RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 
                  Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Da isarsa gida ya sami Nasreen ce kadai a falo tana goge-goge. Saura Kiris wata kwalba ta fado mata, ya Karasa cikin sauri ya rike kwalbar tare da sauya mata wuri. Ransa ya kai matuKa abaci don haka ya ce, “Ke! Waye ya sa ki wannan aikin? Iyye Nace wa ya sanya ki aikin nan?” Nasreen ta yi shiru saboda wani irin tsoronsa da take ji, ga shi dama dazu ta gama kukan rashin Nawfal dinta a kusa da ita, da yana nan duk irin ayyukan nan zai iya amsa yayi Ga masu aiki nan birjik a gida, amma Umma ta tsani ta ganta a zaune yanzu za ta hau Kirkirar aiki tana sanyata. Ita ba gani take yi ba..Ta Kone a hannunta, don haka bata son ya guni ta dunKule jikinta, duk da . irin azaban da hannun yake yi mata. Da Karfi ya - daka mata tsawan da yasa ta daya hannunta har ya ci nasarar ganin Konewar da ta yi. Shiru ya yi yana duban hannun, hakan yasa hawayen - fuskarta Samiun daman ci gaba da sauka. Yana da

ZAMU TASHI 

tabbacin Watarana sai sun kashe masa ita sannan hankalin su zai kWanta. Sakin hannun yayi yana sake dubanta cikin tausayawa ko wanene yayi masa hakan bai kyauta masa ba.

Umma ce ta fito tana fadin, “ihun da kake yi na menene? Babu yadda ba ayi da yarinyar nan ba, ta bari ga masu aiki nan amma ta ki amincewa: Shi ne ta Kone’ amma bata haKura ba. Duk nan babu wanda zai tsaya wai sai ya lallaba Nasreen, domin ta fi kowa sanin abinda ya kamata da wanda bai kamata ba.” Ran Sultan ya sake baci, kawai ya rufe ta da fada, “Na gaji da lamarinki Nasreen, na kusan daukarki in mayar da ke gurin Abba. Me zai sa ke ba gani kike yi ba ki ce wai dole sai kin yi ayyukan nan, ina kika taba ganin hakan? Kinsan Allah nan gaba kika sake yin rashin hankalin nan. dukan tsiya zan yi maki.”

Farin ciki ya kama Umma yana kallonta da gefen idanu yadda take murmushin mugunta. Nasrecn kuwa kuka sosai take yi. Ga zafin Kuna - ga zafin sharrin da Umma ta yi muta, ga kuma zatin kalaman Sultan akanta. Kuka tayi sosai har da shessheka. Umma ta ce, “Oh ji gulma. Ke shi kenan babu wanda ya isa ya yi maki dada sai ki kama kuka? Duk kai ka lalata yarinyar nan Wallahi.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Sultan dai bai ce komai ba, sai kamo hannun Nasreen da ya yi yana cewa, ‘Mu je insa maki magani a ciwon. Idan kin gadama ki yi kukan jini ma bai dameni ba, jikinki ne ke kike jin zafin ba ni ba.” Sultan ya kama hannun Nasreen suka shiga cikin dakinsa, a lokacin su Hafsat suka fito suna KyalKyatar dariya, har da tafawa. Sultan yana shiga dakinsa ya mayar da Kofa ya rufe, ya maidota jikin Kofar ya rungumeta tsam yana mayar da ajiyar zuciya. Sai a wannan lokacin ta tsagaita da kukan, itama ajiyar zuciyar ce ta Kwace mata da Karfi. Cikin natsuwarsa yake magana, “Sorry Wife. Ciwon nan da kika ji ya gigitani matuKa. Bana son dai-dai da sauro ya cizar min fatan nan naki. Ban yarda ke kika kai kanki wajen wuta ba. So gaya min me ya faru?” Nasreen ta sake sanya . marainiyar kuka, ita ta san ta tabbata marainiya. Bubbuga bayanta yake yi, daga bisani ya rabata da jikinsa ya dubeta yadda take kukan, yasa hannu ya dauke hawayen fuskarta sannan ya Sake mayar da ita kafadarsa, “Bana son kukan nan Nasreen, idan kina irin wannan kukan zuciyata tana Kuna ina jin kamar ina cutar da ke, idan hakanne kina sane da sai Allah ya kama ni? Ki yi hakuri ki natsu.” Ta daina kukan amma hawayen nan kamar ruwan famfo. Hannunta ya kama ya dawo da ita kan gado ya zaunar yana sake dubanta. “‘Nasreen naso a ce kina iya ganina da kin ga irin tashin hankalin da nake ciki, duk da haka za ki iya fahimtar yanayin da nake a ciki idan kika taba zuciyata da ke Jullue a cikin Kirjina.” Hannunta ya tura a daidai saitin zuciyarsa, tana iya jin yadda yake bugawa da Karfi. Jikinta ya yi sanyi ta yada kanta a fadarsa, ya ci gaba da cewa, “Idan nayi maki fada a gaban Umma, ba wai nayi da gaske bane, a’a nayi ne domin su yi zaton bana sonki, yin hakanne kadai zai rage maki wahalar da Umma take shirin baki a cikin gidan nan. Ina jin daci idan na zo na sami fuskarki ba yadda na barki ba, ina jin ciwo idan naga kina aikin da bai kamata a ce kina yin sa ba. Gara in yi maki fada a gaban jama’a in shigo daki in lallashe ki. Soyayyar da nake yi maki ta yi yawan da bana iya boyeta a gaban kowa, shiyasa na nemawa kaina Control.”

Nasreen har yanzu bata yi magana ba, amma kuma tausayin Kanta da na mijinta yana sake kama ta. Bata san a nan gaba me kuma zai faru ba. A hankali ta yi magana, “Ka yarda da ni Dee? Ka amince ba zan taba ha’intarka ba? Ka yarda da tarbiyya irin naka
Sultan ya sake dauke hawayen fuskarta yana Www.bankinhausanovels.com.ng dubanta, “Idan har za ki iya aika ta
idan kika ji zafi za ki kiyaye sake Kona min fatan jikin ki.”
Nasrecn tana murmushi tana daga kanta alamun ta amince. A gadon ya mayar da ita ta kwanta, ya hada kansu wuri guda ya dan bata fake, ta shafi kumatunta tana murmushi, “Idan irin wannan horon shi ne horo, lallai kullum zan dinga aikata laifuka masu tarin yawa don in sami horo mai sanyi daga gun Dee.” Shi ma murmushin yake yi, yana son ganinta cikin nishadi.Mikewa ya yi da nufin dauko abu, kawai ya ji anbanko Kofar dakin , babu Sallama. Ya mance shaf bai sa key a Kofar ba. Zuba wa Hafsat idanu yayi yana jin ransa yana Kuna. Ta yaya za a koyawa budurwa shiga dakin matar aure babu Sallama? Idan ta taso a hakan watarana za ta yi hakan a in da bai kamata ba. Ita kuwa Nasreen tsoron Karar Kofar da ta ji yasa ta maKale jikinta. Sultan ya kafe ta da
-idanunsa da suka rine saboda bacin rai,
“Ina jin ki wani uzurin gareki kika shigo min daki babu Sallama?” Kame-kame ta kama yi, ta rasa me Za ta ce, sai kawai ta juya da nufin fice wa daga dakin. Sultan ya fincikota ta dawo, ya hada kanta da bango wanda yasa ta saki razanannan Kara. Tuni ya rufe Kofarsa ya murza dan makulli. Ya je ya dauko Belt dinsa ya dinga shimfida mata a jiki. Ihun Hafsat kawai ake ji, a ya yin da Umma da Zakiyya suke ta buga Kofar, Umma tana masifa tana cewa idan bai bude Kofar ba, sai ta tsine masa, amma ina Sultan baya ma jin abinda take cewa.  Nasfeen kuwa kuka take yi da iya Karfinta tana roKonsa, sai dai itama baya _ sauraren muryarta. Dole ta tashi tana lalube, Hafsat tana . ganin hakan ta fahimci so take ta taimaketa, don haka ta koma bayan Nasreen tana kuka tana roKonsa, idanunsa sun rufe baya gane komai, domin yana ji a ransa da ta zo ta same su a wani yanayi bai san irin kunyar da zai ji ba. Haka yana da tabbacin sai ta gayawa mahaifiyarsa.

Nasreen tana KoKarin kareta, Sultan yasa hannu ya fizgo Nasreen ya watsar da ita gefe, hakan yasa ta fadi akan hannunta har hannun ya yi wani irin Kara. Nasreen ta fasa ihu, ta zube a wurin. Hakan ya jawo hankalin Sultan akan abinda zuciyarsa ta jawo masa ya aikata. Cikin tashin hankali ya Karasa wurinta, yana jijjigata. Abinda bai sani ba, tuni hannun ya gurde, idan ba karaya ba, gocewan Kashi. Www.bankinhausanovels.com.ng

Hafsat kuwa sauri ta yi ta bude Kofar ta fada jikin Umma da suka gaji da bugun Kofar, — suka tsaya jigun-jigun. Kuka take yi sosai saboda duk ta gigice. Ga jini ta gefen bakinta, haka jikinta duk ya farfashe saboda duka. Umma ta zura kanta cikin dakin nasa, sai dai a yadda suka ga Nasreen yasa kowa ya tsaya kallon ikon Allah. Sultan gaba daya ya fita hayyacinsa girgiza ta kawai yake yi, yana shafar kanta, amma babu ko alamun motsi.

Cak ya dauketa da nufin kaita asibiti, Umma ta Harare shi ta ce, “Gidan uban wa za ka kaita? Maza ajiyeta babu ida za ka je da ita. Al shi mai zuciya Karshensa danasani ne. Mayar da ita. Ke Zakiyya samo ruwa a watsa mata. Yadda Hafsat ta sha wahala ita ma sai ta dandani wahalar nan. In banda ka raina ni, saboda ina zaune a gidanka shi ne za ka tasa Kanwarka da irin wannan duka kamar ka sami jaka? “ Kawai Umma ta sa kuka. Hankalin Sultan ya sake tashi ganin mahaifiyarsa tana zubar masa da hawaye. Dole ya mayar da ita ya shimfide ya karbi ruwan da Zakiyya ta kawo yana shafa mata a hankali. Dago kansa ya yi yana son rokon mahaifiyarsa ta yi hakuri ta bari a kaita asibiti,
sai dai dukka sun watse babu kowa akansa. Mayar da idanunsa ya sake yi kan Nasreen, ya rasa me ke masa dadi. Ganin tana motsi ya sa ya saki ajiyar zuciya da Karfi, “Nasreen ki yi hakuri ki tashi, ban san lokacin da na aikata maki hakan ba. Bai kamata ina daki da matata, Kanwata ta fado dakin babu Sallama ba, idan ‘na barta haka za ta ci gaba, har ta zo watarana ta aikata hakan a in da za ta yi danasani. Ki yi haKwri Nasreen.” KoKarin tashi take yi ta ji hannunta ya riKe wani azaba ya ziyarci Kwakwalwarta, ta fasa Kara. Da sauri ya mayar da ita ya kwantar yana shafar gashin kanta, “Nasreen kin fadi akan hannunki akwai matsala a ‘hannun, ki bari zan kira mai dori yanzu ya zo ya duba ki. Ina tunanin karyewa kika yi, yadda hannun ya saki.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Nasreen ta mayar da kanta ta kwanta, sannan ta yi magana a hankali, “Allah ya rubuto sai hakan ya faru. Ka daina tayar da hankalinka Dee, babu wanda ya isa ya kauce wa faruwan hakan.” Tana magana tana cije wa saboda tsananin azaba. Bai iya furta komai ba, ya mike ya bar ta a nan yana tafe yana sake waiwayo ta. A falo ya sami Umma tana ba Hafsat taimako. Bai dube su ba, ya yi waje abinsa, hakan ya sake Kona wa Umma rai. Yana fito wa ya tashi dan sanda daya ya tura shi ya zo da mai dori a duba Nasreen. Yana dawowa ya sake wuce su Umma ya nufi gun Nasreen, domin har yanzu ji yake kamar ya fizgo Hafsat ya ci gaba da jibganta.Tana nan yadda ya barta, sai rintse idanu take yi saboda zafi. Mayar da kanta ya yi jikinsa, sannan ya manna mata sumba a goshi. “Ina son ki Wife.” Cikin rufewar idanu tace “Ina son komai naka Dee. Zan jure komai idan hakan zai faranta maka.” Ji ya yi kamar baa taba gaya masa kalamai masu sanyin wannan kalaman ba, ga su dai ba su da yawa amma sun > gamsar da shi. Zakiyya ta shigo take gaya masa - zuwan mai gyaran, ya ce bari ya fito da ita. A hankali suka ta ko zuwa falon, Umma ta zabga masu harara ya kauda kansa zuwa gefe, yana jin damuwa a can Kasan ransa. Da za a fara kama hannun Nasreen Sultan ya saketa yana son fice wa, a lokacin da ita kuma ta riKe hannunsa sosai. Duban mai gyaran ya yi ya ce masa, “Zan dan fita ba zan iya tsaya wa a gyara hannun a gabana ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

” Umma ta ce, “Wallahi a gabanka za a gyara hannun, ashe kana da imani akan matarka?

Akan Kanwarka kuma ko a jikinka ko? To sai ka tsaya an gyara hannun, sai ka hadiyi zuciya ka mutu, ‘yar Gold dinka ta sami matsala.” Sultan dai bai ce komai ba, ya koma ya sake riKe ta sosai ya yl magana a hankali wanda ita kadai ta ji mai yake cewa, sai kuwa nai gyaran da ya dago yana duban su cike da sha’awa, “Wife kada ki damu babu inda zan je ina tare da ke.” Nasreen ta dinga daga kai alamar ta ji. Ana riKe hannun ta yi iya bakin KoKarinta domin ta daure abin ya ci tura, dole ta dinga kuka tana fizge kanta. Sultan din kadai ya isa ya rike ta, idan ba haka ba, riKe ta sai wanda yaci ya Koshi. Umma suna nan zaune ko kallo bata ishe su ba, Sultan kuwa ji yake kamar naman jikirisa ake yanka. Sai da ta kai ya dago yana duban mai gyaran, yace “Don Allah ka yi mata a hankali.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Mai gyaran ya: yi murmushi yana kallon tsantsar Kauna, shi bai taba yarda akwai irin wannan son a tsakanin mata da miji ba, sai yanzu da idanunsa suka gane masa, “Ka yi haKuri yallabai, idan aka ce za a tsaya lallabawa ba zai yi kyau ba, gocewar Kashi ne.” Sultan ya kauda kai ya ce, “Duk da hakan ka yi a hankali.” Mutumin ya amsa yana murmushi ya ci aba da abinda yake yi. Ana gamawa Nasreen ta saki ajiyar zuciya, ta laluba ta kamo dayan annun Sultan, ta yi magana a hankali cikin yanayinta, ‘“‘Dee ka kira min Nawfal, don Allah ka awo min Nawfal.” Tausayinta ya sake cika masa zuciya, kamar ya taya ta kukan, ya ce. “To ki daina kukan insha Allahu zan tafi da kaina in je in kawo maki shi.” tana son ta daina kukan amma wahala ta hana, don haka ta sake cewa, ‘“‘Dee ka samo min maganin barci idan nasha zan daina jin radadin.” Ya so Kwarai ya zolayeta akan idan ta tashi haihuwa ya za ta yi? Sai kuma ya ga idanun Umma gaba daya akansa don haka ya basar yana duban Umma, ta kauda kanta wanda ke nuna alamun tana fushi da shi, yana son ya gama da Nasreen ne, kafin nan ta sauko sannan ya je ya lallaba ta. Da Kyar Nasreen ta iya tashi ya kaita cikin dakinta, shi kuma mai gyara dan sandan ya Sallame shi. Tana kwanciya ya ce, “Wife ranar haihuwa ya za mu yi kenan? Likitoci ba za su barni in zauna kusa da ke ba, bare ki rike hannuna.”
Nasreen ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba. Ya sunkuya dai-dai fuskanta yana gaya mata kalamai a hankali kuma ya dinga hura mata iska a fuska, tana jin kasala tana shigarta, hade da barci wanda ba ta san lokacin da barcin ya yi awon gaba da ita ba. A fili yace, “Allah ya baki lafiya Wife.” Ya sumbaci goshinta ya fice. A falo ya sami Umma da hafsat fuskar nan tata ta kumbura gwanin ban tausayi. Www.bankinhausanovels.com.ng

Har zai wuce Umma ta ce, “Zo nan ina son magana da kai.” Babu musu ya dawo ya zauna yana duban Umman, sannan ta fara magana, “Ka ji tsoron Allah Sultan ka gaya min me Hafsat ta yi maka haka da zafi da har kayi mata irin wannan dukan? Gaya min me ta yi maka? Idan babu laifin da ta yi tsabar mugunta ce kawai, ka gaya min sai in dauki mataki.”

Sultan bai ji dadinl da Umma za ta yi masa magana irin hakan a gaban su Hafsat ba, wannan kamar ta ce gobe su sake aikata irin laifin ne. A natse yake magana kamar babu abinda ke damunsa, “Umma ina daki yarinyar nan ta fado min babu Sallama, ta yaya za ayi da girmanta ta dinga shigo wa mutane babu Sallama? Ashe karatun addininta, da yadda kika ba mu tarbiyyaHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...