NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Salma,Www.bankinhausanovels.com.ng “Bari na gwada dabarar da na ce miki zar gwada mu gani’ Salma bata iya tankawa ba, illa ta bi Antin da kallo cikin shanye baki da bugawar zuciya. A mugun tsorace take, tana fargabar abinda zai . biyo baya idan Kwai ya fashe, akwai zallar kunya a ce wai ita ce budurwarta da ita kuma ‘yar uwar Adamu a ce ta kai kanta gurin boka neman soyayyar saurayi, saurayin ma dan . uwanta. Haba wannan abin kunyar har ina! Anti Sa’a ta sami Maigidanta kishingide yana hutawa, akwai alamun hankalinsa a. kwance yake, don haka ta Karawa fuskarta da. furucinta nutsuwa, amma fuskarta a Bace ta yi sallama, .hakan ya sanya ya karkato da hankalinsa gareta fuskarsa babu yabo babu fallasa, -  “Ke da wa na ga fuskarki da fishi?” _ Tanemi kyarar da ke fuskantarsa ta zauna tana ajiyar zuciya, . “Ba fishi ba ne bacin rai ne Alh. wani ta’addanci Abokin Adamu ya. kwaso ya kawo mana, wanda idan an bar shi ya sha gaskiya ba. akyautawakaiba” 

ZAMU TASHI 


Aih. ya tsura mata ido cikin kallon rashin fahimta, ya ce, . “Abokin Adamu wanne, me yayi?””

Kai tsaye ta amsa, .

, “Ka san dai me ke tsakanin Adamu da Salma; yau ya kwaso soyayya ya ya kawo - mata, gobe idan sun yi fada yace ya fasa haka su ke, dama dai shi ka san shi, Kuli-Kuli ne ba a

. gane gabansa. To kwanan nan sai ya fara maganar aure muna dai ta yi masa tsiya har ita Salman na cewa da me zaka aure ni? Anata. wasa da raha, amma dai na fahimci shi wannan abokin nasa Salmanu ba son abin yake ba, ban san dalili ba,.....”

Alh. ya ji ya gajida wannan dogon sharhin_ kafin furta laifin, kawai sai ya tare ta cikin. ‘nuna Kaguwa da siKewa, , :

“Bar wannan labaran don Allah ki fada min gudarin abinda ya faru”. .

: Nan da nan ta yi fuska ta furta, -

“Ai kai ka nake Alh. kawai jiya Salmanu. ya fitar da maitarsa a fili, inda na aiki Salman gidan Hajiya da dare ya makure ta a soro ya dora mata wuKa a maKogwaro yana tuhumarta

Www.bankinhausanovels.com.ng da ccwa wai asiri tayi wa Adamu _ yake sonta,wai in ba-hakan ba ‘babu yadda za’ayi Adamu ya so ta, wai in bata je ta karya asirin ba sai ya kashe ta” Duk da maganar ta zo wa Alh. a ba ‘zato kuma ta firgita shi, amma dole wani saida ta sakashi dariya, ya dan murmusa ya ce,
“Yaya ba zai so ta ba, saboda ita ba’ mace ba ce?” -
Sa’a ya ji takaicin rashin daukar maganar ‘da muhimmanci -da bai yi ba, amma dai ta -hadiye ta yi fuska tana dan taya shi dariyar a yake ta ce, . Ai To abinda na gani kenan Alh. salmanu dan iska ne kawai” Alh. yayi shiru cikin tunanuwa barkatai, shakkunsa shi ne, ya san-Adamu da kyar bai cika Boye so ko Ki
ba, sun yi maganar Salma da shi ya nuna babu ‘soyayya tsakaninsu, sannan duk labarin soyayyar Salma da Adamun - da ake karade dangi da ita:'daga bakin Sa,a dai take fitowa kamar dai yadda ta zayyano yanzu, sai Alh. ya ji kansa ya kulle ya ma rasa qpinda

Www.bankinhausanovels.com.ng ya kamata ya yi
nazari a kai ko kuma ya maganta, sai ya ci gaba cikin shiru. , _ Cikin bugun Kirji Sa’a ta dube shi ta ce, “Alh. ka yi shiru’: —_ Ya dan yi murmushin yaKe, _
“Abin ne ya daure min kai, ribar me Salmanu zai ci in ya raba Salma da Adamu, kuma-me zai rasa idan sun aurijuna?” -  Sa’a ta kawar da kai tana dan Bata fuska; ' .“oho’ masa! Ni ba abinda ya dame ni’ . kenan ba, ni abinda ya dame ni shine ta’addancin da lamarin ya zo dashi, Alh. dole - ~ ka dau mataki gaskiya” .
In Sa’a ta yi irin wannan Bata ran Alhj. ya sani bata bukatar musu, abinda take buKata — kawai shi ne a aiwatar da abinda ta nufa. Ba wai in bai aiwatar din tube masa jiki zata yi ta - zane ba, a’a kawai shi ne yake jin ba daidai ba - ne ya Ki bin umarnin nata ko aiwatar da abinda _ take so, don haka kawai sai ya kada kai cikin sanyin jiki, . “Ai dama zan dau mataki, raba su ma zan _. yigaba daya” ~

Www.bankinhausanovels.com.ng “Yauwa yanzu na ji Magana Alh. shegen yaro kawai ya gagari iyayensa sun sallama shi , mu zai shigo namu dangin mai doka da oda ya__ bata mana tarbiyya”’ .  Ta fada cikin jin dadi da karsashi saboda yaKininta na sanin mijinta, tabbas zai dau matakin kamar yadda ya sanar.

Suka yi shiru tsawon lokaci su duka kowa - ' da sakar zuciyarsa. Alh. ba a son ransa zai _ « Shiga lamarin Adamu ba, domin tun lokacin da ya nuna masa iyakarsa akan karatunsa yayi. « niyyar fita harkarsa har sai duniya ta jima shi ya nemo shi da kansa, to amma Iyalinsa ta shiga lamarin, shi kuma ba ya iya ja da abinda _ ta zo da shi, kenan a dole zai bi.ko? Ita kuma Sa’a tana can duniyar shirya ‘yadda zata bullowa da Alh. dabarar yadda zai _ tunkari Adamu da batun auren Salma, ta saKa. .wannan ta kwance ta Kulla wannan, har dai a Karshe ta zabi fadin abinda ya zo bakinta. . Cikin dakewa ta daga kai ta dube shi, “Ni ina ganin me zai hana ka tuntube shi, ~~ . in suna son juna kawai ayi abin nan mu huta, sai ka sami ‘yan wasu kudi masu kauri ka bashi .

Www.bankinhausanovels.com.ng yaja jari tunda ya ki karatun ai bai kamata a bar shi ya lalace a banza ba, yana faman bin ‘ya’yan iska irinsu Salmanu”
Game da maganar bayar da jari yaga gaskiyarta, don shi kansa ya lura Adamu ya
kama turbar lalacewar tunda ba shi da. abokin
da ya wuce Salmanu, kullum kuma sai an gansu sun sha wanka sun fice tare, to amma batun yi masa maganar auren Salma shi bai ga dabara ba don yayi masa maganar kuma bai ga wani hasken son salma a fuskar Adamu ba, sai , dai ba ya son gwale Sa’a, don haka ya gyara zama ya ce,
“Haka ne, ni ma na lura ya dauko turbar ‘lalacewar, dole hannunka ba zai rube ka yanke ka yar ba, zan yi wani abu akan sana’ar tasa, -maganar Salman ma zan kira shi mu yi maganar. Ni abin ne’ yake ban shakka, ranar da - na yi masa maganar ba ki ga baKar maganar da ya zabga min ba, kin dai san shi” .
Ta yi fuska ta tare shi, -“Alh. in kana shakka ka hada su tare ga shi ga Salman, ai maganin Karya hallara” Cikin fuskar jimami ya girgiza kai, ,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Ni ba nufina kenan ba, ba na son shiga shirgin da zan zama Karamin mutum, shi Adamu ba ya jin komai in yayi Karanta, ba zai. ji kunyar in na hada su gabana ya keta idon Salman yace ba ya sonta ba, ai kin ga in an yi hakan ba a kyauta ba” Ya Kare da zura mata ido. .
Ta tamke fuska ta shiga kallon gefe, ba _ tare da tatanka masaba. . * Dole ya saki nasa ra’ayin ya bi nata ta hanyar kada kai.cikin sanyin jiki ya ce, “Amma shikenan yadda kika fada din haka za’a yi, ki sanya Salman ta kira min shi a waya”

Salmanu ba yadda bai yi da Adamu kan su je su sami wani ya karanta musu wasiKar Husna ba amma fur Adamu ya Ki, a cewarsa cin amanar Kauna ne wannan ya kai wa wani ya gane masa sirrin mata, ya Kara da cewa, “Kai ko surar zagi Husna ta sauke min a wasiKar nan cin amana ne na kai wa wani ya ~
Www.bankinhausanovels.com.ng karanta min, ni a wajena daidai ne da na bashi damar ya Kare mata kallo ita Kanta...” Salmanu ya tare cikin mamaki, - “Zagi fa kace? In nine duniya zan nunawa  don in na rama kar asan zalinci na yi” . ’ Kai tsaye Adamu ya amsa, “Kai da idan ta zage ka zaka dena sonta
kenan, ni zaginta gareni ba zai rage komai a son da nake mata ba shiyasa in na tona sirrinta nake jin So ba zai yafe min ba” Cikin dariyar Keta Salmanu yace,
“Shikenan ina jiran ganin ta yadda zaka: kwaci kanka, ka san me ke cikin wasiKar har ka sami damar bada amsa” .

- “Don amsa zan bayar da amsa, ka .zuba ido ka sha kallo malam, cutar da aka min daya ce, kawai ban san me ta rubuto min ba, ko zagin  ne hakiKa in a son in sani” .In ji Adamu.  Salmanu ya ce, “An ji.an cuce ka baka san abinda aka rubuta ba, ni kuma ina nan ina jiran ganin .yadda zaka amsa alhalin ba ka san abinda aka _ rubutaba”

Www.bankinhausanovels.com.ng ‘Adamu bai tanka ba, kawai ya mike ya fita. Salmanu ya bishi da mita, . “Malam kar ka dade, ya yakama ta muje da wuri mu kammala shirya gurin nan, na fada maka mun baza neman kostomomi daga jibi Kila zamu farazama  Adamu dai bai tanka ba ya fice  Salmanu na dariyar shegantaka. . _ Sawon mintuna goma sai ga shi ya dawo, rike da Biro da doguwar takarda. Ya nemi guri ya zauna Salmanu na bin sa da Ido, “Wato kintatar amsa zakayi ka bata kenan?” . Adamu yayi fuska ya zura hannu a aljihu - ya dauko tiger balm sabo a takardarsa, yana -cewa, -  “Ka tsaya ka yi kallo kawai, yadda ta sani_ a duhu wallahi sai na sa ta ba tare da ta canki " yarenta ne ban gane ba” - “ Har yanzu Salmanu bai fahimci inda Adamu ya dosa ba, yayi saKare yana kallonsa _ yana farke takarda taigan, ya kasa haKuri saida ya ce masa,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Wai man zafin zaka shafa a_takardar - maimakon ita da ta feso turare?” - ‘Adamu ya ki tankawa face ya cigaba da aikin gabansa, wato zaro takardar bayanin da — . ke kunshe cikin taiga wadda ke dauke da rubutun yaren China ya kwafe ya fara kwafewa a doguwar takardar da ya shigo da ita. ~ , _ Sai yanzu Salmanu ya ankare, ya saki ihu yana kai wa Adamu bugu, ya ce, “Shegen kasa Wato yaren China kai kuma zaka yi mata idan ita ta yi maka turanci - ko?” ' , Adamu ya saki dariyar Keta ya ce, , “Ashe ka gane, idan ita gama-garin yare take ji wato turanci to ni ina jin wanda kila a fadin Najeriya ba mu kai mu dari ba?” “A hasahenka kenan” ; Salmanu ya fada cikin tsananta dariya, . shegantakar ta Adamu ta yi mugun birge shi, salin alin ya kubuta daga tozartar bai iya -turanci ba, kuma ita ma Husna ya sata.a kwanar bata iya cainanci ba, yana da tabbacin gaba ba zata yi gigin sake rubuto wa Adamun’

Www.bankinhausanovels.com.ng takarda da turancin ba don kar-a bata amsa da yaren da bata iya ba. . Adamu ya kwafe takarda tsab yayi mata kyakkyawan ninki ya nade a enbilof hankalinsa a kwance, in dai wannan tararradin amsa -wasikar ne ya gama da shi, sai dai ya jira wata, wadda yake da tabbacin da yaren da zai iya - zata iso. . ~ Sun karya kumallo suna ta tattauna zancen “ cikin dariya,'a fakaice Salmanu na yi wa _ Adamu' hudubar kwantar da. hankalinsa ya * manta da wasu mata ya kama sabgar gabansa, yacemasa, .° - “Ka manta da su, ka nemi kudi, wallahi in ka same su mace sai ka ture.....” Cikin kada kai Adamu ya tare shi, _ _ “Husna nake so ba mace ba Salmanu”, Salmanu ya ce, “Na sani, ita ma din cikin sauki zata zo_in dai kana da dan karansinka a aljihu. Abinda nake so ka gane shi ne, sana’armu tana son nutsuwa da Kirkirar basaja da dabaru, in kuwa ka cunkusawa kwanyarka mata don Allah

Www.bankinhausanovels.com.ng yaushe zaka sami nutsuwar aiki bare tuna abin kirki?”Ba don Adamu ya gamsu ba saidan gajarta zancen ya kada kai,

“Babu laifi zan kwatanta, musamman dayake daga yau ma zaman kashe wando ya Kare”Yauwa ashekagane -

Salmanu ya fada da farin ciki. Suna shirin fita sai ga wayar Salma, da Adamu yaga . sunanta sai da ya ji gabansa yay? mummunan faduwa. Cikin wani irin barin jiki ya daga wayar muryarsa na rawa yace, “Ran Gimbiya ya dade” Salma ta ji kamar an tsoma ta a ruwan sukari, ta saki wata ajiyar zuciya, fargabarta da tsoronta suka gushe, a ranta ta raya, cib! Ashe har yanzu maganin na aiki! Amma a fili sai ta tausasa murya ta ce, “Wacce ni ni mai ido ba dan ciki?” Da sauri Adamu ya katse
Www.bankinhausanovels.com.ng ta“Da gaske wallahi, ai ni kin fiye min duk matan duniya? . .Dadi ya sake kashe Salma, ta sauke Katuwar ajiyar zuciyatace, “Kamar gaske” - “Me zan yi ki yarda da ni? Ya tamabaye ta cikin raunin murya. Ta dan ja fasali sannnan ta amsa, ” “Mu bar maganar, yanzu dai kiran ba nawa ba ne, Alh. ne ya ce na kira ka, wai ko * me kake yanzu ka katse shi‘ka zo” Adamu ya dan yi dum! Ransa bai so wannan titsiyen ba,.sai dai ba shi da zabi tunda ta bangaren Salma kiran ya biyo, ba don haka _ ba wallahi matsewa zai yi. Duk da haka saida — ya dan tirje. " so “Kash! Anya ba zan share kiran nan ba sai na dawo? Ina da wani uzuri wallahi”» ~Kamar Salma*zata biye masa . saboda ‘ rashin son bacin ransa, sai kuma ta ji yakamata . _ ' ta motsa Kwanjinta akan. sa, cikin basarwa "tace, . . -Haka dai zaka daure ka zo,inkazoma ai.. ma Samu mu gaisa’. Www.bankinhausanovels.com.ng . Nan da nan ya amsa, , “To babu laifi zan zo yanzu tunda ke ma kina son ganina” Ta sha mur ta sake cewa, ; “Yauwa kar ka dade” . “In Allah ya so ba zan jima ba” Ya sauke wayar tare da sauke ido akan © Salmanu, . “Salma ce ta ce Alh. na kira na yanzun nan, ka zo mu je sai mu wuce dagacan” —~Ran Salmanu yayi mugun baci, ya dorawa_. Adamu Ido tsawon lokaci sannan ya girgiza kai, “Ka na rawar Kafar tafiya ka je ne don Alh. ne yayi kiran ko kuma don Salma ce ta zo da saKon kiran?”Abin tausayi sai Adamu ya yarfe hannu a sanyaye ya ce, - “Nima ban saniba Salmanu” Wani haushin ya sake cika Salmanu, ~ amma dai bai tanka ba sai yayi. zuguri yana kallon Adamu.
Adamu ya figi -mukullin dakin yana. yafitarsa,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Zo mu je mu da sauri mu gama da shi mu wuce don Allah, ko wacce tsiyar ma zai min "oho masa” . Salmanu da yake tsakiyar shaka ya fashe, “Ni fa ba zani ba, kawai ka je in kuka gama ka same ni a can” . . Jikin Adamu yayi sanyi, ya dan yi saroro yana kallonsa, sannnan yace, « + “Ko gidansu Husnan ba zaka raka ni kai takardar nan ba?”’. —_ _ « ° Salmanu yayi fuska, “Kai da zaka gidansu Salma me zaka je yi . - gidansu Husna?” ° SO ‘ Adamu ya debo murmushin yaKe ya sauke,  iDO, “Ka‘manta ni mijin mata biyu ne? ai kayan - nama ba ya kashe kura” _ “Sai ka je ai kai daya, don ni kyanwar- _ lami ne ko banaci bare naman” - “* Bai jira cewarsa ba ya kada kai yayi tafiyarsa.  Adamu ya girgiza kai yana murmushi ya_ - + janyo Kofar dakinsa ya garkama mata mukulli

Www.bankinhausanovels.com.ng Sannan ya shige cikin gida domin yi wa gyatumarsa sallama.

************

Salma na sauke waya ta saki ihu ta bazama dakin Antin Sa’a tana bata labarin yadda akayi

Anti Sa’a bata yi mamakin abinda ta ji ba domin ita tayi wa aikin bokanta farin sani, ta jima da imanin ko ba dade ko ba jima sai Adamu ya kamu a tarko Salma kirif! Ta nuna jin dadinta ainun Sannan ta cewa Salma,Kin san Allah? Da mun sani ma ba mu shigo da Alh. cikin maganar nan ba, ke kanki kin isa raba  Adamu da Salmanu, Na rantse miki da Allah idan kika ce kar ya sake kula shi sai ya hanu”  Salma ta cika da jin mamakin jin abinda. Antinta ta ce, cikin sakin baki ta ce mata, _ “Da gaske Anti?” anti  Sa’a tace, “Har fa rantse miki na yi - Salma ta rausaya kai, -

Www.bankinhausanovels.com.ng “Ai al’ajabi ne yake ‘neman kashe ni, yanzu duk fandarar Adamu ‘zan iya , dankwafewa?” ; _ Sa’a ta jinjina kan jin dadi hirar, ta ce, ‘ “In kina shakka ki gwada daga kan maganar Salmanun nan, kar ki bar shi da . maganar Alh. da zai iya watsarwa idan ya tashi daga gabansa, ki shiga maganar zaki ga abinda » zai faru” _ - - Salma ta kasa Magana sai jinjina kai « kawai, lamarin ya girmi tunaninta, in a da can wani ya sanar mata Adamu zai iya zama haka a hannunta zata musa masa ko da kuwa tsafe shi - za’a yi ba wai Karamin alhaki boka ba , Babu fargaba ko kadan a tare da Adamu ya shiga falon Yayansa domin dai shi ya san ~ » bai yi komai ba bare ace akan sa aka kira shi a ' balbale shi da fada, amma ga mamakinsa Salma na shigowa dakin ita ma ta zauna sai yaji gaba daya Kwanjinsa ya zube, ya dinga jin”. . rashin katabus” hade da faduwar gabaHMMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...