NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA 

Rayuwar ta yanzu gaba daya ta neman dafa’i ce, in kuma ka matse hannun nema to kuwa sai dai-ka zauna a. rayuwar kana ji da gani ka zama mara sa’a, talaka mai bakin ‘jini da mummunar fuska” Sai da Salma ta daga kai ta dubi Anti Sa’a bayan ta diga wa zancenta aya, ta dubi fuskarta da kyau sai ta tabbatar da gaske take a maganar ’ da ta karkare batunta da ita, Salma ta ji hanjin cikinta na wani mugun kadawa da dalilai biyu, na farko in bata nemi wannan dafa’in na zuwa irin wannan Kazamin gurin ba zata zama talaka mai mummunar fuska da baKin jini kuma mara _ sa’a a rayuwa, na biyu idan ta nemi dafa’in _ tabbas tana shirin canjawa ne daga _asalin Salma da ta dade da sanin kanta zuwa wata daban da ba ta gama amanna da irin rayuwar 


ZAMU TASHI 

Data tsoma kafa bata kuma  san inda Zata riska in ta nade hannun zani ta fara tafiya ba. Tana ta wannan tuntuni har layi ya zo kansu, kuma Karin gargaba da bugun zuciyarta, mutum daidai ake shiga dakin bokan, bare ta shiga da Anti Sa’a tayi mata jagora. Haka dai -Anti Sa’ar ta yi ta tausar ta sannan ta fura ta.
Daga bakin Kofa kafin ka shiga akwai wani dogari tsaye riKe da wani bakin KoKo cike da Kananun layu, duk kostoman da zai shiga sai an bashi guda ya hadiya sannan ya shige ciki Har ga Allah ba da son ran Salma ta hadiyi layar nan ba, don dai kawai ta kawo kanta ne, kuma ma dai ta ga gomnonin mutane sun _ hadiya sun shiga sun fito Kalau, kuma gobe ma suna dawowa kamar dai Antinta Sa’a. Tun daga Kolin kanta har tafin Kafarta karkarwa suke, ta bankada labulen dakin ta shiga tare da rafka sallama. Ba kamar yadda ta tsammaci ganin bokan ba, wato sanye da kayan tsafi ko tarkacen kayan bori rakwacam! Maimakon haka sai ta ganshi hakimce kan kujera ya ci manyan kaya ~tamkar wani saraki har da rawani fari tas da www.bankinhausanovels.com.ng shi kamar shi ya zabo kansa musamman da yake yana da alamun yanzu yake dosar - shekarun tsufa ba a cikinsu yake ba. Sai dai fuskarsa a matuKar murtuke ya zubo mata ido ba tare da ya amsa sallamarta ba. Tamkar Salma ta yi girgiza ta zama ba ita ba saboda tsabar firgici da fargaba, ta yi diradira tana cigaba da yi masa sallama.” Ya ci gaba da kallonta rai a Bbace ba tare da ya tanka mata ba, har sai da dan kanta ta yi wa kanta wajen zama ta kuma ja bakinta ta tsuke kai a Kasa, amma tana samun damar kalle nan da can a kusurwoyin dakin wanda yake shaida kasancewarsa dakin bokanci. — Bangwayen dakin duk an lanyace su. da zannnuwan shudin saki da fari, ga kuma hatimin gidan sarauta a guraren da ba su sami — adon zannnuwan sakin ba, abinda kuma ya daure kan Salma kenan. Amma dai ta ci gaba da kallon yadda dakin ya sha Korai masu fenti shantuna da sauran dangin kayan duma, sai layu danKwala-danKwala rarrataye baKaKe da jajaye hade da wuri tare da wasu Karafa da Salma ba ta san sunansu ba. Sannan akan ko www.bankinhausanovels.com.ng wacce kusurwa ta dakin daga Kasa akwai katuwar Kwarya zaune kuma daya cikinta wani hayaki ke fita tamkar dai an kunna turaren wuta, wannnan gaskiya shi ya fi tsorata Salma, : dan tana da yakinin sai tsabar sihiri ne zai - zaunar da garwashi cikin Kwarya ba tare day a Kona Kwaryar ba...
Bata gama shan kallonta da nazarin dakin bokan ba gajiyayyiyar muryar bokan ta kaise - mata hanzari,
“Yanzun haka Adamu na kwance’ gadon asibiti”  Abinda bokan ambata kenan ya. sanya ta razanar dagowa ta kalle shi duk da kuwa kunnuwanta ba su gama tantance abinda ya fada ba illa sunan Adamu da ya bata mamakin ji a wannan muhallin. Ta zuba masa ido da kallon tsoro da rashin fahimta, shi kuma bai yi Kasa a gwiwa baya sake maimaita mata, Masoyinki Adamu a halin yanzu yana kwance a gadon asibiti bai san inda kansa yake ba” - . “Inna liflahi wa inna ilaihi ra‘i’un” Www.bankinhausanovels.com.ng
A guje ta fada da nuna razana a fuska, amma cikin zuciyarta tana Karyata bokan, yaya Adamun da suka rabu lafiya-lafiya za’a fada mata mummunan labari a kansa mara dadin ji irin haka? Wai ma har da maganar bai san inda © kansa yake ba saboda tsabar mugun fata. “Ki tashi ki je gida sai kin tarar da abinda na fada kin gamsu sannan ki dawo ki sami abinda . kike nema akansa”.
Salma ta Kara rudewa da ta gane bokan na gano har abinda ke cikin zuciyarta, nan da nan ta hau cin laya.... . “Wallahi ranka ya dade tun yanzu na gamsu, ka yi min rai ka saurari abinda na zo da shi” Ya jima bai tanka ba, amma idonsa na kanta. . Duk ta bi ta jirkice, zuciyarta na son ta kamo tashar dana-sanin zuwanta, amma tana tsoron hatsabibin bokan ya shiga zuciyarta ya — gano abinda ta raya, don haka ta yi ta faman kakkacewa tashoshi da suka danganci aibu ga bokan, karshe ma kawai sai tayi l dabarar kama: www.bankinhausanovels.com.ng tashar mafarkin soyayya da Adamu ta zama  gaskiya.
Dai-dai wannan gabar ne kuma Bokan ya tanka,
“Adamu ya fada wata zazzafar soyayya ba tare da dalili ba, duk wata mace a duniya yana kallon kawai wadda yake so ta rako duniya, lallai ba don kin zo nan ba har,abada Adamu, ba zai taba sa ki a jinsin matan da zai so ba’
Yanzu tsakani da Allah Salma ta ba wa Boka dukkan imaninta, ko bai san gaibu ba to . ta tabbatar an buda masa wani abu da ya dangance shi. Ta zo wajensa bata sanar da shi abinda ya kawo ta ba, amma ga shi yana batu a kanta, sunan Adamu radau a abakinsa. Cikin sakankancewa ta muskuta ta ce,
“Na fahimci hakan, ranka ya dade tunda da. bakinsa ma ya sha fada min ni ba irin matar da za’a so bace...” Ki bar shi kawai, da mu yake zancen. Ba shi yau ya farfado zuwa gobe duk tsiyarsa sai kin yagi wani abu a soyayyarsa’ Salma ta ji wani irin rauni ya mamaye -zuciyarta har Kwalla ta taru a idonta. Ba yagar www.bankinhausanovels.com.ng wani abu take son yi a soyayyar Adamu ba, kulliyar soyayyarsa take so saboda haka ta ji Sanyin gwiwar yadda bokan nan mai gani har hanji yake batun zata yagi wani abu a soyayyarsa. ‘  “Kin fiye garaje” , Bokan yace mata lokacin da ya miko mata - -wani Kunshin hoda da ba ta san yadda aka yi ya zo hannunsa ba.. “Duk mai hulda da ni Sai ya yi yadda yake so a rayuwarsa kar ki dinga zatawa _aikina ‘ragontaka, Ungo nan!” Ya cilla mata kunshin hodar. _ " - Jikinta na karkarwa ta sa + hannu ta dauka tana - bin sa da kallo, on “Ta zama hodar sawar ki duk lokacin da ki ke hasashen zaku hadu da shi” - Ya sake cillo mata wani daurin magani. “Wannan duk yadda za’a yi ki bashi a abinci ko a ruwa ko da sau daya ne, Adamu ya zama naki in kin yi wannan.., ajiye sadaka ki tashi ki:
tafi sai kin kawo min goron daurin aure” Jikin: Salma sai bari yake ta. zuge jaka ta kwanto dubu biyar din da Anti Sa’a ta bata ta ce Www.bankinhausanovels.com.ng ta bashi, ta miKa masa yayi mata inkiyar ta zube kan dardumar gabansa. Ta ajiye ta mike tana faman sharara masa godiya ta fice yana bin ta da wani irin kallo da har Keyarta ta ji shigar kallon. A waje ta yi jiran Anti Sa’a wadda layin ya zo kanta, ta dinga mamaki da al’ajabin jin cewa ashe wai duk so da kyautatawar da Alh. ke wa . Anti Sa’a ba so da kirkinta ne ya janyo mata ba?  Dama wajen boka ta ke kai shi? Shiyasa ake  ganin tana samun kudi amma a rasa inda take kai su? Yanzu ita ma haka zata sami irin wannan gatan na kwatance wajen Adamu? Amma kuma ta rasa ajiye abin kanta? Ta binne wannan mamaki da tunane-tunanen bayan Antin tata ta fito, suka dauki hanya cikin tattauna tadin Bokan, a nan ne Salma ta ji abinda ya ruda zuciyarta ya kuma so ya sanya ta sauka daga wannan turbar ta bin bokan, wato Anti Sa’a take Kara mata bayanin dalilin da ya sanya aikin bokan ke matuKar ci kamar yankan reza, inda ta ce mata, “Na taba jin bayanin cewa aljanu na yi wa
bokaye biyayya ne gwargwadon yadda suka . shata maka sharadi kabi, shi wannan Bokan. Www.bankinhausanovels.com.ng babban hadimin ajaninsa dan sarkin agadas ne, an ce kafin ya bashi aljanun da zasu dinga yi masa hidima suna yi masa biyayya ido rufe sai da ya ba shi sharadin zai daina sallar la’asar kwata-kwata kuma zai daina halartar sallar juma’a cikin jam’1 sai dai yayi tasa a gida, Sannan wannan karagar.da yake zaune a kai Karkashi shimfidar: akwai kur’ani izifi sittin. Wannna shi ne sharadin da ya cika ake biya masa buKata, don haka duk wanda ya ce miki ya zo wajen malamin nan buKatarsa ba ta biya ba, na rantse miki da Allah ya ci Karya ya kwana da yunwa Wannan bayanin sai da ya so sanya jiri ya kai Salma Kasa, duniyar ta dinga juya mata cikin jin tsananin mamaki tana duban fuskar Antinta wadda ke halartar islamiyya duk asabar da lahadi, amma wai ta dage tana yi mata bayanin bajintar nan ta boka a wajen sabawa Allah da sunan labarin birgewa. Ba ta farko daga rudaninta ba Anti Sa’a ta sake kashe ta da wani labarin takaicin, Www.bankinhausanovels.com.ng “Amma dan tsabar son yara jita-jita irin na mutane, rannan na ji wani malamin addini a radio yana ba da misalin bokan a fakaice ba tare da kama suna ba, wai shi a dole masanin bokaye da sirrin aljanu, yake cewa, wai layun da maziyarta gurin bokan nan ke hadiya kafin ganawa da shi ta wannan hanyar yake zaunar musu da aljanu a zuci da sauran sha’anoninsu wadanda ‘zasu zama ‘yan sa ido kansu da wadanda suke son a yi wa sihiri, kuma wai ta wannan hanyar ne yake sanin abinda ya faru da mutum kafin ya sanar da shi, kuma ta wannan hanyar ne bokan ke ribace imanin masu zuwa -gurinsa har suke ganinsa kamar wanda ya san gaibu, ... ki ji don Allah, hassada kiri-kiri, shin Allah ba zai yi baiwa ga mutum ba sai da wani dalili?” Wani tsinannen takaici ya cunkushe wa Salma a maKoshi, ta yi KoKarin ta hadiye shi ya faskare, dole ta ji ko yaya ne yakamata ta rage wa bokan nan karfi a fuskar Anti Sa’a ko da kuwa da fatar baki ne kuma ko da ragewar ba _zata tsinana komai ba na janyewar su ga bokan, ita kanta ba ta fara mafarkin ta guji bokan ba, Www.bankinhausanovels.com.ng musamman saboda furucinsa na cewa duk mai — hulda da shi sai yayi abinda yake so a rayuwarsa, ita Adamu take so a rayuwarta kuma da alama ta hanyarsa zata same shi. Kila maganar malamin da kika ji a radion gaskiya ce, tunda ko kin ce ai ajanu ne. suka tsaya masa, mu dai mu je ya biya mana tamu . bukatar in ma da laifi sai mu dawo mu yi istigfari” Ai shiyasa nake yawan sadaka Salma, ni ma ai na san akwai laifin, akwai lokacin da nake jira - na dena musamman kwanaki da boka ya sa ni hada wani asiri, ni da kaina na san akwai kaucewa a ciki, sai dai kawai mu yi ta roKon Allah ya yafe mana” so Amin” Salma ta fada a darare, domin ita kanta ta san wannan ta’addaci ne aka kinkimo aka kai wa Allah. “Ko me ya sami damu? A tsorace nake wallahi” In ji Anti Sa’adatu, kum fadar tata ce ta dawowa da Salma damuwarta da ta sanya ta kasa ko tankawa. Www.bankinhausanovels.com.ng

************

Salmanu yayi jiran farfadowar Adamu tsawon fiye da mintina talatin, da bai farfado din ba ne - kuma hankalinsa ya tashi har ya fara sambatu. “Ka ga dan iska, idan ka zarce ai ka yi wa soyayya asara, ni kuma ka janyo min jafa’i a ce ni na kashe ka” Yana ta faman irin wadanna sambatun ya debo ruwa ya shafawa Adamu amma kamar an shuka dusa, sai hankalinsa ya Kara mungun dugunzuma, ya kame Kugu yayi tsaye tsakiyar dakin yana shawarwari, duk hange hangensa ya rasa tudun dafawa, can sai ya sake debo wani sambatun, “Dama ni bokan gaske ne ba sai na fara aikina ta kan wanna shegen ba, daga wasa sai ka kama ka macewa mutane, tun farko ma ban da kai wani shegen tunku ne uban waye yace ka bayar da kudin, yo ko ubana ne yayi min abinda ka yi ba sai na dirka masa naushin da zai ziyarci
Www.bankinhausanovels.com.ng barzahu bai shirya ba, kai ma sa’a ka taka wallahi”’  Maganganun da yake fada ba su yi kan da fuskarsa mai nuna tsananin tsoro da firgicin yadda abokinsa ke kwance hanyar rasa rai ' dalilinsa ba. Ya sha hange-hange kafin ya kullo dabarar da zai je ma Hajiya da ita, ya fito’ dakin yana hawayen Karya amma bakinsa bai fasa kuri ba, dan iska kawai, na rantse da Allah b* da wancan furojet din namu na sana’a in ka mutu zan jima kafin in samu madadinka, Kur’ar Ubangiji da bar ka zan yi ka tafi kawai”™ ‘ Ya Karasa maganarsa.a ciki lokacin daya shiga cikin gidan, aka yi sa’a suka yi kacibis Hajiya ta fito daga kicin rike da galan din kananzir, Tana kallon Salmanu idonta ya shaida mata tashin hankalin da yake ciki, ita ma hankali a tashe ta hau baibaye shi tambayoyi, lafiya kuwa, ina Adamun?” Yanzun nan wani la’anannen tsinanr matsiyacin direban babur ya make shi ya tsere na kwaso shi mun taho gida bai san inda kansa yake ba saboda sisin kobo babu a aljihuna™ Sai ya Karasa maganarsa ta hanyar barkewa da kuka. Kafin ma ya dire Hajiya ta yi hanyar Soro tana rafka salati gami da hirji. : Salmanu ya bita a baya yana ta faman kwashe wa direban babur albarka kuma yana kuka haikKan tare da bawa Hajiya labarin karya akan hatsarin, ya ce mata ta cikinsa ya kusa bi da tayar mashin din, duk yadda aka yi a ciki ya sami matsalar.

Hajiya na jinsa tana ji da danta, ba ta tankawa Salmanu ba sai da ta bugawa Alh. waya ta sanar masa komai ya taho daga unguwar da ya je a gigice sannan ta juyo ta fuskanci Salmanu cikin tausayawa ta ce, Halinku daya dai da abokin naka Salmanu, kun fiye amfani da munanan kalmomi, yanzu don Allah wadannan alkaba’in da kake janyo wa . mai laifin nan da wannan tsine-tsinen da kake masa duk ya cancance su, yaushe laifin nasa ya kai haka Salmanu? To ka yi hakuri don Allah ka yi masa.addu’a tagari wato addu’ar shiriya, shi www.bankinhausanovels.com.ng kuma abpkinka sai ka dinga yi masa ta fatan Samun sauki’ . Salmanu ya hau matsar hawaye yana kada kai ba tare da ya tanka ba. Alh. na zuwa aka kwashi Adamu asibitin Murtala a sume. “Kar mu ce bigewar mashin ce, yanzu sai su sanya mana ka’idar sai mun zo da ‘yan sanda”
Alh. ya kawo shawarar nan, ta yi wa Salmanu dadi ainun, cikin doki da garaje ya ce, Nima na yi wannan tunanin Alh. kawai sai mu ce faduwa yayi kan kwalbar lemo” Haka za’a yi Alh. ya amsa zuciyarsa daya. Bayan sun kai asibitin Salmanu na kan gaba wajen kurda-kurda da kuka shabe-shabe da hawaye, babu wanda bai ji tausayinsa, don haka ne ma da aka ba Adamu gado, Alh. ya bar Salmanun ya tafi gida shaidawa iyalinsa da kuma kwamtar da hankalin Hajiya wadda yayi dabarar kin tafiya da ita don kar ta zo ta daga hankalinta. To ya manta ma iyalin nasa ta je unguwa, don haka kawai sai ya je ya Kara rarrasar Hajiya sannan ya koma asibitin.
Har yammah suna tare da Sulaiman wanda ya fishi tarin damuwa da cutar don hanema sai ya zama kamar shine dan uwan adamun a idon likitocin shi suke kira don karin bayani ko neman wani abun kasancewar asibitin ba,a ganin mara lafiya sai lokacin ziyara wannan tasa shi kansa alhj a bakin salmanu yaji cewa adamu ya farfado kum jikinsa da kyau yana gbaccin gajiya duk suka taru sukayita farin ciki sunce zuwa dare ma zasu sallamemu inji sulaiman alhj ransa yayu dadi yace abin yayi kyau dama ina zaman asibiti yaga dadi ga mahaifiyarsa can hankalinta a tashe gara akai mata danta taga lafiyarsa lokacin ziyara nayi sulaiman yayi dibarar sillewa ya rika alhj shiga wajen adamu ya sameshi zaune jingine da filo yana kurbar maltina wanda salmanu ya siyo masa tun yana mace
Ya zauna bakin gado gefensa sunayiwa juna kallon kuda da alama kowa bakinsa cike yake da zance amma sai salmanu ya rigashi www.bankinhausanovels.com.ng furtawa cikin murya_ kasa-Kasa kasancewar dakin ba Adamu kadai ba ne mara lafiya. Ba Babu alamar ciwo a tare da shi yanzu amma ~ fuskarsa ta nuna jigata da farkowa dagaciwo. Malam ka daga min Kafa, na ce Mashin ne ya bige ka, banza kawai daga naushi daya sai ka macewa mutane?” : Adamu ya jima bai tanka ba. Salmanu ba ya shakkar in Adamu.zai kasa goya masa baya, ba yau yake da shi ba ba jiya ba. Hasashensa kuwa ya ci, domin sai gashi cikin murmushi Aadamu ya ce, Ka ci sa’a ban mutun ba Salmanu, inna -mutu ni da Husna ba zamu taba yafe maka ba, don ba ka bar mu a duniya mun auri juna ba” Salmanu ya kai masa bugu cikin murna da 1hu, “Au har ita ba zata yafe min ba? Ita da bata ma san kana yi ba?” Adamu ya kawar da kai, eh mana, ruhinta ba zai yafe ba domin akwai ranar da zai san a duniya yayi rashin wanda ba zai taba samun wanda ya so shi haka ba”


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 8 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...