NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


                   Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Ai wata biyun aure yake nufi, dauke + Kafarsa gare ni na nuna rashin damuwarsa da ni . Malam, ni kuma ji nake ba zan iya rayuwar da. - babu shi ba, don Allah ka taimake ni...” Ta wuce da goge Kwalla. ' Ta yi shiru, Salmanu yayi shiru saboda rashin abin fada. . So Ita ta sake Magana cikin hawaye, Ina zargin ma ni asiri ya yi min, ban san ana son mutum irin haka ba, Malam da tunina - cire shi daga sabga ta wallahi” Tausayinta ya Kara damun Salmanu, ya .. yarda Adamu ya cuci Husna,.shi ya dinga zazzafar addu’a kan soyayyarta da samunta, gashi Allah ya amsa masa shi kuma ya juya — mata baya ya bar ta da wahala. - Www.bankinhausanovels.com.ng 

~ Dole dai ya kakaro abinda zai Karfafa mata gwiwa lokacin da ya janyo kasko ya fara yafa turare.  “Ki kwantar da hankalinki ba zai wuce watanni biyun da ya dibar miki ba, zai zo ya baki mamaki, ni na yi miki alKawarin sai kin juya Adamu a tafin hannunki, sai kuma ya ninka miki son da kike masa, amma-ba wani asiri da yayi miki. Husna ta sake jin wata nutsuwa a zuciyarta, ta fara godiya ba KakKautawa.  Tamkar Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu ya saki fitsari a wajen lokacin daya ji tsayuwar mashin din Tanimu da Adamu ya fita da shi a harabar gidan gonar, . ya tabbatar kuma hanyar da zai biyo ko inda zai labe dole wadda’ zai iya ganin Husnace. Da sauri ya mike daga zaune ya shige _ cikin dakin yana cewa, : . “Ina zuwa, bari na kawo miki wani turare - da zaki zuba a cikin lallen Kunshi” . - Bai jira amsarta ba ya shige. ° . Ya yayimo Tanimu da ke lafe a duhu da tiyo a baki yana jiran alamar da zai saki muryar ~ aljanu, ; 

“Maza je ka ka tare min Adamu kar ya shigo gidan nan, bitabaya?” = - - Tanimu ya tsaya yana, radar neman ba’asi - amma sai Salmanu ya tunkuda shi sai da ya kusa kifawa, dole yana tashi bai nemi wani . ba’asin ba ya fice ta Kofar bayan,; amma tuni Adamu ya kafe mashin cikin zafin nama ya _ tunkari masaukin bakin da suke jiran shiga . . Wajen boka Salmanu.  Amina da Jamila na. zaune suna dako, kuma yana wuce su Husna zai tarar gaban Boka Salmanu

ZAMU TASHI 

Adamu na dab da shiga cikin falon ya ji . da karfi an shako shi ta baya an yi waje da shi, bai sha wahalar gane cewa Tanimu ne ya yanke masa wannan danyen hukuncin ba, abinda kawai ya zarge zuciyarsa shi ne neman dalilin wannan shegiyar shakar. .

Da kyar ya kwaci wuyansa daga hannun Tanimu bayansun zagaya baya, sai da ya duma masa naushi ya ture shi gefe sannan ya shiga hargagi,

‘dan iska kana son ka kashe ni ne? ina da tarin. burikan da suke layin addu’a kafin Kasa ta rufe min ido

Tanimu ya fadi a gefe yana dariya,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Wallahi ramawa na yi, irin wannan muguntar Salmanu ya girba min da yaje ba ni sakon in zo in tare ka kar ka shiga”’

Adamu ya kalli hanyar da suka biyo cikin tsarguwa da alamun rashin fahimta, sannan ya mayar da kallonsa ga Tanimu, .

“Kar a bar ni na shiga? Bisa wacce hujja?” “Kila in an tsaya fadar hujjar lokaci ne zai

Kure da alama, amma kar ka damu, na san wata

harkallar ce da idan ka je zata iya wargajewa’

Adamu bai tanka ba, illa son fadawa tunani  daya ji ba tare da ya shirya ba, yanzu da yayi maganar buri, ba komai ne burin nasa ba sai Husna, ba kawai an tura Husna can bangon rayuwarsa an bawa banza ajiyarta ba ne, a’a barna take a muhallin da take, kullum rami mai zurfi take hakawa wanda zai yi gaba da. farin. cikinsa da dukkan wasu muhiniman  lamuransa. Yanzu tazo ransa ne sosai domin yaci karo da irin kamshin turarenta . a yayin da yake shiga masaukin bakinsu “Wai meye na ga kayi wani tsuru? Kai ka fini rashin shakku akan Salmanu, kai ka fi kowa . shaidarsa akan baya cuta, ba zai cuce.mu kobo ba, saboda haka bai kamata yanzu nafi ka nutsuwa ba”Da sauri Adamu ya saki fuskarsa, yana . ‘" dariya ya amsa,“Zuwa yanzu ai kai ma ka yi masa wannan shaidar, shiruna yana da alaka da gabadayan ° rayuwata ne, na fito neman kudi domin mallakar . abinda na fi so a filin rayuwa yanzu, amma kaga yayi min-nisa, in. wannan ya zo raina ina jin jinyar da ta fi ta kwanciyar shekara goma” . Cikin tausayawa Tanimu ya tare shi da rarrashi kamar yadda ya ga Salmanu.na yi masa,Www.bankinhausanovels.com.ng 

‘““Ayya ka manta kawai, kai mutum ne mai gata mai sa’a, haka Salmanu ke cewa, zamu tsaya maka”.

Ya Kare maganarsa da dariyar zolaya.

Dole Adamu yayi dan Karamin murmushi, a zuciyarsa kuma yana yarda da cewa lallai yana da gata a wajen Salmanu, duk duniya shi kadai ya fahimceshi, kuma shi kadai ya damu da abinda yake yakushin rayuwarsa, gashi kuma cikin fahimtar tasa ya fara kokarin fahimtar da wasu irinsu Tanimu cewa su saurari Adamu mai rauni ne mai kuma buKatar taimako ne. _ ‘

Sun jima nan tsaye suna hira har suka isa wadan nan bakin su fito su tafi don su samu su yi kyakkyawan shirin taron bakonsu na musamman Honorable

“Kudin zance zan kai in na sami wannan sallamar da. muke sa ran samu daga Honorable”.In ji Tanimu. : .

Adamu na dariya ya ce,

“Ni ban yarda rashin kudi ke hana ka aure ba a yanzu, ba kamar yadda ya hana ni a lokacin da rashin kudin ne kawai abinda ya isa ya hana ni aure ba, yanzu ga kudin sun samu, amma sun ~

kasa Samar min abinda nakce so”. . “Yau sambatu kake ta faman yi mana”

. Tanimu ya fada yana mai Kura masa ido, Adamu ya dinga kada kai a sanyaye, “Kawai na ji Zuciyata ta narke, tamkar tana son dawowa sabuwa’ .

. Tanimu bai amsa ba saboda mayar da hankali da yayi kan amsa wayar Honorable, yana  wayar a ladabce kuma cikin siyasa.

Hankalin Adamu na ga Kofar fita daga gidan lokacin da su Jamila ke ficewa, Allah ya sa.

-Husna ce a farko ta riga ta fice, wadda ko inuwarta ya gani yana da tabbacin zai shaida ta

' ba wai ta juya masa baya ta tafi ba.

Ya mayar da hankalinsa akan Tanimu, kafin yayi magana Tanimun ya riga shi cikin

_ yanayin jimami,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Honorable ba zai sami zuwa ba yanzu,

"ya ce sai gobe Karfe tara da rabi na safe”.

Adamu ya amsa,_ .

*“babu matsala, za mu fi samun damar shiryawa zuwan nasa ma, ka ga fitar da na yi yanzu ma ban samo manyan Kusan ba, sai-Kanana wadanda ba zasu yi nutsewar kirki ba...”

Ya katse maganarsa saboda shigowar kiran
Salmanu wayarsa, bai daga wayar ba ya yafici—Tanimu, Zo mu je wancan banzan da ya shanya mu. ya ga bushewar tamu ta isa”. ° : . Suna dariya suka zagaya ta kofar baya suka = shiga.  Salmanu na tsaye a taskar tsubbunsa yana dan safa da marwa, daga gani baKin da ya gama sallama sun zo masa da babban al’amari, yanayinsa da fuskarsa ba su Boye komai ba. Adamu ya gintse fuska ya nemi guri ya zauna, sai Tanimu ne ya bi Salmanu da neman  ba’asi, - “Ba su zo da kudi ba ne ko sun zo da salon Kure mu ne?” - Da sauri Salmanu ya girgiza kai yana dariya, . . “Koshi ne da kwanan yunwa, daya Hajiyar __ ta zo da harkar samu, amma a yadda na so in fahimci maganarta tasan Adamu” Fuskar Tanimu ta nuna tashin hankali, amma Adamu ko gezau bai yi ba, Tanimu ya  daKumi Salmanu yana bade shi da tambaya, . “A ina ta san shi, sanin kusa ne ko na nesa?”. : :

- Salmanu ya saci kallon Adamu wanda yayi bakam yana jin su, sai ma ya kishingida ya lumshe idonsa alamar gajiya da bacci, Salmanu ya ce,

“Cewa na yi kamar ta san Adamu Tanimu, abin buKatar kawai shi ne, duk ranar da zata zo Adamu ya dinga yin nesa da haduwarsu”. _

Tanimu ya juya ya kalli Adamu,

“Ka ga shi kamar ma abin bai dame shi ba”

Adamu ya daga ido ya dube shi, Ai bari nake ku gama tattaunawar sai inje - in rungumi taransufoma na mace, tunda an ga matar da ta san maKarar kwanana”.

Duk suka tuntsire da dariya, ta Salmanu har Kasan zuciya, don a tsorace yake da shakkun in Adamu bai ga Husna lokacin da suke ficewa ba, don akan idonsa ya ga yadda Adamu yake neman cinye su da kallo, yanzu kuwa furucin da Adamun yayi ya tabbatar masa tabbas Adamu bai ga Husna ba.

“Kai matsalarka baKar magana bata yi maka wuya Adamu”.

In ji Salmanu. Ya zarce da cewa,_ Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Me ye matsalarka ne? lafiya fa muka rabu

da kai ka tafi siyo mana Kusa yanzu kuma ka zo kana yi mana mashau-mashau”.
Karaf Tanimu ya amsa, . “Husna ya tuno”.

Da kyar Salmanu ya shawo kan razanarsa ya binneta a Kirji, ya dinga fanshewa da kallon Salmanu cikin. shanye baki, sannan da kyar ya iya cewa,

“Ya tuna Husna kuma? Husnan da tuni ya. watsar da babinta ashara?”,

Cikin rauni Adamu ya shiga zancen,

_ “Cikin matan da suka tafi yanzu akwai_ wadda ta yi amfani da irin turaren da Husna ke amfani da shi, ban san buyan da son Husna yayi

a zuciyata haihuwa yake Kara yi ba sai yau” Tanimu ya tuntsire: da dariya, amma

Salmanu ya kasa gane me zai canka yaji.

Tausayin Adamu da Husna zai hada yayi ta ji

ko kuma murnar Adamu ya dawo da son Husna

sabo a yanzu daidai gabar da matsayinsa na

bokan Husna zai iya taka muhimmiyar rawa?

- Ya kara kusantarsa da alamun Karfin

gwiwa da boye karayarsa da tausayinsa,

“Ok. Dama kana tune da Husna? Tsakani da Allah na zaci ka manta da ita”

_ Adamu bai iya dubar Salmanu ba muryarsa a raunane ya ce masa, . ,

“Yau tamkar ana sauya min zuciya, ko shaidan ya ki ko yaso, tsarkakakkiyar zuciyata ta bawa Husna matsayi... da wuya idan abubuwa Kanana zasu iya sawa na manta da ita, Kanshin irin turarenta kawai, ya iya rauni a zuciyata’.

Salmanu ya ji yana son fashewa Www.bankinhausanovels.com.ng 

* hawaye, don haka ya tattara maganar yana son _ turbudawa kwandon shara, ya dubi Tanimu ya ~ ce, .  “Ku mu fara shirin tarbar Honorable ko Tanimu?”. . . ‘Mun yi waya wai ya ce a daga masa zuwa_ gobe’. Cikin rashin kuzari Salmanu ya wuce yana cewa, “Ya hutar da mu, sai. mu tashi haka dama na gaji’ Sororo kawai Tanimu ya dinga bin su da kallo, in ya kalli wannan ya juya ya kalli wancan, Karshe yana son yin magana Adamu ya riga shi — da dakatar da Salmanu ficewa, “Ka gaji, sauraron matsalolina suka gajiyar da kai, ko kuma don kana ganin basu shafe ka ba? ne

Har Salmanu zai yi magana_ cikin kyakkyawar fahimta sai ya ga asarar hakan, _

“Ina ganin duk biyun ne, na gaji da maganar don kullum maimaita ta ake, sannan kuma gaskiya ne bata shafe ni ba”.

Ya jira cikin shirin jin baKar magana daga Adamu, amma sai ya ji cikin sanyin murya Adamun ya ce, -

“Eh, kuma kana da gaskiya”. .

Salmanu ya ji sanyin gwiwa, amma ya kore da nuna ko in kula, yayi fuska ya ce,

. “Ba na buKatar shaidarka”. . “Allah ba ka hakuri”.

Abinda Adamu ya ce kenan, ya mayar da kai a sanyaye ya kishingida.

Salmanu ya kawar da kai a Boye yana shanye damuwarsa sannan ya kada kai ya fice daga dakin, aka bar Tanimu cikin wasi-wasi, Karshe ya zabi bin Salmanu, ko banza ya fi Adamu hira kuma ya fi shi warware labari, amma yana zuwa sai Salmanu ya daga masa hannu,

Na fi Adamu shiga damuwa Tanimu, don Allah a bar ni na yi tuanani”.

Tanimu ya so ya ji haushi, *Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Eh, na biyo ka ne don ka manta baka yi mana bayanin kudaden da muka samu daga _ wadannan matan ba”, _ “Mun caji ko wacce dubu goma...” Tanimu ya tare shi, ; “Dubu talatin kenan”. . A Kufule Salmanu ya zura hannu a aljihu ya dauko dubu ashirin ya wurga masa. Duk da ba buKatar Tanimu kenan ba bai ~ fasa sanya hannu ya dauka ba, amma sai ya tarar da dubu ashirin, ya kalli Salmanu sororo, “Dubu ashirinnagani”, — _ “Na ranci gomar”. Tanimu ya zuba masa ido cikin shakku, amma tunda zuciyarsa ta nutsu da amanar _ _ Salmanu sai kawai ya dauki kudin ya wuce ya bar shi nan.

***********

Tun da suka baro gidan boka suke tattauna yadda aka yi tsakanin Jamila da Amina, Husna dai ta yi dif tamkar ruwa ya shanye ta. - . Zuwa yanzu kunyar ta kai kanta gidan boka_ a kan saurayi ta fara daurayewa daga zuciyarta, nadamar ma haka, yanzu babu abinda ya karade

zuciyarta face yakinin ta kamo turbar da zata sami cikar burinta, duk duniya babu wanda ya san matsalarta ko kuma yadda son Adamu ya haka mata rami a zuciya daya zuciyar tata sai boka wanda da alama warakarta a hannunsa take, don haka juya wannan nasarar a zuci ba zata iya hadawa da shiga surutan su Jamila wadanda gaba daya sun kawo mazansu ne bisa son zuciya,ba jamila ta zo neman Kyallin duniya wato mota, Amina ta zo a hana mijinta kallon Kwallo, ita yadda take son Adamu zata iya cigaba da sonsa da rayuwa da shi ko da ace a Kafa zata dinga dukkan tafiyarta ba wai motar haya ba, sannan da Adamu ne yake son kallon Kwallon Kafa, tana da yakinin sai ta fi kowa son Kwallon Kafa albarkacin Adamu yana sonsa.

Jamila ta zunguro ta,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Wai Husna me ye matsalarki ne, baki ga alamun biyan buKata ba?”, .

. . Husna ta dage ta gayyato wani mashahurin —

yake, alamun hankalinta ba ya tare da su,

“Wallahi na ga alamu”.

“Ai malamin nan yayi a rayuwa, abinda ya burge ni kuma yau babu cajin kirki’”. In ji Jamila. :

- Amina ta ce, . * “Nawa ya caje ki? Ni dubu goma ya karba”, Jamila ta amsa, . “Nima hakan ya karba, Husna fa?” . ' A sanyaye Husna ta dago ta kalle,su, : “Ni bai. karbi komai ba, ya ce na fara zuwa ” na gwada maganin da ya ba ni” Suka cika da mamaki duk su biyun,Jamila tace, “Na san aikin bokan nankamar yankan wuka, amma sam.ba shi da sauki akan kudi, ya aka yi ke ya daga miki Kafa?” Husna nadariyatace,;,Kila ya hango babu dubu goma a jaka ta, _ dubu biyu natafidaita’. “Ni kuma ba haka na zata ba”. Keto Inji Amina, “Me kika zata?”. Jamila ta tambaya. :

- “Ko gani yayi buKatarta ba-zata biya ba? .

- Inda ya birge. ni abinda ba-zai yiwu ba, ba ya* yaudarar mutum, ni dai, Kiri-Kiri ya fada min cewa, in dai an hana Kamalu kallon kwallo to. - lallai ni kuma zai rakita min kishiya,..Jamila .ta tare ta cikin tsananta dariya,


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...