NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


                   Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Dole Adamu ya dara yana bin Salmanu da kallo cikin wani irin Kaunarsa, ji yake ban dashi da Husna ba shi da kowa a duniya wadanda suke iya son abinda yake so, suke kuma iya

yunkurin ba shi abinda yake so. °
.
++++++++++

Karfe goma sha biyu da rabi daidai « ‘bakuwarsu ta farko ta zo, maimakon matar * Alaramma Hajiya Kumbo ce ta fara zuwan Www.bankinhausanovels.com.ng 

Salmanu na hakimce kan shimfidar buzun da suka lullbe da fatar Maciji, ya wadatu da wani irin kwarjini irin nasu na bokaye, sai muzurai yake.

Adamu kuma na daga can uwar dakin riker da tiyon da suka huda bango suka zura daidai saman kan Salmanu amma sun yi wa gurin basaja da adon kayan tsubbace-tsubbace.

. Ba kadan ba Hajiya Kumbo ta ji shakkar wannan Boka, sannan ta ji yakinin tabbas in

» wannan bokan yayi aiki ba za a tarar da wasa ba.

Tunda ta shigo Salmanu bai daga kai ya kalleta ba, illa ya Kurawa fararen takardun Www.bankinhausanovels.com.ng 

. gabansa idon.

Hajiya sai dan nishi take na baKunta da nuna sallamawa wannan hamshakin Boka, wanda a labarinsa da aka bata an ce ba a fara yi masa Magana, shi yake fadar dukan abinda ya kawo mutum sannan ya magance masa damuwarsa.

Kamar Salmanu ya san abinda take tunani ya dauko daya daga cikin fararen takardun nan . ya mika mata

ZAMU TASHI 


- Tun da safen suka samu. kyandir suka rubuce sunan mijinta da na kishiyarta da rowan kyandir din yadda ya saje da farin takardar babu yadda za’a yi farat daya a gano rubutun.

Hajiya ta karbi takardar cikin ladabi da Barin jiki. Salmanu ya cilla mata” Kullin niKakKen . . gawayi wanda suka gauraya da garin dayis. Ta hada su duka biyun tana juyawa a * . hannu tana kallonsa cikin rashin fahimta.. . “Ki bude wannan maganin” — - Boka ya fada mata cikin murya mara Karfin sauti, sai da ma ta nutsu sosai sannan - ’ kwanyarta ta ruwaito mata abinda ya ce. Da sauri ta shiga warware Kullin gawayin da suka nade da takarda, ta daga kai ta dubi , Boka cikin

rawarmuryatace, - —°“Na ware Malam” . ; Salmanu yayi shiru tamkar yana karbar . Wani saKo daga sama, sai can ya sauke gani a kanta,  “Ki barbada garin maganin nan kan wannan takardar ta hannunki” Jiki na bati tuni Hajiya taidar. Www.bankinhausanovels.com.ng 

“To karkade”  Nan ma ta karkade sai ga zanen sunan mijinta da na kishiyarta ta dinga bi da kallo — ‘ cikin dukan zuciya. , . _ “Ba ni nan mu gani” ne Boka yayi mata umarni . Nan ‘Ta mika masa jikinta na bari, ta kasa _Magana.  . Salmanu ya Kura wa takardar ido sannan _ ya mayar da kallonsa gareta, So “Wane ne Usman?” Yatambayeta, = -* ° . Cikin sallamawa da rawar murya ta amsa.. ‘masa “Mijinane” “Hadiza fa?” _Sai data Bata rai sannan ta amsa,. — - . “Ita ce kishiyar tawa” ' _ Salmanu ya dinga gyada kai nuna al’ajabi da mamaki.  Hajiya Kumbo duk ta bi ta tsure. ; Ya sake mika mata takardar, . ' “Ungo .juya bayan ‘takardar ki sake barbada maganin nan”

“Boka me ka gano? Na shiga uku!”

Da kyar ta karbi takardar saboda rudewa.

Salmanu yace,

. “Abin babu kyan gani, amma _ sake jarrabawa muga sunan wanda zai fito”.

Da ta sake sai ga Usman da Hadiza sun sake fitowa, ta mika masa hannunta na_ karkarwa.

* Ya duba na wasu sakanni ya kada kai sannan ya ajiye takardar gefe yana cewa, ai wadannan mutanen da gaske suke”° Ya janyo wani kasko a gefe wanda ke cike da rushi ya bude wani kuttu ya duntso garin magani ya yafa wa wutar, wani irin hayaki gauraye da Kauri ya tashi a dakin, shi kuma ya runtse ido yana ta faman mus-mus da baki tsawon wasu mintuna marasa yawa. Can kamar daga sama sai ga-Adamu ya fara wani irin nishi a Tiyo, Ba Hajiya Kumbo da nan take suka gama siye imaninta ba, hatta Salmanu da ya kwana da sanin basajar sai da salon na Adamu ya so

‘tsorata shi da zargin wani aljanin na gaske yayi

musu kutse a aiki, amma dai haka ya cigaba da

matsewa yana gurnanin da ke Kara. Tsorata Kumbo.  Sai da Adamu ya gama nishinsa can kuma - yayi dif! Tsawon wani lokaci sannan ya dage ya kwararo wani ihu mai gigitarwa wanda ya sanya Hajiya zabura zata.arce sai da Salmanu ° ya dakatar da ita da hannu tare da dora yatsa a bakinsa alamar ta yi shiru, nan ta zube jikinta - * na Bari. : _ Adamu ya zarce da Magana cikin nishin * da ya fara da shi,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Bisa wane dalilin ka taso ni ina baccina,. me yasa ku bil adama ba ku cika tausayi ba ne?”
Salmanu ya marairaice murya cikin ladabi’ ‘ -yace, ; “Wani bahagon aiki ne ya zo gabana ranka ya dade, dole na kira ka, ka zo ka sanya hannu ka ceci mutuncin baiwar Allah na...” : '. ° Kafin ya rufe baki Adamu ya amsa da . wata irin dariya, ya ce, a “Wai Kumbo da ke zaune gabanka?” , Salmanu ya dago ya kalli Kumbo wadda _ razana ke sata jin neman sakin fitsari a wajen,

sai dai can cikin zuciyarta cike take da farin cikin abinda ke faruwa, wannan sabon bokan nata da manyan aljanu yake aiki wadanda suka sanin da matsalar da ka zo da ita. . Salmanu ya ce, . . - “Ita ce ranka ya dade” -To ka fada mata ta tashi ta tafi gida, da mijinta aka hada baki aka cuce ta” , Salmanu ya marairaice Murya,.= “Ita da tazO neman waraka wajen manya irinku ai ba kwa kora ta ba Ranka ya dade” ‘ - “A taimaka min” . . ‘ka shiga maganar cikin .barin jiki. ’ Adamu yace,  “Ina buhun dankalin turawan da ya kawo. miki kamun azumi?”  Hajiya Kumbo ta shiga tunani. Ta tuna cewa duk wata mijinta buhun dankali yake direwa kasancewar gidansu na mutane, amma watan azumi har buhuna-hudu yake direwa a raba wa makota buhu biyu, azumin da ya gabata satin kama azumin ya kawo dankalin. ‘ Nan da nan ta gyada kai, “Eh na tuna, buhu hudun nan ko?”

Adamu ya amsa cikin dariya da ihu. “yauwa so! Kin san daga hannun wa suka fito?”? , Ta gwalo ido tana girgiza kai, - “Ban sani ba ranka ya dade” _ — Adamu ya amsa, “Daga hannun Hadiza matar mijinki suka fito, shiyasa na ce duk abinda aka yi miki da — - sanin mijinki..”' Hajiya ta saki wani irin nishin fargaba ta ce, “Oh ni Allah! Alh. ya ci amanata...” * Adamu yatareta, _—. _ “Duk asirin da zata yi miki ta hannunsa take kawo miki shi take bawa ya kawo miki a zuwan daga gare shi ne, amma lamfa kawai suka yi miki dukkansu, suna nan suna niyyar _ tarwatsa miki rayuwa.. Sai ga Hajiya na son Barkewa da kuka,Www.bankinhausanovels.com.ng 

- “Na Tuna da haka wallahi, don a da Alh. komai na gindaya ba ya musawa amma yanzu ko jinjirin jaki haka ya ganshi akan yadda  yake jayayya dani”

““Ai ta gama da shi,kiris take jira ta Karasa kassara ki, ko yanzu gata can na hango ta zaune gaban wani matsafi suna shirin yo miki aike...”

Hajiya ta dora hannu aka tana ambaton na shiga uku, . Adamu ya cigaba da ruda ta, “Rannan da kika tsefe kai an turo Duna ya saci gashin kanki, gashi can ana kullewa a cikin kwai za a jefa teku, in har hakan ta * kasance to ke da mujiya ba bambanci a idon mijinki”.- Hajiya ta sake rikicewa ta cigaba da kuka . haikan tana roKo da a taimake ta. Sai da Adamu ya. gama tabbatar da imaninta sannan ya ce mata, .

“Zauna ki dakata a nan, na san Aljan Cunkokuwaso za su tura ya je tekun, ni kuma zan tura Migadir ya Kwato ya kawo miki nan ki gani” so,

Da haka Adamu yayi musu Sallama yayi Www.bankinhausanovels.com.ng 

nishi ya Bace. . Hajiya ta kife kai wajen tana ta faman - kuka, Salmanu kuma yayi Kus yana sauraronta

a zuciyarsa yana saKa yawan kudin da zai wafta. . ; a . Damuwarta ya sanya bata kula da lokacin da Salmanu ya dauko farin kwan kazar gidan gonarsu ba wanda suke da irinsa ya kai hamsin, yadda suke wa Kwan shi ne, suna_ tsaga shi daga Kokolinsa cikin hikima da wata siririyar aska yadda ba zai fashe yayi baraguzai ba, sai su zazzage ruwan su cusa tarkacen da suke so, _ Wani su sa gashi wani allurai, wani sucusa danyen nama wani kyanyasai, wani kuma su. hada gashin da rowan Kwan, sai su mayar da | murfin su like da gam ko super glue yayi ~~ tamkar ba a taba bude shi ba. To Hajiya mai gashi hade da rowan kwai aka dauko mata wanda zuwa yanzu yayi wari. Salmanu yayi tafi da hannu dan janyo hankalinta kasancewar ta kife kai tana ta faman kuka shi kuma yana ta faman Magana ba ta san yana yiba, “Magadir har ya kawo Kwan ya wuce kina faman kuka, ban da abinki meye na kuka bayan. kin gamu da Sarkin Aljan ShakaKiriro ya shiga aikinki da kansa?” . Hajiaya ta hau murzar ido tana kallon Salmanu,

Ya mika mata Kwan ya mika mata wata tasa yana cewa fasa shi mu gani,

Ta karba da Kwarin gwiwarta cikin dokin ~ fasawar, don Allah Allah take ta fasa shi ta san fasawar ce tarwatsa asirin da kishiyar tata ta yi. mata ko take shirin yi Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan ta fasa, ba,ita ba hatta Salmanu sai_ . da ya toshe hanci saboda azabar doyi, ya dinga tari yana Karawa da shegantaka, ita ma , hancinta toshe tana bin fasasshen Kwan da kallo, sai ta ga tabbas ma gashin kanta ne, hatta kududunen da tayi masa kafin ta watsa shara yana nan ba su ware ba.

“Malam ka taimake ni mana, me ye abin

_ yi yanzu? Ga sharrinsu dai an dauko shi” .

Tana nuna rubabben Kwan da ta fasa

“Ki tashi ki je gida zaki ga aiki da cikawa, ShaKaKkiriro ya zuciya sosai, na san ba sai an bashi zabi ba, ba zai wa Hadiza da kyau ba”

Cikin farin ciki da doki ta ce,

. “Allah ya sa, ni ko kashe annamimiya ma yayi ita ta sai wa kanta”

“Na fada miki ba sai kin bashi zabi ba, ke dai ki dawo nan da sati guda” Ta shiga zuge jaka cikin jin Kwarin — gwiwa. Salmanu ya dinga satar kallonta yana , tunanin ta inda zai bullo mata in ta ba shi abinda ba shikenan ba. ; . “Malam nawa zan bayar kafin alKalami” Salmanu yayi fuska iyakar fuska, . ~ “Ki bada dubu hamsin” : Ta dan ji dukan zuciya, amma da ta tuna ° bokanta na baya wanda ko kama Kafar wannan bai ba shi kansa yana cajar sama da haka kawai. - sai ta zage jaka ta ciro ta miKa masa, ya tura_  mata wani faifai ta ajiye a kai sannan ta tashi tana yi masa godiya ta fice.  Sai da ta jima da fita sannan Adamu da Tanimu suka fito maboyarsu suka shiga hayaniya da ihun murna tamkar sa Balla dakin. Tanimu ya dubi Salmanu yace, : “Yanzu kai Salmanu tuni ka san da ‘_wannan sana’ar ka bar mu muna ragaita a titi?” . ‘* “Rabonmu ne ke nesa” Salmanu ya amsa cikin farin ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Adamu kuma ya ce, ; “Ni kam yanzu na nade hannun riga zan fara sana’ar nan, ko kun tuba ni kam zan Zarce” Cikin shegantaka Tanimu ya ce, , “Ai tuban tafi-da-gidanka zamu dinga yi, muna aikinmu muna tuba, Allah sa su ma masu zuwa wajen namu su dinga zuwa tafe da tubansu” — . Cikin sati daya sana’ar tasu ta shahara, .* Tanimu na da ido a sanin mata da ‘yan siyasa_ kasancewarsa dan bangar siyasar da ya tuba ya ~ fada bokanci, don haka shi ne mai kawo musu_mutane, mata da Alhazai, ‘yan siyasa da ‘yan . kasuwa, su ma a junansu duk wanda ya zo ya sha basaja, aka sace imaninsa in ya tafi sai ya _ fada wa amininsa wani shahararren boka ya bayyana, shi ma in-yazo sai ya fada wa nasa Aminin ta haka tafiyarsu ta fara nisa. .

*************

Tun bayan kwana hudu da auren Salma da Adamu aka kamala duk gyaran da za’a yi wa

gida, aka yi jere aka kuma zuba kayan kanti  aka kai wa Adamu Salma kwana goma sha daya da auren. Ranar da za’a kai ta da safen ne Alh. ya  shammace shi ya biyo shi gida bayan sallar - asuba, kasancewar kullum daga ya dawo sallar asuba yake shiryawa ya fice, ba za’a Kara ganinsa a gidan ba sai bayan sallar isha,  -wataran ma har Karfe goma yana kai wa. Babu ko sallama Alh. ya bankada masa ». Labule ya bi bayansa. . . Suka yi cirko-cirko a tsakiyar dakin suna kallon juna, fuskar Adamu da fishi, fuskar Alh.. _ na nuna halin ko in kula. . Alh. ya sanya hannu a aljihu ya ciro mukullai ya miKa wa Adamu, “Don Allah ka taimaka idan ka dawo ka zarce gidanka, yau za a kai maka matarka” Adamu ya miqa hannu saroro ya amshi makullan, ba tare da ya tanka ba, ya dinga motsa baki kamar yana so ya gode wata zuciyar na kwabarsa cewa bai kamata a cuce ka kuma ka yi wa macucin godiya ba, da haka_ . ya biyewa zuciyar ya Ki godewa, kuma ya Ki

tankawa har Alh. ya gaji da jiran cewarsa ya . kada kai ya juya ya fita cikin kada kai da murmushin mamaki

Adamu ma ya dauke ido daga kallon  wucewarsa zuwa kallon mukullan hannunsa, wasu irin abubuwa na zagaya kansa a guje, suna raya masa cewa, ba wai rayuwarsa ce kawai take shirin canjawa ba, shi kansa Adamu ake son acanja. _ Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wai shi ne da ya sha mafarkan bacci da  ido biyu a auren mace daya kacal wato Husna, shi ne kuma yau da auren wata macen wai ita  Salma? Abin sa kuka amma ba hawaye.

Bai bari wata damuwa ta ci Karfinsa ba ya. shirya ya fice harkokinsa. Bai sanar wa

. Salmanu komai game da tarewarsa a gidansa ~ da sabuwar amarya ba, sai da ya tashi tafiya Karfe tara darabinadare, .

“Au! Kai yau fa zaka raka ni siyen baki”

Ya fada wa Salmanu cikin yafe da KoKarin hadiye damywa.

Salmanu ma ya dabe shi cikin mamakin da yake son shanyewa,

“Wai da gaske kake mantawa ka yi ko - kuma tsabar basarwa ce?” Adamu ya hada da dariyar yaKe, “Oho! Ni ma ban san takamaimai a ciki ba” Salmanu ‘ya kame hannu ya rungume a kirji yana bin sa dakallo, To Allah kiyaye hanya, Allah ba da - juriya mai kyau” Adamu ya yi saurin dubarsa saroro, ; “Au wai ba zaka raka ni ba, haka zan tafi. zikau ni kadai?” * ; .
Salmanu yayi dariyar Karfin hali,

- “Kai kadai zaka tafi mana, ka manta kai ~ . kadai Salma ke son gani, ko ka manta sharuddan da ta gindaya maka cewa karka sake kazo mata gida?”dani Adamu ya dinga gyada kai alamar tunawa, ~

“Haka nenatuna”. . .

_ Salmany ya ji-takaicin goyon bayan da Salma ta samo a wajen.Adamu, dubi dai yayi . masa gatse amma bai damu ba ya mayar gaske saboda umarnin Salmanu Www.bankinhausanovels.com.ng 

Amma duk da haka Salmanu bai nuna a fuska ba, sai ya cigaba da dariya yana cewa, “Idan gidan Salma ya zama nasu su biyu Kila a gan ni, in dai zan iya zuwa wajen Husna ba wajenta ba” Nan da nan fuskar Adamu ta rakito walwala, amma dai bai tanka ba. Salmanu bai damu ba ya cigaba da Magana, * « “Amma ‘idan ba ka sami damar auren Husna ba, to har mu Kare rayuwarmu a idon danginka da Salma zamu cigaba da nuna dama munrabu” ~*~ ' Adamu ya banka masa harara tamkar idonsa’zai fado sannan yayi gaba yana mita, - ' “Ka kwana biyu ba ka zage niba dama, yau in ka yi min muguwar addu’a ba laifi, to in ' Allah ya ba ni Husna ka hana mana” - Ba tare da sallama ba ya fice daga dakin. _ Salmanu ya bishi da kallo cikin tausayi tare da Kara Kullatar Salma. . “Allah ya tsine miki Salma” Ya fada a fili kuma har cikin zuciyarsa so yake Allah ya amshi addu’arsa.

Kamar kullum duk wani abu da ya danganci Salma zuciyarsa ba ta _bashi muhawara bare ya tantance ya zaba, kai tsaye daga can saman zuciyar tasa wani ke bashi zabi. ya aiwatar bisa dole. ° ‘ Yau ma ya so ya ji bijrewa da nuna wa Salma iyakarta, amma ya ji wancan Karfin na son matsa masa murnar zama angon da yake tafiya ga amaryarsa, hakan kuwa ya je mata har da siyayyar kaji da kayan jiKa maKoshi. Ya’ dinga nuna mata doki da zumudi tamkar dama ita kadai ce sauran burinsa a duniya ya kuma samu. Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Ban san kana sona haka ba Adamu”

Da kalmomin da ta dinga zolayarsa da su kenan, shi kuma yana amsawa tsakaninsa da_ ‘Allah,
“Yanzu kin sani Salma, ina son ki fiye da -son kowa a duniya”

In ya fadi haka Salma na jin wani munafikin hawaye na kurdo mata ta samu ta goge abinta, abinda take so kenan wato Adamu, ta kuma samu, in ba shi kadai ne burinta a duniya ba tana jin dai ya fi rabi.HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...