RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA 

Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.” Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace - ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.” Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar — gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu 


ZAMU TASHI 

ba? Allah ya kara nesanta su da mu, yasa ko a lahira haduwar ta yi wuya.” Hafsat ta mike ta ce, “Tabdijan! Nasreen matar Yaya Sultan? Allah ka tsaremu da hada zuri’a da shegu. Allah ya ga abinda ya gani.” Haidar ya mike yana fadin, “Af yanzu sai a nemo wata matar amma dai ba Nasreen ba.” Sultan bashi da Karfin furta komai, sai idanu da yake bin su da shi. Haka Abba ya kasa magana, ya tabbata yau zai yi barcin wahala na rashin ‘yan biyun da ya Kwallafa ransa akansu. Yaran suna da matuKar shiga rai. Sultan kuwa tunda ya duKar da kai bai sake motsawa ba. Shiru-shiru babu wanda ya sake yin magana hakan yasa mahaifinsa ya tsargu. Yana dago shi yaga baya motsi hakas yasa Abban sake gigicewa ya Kwala masa kirs yana girgiza shi. Umma da su Hafsat suka fito 8 guje. Ganin baya motsi yasa Umma ta dora hannu akai tana ihu. Haka ma Hafsat. Shi kanshi Haidar sai da ya yi Kwalla domin suna son? Yayansu fiye da komai, kawai hudubar uwarsu suke dauka. ) Cikin Kankanin lokaci aka isa da shi asibiti. Umma ta rike keken da ake gungura shi,

Www.bankinhausanovels.com.ng tana bin nursis din Abba ya fincikota daga jikin keken yana huci, “Ina ruwanki da shi? Dama kina sonsa kika ganshi a cikin wani hali kika sake tura shi ciki? Ashe kina sonsa kike watsa masa kalaman batanci? Idan Sultan ya mutu ke kika kashe min da kuma ba zan barki ba, dan sai nayi shari’a da ke. Salma ina matukar zarginki akan bacewar yaran nan. Yau da ina da hujja a hannuna da babu abinda zai hana ban kai ki Kara ba. Amma a juri zuwa rafi.. Abba ya koma gefe kawai yana sharar Kwalla. Ya sani, ya sani duk inda Nasreen suke suna cikin mawuyacin hali. Ya fi tausayawa rayuwarsu fiye da ta dansa. Umma kuka take yi sosai, ba don danasani ba, sai don halin da danta yake ciki, Sultan yana farfadowa ya zubawa mutanen cikin dakin idanu. Tabbas ya tabbata ba mafarki yake yi ba kamar yadda yake fata ba. “Abba angano inda su Nawfal suke? Abba a ina za su kwana? Wa zai dubi maraicin su ya basu abinci? Wa zai taimaka min ya yi aikin lada ya kula min da su? Abba a ina zan samo su? Shi kenan rayuwarsu Nasreen ya tafi kenan? Me ya sa ba ka gaya min Nasrecn matata ce ba? Da ka
Www.bankinhausanovels.com.ng gaya min da na gaya mata Kalmar da take ta dako ta ji daga bakina. Da ban yi mata Karyar babu aure a tsakanin mu ba. Da na bata kulawa a matsayinta na matata ko da sau daya ne tak! Abba ba zan taba sararawa wanda ya yi min wannan yankan Kaunar ba.” Abba ya zura masa idanu yana kallon yadda Sultan ya fita hayyacinsa a wuni guda. Shi ya san Sultan zai shiga halin da ya fi wannan ma, akan su Nasrecn. Sunkuyawa ya yi yana shafa kansa, “Sultan kai ba yaro bane, bare in ce har yanzu baka gama tantance menene Kaddara ba. Kana da hankalin tantance baki da_fari. Rayuwarmu bata tafiya a dai-dai dole sai jarabawa ta dinga ratsa mu. ‘Insha Allahu Nasreeri za ta dawo ku ci gaba da rayuwa a matsayin miji da mata. Kada ka mance Nasreen RUBUTACCIYA ce, tun tana cikin mahaifiyarta take haduwa da Kaddara, har yanzu tana rayuwa. Dole duk inda Nasreen take ta dawo domin bata da wani wurin da ya wuce nan gidan. Ka kwantar da hankalinka mu dage da addu’a.” Lumshe idanunsa ya yi yana tunanin a wani hali suke a yanzu? Wasa-wasa sai da Sultan ya yi www.bankinhausanovels.com.ng  kwanaki biyar yana jinyar kansa. Ko da ya dawo gidan ma sai ya koma yi masu yajin magana. A take ya kira su Mahbub ya gaya masu komai, hakan yasa dukkansu suka baro aikin su suka iso wurinsa. Barr Tajuddcen ya fara magana kamar kullum, “Sultan akwai sarkakKiya a_ cikin wannan lamarin. Ta ya ya hakan zai faru? Ta ya ya za a sace Nasreen da dan uwanta? Dole mai wannan aikin yana kusa da kai ne. Nasreen -matarka ce? Daman da ita Abba ya daura maka aure? TirKashi! Abin akwai sarKaKiya.” Haisam ya karBe da cewa, “Ko dai mahaifinsu ya gano akwai ‘ya’yansa a gidanku ne? Zai yuwu sai kawai ya aiko a sace su.”
Aslaf ya girgiza kai, “Ni ma tunanin da nake yi kenan, idan ba haka ba waye zai sace su?”” Mahbub ya girgiza kai, ““A’a mahaifinsu bai san da zaman su ba, bana jin shi ne zai yi wannan aikin. A dai sake bincike.”Ashmaaan ya dago yana duban kowa, har anfidda rai zai yi magana, sannan ya tanka, “Ku natsu sosai ku dubi maganar Mahbub, Idan har mahaifin nasreen yasan suna raye, ba zai bari su kawo wannan shekarun ba, zai aika a yi farautar ransu www.bankinhausanovels.com.ng kamar yadda ya yi na uwarsu. Amsar wanda ya aikata hakan yana wurin Sultan domin kuwa shi ne yasan mutanen da take takun saKa da su.” Khamis ya dan murmusa ya ce, “Dadina da kai kaifin basira dan mutan Sudan. Maganar gaskiya ba mahaifinsu ba ne ya yi aikin nan, wanda ya aikata laifin nan makusancin Sultan ne, na kurkusa. Sultan kayi sakaci gaskiya. Yaran da suke dauke da abubuwa masu rikitarwa, za kabar su kara zube? Kana da irin matsayin nan a hukumance amma kake barin ~wani lagwanin direba ya jasu zuwa Makaranta? Ai yaran nan tsaro suke bukata. Ka mance na yi irin wannan sakacin aka tafin min da mata? Ka mance Ashmaan ya yi irin wannan gangancin aka kusa kashe masa mata? Daga Karshe me ya biyo baya? Dabararsa ta Kwace shi, da ya dauke matarsa ya turata London. Shi Mahbub da ya fimu dabara, ai hada matarsa ya yi da ‘yan sanda ya kuma sanya doka mai tsanani akanta. Yanzu dai menene abin yi?” Al-ameen ya ce, “Aikin gama ai ya gama. If not da gidajen daya daga cikin mu ya kawota aka boyeta har a gama bincike, mu zaKulo masu www.bankinhausanovels.com.ng laifukan. Yanzu maganar bincike a kan wadanda suka yi kisa dole a dakata tunda shaidun sun Bace. Kawai mu mayar da hankali wajen nemanta.” Sultan ya girgiza kai, “Mahaifiyata ce kadai ta tsani Nasreen da dan uwanta tsana mai tsanani. To kaina ya kulle ko ita ce za ta sanya ayi hakan domin nisanta su da mu? Sai kuma wani dan iska da ya taba zuwa wai yana sonta Wai sai ya aure ta. A lokacin bansan andaura mana aure ba, zafin da mahaifina ya dauka ya bani mamaki. Su dai nake zargi.” Barrister Tajuddeen ya danyi rubutu ya -. dago yana duban Sultan, “Sorry to say Sultan, Umma ita ce asalin suspect! Amma kuma tafi Karfin mu gaskiya. Sai dai mu bi komai a hankali har Allah ya warware mana ‘wannan tashin hankali. Sannan zamu sa malamai suyi ta sauka suna addu’a. Allah ya bayyana maka matarka da dan’uwanta,”
Gabadaya aka amsa da Amin. Sultan ya dan shafi sajensa ya ce, “Zan bar garin nan. Ba zan iya zama a cikin gidanmu ba, sai in ga kamar zan ga Nasreen. Yarinyar da bata ganin gabanta ya za tayi rayuwa a wurin da babu tattali? Ba www.bankinhausanovels.com.ng zan yi aure ba, zan tsaya in jirata har ta dawo gareni.ba” Babu wanda ya nemi ya dakatar da shi, domin dukkansu sun dandani dacin soyayya. Haka suka tashi suka yi musabaha sannan duk suka rabu. Sultan yana isowa gida ya same su suna zaune ya gaida su, sannan ya dube su fuskar nan babu fara’a. “Abba nan da wasu lokuta insha Allahu zan koma Abuja da aiki. Sai a taya ni addu’a.”” Abba ya dube shi da tausayawa ya ce, “Sultan ya zama dole kayi aure. Ba zan zuba ido ka kai wannan shekarun babu mata ba. Ka yi hakuri kada kayi fushi, ka raya sunnar manzo. Kullum matsayi sake zuwar maka yake yi, amma ka kasa haKuri da Kaddararka.” Shiru ya yi yana sauraren Abbansa. “Abba zan jira ta har ta dawo.” Shiru dakin ya yi har yaushe za a tsaya jiran dawowar Nasreen? Wa ya san rana? Kyale shi kawai ya yi domin ya samu natsuwa. Umma zata yi magana ya daga mata hannu. Sultan har ya fice zai shiga dakinsa ya dawo da baya yana kallon Kofar dakin Nasreen da babu kowa a ciki. Girgiza kansa kawai ya yi ya wuce., Duk wasu www.bankinhausanovels.com.ng kayayyakinsa da yasan zai iiya nema ya tattara su wuri daya. Hoton da suka dauka su uku ya kafe. da idanu. Shi Nasreen sai kuma Nawfal. Ya jima yana kallon hotunan kafin ya zuba su a cikin kayansa. Cikin gaggawa aka daga shi zuwa Abuja, a lokacin ne kuma ya sauya sabuwar rayuwa.

Da asubahi suka tashi suka gabatar da Sallah,
a lokacinne kuma mai abinci ta 1so tana Kokarin hada murhu. Nasreen da Nawfal suka gaishe ta, Ya jawo hannun Nasreen ya zaunar da ita a gefe guda, ya taya mai abincin hura wuta. Duk ruwan da ake dibo mata shi ya-diba mata, hakan yasa ta fahimci yaron yana da zafin nama, duk da jikinsa yana nuna hutu. Gari yana yin haske mutane suka shiga zuwa siyan abinci, a lokacinne kuma ta zuba masu nasu abincin ya {Karasa inda Nasreen take zaune ta yi tagumi ya janye tagumin yana dubanta, ‘‘Nasreen ki daina damuwa bana so. Ga abincin ki ci, ni zan je inwanke mata kayan miya.” Tausayin Nawfal ya kama ta, yau kwatakwata bai huta ba. Tana cin abincin tana kuka. Ta rasa ta yadda za a yi ta taimakawa dan www.bankinhausanovels.com.ng uwanta yau yasha wahala sosal. Basu suka samu suka zauna a inuwa ba, har sai da aka kira Magrib. Haka idanuwan mazan nan ya koma kanta. Da zarar suka fahimci makaunlya ce sai su tausaya masu. Haka basu yarda angane a wurin - suke kwana ba. Sai da dare ya yi sannan ya zagaya ta baya ya ajiye mata ruwan wanka, saboda Amina ta basu aron bokiti da soso. Ya ce, “Nasreen ta shi kije ki yi wanka.”

Babu musu ta tashi ta zagaya. Yana nan tsaye yana gadinta har ta gama kintsawa, ta mayar da kayan makarantarta...RiKe hannun Nawfal ta yi, tana kuka, “Nawfal kana shan wahala da yawa. Nawfal ba zamu iya wannan rayuwar ba.” Shima riketa. ya yi “Zamu_ iya Nasreen, ki Karfafa zuciyarki zamu _ iyaWatarana sai labari.” Da haka ya samu yake Karfafa mata guiwa, Haka suka kwana cikin cizon sauro da cinnakai, gaba daya jikinta sun yi rudu-rudu saboda azabar cizo. Washegari ta ce, “Nawfal ba zamu nemi wani wurin kwanciyar ba? Na gaji da, nan. Www.bankinhausanovels.com.ng Sai da ya yi murmushi sannan ya ce, “Allah ya bamu.sana’a mai dan Karfi ko Daki ne mu kama sai mu ga abinda Allah zai yi. Nasreen ta yi na’am da bayanan Dan uwan nata, wanda ya fita nisan tunanin, A kwanaki biyar kadai Nasreen ta fita hayyacinta, shi kuwa Nawfal har ya fara sabawa da wahala da kuma kwanar siminti, Sultan. kullum yana ¢ikin ransa, yasha komawa gefe ya yi kukansa yadda ransa ke so, ya dawo ya share hawayensa. Ana hakanne akayiwa Amina Sata a shago, aka likawa Nawfal wai shi ya saci kudin,: Wannan abu ya yi wa Nasreen ciwo. Amma sai Nawfal ya nuna mata babu kemai jarabawa ce, Haka ta kore su a ~ gaban jama’a ta kunyata su, ta dora masu laifin sata. Suka fice titi Nasreen tana bara ana ba su kudi a nan ne suke samun na cin abinci, Nawfal ya dube ta zaune a gefen titi ya ce, “Nasreen dole mu san abin yi, bara alamun mutuwar zuciya ce da ke addabanmu ‘ya’yan hausa, bana son mu kasance daga cikin su. Gara mu bemi na kanmu Zan dinga zuwa wajen mai garuwan nan yana bani ina siyar masa sai ya bani Www.bankinhausanovels.com.ng wani abu. Ni yanzu makwancin mu yafi damuna. . Na gaji da bin kangon nan da muke yi.” Nasreen ta sharce hawayenta ta ce, “Nawfal ina son ganin Deedi, bansan halin da yake ciki ba, Nawfal mu koma gida don Allah.” Girgiza kansa ya yi, “Gara mu mutu a nan da mu koma gida. Nasreen Umma tana neman rayuwarki ne, idan ta kashe min ke wa zan gani inji sanyi a raina? Wacce irin rayuwe zanyi ni kadai babu ‘yar uwar haihuwata? Nasreen har yanzu na kasa yafewa Umma da ta makantar min da idanunki. Na kasa ganin farinta. Don haka kiyi haKuri da talaucin mu, mu nemi-na kanmu. Zanje wani gida mai zaure mai kyau inroka mu dinga kwana a ciki kin ji?” Kanta kawai ta daga ba tare da ta iya furta komai ba. Zazzabi ne mai zafi ya rufeta sai karkarwa take yi. Hankalin Nawfal ya kai matuKa a tashi dole ya fice ya nemo karare ya kunna mata, sannan ya nufi Chemist da ragowar - kudin hannunsa ya siya mata magani. Wasawasa sai da Nasreen ta koma sai andagata ankwantar. Kullum magana daya take yi masa ya kaita wajen Deedinta kada ta mutu. Shi kuma ya www.bankinhausanovels.com.ng yi alKawarin babu inda za su sake komawa a gidan nan.’ Kasancewarsa mutum mai zuciya. Haka kuma yana da lambar Sultan akansa da ta Abba, amma yaki barin ma tasan da hakan, domin yasan za ta matsa sai an je an kira su, shi kuwa roKon Allah yake yi Allah ya Kara nesanta
Su. Sultan cikin ikon Allah ya dinga samun daukaka da kuma Karin girma akai akai wanda hankalinsa yafi kwanciya da yake nesa da mahaifiyarsa, sai dai Nasreen da take nan daram kamar yau ya fara sonta. Ya Kara kyau da haske, sai “yar rama da ya yi: Baya son magana idan ba ta kama dole ba. Haka baya ziyartar gida aikin kawai yasa a gaba. Katon gidansa babu abinda babu na more rayuwa, haka gidansa cike yake da ‘yan sanda masu kare lafiyarsa. Ya zama aiki yake yi babu ji babu gani, wanda a yanzu ya hau kujerar G Wannan girma ba shi kadai ya shafa ba, hatta iyayensa da ke garin Kaduna sai da abin ya zame masu abin alfahari, a dan shekarunsa ya taka matsayin da ba kowa yake da wannan arzikin ba. Farin jininsa a jini yake, ya zama dan gaban goshi a cikin ‘yan sanda. Www.bankinhausanovels.com.ng Ganinsa wahala yake yiwa jama’a haka bai cika zama a gida ba, saboda ayyuka. Da zuwansa ya kawo sauye-sauye na ban mamaki. Ya zuwa yanzu ya gama fahimtar ya rasa Nasreen har abada. Sai dai kuma ya fara samun surutai a gidajen jaridu akan rashin matarsa. Tun abin baya damunsa har ya koma yana daga masa hankali. Babban burinsa. Nasreen ta dawo ta shiga dakinta. Yau a wurin aiki ya kwana, saboda wasu mahimman tattaunawa da suke yi da IG. Yana dawowa gida daya daga cikin ‘yan sandansa ya sanar masa da zuwan iyayensa. Haka kawai ya ji baya farin ciki da zuwansu. Yana shigowa ya ga mahaifinsa yana zaune yana karanta Jarida. Farin cikin ganin mahaifinsa yasa shi murmushi. Frij ya nufa ya fincike hancin Coke ya dora a cikinsa, tare da _ furta, “Alhamdulillahi. Abbana na ji dadin zuwanka.” A Kasa ya zauna sai ka ce ba shi ba ne idan zai fita yake shan, mur, ana biye da shi kamar wani sarki, Umma ta fito ita da wata yarinya, kallo daya ya yi mata yaji wani irin tsanarta a ransa. Kai da ganinta ka ga mara tarbiyya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sama-sama suka gaisa, kafin Abbansa ya dube shi ya ce, “Sultan baka da alamar aure. Baka san hakan tonon asirinka bane? Duniya tana kallon kowane shige da ficenka. Girma ne ya same ka tun kana da Kananun shekarunka. Don haka mahaifiyarka ta samo maka mata har andaura auren da kanmu muka kawo maka. Nasan kai mai biyayya ne, baka taba ce min a’a ba. Me kika ce Hajiya?” . Sultan. ya .kafe mahaifinsa da idanu, sai yanzu ya kula da wata rama da ya yi abin akwai al’ajabi. Haka ya cika da mamakin yadda mahaifinsa zai amincewa mahaifiyarsa wajen nema masa mata. A sanin da ya yi wa mahaifinsa mutum ne mai Zafi, ba ya son wargi, haka ummansa tana shakkarsa duk kuwa_ irin masifarta. Yau ga shi Abba yana mata magana cike da ladabi. Yau ga Abba yana bin dukkan shawararta. Haka ya nuna alamun tsoronta da yake ji Karara. Sake zuba masu ido ya yi yana son ganin Karshen wasan, Umma ta dubi yarinyar da fuskar nan ta sha kwalliya ta ce, ‘“Kaima Alhaji sai ka bari ingabatar da ita. Wannan dai sunanta Zakiyya, www.bankinhausanovels.com.ng ita ce ‘yar Hajiya Ladidi da na taba yi maka maganarta. Ba ta da matsala za ka ji dadin zama da ita. Bana son Kananan maganganu don haka nake son ka riketa da amana, ka fito da ita duniya ta santa. Ko ya kace Alhaji?” Abba yana magana kamar jikinsa har rawa yake yi, idan har ba idanunsa ne suke yi masa gizo ba. “Haka ne Hajiya. Ai shi Babana bai taba yi min musu ba. Allah ya yi maka albarka.” Bai iya amsawa ba, sai idanu da yake bin kowannensu da shi. Suna nan zaune mai aikinsa ya kawo masu abinci, kowa ya zuba yana ci, amma Sultan ya kasa kai koda cokali daya bakinsa. Zama ya yi kawai yana zare safar Kafarsa, ya mike yana fadin zai dan watsa ruwa. Umma ta Kyafta mata idanu Abba sai faman yashe bakinsa yake yi. Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?” Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Www.bankinhausanovels.com.ng Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.” Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.” Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen,

HMMM LABARI FA NATA ZAFI SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...