NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Adamu ba shi da amsa sai wani hawayen, amma dai kaso tamanin cikin dari zuciyarsa ta

rage nauyi don ya sami tabbacin dari bisa dari Husna na yi masa irin son da yayi ta fata daga gareta... sauran nasa ne, kuma in ma ya rasa ta yana da tabbacin daga gareshi za’a sami akasin wanda baya fata. ,

Yanzu zuciyar Husna ce ke raunane wadda take jin duk inda adalci yake to ba ta yi wa soyayya shi ba, tunda ta shiga zuciyar masoyinta Adamu da Karfin asiri ta sa ta abinda ba ta yi niyya ba Www.bankinhausanovels.com.ng 
Amma dai duk da haka sun bar komai sun _ ji da soyayyar, sun bata haKinta da suka hanata. ~* a tsawon kusan wata biyu na zantar da juna. abinda ke cikunansu, kalamai masu sauki da

_ laushi a zuci da kunne sannan masu Kara mutunta

soyayyar tasu kowa ya kai Kwarya ana biyo shi da ramuwa.

Daga Karshe dai da Kyar suka shirya rabuwa lokacin da ake kiran sallar magariba, Adamu ya tattaro mata dukkan kudi aljihunsa wanda suka haure dubu ashirin ya mika mata.

Husna ta karba ta shiga juya su tana Kare musu kallo tamkar tana tantamar in na gaske ne har sai da Adamu ya tsargu, amma tsakaninsa da Allah yayi magana, Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Ki yi haKuri babu. kudi sosai tare da ni... ’ Ta tare shi cikin Kwalla da mamaki, “Me kake cewa Adamu?”, Kallonta yake kawai. Ta mika masa kudin tana girgiza kai. “Ba zan karba ba, wannan kudin fa sun isa ka kawo gidanmu a matsayin kudin aure, ni babu wani farin ciki da zasu bani fiye da wannan, don - ba ni da tabbacin in ka tafi abinda ya fi zuciyarka jarumta ba zai sake hana ka na ga ko kyallin ; . fuskarka...ba”. Ya tare ta a raunane, “Kar ki ce haka, kwana nawa to kika ba ni, _ ko kwana nawa kika dibar min zan_ cika alKawarin ki ga waliyyaina a gidanku”. ; Da sauri ta miKa masa kudin tana cewa, , “Sati daya”. Yana dariya ya ce mata, . “Ba za’a ga garajenmu ba?”. - “Kanmu yakamata mu duba ko wasu?”. _ Da sauri ya kada kai,

************

Duk da Salmanu a dokance yake da jin

ZAMU TASHI 

yadda Adamu suka yi da Husna ko dan sanin makamar da zai kama idan Husna ta zo yau, ya  rasa da madafar da zai tambayi Adamun yadda - suka yi. .

. Sannan ya shiga tararradin yaushe Husnan zata zo? .Kar a yi Garwa ta zo ta tarar da Adamu, gashi ya rasa da hikimar da zai kori Adamu

- -wunin ranar. a Wannan dalilin ya sanya ya dinga kasa . hankalinsa sama da yadda zai samar da nutsuwar yin aikinsu yadda yakamata. . Sai yau HONORABLE ya zo, Tanimu da Adamu kansu sai da suka gane cewa Salmanu ba shi da - nutsuwa; tun a wajEn gwajin damfarar da za’a yi wa Honorable, sai da ya sha gwaji ya kai sau goma kafin a samu Salmanu yayi yadda _ - yakamata. . Karfe uku da kwata Honorable ya sami _ Karasowa, ya sami boka Salmanu tirgijijn kamar yadda aka sha ba shi labari, komai babu sauki sai ka ce hararar abu kawai zai yi ya samar da shi. Hankalin Honrable kwance ya fara karanto - buKatarsa, “Ranka ya dade a duba min, kujeru biyu na ‘hararo domin darewa kan daya, ta farko kujerar

wakilci_ a majalisar tarayya, sai kuma ta biyu kujErar Gwamna amma ta zabe na gaba, yadda abin yake shi ne, gaskiya Ubangidan sIyasata, Www.bankinhausanovels.com.ng

mugu ne, shi burinsa duk kujerar da yazo hannuna na dare to duk abinda zai shigo aljihuna idonsa na kai, don haka nake son ware tafiyata na

yi ni kadai, wakilcin ko takarar gwamna ko da ta neman suna in yaso zabe mai zuwa na shigo da Karfina, yan zaben fidda gwani za’a yi wato  cikin gida, shi ne na zo neman sa’a wajenka.”” Dayake bayanin Honorable ya dan yi . tsawo kuma hankalin Salmanu na can ga Husna ya dan sanya shi inda-inda har Karshe dai ya ce, . Mema ka ce?”,

Sai kawai Honorable ya tsaya yana kallon Salmanu, hakan ne kuma ya sanya shi dawowa _ hankalinsa, yayi firgigita ya matse, dayake kuma ya tsinci batun cewa Honorable yana son bashi zabi ne, sai kawai ya sanya hannu ya dumbuzo wasu Kananan AlKami guda takwas yana nuna  wa Honorable, “Jam’iyyu nawa zasu tsaya takarar Gwamna a jihar nan?”, - SO . Da sauri Honorable ya amsa,  “Takwas ne... . ~ Kafin ya rufe baki Salmanu ya tare shi da cowa, “To Kirga mana alKaluman nan mu gani’.

Jikin Honorable na bari ya Kirga Alkaluma sai ya tarar da guda takwas, ya daga kai ya dubi Salmanu baki na rawa ya ce,

“Takwas ne...”.

Salmanu bai ce komai ba ya _ watsa ya alkaluma a ruwan da ke wata Katotuwar Kwarya, nan take sai gashi ko wanne alKalami ya tashi daga fari ya koma mai launukan dake Kunshe da . ; ko wacce jam’iyya daya bayan daya, ma’ana ko Www.bankinhausanovels.com.ng

. wanne alKalami daya ya zama mai wakiltar

jam’iyya daya. Duk cikin abinda bai gaza

_ Sakanni ashirin ba ‘sai ga alkaluma bakwai sun nutse a Kasa sun bar daya na shawagi a sama.

Da Honorable ya Kurawa alKalamin nan da

' ke shan sharafinsa a saman ruwa sai ya gane shi yake wakiltar jam’iyyarsa ta MML, da sauri ya — kai ganinsa ga Boka Salmanu yana yi masa duban rashin fahimta fuskarsa a hargitse

Cikin karsashi Salmanu da ya. gama fahimtarsa ya amsa masa, ' “Ka gan ka fa ranka ya dade, ka tattake .

kowa amma kana kira wa kanka asara”.Har yanzu jikin Honorable bari yake, tsakaninsa da Allah ya ce, “Ban gane wannan lissafin ba malam, a. taimaka min a fito da ni duhu”. Kai tsaye babu wani alamun_ shakku Salmanu yace “Mulkin nan fa naka ne, muna ture wasu — yan kanana tsuntsaye zaka dare abinka, ba zaka - sauka daga kan wannan kujerar ba sai ka sami __wadda ta fita...”na “Kujerar Shugaban Kasa ko Malam?: Na dade ina harararta...” : _Honorable ya fada cikin zumudi. “Gaskiyar maganar kenan, matsalarka daya kana da magauta dole sai ka tashi tsaye a kansu komai zai zo cikin sauki, amma da alama sun shirya ayi faduwar guzuma a tsakaninku, takanas_wani a cikinsu ya bar Nigeria don ya hana ka cimma nasarar da jininka ne ke tare da ita...” Honorable tsakaninsa da Allah ya tare Salmanu fuskarsa cikin damuwa, “A shiga tsakanina da su Boka, a daidaita - tasu nasarar kar a basu abinda suke nema...”. Shi ma salmanu ya tare shi,

‘Ai an gama, amma akwai sharuda”.

Jikin Honorable a sanyaye ya zura wa Salmnu ido kawai, . Kai tsaye Salmanu ya shiga karanto masa sharadin,

“Za ka Kauracewa sanya ko wanne irin turare sai wanda muka ba ka a nan, idan kana da — wani nau’in turaren da kake sanyawa ma kake jin - dadinsa to ka dinga kawo shi nan muna aiki a kansa, ina tabbatar maka zaka zama a ido da zuciyar mutane wani mai muhimmanci tamkar iskar da suke shaka...”.dan

-“Wannan ai ba sharadi bane Malam, yi min gyaran hanya ne to an gama”.Salmanu yayi fuska yace
To sai ka ajiye abinda ke aljihunka ka tashi ka tafi”

Honorable na kokawar tattaro  dukkan kudaden aljihunsa Salmanu ya faki ido ya danko wasu nannadaddun takardu guda biyu sannan yayi wa aljani Adamu Inkiya. Www.bankinhausanovels.com.ng

Ba zato ba isammani Honorable ya ji an kurma ihu kamar za’a tsaga dakin, kafin ya dawo hayyacinsa an fara sakin nishi a wahalce, nan da

_ nan tsananin razana ta bayyana a idonsa, ya shiga

kama kansa yana hangen ta Kofar da zai bi ya

arce ko da zata baci, duk da dai nishi yake ji bai

san daga inda yake tasowa ba, sannan daga jin

nishin ba daga bil adama yake tasowa ba, can ya

ji wata hakaKiyar murya na cewa, “iyakar wuya na sha ta a wajen hidimarka

Honorable, da kyar ma in zan rayu...”.

- A firgice Salmanu ya ce, Me ya same ka KusKundiyana?”.

. Cikin kuka-kuka nishi-nishi Adamu ya ce, “Ina wucewa ta. na ga Dr Abaji

«+ gaban Masu bautar shaidan suna cinikin jinin Honorable, da jininsa zaa haliccin nasu mulkin...

“ tir da su makiya Allah, ni musulmi ne ban yarda da zalinci ko salwantar da rai ba, amma ba na .

- yafewa azzalimai, mun fafata da maridan aljanu . na hana afkuwar hakan, da kyar na kwaci kaina bayan na sato muku Dr.Abaji da dan - rakiyarsa...”.
Tun daga Kwaryar kan Honorable wani kidan razanarwa ya taso har yatsan kafarsa, ya tabbatar a cikin cikinsa ma wato kayan cikinsa bikin da suke kenan, dole dukkan hankali da nutsuwarsa suka bar shi. - Www.bankinhausanovels.com.ng

. Salmanu da azababbiyar fuskar jimami, ~

Adamu kuma na can yana nishi, sai can cikin wahalalliyar murya yace

“Hnorable dunkule hannunka in danka maka maKiyanka ka Kone su da hannunka, ba zasu Kara wani tasiri ba sai abinda ka zaba musu”. . .

Adamu bai rufe baki ba sai da ya zabge da wani matsanancin ihun da gaba daya ya Kara sukurkuta Honorable, jikinsa ya Kara daukan Bari don haka hannunsa ya kasa dunKuluwa.

Adamu ya sake nishinsa ya ce, -

“Tunda ya Ki karbarsa da hannunsa  malam kai karbe su ka Kone masa.

. A idon Honorable Salmanu ya dunkule - hannu, gaban Honorable ya cigaba dukan tara-tara, ba a fi sakan talatin ba Salmanu ya bude hannun sai ga wasu takardu biyu sun fado, Honorable ya dinga kallon Salmanu ba ya ko Kiftawa har ya ware takardun sai ga zanen hoton—_ Dr. Abaji da wani bature durKushe gaban wata _ Kwaryar jini, abinda ya Kara gigita Honorable kenan, shi kadai ya dinga jin mutuwa da kabari na kawo masa gaisuwa. .

Bai iya hasala komai ba har lokacin da Salmanu ya jefa takardun cikin wuta yana wata

irin magana tare da_surkullec amma_ dai Honorable ya tsinci wasu_ harufan a tsittsinke, “Abaji ka tafi a wulakantacce, duk abinda zaka samu a duniya sai wanda Honorable ya ci ya rage maka sannan sai wanda ya so kaci”. Diff suka suka nemi ihun Adamu suka ~ rasa, shi ma Salmanu ya rage surkulle da canja murya, ya dinga magana da Honorable kai tsaye, wanda ya gama siye wa Imani, shi da kansa ya dinga jin nauyin ai lallai kudin da ke aljihunsa ba _ zasu iya biyan wannan aikin da aka yi masa ba. Shin ko Aljanin: KusKusdaniyatun ma zai rayu? Ya sha jin ana bayar da labarin tsakanin _ Kafiran aljanu da musulman aljanu ba a ga maciji, sannan kafiran sun fi musulman Karfi da zalunci, yadda suke cutar da dan adam haka suke cutar da yan’uwansu aljanu, to shi gashi Aljani KusKkusdaniyatu yayi fada da su akan cetonsa, ko sun bar shi yanzu Kila in sun kuma gamuwa su kashe shi. Tausayi da imani duk ya cika Honorable, ya zube kudinsa kimanin sama dubu dari da hamsin yana bayar da hakuri, “Ban san cewa zan tarar da wannan danyen aikin ba, don haka ban fito da kudin kirki ba, amma a karbi wannan in na tashi dawowa zan yi wani abu...”.
Salmanu bai damu da godewa ba ya mayar da hankali wajen Karfafawa Honorable din - gwiwa da ci masa alwashin ai ya gama darewa kujerar mulki ya huta. Www.bankinhausanovels.com.ng

Motar Honorable ko Karasa ficewa daga gidan bata yi ba su Adamu suka fito daga maboyarsu suka daga salmanu sama suna ihu!

‘“Yanzu da akwai irin wannan sana’ar mai _ romo muka dinga rayuwar talauci?” - Inji Tanimu bayan sun gama Kirga kudin suka tarar da dari da sittinda daya.. Adamu ma irin wannan farin cikin yake ciki, har ya fara hango aurensa da Husna hankal kwance. Salmanu na cikin farin ciki yana kuma tararradin cewa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci Husna zata iya zuwa ta tarar da Adamu, don haka ya shiga yanayinsa na rikita irin na dazu wanda ya tunatar da Adamu abinda yayi, “Amma fa da farko ka kusa ka kwafsa mana Salmanu” Salmanu ya yi murmushin Karfin hali, “Mtss Wallahi hankalina ke wani gurin daban”. . . Adamu ma ya nuna fuskar jimami, _

“Ni ma _ gaskiya da nine a_ kujerarka shirmen da zan yi a yau din nan ya fi naka, gabadaya ba na tare da ku”.

Salmanu ya dan bi Adamu daido, — .

“Kai meye matsalarka?”. Kai tsaye Adamu yaamsa,__.

“Husna’’Kallonsa kawai Salmanu ya cigaba da yi ba tare da ya tsinka ba, idon Tanimu ke sukan sa don Allah ya sani ba komai nasu yake son ya zamana Tanimu ya sani ba duk da bai taba nuna

,. wasu alamu na cin amana ba. _ _ “Na zaci ma ko kana tunanin zuwa ka gai _ da Hajiya ne, ka shagala da yawa, tun bayan. aurenka sau daya tak na ji ka ce min zaka je gaishe ta, yakamata kajeyau”. = _ Cikin sanyin jiki Adamu ya gyada kai,

“Abinda ke raina kenan, ko yaya ne wannan lokacin dole na nemo hajiyar, na yi wa Husna alKawarin kai kudin aure nan da kwana bakwai...”,° Tanimu ya zaro ido,°“Da gaske? ”. ,

-’ Murmushi kawai Adamu yayi yana satar kallon Salmanu wanda ke ta shan tsallen

murnarsa a zuci, amma fuskarsa ta Ki nuna duk wata alama da zata bayyana abinda ke ransa. Sai Adamu ya shiga tararradin ko kudi ne Salmanu baya son ba shi, Www.bankinhausanovels.com.ng

“Na ga kamar ba ka yi murna ba, alhalin da kana nuna min ka fi ni son na auri Husna”.

“Ba na son na yi murnar ne kuma na dawo na yi kuka, gara na bari idan na ga tabbatar abin sai na yi da hujja’. . In ji Salmanu. . . Adamu ya masa da alamun karsashi, “In sha Allah wannan karon zan dage na ga cikar burinmu”,

, “Zan tayaka”. Shi ma Salmanu ya amsa tun daga Kasan ~ zuciyarsa. Sannan yayi fuska ya ce, - “Yau ba mu da wasu muhimman baki me zai hana ka tafi yanzu?”

Adamu ya dan yi shiru alamun akwai wani abu a Kasa, ;

Cikin zaKuwar jin ba’asi kawai Salmanu ke kallonsa, har Adamun yayi ta maza ya ce,

“Zuwa yanzu kudin da muka tara zasu ishe Www.bankinhausanovels.com.ng

- ni aure?”. . Tanimu da Salmanun suka fashe da dariya

‘don yanzu suka gane inda Adamu ya dosa, Salmanu ya janyo hannunsa yana cewa, - “Kana da shakku a kaina Adamu? Ban — cancanci haka ba wallahi”. Dariya kawai Adamu yayi ya tashi ya fice.

**********

Hajiya nata ina ka saka ina ka aje da Adamunta duk duk da ya zo mata da fuskar shanu sai faman cin magani yake yana hura ~ hanci, amma dai ta’ yi farin cikin ganinsa musamman ganin yadda yayi Kiba yayi haske tamkar ba Adamunta mai busasshen lebe kullum ba. Kodayake canjin nasa ba Karamin kada ta yake ba, tun tuni dama take son ganinsa don dama tana cike da labarin cewa Adamu fa na bacewa kamar walkiya ba a sanin inda yake zuwa, sannan shagon da aka tude masa domin ya rike shi ba ya zama a cikinsa, kai bai ma damu da sha’anin shagon ba iyakacinsa ya bidi kudin cefane ya bawa Salma, hasalima an.ce bai taba shiga lamarin shagon ba kusan komai a hannun Salman yake. a Ina Adamunta yake zuwa kuma wacce wainar yake toyawa? Wannan ya dami Hajiya


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...