NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Anti Sa’a bata yi mamakin abinda ta ji ba domin ita tayi wa aikin bokanta farin sani, ta jima da imanin ko ba dade ko ba jima sai Adamu ya kamu a tarko Salma kirif! Ta nuna jin dadinta ainun Sannan ta cewa Salma,Kin san Allah? Da mun sani ma ba mu shigo da Alh. cikin maganar nan ba, ke kanki kin isa raba  Adamu da Salmanu, Na rantse miki da Allah idan kika ce kar ya sake kula shi sai ya hanu”  Salma ta cika da jin mamakin jin abinda. Antinta ta ce, cikin sakin baki ta ce mata, _ “Da gaske Anti?” anti  Sa’a tace, “Har fa rantse miki na yi - Salma ta rausaya kai, -

Www.bankinhausanovels.com.ng “Ai al’ajabi ne yake ‘neman kashe ni, yanzu duk fandarar Adamu ‘zan iya , dankwafewa?” ; _ Sa’a ta jinjina kan jin dadi hirar, ta ce, ‘ “In kina shakka ki gwada daga kan maganar Salmanun nan, kar ki bar shi da . maganar Alh. da zai iya watsarwa idan ya tashi daga gabansa, ki shiga maganar zaki ga abinda » zai faru” _ - - Salma ta kasa Magana sai jinjina kai « kawai, lamarin ya girmi tunaninta, in a da can wani ya sanar mata Adamu zai iya zama haka a hannunta zata musa masa ko da kuwa tsafe shi - za’a yi ba wai Karamin alhaki boka ba , Babu fargaba ko kadan a tare da Adamu ya shiga falon Yayansa domin dai shi ya san ~ » bai yi komai ba bare ace akan sa aka kira shi a ' balbale shi da fada, amma ga mamakinsa Salma na shigowa dakin ita ma ta zauna sai yaji gaba daya Kwanjinsa ya zube, ya dinga jin”. . rashin katabus” hade da faduwar gaba

ZAMU TASHI 

  musammman da ya saci kallon Salma ya ganta. tana kuka, sai ransa ya ji a duniyar nan bai taba cin karo, da wani abu mai ciwo irin zubar ° hawayenta ba, amma dai haka ya daure ya sunkwi da kai gaban yayansa wanda ya dauko ~ - + jawabin da ya fi zubar hawayen Salma buga 'masa zuciya, “Da kai Salmanu ya hada kai ya kawo mana ta’addanci gida? Kana sane da ya tare

‘Salma jiya ya aza mata wuka a maKogwaro ' ” yana mata kashedin ta fita hanyarka Adamu ya ji kansa yayi masa wani mugun nauyi, da-kyar ya cire kai ya dubi Alh. sannan ~ ya mayar da ganinsa ga Salma wadda ke ta faman matsar hawayen Karya. Da’ sauri ya ‘ girgizakai yace,~“Salmanun? Wallahi ban san da maganar ba Alh.”  “To yanzu ai ka sani” _ ' Alh. ya fada cikin daure fuska. Adamu bai damu da cin maganin Alh. ba shi ta masoyiyarsa Salma yake, wadda yake jin kamar ya shiga zuciyarta ya sanyaya mata rai ya hana ta kukan da take, ko kuma ya nuna

Www.bankinhausanovels.com.ng mata lallai ba da hadin kansa aka cutar da ita ba kuma ba za a taba hada kai da shi a cuce ta ba bare har da hukuncin dora mata wuka a ' wuya, shi mai dora mata wuKar a wuya ma ya gani ba sai inda Karfinsa ya Kare ba ko kuma . ayi mutuwar kasko. Cikin mugun sanyin jiki ya mayar da kai . ga Alh. ya ce, “Wallahi Alh. ba ni da masaniya, to wai laifin me tayi masa da har zai tare ta da wuKa ~ kamar wani shirin fim?” “In kana shakkar Karya ta yi masa ai ga ka - nan sai-ka tambaye ta...” . A ladabce Adamu ya tare shi, ~ . ‘Ni ba haka nake nufi ba Alh. tsabaragin beken Salmanu na gani da haukansa wa zai zuga shi tare mace da wukKa, macen ma wai Salma wadda ya san dangantakata da ita” _ “Kila sholishon nasa na sabo'ya sheKa” . Alh. ya fara sakowa saboda imanin da - yayi babu hannun Adamu a abinda Salmanu yayi tunda yake wannan fitittikewar, sai ya hau bashi labarin abinda ke akwai kamar yadda Sa’a ta sanar dashi, ya KarKare da cewa,

Www.bankinhausanovels.com.ng Ni mamakina shi ne, menene ribar Salmanu in ya raba ka da Salma? in kuma ka aure ta me Zai rasa?”  Adamu ya rausaya kai, ya rasa abin cewa, a can cikin kansa ya ji wata shegiyar gaĎa ta Barke, ya rasa me ya tashe ta,. amma dai haushin Salmanu ma ya kunno, don ya ji mugun ciwo abinda yayi, ji yake kamar ma abotarsu ta zo Karshe daga yau din nan. Yana can duniyar tunani da lissafi ba ya tare da  dogon sharHIn da Alh. ya kunno wanda yake nufin lallai ya fita hanyar Salmanu ba mutumin kirki ba ne, kuma dama hausawa sun ce zama -  da madaukin kanwa yana kwo farin kai, lallai . ko yanzu bashi da irin tarbiyyar Salmanu idan suka cigaba da tafiya nan gaba za a wayi gari babu abinda ya bari na LaLatATtun halayen Salmanun. Alh. ya KarKare da cewa,

“To ka fita hanyarsa, kar na sake ganinka da shi, in ba haka ba ranka zai yi mummunan Baci”  Adamu bai ji komai ba a KoKarin raba shi da amininsa da ake, shi ma haushinsa ya ji

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG sosai don bai ga dalilin wannan danyen hukuncin da Salmanun yayi ba. Hankalinsa ba sosai yake tare da Alh. ba yana can ga Salma ~~ .da tayi kicin-kicin cikin hawaye, _ A dan raunane yace mata, ‘Wai da yaushe ne hakan ta faru?” Sai da tayi ta faman goge hawaye sannan  ta amsa, “Jiya da dare ne ya kira ni a waya ya ce min kai ne baka da lafiya wai na zo da sauri”’ A rikice Adamu ya ce, -
“Kin gani ko? Ke ma da laifinki, ko nine babu lafiya me ya kai ki fita da dare? Lallai Salmanu ya isa makiri”’

Babu wanda ya tanka tsakanin Alh. da Salma. Salma goge hawaye take amma tsakiyar zuciyarta bata taba samun kanta da farin ciki irin na ranar yau ba. .

_ Alh. kuma kallonsu kawai yake cikin  nazari, sai yanzu ya _ gasKata maganar soyayyarsu da ya sha ji a bakin Sa’a. cikin ransa sai yaji gaba daya haushin Adamu da yake ji ya gushe, ya ji ma kawai ya yafe masa __. Bata masa ran da yayi a kan maganar karatu. Www.bankinhausanovels.com.ng Cikin ransa yayi ta bitar Allah ne kadai ya san

' abinda ya Boye game da lamarin, aurensu zai  masa dadi don shi dai yana alfahari da auren — zumunci, ya gwada ya ji dadinsa, abu na biyu kuma shi ne, auren nasu zai farantawa Sa’a rai, don ya fahimci abinda ta fi so kenan a yanzu. Saboda haka bai yi Kasa a gwiwa ba ya kunno wa da Adamu maganar, .

“Tun kafin wannan cece-kucen yayi nisa ina ganin yakamata manya su shiga maganar,' — in da gaske kuke son juna ku fito ku fada mu san na yi. Ni zan dauki nauyin komai har in ga burinku ya cika, dama dukkanninku ai nauyinku a kaina yake. Kai tunda ka Ki karatun dole ba zan zuba maka ido ba, zan baka jari_ - bayan’ kayi aure, don ba‘ zan baka yanzu ka shashantar min ba, in kuwa ka yi aure ka ga nauyin iyali ya hau kanka na san dole zaka  mutsu”

Kunya ta bayyana ga Salma, amma Adamu babu abinda ya bayyana tasa fuskar sai yarda — da amincewa, duk da cewa zuciyarsa na mika wuya tana kuma karbowa, yana so yaji mamakin shi za’a yi wa aure kuma Salma za’a_

Www.bankinhausanovels.com.ng aura masa, sannan yana so yaji murnar za’a. aura masa Salman duk da cewa wata zuciyar _tasa najin nuna anfacuceta, = “Ba ka ce komai ba” . Alh ya farko da shi dagatunani. . - Yayi firgigit ya dago kai ya kale shi,. “Ai babu komai Alh. duk yadda kuka yi ina maraba; Allah bar zumunci ALLAH kuma ya. -*’ Kara arziki” Cike da jin dadi Alh. ya amsa. Amin, ba wani dogon lokaci zamu ja ba .ma, in dai kun so hakan” Ba tare da jin wata kunya ba Adamu ya _ kalli Salma cikin murmushi ya ce, . “Ba komai muna so Alh.” Cikin raha Alh. ya ce, - “To rasa kunya” - Adamu ma yayi dariya - - ' Alh. ya dan nutsu yana duban agogo yace, — ' “Abinda ya rage min yanzu shi ne zuwa ' ofishin “Yan sanda in nemi ayi wa Salma iyaka. ~° da Salmanu” Duk da Adamu cikin jin haushi Salmanu _. yake amma sai ya ji kamar bai kyauta ba idan

Www.bankinhausanovels.com.ng in-aka tozarta Salmanu, cikin sanyin jiki-da jin Karfin gwiwa ya ce, - “A’a ka bar ni da shi Alh. ni da kaina zan yi maganinsa, zai fi jin hukuncina ma akan.na ‘yan sandan ka san shi dataurinkai” --- Alh. da ya gama sakankancewa da Adamu nan da nan ya mika wuya, . “+ "In dai kana ganin zaka iya yi musu-tsakani ai shikenan, ni kaina bana son shaidar zuwa ofishin ‘yan sanda da mutuncina da - komai, musamman a irin wanna lamarin da . ~ babu shaida, in yaso yana iya cewa Karya aka~ - yi masa mujikunya” . . A dokance Adamu ya ce, . *“Hakane wallahi Alh.”

' Daga nan Alh. ya sallame su, Adamu da. Salma suka rabu suna kallon-kallo har Adamuya bar gidan. L

Salma ta fada daki a guje cikin mura kamar ta shide, Sa’a bata saurare ta ba sai da ta je gun Alh. ta jiyo kanun: zancen sannan ta - dawo ta sami Salma,  iye Amaryar kwanan nan”. —,

Www.bankinhausanovels.com.ng Salma ta Kara fadawa katifanta tana birgima da girgiza kai, ta ce,  “Kai Anti!” Sa’a ta dan kai mata dukan wasa ta ce, “Me ye wani kai Anti, Karya nake?” . Salma ta tashi zaune tana sussunKe, fuska, ; “Na gode Anti..:.” . Sa’a ta katse ta, oo “Da aka yi me? Kin fiye shirme, ki bar murna ina ganin fa da sauran rina a kaba, har  yau Adamu bai gama zuwa hannu ba kina ganin fa yadda ba ya zuwa inda kike in ba ke kika nemo shi ba” A sanyaye Salma ta dago ta dubi Sa’a, “Haka ne Anti, to yanzu me ye abin yi?” Sa’a ta ciji lebe, “Dole ne zamu koma gurin boka, Adamu_yana da taurin kai da alama, Alh. zuwan farko  dana yi masa na kama shi kirif! Amma kin ga shi yana neman ba mu gudu” Jikin Salma ya Kara sanyi, Allah ya sani ita ba ta je gidan Boka domin ta dauwama tana  zuwa ba, ta je don Adamu ya yarda ya aureta, kuma don Sa’a ta ce babu wata mafita bayan

Www.bankinhausanovels.com.ng . wannan,.amma bata taba yi wa kanta mafarkin ta tabbata a wadanda bokaye ke biya wa bufata ba. Amma ba-yadda ta iya, Adamu take .so, har yanzu bata samu ba bare ma ta ga in zata iya nade hannun zani ta yi wa gidan bokan . tawaye. —
A fuskarta ta nuna ta amince su koma. _° Sa,a tace, — . _ “Sai.dai gobe mu je, kin ga yau Alh. yana gida” , Salma ta amsa,  “Allah yakaimu”

***********

Da har Salmanu zai wuce sabgarsa ya jira Adamu  can, yana tuno .wasiKar cainan Adamu zuwa ga masoyiyarsa wadda ke’ aljihunsa kawai sai’ ya saki. hanya ya dauki hanyar gidansu Husna. , Yana: tsaye jiran yaron da zai aika_ kasancewa hantsi ne kusan ko wannne yaro na makaranta. - -

Www.bankinhausanovels.com.ng Yayi tsayuwa ta kusa ta minti goma, cikin _alfarmar Ubangiji sai ga Husnan ta fito daga _gidan zata siyo kayan dinki.

Tana ganin Salmanu ta saki wata matsananciyar fara’a tamkar Adamun ta gani, ~ cikin barin jiki ta shiga yi masa maraba da Www.bankinhausanovels.com.ng mugun tausayinsu ya shige shi, bai iya Boyewa ba maimakon ya rama mata da nata murmushin ko dariyar sai ya buge da yake ya nacewa,
“Husna manyan Kasa, tun dazu nake tsaye . ina jiran bullowar yaron da zan aika, sai kuma -

gashi Allah ma ya bullo min ke da kanki” - . Cikin kada kan farin ciki Husna tace,

“Ka san unguwar tamu manya irinku sun

" fi yawa, to bare kuma lokacin makaranta”. , _ Salmanu ya amsa,

“Gaskiya na ga alama, to ya garin?”

Husna ta jinjina kai ta amsa,

“Komai Kalau wallahi, Na yi farin cikin ganinka, amma dai da Adamu na gan ku zan fi haka farin ciki...

Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya katse ta saboda ya ji tausayin da yake mata ya nunku, da gaske Husna tana son Adamu tana son ya zo wajenta shi kuma gashi ~ can ya tafi gurin ‘yar fashi da makamin soyayya watakila ma ba zai tuna da itaba bare’ - rainin hankalin da ‘yayi mata a_ takarda. Salmanu ya daddage dai yayi mata Karya.

“Sabga ce ta tare shi, kin san yana dan koyarwa a wata makarnta mai.zaman kanta, jiya da shekaran jiya yayi fashi don haka yau ~ ~ aka ki lamince masa dole ya wuce bayan ya bani saKon amsarki, amma dai yau da dare ya ~ ce zai Bullo. Husna na bayyana kunya amma murna na yin gaba da kunyar tata. Cike da farin ciki tace, “Babu laifi Allah ya kai mu”
Salmanu ya zaro wasiKar daga aljihu ya mika mata, wasiKar tun daga matunshinta ta nuna da yaren da aka rubutota.

Husna ta karba cikin mamaki tana godewa, amma dai bata yi nauyin baki ba tabi ba’asi tana ta faman juya gaba da bayan wasiKar, ,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Anya wannan tawa ce kuwa”’ Salmanu yayi fuska, .. “Taki ce mana, me kika gani?” _ _ Tanuna masa rubutun bayan enbilop din, - '. “Ka ga rubutun da ya sa ni zaton ba tawa bace” Salmanu ya basar yana yarfe hannu alamar ko in kula,; “Au ba kya jin wannan yaren?” - .’_. Husna ta shiga nazarinsa don ta gane da gaske yake ko da wasa? Alamunsa ya nuna da _ gaske yake saboda haka ta kada kai, “Ban da a fim: ni ko wanda ya taba jin yaren ban gani ba...” Yatare tadasauri, . “A’a da wasa kike” Ta kada kai tana dariya,. - Me yasa zan maka wasa? Wallahi.da - . ' gaske nake, in kai ka taba ganin mai iya yaren = sai ka bani labari”’ _Salmanu ya sake yin fuska, babu ta yanda zaka dube shi ka zaci Karya yake shirgawa, _


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...