RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA 

duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.” Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.” Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.” . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu " sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.” 


ZAMU TASHI 

Hajiya Ladidi ta saki dariya sosai sannan ta ce, “Ashe ‘yan iskan nawa suna da rana? Shi yasa nace maki a hada aurensu da ‘yata amma wannan kafaffen mijin naki ya hana. Wannan aiki ne mai sauki, Rainbow dinnan dai shi za mu sake sawa ya yi aikin nan.” A nan suka gama kintsawa akan idan Nasreen za ta je Makaranta a nan za a saceta ita da Nawfal. Tana isowa gida ta sami Sultan yana gyara mata gashinta, da take ta mitan yana damunta ya taimaketa ya aske mata. Bai ce mata komai ba, ya tattare mata gashin ya Kulle a cikin Katon ribom. Hajiya Salma kamar za ta yi magana, sai kuma ta hadiye da ta tuna da komai ya kusan zuwa Karshe. Mikewa ta yi tana fadin, “Dee kama ni ka kai ni daki ina son shirin zuwa Makaranta, bansan inda Nawfal ya tafi ba. Babu musu ya kamata ta shiga dakin, ya fitar mata da kayan Makarantarta kafin ya fice daga dakin ya tafi neman Nawfal. A tsakar gida ya same shi yana Kwallo, ya Karasa ya tallabi Keyarsa tare da riko

Www.bankinhausanovels.com.ng  kunnensa daya. “Kai baka jin magana ko? Karfe nawa yanzu?” Nawfal ya rike hannun Sultan yana rintse ido, “Wayyo Deedi ka yi hakuri don Allah na tuba ba zan sake ba.” Hannunsa riKe da kunnan Nawfal ya tasa shi gaba har cikin daki. Da suka tashi tafiya Makarantar shi ya dauke su da kansa ya kai su har Makaranta. Daren ya tsala wuri ya yi shiru, baka jin motsin komai, sai na tsuntsaye. Nasreen ta fito tana lalube a yanzu ta haddace inda komai na gidan yake, don haka ta nufi dakin Sultan. Yau bai kwana a office ba, yana gida don haka ta iso har kan gadonsa. Yana kwance yana kallonta, haka ya zuba mata ido ne kawai ya ga iya gudun ruwanta. Lalubansa take yi har ta tabbatar ga inda yake, sannan ta kwanta shiru a Kirjinsa, “Deena me yasa bana iya barci sai da tunaninka? Me ke shirin faruwa da rayuwata ni Nasreen? Ina jin damuwa a kwana biyun nan, ina jin kamar zan rasa ka. Deee ka tashi ka gaya min mene ne ke shirin faruwa da ni? Dee.,.” Ta ja sunansa tare da Www.bankinhausanovels.com.ng  dora hannayensa a bisa fuskarta da ke kwararar hawaye. Shi dai bai ce komai ba, sai kallonta da yake yi. Ya zama dole ya ajiye wasan kwaikwayon nan shi da Nasreen ya tabbatar mata da yana sonta. Irin abinda Nasreen take ji, shi ya fi ta jin fiye da hakan. Hawayenta ya kafe da ido yana dubanta. Da gaske tana bashi tausayi musamman rashin idanun da yafi so fiye da komai. Idan ta ware idanunta tana dubansa, sai ya ji kamar ta kwashe dukkan kuzarin jikinsa ne. Ta ya ya zai iya fitowa ya ce Nasreen yake so? Me yasa? Idan ya yi hakan zai sa rayuwar Nasreen a cikin matsala! Haka kuma ba zai taba samun natsuwar da yake nema ba, saboda mahaifiyarsa duk za ta hana hakan, Sannan ba Zai iya ce mata yana sonta ba, har sai ya gano su waye iyayenta? Me ya jefa mahaifiyarta a cikin irin wannan halin bakar rayuwar? Yatsunta ya kafe da ido gabansa yana tsananta fadiwa. Babu inda ya tsunta ya bambanta da na Haidar Kaninsa. Kafafunta kuwa iri daya da nasu. Wannan abu yana sake daure masa kai Sai yanzu yake takaicin Kin bude hotunan nan ya Www.bankinhausanovels.com.ng fi tunanin a nan ne zai gano komai. Sai dai yasan ko wasu irin hotuna ne ba zai wuce hotunan . mahaifiyarta ba, shi kuma idan har zai dubi hotunan nan sai mutuwar Saudat ta dawo mata sabuwa fil! ‘““Nasreen.. Ya kira sunanta, wanda yasa ta yi firgigit! Ba ta yi magana ba, don haka ya dora, “‘Nasreen kina jin son Deedinki a cikin zuciyarki? Nasreen babu aure a tsakanina da ke. Ki dauke ni a yadda kike daukana a da kin ji? Nasreen Abbana shi ne mahaifinki anboye ne saboda wasu dalilai idan lokaci ya yi zaki san komai kinji? Nima da farko da bansan hakan ba, irin abinda kike ji shi nake ji, daga baya na sawa raina hakuri. Sannan idan auren za a yi, ban yi maki girma ba Nasreen? Yaro Karami zan baiwa aurenki, wanda bai wuce sa’an Haidar ba. Kin ga ni na wuce talatin ko? Maza _ ki share hawayenki.” Kukanta ya Karu da yawa, bata jin za ta iya cire abinda ke cikin zuciyarta, ba ta jin za ta iya rage son Sultan wanda bata ko tantama da soyayyarsa aka haifeta. Tana son tasan wacce irin alaKa ce ke tsakaninta da Deedinta. Duk da ta kadu da kalamansa, amma hakan baisa ko digo daya daga cikin soyayyarsa ta ragu ba. Www.bankinhausanovels.com.ng  Tana sonsa da gaske. Ta shirya wa tunkarar kowacce matsala a kansa. Sake damKe hannunsa’ ta yi tana jin duk wata kunya ta kau a idanunta, tana jin za ta iya gaya masa komai. “Dedena, ina son ka, zan iya mutuwa Ko babu aure a tsakaninmu zan zauna da kai. Ba zan taba iya yarda da wani namiji ba, yin hakan zai gurgunta rayuwata. Ka rike ni a gidanka zan zauna da matarka. Don Allah ka roKe ta kada ta raba ni da kai. Ban san kowa ba sai kai da Abba. Kai ka koya min wannan rayuwar, Sai dai na yi nisan da ba za ka iya cire min abinda ke cikin zuciyata ba.” | Kalaman da Nasreen take ambatowa sun yi matuKar bashi mamaki, ta yaya Nasrecn ta iya irin wannan kalaman? Ya aka yi Nasreen tasan soyayya haka? Yaushe ta cire kawaicinta ta iya furta masa wadannan kalaman? Tausayinta ya kwaranyo masa, baya jin zai iya hada Nasreen da kishiya bare har ta cutar masa da ita, Yana yi mata irin son da duk wanda ya kama da cutar da ita zai dauki matakin da sai duniya ta girgiza da irin matakinsa. Ya danganta rashin kawaicinta a yau da rashin idanunta, ya tabbata da za ta hada Www.bankinhausanovels.com.ng idanu da shi, ba za ta taba samun Karfin halin da za ta fada masa wadannan kalaman ba. Share mata hawayen ya yi ya rungumeta tsam a Kirjinsa. A lokaci guda yake jin kamar shaidan ke son cin galaba akansa, idan ya yi la’akari da yadda komai ya sauya daga cikinsa. Bisa labbansa yake magana, “Ina jin irin abinda kike ji Nasreen.” Shiru ya biyo bayan hakan, sakamakon saKon da ya bata mai matuKar tasiri. A lokaci guda ya zame kansa, yana jin meyasa zai zama mutum na farko da zai gurbata amanar da Saudat ta bashi? Sai da ya natsu sannan ya ce, “Nasreen ki tashi ki koma dakinki.”Shiru ta yi sakamakon yadda Kafafunta suke rawa. Haka ta tsinci kanta cikin wani baKon al’amari. Yawun baki wani irin abu ne mai kama da guba, idan suka hadu wuri guda suna sanya zazzafar soyayya da kuma shaKuwar dake da wahalar rabuwa. Hakan ce ta kasance da Nasreen @ wannan daren. Hannunta ya kama suna mikewa tsaye ta yi baya za ta fadi, ya yi saurin dawo da ita ta fadi a jikinsa, “Nasreen! No kada ki yi min haka. Ki Karfafa jikinki don Allah. Ki tuba ga Allah Www.bankinhausanovels.com.ng  wannan abun haramun ne kin ji? Kada ki sa shi a ranki kin ji?” Ba tayi magana ba, amma ta dan Karfafa jikinta. Da kansa ya rakata dakinta ya kwantar da ita, tare da addu’a sannan ya jawo mata bargo ya rufeta. “Sleep!” Ya furta tare da hure mata fuska. Luf idanun suka sake  rufewa. Ta shaki Kamshin bakinsa tana sake rurrufe idanun da daman a rufen suke. Ya tashi ya kashe mata wuta ya fice abinsa. Wannan lamari akan idon Umma ya faru, hankalinta idan. ya yi dubu to ya tashi. Abinda ya sake ba ta mamaki Abbansa ashe yana tsaye shi ma yana kallon su. Duban fuskar Abban ta yi da mamaki yadda yake ta murmushi. Ta sake leKa fuskar Abban ta tabbatar da murmushin yake yi. Kafin ta yi magana Sultan ya Karaso falon ya bude frij zai dauki ruawa. Domin ji yayi makoshinsa ya bushe saboda halin da ya tsinci kansa a ciki. Ji ya yi kawai an shaKo shi, kafin yayi wani abu, ya ji saukar mari ko ta ina @ fuskarsa, Sai huci take yi, “Kai kai! Baka isa ka kasheni ba, Zina kake aikatawa da Nasreen? ‘Ya’yan mazinatan ne suka shigo rayuwarka su Bata maka tarbiyya? Wallahi idan ka kasance Www.bankinhausanovels.com.ng  mazinaci ba zan taba yafe maka ba a cikin gidan nan, sai na tsine maka kabi duniya! Kaf zuri’ata babu mazinaci, kai kuwa baka isa ka jawo min wannan abin kunyar ba. Dama sonta kake yi dan ubanka! Za ka yi min magana ko sai na kasheka a gidan nan?” Ta daga hannu da nufin sake marinsa, Ta ji anriKe hannunta. Abba ya tunkudeta gefe saura kadan ta kifa. Yana dubanta yana huci, “Insha Allahu ban haifi mazinaci ba, bana fata idan Allah ya jarabceni da da mazinaci ba zan tambaye shi dalili ba, haka ni nasan ban zagi ‘ya’yan wasu ba, sai dai idan alhakin zagin da kika yiwa ‘ya’yan wasu ne ya sauka akanki. Haka ba dai dana Sultan ba, sai dai idan ‘ya’yanki da kika lalata da irin halayyarki.  Wannan yaron da kike gani, shi ne dan da nake fatan ya gado ni kuma na gode Allah. Kada ki sake danganta min da da zina, yin hakan zai jawo maki mummunan bacin rai Wallahi!” Umma ta dube shi da mamaki, “A gabanka fa ya fito manne da ‘yar iskar can!” Abba ya yi saurin tare numfashinta, “Sai _me? Idan kin ganshi rungume da ita nace sai Www.bankinhausanovels.com.ng  mene? Kuma ina son ki gane, kin taba fuskar yaron nan na Karshe! Sultan ya wuce mari a yanzu sai dai nasiha. Kai Sultan zo ka wuce dakinka. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya. Maza ka wuce.” Sultan ya juya kawai yana jin dacin furucin mahaifiyarsa akansa. Ya maimaita Kalmar zina tafi a Kirga. Hakan yasa ya kasa barci. Tunanin ya yi nesa da Nasreen da iyayensa suka darsu a zuciyarsa. Ita kuwa Nasreen ta lashi labbanta da suka yi laushi ya fi a Kirga. Tunanin Sultan ya ci gaba da gallabanta. A haka har barci barawo ya sace ta Washegari suka shirya zuwa Makaranta, a lokacin Sultan ya jima da barin gida. Akan hanyarsu ta dawowa ne aka tare direban su aka cunkusa su a wata mota. Nasreen dai tana rungume da Nawfal bakinta bai fasa addu’a ba. Wani irin Kunci ya ziyarceta, Yanzu mutanan nan ina za su kaita? Ita dai damuwarta kada a rabata da dan uwanta. Da zarar ta tuna da Sultan Sai taji wasu hawaye suna kwaranya. Nawfal dai ko Kwakkwarar motsi ya kasa yi. Tafiya ake yi tun suna sa ran sauka har suka sadakar da kwanakin su a duniya ya Kare. Sai wajen Www.bankinhausanovels.com.ng  Magriba aka bude Kofar mota aka cillo su waje sannan suka Kara gaba. Nawfal ya dubi Nasreen cike da tausayawa ya ce, “Nasreen kin ga wata duniyar suka ajiye mu. Yanzu ina zamu dosa?” Nasreen ta ce, “Duba ka gani akwai jama’a a garin?” Ya dudduba ya ce, “Daji ne wurin babu wasu jama’a. Amma zo mu Kara gaba ko zamu sami abinda zamu ci.” Haka suka yi gaba babu wanda suka samu sai wata mai siyar da abinci da take shirin rufe wurinta. Nawfal ya fara magana, “Sannu. Don Allah wani gari ne nan?” Matar ta dube shi ta ce, “Ku kuma daga ina haka? Wannan garin Katsina ne Kankia. Me ya kawo ku nan?” Nawfal ya dan yi shiru, “Wallahi wasu ne suka sato mu suka kawo nan. Don Allah ina Zamu sami makwanci? Sai ki daukeni aikin wanke-wanke kina ba mu abinci, ° Matar mai suna Amina ta nuna masu Kofar shagonta wanda akwai rumfa, “Sai dai ku dinga kwana a nan domin ba zan iya baku makwancl Www.bankinhausanovels.com.ng  ba, kun san duniyar babu amana. Ita wannan makauniya ce?” Ya dan durkusa, “Mun gode _ sosai. Makauniya ce” Ta dan tausaya masu, sannan ta cire zanenta daya ta basu ta ce, su lulluba. Har ta tafi ba ta daina waiwayarsu ba. Ita kuwa Nasreen umartar Nawfal ta yi da ya samo masu ruwa suyi alwala. Bayan sun yi alwala ne suka raba dukkan sallolin da ke kansu sannan suka dan rabe. Nasreen tana jin yunwa, amma kuma ta kasa gayawa Nawfal yunwa take ji, saboda kada ya shiga damuwa. Shi kansa yunwar yake ji amma ya kasa furtawa. Can ya tuna da awaran da ya siyo daga Makaranta don haka ya ciro jakarsa ya fitar, a lokacin ne kuma Nasreen ta jiyo Kamshi da fara’arta ta ce, ““Nawfal menene wannan kuma?” Sai da ya kai bakinta ta gutsura sannan ya bata amsa, ““Dazu ashe na siya wara na manta ne. Zai ishemu mu ci.” A nan suka cinye warar, Nawfal ya dibo masu ruwa suka sha. Cikin dare dukkansu suka kasa barci saboda azaban cizon sauro. Shi dai Nawfal sai korarwa Nasreen Sauron yake yi. Ga kwanciyar Kasa, ga cinnaku, ga sanyi da ke ratsa su. Nasreen ta Www.bankinhausanovels.com.ng  dinga kuka ba tare da ta bari Nawfal ya sani ba. Can ta yi magana a hankali, “Nawfal waye zaiyi .mana haka? Me yasa za a raba mu da danginmu?” Nawfal ya girgiza kai, ‘“‘Nasreen idan kina tunanin su Abba danginmu ne ki daina tunanin hakan. Da wahala idan ba tsinto mu aka yiba. Rannan naji Umma suna magana da wata Kawarta take cewa Deedi ne ya rakito mu, ya kawo masu masifa cikin gida. Amma tabbas! Mu ba “yan gidan bane. Ya zama dole mu mance duk wani jin dadi, mu fuskanci abinda ke gabanmu. Mu koyi zaman wahala mu koyi nema da kanmu, mu koyi maraici, tunda dama mu din marayu ne. Idan muka ce zamu yi ta zama a gidan nan watarana Umma za ta sa ashana ta Kona mu. Kin ga ta nakasa maki idanu, yanzu haka ita ta sa,a kawo mu nan, Don Allah Nasreen mu mance gidan nan mu jure dukkan gwagwarmayar nan watarana sai labari.” Nasreen ta gigice da kalaman Nawfal, don haka ta bashi labarin yadda suka yi da Sultan a daren jiya, ta ci gaba da cewa, “Yanzu Nawfal mu dauka ba mu hada komai da su Abba ba, idan muka barsu munyi Www.bankinhausanovels.com.ng  masu adalci? Wane hali yanzu su Deedi suke? Sun raine mu tsawon shekaru goma sha bakwai, yau don mun yi fushi sai mu guje su? Da wannan zamu saka masu kenan Nawfal? Ya kamata muyi tunani.” Nawfal ya ce, “Nasreen bamu yi laifi ba idan muka yi hakan. Zamu bi su da addu’a wanda duk nisan inda muke zai je ya same su. Maganar kuma babu aure a tsakaninki da Deedi ya dai fada maki hakanne domin baya son ki damu da lamarinsa, yana hango tashin masifun da zaki iya shiga ne idan har Umma tasan akwai soyayya a tsakaninku. Don Allah mu mance baya mu fuskanci gaba.” Nasreen ta fitar da kukanta fili, wanda har yasa zuciyar Nawfal ya karaya, “Nawfal ka yi min addu’a domin na fada cikin hatsarin son Deedi. Ba zan iya raba kaina da irin wannan soyayyar ba, domin bansan lokacin da ta shige ni ba.” A lokacin wani Katon sauro ya cije ta ta kai wa kanta duka, Nawfal ya share hawayensa ya ce, “Zan taya ki da addu’a insha Allahu komai zai zama labari.”Www.bankinhausanovels.com.ng A can garin Kaduna kuwa, Sultan yana Office ‘ya ga kiran mahaifiyarsa, abin ya ba shi mamaki domin ba zai tuna ranar da ta kira shi ba. Ya dauka da Sallama tun kafin ya gaisheta ta fara magana, “Sultan su Nasreen ba su dawo daga Makaranta ba, ko kuna tare ne?” Mikewa ya yi tsaye kafin ya ce, “Umma ban gane ba? Ina shi direban yake?” Umma ta tabe baki, “Babu direba, babu su Nasreen. Allah ya sa ba wani gantalin aka wuce ba.” Sultan ya katse wayar kawai ya hada ‘yan sanda suka fita a cikin motarsu. Kai tsaye hanyar Makarantar suka nufa, a nan suka sami direba a yashe, ga mota a gefe, haka mutane sun fara taruwa. Shi ya fara sakkowa daga motar ya tallabo Direban, Sumewa ya yi don haka yasa a kawo masa ruwa ya watsa masa, gabansa yana tsananta faduwa. Yana farfadowa ya ce, “Ina su Nasreen? Ina suke!” Ya daka masa tsawa. A gigice yake magana, “Yau na shiga uku! Wasu suka zo a farar mota suka tafi da su.” Sultan ya shake dircban nan jikinsa yana rawa, “Idan wani abu ya sami su Nasreen ina Www.bankinhausanovels.com.ng  tabbatar maka sai na kashe ka! Ka gaya min da su waye ka hada baki aka sace min su? Gaya min waye ya turo ku?” Sultan fa ya haukace, ya fita hayyacinsa. Da Kyar ‘yan sandan nan suka Kwaci direba, sannan suka sa shi a baya tare da wani dan Sanda aka samu aka lallaba Sultan ya shiga motar gidansu dan sanda ya shiga ya wuce da shi gida. A lokacin Abba ya dawo, don haka ya Karaso gaban Abba jiki asanyaye. “Abba..” Ya ja sunan mahaifinsa, ya kuma kasa furta komai. Sai dan sandan nan ne ya korawa Abba “bsyani Da Karfi Abba yake Salati. Sultan kuwa ya kasa magana, sai idanunsa da sukayi jazir kamar  gauta. Jikinsa har rawa yake yi. Ita kanta Umma yadda taga yaron nata ya sauya a lokaci guda yasa jikinta mugun sanyi.,,Gaba daya suka shiga falo, Abba ya baiwa dan sandan umarnin a bi ko ina a sanya cigiyarta. Kafin ka ce me? Gari ya dauka an sace "yan biyu mace da namiji, Sultan ya zauna a kujera jikinsa asanyaye babu Kwari, Haduwarsu kawai yake tunawa a jiya, ya kasa magana ya kasa duban Abbansa. Www.bankinhausanovels.com.ng  Shi kuwa Abba tashin hankalinsa ya ninku da ya tuna bai sauke Katon nauyin da ke kansa ba. “Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.” Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace - ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.” Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar — gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu HMMM LABARI NATA ZAFI FA SHIN KOYA ZATA KAYA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...