NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CH - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CH

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


Www.bankinhausanovels.com.ng 


A JIYA MUN TSAYA 

Bayan sun dawo. suka wuce cikin gida Salmanu ya gai da Hajiya, suka dan jima tare da ita suna hira tana Kara yi musu nasiha kamar. ‘yadda ta saba, ta yau har ta fi ta kullum kasancewar tana cikin firgicin halin da Adamu yake shirin fadawa. - Bayan sun dawo dakin Adamu suka ci abinci suka cigaba da hira. Wai me yasa na ga Hajiya a firgice? Ina fatan ba zuwana ba ne?” Salmanu ya tambaya. “Kan zargin na je wajen Malam-na-Allah - ne , -Adamu ya amsa. 

ZAMU TASHI 

Tana da gaskiya, kuma da na san haka ne, da na kwantar mata da hankali na fada mata gaskiya “Gara da baka sani ba din, yanzu mu je ga abinda ya kawo ka” Salmanu ya gyara zama cikin jin kumari da nishadi, “Faduwa ce fa ta zo daidai da zama, hanyar neman kudi da samunsu cikin sassaukar hanya na kawo mana, dabararmu ce kawai zata yi aiki..” “Kai da ka ce baka son ganin Kato na jiran kudi a huce?” Adamu ya fada cikin gwasalewa. Salmanu ya girgiza kai, “Ai ba irin naka ba ne Adamu, ku da kuke - jiran Aljanu su sato na mutane su kawo muku kuna kwance, akwai bambanci da sana’ar da kana zaune mutane ne zasu tako sayyadarsu su kawo maka, hasalima sai ka zuba  jari, ka ga da bambanci?” ~ Adamu ya rausaya kai, Www.bankinhausanovels.com.ng (hum ina jin ka, kar ka manta ka dai sa ni na karya azumi, da ka bar ni na kai abina ai in nayi kudin kai ma ka huta.. “Allah ya kiyaye, me zan yi da kudin jini” Suka sa dariya sannan Salmanu ya dora, “Ka na ji ko? Muma malaman tsubbu zamu_ zama a _yanzu babu sana’ar. da ta fi ta kawo kudi... 

An ki cin Biri an ci Dila... Adamu ya fada cikin dariya.| “Na fada maka da bambanci, mu fa har jari zamu zuba, kuma harkar mu ba ta shirka ba ce “Hmn” Ragon . nishinda Adamu ya iya saukewa kenan. Salmanu yana dubansa } yace, | “Allah kana daukar lamarin nan wasa, ka yi shahada ka sa kai kawai, a  gaba zaka yi dariya | _ ka gode.min”Adamu ya yamutse fuska ya mike tsaye, To ni wallahi kaina ya fara ciwo, kawai ka Je gobe ka dawo, ga kiran sallar isha can ma an fara”’ Salmanu ya daga kai ya bi shi da kallo _ kamar zai Kulu, amma sai ya dake, shi ma ya mike tsayen,Banza gwangwani kawai” Adamu ya Ki tanka shi, don tsakani da Allah da gaske kansa ya fara ciwon, wannan  na dafe da Salmanu yayi masa ya rasa da abinda zai gwada shi. Salmanu ya Kulu, a fusace ya nufi Kofa. Adamu ya daga' murya, “Sai ka zo da wuri goben” Salmanu yayi tsaki, ~ Zuwa goben kai ma ka tanadi dubu goma wadda za mu hada mu zuba jari’. Ya shafa aljihun wandonsa, “Ni kaga tawa na tanado” Adamu ya kebe baki, “To babu laifi. Ga duhun dare ga bindiga, al’amuran duk sun zo da sauki... “Ga kuma layar zana ba” Salmanu ma ya rama baKar maganar. Adamu ya tuntsire da dariya yana cewa, “Allah baka hakuri, tsaya mana muje sallar Isha sai ka wuce” Www.bankinhausanovels.com.ng In na je tamu Unguwar na yi, dama bana son bin sallar ‘yan Kabalu”’. 

***********

Salma ta kwana da damuwar halin da take zargin Adamu na neman jefa kansa, ta yi tunanin duniyar nan dan samo masa mafita ko kubutar da rayuwarsa daga mutuwar tsaye a duniya tare da zuwa lahira fankan fayau ta rasa, shi dai Adamu ba wani yake shakka ba bare ta dogara dashi ta kai masa kararsa. A zahirin ido Alh. yake tsoro amma shi din ma tuni ta fahimci tsoron na ta gina bata shiga bane, domin duk abinda ya -hana shi ko kuma ya sa shi a gaban idonsa zai nuna ai ya hanu har __ abada, amma Alh. na Bacewa zai hau mita da jefar da bakar Magana har da cin alwashin in - yayi kashe shi za’a yi? Wai ma Alh. haifarsa yayi da zai dinga sa masa ido alhalin uwarsa da ubansa basu sa masa idon ba? Kai kanka ma. yadda ya ci lagon Alh. akan gudun makaranta ya tabbatar mata babu abinda Adamu ke buKata illa addu’a. Www.bankinhausanovels.com.ng Kwana biyun nan Sa’adatu ta fahimci sam Salma ba ta cikin walwala, kuma dama tuni ta dade da sanin matsalarta bata wuce Adamu ba, amma abinda yake shake mata maKoshi bai wuce kaukauce wa iyakar hanyar da zata iya taimakonta ba. A wajen Sa’adatu duk abinda_ . kake so a rayuwa ko wani baya so. zaka iya samun abin in dai ka san hanyar da ake bi a samu, to ita ta san hanyar saboda haka duk abinda ta nema a rayuwarta ita ta same shi, ta sami mijin nuna wa sa’anni wanda baya tsallake buqatunta, ta sami kudi ta silarta da ta  silar sana’o’inta, ta sami ‘ya’yan da ko mutuwa tayi dole an san ta bar lyali, ‘ya’ya takwas ba wasa ba, ta cusa wa kowa soyayyarta yadda mutane na nesa da na kusa ba sa ganin laifinta ko da tayi. Duk da dai ta hakKaKe ba waccan dabarar tata kadai ta bata ba har da KoKarinta na_ kyautata kowa daga fuskarta zuwa aljihu. Hakan ya toshe ko da zaginta wani zai yi a gaban mutanen da take kyautatawa sai ta sami me karba mata. Www.bankinhausanovels.com.ng Ta zari jiki ta sami Salma kwance kamar ruwa a daki “Wai Adamun ne yayi miki irin ‘wannan raunin haka?” Salma ta dago ta dube ta a jahilce, duk da ta san ta dauki turbar kwance abinda yake faruwa a ainihin zuciyarta. “Wanne rauni kuma Anti?” - Sa’adatu ta nemi guri na zauna. “Na fahimci son da kike wa Adamu ya fara kai wa mizanin da ba zaki iya riKe shi ba” _ Salma ta kawar da kai ba dan ta saduda da fasawa Anti Sa’a cikinta ba sai dan tana jin kunyar ta karyata abinda yake gaskiya. A labarai da fina-finai ta saba ji da ganin irin son da ke maKare cikin zuciyarta bata taba - tsammanin ko da mafarki akwai shi a zahirin rayuwa ba. “Haka ne?” - Anti Sa’a ta sake tambaya da fuskar neman tabbaci mai kuma bayyana ta riga ta tabbatar tuni. Www.bankinhausanovels.com.ng  Salma ta tashi kwance daga kwanciyar da take cikin matsanaciyar kasalar da take tasowa tun daga zuciya. “Ba ni da tabbas Anti Sa’a, har yanzu cikin Karyata zuciyata nake, abinda nake ji a cikin ’ raina kamar ba shi ne son da aka saba ji ba, in. - ‘ma an saba ba’a taba tarar wa mace ce take irinsa a inda ba a san darajarta ba”. _ “Kar ki sare wa kanki gwiwa da wannan hasashé-hasashen ‘Salma, ni ban goyi bayan’ mutum ya tauye wa zuciyarsa abinda take so ba matukar zai amfane shi. Adamu ya cancanci a’ so shi kuma ya cancanci zama miji saboda haka sarewa kai gwiwa ne ki dinga sonsa tare da kallon taki gazawar ko wacce iri ce” Tun da. Sa’adatu ta ambata Adamu ya cancanci a so shi Salma ta saki baki tana kallonta cikin shakku da alamun neman ba’asi. Sa’adatu ta lura da ita don haka ta amsa mata kai tsaye, Kyautata wa iyali a tsatso Alh. ya tsinta, haka kakansa yayi, haka babansa yayi shi ma gashi ina sahun farko na matan da ke jin dadin miji ina kuma da akinin Adamu ba zai yar a  Kasa ba,Www.bankinhausanovels.com.ng wannan yasa tun kafin ma ki fara sonsa nayi miki sha’awar aurensa. Salma ta rausaya kai kawai ta nemo abin cewa ta rasa, amma dai zuciyarta na raya mata ko babu abin moro a Adamu ita dai ta fada tarkon sonsa ba tare da sa ran ko a tukwici ya kyautata matan ba. “In kuma kin ga na Kyale tawa hobbasar shikenan, amma ina da yakinin in na sa hannu ko Adamu ya Ki Hajiya sai ya aureki....” Cikin faduwar gaba da dukan zuciya Salma ta sami kanta da rawar jikin kada wa Sa’ a kai baki na rawa ta ce, “Na amince ki sa hanaun Anti. _ “To ba ni sati biyu ki gani’” | Anti sa’a ta fada cikin karsashi da yarda da kai. 


*******


Sai Karfe sha daya na safiya ya sami shiga gidansu don ya gaishe da Hajiya, suka a gaisa ya ci abincinsa suna hira. Www.bankinhausanovels.com.ng  Wajen sha biyu sai ga kiran Salmanu ya | shigo, sai a sannan ma ya tuna yadda suka rabu. Yana ta faman tuntsira dariya ya daga wayar, | “Malam gobe-da-nisa’ ’ Salmanu ma ya tuntsire da dariya yace; “Kai na fi haka mukami, ‘Malam ba-jira kawai zaka kira ni’ | Adamu ya sake tuntsirewa da dariya, kafin yayi Magana Salmanu ya tare shi, “Kai babu sanya fa! Ina hanyar gidanku da fatan ka tanadi kudin nan?” “Sai dai in ni zaka kai kasuwa ka siyar amma ko na tauna goro ni kam ba ni da shi” Salmanu ya sauke dogon tsaki yace, - “Malam Yawa kake wallahi” > Kafin Adamu yayi Magana ya kashe wayar. Shi ma Adamu ya sauke tasa yana bin ta da kallo da murmushi, —_. Jikin Hajiya a sanyaye ta Kurawa Adamu ido, | ‘Da wa kayi waya?” Salmanu ne“ kai tsaye ya amsa Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu da yazo jiya? : _ Ta sake tambaya cikin alamar tuhuma. Cikin dauriya Adamu ya kada kai. Ya san Hajiya na son Salmanu amma sam bata son mu’amalarsa da danta don haka yanzu duk sai ya tsure, gani yake kamar zata iya shiga zuciyarsa ta ramfo kasuwancin da suke shirin. Kullawa ta kafa musu Kusa. Hajiya ta sake sanya masa ido cikin shakku “Amma maganar kudin naji kuna yi? Ya fara hirji cikin zuciya. kuma yana iyakar Kokarinsa na boye damuwar fuskarsa lokaci guda kuma zuciya da kwanyarsa na saka wa Hajiya amsa, . Kamar ya san ina cikin halin ha’ula’ In neman sana’a, jiyan nan sai gashi ya zo min da maganar mu fada aikin gini mana? Shima ana samu kudi musamman na kWangilar tituna ko gine-ginen gwamnati da ake samu, a wuni daya kusan kullum sai mutum ya sami dubu biyu zuwa sama., Hajiya taji hawaye na neman kece mata amma ta danne shi. “Sai kai kuma kace ma. me?” Www.bankinhausanovels.sannan  - “Ni kawai sai na. amince, don dama akan gwiwa nake da neman sana’ar’ Hajiya ta sake jin wani yaji ya shake ta na tausayi da takaici, ba tare da ta shirya ba ta ji ta - tambaye shi, _“To kudin da naji yana Magana na meye? Cin hanci zaku bayar kafin a dauke ku aikin?” Nan ma bai yi Kasa a gwiwa ba ya amsa mata yana dariyar yake, “Haba dai, wannan ai sai aikin gwamnati. Wukar sumunti zamu siya kwangiri da sauran kayan aiki, in masu daukar aikin suka gan mu . da shirinmu sai sun fi gane cewa da gaske -muke, saboda ba ma so muje a Kananan leburori” Hajiya ta saci idonsa ta goge Kwalla. Cikin shanye damuwa a murya ta juyo ta dube shi, “Wannan sana’ar da wannan rayuwar sun fi baka sha’awa ko Adamu? Kaico baka iya zabi ba kuma tsaurin ra’ayinka aikin banza ne da wofi tun da bai san inda gata da kamata _suke ba bare ya nemo maka su” Yayi fuska ya kawar da kai, kamar zai yi Magana sai kuma a hadi  abarsa. Www.bankinhausanovels.sannan Hajiya ta daure shaKar hanci. ~“Menene wahala a karatu da yiwa: kai kyakkawan gini har da ya fi aikin leburanci — wahala ko jiran tsammani.. Kamar Adamu zai cigaba da yi mata kunnen uwar shegu, amma da ya tuna cewa in ya dauki wannan matakin ita. kuma zata cigaba da kwakkwafarsa sai kawai ya murje ido ya fara shirin yi mata bore, “Sau nawa kika yi min alKawarin cewa ba ' zaki sake yi min maganar karatu ba? Hajiya in * - gani na ne ya isheki ki sha kuruminki ina fara sana’ata sai ki wuni ki kwana ma baki sanya ni a ido ba....” _ Ya fara kokawar tashi yana barazanar tafiya kamar yadda ya saba yi mata. . Da alama ta rasa abin yi yau, a maimakon kira shi ta lallaba kamar kullum yau kawai sai ta sanya masa ido. Shi da kansa ya ji kamar bai kyauta ba sai ya dan dakata a Kofar daki yana cigaba da mita cikin yanayi kamar zai yi kuka. Ko ban fada wa kowa dalilina ba aike dai ban boye miki ba Hajia nace aure nake so an ce Sai na yi karatu, shin a duniyar nan ni kuwa Www.bankinhausanovels.com.ng in ban tsani karatu na tsine masa ba anya akwai wanda zai tsine masa?” Har yanzu kwanyar Hajiya ta kasa dawowa kan doka da oda bare ta yanke hukunci, kallon ~ Adamu kawai take zuciyarta cike da fargaba iri-iri. :Shiru. duk sun yi jingum-jingum shi yana dogare nauyi da kunya sun hana: shi tafiya ita - kuma tana ta faman kallonsa cikin hada kan kare da na doki. Sai daga can ta nisa, - “To kayi tafiyarka mana’. = Ya ji wani turus don bata taba yasar da fishinsa ba sai yau. Har yayi gaba kamar zai tafi cikin rashin Kwarin gwiwa sai kuma ya dawo cikin sanyin jiki, da muryar tausayl yace mata,“To kin amince in je?” “Ina?” ._. Ta tambaya cikin rashin fahimta. Ya amsa, “Kwadagon ginin ” “Ina da wannan mutuncin ne?” ‘ Ya dube ta saroro Www.bankinhausanovels.com.ng - Ta kada kai mai nuna yaKini, - “Kwarai da gaske, na san da ina da wannan mutuncin ko alfarmar a wajenka da kafin ka zartar da hukuncin sai ka zo ka same ni ko kasami yayanka, to yanzu me kake son in ce” Ya dawo cikin Karfin gwiwa ya nemi guri ya zauna yana dubanta kai tsaye, “Idan na ci. baya a. Rayuwa ko na kasa albarka ina’ da yakinin da -sanya hannunki Hajiya, duk al’amurana sai kin kushe kin - turbuda musu kasa kuma ba haka na ga kina yi wa Alh. ba......° Sal ya zarce da shasshekar kukan da yanzun nan yaji zuwansa makogwaronsa, ba dan tausayin Hajiya ba sai Husna da ta dan kawo shawagi kirjinsa daidai wannan lokacin. __, _ Dole ya baibaye Hajiya da tausayi ita ma ta ji kukan na neman kamata, nan da nan ta hau girgiza kai tace, * “Sam ba haka ba ne karka tauye wa kanka albarkar mana.. . Ta katse maganarta saboda shagala da - Kallonsa tana matsar hawaye sai ta hau tunanin. me ya sa shi kukan? Suka jima haka Www.bankinhausanovels.com.ng har ya gaji ya share hawayensa cikin nutsuwa kuma ya dube ta ya fara yi-mata sallama. Ta miqe cikin sanyin jiki tana dakatar da shi, : “Tsaya ka karbi wani saKo” Bata jira cewarsa ba ta tashi ta wuce uwar daka. Ba jimawa ta fito dauke da leda. mai yalo da baki, da alama tufa ce a ciki. Tana zuwa ta mika masa. ° Ya karba fuskarsa cike da alamun rashin fahimta ya karba ya buda, sai ya tarar turmin atamfa da na leshi ne. ya sake dawo da ido kanta cikin alamar tambaya. . Da alamun karsashi Hajiya ta ce masa, Ankon da Salma ta baka ka siyo mata ne, wanda na dauki nauyin sai maka ka bata, gashi nan sai ka kai mata kar ma ka ce ni na siya” Zuciyarsa ta buga da jin wannan siyasar ' amma fuskarsa ta shanye, nan da nan ya fara murmushin yake muryarsa na rawa yace, Ai kuwa kin ceto ni Hajiya, na san da zummar Kurewa wannan tumbular yarinyar ta kawo min tallen anko” Ba wannan sharhin Hajiya ta so ba wanda ke nuna abinda take wa har yanzu gefensa ma Adamu bai bi ba, wato Kulla Kauna tsakanin Adamu da Salman, musamman kuma a daidai wannan lokacin da yake ta yi mata kururuwar aure yake so, tana da yaKinin in dai an so zama -dafiya to gara ma ayi masa auren a kuma zuba wa sarautar Ubangiji ido. Cikin sanyi jiki ta mika masa nairarta dubu datake makale ahannunta, _ “Ungo wannan ka rike a hannunka ko zata buKaci kudin dinki, ka ga ba sai ka bada maza ba” : Ya sa hannu ya karbe kudin ya kalmashe a aljihu yana tura wa Salma ashar cikin Zuciyarsa, ya rasa da abinda wannan tulun yariyar ta rudi su Hajiya har suke ganin bata da abokin rayuwa sai zukeKen saurayi irinsa. Ya sake jaddada wa Hajiya godiya sannan ya sa kai ya fice da kaya a hannu zuciyarsa wadda ya dinga rantsewa ko tayi kwalliya ba kyau take ba, lallai mijinta zai sha barnar kudi 


Hmm LABARI FA NATA TAFIYA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU DOMIN JIN YADDAH ZATACI GABA DA KAYAWA WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CH"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...