RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAY

Dan sanda yana sa Shugaban ‘yan daba ya yi bayanin da kudi www.bankinhausanovels.com.ng basu isa su sa shi ba. Muna da abin da za mu jona masu suyi bayani ko basu yi ninya ba.” Ashmaan ya yi murmushi, “Kada ka wahalar da su, na tabbata za su yi bayanin.” Zakuda kafadunsa ya yi, “Kada ma su yi. Idan miliyan daya bata sanya su bayani ba, ina tabbatar maka batir da wayan wuta za su kawo bayanai dalla-dalla.”

Sultan yana nan zaune, yana jin yadda Ashmaan yake soyyaya da matarsa kamar yau aka daura masa auren. Sai da ya sauke wayar Sultan ya dan dube shi ya ce, “Kasan wani abu ne? Wallahi ina mancewa ina tare ~ da wata mata a cikin gidana. Abinda ke daga min hankali yarinyar nan duk abinda muka yi sai ta gayawa mahaifiyarta? Kai ranar da naji da kunnena ban iya barci ba.”

Ashmaan ya shafi kansa ya ce, “Mahaifiyarta fa ka ce? Wannan kam yafi Karfina. Wayewar ta yi yawa.” Sultan ya ce, “Yauwa kasan Allah? Idan ka sake ce min ni musulmi ne sai nasa anboye min kai, inga yadda Ibtihal za ta yi . Baka san dazu

ZAMU TASHI 

naji haushi ba? Ashe haka mutum yake ji yana da addininsa a cire masa da Karfi da yaji?’ Ashmaan ya yi murmushi har sai da hakoransa suka bayyana, “Kawai a lokacinne sai ka juye min sak!” Kafin ya Karasa Sultan ya jefe shi da gwangwanin Power Horse kuma ya ci sa’a ya same shi. Ko waiwayarsa bai yi ba ya tunkari Kofar fita yana cewa, “Zanje ingaida ‘yan gidanmu. Ashmaan ya mike, “Jirani mana malam. Kai kadai za ka kwashi ladan? Nima zan je.” Sultan da kansa yake janmotar, Ashmaan yana gefensa. A tsakiyar titi yaja burki da Karfi, sakamakon ganin wani a gefen titin yana wankawa mace da namiji mari, haka kowa ya tsaya yana kallo babu wanda ya iya cewa komai. Da Karfi ya ce, “Nasreeen!!” Ashmaan ya ware idanu, “Kashe mu za ka yi ne? Wacce Nasreen kuma?” Bai bashi amsa ba, sai balle belt din da ya yi ya fito yana Karasowa ya dinga wanke mutumin da mari yana Karawa. Ashe wai

Www.bankinhausanovels.com.ng soja ne, yaran sun kusa sanya shi ya yi hatsari shi ne ya dage yana hukunta su. Yaso suyi dambe da Sultan amma ina... Karfin ma ba daya ba. Ashmaan yana tsaye yana kallon wanda ya fi shi zafi da zuciya. Daga baya ya Karasa ya finciko yaron daga hannun Sultan yana dubansa, “Kai baka da hankali da A.I.G za ka yi fada?”’ Tsoro da firgici suka shige shi, a take ya sara masa yana mazurai. Sultan ko dubansa bai yi ba, ya Karaso gurin yaran yana duban su. Ko alamar kama basu yi da Nasreen ba, idanunsa kawai ke gizo yana nuna masa wasu mutanen daban a matsayin Nasreen. Sultan ya basu kudi yasa su a dai-daita sahu, sannan ya fincike Id card din gaban rigar mutumin ya gama dubawa, sannan ya. jefar masa. Har bakin mota mutumin ya bi su yana bashi hakKuri, Sultan ya dube shi sosai ya ce, “Kunsa ana zagin kaki, kunsa ana yiwa Soja kallon mara hankali, mara sanin ciwon kansa. Kun sa tsofaffi, yara, malamai, da ‘yan iskan gari, da zarar suka ji

Www.bankinhausanovels.com.ng fadi sunan hukuma sai su kama tsine mana, wanda bamu san bakin wasu ba, kai tsaye tsinuwar ke isowa garemu ba tare da wani shamaki ba. Kuna sa kaki kuna wulaKkanta duk wanda tsautsayi yasa ya biyo ta layinku, wai a ganinku wani matsayi gareku. Kun mance idan za a kaiku lahira kwaye kakin za a yi a ajiye a gefe. Mutum baya taba tafiya da muKaminsa lahira iyakarsa a duniyar nan da ya samu, sai dai ya je can ya dibi dukkan zunuban da ya kwaso wa kansa. Ni zan yi maganin irinku sannu a hankali. Bana zalunci ban yarda a yi ba!” Sultan ya jawo Kofar motarsa suka wuce. Sannan ya shafi kansa ya ce, “Kasan wani abu ne? Bana tuki saboda idan har nayi sai idanuna sun hasko min Nasreen. Hakan yake sawa nake take burki a ko ina ba tare da nayi la’akari da motar da ke bayana ba.”


Ashmaan ya ware idanu, “Da gaske kake wannan maganar? Dan tsaya a nan akwai abinda zan yi.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Sultan bai kawo komai ba, ya ja ya tsaya. Ashmaan ya fito daga motar ya zagaya ta wajen zaman direban ya ce, “Fito! Ka fito mana.” Sultan ya fito yana dubansa.

Ashmaan ya shige mazaunin direba ya yi wa mota key, sannan ya ce, “Zagaya ka zauna mu tafi. Ina da mata da ‘ya’ya uku, idan na mutu Ibtihal za ta iya haukacewa, kai kuwa baka ma san zaKin macen ba. Ka . bari in lallaba rayuwata mu tsufa tare. Ta ya ya zan zauna kana jana a mota kana taka - burki a tsakiyar titi saboda soyayya? Ko zamanin nawa soyayyar a hankali na dinga bi da kaina, har na samu na mallaketa.”

Sultan ya yi murmushi abinsa, ya wuce suka ci gaba da tafiya. Sun iso cikin gidansu sun kuma sami Abba, don haka ya yi ta basu shawarar yadda ya kamata su yi. Ashmaan ya ji dadin kasancewarsa a cikin gidan su Sultan domin yaga kara da karramawa.

Www.bankinhausanovels.com.ng  Gabadaya suna zaune a Katon falon kowannen su gabansa dauke yake da laptop Kanana masu tsada da kyau. A tsakiyar falon Nora ce da Daniel jikinsu babu inda baya rawa. Sun gama sakankancewa Alhaji ne ya turo mutanen nan domin ya ji ko sun mance labarin, sai aka yi rashin sa’a kwadayin abin duniya yasa suka furta wasu kalaman da yake nema ya jawo masu masifa.

Sultan ya ba yaransa umarnin su fice daga falon, sannan ya dawo da kallonsa a kan Nora, “Sunana Abdullahi Lukman, wanda aka fi sani da Sultan wato S. Lukman. Ni jami’in ‘yan sanda ne, a tare da ni kuma akwai abokaina. Ina nufin a nan akwai Soja, akwai Dan jarida, ga kuma Barrister da likitoci. Ina nufin bamu neman wasu ma’aikata a waje, shi ya sa muka hada kawunan mu domin duk irin taimakon da muke nema a cikin mu akwai masani akan abin. Ku saki jikinku, bamu cutarwa, amma idan ka yi mana gardama ina da kayayyakin

Www.bankinhausanovels.com.ng aikin da za su sanya a yi maganar gaskiya.

Ina son sanin tarihin Justina, da kuma dalilin da yasa aka biyota cikin dare aka sassareta da ciki. An tabbatar min kina da masaniya akan komai. Shi wancan barazana ya yi maki zai kashe ki ko? Ni kuma bana barazana, sai dai insa bakin bindiga indauke numfashinki.” Yana maganar yana shafa mata bindiga a hanci.

Nora ta kidime iya kidimewa. Daniel kuwa tuni ya yi alKawarin bayar da wadannan amsoshin domin gujewa tarin masifar da mutanen nan masu kwarjini suke dauke da shi. Kafin ya yi magana Nora ta fara magana, “Mu ba mu san komai ba, a kan mutuwar Justina, ku yi haKuri kada ku kashe mu.”

Sultan ya dubi Ashmaan, sun tabbatar da kafiyar matar nan ya wuce tunanin su, haka za ‘ta yi wahalar shigowa cikin musulunci, saboda irin kafewarta. Sam Sultan baya son taba lafiyarsu, yana son  yadda aka dauko su salin alin a mayar da su

Www.bankinhausanovels.com.ng Don haka dabara tana neman ta Kwace masu. Khamis ya mike ya kama dan yatsan Nora ya yi mata wani irin izaya da yasa ta bude bakinta tana magana cikin wahala da tashin hankali. “Zan gaya maku komai zan gaya maku.”

Ya sake ta yana murmushi, sannan ya jawo Stool ya zauna kusa da_ ita. “Dukkanmu nan muna da abubuwan yi, ki yi maza ki gaya mana abubuwan da muke son ji. Idan kika yi mana Karya, akwai

littafin da ta yi rubutu zamu gane gaskiyar ki ne idan kina magana muna duba littafin. Khamis ya ware littafin wanda rubutun ba ta yi su a bude ba, bayanai ne dai irin wanda zai iya sa ka isa ga inda kake da_ buKata. Daniel ya dubi Nora ya ce, “Nora ki gaya masu, yaranmu suna buKatarmu a raye.”

Nora ta dago kanta tana son Kare masu kallo, amma kwarjininsu ya wuce dukkan yadda take tunani. “Sunana Nora, sunan Kawata Justina, mun taso a unguwar

Www.bankinhausanovels.com.ng Magajiya. Justina yarinya ce mai kyau da ilimi, yanayinta yafi kama da Fulani, shi ya sa mutane daban-daban suke cewa suna sonta, tun tana ‘yar Karamarta. Abin mamaki harda hausawa. Hakan yasa iyayen Justina suka dage akanta, kasancewar suna sonta kamar su kashe kansu. Komai suka samu ita suke siyowa. Justina ‘yar gata ce da ta taso cikin so da Kaunar iyayenta. Sun ci buri akan iliminta, haka kullum sai sun kaita wajen addininmu an yi mata addu’a saboda suna ganin idon mutane yana kan yarinyarsu. Asalin su ‘yan Zangon kataf ne, . amma an ce asalin Mamanta ‘yar Adamawa ce.

Watarana muna hanyar dawowa daga Makaranta, wani saurayi ya tare mu ya ce yana son magana da Justina, ta Ki tsayawa. Haka saurayin nan kullum idan muna hanyar dawowa sai ya biyo mu, tun ba ma tsayawa har ta koma tana saurarensa. Na yi mata magana na ce, “Justin ba addininki daya da mutumin nan ba, me zai sa ki tsaya

Www.bankinhausanovels.com.ng kina kula shi? Kin san halin iyayenki idan suka ji duk yadda suke sonki sai sun bata . maki rai.”

Ba ta ba ni amsa ba, amma na ga tana ta murmushi. Sai daga baya nasan sunan saurayin Sani, haka Justina bata da hira sai na Sani, daga baya ma ta gaya min tana son Sani. Na damu sosai haka ina tsoron kada iyayenta su sani, shi ya sa nake basu wajen

hira daga nesa da gidajenmu. Sani ya nunawa Justina yana son ya aureta, amma yana son ta musulunta ita kuma ta gaya masa gaskiya addinin shi baya burge ta ba za ta musulunta ba. Idan Justina za ta kama hannun Sani sai ya gaya mata addininsa ya hana hakan, haka ya ta6lba yin tafiya ya dade bai dawo ba, ranar da ya dawo ta ruga za ta rungume shi saboda farin ciki, amma sai ya dakatar da ita, ya gaya mata shi addininsa bai amince masa da aikata hakan ba. Da haka ya fara jawo hankalinta, har ta fara zama tana jin abubuwa akan addininsa. Ya ci gaba da ce mata, “Addininmu addini ne

Www.bankinhausanovels.com.ng mai sauKi, a wajen jarabawa ce kadai mutane suke fadiwa imaninsu yake rauni.” Bayanan nan nasa yasa ta koma gida tana ta tunani, da naje gidan su take bani labari, nayi mata fada, na jawo hankalinta akan kada ta yarda iyayenta su ji.

““A hankali shigarta ta fara komawa ta addinin musulunci, tun iyayen basu kula har hankalin su ya dawo kanta. Babu Bata lokaci suka dauketa suka kaita wajen addu’a ° a ganinsu wani abu ne ya shiga kanta. A maimakon abun ya ragu sai ya cigaba da ” Karuwa. Hakan yasa suka tsananta bincike suka sa aka kama Sani har tsawon kwana biyu yana kulle. Justina ta yi kuka ta Ki ci ta Ki sha, shi kuma yaki amincewa a sanar da kowa. Wannan lamari yasa Justina kwanciya ciwo har sai da aka sake shi.

“Bayan ya fito ne ya yi ta neman hanyar da zai sake ganin Justina, amma abin ya faskara, domin ko Makaranta anhanata zuwa. Ni na nake kai mata wasika idan ya rubuto sai ta bayar da amsa inkai masa.

Www.bankinhausanovels.com.ng Justina ta rame ta lalace amma kuma iyayenta basu tausayawa mata ba. Babanta ma cewa ya yi gara ta mutu da ya ganta tana cikin musulunci. Rana ta Karshe ne, ta gudu, taje ta sami Sani. A ranar ma ni na raka ta. Ya kama hannayenta a karo na farko ya ce, “Justina daga yau sunanki Saudat kin ji? Zan dauke ki in kai ki wurin wani babban Malami domin ya musuluntar da ke, ki daure komai zai zo mana da sauKki kin ji?” Babu musu ta amince masa, suka je wurin malamin ya gaya mata dokokin shiga musulunci ta ce, ta yarda. Sannu a hankali ya mayar da ita gidansu, ba tare da ansan ta fita ba, ta koma tana yin addininta a Boye haka duk lokacin da za su hadu da Sani ni nake hada yadda haduwarsu za ta kasance. Sani ya taimaka sosai wajen koyawa Justina _abubuwan addininsa.

. “Da yake yarinya ce mai Kwakwalwa nan da nan take kwashe dukkan bayanansa. Har aka zo gabar aure. Ya tabbatar mata da zai aureta, zai dauketa ya kaita wajen

Www.bankinhausanovels.com.ng babban yayansa. Haka suka shirya suka tafi wajen Yayansa. Sai dai ya Boye masa sauya addinin da ta yi zuwa nasa, kasancewar yasan halin Yayan akwai tsauri da Kin addinin da ba nasa ba. Don haka yasa Alkhairi ya nuna masa zai tura a nema masa aurenta. Sai dai suna fita daga gidan yayan yasa aka bi bayan su, har aka gano komai akan Justina.

“Da aka gayawa Yayan hankalinsa ya ~ tashi jin cewar ba addininsu daya ba, amma kuma da yake yana da irin nasa burin sai ya ” share ya bar zancen. Justina taje ta nemi gafarar iyayenta tace masu ba za ta Kara ba. Hakan yasa suka amince da ita, suka Kyaleta ta ci gaba da zuwa Makaranta. A hanyar dawowarmu ne aka sace mu da ni da ita aka sanya mu a cikin mota sai wani gida. A nan wurin mutumin nan ya yi wa Justina fyade. Tana kuka aka dauke mu aka dawo da mu inda aka dauko mu. Justina ta yi kuka, ta yi kuka kamar ranta zai fita.

Www.bankinhausanovels.com.ng Ni nake ta ba ta haKuri, na kuma gaya mata ta kira Sani ta gaya masa komai, sai ta ce min, “Nora kin san waye ya yi min haka? Yayan Sani shi ya aikata min haka. Ba zan iya gayawa Sani ba, ko na gaya mashi ba zai yarda ba. Ya gaya min Yayansa malami ne. Me yasa zai yi min haka? Yanzu Nora ya zanyi?” Na ce mata ta yi_ shiru ta bar maganar. Abu kamar wasa sai da yayan

“Sani yasa aka sace mu sau uku yana biyan buKatarsa da Justina.”

* Al-ameen da ya yake jin sunan Justina din yana Bata masa rai ya dubeta ya ce, “Anti pls kira ta da Saudat dinta.”

Kowa ya gyada kansa don sun fi gamsuwa da Saudat din fiye da Justina.

Nora ta gyada kanta ta ci gaba da magana tana hawaye, “Ana haka kawai sai ga ciki. Ta shiga tashin hankali da bayyanar cikin nan, haka ta gaya min ba za ta iya zubarwa ba, domin angaya mata hukuncin wanda ya zubar da ciki tamkar ya kashe rai ne. Babu yadda ban nuna mata irin matsalar

Www.bankinhausanovels.com.ng da za ta iya shiga ba, amma taki amince wa maganata. A lokacin da iyayenta suka ankare sai suka yi mata dukan tsiya suka koreta, ni na boyeta a gidanmu nasa aka nemo Sani ta fito tana kuka ta gaya mashi komai, sai ya gaggaya mata magana, ya zazzageta ya kuma ce-bai yarda fyade akayi mata ba, taje ta nemi wanda ya yi mata ciki — amma kada ta sake tunawa da wani mai suna irin nasa. RoKon duniyar nan mun yi - wa Sani amma yaKi taimaka mata. Ita kuma ta Ki gaya masa wanda ya yi mata hakan, sai ’ take ganin wannan wani al’amari ne mai girman da bai kamata yaji ba. Da farko a gidan mu ta fara zama, iyayena suka koreta shi ne tabi titi. Saudat tasha wahala a duniya, ta koma bara, tana samun abinda take ci, duk da hakan tana nan a cikin musulunci kullum da dogon hijabinta. Har sana’ar wankin mota ta yi domin ta dinga samun abinda za ta ci. Daga baya ne da mutane suka ankare da cikin jikinta shi ne musulmanku suka tsaneta, suka sa ta tsani

Www.bankinhausanovels.com.ng duniyar gaba daya. Hakan yasa ta je har gidan Yayan Sani, ta bada sako a ba shi. Wannan lamari ya daga_ hankalin Yayan Sani har ya aiko mata da barazana. Haka ta ci gaba da renon cikinta cikin wahala da Kuncin rayuwa, shi kuma ya ci gaba da farautar rayuwarta, har Allah ya bashi ikon cimma burinsa na ganin ya kasheta. Wannan shi ne abinda na sani a kan Saudat! Idan an gaya maku wani labarin

. sabanin wannan to Karya ake yi, wanda na gaya maku a yanzu shi ne gaskiyar.” -

Sultan ya sauke ajiyar zuciya ba yadda ya kamata ba. “Kinsan waye Yayan Sanin? Kin taba ganinsa? Me ya sa ya kafa maki doka yake bibiyar rayuwarki?”’

Ajiyar zuciya ya Kwace mata ta ce, “Ban taba ganinsa ba, ban san shi ba. Duk abubuwan da yake yi yana turowa ne. Kamar lokacin da aka kashe Justi... Ku yi haKuri aka kashe Saudat. Sai aka ce ba a ga gawanta ba, haka ba asan me ya biyo bayan kasheta da aka yi ba. Shi ne yake zargin ta

Www.bankinhausanovels.com.ng gayawa wani ne kamar yadda ta yi ta aiko masa da barazana akan cikinta, da kuma cewar za ta tona masa asiri. Anduba kayanta babu wasu hujjoji, don haka aka biyoni gida akayi bincike a gidana aka ga babu komai,__, daga nan aka yi min gargadi da za a iya kasheni idan har na kuskura na fada wani abu. Iyayen Saudat sunyi kuka, sun so ko gawanta su samu, sun yi danasani. Yanzu haka Babanta yana kwance yana fama da ciwon zuciya, saboda rashin ‘yarsa. Amma ni har yanzu ban taba ganinsa ba, ko

- gunansa ban sani ba, ku yarda da ni ba zan yi maku Karya ba.” Sultan ya bugi bango da Karfi yana jin
babu ma amfanin wannan tatsuniyar. “Shi . Sanin ya za a yi mu gan shi?”
Girgiza kanta ta yi, “Ban san yadda za a yi mu ganshi ba, amma akwai abokinsa wanda shi yake hadamu da shi a duk san da muke son ganinsa, zan je innemo shi sai ya gaya mana inda za mu je mu ganshi.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano

wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.” Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita.

Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.”

Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?”

Aslaf ya zare glas din idanunsa yana sake duban Ashmaan, “Idan kayi hakanHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...