gidan Baffansa Kanin

mahaifinsa Builder Zubair Nafada.

Tun daga lokacin kuwa zaman shi ya fi yawa a hannun Kanin mahaifin nasa, don ba

kowane hutu ma yake zuwa gidansu ya yi ba. Sai a nan Abuja yake hutunsa. Koda

ya tashi tafiya jami'a. Baffansa (Abba) ne ya yi masa duk wani abin da ya dace har

ya wuce India, inda ya karanci aikin Injiniyar sadarwa. (Telecommunications Engineering).

Kallo daya za ka yiwa Zaid, ka fahimci shi ba mai yawan magana bane.

Bayan ya kammala karatunsa na digiri ne, ya wuce karo ilimin Masters dinsa inda

ya tafi jami'ar Hertfordshire da ke United Kingdom, duk dai kan IT, ya karo ilimin.

Mutum ne wanda ya riki neman ilimi da tsantsar muhimmanci, haka nan yana da

karambani wurin yawan bincike da nemo sabon abu, wannan ya sa ya yi suna har ya

yi fice. Dalilin haduwarsa da wani bayarabe ma kenan wurin wata gasa ta Kasa har

suka zamo abokai.

Kowa yana inda yake, yayin da Zaid yake aiki da ma'aikatar kimiyya da fasaha ta

Kasa. Femi yana aiki a Warri, amma a hankali suka zame suka tada wani dan

kamfaninsu na gina Softwares da kuma Kera gamayyar kwamfuta (Hybrids), a Www.bankinhausanovels.com.ng

hankali abinsu na bunKasa har suka gamu da wani mutumin Adamawa Sufyaan. Shi

ma ya zuba hannun jarinsa, aka ci-gaba da tafiya, ga shi yanzu bayan watsa kayan

kamfaninsu da suke yi cikin Kasa, suna shigo da na waje, sannan suna bada

shawarwari wa masu neman shawara .

Wannan ya sa suka yi fice kan ka ce meye (AZ IT Consultants), ya yi suna a fadin

Kasar, don ba inda ba su shiga domin hada Networks da kuma Kaddamar da sabbin

Softwares, kama daga bankuna da kamfanoni, asibitoci zuwa ma’aikatu da kuma

kafa na’urar tsaro na kamfononi da ma’aikata har ma da gidaje.

Zaid Abdur-Rahman mutum ne tsaurarre da ba ka taba gane alKiblarsa kuma mutum

ne murdaddde, idan ba ka yi sabo da shi ka dade da fahimtar cewa hakan yake ba,

za ka dauka ba wanda ya kai shi fadiin rai. Wannan ya sa duka abokan Www.bankinhausanovels.com.ng

kasuwancinsa guda biyu suke mamaki, idan suka samu abokin ciniki, (Client) ta dalilin Zaid.

Ganin kamfaninsu ya bunkasa ya sa suka yi masa tsari na zamani suka samu ofishi

na musamman suna kuma diban ma'aikata, har makarantar horar da mutane kan

harkar Kera Softwares da kula da Komfutoci, (Maintainance), suna da shi a wannan

kamfanin. Yanzu shekaru bakwai kenan da fara wannan harkar tasu.

Yawan kamewarsa ce ta sa bai ganin amfanin ma ya tsaya wai bin mace, tana ba

shi wahala. Wannan ya sa shi sam mata ma ba su gabansa bare wata aba wai

soyayya. Soyayyarsa daya ce, ita ce ga Komfutarsa. Idan har ka ga yana sakewa

mutum fuska, to 'yar-uwarsa ce, mutum daya ce jininsa ya hadu da nata wato

Asma’u.

Abinda ya sa kuma ba ta daukarwa kanta halayyar shisshigewa da namiji ba,

sannan kuma tana da gudun zuciyar mutum. Tun tasowarta yake kulawa da lamarinta, domin tasu ta zo daya.

**********

Www.bankinhausanovels.com.ng


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 1 BY AZIZA IDRIS GOMBE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...