RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
                 Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA 


Nan da nan annurin fuskar wacce aka kira da shugaba ya bace bat! “Ke! Kada ki kawo mana zancen banza kin ji? Ya zama dole ki kawo mahaifiyarki da kanki ba sako zan ba wani ya kawo min ita ba, albarkar da ) na samu agun iyayena kafin su bar duniya, sai kowannenku ya sami wannan albarkar. Za ki kawo ta ko kuma sai na dauki mataki akanki? Zan iya daureki shekaru dari ina gana maki azaba, bayan kuma na daukota da Karfin tsiya.”

Sake KasKantar da kanta tayi, “Ina neman tuba ya shugabata. Na amince zan kawo mahaifiyata da ranta. Farin cikinki a kullum shi ne nawa.”

A nan suka yi wasu maganganu wanda su kadai suka san abinda suke cewa. Sannan aka ba wani wuka ya karba yana mai sake rusunawa alamun girmamawa.

Wannan yarinyar da ke kwance kawai ya caka mata wukan, wanda yasa Nawfal gigicewa ya ture wani abunda bai san ko mene ne ba, jikinsa babu inda baya rawa.

A gigice suka walwayo basu ga kowa ba, a take aka tura wasu guda biyu su je su bincika waye yake yi masu leken asiri? Jikin Nawfal yana rawa, yana KoKarin komawa dakin da aka kai su sai dai ko sama

Www.bankinhausanovels.com.ng  ko Kasa ya rasa gane wani dakin ne? Hakan yasa ya sami wuri ya labe jikinsa yana kyarma. Ita kuma Nasreen da ta ji shiru, sai kawai ta fito tana lalube tana neman Nawfal. Duk a tunaninta sun tafi da Nawfal dinne shi ya sa ta gigice, tana tafe tana cin karo da abubuwa. Don haka mutanen nan suna fitowa suka yi arba da ita tana lalube. Cak! Suka dauketa suka kai dakin tsafin. Nawfal yana jin shiru ya koma yana duba dakin, da Kyar ya gano dakin yana shiga babu Nasreen babu dalilinta. Ya duba ko ina bai ganta ba, hankalinsa ya sake tashi, ya fito yana dube-dube. Kai tsaye dakin tsafin

ZAMU TASHI 


ya koma ya sake labewa. Ganin Nasreen a hannunsu yasa jikinsa ci gaba da bari. Har yanzu yarinyar da suka kashe tana nan kwance an sa wani KoKo antara jinin. Nawfal ya rasa abin yi yana nan a labe ya ji suna cewa, “Makauniyar banza! Me zai sa ki fito kina yi mana bari bayan ke ba ganin komai kike yi ba? Sai gobe da daddare zamu yankaki saurin me kike yi da za ki kawo kanki?” : Nawfal ya saki ajiyar zuciya. A lokaci daya tsoronsa ya dawo da yaji shugaban~ - tana cewa, “Ina jin Kamshin mutum a kusa da mu. Ba yarinyar nan ce muka ji motsinta ba, saboda sai da aka caka wukKan nan sannan muka ji barin abu alamun antsorata. Ku je ku sake duba min sosai, haka ku duba dan uwanta dinnan naga yana da tsaurin ~ idanu, idan shi ne ku kawo min shi inyanke kansa musha farfesu. Nawfal ya lallaba cikin sa’a ya koma dakin ya kwanta kamar mai barci. Duban duniyar nan sunyi basu ganshi ba, da suka koma dakin suka haske 


Www.bankinhausanovels.com.ng  shi, suka tabbatar da barcin yake yi, kafin suka fice. Hankalin Nawfal yana gun Nasreen, idan bata dawo ba, ya zama dole ya-tashi ya bi bayanta sai dai komai zai faru ya faru. Yana jin aka shigo da ita, sannan wanda ya shigo da ita din ya fice abinsa. 


Nawfal ya tashi zaune ya jawota jikinsa yana jin yadda take kyarma, “Nawfal ina ka tafi ka barni? Nawfal me yasa za ka 


. dinga yin nesa da ni?” Hakuri kawai yake ba ta. Yunwa da ~ Kishin ruwa sun hadu suna neman su yi 


masu illa, domin tunda aka kawo su sun KI cin komai haka sun ki shan komai. Gaba daya sun soma galabaita. Sai ga wani namiji da abinci da ruwa ya kawo yana hararar su, “Ga irin abincin da kuke son ci nan ankawo maku. Kin ci sa’a ba ma yanka mutum idan « yana jin yunwa, da haka zamu sha farfesun ki. Maza ku cinye.” 


Nasreen ta ce, “Oh Nawfal kana jin yadda ake fadin yanka mutum kamar za a yanka rago?” 


Nawfal ya dinga diban abincin yana sa mata abaki, haka take amsa tana ci tana shan ruwa har cikin ya cushe, sannan shima ya ci sosai. Tsohon nan ya dube su ya tabe baki. Nawfal yana son sanin dalilin kawo wannan tsohon a cikin yara. Haka ya ishe su da kallon rainin hankali. 


Washegari kamar yadda suka yi alkawari haka suka shirya Nasreen za a kaita a kasheta. Tsohon nan sai ya dubi_.” Nawfal ya tuntsure da dariya. Nawfal dai addu’a yake yi iya Karfinsa bai daina ba, + haka ma Nasreen gabanta yana fadiwa tana addu’a. Tunda suka kama hanyar dakin da ita, ta nemi duk wani tsoro ta_ rasa. Damuwarta daya Nawfal da za a raba su. Ta fara tirjewa suka jawota da Karfi. Nawfal ya Www.bankinhausanovels.com.ng 


~ dubi ruwan da suka sha suka bari, ya dauko ya kafa kai yana addu’a. 


A lokacin ita kuma aka shiga da ita, aka kwantar da ita. Shiru. ta yi tana ambaton sunayen Allah. Bayan sun gama surKullensu ne aka daga wuKar da ninyar 


soka mata. Ba tare da sun ankare ba, suka ji saukar ruwa kamar yayyafi, wanda Nawfal ya watso. A take kowannensu ya fara atishawa tun suna yi har suka bar dakin, ba tare da Nawfal yasan ina suka buya ba. Shi dai ya Karasa ya daga Nasreen yana janta tana cewa, “Nawfal har yanzu Kafata da ciwon nan bana iya taka ta sosai. Shi dai janta kawai yake yi. Bai san inda yake tsoma Kafafunsa ba. Tsayawa ya yi yana haki a lokacin da yaga Kofofi sun rabu biyu. 


Nasreen da ba gani take yi~ba ta ce, “Nawfal me yasa muka tsaya?” Ya ce, “Nasreen Kofofi biyu na gani na rasa wacce zamu shiga?” 


“Ka duba hannun dama mu bi hanyar. Kafin ka shiga mu _ karanta Ayatul Kursiyyu.” Babu musu ya aikata abinda ta gaya masa. Yana tsoma Kafafunsa ga mamakinsa sai gasu a waje a bakin titi. Waiwayowa ya yi yana son ganin Kofar. Sai dai ko sama ko Kasa babu wannan Kofar. Www.bankinhausanovels.com.ng 


Nawfal ya saki KakKarfar ajiyar zuciya ya ce, “Allah mun gode maka. Nasreen kin ganmu nan a titi.” Nasreen ma ta yi godiya ga Allah sannan ta ce, “Ka tari a dai-daita sahu daga nan ka tambaye shi nan ina ne? Sai ya kaimu tasha muyi shatar mota zuwa Kaduna ko?” 


Babu musu ya aikata abinda ta gaya masa. Abin mamaki antabbatar masu suna cikin garin Abuja ne. Don haka suka tari taxi suka ce ya kai su tasha. Sun kama ~ hanya dukkansu da kalar tunanin su, ita dai Nasreen sai addu’a take yi Allah ya kaisu ~ gida lafiya ba tare da wata matsala ta sake samun su ba. 


Sultan yana zaune a cikin mota yana duba jarida, kansa yana matuKar sara masa, ya rasa meke masa dadi. Dole ya ayjiye jaridar ya koma dabi’arsa na kallon gefen titi. Nasreen tana yawan zuwar masa a cikin mafarki abin har ya kai ya fara samun sabani a tsakaninsa da Zakiyya. Duk da su Umma sun koma, hakan baya hana Zakiyya Www.bankinhausanovels.com.ng 


kiran Umma ta kai Kararsa. Shi kansa yawan shirunsa yana damunsa, hatta I.G sai da ya kula da hakan. Da yake tafe yake da motar ‘yan sanda, hakan yasa ake basu daman wucewa, ba kowa ne ke iya shiga gabansu ba, sai dai cikin tsautsayi taxi din da ke dauke da su Nasreen ya shiga gabansu wanda kafin ya ankare har motar ‘yan sandan nan ta yi ciki da su. Hakan ya kawo * mummunar hatsari. Sultan yana cikin mota bai san wainar da ake toyawa ba, domin ba ~ motar da yake ciki ba ne abin ya faru, sai da yaga antsaya cak! Wani daga cikin dayan motar ya Karaso cikin gaggawa, yake sanar da abinda ya faru, ya ce a wuce da Sultan za su ji da komai. Shi dai ko tari bai yi ba, haka ya rasa dalilin da gabansa ke fadiwa. Can ya yi firgigit ya ce, “Kuna tuki cikin ganganci da nuna isa a titi, wanda shi titi babu ruwansa da muKaminka ko girmanka, haka shi bai da sabo. Yanzu wannan matsalar ta faru kuna fadin mu wuce ku zaku ji da komai akan me? Su wadanda aka 


buge din ba mutane ba ne? Ko kuwa basu da gata ne? Dakata infita.” Da yake sun san halinsa don haka suka tsaya ya fito gaba daya suka rufa masa baya. Abin takaici Www.bankinhausanovels.com.ng 


. babu wanda ya yi yunKurin daukar mutanen da aka buge, da suke kwance cikin jini, sai ma daya daga dan sandansa da ke neman dukan direban. Sultan ya girgiza kai, yana dubansu, “Yanzu don Allah menene amfanin wannan abun? Me yasa haka? Zaku - ji da mutanen da aka buge ne ko kuwa zaku tsaya surutu ne har su Karasa? Sultan ya - ratsa cikin jama’ar haka hanyar gaba daya bata motsawa saboda sun rufe hanyar. Yana zuwa kusa da su ya ware idanunsa. Ko shekaru dari suka yi basa tare ba zai taba mance su ba. Cikin sauri ya Karaso gabanta, 


" “Nasreen!” 


A hankali ta kai hannu tana lalube, ba ta da idanun da za ta iya kallonsa, amma kuma zuciyarta ta gano ko waye, “Dee...” Luuu ta yi baya. 


Kafin ta zube, gabadaya har ya samu ya tarota. Ya sa hannu ya tallabeta sosai. Ya rasa farin ciki zai yi ko kuwa bakin cikin ganin yadda Nasreen ta koma? Ya zama dole ya yi farin ciki da Allah ya bashi ikon sake ganinta. Cikin daga murya yake fadin, “A kawo mota cikin gaggawa.” Jikinsu yana Bari aka kawo mota yasa aka dauki Nawfal 


- shi kuma yana rungume da ita, ya hana ' kowa ya taba ta, suka shiga mota sai asibiti. Kura mata idanu ya yi yasa hannunsa yana “ shafar fuskarta, yana mamakin ina suka shiga haka da gaba daya kamanninta suka sauya? Ji yake kamar ta bude idanunta suyi ta kallon juna. Gaba daya dabara ta Kwace masa. Babu bata lokaci suka shiga da ita asibitin Dr. Aslaf. Cikin sa’a daga shi har  Aminu suna nan a office. Don haka su suka karbi su Nawfal. Yumnah tana tsaye akan Nasreen shi kuma yana can tsaye akan Nawfal. Shi kuwa Sultan gaba daya a rikice Www.bankinhausanovels.com.ng 


yake ya rasa me ke masa dadi sai kaiwa 


yake yana komowa. A lokacin ne Dr Aslaf ya fito daga inda suke kula da Nawfal. A gigice ya Karaso gabansa ya ce, “Dokto ya jikinsa? Ya farfado kuwa?”’ 


Dokto Aslaf ya dube shi kamar bai taba ganinsa ba, ya tabe baki, “Ka biyo ni office.” Sai yanzu ya tuna da Dokto Aslaf ne fa ba wani ba, don haka ya harare shi tare da jan tsaki. A lokacin ne kuma Yumnah ta fito don haka ya rabu da Aslaf ya Karaso gurinta, ““Kanwata ya ake ciki ne?” 


Fuskarta cike da fara’a za ta yi magana, Aslaf yasa hannu ya jawo hannunta ya ce, “Ba’a sani ba. Kin ji zo mu je kiyi min wani abu.” Sultan ya dube shi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Dole sai da ya biyo su office Yumnah tana dariya ta ce, “Wallahi Yaya Sultan babu ruwana laifinsa ne. Nasreen tana cikin Koshin lafiya, dan buguwa kawai tayi, yanzu haka barcinta . take yi.” 


Sultan ya saki ajiyar zuciya ya ce, “Kada ka damu zan rama.” Mikewa ya yi ya 


shige bandakinsa ya dauro alwala ya zo ya shimfida dadduma. Nafila ya yi ya gode wa Allah ya kuma yi addu’ar Allah yasa Karshen wahalar kenan.” 


Yumnah ta bude masu abinci, amma fir Sultan ya Ki cin abincin, shi damuwarsa kawai ya ga Nasreen da Nawfal. “Yumnah ki taimaka kiyi min jagora inga Nasreen. Babu musu Yumna ta mike Ta jawo hannun mijinta suka fice a tare. A bakin gadon ya zauna yana Kare mata kallo. Www.bankinhausanovels.com.ng 


Yumna ta dube shi cike da damuwa a fuskarta ta ce, “Don Allah Yaya Sultan ka barni da Nasreen da dan uwanta su dawo gidana na wasu lokuta ingyara maka matarka. Dubi Nasreen sai ka ce ba ita ce yarinyar nan da ke jikin hotunan nan ba? Anya ba a cikin rami suke rayuwa ba? Dazu sai da nayi mata kuka, gudun kada my Dokto ya ganni ya yi min fada yasa na share hawayena. Ina ganin ka ara min ita indawo da ita asalin Nasreen dinta, sannan ka gayawa duniya ka ganta, idan kayi saurin 


cewa ka ganta a irin wannan yanayin, masu neman ta za su ci gaba da farautarta ne.” 


Sultan ya yaba da abinda Yumnah ta yi masa, amma jin cewar masu farautarta za su sake bibiyarta yasa ya dube ta, “Idan a lokacin baya sun ci nasarar cutar min da ita, a wannan karon babu wanda ya isa Wallahi! A baya sun yi ganganci, a yanzu kuwa duk ‘wanda ya ce, zai sake aikata wannan - gangancin ina tabbatar maki sai ya kasance yaji a ransa me ya sa_uwarsa ta haife shi bata zubar da cikin ba? Na amince zan Boye dawowar Nasreen saboda matsalar cikin gidana. Bayyana dawowarta a yanzu tamkar wata hanya ce ta ruguza farin cikina agurin Umma.” Sultan ya saki ajiyar zuciya da ke nuni da yana cikin tashin hankali. Haka mafarkin da ya yi akan Zakiyya yaki goge masa. 


Dokto Aslaf yana zaton Sultan zai koma gida ne, sai dai ya sha mamakin yadda ya nannade hannun rigarsa ya jawo Www.bankinhausanovels.com.ng 


kujera ya kafeta da idonsa, haka hannunta mai Karin ruwan yana cikin nasa. Aslaf ya zaro idanu, “Haba haba! Muna da mutanen da za su kula da lafiyarta. Don Allah ka tashi ka je gida ka huta.” Sultan ya girgiza kai, “Ba zan iya tafiya ko ina inbar Nasreen ba. Ka taimaka min don Allah ka sa a dawo da Nawfal nan, saboda insami sauKin zirga-zirga. Ni zan kwana da su.” Aslaf zai yi magana, Yumnah ta sa ” hannunta a kunnensa ta murde ta ce, “Juya ‘ mu tafi mu aiwatar da abinda Yayana ya ce. , Ba gara kowa ba da kai? Soyayya ce kowa yana yinsa, a fili ko a sirrince, don haka ina . bayansa ya zauna ya kula da ita. Yayana 'yanzu za a dawo da Nawfal nan.” Sultan ya kafe su da ido yana kallon yadda ta tasa shi a gaba har suka fice. Ya ; dawo da kallonsa kan Nasreen ya zuba mata * kyawawan idanunsa, wadanda suke Boye a cikin glas fari. “Sorry Nasreen. Za ki ji , sauki. Na yarda da maganar Abba da ya ce 


ke Rubutacciya ce. Na shirya_ tunkarar kowacce irin matsala akanki. So gaskiya ne, duk wanda ya Karyata faruwar hakan, bai zo kansa bane. Nasreen ki tashi ko ba za ki iya ganina ba, idan naji muryarki zan sami gamsuwa.” 


Shiru Nasreen bata tashi ba. Dole ya 


' _yi alwala ya tafi Masallaci kafin ya dawo 


har an dawo da Nawfal dakin. : Kai tsaye gaban Nawfal ya nufa, ya kamo hannayensa, “Nawfal..” Ya kira . sunansa a Sanyaye, sai dai ko motsi bai yi ba. Kallon tausayi yake yi masu, babu abinda yake tunawa sai amanar da Saudat ta damka masa. Sai -yake ganin_ tsabar sakacinsa ne ya jawo masa wannan abun. A bayyane ya yi magana bayan ajiyar zuciyar da ta Kwace masa mai _ karfi, “Alhamdulillah! Allah na gode maka.” 


Yana nan zaune kiran waya ta shigo wayarsa, duk da tana silent hakan bai hana shi ganin hasken wuta ba. Ya Kurawa lambar idanu yana son sanin waye mai layin Www.bankinhausanovels.com.ng 


nan? Baya daukar layin da bai sani ba, don ‘haka ya katse. 


Can saKo ya shigo ya zubawa sakon idanu, haka ya karanta yafi sau a Kirga. “Ina da buKatarka, kaje ka zauna.” Har yanzu ya kasa gane waye zai aika masa da irin wannan saKon? Haka kuma menene dalilin aikowar? Babu bata lokaci ya biyo lambar. Muryar Zakiyya ya ji tana magana kamar 


" wacce tasha wani abu. A hankali ya sauke wayar yana mamakin inda ta sami lambarsa, 


* domin shi tunda yake da ita bai taba kiranta ba, bai ma san lambarta ba. 


Daga kansa ya yi sama yana tunanin ta yadda za a yi irin wannan zaman. Matar da babu Nasreen ma baya dubanta bare kuma Nasreen tana nan? Ya zai Kare da Ummansa? Gabansa ya fadi da Karfi domin ya san akwai tashin hankali mai girma a gabansa. Ada mahaifinsa ke tsayawa yana Kwatar masa ‘yancinsa agun Umma, to a yanzu Umman tabi dukkan hanyar da za ta bi, ta kanainaiye Abban sai abinda ta gaya 


masa sannan yake iya aikata shi. Tunani yake yi ya kira Abban a waya ya gaya masa dawowan su Nasreen, sai dai ya bi shawarar zuciyarsa da take gaya masa gara ya bari ta murmure ya dauke su ya kai su gabansa da kyan gani. 


Yana nan a zaune har Aslaf ya dawo ya matsa masa sai da yasa wani abu a cikinsa, sannan suka yi Sallama ya wuce gida. Misalin Karfe ukun dare take Kokarin , bude idanunta da suke a rufe. Lalube take yi tana magana cikin muryar marasa lafiya, s “Nawfal..” 


Sultan yana nan zaune yana kallonta. Farin ciki ya tsirga masa. Yumnah ta gaya masa babu wata matsala mai girma, amma abin mamaki sai yanzu Nasreen ta farka. Hannunta da taji a hannun mutum yasa ta yl shiru. Ta dora tunaninta akan abinda ya faru kamar cikin Mafarki. Ko mutuwa ta yi ta dawo, inhar Sultan zai zauna a wun kawai ya tashi sai ta gane, bare kuma ace wai yana kusa da inda take. Ta gigice da 


yawa, sai kama hannunsa da tayi, “De... Don Allah Dee kayi min magana. Kana kusa da ni kai ne, hannunka ne. Dama dama zan sake jinka a kusa da ni? Deee..” Www.bankinhausanovels.com.ng 


Cike da nishadi, ya sa dayan hannunsa ya lakaci hancinta, “Deee... Ga Dee a kusa da Nasreen dinsa. Bana son kuka, baki da lafiya ki koma ki kwanta kin ji?” 


. Babu abu daya da ta iya aikatawa a cikin abinda ya ambata mata. Sai sake jawo Www.bankinhausanovels.com.ng 


shi ta yi ta kwantar da kanta a bisa kafadunsa. “Dee kada ka sake barin a rabamu da kai. Mun sha wahala. Nawfal ya yi Kokari, Dee ina Nawfal? A dawo min da dan uwana kusa da ni.” 


Zuba mata ido ya sake yi yana kallon yadda Kasusuwa suka fito mata kwance a wuyanta. Ko bata gaya masa ba, ya san sun sha wahala. Hannu ya sa a cikin gashinta da duk suka dunkule saboda wahala, “Allah ya yi maku albarka. Allah ya sakawa Nawfal ya baki ikon kyautata masa. Nawfal yana nan kwance kusa da gadonki bai da lafiya, 


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...