RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO                  Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Hannunsa yasa ya dawo da ita baya, yana Kokann banKadeta, Tana son yin ihu babu dama haka kuma karfinta ya soma

Www.bankinhausanovels.com.ng Karewa. Mutumin da ke kwance akanta yaji anbuga masa wata sanda, mai girma da kauri. Da Karfi ya rike kansa sannan ya dago yana mazurai.

Nawfal ya zaro dukkan idanunsa, “Mansur! Kai ne? Kai da ka yi tafiya yaushe ka dawo har kake KoKarin kashe Nasreen? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Nasreen Mansur ne yazo yake son nakasa maki rayuwa. Ai na gaya maki mutumin nan baya sonki amma kika nuna min Karya nake yi. Ga shi ai shi yake baki wahalar nan.”

Nasreen ta shafi goshinta da yake mata radadi, “Nawfal ai Mansur baya garin nan ya akayi ya dawo? Mansur baka sona ka fitar da ni daga wannan gidan Wallahi na gaji.”

Mansur ya dan shafi kansa. “Kin gane ko? Kawai ina can ne aka yi min waya wai kuna son ku gudu ku bar gidan nan, ni kuma " da na ankare sai na shammaci kowa na dawo. Abin mamaki sai na sami kuna nan, Shaidan ne ya rinjayeni a kan ki Nasreen ke

ZAMU TASHI 

ma kin san na yi matukar Kokari a kanki kamata ya yi ki jinjina min. Zo mu ga goshin.”

Yana foKarin kai hannu_jikinta, Nawfal ya mika hannu kamar wanda zai Kwace ta, Nasreen ta buge hannunsa tana ci gaba da danna wurin da hannu, “Mansur na " yarda da kai a duniyar nan, ban san meyasa za ka bari har shaidan ya ci galaba akanka ba. Ni nace maka ka kwantar da hankalinka. Amma ji yadda kake yi min kamar baka taba sanina ba? A zatona ma wasu ne suke son cin amanarka?”

‘ A nan fa Mansur ya gigice yana ta bata haKuri sannan ya fice ya barta daga ita sai dan uwanta. Yana ficewa Nawfal ya Karaso da sauri ya zauna kusa da ita, “Sannu Nasreen ba ki ji ciwo ba? Sannu kin ji?”

Nasreen ta dan ture hannunsa ta ce, “Nawfal me yasa za ka dinga yin nisa kana barina? Yanzu da wannan mutumin mai warin bunsuru ya sami nasara akaina fa? Gaskiya ni Nawfal na gaji da zaman nan, ka

Www.bankinhausanovels.com.ng taimakeni ka fitar dani idan ba haka ba zan iya rasa raina. Wannan gida da zamansa gara zaman mu a can Kankia tunda zamu fita gari muna jin hayaniyar jama’a. Mansur din nan bashi da imani Karya yake yi baya sona, mai sona mutum daya ne shi ne Deedinmu. Nawfal kayi wani abu mana kada na mutu abarka da gawa.”

Nawfal ya girgiza kansa yana jin saukar kowacce kalma ta Nasreen kamar ana buga masa guduma. “A’a Nasreen insha Allahu ba za ki mutu ba, da Kafafunki zamu koma gida. Kin ga ina hada mana yadda zamu fita daga gidan nan, shi ya sa hankalinsa bai kwanta ba, yake tarwatsa dukkan shirin mu. Amma ki kwantar da hankalinki mu ci gaba da addu’a insha Allahu muke da nasara.” Nasreen da ta riga ta sare tace, “Wani abu kake yi akan fitar mu?” Kansa ya riKe dole tana son sai ta Kureshi, “Zan gaya maki kin ji? Ni dai ki kwantar da hankalinki.”

********(((

Www.bankinhausanovels.com.ng Zakiyya da ta kwankwadi magungunan mata harda na hauka tashin hankali ya sauka a jikinta, sai wahala take tana nishi tana mayar da numfashi. A lokacin ne cikin sa’a Sultan ya shigo gidan da ninyar daukar wata takarda. Sai dai rashin sa’ar da ta tafka Sultan baya cikin hayyacinsa, hankalinsa yana kan binciken Nasreen da wani ya tabbatar masa yaga _ Nasreen tana yawon bara ita da dan uwanta. Sultan ya dube shi rai a babace, “Ka ga Nasreen ka kasa zuwa ka sanar min? Har kake cewa ka basu sadaka? Ta ya ya za ka yi min haka?”’

Mutumin da yake matsayin kamar yaron aikinsa ya girgiza kai, “Ka yi hakuri yallabai a lokacin bansan sun bata bane, shi ya sa kawai nake ta yi masu kallon sani. Sai yanzu da nake ji. Amma tabbas Nasreen ce na gani da idanuna tana riKe da sandar bara, a Cikin garin Kankia.”

Sultan fa ya gigice damuwarsa kawai ya isa garin Kankia da kansa ba aike ba.

Www.bankinhausanovels.com.ng Zakiyya ta rungume shi tsam a jikinta tana sakin wani irin mahaukacin ajiyar zuciya. A duniya Sultan ya tsani yaga ana wulaKanta mace, shi ya sa yake daurewa kansa akan Zakiyya yana kiyaye abubuwa da dama. _ “Zakiyya kiyi haKuri inje indawo ina da aiki mai matuKar mahimmanci.” ; Kauda ta ya yi daga jikinsa y. shige ' abinsa yana amsa waya, yana gaya masu Nasreen tana Kankia yanzu haka can za su nufa. Karaf a kunnen Zakiyya, a take ta nemi duk wata sha’awa ta rasa. A tunaninta Sultan ya gama zama da wata mace fece ba ita ba, ta ya ya ma za ace anga Nasreen? Ta daure iya dauriya ta ji, har ya kai bakin kofa ya juya yana kallonta da tausayawa. Allah ya gani baya sonta dai-dai da minti «: ya, amma martaban _ samunta a budurwa da kuma yadda ta kwantar da kanta ta zauna, ya sanya masa har ya ji a zuciya: yana_ tausayinta. Dawowa ya yi ya shafi kumatunta yayi mata sumba a goshi. Bai taba yiwa wata

Www.bankinhausanovels.com.ng mace hakan ba, sai Nasreen dinsa, haka bai taba tusanin wata mace za ta iya samun kulawan.ba, idan ba ita ba. A natse ya yi amagana, “Idan kika zama mai haKuri za ki ji dadin zama da ni.” Kawai ya juya ya fice, yana jin takaicin yadda ko arziKin addu’a bai samu ba. Yana ficewa ta dauki waya jikinta hqr kyarma yake yi. A lokacin Hajiya Ladidi tana gidan . Hajiya -salma don haka ta amsa babu ko gaisuwa tsakaninsu ta hau bata labari, “Mama mun shiga uku. Angano Nasreen a Kankia, yanzu haka Sultan ya kama hanya ya tafi da ‘yan sanda. Mama idan Nasreen ta dawo na shiga uku domin sai ta koro ni waje. Yanzu mama ya zamu yi kenan? Ko za ki kaini wajen bokan nan ne tunda naga aikin malamin yakan yi masa aiki.” maman ta yi shiru na wani lokaci sannan ta ce, “Ki wantar da hankalinki Nasree: bata Kanki., tana can Mansur ya kusa aureta. Amma yanzu ina gidansu ne tunda “ya fara jin Kanshinta zai iya lalubota j?

Www.bankinhausanovels.com.ng ba tare da mun ankare ba. Bari inyi magana da mahaifiyarsa zan sake kiran ki.”
Ta sauke wayar jiki a sanyaye tana duban Hajiya Salma, “Hajiya yaronki Sultan yana da taurin kai, haka baya jin maganarki sam! Yanzu haka ya tara ‘yan sanda roka guda, wai sun je neman Nasreen a Kankia.”

Hajiya Salma ta ware manyan idanunta gabanta yana tsananta fadiwa.

‘ “tirkashi! Lallai ma yaron nan! So yake ya tona min asiri? To Wallahi bai isa ba, ba dai a wannan gidan ba. Kai akan yarinyar nan ina iya tsine masa in yi masa Allah ya isa nonona da ya sha. Bari in kira shi ingaya masa idan ya sake ya Karasa garin nan ban yafe ba.”

Raruman_ wayarta ta yi tana daddannawa, ta sa a kunne. Zuciyar Hajiya Ladidi fari Kal! A zuciyarta ta ce, Mahaukaciyar banza! Yaushe zan iya wulakanta dana akan wata can! Yaro yana maki biyayya duk wata kina da kudi masu tsoka daga wurinsa, amma da yake banza ce

Www.bankinhausanovels.com.ng ke sam baki fahimta. Ki tsine masa din mana ni ‘yata bata da asara, sai ya sako min ita ta auri wani miji goma ai ba uban goma bane. Firgigit ta yi a lokacin da Hajiya Salma take ce mata, “Kin ga ya ki dauka ko? Sultan saboda ya taka matsayin nan ne shi ya sa idan za a kwana ana kiransa baya dagawa? Zan ci gaba da kiransa har caji ya Kare da ni yake zance.” Sultan kuwa suna hanya, wayarsa tana Silent, bai ga kiran mahaifiyarsa ba, sai can ya lura da hasken wayar, yana kallo har ta tsinke bai dauka ba, haka kawai hankalinsa bai kwanta da ya dauki wayar ba. Isowarsu Kankia suka bazama nemansu. Da kwatance har suka iso wurin mai abinci.

Tana ganin mota ‘yan sanda sun fito hannayensu dauke da bindigogi hankalin Mai abinci ya tashi.ta nemi ta tsure a nan tsaye. Aka budewa Sultan Kofa ya fito yana Karewa wurin kallo. Da ganinsa ka ga fulanin Yola, fuskar nan tasa babu fara’a bare alamun murmushi. Abin mamaki har

Www.bankinhausanovels.com.ng gaban-mai abincin ya tsaya yana dubanta, ' “An-ce Nasreen da Nawfal suna wurinki, ki nuna min inda suke.”

Hantar cikinta ya kada ta girgiza kai tana zaro idanu, “Wallahi sun dade da barin wurina, tun lokacin da dayan almayirina ya ce, Nawfal ya satar min kudi na kore su, amma ada a bakin shagon nan suke kwana shi da ‘yar uwarsa.”’

Sultan da yaji wani irin jiri yana neman kifar da shi, ya tsaya tare da tokarewa yana sake zuba mata idanunsa da
suka sauya kala saboda bacin rai. “Nawfal ne barawo? Saboda Kaddara ta kawo shi wurinki kike tunanin barawo ne? Ni ban raini barawo ba, haka ban ba Nawfal tarbiyyar sata ba. Yarinyar da_ bata gani makauniya, da Kananun shekarunsu kika kore su? Bakin shagonki kawai kika bar masu su dinga kwana, cikin Kazanta, cikin sauro, cikin sanyi? Hasbunallahu wani imal wakil.” Www.bankinhausanovels.com.ng Sultan ya dinga nanata addu’ar nan yana sake jin idanunsa suna lumshewa.

. “Babu damuwa mun gode. Amma daga yau

ki cire a ranki Nawfal ba zai iya satan koda abincin ci ba, bare akai ga kudi.”

Juyawa ya yi kamar zai hau mota sai ya juyo yana kallon yadda mutane suka taru suna dubansa, “Don Allah duk wanda ya ganta ko yake da labarinta, a kawo min ita zan bada kyautar miliyan goma, da wasu abubuwan more rayuwar dan adam. Ko da kuwa basa cikin hayyacin su ne, ko kuma — gawarsu.”

Yana Karasawa ya fada mota. Dan sanda daya ya Karasa ya rubuta address din da za a iya samun su, idan har Allah yasa angansu. Yana wucewa a bakar motarsu, ‘yan wurin suka hau cecekuce, suna fadin ai ko da ganin yaran kasan ba talakawa bane, kaddarar rayuwa ce kawai ta kawo su irin wurin nan. Kowa da abinda yake fada, haka jin makudan kudaden nan yasa kowannensu cizon yatsa, wasu ma cewa suka yi za su

Www.bankinhausanovels.com.ng bazama nemansu a duk inda suke a fadin duniyar nan. Sultan dai ya tafi ya barsu da cizon yatsa. Wannan yana cewa da ya sani shi ya dauke su ya ajiye a gidansa.

Kai tsaye Sultan gidan Al-ameen ya wuce da tuni yasan da zuwarsa, aka shirya masa abinci kala-kala. Bayan sun kintsa ne, Jidda ta shigo dakin tana dariya. Sultan idan yana tuna abubuwan Jidda sai kawai ya hau murmushi, “Jiddan Uncle kina lafiya?” ;
Ita ma murmushin ta yi ta Boye a bayan Al-ameen, “Ina yini Yaya Sultan?”

Sai da ya sha sassanyan zobonsa tukun sannan ya amsa, “Lafiya lau. Idan zan tafi za ki hada min irin zobon nan naki mai * dadi insa a firij.”

Ta amsa masa sannan ta zauna tana dubansa, “Yaya Sultan ka ga Uncle ko? Sai ya yi ta fushi da ni.” Sultan ya zaro idanu, Sai yanzu ya kula da yadda Al-ameen ke shan mur. “Rabu da shi Kanwata yau zanyi maganin Uncle.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Mikewa ta yi tana kwashe kayan da suka ci abinci. Tana fita Sultan ya dube shi, ‘““Meke faruwa ne Prince? Jidda fa ba macen da za ka dinga yin fushi da ita bane. Mace ce wacce samun irinta a wannan duniyar tamu da take cike da makwadaitan mata sai antona.”

Al-ameen ya sha zobon yana lumshe idanu, “Sultan nasan halin Jidda, fushi kawai zan yi da ita ta shiga taitayinta ba wai

“kalaman baki ba. Ni kaina Karfin hali nake yi, idan ba haka ba, sai yarinya ta rainaka.”

Sultan ya ce, “Idan ka karanci mace ka gama cin ribarta. Amma kuma tunda ka iya haKuri da ita a zamanin can baya tun kafin ma ka aureta, ai a yanzu din ma za ka iya fiye da hakan. Ina yaran ne ban ji motsin su ba?”

“Akansu muke fada. Daga an sa yaran nan a babban Makaranta ta addini da boko, a can suke gabadaya saboda akwai masu kula da yara a wurin. Sultan ina son yarana su taso cikin ilimi. Yara biyu kawai?

Www.bankinhausanovels.com.ng Haihuwa ai yanzu ta fara. Amma sai yarinyar nan ta sa min rigima wai indawo mata da ‘ya’yanta sai kace ita kadai take son su ta shaKu da su. Yaran da a Kirjina suke barci sannan nake iya raba su da jikina. Babu lallamin da ban yi mata ba, amma taki, banda kukan cikin dare babu abinda Jidda take yi. Baka ga yadda ta rame ba? Ni har na manta laggonta fitinarta tasa na tuna “da ta tsani inKyaleta. Yanzu ka ga ai ta shiga taitayinta.” Sultan ya yi murmushi kawai yana fadin, “Sai a daina fushin hakannan kada a tarwatsa zuciyar Kanwata. Gobe zanje in gaida mai martaba, daga nan zan koma gida.” Sai yanzu Sultan ya tuna da kiran mahaifiyarsa don haka ya zaro wayar ya kira layinta. Tana dauka ta hau shi da masifa, “Kai ashe baka da hankali? Yanzu yaran nan ka tafi ka sake nemansu ko? Wai Sultan me ke damunka ne? Tun bayan barin yaran nan cikin gidan mu komai ya dawo mana, ka dinga samun daukaka, shi ne yanzu za ka dawo mana da masu fararen
Www.bankinhausanovels.com.ng Kafafu? To baka isa ba! Ina baka umarni da kada insake jin wai kaji labarin su ka sake neman su. Yaran da aka ce duniya ma tsine masu take yi saboda halin karuwanci da Nasreen din ta koma? Shi kuma Nawfal din ai Sace-sace na ji an ce yana yi. Mazinata za ka dawo min da su cikin zuri’a? Wato kai ka rantse sai ka gurbata min zumri’a ko? Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi.” Hajiya Ladidi ta dinga yi mata famfo. Dama kuma lokacin da zai auri Zakiyya, sai da Hajiya Ladidi ta hada da asiri, ta kuma yi mata rantsuwa Zakiyya tana Kyamatar maza. Amma kuma ai tafi kowa sanin Hajiya Salma ‘yar gari ce a wannan harkar. - Da Kyar ta amince shi ma saboda tana tsoron kada Hajiya Ladidi ta tona mata asiri ta gayawa duniya abinda suke aikatawa. Amma har gobe bata daina Kyamatar Hajiya Ladidi ba. Gabadayan su munafuntar juna suke yi, abinda bata sani ba, Hajiya Salma ta hada baki da Mansur ta bashi maKudan kudade aka zubawa Zakiyya maganin hana

Www.bankinhausanovels.com.ng daukar ciki mai tsananin Karfi. Ta ce ba ta amince ta hada jini da su ba, za ta natsu ta samo masa yarinya a dangi, yarinya Karama mai natsuwa ko da kuwa a cikin gidan Alhaji Mu’azzam ne, daga nan sai su haihu. Hajiya Ladidi tana yiwa Hajiya Salma kallon biri, ita kuma tana yi mata kallon ayaba. Sultan da ya ji zuciyarsa tana suya daga irin kalaman Umma akan matarsa da dan uwanta sai ya sauke wayar kawai. Alameen bai tambaye shi ba, domin ya fahimci family issue ne. Yana tausayin abokinsa matuka, domin yanzu shi ne yake fuskantar tasa Kalubalen. Sultan ya mike kawai ya fice zuwa bayan gidan, a nan ya dinga kallon dokunan suna bashi sha’awa. Shi kadai yasan irin tunanin da yake yi. A ranar bai iya barci ba, haka Al-ameen bai matsa masa ba. Washegari da sassafe suka juya ba tare da sun sami cikar burin su ba. Yana zaune a falonsa yana shan ruwan . lipton da ya hadawa kansa yana jin kamar yana shan ruwan magani. Soyayyar Nasreen

Www.bankinhausanovels.com.ng ta ci gaba da gallabar zuciyarsa tana hana shi zaman lafiya. Zakiyya ta shigo tana sanye da Kananan kaya. Tana zuwa ta zauna a gefensa, tana yi masa wani shu’umin kallo. Hannu ta kai bisa kafadunsa tana murmushi mai kama da kuka.

Dayan hannunsa yasa ya zame nata a jikinsa ya dan dubeta, “Zakiyya sai mutum yana da natsuwa sannan yake samun Karfin guiwar aiwatar da wasu abubuwan. Bani da natsuwa ina cikin damuwa ki yi haKuri na tabbata ba zan dauwama a hakan ba, ki bari - da kaina zan nemeki Zakiyya kin ji?” Yadda ya yi maganar ta dan ji tausayinsa, amma kuma da ta tuna akan wata yake yin hakan sai ta ji duk bacin rai ya dawo mata, don haka ta kira Umma babu kunya ta zayyane mata komai. Daman Hajiya Ladidi da Hajiya Salma sun shirya zuwa don haka ta ce ta kwantar da hankalinta tana nan zuwa. Kwanaki biyu a tsakani Umma suka iso cikin shigar alfarma. Kallo daya za ka yi masu kasan naira ta yi kuka a wurin su. A

Www.bankinhausanovels.com.ng Kalla idan ka tsaya duba nairorin da ke jikinsu za ka iya Kiyasta dubu dari biyar zuwa sama. Zakiyya ta fito da gudu daga ita sai rigar barci, a lokacin Sultan yana amsa waya, ya dubi su Umma ya Karaso gabansu.

Ganin Zakiyya yasa ya bi shigarta da kallo cikin tsananin bacin rai. Yana kallon yadda ‘yan sandansa suke kawar da kai. Irin kallon da yake mata yasa Umma da Hajiya Ladidi suka dubeta, ita kanta Umman ta ji babu dadi, domin ita ta tsani rashin tarbiyya irin wannan. Babu wanda ya yi magana har suka shiga ciki a tsakiyar falo Umma ta fara magana, “Ke Zakiyya wani irin rashin hankali ne wannan? Me zan gani? Haka kike fitowa a gaban wadancan mutanen masu kama da dogare? Ni bana son rashin tarbiyya sam!” Hajiya Ladidi da ranta ya baci ta danne tana dan murmushi, “Amma dai ke baki da hankali. Me zai sa ki fito kai ko dankwali babu?”

Sai a lokacin Umma ta kai duba akanta, idanunta suka dinga nuna mata ta yiHMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...