NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Zaka iya fadar duk abinda ya zo bakinka Salmanu, don ba ka san hakiKanin rayuwar da ke gudana a zuciyata ba”.

Kawai sai Salmanu ya ja dogon tsaki ya sa kai ya wuce, zuciyarsa kamar ta babbake da Karin tsanar Salma, shi bai ma san wanne irin mummunan mataki zai dauka a kanta ba.

Haka suka basar da komai suka cigaba da aikinsu, ranar ma sun sha baki kuma sun kwashi kudi. . .

Duk kwana uku ko hudu suke tattara kudin da suka samu su raba, a yau tun Karfe biyar Kafa__. ta dauke musu don haka suka zauna zauna zaman kasafi, sai da suka gama tsab Salmanu ya sake tattare na Adamu kamar yadda ya saba, ya jefe shi da yar dubu biyu.

Ran Adamu ya baci sosai, amma dai ya_shanye ya mayar da hankali ga Tanimu mai

. bincikar Salmanu dubu goman da ya ce ya ranta.

“Ba ka dawo da dubu goman nan ba fa”

Kai tsaye Salmanu ya ciro dubu goma a nasa kudin suka sake kasaftawa. .

ZAMU TASHI 


Tanimu ya tattare nasa ya sake Kirgawa inda ya tarar da dubu sittin da takwas, cikin bayyana farin ciki ya ce, “Kudin aurena sun hallara, dubu hamsin zan mika a kai min, na sha sha’anina da sauri”. Adamu da ya gama zuwa wuya ya fashe yana duban Salmanu a Kufule, To ni wannan dubu biyun da ka ba ni me zan yi da ita?” . Salmanu yayi fuska ya matse yace, “To bata ishe ka ba, ko kai ma kudin auren zakakai?” A tunzure Adamu ya ce, . “A’a kai ne zaka kai shiyasa kake hada rabona da naka ka rike”. — Cikin halin Ko in kula Salmanu ya ce, “Amsar. kenan, ko kai zaka kai kudin aure - zan iya hada maka da nawa™. Takaici ya hana Adamu magana, da ya rasa mafita kuma sai ya magantu, .Www.bankinhausanovels.com.ng 

- - “Shekara nawa zan yi ina tara maka kudin auren? Yakamata mu yi Ka‘ida don nima na san lokacin da zan fara tara nawa kudin auren”.

Cikin dariya Tanimu ya sako baki, “Ban da auren da ka yi?"

Da sauri Salmanu yayi wa Tanimu alamar yayi shiru, shi kuma yayi fuska ya ce, Ko yanzu ka shirya aure ka zo zan hada maka da nawa na baka, ni ban nemi kudi dan in jiyar da kaina dadi ni kadai ba, in na gan ka cikin farin ciki wannan ya ishe ni”
Dadi da farin ciki suka mamayi Adamu, cikin doki ya cewa Salmanu,

“In haka ne ka ba ni dubu goma sha biyar zan ziyarci Husna yau”.

Salmanu ya ji tamkar ya mike tsaye ya tattakura ya kurma ihun da duniya zata shaidi irin

' murnar da yake, sai dai tun da lamuran nasu duka na ‘yan dabaru ne, dole ya shanye abinsa a zuci, ya tsuke fuska ya ce wa Adamu,

“Yaya za’a yi na san ba Karya ka yi min — ba...”. .

“Idan ka san na saba yi maka Karyar to ita na yi maka”.Kai tsaye Adamu ya amsa cikin bacin rai.

Dole Salmanu ya mayar da zancen wasa ya shiga dukan kafadar Adamu yana dariya.

Amma can cikin zuciyar Adamu ji yake kamar ya fasa, haka kawai sai yake jin idan ya je wajen Husna ya ci amanar Salma, ko yaya ne Www.bankinhausanovels.com.ng 

yakamata yayi shawara da ita ya sanar da ita Kudurinsa, dama haka adalci ya tanadar, shi ne dalilin da zai sanya a sami zaman lefiya ko da sun ZO rayuwa tare.

Kamar Salmanu ya san sbinda zuciyar Adamu ke raya wa ya kwabe shi,

“Amma dai ka daure kar dadin hira ya sanya ka sanar da Salma labarin Husna, ka hadiye abinka haka ake wa mata, sai lamari ya zo dab ake basu labari, sai ka ga an fi samu saukin rashin fahimtarsu...”.

Adamu tamkar wani wawa ya saki baki,

“Allah ko? Wai ni har na fara tunanin zan “ sanar da ita, gani nake kamar ranta ba zai so ba...”. °

Da haushi ya ishi Salmanu sai ya tare shi a kufule da cewa,

“Au ko ita kake wa rayuwa ne? Haba! _ Ashe ba banza ba komai ya zame mana jabu...”. .

Kawai sai ya fara KoKarin Kwatar kudin da ya bawa Adamu, nan kuwa suka kacame da kokawa, dayake Salmanu ya fi Adamu Kwarin Kashi sai ga shi kudin sun dawo hannunsa. Ya mike tsaye cikin huci idanunsa sun kada sun yi ja.

Kawai sai Tanimu da Adamu suka daga kai suna bin sa da kallo dukkansu kansu ya kulle,

Salmanu ya dinga ‘jero rantsuwa yana cin laya,Www.bankinhausanovels.com.ng 

_ “Na rantse in dai har mu sami kudi ka je ka kai wa kundubar matarka ta ci ne, wallahi tallahi sai dai a watsa tafiyar nan kowa yayi ta kansa kaje ka zauna jiran shagonka in yaso ta taya ka zama, amma in ta isa mu nemo kudi ta ci Allah ya tsinen..."”

Adamu ya auna yayi magana amma Kirjinsa tuni ya dau zafi, sai Tanimu ne da ya gaji da ganin wannan Karfin halin ya tare Salmanu,

“To wai kai Salmanu ina ruwanka, Kasonka zaka ba shi? Wannan ma wanne irin Karfin hali ne zaka dinga fin me kora shafawa? Haka kawai kai ne zaka Ki masa mata...”.~ . Cikin tsananin fishi salmanu ya dakatar da Tanimu,

“Ka ga Tanimu babu ruwanka, ka bar shi ya musa da kansa in yana da hujja, ba dan Salma Adamu ya fito neman kudi ba, don haka wallahi bata isa ta ci ba... yadda Salma bata Kaunata hakazalika nima bana Kaunarta, kuma zan yi iyakar yi na domin na nuna mata cewa ba na KOunar tata... . Ikon Allah”,

Tanimu ya fada cikin mamaki yana ta kallon Adamu a ransa yana saKa irin danyen hukuncin da zai dauka idan shi ne Adamu, amma sai ya ga Adamun ya rausaya kai cikin sanyin jiki yana murmushin yaKe ya ce wa Salmanu, “To yanzu da na nemi kudi Rakuma na ce ka ba ni na sai wa Salma ko me? Na ce wajen Husna za ni amma baka yarda da ni ba, ban san dalili ba, sai ka ce na saba yi maka Karya”. Salmanu na sacewa a hankali tamkar  fulawar yis din daka zungura, ya Kirgo dubu ashirin ya miqa masa. ,Www.bankinhausanovels.com.ng 

Adamu ya karba yana murmushi sannan cikin siriryar murya yace, ae

“Salmanu ba ka fi ni son na kasance da Husna ba, amma abinda ubangiji ya hukunto babu wanda ya isa ya dakatar da shi”Ya jira cewar Salmanu amma bai tanka ba, ya sake ce masa.

“Ka Kara min dubu goma zan tsaya BoutiKue na sami shigar da zata dace da idon Husna...”. Ba musu Salmanu ya ciro ya Kara masa.

Bai jira cewar kowa ba ya cusa kudin a aljihu ya sa kai ya fice, ya bar Salmanu da sauke ajiyar zuciya yayin da Tanimu yayi saKare yana kallon Salmanun.

Sai da Salmanu ya ja fasali sannan ya juya ya dubi tanimu, ~

“Ka daina Kokarin shiga tsakanina da Adamu, ina da yaKinin ban zo duniya da kason cutarsa ba, duk abinda ka ga na yi masa Kauna ce ta janyo saboda haka babu ruwanka”.Jikin Tanimu a sanyaye ya gyada kai, Na fahimci haka”.

**********

Allah ya taimaki Adamu ranar Salma ba ta gida, tun safe ta tambaye shi zuwa gidansu tare da sharadin in ya dawo zai je su taho tare, don haka ya sami damar fesa wanka ya sha Kananan kayansa da suka yi matukar yi masa kyau, ya sha turare sannan ya cusa kudadensa a aljihu ya fice daga gidan cikin dukan zuciya, tun kafin ya fice daga gidan yake sanda don gani yake tamkar Salma ta sanya wani idon da zai gane mata shi yana wanka ko yana daukan gayun zuwa wajen wata ba ita ba, kai gabadaya ma gani yake

tamkar har can KoKolin zuciyarsa ta sanyawa _ gadi, kuma in yayi abinda ba ta so zata iya hukunta shi. Sai da yayi sha’awar ina ma ba shi da Karfen Kafa Salmanu, ya samu ya tattara masa ~ ‘yan kudadensa ya samu ya sai mashin, zai fi Kima a idon Husna kuma ko banza Kwalliyarsa ba zata sha iskar duniya sosai kafin Husnan ta gani ba. , Karfe shida saura ya aika yaro cikin - _ gidansu kiranta. ; . Tana zaune kan kekenta a tsakar gida tana faman dinki, cikin kwalliya ta ke sosai tamkar .‘mai shirin zuwa Party saboda tsabar zaton zuwansa bisa Umarnin bokanta Salmanu. Subhanallah! Bokan nan Karshe ne! Abinda ta ce cikin ranta kenan lokacin da ~ yaron ya gama sanar mata saKon Adamu. Wasu tawagar hawaye suka zubo mata ta saci ido ta goge su. Jikinta sai bari yake ta zari kujera ta fitako — Umman ba ta sanar wa ba. ' Ta yi arba da masoyinta Adamu tsaye a soron kwarjini da Kamshinsa sun cika mata soron, daurewa ta yi kawai kar ta shide ta bayar da mata, amma iyakar razana ta razanu duk yadda ta so ta ja aji ta gwada ta kasa. . Ta ajiye masa kujerar, ‘ Ga kujera ka zauna”.

Abinda ta iya ce masa kenan, ba maraba babu sannu da zuwa sai tsabar barin jikin Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dayake aAdamu ma. ba cikin hayyacinsa yake sosai ba, sam bai lura da gigitar da Husna ta yi ba, don tunda ya taho babu abinda ke kan harshensa face raya Ayatul Kursiyyu, Allah ya tsare shi da mugun ji da ganin juya bayan Husna

“bisa shakulatin bangaro da yayi da alfarmarta. ~ Shi jikinsa na Bari ya ja kujerar ya zauna : *hankalinsa da idanuwansa na kanta,

“Na zauna cikin neman yarda da amincinki Husna, ina neman alfarmar ko kin tuhume ni to. dan darajar Manzon rahma kar ki yanke min Kauna”’. . .

Husna ta ja tata kujerar ta zauna tana dabarar hadiye Kwallar da ke son kawo mata cikas, ta dago ta kalle shi cikin murmushin Karfin hali, muryarta a sanyaye ta ce,

“To menene na tuhuma Adamu, laifin me , ka yi min?”

Babu abinda ya zo ransa sai maganar

Salmanu,
ba ka yi komai ba wanda zai sa yarinyar nan ta saurare ka, hasalima zuwanka gidansu daya talakanka da kai futuk! Ka nemi yardar aure ta yarje maka... ban taba

’ ganin son tsakani da Allah ba inn wanda take maka, amma bata san kai mutumin banza ba ne ’ . ba ka san darajar irin wannan son ba...”

Shi ma ya sami kansa da KoKarin hadiye tasa Kwallar, amma sai da ta dan bayyana. Ya fara magana fuskarsa da muryasa na nuna dukkan sadaukarwa.

‘Ban miki laifin komai ba Husna, ko dai kin fada min haka ne don ke irin naki hukuncin kenan? Ni ko wanne irin hukunci zan iya karba daga gareki in dai ba na barina ba ne, ki bar ni ne kawai ba zan iya dauka ba Husna”.

.Duk juriyar Husna ta yi KoKari ko yaya ne ta fuzgo kalma ta fada amma ta kasa, ta yi Kasa

da ido kawai tana wasa da yatsun hannunta.

Adamu da yake jin fishin dauke Kafarsa ne ya dinke mata baki ya sa ya cigaba da yi mata sambatu cikin taushin harshe da tausasan’ kalaman da shi kansa bai taba tsammanin yana da su ba, Husna dai bai sake jin harshenta ba, da Www.bankinhausanovels.com.ng 

alama iyakar Kurewar gudu soyayyar Adamu ke take mata baya, duk Kokarinta ko gwajin Karfin halinta ba sa goya mata baya a bangaren Adamu.

Da Adamu ya yanke Kauna da jin cewarta, bai san yaya aka yi ba, kawai sai ganin kansa yayi durKushe gabanta cikin Kunan zuciya da hawaye,

. _ “Husna, ki yarda da cewata, muna dauke da zuciyoyinmu ne dan KanKantar girmansu akan na jikinmu, amma in ana neman mai ji da Karfi su ake nema a bar jikin namu, to ni ban san abinda ke son fin Karfin zuciyata ya hana ta abinda take son ba'tare da ta fasa son ba, wallahil azim ina son ki Husna, in kin ga ban yi aikin da ke bayyana son ba ki yafe min, wallahi ba daga ni ba ne...”.

Hankalin Husna ba ya tare da ita sam, hawaye take sosai ta riko hannun Adamu ya tashi tsaye, .

“Me ye haka kai kuma, na ce maka ban yarda ba ne? kai amintacce ne a wajena ko me zaka fada tun kafin ka'fada yana da muhimmin gurbi a zuciyata na rantse maka da Allah...”.

Adamu ba shi da amsa sai wani hawayen, amma dai kaso tamanin cikin dari zuciyarsa ta

rage nauyi don ya sami tabbacin dari bisa dari Husna na yi masa irin son da yayi ta fata daga gareta... sauran nasa ne, kuma in ma ya rasa ta yana da tabbacin daga gareshi za’a sami akasin wanda baya fata. ,

Yanzu zuciyar Husna ce ke raunane wadda take jin duk inda adalci yake to ba ta yi wa soyayya shi ba, tunda ta shiga zuciyar masoyinta Adamu da Karfin asiri ta sa ta abinda ba ta yi niyya ba Www.bankinhausanovels.com.ng 
Amma dai duk da haka sun bar komai sun _ ji da soyayyar, sun bata haKinta da suka hanata. ~* a tsawon kusan wata biyu na zantar da juna. abinda ke cikunansu, kalamai masu sauki da

_ laushi a zuci da kunne sannan masu Kara mutunta

soyayyar tasu kowa ya kai Kwarya ana biyo shi da ramuwa.

Daga Karshe dai da Kyar suka shirya rabuwa lokacin da ake kiran sallar magariba, Adamu ya tattaro mata dukkan kudi aljihunsa wanda suka haure dubu ashirin ya mika mata.

Husna ta karba ta shiga juya su tana Kare musu kallo tamkar tana tantamar in na gaske ne har sai da Adamu ya tsargu, amma tsakaninsa da Allah yayi magana, Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Ki yi haKuri babu. kudi sosai tare da ni... ’ Ta tare shi cikin Kwalla da mamaki, “Me kake cewa Adamu?”, Kallonta yake kawai. Ta mika masa kudin tana girgiza kai. “Ba zan karba ba, wannan kudin fa sun isa ka kawo gidanmu a matsayin kudin aure, ni babu wani farin ciki da zasu bani fiye da wannan, don - ba ni da tabbacin in ka tafi abinda ya fi zuciyarka jarumta ba zai sake hana ka na ga ko kyallin ; . fuskarka...ba”. Ya tare ta a raunane, “Kar ki ce haka, kwana nawa to kika ba ni, _ ko kwana nawa kika dibar min zan_ cika alKawarin ki ga waliyyaina a gidanku”. ; Da sauri ta miKa masa kudin tana cewa, , “Sati daya”. Yana dariya ya ce mata, . “Ba za’a ga garajenmu ba?”. - “Kanmu yakamata mu duba ko wasu?”. _ Da sauri ya kada kai,

************

Duk da Salmanu a dokance yake da jinHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...