TAME GARI COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TAME GARI COMPLETE

TAME GARI COMPLETE

- - Post a Comment

 TAME GARI COMPLETE 
   Na rantse da Allah bazan yadda ba sai an biyani nikana tun 


kin isa ma wlh kika sake kika je kika fadawa innata yaseen sai kinci ubanki cewar dije dake kara tattake garin dake zube a kasa kuma an barar din duk ranar da kika qara cemin dijan gala tame gari tuwon gidanku ma zanje in barar wlh 


su Shatu dake gefe suna kallo ba damar suyi magana dije taci uwarsu dan haka sukayi gum ko yi hakurin sun kasa fada hafsi kuwa sai rizgar kukanta takeyi dan tasan yau idan taje gida kashinta ya bushe gurin delu dan saita mata dukan mutuwa kuma tasata nemo mata wani garin koda ta tuna ai saita kara bare baki dije ce ta kalleta tace wai ke uwar me nayi miki da kiketa min wannan kukan danma ban faffasa miki baki ba hegiya me idon gyada 


shatu ce ta karaso kusa da ita tace kin san delu dukanta zatayi idan taje gida kin san dai ba imani ne da ita ba 


shuru dije tayi na dan wani lokaci kamar wadda ta tuna wani abun sannan kuma tace toh kinga ke kika jawo wa kanki tunda kika tsoka ne ni amma kiyi haquri kinji tahi nasan yadda zamuyi amma sai kin bani hakuri 


da sauri hafsi tace yi haquri dan Allah 


toh naji ya sunana 


Anti dije 


wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta dan tana masifar son sunan nan na 'yan binni dan haka da sauri tacewa hafsi taso muje gidanmu in baki dawar ki kara kaiwa nikan 


da sauri hafsi ta mike dan tasan ko yanzu takai nikan sai ta ci ubanta dan ta jima dan haka da sauri suka je gidansu dije koda suka je dije bata boyewa inna saudi komai ba aikuwa ta basu dawa suka kai nika har gida dije suka raka hafsi aikuwa delu kamar ta ari baki taita jarabar ta dayake 'yan dukan basa kusa sun dai samu rabon zagi amma bata daki hafsi ba


********

mota ce kirar honda Accord LC ta shigo cikin garin Gawo kasancewar rashin kyawun hanyar ga kuma da alama wanda ke cikin motar yasha tafiya mutum biyu ne ciki matasan samari kyawawa daka gansu kaga wadanda hutu da nera suka zauna a wajen tuki yakeyi kamar wanda aka yiwa dole kafin ya waiga ya kalli dayan yace cikin kasalalliyar muryarsa 


Habeeb wlh nagaji dayawa na matsu mu qarasa cikin garin nan in yada zango kan gadon tsohon nan 


wanda aka kira da habeeb yayi murmushi kafin yace hmm kaima kenan bare kuma ni dana sha tafiya kwana nan gashi yau ma son ganin wannan me ran karfen yasa na biyoka 


hmmm kai dai bari ai wannan tsohon inaga rokon Allah yakeyi mana shiyasa bama iya daukar lokaci bamu ganshi ba ko daddy ma fa kullum shi batun shi baba malam kusan koyaushe yana kan hanya 


toh Allah yaja da kwana dai 


Ameen ya Allah 


kam bala'i ta fada yayin da taga motar na kokarin shigewa alamar ma na ciki besan me yayi ba giginyar dake hannunta ta dauka ta saita glass din motar ta wurga cikin sa'a kuwa ta daki glass din side driver sannan taje ta hada da bakin habeeb wanda yagama amsawa da ameen yanzu 


wani wawan birki ya taka tare da kiran ya Allah sbd ganin abun da yayi kamar a mafarki dubansa yakai inda habeeb yake yaga nan da nan bakinsa ya haye ya wani kumbura kamar bakin jaba ga kuma jini na zuba yaso yayi dariya harga Allah amma ba hali dole ya ambaci kalmar subahanallah ya fara kokarin bude motar ya fito danya zagaya gurin habeeb dan shi har yanzu baisan ta inda abin yafaru ba amma dai kawai yaga wulgawar abu 


tsaye take ta rike kugu da hannu daya dayan kuma wata katuwar giginyar ce datafi ta farko girma 

kwalliyar fuskarta kawai yagani yaji gabansa ya fadi dan wlh babu tantama wannan aljana ce 


wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahir rahmanir raheem ya fara ambata cike da tsoro da faduwar gaba domin dai babu tantama wannan aljana ce duba da yanayin ta gata fara sol saika ce zabiya ga kuma uban bakin kwalli data shafa a bakin nan kamar 'yar auta ga jagira cinku ta hade da kwallin dataja hawayen masoyi 


jikinsa ne ya hau kyarma inda ita kuma dije take ta fahimci meyake nufi aikuwa a zuciyarta tace anzo gurin 


harara taci gaba da wurga masa tanata juya ido inda shikuma hakan ke kara firgita shi cikin karkarwar jiki ya qarasa inda habeeb yake ya sunkuyar da kansa kasa sakamakon nauyin daya yi masa sbd giginyar ta bugi kansa ga haqorinsa guda daya daya fita ga bakin ya kumbura yayi tsayi kamar shantu cikin rawar jiki Nasir yakarasa inda yake ya bude murfin motar yana me karanta duk addu'ar data zo bakinsa dago kansa yayi ya dubeshi jin yanata kwarara addu'a sai ya fahimci lallai gamo sukayi domin ya hango aljanar tsaye da irin tasu giginyar ta Aljanu tanata juya ido duk da jirin dayake ji hakan bai hanashi rudewa ba shima ya kama kokarin fitowar nan suka kankame juna shida nasir wanda har kwalla yafara yi dan tsoro musamman duba da yayi da yanayin gurin babu komai sai tarin bishiyoyi da besan kona meye ba amma dai yasan harda na kuka kuma sune gidan aljanu 


cikin wata irin murya da malkwada harshe dije tace ku bil adama daga ina 


wani irin fitsari ne ya kufcewa naseer shiko habeeb ji yayi kamar ya suma dan kanshi saida ya amsa 


ko bakwa ji ne ina tambayarku?


cikin in i na nasir yace yi....yi..ha.k..uri.daga Abuja Abuja wlh muka zo 


shine aka ce dan kunzo daga binni kubi takan 'ya'yana suna tsaka da yin wasan su wato sbd kun raina mu ko 


ah ah wlh ba...bahaka bane wlh ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba dan girman Allah kiyi haquri wlh bamu sani ba


toh naji zan hakura amma sai dai kubar abin hawanku anan ku qarasa da kafarku inda zaku ko kuma ni inkai ku 


ah ah wlh mun gode suka fada a tare zamu karasa da kafarmu ina ke ina wahala akanmu 


hahahahahaha

tayi dariya sannan tace saini dije uwar aljanu ku wuce amma fa bazan kyaleku ba duba da yadda kuka raunata 'ya'yana yanzu haka suna bangon duniya wajen me magani dan haka sai naje naga yadda jikinsu yake tukunna kafin in san wanne hukunci zanyi muku


kuuuuu cikin nasir yayi wata kara dan girman Allah kiyi hakuri wlh bamu san dasu bane ina mu ina aikata haka muna sane 


toh naji ku tashi ku tafi gobe kuzo ku dauke wannan motar amma ba yau ba 


to toh toh mun yadda wlh


sam habeeb yakasa tafiya yayin da naseer ne ya kamashi da kyar yasaba a kafada ya miki hanya bako waiwaye harda hadawa da dan gudu bako waiwaye 


tunda dije taga haka  ta zube a gurin tanata dariya harda hawaye a irin wannan yanayin su shatu suka qaraso suka risketa nan suka shiga tambayarta sam kin fada musu tayi gashi ba damar su matsa ta dankari banza dan karfi ne da ita kamar yaki inji su duk ta fisu karfi 


sai da tayi me isarta kafin ta mike tace mu tafi 


hafsi ce tayi karfin halin tambayarta ina gyadar da kika samo ?


ban sani ba tafada tana harararta 


ai kuwa tayi gum suka ci gaba dactafiya da zarara ta tuno yadda bakin habeeb ya koma da kuma yadda taga Naseer yayi fitsari saita kuma kyalkyalewa da dariya sudai su hafsi nasu ido amma ba damar tambaya sai uwar gayyar ta so bada labari dakanta

DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "TAME GARI COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...