NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI                   Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Alh. ya shige bandaki shi kuma ya nemi kujera ya zauna ya ci magani yana ta faman muzurai da saKe-sake har Alh. ya fito daga bandakin ya hakimce a kujera cikin kalar nasa « nuna bacin rai

“Ba na so in ce daga ina kake Adamu, don kar in ji amsar rainin hankali ta janyo in tashi in kashe ka da mari” Adamu yayi fuska iyakar fuska, :

“Ni dai namiji ne, bare a ce yawon duniya _ na tafi” .

Mamaki ya cika Alh. wannan fa shi ake kira Karfin hali wai barawo da sallama, daga bisani kuma sai ransa ya baci ya Kura wa ido Adamu cikin bacin rai.

Adamu ya muskuta ya sake muskutawa yana wani basarwa, - .

“Wallahi fashina aka yi” -

.Alh. ya jima bai tanka ba saboda tsabar haushi ya ma rasa me zai cewa Adamu, dama abinda ya guda kenan, ya san Adamu zai iya * zuwa masa da rainin hankalin da zai tunzura. shi, ilai kuwa. Sai faman kokawar hadiye fishinsa -yake, har ya samu ya hadiyu, ya sassauta fuska ya dubi Adamu, Fashi wane iri, su waye suka yi. fashin . naka?” .  Adamu ya sake kawar da kai yana cin magani, _ * “Masu fashin mutane mana, sun ga ba zan yi musu amfani ba suka dawo da ni”

Wannan tatsuniyar ta gajiyar da Alh. sosai, —ya ga kawai mafi a’ala ya rife babinta ya dauko babi na gaba.
- Ya girgiza kai cikin halin ko in kula, . “Allah sarki, to Allah kiyaye gaba”  Amin”?

Adamu yayi fuska ya amsa. .

Alh. ya sake gyara zama sannan ya gyara murya,

“Na zaci lafiyarka lau ka guje mu shiyasa har na yi maka wani karambani”

ZAMU TASHI 


Adamu ya dube shi cikin rashin fahimta, amma bai tanka ba.

Alh. bai damu da shirunsa ba ya cigaba da  Magana.. ~

“Kodayake ba za’a kira shi da karambani ba illa son in faranta maka ko kuma in cika maka wani burinka da <kake fatan tabbatuwarsa”’

Yayi shiru yana jan iska.

Yanzu Adamu ya tattara masa hankalinsa ~ gaba daya, cikin jin dokin jin burin da Alh. zai ce ya cika masa, shi dai ya san a duniyar nan ~ ba shi da wani buri da ya wuce mallakar Husna da kuma zama attajiri domin ya jiyar da ita

. dadi, su ne manyan burikansa, duk sauran da zasu biyo baya Kanana ne mahadin rayuwa_ kawai, amma me!? Kawai sai Alh. ya kunno masa da hagun wannan buri.

“Maganar da muka yi kwanaki kai da Salma, cikin ikon Allah na yi iyakar Koarina na cika muku wannan buri, da safiyar yau aka daura muku aure” -

. Adamu ya ji tamkar Alh. ya wurga shi a tekun ruwan zafi, nan take ya fara hada gumi

tamkar fankar da take juyawa ita ma zafin take bayarwa sai dai harshensa ya sarke, duk KoKarinsa na yayi furuci sai ya kasa illa sa wa Alh. ido yana kallo. ’

Alh. ma ya Kura masa ido,

“Yana lafiya na ga kana hada zufa?”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da za a sakar wa Adamu harshe babu abinda zai hana shi tura wa Alh. ashar, amma an daure harshen don haka ba shi da baka sai__ kunne. .

Alh. ya sake kada kai yana cigaba da nuna mamaki

“Na san ban maka ta’addanci ba Adamu, godiya na cancanci ka yi min ba wannan kallon ba” ; _

Har yanzu Adamu ya kasa _ tankawa, _lokacin da ransa ya raya masa ya tashi ya sa wa Alh. naushi ma sai ya ji duk lakarsa ta mutu, tamkar ko hannunsa ba zai iya dagawa ba.

Da Alh. ya Karaci nuna mamakinsa sai ya daga waya ya kira Sa’a ya ce ta turo masa Salma. ’

Kafin Salma ta zo sai da ta gama tsubbace tsubbacen da boka ya bata, ta taho da maganin

da ya sanya ta barbadawa a inda Adamu zai taka, ta barbadada a Kofar dakin sannan ta yi fuska ta shiga kai a Kasa tana sallama.

Har yanzu harshen Adamu a daure yake, amma idon zuciyarsa bai kasa ganin mugun kyan Salma ba, ya ji a guje wani irin shauki yana zagaye ilahirinsa, sai dai ba bakin tankawa. Ya dauke ido daga kanta bayan ta zauna ya mayar da ganinsa ga Alh. wanda ya fara koro musu nasiha. Ya yiwa Salma shaidar * haKuri, ya yi wa: Adamu ta mayar da kai ga abinda ya sanya gaba, ya ce, .

‘“To ke Salma ina fatan ki dore da Www.bankinhausanovels.com.ng 

haurinki da na san ki da shi, kai kuma Adamu ina fatan za mu ga jajircewarka da taurin kanka wajen kula da iyalinka tare da yi musu adalci” - - . Ko nishi Adamu yayi yunKurin yayi ya - kasa, ya’ dai bi Salma da kallo wadda farin cikinta ya kasa boyuwa lokacin da take kada kanta a Kasa alamar bayar da amsa cikin kunya. -

Wannan shirun da kallon galala din na Adamu ya ishi Alh. amma babu yadda ya iya haka yayi ta yi musu nasiha kana ya sallami

- Salma ya Kara mayar da hankali ga Adamu,

“Karamin gidan nan nawa da na siya kwanaki a Dorayl, anjima zan baka mukullinsa ka je ka duba ‘yan gyare-gyaren da ba zai ci kudi da yawa ba a samu a kwaskware shi ku tare nan da sati guda”

“Hmmn

Wannan karon Adamu ya Kwato nishi da

. Kyar. - Alh. ya sake shanye haushi ya cigaba, . “Ka san gidan akwai shago a Kofar gida ko?” Gyada kai kawai Adamu yayi._ Alh. yace, -“Na lura dan zagayen unguwar gaba daya babu shagon sayar da kayan masarufi, saboda_ - haka tunanina ya fada kan cewa sai na baka jari ka zuba kaya ka dinga saidawa, daidai talaka ° dai ya ishe ku cin abinci da toshe wata barakar” . “To” . In ji Adamu Alh. ya dan ja fasali yana kallonsa, yanzu ya fara zargin anya kansa daya kuwa? > _ Kodayake kafin yayi masa zancen aurensa da Www.bankinhausanovels.com.ng 

Salma ya zo da bakinsa da cin maganinsa har ya dan sassaki rashin kunyarsa da rainin hankalinsa. Kenan Karamin tabin kwanyar da ya same shi na nan take ne bayan jin an aura masa Salma. To bakin alKalami dai ya riga ya bushe, aure ne an riga an daura, yayi haukansa ya warke. Don haka Alh. ya share shi ya cigaba da yi masa bayani,

“Ta bangaren Salma kuma kar ka damu, — na bawa Sa’a ‘yan wasu kudi ta y mata siyayya, babu abinda na ke nema a Bangarenka ~ sai halarci ta hanyar yi‘wa Salma adalci da riKe ta bisa amana, ka ga marainiya ce bata da kowa sai mu wanda ko ba kai ka aure ta ba kai mai tsayawa ne ciki-ba-hatsi ba ka Kwatar mata ‘yancinta idan mijin da ta aura ya danne”’

Da wannan nasihar Alh. ya sallami Adamu ya fito yana layi ya doshi gidansu. Zuciyarsa fanko ce baya tuna komai ko saKa komai, amma

dai wani radadi-radadi daga can Kasa yana

fuzgarta, sai dai ba ya nisa yake cin tuntube ya nuna ba komai. "

. Kafin ya je gida ya dinga jin kansa yana

wata irin Kara tamkar yana shirin bindiga ko

kamawa da wuta, kawai sai ya tsaya wani kanti a unguwarsu ya sai fuyo wata mai dankaren sanyi har leda hudu ya shiga da shi gida. .

Hajiya na kakabin murnar zuwansa da Kokarin fashewa da kuka saboda ganinsa a hargitse, shi kuma yana mika mata ruwan ya tsuguna a gabanta cikin raunin. murya yana cewa,Www.bankinhausanovels.com.ng 

- “Hajiya zuba min ruwan nan a tsakar kaina kar ya kama da wuta”

* Jikin Hajiya na bari ta karbi ruwan ta dinga fashe masa su a aka har leda hudu ba tare da ta damu da jika falonta da take yi ba ta dago kansa cikin fuskar alhini da jimami tana kallonsa, sannnan cikin raunin murya ta ce,

“Adamu ina ka shiga ka bace?”

_ Maganar da tayi cikin rauni ta Karasa raunata tasa zuciyar, ya ja jiki da Kyar ya isa kan tabarma ya zube yana shassheKar kuka.

Hankalin Hajiya ya kai Kololuwan tashi, da sauri ta durKushe a gabansa tana tambayarsa cikin rudewa,

“Adamu me ya same ka?” ,

Ya ji tausayin kansa da na Hajiyarsa wadda ta damu da shi ya ‘mamaye ransa, ya saki kuka mai nuna tsanantar Kunan rai,

“Hajiya Alh. yayi min auren da ba zan taba farin ciki da shi ba har abada” :

Kafar Hajiya na rawa ta silale ta nemi gurin zama tana sauke nishi cikin sauri,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Dama ba kai ka bashi damar ya aura  maka Salma ba? Dama baka sonta Adamu?”

Ta tambaya a rikice, .

Ya amsa mata da rauninsa da kumaiyakar gaskiyarsa,

“Nine, amma ban san abinda ya shiga cikin kaina na fadi hakan ba, wallahi ba Salma ce zabina ba, ban taba zabarta ba, ban taba mafarkin aurenta ba, kuma ban taba fatan ko a mafarkin in aureta ba” .

Kan Hajiya ya so ya shiga dubu duk da a iyakar imaninta ta san iyakar gaskiyr Adamu kenan tunda yake furucinsa cikin kuka, sai ta rasa da Kalmar da zata yi amfani wajen karbar wannan Kalubalen nasa. Ta cigaba da zura masa ido galala shi kuma ya cigaba da. shassheKar kuka kafin ya zarce da cewa,

“Na kasa cewa Alh. ba zan iya rike auren da yayi min ba, amma duk lokacin da kika sami sarari ki sanar da shi, ni dai ya tauye rayuwata ya kuma cutar da ni, ba Salma nake © so ba, wadda nake so ina yi mata son da ko wane hali aka rataye zuciyata ba za’a iya raba ni da son ba... kuma in na sami sarari zan iya ko ma menene da zai iya samar min da ita” . Bai jira cewar Hajiya ba ya mike yana . niyyar barin dakin. Gabadayan kan Hajiya ya kulle, a gigice , take kwarai, amma dai maganganunsa na Karshe sun zabure ta Karfin halin miKewa ta riko rigarsa kafin ya fice, cikin rawar murya ta ce, . . “Adamu zo ka fada min, wa kake so?” Ya dakata ba tare da ya juyo ba yace _... mata,“Husna nake so” . “Wacece haka?” _ Ta tambaya cikin nuna rashin fahimta. Ya kada kai idanuwansa na cigaba da zubar da hawaye, zuciyarsa na wani irin Kuna, .Www.bankinhausanovels.com.ng 

ya koma ya zauna yana kallon Hajiya da ta tsaya kansa hankalinta a tashe,

“ita ce wadda tun tuni nake maganar ina so, akanta na ki karatun boko don in sami kudin d azan riKe ta.... Kai Hajiya ko me na zama akanta na zama, ko kuma nake shirin zama... ina fada miki wannan ne dan ki gane ban fara sonta don in daina ba...”

‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”

Kawai Hayjiya ke Ambato cikin tafa hannu = mai nuna alhini da nadama, tamkar ita ta yi wa Adamu auren dole take ji cikin ranta, ta kasa = yafewa kanta sakacin da tayi aka aura masa. abinda ba ya so.

Ta matsa can jikin bango ta jingina da shi,

“Adamu ni ban san abinda zan ce maka ba, hakuri zan baka ko kuma sakacinka zan nuna maka?”

Ya sake miKewa tamkar kunama ta dalle shi yana girgiza mata hannu,

“Kar ki ba ni komai Hajiya, ko Husna kika ba ni a yanzu ba zaki birge ni ba, don na san . Husna zata rage darajar son da ta ba ni in ta. tarar da wadda Kaddara ta aura min wato

Salma, duk ku riqe abinda zaku fada min don ban ki karbar abinda aka ba niba wato Salma, amma dai ba zan kasa sanar da ku an cuce ni ba, ba zan kasa fadar ba a yi min daidai ba....”

Ya sake ficewa daga dakin cikin fishi.

Wannan karon Hajiya bata iya riKo shi ba, duk da ta fahimci ba cikin hayyacinsa yake ba, yakamata ita ma ta bar shi ya huce, yadda zasu fi fahimtar juna. . i ;

” Haka dai ta zauna tana ta kakabin alhini da fargabarta har lokacin da ta yanke shawarar * daukar waya ta kira Alh. su tattauna. .

*********

Adamu bai damu da goge hawayen fuskarsa ba ma bare ya kintsa tafiyarsa ta Boye rashin nutsuwarsa ko tashin hankalinsa Www.bankinhausanovels.com.ng 

A dazu ya gama Kaddara kwanyarsa ta tashidaga aiki, amma a yanzu da ya gan shia. hanyar gidansu Husna ya tabbatar ko  kwanyarsa zata manta komai ba zata taba manta Husna da abinda ya shafe ta ba. , .

Har ya-isa Kofar gidan bai san abinda ya kawo shi gurinta ba, amma yayi imanin tunda zuciyarsa ta kawo shi ta san abinda zata fada.

A hargitsensa ya sami yaro ya tura shi gidan yayi masa sallama da ita.

Husna na kan kekenta da ta fito da shi tsakar gida tana ta faman dikin, yaron ya shiga da sallamarsa, ta toshe kunnuwanta da head phone tana sauraron wakoKin da ba su fice na soyayya ba, zuciyarta a rude take da tunanin ‘* Adamu har kwalla na tsattsafo mata tana goge abarta a saye. Kuma da yake tana hadawa da_= ~dan rausaya alamun tana jin dadin wakar da take sauraro babu wanda ya damu da gane cewa wuya take sha.

“Wai Husna ta zo”

Yaron ya sake, maimaitawa bayan yayi Sallama duk Husna bata ji ba, sai da Hajara ta fito daga kicin ta tambayi yaron,

“Wanene yake kiranta?” ~

Yaron da yake irin fadi ba a tambayeka bane ya ce,

“Wani saurayi ne, baKi mai dan kauri da tarin gashi, kuma na ga ma kamar kuka yake?”

~ _Kukan da aka ce yana yi ne yayi mugun  jan hankalin Hajara ta yafito Husna cikin firgita, . #Ke shashasha, ki saurari yaron nan ya zo da maganar a kasa kunne a saurara” Husna ta ji haushin kiranta shashashan da  Hajara ta yi, ta debo mita zata sauke Hajara ta  tare ta, . , “Yanzu haka shi ma me neman naki rashin _ kunyar kika yi masa, na san yanzu sai ki zage ni... Sai kawai Husna ta saki baki tana kallonta - . cike da Kunan zuciya. . Hajara ta juya tana cewa yaron, “Ga ta nan ka sanar da ita saKon” Tana rufe baki yaron ya furta, , ’ “Wai Husna tazo in ji wani:..” Shi ma Umma ta tare shi, “Shi wai wa? Ka sanar da ita waye” ' Yaro kuwa ya gyara murya ya kwatanta mata Adamu. . " Tunda ya ambaci' mai tarin gashi ta ji numfashinta na neman daukewa, -zuciyarta ta  dinga bugawa da sauri da sauri tamkar tana ambatar mata, Adamu ne! Adamu ne!

Hajara ta zuba idon ta ga Husna ta kora mai kiran sai ta ga nan da nan ta saki dinki ta hau janyo ruwa tana wanke Kafa, a gurguje ta dauki hijabi ta yi waje.

Kamar yadda ta zata, Adamu ta tarar wujiga-wujiga da shi tamkar an finciko shi daga bakin kura ba, ga shi ba, ba ga zuciyarsa ba wadda fuskarsa ta nuna alama, sannan itama kanta bata sha wahalar gane cewa kuka yake ba. ; .

Ai jikinta na bari tamkar ta riKo hannun Adamu ta yafito shi,

“Shigo shigo nan Adamu”
Ba ta yi gaba ya biyo ta a baya ba sai ita ta sanya shi gaba suka shiga soron. Da sauri kuma ta shige cikin gida tanace masa,

“Bari na kawo maka kujera”

Adamu ya kasa Magana ne saboda yadda kuka ya Kara cika kansa. Ya tabbatar barin jikin da Husna ke yi da shi na so ne, to yaya zata ji idan ta ji cewa an aura masa kunduba Www.bankinhausanovels.com.ng 

- Salma? Duk yadda yayi Kokarin ya dake wa

wannan tausayin sai da ya ci Karfinsa, hawayensa suka Kara araha a fuskarsa dan ma yayi namijin KoKarin hana sautin kukan fitowa.

A haka Husna ta fito ta same shi, tana dauke da kujerar zaman dinkinta da kuma pure water mai dan Karen sanyi hade da tambulan din roba.

Ta kula da Karuwar damuwarsa kuma

. Zuciyarta ta Kara rauni, sai dai bata nuna hakan ba. Ta dire masa kujerar cikin kuzari ta nace. masa, ; “Zauna Adamu” Ba musu ya zauna.
Ta huda pure water ta tsiyaye shi a tambulan din ta miKa masa,

‘Ungo sha ruwan sanyi hankalinka ya dan kwanta sai na ji me ke akwai” .

Adamu ya kasa Magana, kirkin Husna ya sanya shi jin lallai an tafka masa asarar masoyiya, asarar da ba zai taba fanshewa ba.

Sai da ya shaye ruwan tas, bata bar shi ya ajiye kofin a Kasa ba ta miKa hannu ta karba idanunta akansa tamkar in ta rufe ido zata bude ta ga ya Bace, .

“Adamu me ya faru?”

Ta tambaya cikin raunin murya bayan ta fahimci ba shi da alamar niyyar tanka mata,da_alamar kuka ya zo yi mata ba Magana ba. Ya daga jajayen idanuwansa ya dube ta,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Kin karanta takarda ta?”

A nutse ta girgiza kai,

“Ba na jin yaren China”

Yayi Kasa da kai cikin tunani. Ba don ~shegantaka yayi mata’,wannan tambayar ba, yayi mata ne domin-ya kamo bakin zarenta, ~don ta haka ne zai gané matsayinsa a zuciyarta.

Ta dan ja fasali tare da sauke numfashi ta ce masa, ce

. “Mu bar zancen: takarda tunda ga ka gabana, amma abinda, ya fi damuna shi ne ganinka hankali a tashe, wai a haka ka taho tun

_daga gidanku?” -

Kulawarta ta sa ya dan,sami Karfin  gwiwar kada kai yayi murmushin yake,

“Ban ji nauyin ki gan ni a haka ba sai

wasu mutane?” ,
Ta kada kai ba don gamsuwa ba sai don ta yi masa gwaninta,

“Na ji, maya faru?”

“Bai yi Kasa a gwiwa ba ya amsa mata,

“Burikana ne suka tarwatse a Kasa, na san in na tsinto su ba za su yi miki kyau ba, ba zasu dace da irin’ son da nake miki ba... shi ne kawai na debo tsawo na zo neman afuwarki, son da na yi miki ba tare da na samu ba” ’ Husna bata fahimci komai a maganganun Adamu ba sai ba zata same shi ba, cikin Kura masa ido tace, .

~. “Dan Kara bayani ko zan fahimce ka” Kai tsaye ya amsa, . " “Na jima ina sonki baki san ina yi ba,Www.bankinhausanovels.com.ng 

ranar da Allah ya hukunto kuma zaki sani sai aka yi fashin zuciyata da makami ba tare da imani ba, abinda ya faru da mu a ranar nan babu shi a tsarina, kawai mafarki ne daga cikin } munanan mafarkai...”

“Wacce ranar’

Ta tare shi cikin ci da zuci.

Adamu ba ya son hada shirgin lissafinsa da waccan ranar, ba ya son tuna ta kuma baya son abinda zai tuna masa ita, amma tunda shiHMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...