NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Ban ga Alhaji ba, yau da wuri kenan shi ma ya fita”Kai tsaye Sa’a ta amsa,  “Eh, ya je kai kudin Auren Adamu, nan da dan lokaci ma zaki ga ya shigo, don ba nisa”.Zuciyar Salma ta kusa kwacewa ta Bare, amma dai ta yi Karfin halin tattaro ta cikin rashin azanci tana duban Sa’a,“Anti wanne Adamun wai? Sa’a ta san babu.abinda ke damun Salma sai tashin hankali. Don haka ta boye. tata damuwar ta amsa mata, “Adamunki, aure zai yi.zai auri budurwar da yake so, wadda ya bar karatu dominta, Hajiya da Alhaji sun yarda zasu aura masa ita don sunyi imanin bai fara sonta don ya daina ba”.Na shiga uku na lalace”. Cikin tausasawa Sa’a tace, “Ba ki shiga uku ba Salma, Aljanna kika shiga kika kasa fitowa. Ki bar su da ni suke maganar’
Gumi kawai Salma ke yarfewa yana Kara

ZAMU TASHI nuna Karfinsa a dukkan Kofofin jikinta. Sa’a ta dan tashi ta leka windo sannan ta dawo, . Bari Alhaji ya dawo mu fita, KakKarfan asiri za’’a yi wa Adamu wallahi, sai an makanta ' ja’iri zamu sami sauki”
Salma babu baka sai kunne. Halin da take ciki sai da ita kanta Sa’a ta yi danasanin kururuta mata lamarin kishiyar. A wuya ce Salma ta daga kai ta dubi Sa’a ta ce, Wai Anti kin ma gane yarinyar da zai aura?” Cikin azama Sa’a ta amsa, “Husna me dinki ce fa, wadda ta taba yi min dinki sunan Walidi”’. Nan da nan Salma ta kara shiga damuwa, Na tuno ta Anti, tabbas na taba ganinta tsaye tare da Adamu, in ba zan manta ba a ranar _ ne ma aikin boka ya shako shi, don a gabanta ya ce zai aure ni...Sa’a ta katse ta da cewa, “Ai na fada miki sun ce ya.jima yana sonta, amma kun yi hakan ma don ita mayya ce ta amince zata aure shi? Lallai ba ta san kishi da ke Www.bankinhausanovels.com.ng 
daidai yake shiga ramin kura ba”. .


Wannan maganar ta Sa’a ta dan sanyaya ran Salma, gani take ba Sa’a zata iya samo mata komai da take buKata a Adamu, zata iya hana shi aure za kuma ta iya sanyawa yayi ta son ta har bayan rai. .
Suna ta dan tattauna maganar har Alhaji ya dawo, bai san Salma na ciki ba ya shigo falon Sa’a yana cewa, Mun dawo, har an sanya rana wata guda”. .
Sa’a na murmushin yake tace,Allah sanya alheri yasa ayidamu”. Alhaji na ganin Salma sai yayi turus, ya dubi Sa’a cikin bata fuska, . a '“Yanzu don mugunta Sa’a shi ne kika kira ta takanas don ki fada mata, ina ruwanki da sabgar gidanta da ba zaki bari mijinta ya sanar da ita da kansa ba?” a Bai saurari cewarta ba ma ya juya ya fice - cikin fishi. . Ta bishi da sauri tana fadin ya saurari uzurinta, amma tuni ya fice ya bar ta nan tsaye, - don kofar gida ya dosa bai kuma saurara ba ya fice abinsa. Ta dawo wajen Salma wadda ta yi . mutuwar zaune tunda kunnenta ya jiye mata cewa an saka wa mijinta rana wata guda, wannan bala’I ne da sam ba ta da faffadan kan da zai tarye shi. ' A kufule Sa’a ta ce, Kin ga mutumin nan yau ya wani dauki . zafi kamar wata tukunyar Kasa, wallahi Husnan nan sai ta ci ubanta... don na ga alama har da ni ta kai wajen bokanta, gashi nan Alhaji na yi min abinda ba ya yi min, wai ni zan dinga bin sa ina bashi hakuri yake wani kumburi”. - Wannan karya gwiwar Salma ya Kara yi, ta ga kamar da gaske ne wajen bokan Husna ta kai su, kuma ba zasu kubuta ba idan ba -mayar mata raddi suka yi ba.
Cikin kuka da rashin hayyaci Salma ta mike tana saba mayafi, . “Anti zo mu tafi kawai, niko wanne irin tsafi ne-ma a yi mata, wallahi na daina shakkar komai don na kula lokacin da nake tausayi nake shakka sannan ni kuma ake son matsawa tawa. rayuwar . Ran Sa’a a Bace ta amsa, “Dole mu jira Alhaji ya shigo na nemi izini don kar laifin nawa yayi yawa’. Salma ta koma ta zauna jabar a Kasa tana ta faman yarfe gumi, zuciyarta na_ Kara cunkushewa. . Www.bankinhausanovels.com.ng 
Tun suna saka ran dawowar Alhaji har dare bai dawo ba, dole Salma ta yayi damuwarta ta tafi gida bayan ta gama nacin kiran Adamu a waya don ya zo ya dauke ta tana tarar da wayar a kashe. Tana zuwa gidan ta tarar da shi a bude, wannan ya ba ta tabbacin ya dawo, saboda haka ta shiga da azamarta tare da zummar ta sauke masa sha tara ta tsiya duk da tsiyar bata taba hada su ba. Yana kwance a falo cikin nishadi yana waya da Husna ya jiyo shigowarta, nan da nan  yayi sallama da Husna kuma ya tsiri baccin karya babu gaira babu dalili. -
Ko sallama Salma ba ta yi ba ta shiga  falon, abinda ya ji daci da mamaki kenan cikin ransa, sai dai shi ma ko motsi bai yi ba bare _tuhumar ba tayi sallamar ba. Wani matsiyacin haushi ya kara kumeta da -wannan baccin nasa na bayan isha kadan, ta zo kansa ta tsaya rai a bace tace, Yaya Adamu wai har ka kwanta bacci?Yayi bakam tamkar tana magana da dutse Ta sake daga murya,
“Yaya Adamu laftya da sauran maraice zaka hau bacci?”. Nan ma ba motsinsa, Nan ta Kara zuwa wuya, kawai sai ta ja wani dogon tsaki ta juya zata shige daki, me kuma ta tuna? Sai ta juya ta fara dukan kafarsa cikin zafin rai
Tun da ta yi masa tsakin nan ya Kufula, da yana da hali sai ya tashi ya bata mari ya kuma ce -° ta fita ta tafi inda ta fito, yana cikin wannan tafasar zuciyar ne Allah ya bashi sa’a ta dawo take dukan Kafarsa, da gayya yayi wani  KwakKwaran juyi a zuwan na bacci ne ya samu ya kirba mata naushi da Kafa. Hambarin nasa ya Zo mata a bazata, kamar kiftawar ido ta baje a wajen tana wani ihu. Shi kuma ya tashi zaune yana KikKifta ido da alamun farkawar daga bacci, sannan a sanyaye ya dubi_ inda take kwance tana kuka yace,Salma lafiya?”.
Ta yunkura da Kyar ta tashi zaune tana jin kamar kafadarta ta karye, don a Kirji yayi mata kutufo din, shiyasa ta ji kamar ana shirin zare mata rai. Da kyar ta ja jiki ta yi nesa da shi tana cewa, Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Adamu dan zaka yi aure shi ne nida baka so zaka kashe ni?”. Cikin rashin) nuna wa maganarta muhimmanci ya ce, “Au kar dai ke na kutufa Salma? Yi hakuri mafarkin Kwallon Kafa nake, wai an sanya ni
bugun daga kai sai Gola”.  Salma ta ji kamar ta tashi ta shake shi saboda haushi, ta haKikance Karya ya fada mata musamman saboda bai yi jimami ba duk da yana kallonta tana kuka, hasalima ko tasowa daga kan kujerar bai yi ba bare ya nemi goge mata hawaye . ya hana ta kuka, Muryarta narawa tace,
Na rantse da Allah kana sane ka buge ni, sona ka dena, shi ne don zaka yi aure zaka kashe ni.
Adamu cikin ransa ya ce, Ni dama ban taba sonki ba Salma. A fili kuma kawai sai yayi shiru yana kallonta.
Salma ta Kara Barewa da kuka. _Wato dama haka maganar take? Gashi nan ka yi shiru kana kallona ba ka musa ba. Adamu ba shi da wani kuzari ya amsa,
Au ke ma da kika zo da maganar har kike ci mata laya kokwanto kike? Sai ni da ban san hawa ba ban san sauka ba kike son na tabbatar miki, in kuma na yi shiru ke ki tabbatar min?. Ta katse kukanta cikin hasala ta ce masa, “Karya ake maka ba a kai maka kudin aure ba?”. “Haka kika tambaye ni an kai min kudin aure? Tambaya ta kika yi don an kai min kudin aure nake son kashe ki alhalin a mafarki na_ naushe ki ban sani ba”. Yana magana ne cikin sanyin jiki, kalaman’ da yake fitarwa ba masu ladabi ba ne a kunnen Salma, afilima sanyin jikinsa da sanyin muryarsa na nuna ladabin da ya hana tasiri, ta so ya canki daya tsiya ko arziki su yi ta, su yi ta ta Kare ta fito baro-baro ta hana shi auren. Yana dire maganarsa tace, Wallahi ban yardaba”, Ita ma tana direwa ya amsa, “Ni kuma ba zan rantse ba, bisa wacce hujjar zaki Ki yarda da abinda na fada”’. Salma ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi, kawai sai ta mike tsaye da Kyar tana tattaro Karfin halin duniyar nan, ta dubi tsabar idonsa ta ce, Www.bankinhausanovels.com.ng 
Kuma tsakani da Allah ko wata biyu da aure ban yi ba zaka yi min kishiya...” Ya katse ta cikin tausasa murya, Kafin na aure ki na fara sonta Salma, kuma yanzu sai in fasa?” Babu abinda ya zo ran Salma sai maganar Anti Sa’a da ta ce Hajiyan Adamu ta ce Adamu ya ce bai fara son Husna don ya daina ba. Ta ji tana shirin kai takarda saboda tsabar kishi da takaici. Kutse ta yi zuciyar Adamu ta shiga da Karfin tsiya, amma dalilin so ne ba dalilin son zuciya ba, don haka take jin dole ne kishinta ya bambanta da na ko wacce irin mace, kuma_ in ta bar wadda ya sa a zuciyarsa da karan kansa ta_ shigo gidan, to ita kuma za a wurga ta bayan . Zuciyar. Tsakaninta da Allah ta dubi tsabar idonsa ta ce, “To ni dai ban yarda ka auro kowa ba”.
Da a kusa da shi take babu abinda zai hana shi sake wani mafarkin ido biyun ya samu ya kirba mata wawan naushi a baki, in yaso ya ce sauro ya hango zai shigar mata baki ya kashe mata. To ta yi nisa da shi, amma ko kallon banza ba zai iya yi mata a gaske ba, don haka ya jima cikin shiru yana daddafe zuciyarsa yana tausarta abinda zata ce, wanda ba zai zafafawa Salma ba kuma ba zai bar ta ta ci da buguzum ba. Da kyar ya samo abin cewar,
“Ki yi hakuri ba zan iya fasa aurenta ba, na jima ina sonta so ba irin wanda kika saba sani ba”. Kawai sai ya sake kishingida a kujerar ya juya mata baya.
Cikin rashin hayyaci ta ce, “Shikenan, a yi auren mu gani”. Ba ta jira amsarsa ba ta wuce daki a fusace!. .
Shi dai bai tanka ba, ba kuma shi da niyyar tankawar, hasalima ko yatsansa bai motsa ba. . Zuciyarsa ce dai kawai take aiki, aikin son Husna da jin haushin wata kunduba tana jin isar zata iya - hana shi aurenta.

**************

Washe gari yana zuwa wajen sana’arsu ya sanar da Salmanu yadda suka yi -da Salma. Fuskar Salamanu ba ta nuna tsananin damuwa ba, amma a can filin zuciyarsa alwashin Salma yayi mugun kada shi, kuma yana da tabbacin in an sake zai iya yin tasiri. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Awa daya Salmanu na tunani bai iya tuno wata mafita ba, da kyar ya samo wata mai rauni wadda zata iya yi musu katanga ga sharrin Salma kafin su yitunani. Karfe goma daidai yayi kiran Adamu harabar gidan, suka bar Tanimu na dan kara shirya wajen. Adamu yau Salma ta tambaye ka fita?”.
Kai tsaye Adamu ya amsa, “Eh, wai zata gaida Gwaggonta”. Salmanu yayi saurin sanya hannu a aljihun rigar Adamu ya ciro wayarsa ya miKa masa,
“Ungo yi sauri ka kira ta ka ce kar ta je ko ina, zaka iya hakan?”. Gaskiyar magana Adamu ya ji ba zai iya ba, amma don kar Salmanu yayi ta yi masa gorin yana tsoron mace macen ma Salma, sai yayi Kundunbalar karbar wayar yana cika bakin cewa,
Wai me ka mayar da ni ne?”. ‘Salmanu ya Karfafa masa gwiwa da cewa,_Kamar tun da can yadda nake kallonka, wato gwarzon namiji mai tsayawa da Kafarsa”’. Zugar kuwa ta shiga Adamu da kyau,
musamman tunda ba kallon idon Salman yake ba. Salma tana KoKarin rufo Kofar dakinta kenan ta ji rurin kiran wayarta, ruri kuma na zabin da ta yi wa Adamu. Da kyar ta iya hakurin . Karasa rufe Kofar dakin ta ciro wayar a jaka, babu abinda take sa rai sai bata hakuri zai yi ya ce mata kuma ya fasa auren. Ta karaya sosai jiya da suka kwana baram baram, don daga - kwanciyar falon nan da yayi a nan ya kwana ko dosar cikin dakin baccin bai yi ba, da safe kuma yana dawowa Sallar asuba gari ya dan fara haske yayi wankansa ya fice, tambayarsa unguwar ma - §ai da ya zo yi mata sallama ta yi masa. Hannunta na karkarwa ta daga wayar, sai ‘ta ji muryarsa cikin cin magani, “Salma kin fita ne?”.
Gabanta yayi mummunan yankewa ya fadi, ji take kamar zai ce in kin je unguwar daga can ki zarce gida, don haka hankalinta ke neman Kwace mata da kyar ta tattaro shi, “A°a ban fita ba, yanzu dai na fito wanka”. Salmanu na gefe yana yi masa jinjina, wannan ne ya sanya shi Kara Bata murya ya ce, “To kar ki je ko ina, na fasa_ barin unguwar’. . Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin fargabar abinda hana ta fitar zai haifar mata ya biyo baya, kar ta fita ta je gidan bokanta? Abinda ba zai yiwu ba kenan. Ita ma ta dan bata rai ta ce, “Gaskiya Yaya Adamu A’a, har fa na yi waya da su gwaggo, suna nan suna ta shirya gangamin hidimar zuwana...”.
Dayake wayar Adamu na da Kara, Salmanu_. yana jiyo abinda Salma ke cewa, don haka yake ta yi wa Adamu inkiyar budewa Salma wuta, Adamu kuwa ya tunzuru, don haka ya iya tare. Salma da baKar magana, In don abincin da zasu shirya miki ne. wanda ba kya cin irinsa a nan gidan, idan na taso daga sabgata na biya gidan gwaggon na taho miki da shi, ai zasu ba ni ko?”. Mamaki da haushi ya Kara turniKe Salma, . bakinta na karkawa ta ce, “Gaskiya sai na je Yaya Adamu”.
Salmanu ya buga tsalle ya dire can gefe yana cewa, . .“Maca ce take fada maka haka Adamu?”.
Maganar Salma ba ta tunzura Adamu ba sai da Salmanu ya zuzuta ta, muryarsa na sarKewa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...