NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI                    Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Adamu me ya faru?”

Ta tambaya cikin raunin murya bayan ta fahimci ba shi da alamar niyyar tanka mata,da_alamar kuka ya zo yi mata ba Magana ba. Ya daga jajayen idanuwansa ya dube ta,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Kin karanta takarda ta?”

A nutse ta girgiza kai,

“Ba na jin yaren China”

Yayi Kasa da kai cikin tunani. Ba don ~shegantaka yayi mata’,wannan tambayar ba, yayi mata ne domin-ya kamo bakin zarenta, ~don ta haka ne zai gané matsayinsa a zuciyarta.

Ta dan ja fasali tare da sauke numfashi ta ce masa, ce

. “Mu bar zancen: takarda tunda ga ka gabana, amma abinda, ya fi damuna shi ne ganinka hankali a tashe, wai a haka ka taho tun

_daga gidanku?” -

Kulawarta ta sa ya dan,sami Karfin  gwiwar kada kai yayi murmushin yake,

“Ban ji nauyin ki gan ni a haka ba sai

wasu mutane?” ,
Ta kada kai ba don gamsuwa ba sai don ta yi masa gwaninta,

“Na ji, maya faru?”

“Bai yi Kasa a gwiwa ba ya amsa mata,

“Burikana ne suka tarwatse a Kasa, na san in na tsinto su ba za su yi miki kyau ba, ba zasu dace da irin’ son da nake miki ba... shi ne kawai na debo tsawo na zo neman afuwarki, son da na yi miki ba tare da na samu ba” ’ Husna bata fahimci komai a maganganun Adamu ba sai ba zata same shi ba, cikin Kura masa ido tace, .

~. “Dan Kara bayani ko zan fahimce ka” Kai tsaye ya amsa, . " “Na jima ina sonki baki san ina yi ba,Www.bankinhausanovels.com.ng 

ranar da Allah ya hukunto kuma zaki sani sai aka yi fashin zuciyata da makami ba tare da imani ba, abinda ya faru da mu a ranar nan babu shi a tsarina, kawai mafarki ne daga cikin } munanan mafarkai...”

“Wacce ranar’

Ta tare shi cikin ci da zuci.

Adamu ba ya son hada shirgin lissafinsa da waccan ranar, ba ya son tuna ta kuma baya son abinda zai tuna masa ita, amma tunda shi

ZAMU TASHI 


da zuciyarsa ba sa zuwa wajen Husna da wasa, sai kawai ya ji ya amsa mata kai tsaye,

“Ranar da kika kawo min dinkin nan na bayyana miki abinda ke zuciyata game da ke, zuwan Salma kuma ya sanya na rusa abinda na fada da Karfin hali ba da Karfin imani ba... wallahi bakina Karya yayi min Husna ban taba son Salma ba, ke na taba so son da ban taba yi wa ko wacce mace irinsa ba...”Www.bankinhausanovels.com.ng 

So da tausayi da rashin madafa sun fara gajiyar da Husna dole ta dakatar da shi, cikin sanyin muryar da ta Boye ciwon ranta, —

“Kar ka damu da abinda ya faru ran nan, ni tuni ya wuce a gurina”’

Adamu ya mike cikin rangaji ya fara dan kai komo a gaban Husna kasancewar soron gidan nasu yana da yalwa.

Idon Husna na kansa bata ko dauke fuska, Kwayar idon nata na nuna jiran furucinsa take amma a zahiri lissafin yadda zata nada gammon daukan jidalin rasa shi take, tana son Adamu irin Son da ba ko wane mutum ake wa ba, kai ba ma ko wacce irin zuciya  keyi ba, sai

irin Adamun na musamman da irin tata zuciyar ta musamman. ,

Adamu ya dage ya tsayar da hawayen fuskarsa ya kuma kawo wa fuskarsa jarumta, sannan ya daga ido ya kalli Husna. Suka dubi Kwayar idon juna tawalli! Sai duk wata shakka - ta debe musu, Adamu ya fara jin yayi Magana cikin Kwarin gwiwa da zallar gaskiya, Husna ta fara jin sauraron Adamu cikin yakini da

" gasKata shi. “Furucin da na yi rannan a gabanki a_ ' gaban Salma ya tabbata, bayan balaguron da na yi na sati guda, a yau na dawo na tarar an daura min aure da Salma, yanzu na kawo KoKon bara ta gurin ki, ki ba ni dama na tafi, amma idan na dawo da wani Karfin gwiwar don Allah ki karbe ni a haka ki yi maneji da ni”

Ba don idanuwanta da ke kallon Adamu tsaye gabanta ba, da kuma iskar da take shaka mai alfarma Adamu na shaKa ya fesar ba ce, jin wannan labarin ya isa kai Husna Kasa, amma ta dake tana kallo Adamu cikin rashin hayyaci wani malalcin hawaye na sirnano mata.

Ta ci guru da kyar ta tanka masa,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Allah sanya alkhairi” “Ban fada don ki yi min addu’a ba, na fada ne don ki san abinda na tauye ki da shi na auren wata alhalin ke nake so, na fada ne domin ki ji tausayina akan Kaddarar da ta afko - min, na fada don in kin yarda Kaddarar ce ki karbe ni a haka ki yi maneji da ni...” Ya fada cikin son koma wa hawayen da ya baro. . . Husna ta sake cin wani gurun ta girgiza , “Ai duk ba zasu gagara ba. Yanzu me ka fi ” buKata daga gare ni?” Ya Karaso gabanta murya Kasa-Kasa ya amsa mata, . “Nan da wata biyu zaki karbe ni a matsayin miji? - Wata rahma ta tsirgowa Husna tun daga Kolin kanta har yatsan Kafa, amma dai ta shanye nunawa a fuska bare barin jiki. Cikin nutsuwa ta gyada kai, “Ina jiranka” . “Da gaske kike?” ; . A rikice Adamu ya tambaye ta.

~ Tayi murmushin da ya fi kama da yaKe, ba tare da ta tanka ba. “Na gode”

Adamu ya dinga ambata cikin kada kai har bai san adadi nawa ya fada ba, sannan da baya da baya ya dinga tafiya yana godiyar har ya fice daga soron cikin daga mata hannu. _

Sai da ya gama ficewa sannan Husna ta ji kuka ya zo mata a guje, tuni ta durKushe a

~ gurin ta soke kai a gwiwa tana KoKari hadiye Kararsa. Jin zuciyarta take kamar an bulbula fetur an kyasta ashana.

Wannan wane irin so ne ke_ shan sharafinsa a Kirjinta? Wa ya taba irinsa ya bata labari? Jiya ta gama karatun wani littafi wai shi_. Mafarkin Khadija, ta rantse a fili ta rantse a zuci son Adamu da take ji cikin ranta ya ninka wanda Khadija jarumar littafin ke wa mijinta Sunusi.

Ta ci kukanta a soro ta Koshi sannan ta goge ido jiki a sabule ta kinkimi kujera da tambulan ta shiga gida.

Idon Hajara karaf a kanta lokacin da ta janyo ruwa ta hau wanke fuska,

“Kar dai ke ma zuwa kika yi ku ka hadu ku ka yi ta kukan?”

A Kufule Husna ta masa,

“Kuka mu ka yi amma ba ki jiyo , ba?”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Umma ta wuce tana ce mata,

“To uwar bakar Magana, in -ma haukacewa kuka yi ai ku ta shafa” .

Husna ba ta tanka ba, don dama don ta kashe bakin tsanyarta ta fada mata haka.

**********

Yana fitowa masallaci ya canja riga ya fita ba tare da ko sallama yayi wa Hajiya wadda ~

sam bata yi kwanan kwanciyar hankali ba saboda halin da ta ga Adamu ciki, jiya ko . abincinsa bai karba ya ci ba, illah dai ta san a gidan ya kwana. Abinda ya fi bata haushi ma shi ne, da ta kira Alh. ta yi masa wannan Korafin sai ya nuna halin ko in kula. “In dai wannan banzan yaron ne mai halin - _ canje-canje ki bar shi kawai, ni ne maganinsa”

Kalaman da ya fada mata kenan wadanda haushi ya sanya ta shiru ba don wai ta sallama ba.

Da safe ta yi ta zuba idon ganin shigowar Adamu bayan dawowarsa masallaci_sallar asuba kamar yadda ya saba, sai ta ji shiru. Haka ta zauna cikin fargaba da ci-da-zucin kallon Kofa har hantsi ya daga bata ga Adamu ba, ta lallaba ta je dakinsa sai-ta tarar a garkame da kwado, nan fa ta fara tsoron ko ya koma gidan jiya ne, sai sannan ma ta tuno ko tambayarsa inda ya shiga tsawon sati ba a bata damar ta yi ba.

Da hantsin Alh. da kansa ya kawo mata abinci. Ya gan ta cikin rashin walwala amma sai ya share don ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta Koki.

_ “Daga nan dorayi zan wuce”

Ya kamo bakin zarenta da haka bayan ya lura cin maganin nata yayi yawa.

Ta motsa bakidakyar tace, —

“Me zaka yo?” Ya amsa mata

“Gidan da wadancan yara zasu zauna zan sanya a yi wa gyara, Adamu gata yayi masa yawa, jiya na yi masa maganar ya karbi mukullin ya je ya dubo... kai har maganar kudin da nace zan bashi ma bai bi ta kai ba, na rasa wane irin yaro ne Adamu...”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Haushi ya hana Hajiya barinsa ya kai Karshe,

“Idan bai koma inda ya fito ba ko? Ni tun safe ban gan shi ba”

“Zai dawo ne, ai giji lahira ce”

Alh ya fada cikin halin ko in kula don ya fahimci Hajiya bayan Adamu take son bi akan maganar auren nan, shi kuma jin kansa yake akan maganar auren nan babu wanda zai saurara ya tankwabe shi.

Jin hakan ya sanya Hajiya jan bakinta ta tsuke, don dama ita mace ce mai kawaici da hadiye damuwa, in dai ta lura za a daga matahankali sai ta sakar wa mutum.

Alh. ya gama kame-kamensa ya mike yana ce mata,

‘“Dorayin zan je na kula da komai, har kayan shagon zan siyo komai in zuba masa,

Allah basshi idan ya zo in zai gode min  ya gode koya tsine  min” “To Allsh tsare™ Hajyar ta fada a gajarce.

********

Adamm ya tarar Salmanu ya ci Make Up ya zama rifaifen boka yadda in ba su da suka . yi masa farin sani ba kuma suka san dawan garin ba, ba za. a gane shi ba. Yayi tirgiijin a cikin ,,,,, safi hade da wando, an masa tafka tafkan kwalen farin fenti da ja a goshi da kunci, haka ma __kansa ya sha askin kwalkwal an adance shi ta tattoo din kan mutum. Salmanu ya canja kala daga Salmanu zuwa wani shaidanin boka duk aikin Tanimu ne. Suna tsaye da Tanimu yana yi masa lissafin mutanen da ya gayyato masa yau Salmanu ya shigo, “Ka ga akwai matar Aramman unguwarmu, wai ta ji labarin zai dauko uwarsa daga Kauye, uwar tasa kuma muguwar

masifaffiya ce ga jarabar sa ido, shi ne wai take so ta zo a toshe zuciyarsa a hana shi kawo ta....”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Salmanu ya tare shi cikin yamutse fuska,

“Matar Alaramma kuma Tanimu zaka kawo mana? Mijinta malami sannan kuma na san ba Karafa garesu ba, mu fa manyan harka mu ke so”

Cikin tsananta dariya Tanimu ya tare shi,

“Kai matsalarka gajen hakuri aradun - Allah, yo malanta ba yana kan tasa kujerar ba ne kai kana taka?” .

Salmanu ya sake tare shi rai a Bace, ;

“An ji, ni fa ba zan yi harkar naira hamsin ko dari ba”

, “Shiyasa ai na ce ka fiye gajen haKuri, in ka ga dama idan ta zo ka caje ta dubu talatin, na rantse da Allah zata baka... abincin siyarwa fa ta ke, duk anguwar nan ba kamarta, motar doya ake sauke mata duk wata, buhun shinkafa kuina kwana biyu yake mata...”

Fuskar Salmanu ta washe, “A zamu tafi da ita, ta Zo kawai™ . Suka tuntsire da dariya suka tafa.

Tanimu ya cigaba,

“Sai Alh. Habu mataimakin sakatarcn kamafanin tabarma wanda yake son wai ka kashe masa sakataren shi ya samu ya hau kujerar”

Salmanu ya doko wata Katuwar ashar,

‘“‘Wannan da zan iya Allah shi zan kashe”

Tanimu na dariya ya amsa,

. “Tunda ba zaka iya ba, sai ka karbi kudinsa ka sallame shi yayi gaba, randa Kwanan sakataren ya Kare sai Allah ya kashe

" masa shi”

Salmanu yace, °

“Wannan riKe shi zamu yi, in bai wasa ba Allah sai na talauta shi” “Oho maka kuma” -

In ji Tanimu, sannan ya cigaba,

“Sai kuma Hajiya Kumbo, ita kuma Mijinta ne yayi mata kishiya a Boye, bayan ta sakankace wani boka yayi mata alKawarin daga ita ba zai iya kallon wata mace da sunan so ko aure ba, kwatsam sai ga mijinta yayi aure a boye, bayan ta gano shi kuma yake son raina mata hankali wai amaryar zata tare, ta ce zata Www.bankinhausanovels.com.ng 

zo wajenka da neman taimakon, har abada kar Amarya ta tare, ya bar ta tayi ta lilo a gidansu in ma rabon ‘yan dozin ne a tsakaninsu duk tayi ta haihuwarsu a gida...”

Ya sauke numfashi ya dubi Salmanu,

“Ita ma wannan matar tana da Dala.

“To an gama, ta kawo kuka gidan mutuwa.

Suka sake kwashewa da dariya. Sai lokacin Salmanu ya kula cewa Adamu fa ya, shigo da wata irin fuska wadda ta kamata a saurare shi, musamman da ya kasance duk hirar da suke ya ci magani ya Ki sanya musu baki alhalin da idan ada ne ya fi kowa shan dariya,

“Kai kuma fa?”

Tanimu ya tambayi Adamu, da alama kuma ba jiran amsarsa yake ba, don bai jira cewarsa ba ya fice da sauri yana cewa,

“Ni fa ban karya ba, bari na zagaya wajen mai shayin can” ' .

“Salma ce ko?”

Tambayar da Salmanu ya yi wa Adamu kenan.

Adamu da yake jin ya zo da Kwrin gwiwa ya yi taku gaban Salmanu ya tsaya cikin nuna da gaske yake,

“Ban taba nutsuwa da sana’ar nan da ka kira ni mu yi ba sai yau, na zo da imanina da yarda ta duka, ba mai yi muku maganar aljanu ba, ba yi muku basaja ba, ba dan koren boka ba, komai ake so na yi zan yi, don na shirya zama ko mai zan zama in dai zan sami abinda zai shigar da Husna rayuwata, nan da wata biyu ina neman kudaden da zasu aura min ita a

" matata ta biyu, an min danyen hukunci a jiya an aura min Salma a matsayin ta daya....”

“An aura maka Salma?”

Salmanu ya tambaya cikin Karaji tare da jin wani irin mugun takaici ya naushe shi a Kahon zuci,Www.bankinhausanovels.com.ng 

Adamu ya fara naushin hannu cikin alamar fishin da yake ji yafi na Salmanu, kuma danyen hukuncin da yake son dauka zai iya fin nasa in da sarari zai samu. Ya ce,

“Eh. Salma suka aura min don su nuna sun ciyar da ni na girma, ba ni na wayi gari na ciyar da kaina ba”

Ganin nasa fishin ya kai haka ya sanya Salmanu rage nasa, ya kawar da kai yana kadawa,

“Ban cika ganin laifinsu kamar na Salma ba...”

Cikin sikewa Adamu ya tare shi,

“Don me? Don in ba su aura min ita ba zata iya aura min kanta? Kar idonka ya rufe Salmanu don kana Kin Salma bisa Kiyayyar da na yi mata a baya, amma in neman me laifi ake ba sai an wani sha wahala ba ana samun Alh an gama.” "

” Ya zarce da yin Kwafa cikin Kufula, . “ Amma ba komai zan nuna masa tawa iyawar wallahi”

“Ni kuma zan nuna wa Salma tawa iyawar’

In ji Salmanu da haushin Salma ya sake

‘ kashe shi, wato har Adamu ya. daina ganin laifinta da zargin ta yi masa wani siddabarun? In haka ne ta ina ma zai faro wa wannan matsalar tasu tunda mai matsalar bai dauke ta matsala ba?

Adamu sai yi wa Salmanu duban rashin fahimta yake bisa furucinsa na nuna wa Salma iyakarta, har dai da Salmanu ya kara masa haske cikin raunin murya,

“Ka da ka manta fa yanzu Salma matata ce s

. Salmanu ya bugi kafadarsa cikin kuna halin ko in kula,

“Oh na tuna fa! Kuma ba zan sake mantawa ba”

Adamu zai yi magan Salmanu ya tare shi,

“Mu share wannan hayaniyar Adami mu zo mu yi abinda ya fi kamatarmu, ba kai kadai zaka nemi kudin da zaka auri abinda kake so ba, har ni idan’ na nema zai iya zama naka, saboda haka ka kwantar da hankalinka in dai matsalarka a Husna ita ce kudi to zamu taru mu yi ta nemansu ido rufe , ka cire damuwa ka ji gwarzon aminina?” . -

Ya Kare maganar da zolaya.

Dole ba don Adamu ya so ba ya yi dan yaKe, sannan ya fitar da dariya da Karamin sauti. ©

Salmanu ya mika masa hannu suka tafa sannan suka saki ihu. . .

“Kafin wancan Tanimun ya dawo daga Shan shayin ni bari na zagaya baya na yi wani abu...” in ji Saimanu

Adamu ya tare shi, ; .

“Ka zagaya baya ka sha Sigari...”

“Allah ya kiyaye. ji nake na ci maka alwashin  daina shanta kai daga Kauye kake” ko warinta baka so. Kai dai ka zauna nan ya dawo yayi maka naka Make Up din” .

Dole Adamu ya dara yana bin Salmanu da kallo cikin wani irin Kaunarsa, ji yake ban dashi da Husna ba shi da kowa a duniya wadanda suke iya son abinda yake so, suke kuma iya

yunkurin ba shi abinda yake so. °
.
++++++++++

Karfe goma sha biyu da rabi daidai « ‘bakuwarsu ta farko ta zo, maimakon matar * Alaramma Hajiya Kumbo ce ta fara zuwan Www.bankinhausanovels.com.ng 

Salmanu na hakimce kan shimfidar buzun da suka lullbe da fatar Maciji, ya wadatu da wani irin kwarjini irin nasu na bokaye, sai muzurai yake.

Adamu kuma na daga can uwar dakin riker da tiyon da suka huda bango suka zura daidai saman kan Salmanu amma sun yi wa gurin basaja da adon kayan tsubbace-tsubbace.

. Ba kadan ba Hajiya Kumbo ta ji shakkar wannan Boka, sannan ta ji yakinin tabbas in

» wannan bokan yayi aiki ba za a tarar da wasa ba.

Tunda ta shigo Salmanu bai daga kai ya kalleta ba, illa ya Kurawa fararen takardun Www.bankinhausanovels.com.ng 

. gabansa idon.

Hajiya sai dan nishi take na baKunta da nuna sallamawa wannan hamshakin Boka, wanda a labarinsa da aka bata an ce ba a fara yi masa Magana, shi yake fadar dukan abinda ya kawo mutum sannan ya magance masa damuwarsa.

Kamar Salmanu ya san abinda take tunani ya dauko daya daga cikin fararen takardun nan . ya mika mata. . .


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...