NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Ya katse ta saboda ya ji tausayin da yake mata ya nunku, da gaske Husna tana son Adamu tana son ya zo wajenta shi kuma gashi ~ can ya tafi gurin ‘yar fashi da makamin soyayya watakila ma ba zai tuna da itaba bare’ - rainin hankalin da ‘yayi mata a_ takarda. Salmanu ya daddage dai yayi mata Karya.

“Sabga ce ta tare shi, kin san yana dan koyarwa a wata makarnta mai.zaman kanta, jiya da shekaran jiya yayi fashi don haka yau ~ ~ aka ki lamince masa dole ya wuce bayan ya bani saKon amsarki, amma dai yau da dare ya ~ ce zai Bullo. Husna na bayyana kunya amma murna na yin gaba da kunyar tata. Cike da farin ciki tace, “Babu laifi Allah ya kai mu”
Salmanu ya zaro wasiKar daga aljihu ya mika mata, wasiKar tun daga matunshinta ta nuna da yaren da aka rubutota.

Husna ta karba cikin mamaki tana godewa, amma dai bata yi nauyin baki ba tabi ba’asi tana ta faman juya gaba da bayan wasiKar, ,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Anya wannan tawa ce kuwa”’ Salmanu yayi fuska, .. “Taki ce mana, me kika gani?” _ _ Tanuna masa rubutun bayan enbilop din, - '. “Ka ga rubutun da ya sa ni zaton ba tawa bace” Salmanu ya basar yana yarfe hannu alamar ko in kula,; “Au ba kya jin wannan yaren?” - .’_. Husna ta shiga nazarinsa don ta gane da gaske yake ko da wasa? Alamunsa ya nuna da _ gaske yake saboda haka ta kada kai, “Ban da a fim: ni ko wanda ya taba jin yaren ban gani ba...” Yatare tadasauri, . “A’a da wasa kike” Ta kada kai tana dariya,. - Me yasa zan maka wasa? Wallahi.da - . ' gaske nake, in kai ka taba ganin mai iya yaren = sai ka bani labari”’ _Salmanu ya sake yin fuska, babu ta yanda zaka dube shi ka zaci Karya yake shirgawa, _

ZAMU TASHI 


“To ai Adamu yaren da ya fi ji kenan fiye . ma da turanci, shi ma yake koyarwa a makarantar”  Ba Karamin girgiza da jin wannan almarat Husna ta yi ba, ta ji mamaki taji, kuma - Adamu ya Kara shiga ranta da birge ta, sai juya wasikar take tana kallo tana karawa. A Karshe ta buge da kallon Salmanu cikin murmushi, “Ya ji dadinsa wallahi” SO Ta zarce da dariya cikin kallon wasiKar, : *’Amma ban da abinsa ai yakamata ya _ fara sanin idan ina jin yaren, ni ko bindiga za a _, dora min ai ba zan iya kawo kalma daya a nan ba’. . ' “Kamar dai yadda kika rubuta masa yaren’ dakike Salmanu ya fada cikin ransa, amma ya kawar da fuska yanabasarwa,  __., “Haba kar ki ba da mata don Allah, ki... daure ki buda ba zaki rasa abinda zaki gane ba” Ya fara duban agogo yana alamar haramar_tafiya. So . Husna ba don ta so ba ta kasa musawa, sai don kar ta bayar da matan kuma kar ta cigaba

Www.bankinhausanovels.com.ng da rike shi musamman da alamunsa suka nuna yana son ya kauce, dole ta rausaya kai ta ce, : .. “To babu laifi, Na gode ka gaisar min shi” Ya yi gaba yana yana cewa, “In sha Allah”

**********

Maimakon Adamu ya dauki-hanyar fadar — bokancinsu, kawai sai ya gan. shi a hanyar gida. Zuciyarsa ta fara. rabuwa biyu ko ma fiye,

- neman_ dalilan yin abinda yayi, nadamar — abinda yayi da kuma shakkun in ma shi din  yayi. - , - .

Wai shi ne ya karkace baki ya ce a aura . masa Salma? Wai shi ne. ya zabi Salma ya watsar da Salmanu kuma ya kware masa baya ya goyi bayan aka aibata shi alhalin har ga  Allah ya san zuciyarsa ta fi son Salmanu akan Salma, ta fi amincewa Salmanu akan Salma?

_ A yanzu ya fara jin lallai ma kawai — Sharri aka yi wa Salmanu bai aikata abinda ya aikata ba, suna zargin Salmanu da shaye-shaye, . tabbas su ne mashayan, domin yana da yaKinin "

Www.bankinhausanovels.com.ng wata hodar suka busa masa har ya zauna aka saki wadannan sina-sinan da shi a matsayin rayuwarsa ta zabiri, amma an ci Karya an kwana da yunwa ace cikin hankalinsa yace a‘ aura masa Salma, don ma wani tsabar iya dialogue har da fadin da gaggawa.

Duk da yana cikin matsawa zuciyarsa da kwanyarsa mayar da abinda ya faru din, har yanzu kansa a rude yake, sai dai yana Kala wa zargin hodar mayen da suka busa masa ce bata sake shi ba, sai ma ya ji kan ya rude da ciwo, ba zuciyar tasa kawai da take zogi ba.

A daddafe ya isa gida idanuwansa na zagi ya bude dakinsa ya fada katifa ya runtse ido, —babu abinda yake hangowa sai lokacin da Alh. ke masa tayin auren Salma shi kuma yana amsawa cikin murya da karsashi har ma yana jefawa shegiyar Salma kallon so wanda sam bata cancance shi ba, don dai kawai tayi masa fashinsa ne.

Ya jima cikin mawuyacin hali sannan wani. mawuyacin bacci ya silalo ya sure shi

_ dauke da mafarkai marasa dadin ji da gani,—

Www.bankinhausanovels.com.ng

saboda haka da ya farka hankalinsa sai ya Kara. tashi. ;

Dayake Allah yayi masa arahar kuka kawai sai ya ganshi zaune yana ta sharbar hawaye. Zuciyarsa kuma ta fara jin abinda ke — faruwa da shi cuta ce ba Kaddarar haka kawai ba, lallai kyautuwa ne ya je neman magani in ba haka ba yayi mutuwar tsaye.

' Yana nan zaune yana sharbar hawaye da jin lallai wani shaidani ne ya hau kan zuciyarsa yake sarrafa masa ita ba shi ne da kansa ba. Kawai sai ga kiran Salma ya shigo wayarsa, kamar yadda ya gama hasashen kuwa sai ya ji -

. tilashin bashi da abu mafi soyuwa irin daga wayar, jikinsa na bari ya daga yayi mata Magana a ladabce muryasa har sarKewa ta ke,

“Ranki ya dade me ya faru, ko wani

kiran ne”

Daga can bangaren a yangace Salma ta

amsa, ,

“Kai haba dai wani kiran, yanzu kana ina Ya sami kansa da jin sheKa mata Karya,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Ina hanyar gidansu Salmanu in je mu kwashi ‘yan kallo” _ _ Ran Salma yayi fari tas! A yangance ta sake cewa, “Kai Adamu wai dambe zaka yi da shi ne?” Ya sake amsawa cikin Barinjiki, = -. “Sai in yi abinda ya fi dambe da shi mana — - Salma, ke fa ya taba! Yau ni na taba jin irin _ wanna ta’addanci ma? Don kawai ina sonki sai abin ya tsaya masa a rai? Ai kin ga dole ma na bi ba’asi in yake sonki na ji dalili....” Salma ta katse shi cikin dariya, “Kai haba! Allah ya tsari gatari da sara shuka, ni me zan da shi?” me, Muryar Adamu ta nuna tsabar jin dadinta_ - ga kalaman Salma, cike da zumudiyace; Ai kin ga dole na je na fada masa hakan, * in ma sonki ya dauka ba sai ya sauke ba...’ - Salma ta tare, “Eh haka ne kuma, amma dai kar ka yarda - ka yi fada da shi, ka san dan ganye ne, zai.iya Burma maka wuka na shiga uku.,.. kawai dai ka ja masa kunne ya fita harka ta, kai ma kuma

Www.bankinhausanovels.com.ng ka fita harkarsa, ba kai ba shi, in so. samu ne ma ko hanyar da ya bi kar ka bi..... ni fa ko ya baka hakuri kun shirya in mun yi aure kar ka sake ka kawo min shi gidana.....” :

. . Ya tare ta cikin yanayin bin umagni da nuna gamsuwa,

“Ni ma yaushe zan yarda da hakurinsa na

_ shirya da shi’ bare har na kawo miki shi

gidanki? Ai tunda ba kya son ganin Salmanu ni kuma zan mutu wajen hana ki ganinsa’

Ta yi wata “Yar shewar farin ciki a

_ shagwabe, .“Na san zaka iya Adamu, komai ka dauka kai Jarumi ne a cikinsa”’ -
Ya ji matukar dadin yabon da tayi masa, cike da fara’a ya ce mata,

“Ni jaruminki ne kawai Salma ba jarumin kowa ba, zan iya sadaukar miki da rai, ba zan iya sadaukarwa da kowa ba...”

- Kawai sai Salma ta ji wani zazzafan ~

" hawayen tausayinsu ya ciko mata idanuwa, wai Adamu ne ke sakar mata irin wadannan zafafan —

. kalaman soyayyar ba cikin hayyaci ba? Ta ji tausayin wannan dolen soyayya da tayi masa,

Www.bankinhausanovels.com.ng sannan ta ji tausayin kanta da bata cancanci Adamu ya so taba sai ta gusar masa da hankali.. ‘

- “Na gode Adamu’ -

Ta sami kanta da fada cikin raunin muryar . da ta bayyana kukan da take. Nan kuma hankalin Adamu ya tashi, ya  shiga tambayarta, . “Na bata miki rai ko? Ban san Maganata zata bata miki rai ba, don Allah ki yi hakuri ki * yafe min” . . . ' Da sauri Salma ta katse shi tanararrashi, - —~ “Ni ma jarumarka ce Adamu, ba zaka Bata - min rai ba, hawayen farin ciki' nake da jin kamar a mafarki, wai ni kake so haka Adamu?” A dokance ya amsa, So “Ki bar shakku Salma, ina sonki kuma ba zan fasa ba har mutuwata” a Farin ciki ya fara korar hawayen da take, tana gogewa tana amsa masa, ” “Ni ma haka Adamu. Yanzu yaushe zaka zo?” ,. Ya amsa, : . . “Ko yanzu kika ce nataho” : .

Www.bankinhausanovels.com.ng Da sauri ta girgiza kai,

“Ai ba zan so abinda zai wahalar da kai ba, yanzu ka bar gidan kuma na ce ka dawo, ka

. bari da dare ka zo” , Ya ce, .
“Allah ya kai mu, In sha Allahu da wuri * zaki gan ni” .

Ba don ta so su bar hirar ba sai dan kudi wayarta sun Kare, ta yi masa sallama suka rabu dukkansu suna nuna begen juna. — Salma ta sauke waya tana farin ciki.

Adamu ya sauke tasa .zuciyarsa na

_ Kuntacewa, maimakon ya rafsa kuka kamar yadda ya so, kawai sai ya fasa ya hau binciken . wani ruwan madubi da ba shi da amfani a — wajensa sai idan zai yi gyara fuska. Ya shiga duban kansa a madubin tamkar yana tantamar in shi ne Adamu dan Hajia. Bai iya barin abin a zuciyarsaba sai da ya fito fili ya hau . tambayar dodon madubin da muryar tausayi,

“Don Allah fada min gaskiya kai ne Adamu? In ka ce min kai ne, na rantse da Ubangijin day la Kage ni ka zama mugun makaryaci, Adamu ba wawa ba ne, Adamu.ba

Www.bankinhausanovels.com.ng soko ba ne, -Adamu ba Salma yake so ba, Adamu Salma bata isa ya so ta ba....... duk ‘abinda ya jaza wa Adamu zama soko yanzu Allah ya isan sa bai yafe ba!” . .

Bai tsaya a nan ba sai da ya zauna

musamman ya hau turawa Salma iyayen ashar, ba ita ba hatta Alhajinsa ya sha zagi shi da ; Salma, sai kuma da ya gama zagin.ne sannan

ya fara kuka ya hau fadin,

*“Wallahi dama na fada, na haukace, na san na haukace dole sai an yi min Rukiyya ko kuma Girka. Wayyo Na shiga aljanna na kasa fita”

Yana ta faman wannan Samabatun Salmanu da ya gaji da jira ya biyo sawu ta waya, dama ga dokin ya bashi labarin yadda suka yi da Husna ya dame shi, ga kuma aiki

_ yayi musu kaca-kaca har ma suna sa ran fara samun kostoma daga farkon sati. _ Ya gintse murya ya ce masa,

“Wai har yanzu wannan~ kundubar yarinyar bata bar ka ka taho ba ne?”

. “Haukana ne yatashi Salmanu” . .

Www.bankinhausanovels.com.ng Adamu ya amsa cikin rarraunar murya mai ‘son fashewa da kuka. Salmanu ya dauke wuta,cikin rashin abin cewa. - “Shiyasa na so ka raka ni Salmanu, na san - in kana nan komai zai iya zuwa da sauKi, Kila : _ ma ba zasu sami damar busa min hodar da suka - busa min haukan nawa ya tashi ba” . - * Salmanu yayi ta maza ya samo abin cewa,.“Yanzu kanaina?” . .“Ina gida” . ,

Adamu ya amsa. A tausashe Salmanu yace, sTo ka taho nan Zawaciki mu hadu” -
“In.zan iya ko?”  Adamu ya fada a raunane.- Salmanu yace,, Ai daurewa zaka yi, in ka zo din zamu

_tattauna dukkan abin yi, kar ka damu Adamu,_ in dai ina raye sai inda Karfina ya Kare a nemar wa zuciyarka da gangar jikinka Salama, ban taba alkawari irin wannan ba sai a kanka, bani « da gatan da ya fika, ba ni da: wanda ya Ki watsar da ni saboda yadda na sami rayuwa sai

Www.bankinhausanovels.com.ng kai don haka nake jin rayuwata tamkar an ‘samar da ita ne domin in yi maka hidima in -samar maka farin ciki.. ka zo kawai, ina jiranka nan da rabin awa”  Ya sauke wayar ba tare da ya jira cewarsa ba. . Adamu ya ji farin ciki da nutsuwa a maganganun Salmanu, ko bai samar masa mafitar da yake lissafi ba, ‘tabbas yayi masa - ' abinda ake cewa zoka ci tuwo yafi tuwon dadi. © Da Karamin kuzarinsa ya shirya ya dauki hanyar Zawaciki. — Ba Karamin girgiza Salamanu yayi da jin labarin da Adamu ya bashi ba, wanda bai rage masa komai ba tun daga kan kashedin raba sun” - da aka yi masa da kuma maganar aurensa da. Salma da ake shirin yi nan kusa har ma da wayar da suka yi da Salma daga baya. ~ Salmanu ya sake gasKata zaton da yayi wa Salma na cewa sihiri suka yi wa Adamu, ya. fito fili kama ya shaida masa cewa tabbas shi ya tare Salma yayi mata abinda ta fada ya kuma fadi dalilinsa na yin abinda yayi, ya Kare da cewa, ;

Www.bankinhausanovels.com.ng “Ko a jikinka yakamata ka ji sauyi, in ba rami babu abinda zai kawo rami. Ko Husa da kake so da gaske don Allah kana yi mata barin ~ jikin da kake wa Salma idan ka ganta?” , Adamu babu bakin Magana sai kallo. oo Salmanu ya dora, So “In mun nutsu dole mu karya asirin da suka yi maka, ni ban yarda abinda ke faruwa _ _ daga Allah ba ne” . ‘Adamu yayi kasaKe kamar ba zai tanka ba, amma cikin yanayin Kuluwa sai ya kada kai,. “Ka zauna kai ka nutsu, ni kuma zan san abin yi”  Salmanu ya. dan yi nazarin Adamu da kyau, sannan ya nisa yace, , ' “Babu laifi, amma dai duk abinda zaka yi © - ° kar na ji ka a wajen Malam-Na-Allah, don na san kai duk duniyar nan ba ka da malamin da ka amincewa kamarsa” ' . Haushi ya cika Adamu, amma dai bai. ' tankaba. ~~ - . Shirun da ya yayi ya tabbatarwa da‘Salmanu wajen nasa zai je in dai har.zuwan da -

Www.bankinhausanovels.com.ng gaske ne, dole ya shiga tunanin hanyar da zai tankwabe shi. .

Da KoKarin tunanin mafitar ya basar da shi,

“Ka zo mu yi katangar nan ta cikin daki, yakamata mu kammala duk wani gyara kafin
mu fara aiki”

Bai jira cewarsa ba ya bar falon zuwa cikin tafkeken dakin ya hadu da samarin da suka gayyato taya su aiki.

Adamu ba shi da zabi, dole ya watsar da tunani da damuwa ya bi Salmanu, don yana jin in bai yi wasa ba haukan nan dab yake da fara sanya shi zabura. Sai dai fa ya Kudure a ransa_ dole ne da yamma ya halarci gurin Malam-NaAllah. :

Salmanu ma ya kudure a ransa, duk runtsi ba zai sake Adamu ya kubuce ya je gurin Salma kamar yadda yayi mata alkawari ba, saboda haka ya dinga kaffa-kaffa da shi bayan ya sace wayarsa ya kashe. Daga bisani ma sai yayi masa dabarar cewa shi zai raka shi wajen Malam-Na-Allah su kai masa kuka.
Www.bankinhausanovels.com.ng

Haka kuwa aka yi, Karfe shidda na yammacin Ranar suka kwashi jiki suka tafi Warure. Komai a gaban Salmanu aka yi, abin mamaki Adamu bai kawo maganar Salma ba sai ya kawo maganar neman kudinsa da neman dafa’1.

. Malam kuwa ya sake danKara masa wurudi mai zafi,  kuma ya sanar da shi a yau ba . gobe ba in yayi wurudin Aljanin kudin zai zo —

. masa ya nemi buKatarsa. Salmanu da kansa ya zube wa Malam-_~ - sadaka suka fice, a nan ne ya tambayi — Salmanau, _ “Mun yi da kai zaka kawo matsalar Salma da Husna, me yasa ka kawo zancen kudi wanda muka kamo hanyar samunsu?”

Cikin yanayin tabbaci Adamu ya kada kai,

“Tun da sanyin la’asar ya busa na dena jin " matsalar Salma a matsala, har wacece ita da - zan aura dole? Na ga shegen da zai aura min. ita” Salmanu ya kada kai cikin jin dariya. . -amma ya hadiye, ya ce.masa, , .To Husna fa?” :

Www.bankinhausanovels.com.ng Nan ma cikn.yakini Adamu ya amsa,

“Ban taba cire yaKinin bazan auri Husna ba, ina jin kuma na fada maka dalilin”

Salmanu ya kawar da kai kamar  acikinsa, -

“Ai shikenan, ka je kayi wurudin nemankudi ka kira aljan, in naga ka samu kuma ka
wuce lafiya sai nima na bi hanya ka dan kar ka canja ni daga zama aboki idan kayi Kudin” salmanu Ya Kare zancensa cikin dariya,  Adamu ma ya dara. Salmanu ya sake cewa, —- . “Ka san abinda za’ayi?”  Adamu ya girgizakai. ” Salmanu yace, —“Don ma kar Salma ta biyo ka gida ta sammace ka ka zo mu je gidanmu mu kwana° Da sauri Adamu ya dube shi' , “Wanne gidan naku?” - Wajen sana’armu nake nufi, ka ga  dare kai kana wurudin neman kudi ni kuma ina yi mana na neman tsari da ‘yan sa ido, koda yake babu ma wanda yasa cewa
ta silar sana’ar taka zamu samu kudin da wurudin naka ya samar” Adamu ya dan yi jimami kafin ya amince, ya ce, “Ni fadan Hajiyanake tsoro”  Salmanu ya shiga rarrashi, , , “Kar ka damu, ka san mu da dabara dole zamu san Karyar da zamu Kirkiro mata” : Da wannan Adamu ya yarda suka koma Zawaciki,

. Kafin su isa magariba ta Karato. Adamu ya — tsaya masallaci, Salmanu kuma ya wuce gida a guje ya fara shirin zama aljanin Adamu na  tsakar dare domin katange shi daga masifar da _ yake shirin jefa kansa. .

*************

- Salmanu ya tanadi fararen kaya da farin ~ bokitin fenti mai murfi, hade da fararen rawani

- ya hada biyar guri daya sannan ya zauna ya nada wa bokitin fentin nan rawani tamkar wani _ jibgegen kan ifritu,. yayi masa .Karamin _. masakali yadda zai hau kansa kai tsaye yaHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...