RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 


Abbansa. ' A falon ya tara kowa yana faman kaiwa da komowa ransa a matuKar bace.,“Ya zama dole ku gaya min wanda ya aikata wa Nasreen wannan abin,:ko kuma in hada ku dukka in kulle.” Hajiya Salma da ba ta dauki lamarin zai yi irin wannan zafin ba, ta ware idanu, “Yanzu a kan wannan yarinyar za ka kulle su?” Alhaji Lukman ya Karaso har gabanta kamar zai dake ta, “Me ya sa kike cire kanki a cikin mutanen da zan dauki mataki a kansu? Ke ce mace ta farko da zan fara kiran “yan sanda su tafi da ke, su tuhumeki. Domin na fi zarginki, 


ZAMU TASHI 


Www.bankinhausanovels.sannan abinda yasa na hada da ‘yan aikin nan, saboda ban san aikin me suke yi da har za a yi wannan rashin hankalin wai a ce dukkanku babu wanda ya ji. Don haka idan kuka tsince ku a Police Station duk za ku yi bayani.” Yanzu Abban Sultan a kan yaran nan za ka zarge ni? Kana tunanin zan iya aikata wannan rashin mutuncin? Rashin imanina bai kai nan ba, duk abinda zan iya yi, ba zan iya kashe rayuwar idanun Nasrcen ba.” Kawai tasa kuka mai tsuma zuciya. A take nadama ya shige shi, haka kuma ya gaskata ba ita ba ce, to amma idan ba ita ba ce wace ce? Ta ya ya duk suna cikin gidan a ce an rasa gane wanda zai yi wa Nasreen hakan? A fusace ya fice daga gidan gabadaya. Kai tsaye gidan mahaifityarsa ya nufa ya zayyane mata komai. Hajiya Gwaggo ta dinga Salati tana Karawa. Cikin kuka take ambaton bala’i ga duk wanda ya aikata mata wannan mummunar aiki, Alhaji Lukman ya yi shiru yana sauraren addu’ar mahaifiyarsa haka kuma yana amsawa da Ameen. Yana sane da yadda mahaifiyarsa take Kaunar ‘yan biyun

tamKar jininta. Karfe ukun dare agogon bangon ya buga, a wannan lokaci Alhaji Lukman ne tsaye cikin dogon nazari. An dade ba a yi abinda ya tashi hankalinsa ba, kamar mutuwar idanun Nasreen. Yana kallon yadda dan uwanta ke riKe mata sanda idan za su je Makaranta. Hankalinsa yana Kara tashi ne idan ya tuna duk ranar da Sultan ya dawo, me Zai gaya masa akan amanar Nasreen? Sultan ya dauki burin duniyar nan ya dora a kan yaran, yana hango masu tarin ilimi a nan gaba. Musamman Nasreen da take: gaf da sauke Alqur’ani. Yarinyar ta taso da wani irin ilimi na ban mamaki, wanda ya sake sanya Kyashi a zuciyar Hajiya Salma. Haka abinda ke damun ta, Hafsat ta zama cikakkiyar budurwa amma babu ko mutum daya da ya taba zuwa da sunan yana sonta. Amma Nasreen sai dai idan ba a ganta ba, sai an ce “Tubarkallah masha Allah.” Wannan abu yana damun_ Hajiya Salma, shi ya sa ta yanke shawarar mayar da ita makauniya tun kafin wataran Haidar dinta ko Sultan din da kansa wani ya ce yana sonta. Idan Www.bankinhausanovels.com.ng  ta tuna hakan takan yi rantsuwa da sai ta batar da ita a duniyar gabadaya. Abba ya sami Kaninsa kasancewar shi ne babba a gidansu don haka suka zauna da Baba Sani ya yi masa bayanin tunaninsa da kuma hukuncin da ya yanke. Baba Sani, Anti Iyami, da kuma Hajiya Gwaggo duk suka yi na’am da wannan shawarar nasa. Suna zazzaune a falo, wayarsa ta yi Kara, ya daga yana murmushi. Haidar ya dubi Hafsat suka tabe baki, domin har sun gane idan har mahaifinsu yana fara’a to dan gaban goshinsa ne ya kira shi. Bayan sun gaisa ne, Sultan ya tambayi dukkan mutanen gida, daga bisani ya ce a baiwa Nasreen wayar. Abba ya Kwala mata kira, ta fito tana harba sanda, “Na’am Abbana gani nan zuwa.” Za ta fadi Abba ya Kwala kira, ‘“Nasreen kada ki fadi. Tsaya kawai in Karaso.” | Mamaki ya kama Sultan. Ya kasa gane me Abbansa yake nufi da kada ta fadi? Bai ce komai ba har lokacin da ya ji sassanyar muryarta tana kwarara masa Sallama. “Nasreen kina cikin “Www.bankinhausanovels.com.ng kuna cikin Koshin lafiya ko? Na ji Abba yana cewa kada ki fadi me ya sa za ki fadi?” Shiru ta yi_ ta rasa me za ta ce masa, sai kawai ta gaida shi, ta fara ba shi labarin Islamiyyarsu. Ya ce, “Yi min karatunku na jiya in ji.”  Nasreen ta gyara murya ta fara karatun da kaf dakin suka kafe ta da ido. Yadda take baiwa kowanne harafi hakkinsa ya isa ya sanya ka fi Kaunarta. Sultan da ke kwance ya sake mayar da kansa ya lumshe idanunsa, dama kansa wani irin ciwo yake yi masa ga gajiya ga shi yana son yin barci. Jin Kira’anta yasa ya sake samun natsuwa, yana lumshe idanunsa har barci ya yi awon gaba da shi. ‘ Nasreen tana saukewa ta shiga kiransa, “Dee.. Akwai gyara? Dee!” Ta cire wayar daga kunnensa, “Abbana duba ka gani ko ya kashe © wayar ne?” Abba ya karba yana sake duban Nasreen, ta burge shi Kwarai. Idan ya tuna rashin idanunta kuwa, sai ya ji kamar babu wanda ya kaishi zama cikin Kunci. Abba ya Kwalawa Nawfal - Www.bankinhausanovels.com.ng  kira, ya shigo da Sallamarsa, ya dube shi, ‘“‘Nawfal kama hannun Nasreen ku koma ciki.” Nasreen ta ta yi murmushi wanda gefen kumatunta suka lotsa ta ce, “A’a Abbana ni ma ina son in zauna a wurinku, ko ba zan iya kallo ba, zan ji sautin muryar talabijin din.” Abba yana sake al’ajabin Karfin tawakkali irin na Nasreen, kwata-kwata bata da damuwa da irin wannan jarabawa da Allah ya yi mata. Nawfal ya riKe mata sanda suka Karaso falon ta zauna a Kasa tana aikin murmushi. Tana jin nishadi ne a duk lokacin da ta tsinci muryar Sultan yana mata magana. Hafsat tana son yin tsaki tana tsoron Abbanta, don haka ta yi shiru kawai tana kallon Nasreen cike da haushi da tsana. Abba ya sake kiran Sultan ya rarumi wayar ya manna a kunne yana sake lumshe idanu. Abba ya ce, “SP tashi mu yi magana.” Babu musu Sultan ya tashi zaune tare da tattaro natsuwarsa ya zuba su a kan Abban. “Ina saurarenka Abba.” Sai da Alhaji Lukman ya saci kallon Hajiya Salma sannan ya ce, “Jiya na je gidan Hajiya Gwaggo, ka san mitarta kullum ba za ka Www.bankinhausanovels.com.ng yi aure ba? Sultan na zuba maka idanu inga iya gudun ruwanka sai dai baka da alamun raya sunnar manzon mu. Ga Kaninka nan shima har ya tasa. Hafsat kuwa ko yau miji ya fito za_ ta yi aurenta. Don haka kana babba kai ya kamata ka fara yin abu mai kyau wanda zai sa su yi koyi da kai. Na yi maka magana ko kana da yarinya amma sai kace min babu. Mahaifiyarka ta nuna min wata yarinyar Kawarta da suka so su hada aurenku, nayi irin nawa binciken ba za ku shirya da yarinyar ba. Na san abinda za ka iya zama da shi ka sami natsuwa, amma ba ‘yar Hajiya Ladidi ba. Don haka mun taru da ni da ‘yan’uwana mun yanke shawarar za ka auri yarinyar Alhaji Mamman da ke karatu a Rasha. Yarinyar tana da natsuwa da kamun kai. Na tabbata ba za ka yi da-na-sanin zabina ba. Za mu daura auren baka nan, amma kana dawowa za ka sami goron bikin zan adana maka koda kuwa ya bushe ne sai ka ci. Ina fatan amsar magana ta za ta kasance eh ne ba a’a ba?” Sultan da gabansa yake tsananta faduwa ya rasa me zai cewa mahaifinsa? Kawai ya tsinci bakinsa da furta, “Duk abinda ka yanke a kaina Www.bankinhausanovels.com.ng Abba dai-dai ne. Wannan ne amfanin haihuwar, idan har za ka iya sanya yaronka ya yi, za kuma ka iya hana shi ya hanu. Abba na kasa amincewa wata mace ne, a dalilin duk yawancin mata halayyarsu iri daya ce. Ka dubi duk irin zaman da kake da Umma, yau a kan taimako Umma ta watsar da lamarinmu, ta tsame ni daga cikin ‘yan’uwana, ta sa suna yi min kallon wani mugun mutum. Duk irin ilimin Umma da kuma girman tarbiyyar gidansu, amma Umma ta kasa karbar Kaddara. Abba abokin aikina Mahbub macen da take tsananin Kaunarsa taso ta kashe shi, abokina Ashrmnaaan matarsa ce take kawo masa maza a cikin gidansa, abokina Haisam, matarsa ce take aikata madigo a cikin dakin aurenta, dakin sunnah! Ba ta taba jin tsoron akwai ranar da Allah zai hukuntata ba. Abba ireiren wadannan matsalolin suna nan da yawan gaske, ta yadda idan ba rufe ido mutum zai yi ba, ba zai taba iya yin auren ba. Ina tsoron aure sosai Abba. Amma tunda ka amince nima na amince.” , Abba da ke aikin murmushi ya ce “Kowacce da irin halayyarta, zai yiwu Fatima Dan borno ce ta sa. jarumanta a hakan, ba lallai a www.bankinhausanovels.com.ng a same su da irin halin ba, idan ma ansamu za ka gaa yanzu haka sun shiryu, tun daga lokacin da ta furta Alhamdulillahi ta kammala. Daman haushin abun daya ne, mutum yana aikata kuskure ya kasa tuba ya koma ga Allah, irin wadannan mutanen su ake gudu a rayuwa. Amma duk wanda zai tuba irin tuban da Allah ke so, ai abin a gode wa Allah ne. Sunan yarinyar Fa’iza bayan daura auren zan sa ta kiraka ku gaisa.” Hajiya Salma ta mike a fusace ta tsaya masa a tsakiyar kai, “Wai Sultan dinne ka zauna da danginka suka bashi mata? In haifi yaro wasu su nuna min sun fi ni iko da shi? Me yasa a lokacin da zan haife shi baka kira danginka sun amshi nakudar da nayi ba? Ban yarda da wannan auren ba, dole zabina zai aura. Daman nasan kai kake sawa yaron nan yake raina ni.” Sultan yana sauraren hayaniyar mahaifiyarsa hakan yasa ya yi saurin kashewa ya rike kansa, “Ya rasa asalin dalilin da yasa bai yi na’am da wannan auren ba. Zuciyarsa tana gaya masa akwai wani abu da yake so amma kuma ya rasa menene? Www.bankinhausanovels.com.ng Nasreen ta duKar da kanta tana jin damuwa sosai. Ta fi danganta damuwarta da irin tijarar Umma. Shi kuwa Abba har ta gama maganarta bai ce mata komai ba. Dukkansu suka mike fuuu suka fice. Falon ya rage daga Abba sai su Nasreen. Ya dubi Nasreen ya _ ce, ‘“‘Nasreen ke ma zan iya aurar da ke a kowani irin lokaci.” Nasreen ta yi dariya har jerin haKoranta suka bayyana, “Abbana, duka-duka shekaruna sha shida a duniya. Ai ban isa aure ba, anti Hafsat ce ta isa aure da Yaya Haidar. Abbana na Kasa a yi auren Dee, sai mu koma gidansa da zama ko?” Abba ya ce, “Kwarai kuwa.” Nawfal ya ce, “Abba ni kuwa na isa aure ko?” Gaba daya suka yi dariya. Haka Abba ya zauna a cikin su suna ta hirar su. Idan ya tuna Sultan zai dawo ya sami Nasreen babu idanu, sal yaji damuwarsa ta ninku. , Yau juma’a a yau ne Abba ya shigo hannunsa dauke da goro yana aikin murmushi. Hajiya Salma tana zaune idanunta sun yi jazir saboda kuka. Ajiye mata goron ya yi ya shige ciki wajen Nasreen. Goron ya dan gutsura ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng Nasreen bude bakinki insa maki wani abu mai zaKin gaske a baki.” Babu musu ta bude bakin tana fara’a “Abbana har na Kosa ka sanya min.” Ta bude bakin ya sanya mata ballin goro. Ta rufe bakin tare da taunawa, “Abbana akwai zakin sosai. “ Ajiyar zuciya ya Kwace masa, - “Wannan goron na daurin auren Daddynki ne. Kiyi masa addu’a.” Murmushi ya _ wadaci zuciyarta zuwa fuskarta, “Allah ya basu zaman lafiya Abbana. Ka bani waya infara yi masa albishir.” Babu musu ya zaro wayarsa ya mika mata, bayan ya danna kiran Sultan. Muryarta yaji cikin sanyi tana magana, “Ina tayaka mura Dee, Allah ya kade fitina. Yanzu na ci goron daurin aurenka.” Sultan ya danyi jimm.. Alamun abin bai yi masa dadi ba, daga baya kuma ya ce, “Har andaura? Zan kawo maki tukuicin fara gaya min da kika yi. Allah ya yi maku albarka.” Sama-sama suke magana, wanda ta fahimci yana cikin damuwa, dole ta hakura da hirar suka yi Sallama. “Abbana sai naji kamar Daddyna baiyi farin ciki da wannan auren ba. Abba me yasa baka barshi ya nemi matarsa ba? Ka bani matarsa a waya ingaya mata matsayina na “yarsa don ta fara gyara mana dakina da na Nawfal tunda can zamu koma da zama. Abba ya ce, “Idan bai yi farin ciki a yanzu © ba, na tabbata akwai ranar da dole zai yi farin cikin. Akwai ranar da zai gode min. Matarsa kuma ki bari ta kusa gama karatunta ta dawo, da zarar ta kammala sai ayi bikin tarewarta.” Nasreen ta langwabar da kanta ta ce, “Haka Allah ke ikonsa. Na ci burin ganin irin matar da Dee zai aura. Ashe ba zan iya ganinta ba, sai dai in ji muryarta. Allah ya kawo mana ita lafiya.” Abba ya rage murya ya ce, “Insha Allahu ba zaki dauwama a hakan ba. Ki kwantar da hankalinki kinji? Ina jiran dawowar Sultan ne a shirya a fita da ke Kasar”waje Bata ce komai ba, sai duKar da kai da ta yi, hakan yasa Abba saurin ficewa yana girgiza kansa. Yana ficewa Nasreen ta sunkuyar da kanta ta kama kuka sosai. Furucin da Umma da su Hafsat suke jifansu da shi yana sanya ta cikin damuwa da tashin hankali. Tasha kwatanta tambayar Abba sai kuma ta fasa. Nawfal ya shigo ya dafa guiwowinta, “Nasreen menene? Me ya saki kuka a ranar daurin auren Daddy? Www.bankinhausanovels.com.ng mene ne ke damunki bai kamata kiyi kuka a irin wannan ranar ba.” Nasreen ta lalubi hannun Nawfal ta rike tsam. “Nawfal! Umma ce take ce min mu ‘ya’yan shegu ne, haihuwar Karkashin gada. Me hakan ke nufi Nawfal? Ko dai ba mu da alaka da gidan Abba ne? Idan bamu da alaKa me yasa muke diban kama musamman da Umma? Abin yana damuna.” Nawfal ya yi dariya, “Shi ne kike kuka? Mu ba shegu ba ne, Abba ya gaya min bata son mu ne kawai, ba wai don mun yi mata wani abu ba. Kuma mahaifinmu da mahaifiyarmu sun rasu ne a dalilin hatsari. Daddy shi ya yi ta kulawa da mu ya rene mu. Kuma ai ba mu kadai take yi wa hakan ba, hatta Daddy Sultan ba ta bar shi ba, kuma kin ga ita ta haife shi. Ki daina damuwa kin ji ‘yar uwata?”’ Ta gyada kanta kawai tana jin zuciyarta babu dadi. Karfe daya na dare, ya dawo gidan, a matuKar gajiye. Tsaye yake daga bakin tagar yana kallon yadda hadari ya hadu walKiya kawai ake yi. Idanunsa sun riga sun soye baya jin ko Www.bankinhausanovels.com.ng  alamun barci. Yana tsintar kansa a cikin nishadi da kuma tunanin abubuwa masu mahimmanci a cikin rayuwarsa, sai dai yau akasin hakanne kwance a zuciyarsa. Yana son mahaifinsa fiye da kowa, bai taba yi masa musu ba, haka baya son yadda ya nuna masa Kauna a lokaci guda ya watsa masa Kasa a idanu, yasan yin hakan zai jawo mutanen cikin gidan su suyi masa dariya. Ya kasa amincewa kansa wai shi ango ne, akwai igiyoyin wata a kansa. Bai taba kawowa kansa yin aure yanzu haka ba. Akwai matsayin da yake kwadayin hawa wanda idan yana da aure a yanzu, zai dinga kaucewa zuwa kwasa-kwasan nan na Karin girma, Nasreen! Zuciyarsa ta ambata da Karfin gaske. Ya rasa dalilin da kwana biyu yake yawan ganin yarinyar a cikin farkinsa tana neman taimakonsa. Gaba daya ya ji garin ya fice masa a rai. Gida kawai yake hange. Sannu a hankali ya fice daga cikin dakin ya tsaya a bakin Kofa yana kallon yadda ruwan saman ke zuba a hankali, Nawfal da Nasreen kadai yake hange. A irin lokacin nan ne Nasreen da ke kwance a Katon gadonta ta lume cikin bargo sal juye-juye take yi tana jin ciwon kan, yana sake Www.bankinhausanovels.com.ng  ratsa kanta. Duhun da take gani kadai a idanunta yana damunta, bare kuma wani Katon abu da yake tokare a Kirjinta wanda yaki wuce wa haka ta rasa menene. Da gaske take kewar Dee dinta, ta Kosa ta ganshi ya dawo. Bata Kaunar ci gaba da zama a tare da Umma ta Kosa matarsa ta tare, su koma gidansa. Tashi ta yi ta yaye bargon da ta rufa, ta dinga lalube har ta isa ga bandaki. Alwala ta yi ta dawo ta fara gabatar da nafifili. Ta jima tana yiwa Sultan addu’a kafin ta bude Qur’ani tana karanta Suratul Maryam cikin natsuwa da zakin muryarta. Da safe ta gama shirin zuwa Makaranta jikinta yafi na kullum yin sanyi, ta jiyo hayantya, hakan yasa ta yafito Nawfal ta ce su je falon. Nawfal ya kafe Umma da idanu da ta rike Abba tana kuka tana fadin sai ya saketa ta bar masa gidansa, ba za ta iya ba. Ya sa danta ya rainata, yanzu kuma saboda a nuna mata iyakanta aka yi masa aure. Ta nemi a gaya mata wacece matar idan da hali a nuna mata hotonta amma yaki kallonta, don haka ita za ta bar masa gidansa. Haidar ne ya shigo yana duban mahaifiyarsu shi da Hafsat suka Banbare hannunta da Kyar Abba ya samu yana KoKarin ficewa daga gidan yana fadi a ransa zai yi maganinta. Kawai suka ci karo da Alhaji Mu’azzam! Kallon kallo suka aikawa juna sannan Abba ya dawo da baya suka gaisa babu yabo babu fallasa. Alhaji Mu’azzam. ya gyara zaman babbar rigarsa ya ce, “Anya Alhaji Lukman babu abinda ke damunka? Me yasa kake son mayar da kanka Karamin yaro ne? wanda bashi da ra’ayin kansa? Ta ya ya za ka yi wa Sultan aure wanda mu nan da muke dangin mahaifiyarsa bamu sani ba? Ko kana nufin bamu da hakki akansa ne? Akan ‘ya’yan zina kake son Sauya tsarin gidanka? To idan aure babu albarkar uwa auren nan bai dauru ba.” Abba ya yi saurin bashi amsa, “A fatawarka ba! Amma ni ne uban yaro kuma na aurar da shi ga diyar da ta dace. Zina kuma babu mai tabbacin wane yana aikata zina, sai idan yana da shaidu, kawo shaidun kuma akwai wahala. Ina yiwa kowa kyakkyawan zato. Kowa a duniyar nan yana da tarin matsala akansa, idan baka zina, kana shan giya, idan baka shan giya kana caca, idan baka aikata dukkan laifukan nan kana aikata mummunar laifi wanda yafi muni, wato shirka, hada Allah da www.bankinhausanovels.com.ng  wani. Ban ga dalilin da za ka dinga bin diddigin wani dole sai ka gano laifinsa ba. Kowa ya ji da tarin matsalarsa. Hajiya Salma kuma ta bi bayanka zan zo da abinda take buKkata, matar Sultan kuma bata isa ta santa ba, har sai ta tare, bare ta zagaya ta kashe masa auren. Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.” Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.” HMM LABARI FA NATA DAUKAR ZAFI KOYA ZATA KAYA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...