MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 1 BY REALFAUZAHTASIU - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 1 BY REALFAUZAHTASIU

MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 1 BY REALFAUZAHTASIU

- - Post a Comment

 MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 1 BY REALFAUZAHTASIU


                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MIJIN AMINIYATA 


Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya ringa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qaunarsa and end wasu abubuwa sun faru. 


Yanayi ne me sanyi da kwantar da hankalin duk Wanda zuciyarsa ke cikin nutsuwa inda zai kasance matashin hankalin duk wanda nutsuwa tayi qaura cikin rayuwarsa, yaf yaf yaf ruwan yake sauka a saman manyan motoci da suka parkar a harabar Event center din da akayiwa laqabi da *Beautiful bridal*

Bude qofofin akayi a tare Kuma lkc daya wasu zafafan kyawawan yammata suka fara fitowa a jere a gefe guda Kuma sautin sassanyar iska da kida me zama a zuciya ya qawata gurin da yasamu qawatuwa da wasu kyawawan manyan flowers abindai sai Wanda yagani.

Salon kidanne ya sauya lkcn da wata arniyar mota ta samu matsuguni aka bude mawa wadanda ke cikin motar suka fito yammatane guda biyu kyawawa cikin shigar da take nuna amare ne sanye suke da farar wadding gown data karbi jikinsu, tare Kuma a lkc daya Suma angwayen suka  fito a tasu motar suka nufosu inda suke tsaye kansu a lullube.


Tahowa angwayen sukeyi inda sukuma amaren suke tsaye qiqam bude musu fuskar akayi inda duk Wanda ke gurin yayi mutuwar tsaye suka zuba musu ido dukkansu kyawawane na kwatance daya farace tas kamar bargonta zai fito inda dayar ta kasance wankan tarwada duk da hasken ya rinjayi baqin da ya sirka fatarta.

Dawowa sukayi a tare suka sauke idanunsu aka cikin na angwayen wankan tarwadar ce ta saki wani murmushi ta Kama hannun farar ta kamo hannun daya cikin angwayen ta saqala a nata ta bude Dan qaramin bakinta tace “Hml Mr Ja'afar Wakil"

Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke tare da qoqarin tattaro nutsuwarsa ya hada guri guda ya kama hannun amaryar tasa ya janyota jikinsa har yanzu idonsa nakan na dayar budurwar ya bude bakinsa cikin sanyin yanayi yace “koda bantaba ganinki ba kamanni da siffa da yanayin sanyin halitta ya bayyanamin waceceke tabbas tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicci kyawawa guda biyu Kuma ya sanyasu suka zama aminan juna..."

Dariya wanda yake babban aminin angon yayi yace “Rafi'ah Nasir Darazau kenan aminiyar arziqi wannan itace remote control din matarka aduk lkcn data rikice maka to ka nemo Rafi'ah zata daidaita maka ita cikin sauqi" har yanzu idon Ja'afar akan Rafi'ah yake inda har ta fara qosawa da kallonsa ta juya ta dubi dayan tace.

“Muhseen kodai abokinka yayi ciwon makanta ne Bestie mijinki ya taba samun eyes issues ne" hannu takai zata janyota ta janye da sauri tana murmushi yayi saurin riqota yace “kinga Ni'imah qyaleta zamu rama ne danma ta samu an kalleta shine take wani jin dadi?" Muhseen ne yace “abin mamaki miskilai biyu ku mu qarasa fili nasan mu ake jira a fara program"

Takawa sukayi muhseen na gefen Ja'afar ita Kuma na gefen Ni'imah suka Isa cikin Hall din inda gurin ya kaure da tafi da sowar mutane a haka suka qarasa ango da amarya suka zauna MC ya fara aikinsa bayan kowa ya nutsane ya gabatar da Muhseen da Rafi'ah a matsayin wadanda zasu bada tarihin amarya da ango.


Rafi'ah ya fara bawa Abin mgn ta karba cikin qwarewa tayi sallama tare dayiwa kowa godiya da nuna farin cikinta da zuwan wannan rana ta farane da gabatar da kanta a matsayinta na best friend ta amarya sannan tabada tarihin amarya kamar yanda aka buqata sannan  tabada tarihin amintarsu anan ne zuciyarta ta karye hawaye ya fara zuba a idonta inda take cewa.

“Tabbas burin kowacce mace a rayuwa shine samun masoyi na haqiqa amatsayin miji duk da yau itace rana ta farko dana fara ganin Mijin Aminiyata na yaba da zabinta Kuma nayiwa Allah godiya daya kasance a matsayin mijinta Ja'afar Ina cikin wani yanayi na quncin zuciya saboda zan fara rayuwar kadaici ka rabani da bestie na  munsan dama wannan ranar zatazo amma bamu shirya yanda zamu dauketa ba inayi maka fatan nasara da addu'ar riqemin Bestie na amana don Allah bayan matsayin miji da ubangiji ya baka ka maye Mata gurbina a matsayin amini kada kabarta tayi kuka ko kewar rashina duk mace haka ta gada sai haquri haka Allah ya tsara mana mubar iyayenmu mubar yan'uwanmu da qawayenmu mu tafi sabuwar rayuwa da itace zata zamo hanyar samun tsiranmu duniya da gobe kiyama....."


STORY CONTINUES BELOW

Muryarta ce ta fara sarqewa da gaske tayi qoqari domin tun a harafin farko kuka yakeson qwace Mata inda gurin ya dauki kabbara da tafi a lkc daya, bawai don ta rasa abin fadaba saidon ganin qawar tata itama tana kuka yasata miqawa MC din abin mgnr  ta nufi step din zata sauka kasancewar duk wata nutsuwarta ta qaura sun dade suna kukan zuwan wannan ranar Amma Basu tabajin dacinta kamar yau datazo ba.

Jitayi an riqo hannunta ta baya ta juya da sauri idonta na shararar da hawaye ga mamakinta sai taga Mijin aminiyar tata ne murmushi ta qaqaro ta janye hannunta ta bude bakinta tace “karka damu Ja'afar bakayi laifiba hakan shine cikar gatan kowacce ya mace munsan da zuwanta rashin hankaline yasa muka kasa shiryawa zuwan nata..."

Fakar idon mutane yayi ya dora hannunsa a bakinta yana me qare Mata kallo yanajin bugun zuciyarsa daya fara tun farkon haduwarsu yana qaruwa yace “Nasani Rafi'ah amma Ina Zaki?" Janyewa ta kumayi tana saita qoqarin bashi space kasancewar qarancin taqin tsakanisu yayi yawa tace “zan zanje na sallami baqinmu ne abokan karatunmu"

Jinjina Kai yayi yace “Ni'imah tace kince idan kika kawota tafiya zakiyi why?" Shiru tayi tanaci gaba da jan zuciya yayi murmushi yana ayyana abubuwa da yawa a ransa yace “kiyi har kada ki tafi ki jira a tashi mu tafi mu tare mu kaiku gda please kada kiqi kinji?"

Daga masa Kai tayi ta juya da sauri saboda tagaji da gwama numfashi dashi binta yayi da kallo shikadai yasan me yake saqawa a ransa ya juya ya koma gurin zamansa ya kamo hannun Ni'imah yace “ta hqr daqyar qawarnan taki akwai wayo" murmushi tayi me hade da kuka tace “danma kaine tana ganin girmanka da bazata tsayaba kafaffiya ce akan ra'ayinta daqyar Dad ya rarrasheta tazo shima don ance ita zatayi history ne"

Numfashi yaja yace “tanada kyau...." Dariya Ni'imah tayi kadan tace “danma bata cikin nutsuwa ne shiyasa duk a hargitse take ko kwalliya taqiyi" da wannan akaci gaba da gabatar da dinner din duk wani motsi da Rafi'ah takeyi idon Ja'afar akanta bayako qiftawa hakanne yasa tasha jinin jikinta ta koma gefe tana caje kanta ko want abune yasa yake kallonta da bazai iya fada mataba


Ta jima tana qarewa kanta kallo a madubin motar kawai saiji tayi ance Mata “sannu" a tsorace ta juya kuma a firgice hakan yasata karo dashi tayi taga taga zata fadi yayi saurin tarota ta daidaita a qirjinsa yaja wata ajiyar zuciya tare da dora kansa saman kanta ya shaqi qamshin gashinta, jin yasa hannu ya qara shigar da ita jikinsa tayi saurin janyewa don ganin waye.

Ja tayi da baya da sauri tare da cewa “lfy?" Duk da baiji dadin tambayar ba haka ya hadiye ya shafa kansa yace “ankirani a waya na taso don amsawa kawai na hangoki so nayi tunanin kukan kikaci gaba dayi shiyasa na qaraso am sorry please na tsorataki ko?" Numfashi taja ta furzar tace “ok ka koma gurin Bestie bani bakai zata shiga damuwa"

Binta yayi da kallo yace “ke Kuma kinason zama a damuwa ko?" Wani kallo tayi masa daya sanya lakar jikinsa tsinkewa tace “ita ce yake wajibi a gurinka kayi qoqarin gusar nata da damuwa nima inada me gusarmin da tawa shi nake Shirin Kira ma yanzu kaje na gde da kulawa...."


Batayi aune ba tajita a qasansa a jikin mota yadan janye kadan yace “ni na rabaki da farin cikinki saboda haka ni zan samar Miki da wani farin cikin Rafi'ah kijira" haka kawai ya fada ya juya yana amsa waya ya koma ciki tabi bayansa da kallo tare da cewa “wannan wanne irin mutum ne?"

Tabe baki tayi ta juya taci gaba da harkokinta hakanan taji ranta yana baci batason mutum me shisshigi a rayuwarta wannan dalilin ya hanata komawa gurinsu taci gaba da sallamar baqi bayan ta gama sulale ta koma can qarshen hall din ta zauna tana chart dinta da qawayensu.

Yawanci wadanda Basu samu damar zuwa dinner din bane suketa bata hqr tare dayi musu fatan alkhairi Saida taji ankusa tashi sannan ta tashi ta koma mazauninta cikin dan zaman da  tayi dau dagowar duniya idonta a cikin na Ja'afar yake fadawa taja wani dogon tsaki da yasasu dagowa duka harda Muhseen daya lura da abinda ke faruwa tun dazu, dubanta yayi yace “yadai ammata?" Murmushi ta qaqalo tana kallon Ja'afar din tana yatsina fuska tace “saurone ya takuramin anan gurin wlh tunda ankusa tashi ku sameni a mota kawai"


Bata jira amsaba ta miqe shina Muhseen ya miqe yana tsokanarta yace “daki ai baya tashi ragaya ta zauna ba muje tunda mun sallami baqinmu mu jira ango da amarya danni wlh bacci nakeji ma" da wannan suka jera suka Isa inda motar take suka shiga suka zauna suna dan taba hirarsu.

Duk hirar akan bikinne sukeyi inda rabin hankalinta yake kan tunanin dalilin wannan mayataccen kallo da bibiya da mijin aminiyarta yafarayi Mata tundaga kallon farko, kasa jurewa tayi ta dago ta dubi Muhseen da hankalinsa yake kan danna wayarsa tace “Mr Muhseen Wlh banason kallo a rayuwata takurani yake ya hanani sakat"

Dagowa yayi ya zuba Mata ido yace “waye ya dameki da kallo?" Ajiyar zuciya taja ta kawar dakai tace ka share kawai" yariga yasan inda ta dosa fada masane bazatayi ba hakan yashi sake kallonta yace “to Rafi'ah meye laifin mutane don sunbawa ido abinci kedince Allah ya ginaki ginin gaske wlh na dade banga mace me cikar halittarki ba kinsan ba kowa yake iya gani ya dauke Kai ba kekuma gaki kamar me aljanu da mutum yace yanasonki sai ki Kama gaba dashi"


STORY CONTINUES BELOW

Murmushi tayi tace “wannan dalilin ne yasa banason kallo saboda nasan daga kallo saqo yake shiga zuciya nikuma na tsani ma ace anasona wlh tunda Yassar ya rasu nakejin bana sha'awar sake soyayya da kowa" tabe baki yayi yace “wanda ya tafi ya tafi kenan bazai dawo ba garama ki manta da komai ki fara sabuwar rayuwa kina ganidai ga aminiyarki yanzun bikinta akeyi ke kanki bazakiji dadin rayuwa ke dayaba ko Ina kun tare ku tashi nan ku fadi csn kwanciyar bacci ke rabaku itama in kunso"

Hadiye wani Abu tayi me ciwo tace “babu komai ana tare insha Allahu inasa ran zabi mafi kyawun kyau gurin lillahi Muhseen badagani bane zuciyata takasa karbar madadin Yassar shi na fara so shi ya huda zuciyata shiyasa madadinsa yayi wahala"

Ji sukayi ana qwanqwasa glass din gabanta ya fadi lkcn da Muhseen ya sauke glass din idanunsa akanta yace “kazo ka sata a corner me kake karanta mata?" Shafa kansa yayi ya bude masa yace “kawai nasiha nakeyi Mata itama ta fitar da miji cikin masoyanta tayi aure saboda lkc qurewa yakeyi" bai wani bawa mgnr muhimmanci ba suka shiga shida Ni'imah Muhseen yaja motar suka tafi.

Tunda suka taho babu me cewa wani qala lkcn da sukaje duk motocin sun jima da zuwa anayin parking Rafi'ah ta bude qofar tanayiwa Muhseen Saida safe ta shige cikin gidan mutane nayita yimata tsiyar saura ita itama ta fitar da miji suzo susha shagali murmushi kawai takeyi ta shige ciki ta haye saman ta fada dakin Ni'imah ta kwanta tana mayar da numfashi.

A haka Ni'imah tazo ta sameta t zauna a gefenta tace “Sweet yace kiyi hqr da laifin da yayi mki kike gudun hada inuwa dashi"

Dagowa tayi ta dubeta tace “baimin komai ba Bestie kaina kw ciwo nakeson samun relief" miqewa Ni'imah tayi ta cire kayanta tace “ke kika sani ni wanka zanyi na kwanta" itama miqewa tayi ta cire rigar jikinta ta daura zani Ni'imah na fitowa ta fada wankan tana fitowa taja bargo tare da addu'a bacci ya dauketa.

Saboda gajiyar da sukayi Basu farka ba sai da Rana ta fito shima momy ce mahaifiyar Ni'imah tazo ta tashesu suka tashi Ni'imah tayi wanka tayi sallah kasancewar sun makara ita Kuma dake ba sallar takeyi ba tayi wankan sukazo sukayi zaman shiryawa me kwalliyar ta  shigo tayi musu suna gama shiryawa aka daura auren rungume juna sukayi suka saki wani ihu daya janyo hankalin kowa dake gdan.........


Nufosu sukayi da sauri suka riqosu aka rabasu daqyar tare da zaman rarrashinsu itadai Rafi'ah zazzabi ne ya rufeta ta koma ta kwanta tana rawar sanyi angwayen da suka shigone sukaga meke faruwa Ja'afar ya Kira wani abokinsa likita yazo ya dubata yabata magunguna tasha ta kwanta yinin ranar bata iya tsinanawa kanta uwar komai ba sai bacci da takeyi har aka gama bikin da yamma ta farka anata shirye shiryen Kai amarya batare data bari kowa yaganta ba ta sulale tabar gidan bikin ta cikin saa tana fita tasamu napep ta nufi unguwarsu ta shiga gidansu babu kowa sai kishiyar mamanta mama tana wajen kai amarya.


Aunty Murja tana ganinta tasan ba lafiya ba ganin bata saurari kowa ba ta shige dakinta ta kullo yasata miqewa tabita ta tarar da ita zaune ta hade Kai da gwiwa sai kuka takeyi, zama tayi kusa da ita tace “ni bantaba ganin irin wannan rayuwa taku ta qaryaba to dawwama zakuyi babu aure yanzu da Allah yayi naki auren ita ya zatayi da sai yanzu Allah ya nufi nata? Dama kun hqr kunsawa zuciyarku hqr da salama kowacce mace wannan lkcn take jira ita ta tafi Abuja ke Kuma waye yasan inda zaki"

Shiru tayi batace komai ba sai kukanta da takeci gaba dayi ganin bajin lallashin zatayi ba yasa Anti Murja miqewa tacd idan ya isheki kyayi Shiru nikam nayi nan" tana fita wayarta tafara ring ta duba taga number Bestie ce ta mayar ta kife saboda bata buqatar wani Abu da zai qara daga Mata hankali a wannan lkcn hakance tasata tayi kwanciyarta, Ni'imah tayi Mata misscall yafi ashirin taqi dagawa qarshe ma ta kashe wayar haka tana kuka tana Kiran Bestie aka sata a mota aka nufi wani Martaba Estate dake cikin garin na Bauchi domin Kai amarya.


Saida komai ya lafa akakai amarya dakinta gdanta babba me kyau da tsari an zuba kaya Kuma ankashe kudi a gidan kasancewar iyayen Ni'imah masu haline shima kuma mijin da arziqinsa dan sarautar Azare ne Ja'afar Wakil suna tashen kudi da mulki mahaifinsa ne abokin mahaifin Ni'ima sune suka hada auren cikin wata biyu akayi komai aka gama abinka da masu data a hannunsu.

Angwayen ne zaune cikin mota Muhseen ya dubi Ja'afar yace “kai kanada matsala baka iya control din zuciyarka ba don Allah Ja'afar na roqeka kads ka soma wannan katobarar ita zuciya tausarta akeyi ba komai ake qyalets tayi abinda takeso ba kada kasa ka zamo silar yankewar wannan kyakkyawan zumunci da aka faroshi tun yarinta Ja'afar Mata basuda hankali akan wannan qaramin issue din sai hankalin kowa ya tashi koda yake inada yaqinin Rafi'ah bazata taba baka fuskaba"

Girgiza Kai yayi yace “Muhseen bakada adalci a rayuwarka 34 years muna tare dakai katabajin nace maka inason mace da aure wlh da gaske nakeson Rafi'ah tsakanin jiya da yau zuciyata tana azabtuwa da qaunarta bansan meyesa hakan ta faru ba meyesa bansanta ita kadaiba meyesa batazomin babu alaqa ba sai tazomin a matsayin aminiyar matata Muhseen kabani mafita wlh idan har banga Rafi'ah a daren nan ba bazan iya yiwa yarinyar nan komai ba Kai nifa badan lkc ya qure ba da zuwa zanyi na samu Dad na fada masa a janye na samu wacce nakeso wacce na dade Ina mafarkin samu irin matar da na dade Ina zanawa a zuciyata"

Sarai yasan halin abokin nasa iyakar gaskiyarsa yake fada shidin ba mutumne ma'abocin qarya ba kuma bai iya boye Abu a ransa ba, ji yayi ya damqesa yace “don Allah don annabi kakaini naganta wlh babu abinda zance Mata Muhseen iyakar ganine insson sanin halin da take ciki bansan hanyar gidansu ba da tuni na tafi"

Badon Muhseen yaso ba ya juya motar daga gurin da sukazo siyawa amarya kaza suka nufi unguwar su Rafi'ah a bakin get suka tarar da Abba da me gadi suna tattaunawa saboda haka Kai tsaye shi suka nufa suka gaisa yace bai ganesu ba Muhseen yace “Abba surukanka ne mijin yarkane da ka aurar yau Ni'imah shine tace muzo mu gano Mata meye ya hana Bestie dinta zuwa rakata gidan mijinta"

Dariya Abba yayi irin tasu ta manya yace “kayy Amma yaro yarone shine kums kuka dauko jiki Kuma da taya shirme hauka, bari na shiga na gano muku ita  naji uwayenta suna cewa batada lfy ma"

Shigewa yayi ciki Ja'afar ya miqe ya daga hannu sama yayi hamdala babu jimawa saiga Abba ya fito yace “ai kawai ku shiga tanacan ma amai taketa fama ita dama jinyarta amai kamar me yaron ciki" wani dadine ya cika zuciyar Ja'afar ya fadada murmushinsa Muhseen ya harareshi tare dayin qwafa kan ya ankara tuni Ja'afar yaje qofar falon suka shiga da Abba jansu Abba yayi har saman ya tura qofar ya shiga tana kwance daga ita sai dogon sikert da taja har qirjinta ko bra babu a jikinta har yanzu kuka takeyi Ammi na rarrashinta tsaki Abba yayi yace.


“Do Allah amina ku qyaleta tayita kukan gajiyane batayi ba yo naji iskanci so kike a qyaleta kuyita babare a gari ke babu aure ita babu kaji wani sakarci" sake shigewa jikin Ammi tayi ta shafa kanta tace “to bandama abin me sunan manya kema ai addu'a mukeyi Allah ya kawo mijin mu auraddake kema kije kiyi bautaTashi tayi zaune daidai lkcn da Ammi suke gaisawa dasu Muhseen idon Ja'afar akan qirjinta ya sauke numfashi tare da cewa “ya jikinki" wata uwar harara ta watsa masa ta dauki hijjab dinta ta zura ta koma can qarshen gadon ta kwanta ba Shiba hatta Abba Saida abin yabashi dariya yace “to Ja'afaru kai me laifine fa ka rabata da aminiyarta"

Murmushi yayi a ransa yace “kema very soon zan daukeki sai naga ya amintar zata kaya tunda kunayiwa dodo daya tsafi" a fili kuwa cewa yayi “kiyi hqr bansan da wannan amintar ba dana bari anyi Rana daya Kinga da duk haka bata faruba".......

*

Murmushi Abba yayi yace “yo shirmene irin nasu Koda anyi Rana daya ai bazaa tare gda daya ba Tunda kowacce dai mijinta dole dabanne" shafa Kai Ja'afar yayi yana sake saita injin idonsa akan Rafi'ah data koma qarshen gadon ta qudundune yaja numfashi aransa yanajin dama ace itace zaije ya tarar a gida matsayin matarsa Amma a fili saiya duba agogo yace
"Wanne saqo zaki bani gurin Bestie dinki zamu tafi dare yayi" numfashi taja batare data juyo ba tace “fatan alkhairi" daga haka bata Kuma qara ko harafi daya ba ya sake kafeta da ido Saida Muhseen yajashi suka fita a parlour suka hadu da Abba sukayi masa sallama suka tafi, Basu jima da fitaba suka turo maigadi da ledojin da suka siyo domin kaiwa amarya suka fice daga gidan.
Dubansa Muhseen yayi ganin yanda ya zubawa rufin motar ido yasashi dafashi yace “akwai qura mutumina ka canza tunani don Allah kada ka zamo takobi me yanke qauna kayi qoqarin dannar zuciyarka da hqr da abinda yake halal kodan mutuntaka da Kuma kunya" batare da ya kalli Muhseen ba yace “ka tabbatar da halal dinne dai ko?" Jinjina Kai Muhseen yayi Ja'afar yayi murmushi yace “indai ka yarda halal dinne to kada ka qara cemin na hqr Muhseen bana iya control din zuciyata akan abinda takeso"

+
Parking Muhseen ya sakeyi ya fita ya sake siyo kayan siyan bakin amarya ya dawo suka tafi suna zuwa yayi musu jagora har parlourn da Ni'imah take zaune tana jiran zuwan angonta suka shiga da sallamarsu duk da cewa Muhseen ne yayi sallamar, Bata amsaba sai qarawa kukanta sauti da tayi suka zauna Shiru na dan lkc shidai Ja'afar zuciyarsa ce ke bugawa inda Muhseen yake tausayin Ni'imah da Rafi'ah kasancewar yafi kowa sanin kafiyar Ja'afar tunda ya furta yanaso to zaiyi duk me yuwuwa yaga ya samu saidai idan abinne yafi qarfinsaGyaran murya Muhseen yayi yana mai farawa da addu'a sannan yayi musu yar tunatarwa ya miqe tare dayi musu sallama  Ja'afar ya rakashi ya tafi shikuma ya juya cikin gdan ya zauna a gefen Ni'imah yana kallonta sunfi 30 minutes a haka kafin yasawa kansa jarumta yakai hannu ya bude fuskarta tare da matsawa ya janyota jikinsa ya bude bakinsa a hankali yace.
“Kukan ya Isa haka tashi muje muyi sallah mu kwanta" sake narkewa tayi a jikinsa ta bude bakinta a hankali tace “Bestie na Ja'afar bansan halin da take ciki ba na Kira wayarta taqi dagawa" murmushi yayi ya shafa fuskarta ya dora bakinsa saman goshinta yace “cool down please bestienki tana lfy yanzu kafin mu qaraso saida mukaje muka gano halin da take ciki Kuma da safema zan koma kinji"
Daga Masa Kai tayi cikin qauna da sallamawa abokin rayuwa kai ya miqe itama ta miqe yana riqe da hannunta suka isa bathroom din yayi alwala itama tayi suka fito yajasu sukayi raka'a biyu tare da doguwar addu'a a qarshen addu'ar yake fadawa Allah ya shige masa gaba ya bashi nasara akan abinda yasa a gabansa ya dade yana addu'ar sannan ya miqe ya  dubeta yace “dauko Mana flat a kitchen yunwa nakeji"  miqewa tayi taje ta dauko ta dawo sukaci abincin sukayi brush sukayi Shirin kwanciya.

Koda suka kwanta ya dade yana saqawa da warwarewa kafin ya arawa kansa jarumta ya shige jikin amaryarsa ya fara rage musu nisan lkc ta hanyar yan wasanni Wanda a zahiri yanayi ne don yasan duk amaryar duniya a darenta na farko hakan take buqata Amma badon a kankin kansa yanajin dadin yanayin ba.
Haka dai ya rinqa rarrashin Ni'imah yana bata hqr har yayi nasarar kaiwa ga inda yakeso yakai din ta qanqameshi tana kuka tana kiran Bestie dinta shikuma ya dora bakinsa a nata, dadewa sosai yayi yana raya daren kafin ya samu nutsuwa ya janye jikinsa daga nata ya shiga  bathroom ya hada Mata ruwan zafi yazo ya dauketa ya gasa Mata jikinta har yanzun Kuma kuka takeyi tanata jijjiga kai shidai baice qala ba qwarai yadan samu nutsuwar da kowanne ango yake samu a darensa na farko da amaryarsa,
Bayan ya gama taimaka mata suka kwanta tana lafe a jikinsa shikuma zuciyarsa na gurin abar muradinsa aminiyar matarsa Rafi'ah shidai kamar daren jiya bai rintsa ba Saida dare yayi nisa yanata tunanin ta inda zai fara.
STORY CONTINUES BELOW
Da safe ya rigata tashi ya koma palo ya zauna ya rafka uban tagumi shi kadai yasan yanayin da zuciyarsa take ciki yanajin sarewar gwiwa tare da qoqarin tursasa kansa ya janye daga wannan nannauyan qudurin amma ya kasa samun amintar zuciyarsa, baiji fitowarta ba saijinta yayi a gefensa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya riqota jikinsa ya dora lips dinsa a kuncinta yace “kin tashi lfy amaryata" kunyace ta kamata ta sunne kanta yayi murmushi yace.
“I hope babu inda yakeyi Miki ciwo girgiza masa Kai tayi yace “ok tashi mushiga kitchen ta tayaki ki sama mana abinda zamu karya bana jure yunwa kuma duk na juye Miki abinda naci daren jiya" sake sunne kanta tayi yayi murmushi yace “zama ki daina kunyarnan ne" da haka yajata kitchen din yasha mamakin yanda saishi ya rinqa cewa da ita kaza zakiyi kazafa duk bata iya wasu abubuwan na kitchen ba, yaja numfashi yana mamakin yanda akayi hakan ta faru budar bakinta sai cewa tayi.
“Bestie tayi tayi na tsaya na koyi girki ko a gurinta ne naqi  saboda ni gsky girki na bani wahala sweet a nemo kuku ko macen data iya girki takeyi ma sosai nake wahala a lamarin daya shafi kitchen" kallonta yayi da qananun idanunsa yace “meyesa qawarki ta iya ke baki iyaba?"
Dariya tayi tace “wannan ai ta daukarwa rayuwa buri 15000k taje tasa Abba ya biya Mata ta shiga cattering school tayi course na 3 months akan girke girke da kula da miji ita ta kasance me buri a rayuwar aurenta tanayiwa mijinta tanadin farin ciki da'iman dawa'un

Wani gwauron numfashi yaja ta dago ta kalleshi yayi murmushi yace “maxa yan gatan Mata Allah yabawa me rabon nan saa" amsawa tayi da Amin sukaci gaba da hirarsu bayan sun gama break din suka koma suka kwanta bai wani takura Mata ba saboda dan banzan raki gareta shikuma bai cikason qorafi ba suka dan taba bacci ya tashi yayi wanka ya fice lkcn goma saura saboda sanin da yayi zatayita baqi.
Kai tsaye Family house dinsu ya nufa ya kwashi gaisuwa gurin mahaifinsa sannan ya shiga cikin gidan matan mahaifinsa uku Hajiya Kaltume itace babba tanada yara biyu Zainab da Ummah sai Hajiya Fatsum wacce itace mahaifiyarsa itace ta biyu tanada su hudu biyu Mata biyu maza sai Hajiya Inna mace me hqr da hangen nesa ya daya Allah yabata Fiddausi Kuma itace qarama a gidan,
A zahirin gidan sarautar Azare wanda yake waje zaike sha'awar mutanen gdan kasancewar daga nesa zakace lfyr Allah suke zaune amma ta qarqashin qasa zaman bashida dadi Hajiya Kaltume da Hajiya Fatsum basa jituwa kullum cikin jifan junansu suke da mugayen asirai hatta Hajiya Inna da take gefe bata shiga lamarinsu idan tsiyarsu ta motsa ba basa barinta Amma dake ta riqe Allah sai ya kasance duk abinda du suka nufota dashi baya tasiri a game da ita.
Akwai wata shaquwa ta musamman taakanin Hajiya Inna da Prince Ja'afar wacce take ciwa Hajiya Fatsum tuwo a qwarya Amma ta kasa maganinta don ko tayi asirin rabasu baya tasiri wannan abin yasa ta qyalesu ta zuba musu ido amma duk lkcn data samu dama takan kushe Hajiya Inna a gurin Prince Ja'afar saidai yayi murmushi kawai tunda yariga yasan halin mahaifiyarsa.
To yauma daya shiga gidan Sarautar bai nufi bangaren mahaifiyarsa ba bangaren Hajiya Innah ya nufa domin ita kadai zai iya tunkara da damuwarsa ta bashi shawara ta gari, Saida ya faki idon mutane ya shiga ya isheta saman kilishi tana lazumi alamu sun nuna sallar  walaha ta idar ya nemi guri ya zauna kusa da ita yana wasa da yatsan hannunta,
Sallamewa tayi ta zuba masa ido tun shekaran jiya ta lura da rashin nutsuwarsa da farko tayi tunanin hidima ce da tasha kansa Amma ta fahimci har yanzu yana cikin damuwa, dafa kansa tayi tace “Zuciyar Inna sarkin gobe meye yake tabamin Kaine na fahimci damuwa a tattare dakai tun ranar dinner bikinka" kansa ya dora a kafadarta ya lumshe idonsa sosai mamaki ya Kama Hajiya Inna da taji dumi a kafadarta ta dagoshi tace “subhanallahi Baban  Innah me yayi zafi haka don Allah fadamin wlh nayi alqawarin baka mafita a kowacce damuwa ta rayuwarka kaji"

Rungumeta yayi ya fashe da kuka kamar wani yaro ta sake matseshi a jikinta hankalinta yana qara tashi duk da tasanshi da shagwaba kamar mace Amma kuka ba dabi'ar Ja'afar bace, ta jima tana rarrashinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya ta sanya gefen hijjab dinta ta share masa hawayen tace “kasa Innah a damuwa baban Innah fadamin mana idan baka fadamin ba waye zaka fadawa?"
Numfashi ya sauke yace “inasonta Innah bazan iya hqr da itaba wlh" sakin baki tayi tana kallonsa tace “to ai ka sameta baban Innah me Kuma kake nema?" Murmushi yayi me hade da Hawaye yace “not ba itaba Innah bantaba qinta ba kuma bantaba sonta ba itakuwa wannan daga kallon farko na fada komarta wlh daga daren ranar asabar zuwa yau zuciyata azabta takeyi akan Rafi'ah"
Dariya Hajiya Inna tayi tace “to Banda abin baban Innah wannan ai me sauqine kaida Allah ya halatta maka hudu kayi daya meye na damuwa dan kaji kanason ta biyu addu'a itace zakayi duk da nasan akwai qura domin mahaifiyarka bazata aminta da wannan sawalwalar ba zatace yaushe ma kayi auren da zaka dauko wani" share goshinsa yayi yace “ba ita kadai ba Innah kowa ma Innah Rafi'ah ta kasance aminiyar matat...." Wata zabura da Inna tayi tasashi yin shiru ta saki salati tace “garin yaya Baban Innah wannan ai abin kunyane Dama Pretty Raf kakewa wannan qwawar aikuwa dole ka hqr wannan amintar bakayi gangancin shiga tsakaninta ba to bandama abinka inakai ina son Bestie din matarka"

STORY CONTINUES BELOW
Kallonta yakeyi harta gama ya miqe zai fita tayi saurin riqoshi tace “kafa cire wannan tunanin a ranka zamu bata sarai dakai banson sakarcin nan naku na yayan zamani wlh ka kiyayi Hajiya Kaltume taji wannan katobarar takaGirgiza Kai kawai yayi ya fice ta dafe qirji tace “wannan da da rigimar tsiya kake inakai Ina wannan sakarcin" shikam yana fita bangaren Hajiya kaltume ya nufa suka gaisa tanata tambayarsa amarya ya amsa Mata da cewa da sauqi ya tashi ya fice, suka gaisa da baqi ya nufi bangaren Hajiya Fatsum ya tarar da ita tanata cika tana batsewa ya zauna yana gaisheta tana amsawa a daqile bai wani bawa fushinta muhimmanci ba   ya miqe ya fice ya dauki motarsa ya fice kawai ya rinqa zagaya gari ya jima yana yawo sannan ya Kira Muhseen yace masa yana gidan  ya rakiceshi suka fice yace.
“Rakani zakayi da dubo Rafi'ah" harararsa yayi yace “bakasan gidan nasu bane sains rakaka Kai nifa bazan yarda ka dauramin jarfa ba kaidai da baka tsoron abin kunya sai kaje kayitayi ka shiryane"

Bude Masa mota yayi yace “jeka kawai  don Allah basai ka zageni ba" ficewa yayi daga motar yace “eh naji bazani ba idan nayi niyyar zuwa ai basai naje tare dakai ba"  Bai kulashi ba yaja motarsa ya nufi unguwar tasu Rafi'ah me gadi ya bude Masa ya shiga ya turashi yace ayi masa sallama da Rafi'ah tana zaune a parlour Mado megadi ya shigo yace “Hajiya kinads baqo a waje" wani tsaki tayi tace “kaje kace bananan" kallonta yayi da sauri yace “baayi hakaba Hajiya baqin jiyane fah daya cikinsu ne ya dawo" murmushi tayi tunaninta abokinta ne Muhseen ta miqe tana gyara mayafinta ta fito tana dariya dake baya ya juya bata ganeshi ba ta qarasa takai hannunta ta lakaci wuyansa tace.
“Ya Bestie na ta kwana Muhseen jiya ban iya bacci ba inata tunanin yanda zasu kasance Bestie na akwai raki da mit...." Mgnr ce ta maqale lkcn daya juyo ya zuba Mata ido taja baya da sauri harda dan tsallenta tace “wayyohh sorry don Allah...." Yanda tayidin ne ya bashi wani nishadi yayi murmushi yace “Notting is true haka bestienki take ta cika raki" ajiyar zuciya tayi tace “tayi maka ko? Ai dama nasan zatayi saidai hqr" lips dinsa ya lasa qirjinsa na bugawa yace “ya jikinki Ina fatan kinji sauqi" murmushi tayi tace “naji sauqi wlh yanzu ma Shirin fita nakeyi yau Monday inda lecture 2:00pm" agogo ya duba yadan zaro ido yace  “kuma har 1:40 kina gda ai kin makara murmushi tayi tace “driver ne ya batamin lkc ya fita cefane bai dawoba dama ai ta wucceni shiga Bauchi a wannan lkcn kawai dai zan tafine na zauna a hostel bazanke dawowa ba sai weekend"

Agogo ya yaske dubawa yace “to ki fito muje na saukeki dama nima Bauchi zan shiga" kallonsa tayi taga ita yake kallo taso musawa ya daga Mata hannu yace “don Allah kada mu fara haka dake wlh banson musu kashemin gwiwa yakeyi" Shiru tayi tana jujjuya abin a ranta a ganinta dai sai take ganin kamar Bai daceba ta bisa su tafi, katse Mata tunani yayi da cewa “ki dauka Nima Bestie dinki ne mijin Bestie ai shima ai Bestie ne ke dagayau ma nima sunana Bestie"
Dariya tayi data bayyana kyawawan haqoranta yar kyakkyawar wushiryarta siririya sama da qasa ta dauki hankalinsa ya kwantar da kansa a saman mota ya zubanta ido  katse dariyar tayi yayi ajiyar zuciya yace “jeki fito Ina jiranki" juyawa tayi ya sake lefewa jikin motar yana me qare Mata kallo yana sauke numfashi sosai take daukar hankalinsa.

Bata jimaba ta fito dauke da Jakarta da dan qaramin trolley dinta ya karba yasa a but ya bude Mata ta shiga suka tafi, tafiya sukayi ta kurame babu me cewa da wani qala Saida suka biya wani guri yayi Mata siyayya sosai sannan suka qarasa tayi masa godiya ta shiga ciki  ya jima sannan yaja motar ya juya domin bashida wani uzuri a cikin Bauchin ya dauki hanyar komawa gida, cike yake da nishadi duk da bata wani basa fuska ba Amma yaji a jikinsa zai samu dama sosai ya shigeta zaiyi amfani da qawarta ya kafa kansa a zuciyarta.
Bai koma gidansa ba sai dare yana shiga ya tarar da ita a kwance a parlour ya qarasa ya zauna kusa da ita tace “ina ka shigane tun safe inata kiranka busy?" Shafa kansa yayi yace “wlh naje duba Bestie dinki na tarar tana Shirin komawa school Kuma driver ya tafi cefane bai dawoba so kawai saina dauketa nakaita shine sai yanzu na dawo" hawaye ta share tace “kuma shine baka kawota naganta ba ka wucce kakaita school?" Murmushi yayi yace “sorry naga bata buqaci zuwanba tukunna  kinsan yanzu ni takejin haushi har mukaje hararata takeyi ta gefen ido"
Dariya tayi tace “Allah Sarki tawan bari na kirata" daukar waya tayi ta kirata Saida tayi ring sau uku sannan ta daga tace “zuciyata ya kk" dariya tayi tace “lfy ya gwauranta?" Dariya tayi tace “alhmdllh masu miji kiyimin godiya yau na wahalar Miki da mijinki" haka sukayita Hira yana kallon Ni'imah daga qarshe ma ta tashi ta shige ciki tabarshi shanye da baki tunani ya addabi zuciyarsa ya miqe ya shige daki yayi wanka yayi Shirin kwanciya ya fito ya dan tsakuri abinci ya sake komawa ya kwanta saman kujera, fitowa tayi a shirye tsaf cikin Shirin baccinta itama zama tayiYa riqota jikinsa tace “wai ita Bestie yaushe zatayi aurene?" Murmushi tayi tace “ai batada niyya saurayinta ne Kuma dan uwanta Yassar ya rasu 2 years back so tun lkcn taqi bawa kowa dama wlh sweet munji mutuwar Yassar a lkcn bikinsu saura wata biyu"
Jinjina Kai yayi ya miqe ya shige daki ya kwanta tare da daukar wayarsa ya fara danne dannensa ya jima sannan ta shigo ta zauna a gefensa ya janyota jikinsa suka kwanta daqyar suka raya daren tanata kukanta da Safe ya sake ficewa a cikin kwanakin satin an barji amarci daidai gwargwado duk da amaryar raguwace bata iya dauke mijin yanda ya kamata hakadai aketa tafiya gefe kuma kullum wutar qaunar aminiyar matarsa qara ruruwa yakeyi a ransa duk wata hanya da zaibi yaga ya samu kusanci da ita Amma ya kasa samun dama dabara ce ta fado masa ya dauki lambarta a wayar Ni'imah sai yayi kamar zai kirata sai tsoro ya kamashi ya hqr ya qyaleta amma hqrnsa kullum qara qaruwa takeyi.

Yau tun dare yakejin qarshen qarewar hqrnsa daqyar a daddafe yakai safe tun safen ya tashi ya shirya tana kallonsa har ya gama ya dubeta yace “zan shiga cikin gari me zan taho Miki dashi ki gama hada kayanki jibi zamu tafi" bai jira amsarta ba ya fice da sauri ya fice daga gdan ya dauki hanya,
Kai tsaye ATBU ya nufa ransa fess ya lodar Mata uban kayan shop ya qarasa makaranta yayi parking ya dauki wayarsa ya kirata bugu daya ta daga suka gaisa taso gane murya tace “bangane me mgn ba" murmushi yayi yace “kizo  bakin get dinku rumfa ta biyu zakiga wayene" yana fadin haka ya kashe wayar ta zubawa wayar ido tana mamakin irin wannan Kira miqewa tayi ta dauke mayafin rigarta tayi rolling ta fito riqe da wayarta tana tunanin to wayene wannan?
Tsayawa tayi a harabar gurin tana kallon motocin can nesa taga an bude wata zazzafar mota ya zuro qafafunsa ya jima yana kallon yanda take waige waige ya fito ya jingina jikin motar ya harde hannunsa a qirjinsa tana juyowa suka hada ido yana sakar Mata wani ni'imtaccen murmushi gabanta ne ya fadi ta qaqaro murmushin qarfin hali ta tako ta tsaya a gabansa tace “yau a gari daga Ina haka hala dai daurin aure kazo?" Lumshe idonsa yayi ya bude gabansa shima na faduwa yace “wlh takanas dominki nazo"
Murmushin fuskarta ta dauke ta zuba masa ido tace “takanas domin ni kazo?" Jinjina Kai yayi da izzarsa ya bude Mata mota ta shiga ta zauna shima ya zauna yana kallonta da qananun lumsassun kyawawan idanunsa yace “takanas domin nazo na ganki naga lfyrki nazo Bestienmu ya karatu?" Numfashi ta sauke tace “babu sauqi wlh karatun medicine akwai wuya nadama nakeyi da na karbi ra'ayin Bestie na da bansha wahalar nan ba"
Hannunsa yakai ya kamo hannunta yace “meye wahalarsa" janye hannunta tayi tace “coursis din suna bani wahala" murmushi yayi yace “kinsan me?" Girgiza masa Kai tayi yaja numfashi ya kawar da kansa yace “akwai wani Abu da nakeji a Raina Amma ki jira lkc idan yazo zan fada Miki am bestie dinki tana gaisheki tace na tambayeki yaushe zakizo?" Kallon da yake Mata duk ya takurata ta kasa sakewa tace “zamuyi hutun brain zan dawo azare idan na dawo zanzo" dagowa yayi ya dubeta yace “gobe zamu tafi Abuja Amma zamuyi waya Koda yake ni zanke dawowa duk sati saboda Mai martaba" Jinjina Kai tayi tace “ok babu damuwa mun mayi waya dai da ita dazu Amma ka gaisheta" tana fadin haka ta bude motar zata fita ya riqo hannunta kawai ya janyota da gayya ta fado cinyarsa tayi saurin janyewa ya rintse idonsa yanajin wani sabon salon nau'in masifa yana shigarsa yace “ashhhh" kallonsa tayi da sauri yayi murmushi tare da sakin hannunta ya daga Mata gira yace “kije ki huta abinki"_Kullum saina fada wannan book din Free ne comment kawai nake buqata OUM HAIRAN PALACE 1 Bakwa comments wlh daga wannan page din idan baa gyaraba zan daina yimuku post kwake gani a moqota Ina gdy OUM HAIRAN PALACE 2 inayinku Allah yabar qauna kuci gaba da zuba comments nikuma zanci gaba dayi muku typing._Kallonsa takeyi cikin tsananin ta'ajibi tace "me hakan yake nufi?" Bude idanunsa yayi da suka kada sukayi red ya motsa dan qaramin bakinsa tare da qanqantar da qananun idanunsa yace "like feels...." Gabanta yabada wani ras ta cije lebe tare da bude motar ta fita shima ya fito yana gyara hularsa ya bude but din har tayi masa nisa ya Kira wasu samari da suke qoqarin giftashi ya nemi alfarmarsu suka daukar Masa kayan suka bita jin alamun ana bintane yasata tsayawa ta juyo kawai sai ta ganshi sauke da kaya niqi² ta dan bata fuska tace "meyesa kake haka bana buqatar qarin komai Mr Ja'afar Wakil Ina da komai enough...." Saukar hannunsa a bakinta ne yasata daga qwayar idonta ta zubashu cikin nasa shima nata idon yake kallo ya qara yalwata murmushinsa dimple dinsa ya lotsa farar fatarsa ta fulanin azare da ta hadu da hutu sai glowing takeyi yace "duk abinda nayi niyya baa dakatar dani Ja'afar Wakil baison sorry please baison...."

+

Shiru yayi yanaci gaba da kallon qwayar idonta ta sauke numfashi qamshin turaren hannunsa yana ratsa hancinta ta sanya hannunta ta dauke nashi inda matasan suka ajiye Mata kayan a daidai qafarta ya zaro kudi me auki ya Basu sukayi godiya suka tafi jan hannunta yayi yayi kissing nashi ya juya da sauri yabar gurin ya barta da sanyayyiyar gwiwa mamakin lamarin mijin aminiyar tata takeyi gabadayansa ta kasa gane inda ya dosa tun ranar dinner take tuhumar kanta me wasu abubuwan da ya rinqayi suke nufi amma ta kasa ganewa,

Tabe baki tayi ta debi kayan ta shiga ciki zama tayi a bakin gadonta ta fara bude kayan daidai lkcn da Nina wata abokiyar karatunta ta shigo ta zauna a kusa da ita tace "kay Hajiya ta kina wanke garori fah wannan hadadden guy din fah Ina kika samoshi?" Tsuke fuska tayi tace "ke banson iskancinki fah mijin Bestie nane wlh" zaro ido Nina tayi tace.

"What wanne irin mijin aminiyarki me ya kawoshi gurinki?" Yarfa hannu tayi tare da tabe baki tace "nims bansani ba wlh nayi tunanin daurin aure yazo ko wani Abu amma na tambayeshi yace takanas danni yazo"


Jinjina Kai Nina tayi tace "na dade Ina kallonku fah ni wlh na dauka saurayinki ne Amma gsky akwai alamun tambaya a cikin kallonsa gareki Kuma fah shi namiji bayada tunani wani lkcn lissafinsu na abinda yayi musune basa lissafin meye zaiyi daidai da tunanin dan' adam nifa na hango wani Abu a qwayar idonsa Pretty anya bazaki dakatar dashi ba"

Numfashi taja ta sauke tace "ni kaina yasani a compus inata tunanin abubuwa mabambamta Amma idan na tuna wayeshi kuma na tuna alaqar dake tsakanina da matarsa da irin soyayyar da sukayi ta one month before aurensu sai na qaryata zuciyata nakan dauki abubuwansa a matsayin son farantawa bestie na tunda yasan cewa bata da farin cikin da ya wucce taganni cikin farin ciki wannan dalilin yasa nake qaryata mind dina Nina Ja'afar Wakil bazai aikata abinda zuqatanmu suke fadi mana ba kawai dai shidin haka yake meson damuwa da damuwar wani" a kusan tare suka sauke numfashi Nina tace "Uhm to! Da wannan don wannan Amma dai gsky kiyi takatsantsan Rafi'ah ni na hango abinda ke baki hango ba" da wannan suka fara duba kayan tayi murmushi tace "gashi kuwa ya iya siyayyar Mata bari na Kira Bestie na nasata tayi masa gdy" saurin dakatar da ita Nina tayi tace "idan kikayi haka zaki iyafa sosa zuciyarta kinsan ita batada qashi" harara ta galla Mata tace "ashema ba Bestie din nawa bace ai bazataji ko ta kawo komai ba kuma bari kiji"


Wayarta ta fito da ita ta latsa number Ni'imah bugu biyu ta daga tace "My Bestie yanzu sweet yake cemin yazo ya kawo miki ziyarar bazata" ajiyar zuciya ta sauke tace "eh wlh yanzu bai dade da tafiya ba kawai sai naga Kira unexpected na daga yace nazo na sameshi a two park Ina zuwa naganshi naji dadi sosai sai naji kamar ke nagani"

Murmushi tayi tace "inanan inata fama da tunaninki sai yanzu na samu nutsuwa gashi zamu wucce Abuja baki dawo ba" jikinta ne yayi sanyi taja numfashi tace "kiyi hqr Bestie kina Raina banzaci zan dade hakaba a school so kinsan karatun namu sai a hankali Amma nayi Miki alqawarin indai na dawo hutun section zanzo har Abujan nayi Miki sati guda" wani ihu Ni'imah tayi tace "amma dakin burgeni kinsan me?" Girgiza Kai tayi tace "aa saikin fada" dariya tayi tace "sweet ya dameni da mgnrki kullum sai ya tambayeni wai bakida tsayayyen saurayine da bazakiyi aure ba idan nace masa bakya kula samarin ne sai yacemin Wai to ko bakida lfyne nace masa qalau kike ya Kuma cemin Kuma idan kika samu mijin zakiyi sure Niko nace masa to ko yana cikine wannan tambaya haka"STORY CONTINUES BELOW

Duk da gaban Rafi'ah Saida ya fadi Amma hakan be hanata qaqalo dariya ba tace kukam da abin dariya kuke kinsan kema bazai yuwu bane shiyasa kike fadar haka yanzu dai duk ba wannan ba yaushe zaki haifamin baby?" Dariya tambayar tabawa Ni'imah tace "wlh kinada abin dariya Bestie to ni yanzu yazaayi na sani abinda bani zanbawa kaina ba kuma ma yaushe akayi bikin har yanzu banyi cikakken 2 mouths ba har zaku dameni da maganar beby"

Hakadai sukayita wayarsu gwanin dadi a qarshe sukayi sallama kowacce ta ajiye Nina ta dubi Rafi'ah tace wato amintarku tana burgeni amma ga bisa dukkan alamu yanayin danagani yau da Kuma kalaman Bestie dinki yana nuna cewa lkcn katsewar wannan amintar yazo Rafi'ah mijin qawarki sonki yakeyi da gaske ko ki yarda ko karki yarda duk kalamansa na qaunane...."


Rafi'ah akwai zuciya batasan sanda ta Kai hanu ta bige bakin Nina ba tace "ke mahaukaciya ce bakida lissafi to ai abune da bazai taba yuwuwa ba kema kin sani kamar yanda Allah ya haramtamin auren mijin Raziqa yayata da muke uwa daya uba daya matuqar tana raye nikuma na haramtawa kaina Koda bata raye to haka mijin Bestie ya haramta gareni har gaban abada don Allah ki dainayi mana wannan mugun fatan mudai wannan qaddarar bazata ratso ksnmu ba"

Miqewa Nina tayi tace "karki yarda yanzu nsn gaba kadan Zaki gasqatani bana magana saina samu madafa" tsaki Rafi'ah taja dogo tace "bakinki ya sari sabon danyen kashi yar neman bala'i" tashi tayi ta fara shirya kayan daya kawo Mata a loccar ta bayan ta gama ta shiga wanka tana bathroom din taji wayarta na ring Saida ta fito ta dauka dake batayi saving number ba bata gane ba tayi sallama da sanyin muryarta


Amsawa yayi tare da cewa "Bestienmu na tafi da tunaninki kamar bakiji dadin zuwana ba ko?" Dariya tayi tace "kayy My Bestie's husband ya zaayi nace banji dadin ziyararka ba kawai dai naso ace da Bestie kukazo ne ins fatan kaje gida lfy" ajiyar zuciya yayi saukar muryarta na saukar masa da kasala yace "normal wlh wanka ma zanyi na kwanta kina bawa zuciyata aiki"

Shiru tayi tana tunanin kalmarsa kafin ta gama yace "don Allah tambayarki nakesonyi Rafi'ah please kada ki fadamin ba daidai ba shin meye yasa bakison kula samari?*

Dif tayi na tsayin lkc har saida ya maimata kalmarsa sannan ta sauke numfashi tace.


Bafa wani abu bane kawai har yanzu mutuwar yassar bata sakeni bane nakasa samun madadinsa a duniya" murmushi yayi me sauti yace "idan kika samu wanda yafishi zakiyi aure?" Tambayar tayi Mata bambarakwai tace "kamar yafa?" Fasali yaja yace "kinsan shi aure Allah ne yakeyinsa akwai wani abokina da ya ganki ya nunamin yanada interested akanki so shiyasa nakeson tabbatar da yardarki kafin na bashi number ki" daqyar ta bude baki tace "amma...." Katseta yayi da cewa "amma me baki shirya aure ba ko baki aminta da zan iyayi Miki zabin abinda yafi daidai daidai da rayuwarki ba? Rafi'ah kiyi Believe cewa komai yana faruwa ne bisa yarda da buwayar Ubangiji idan yaga damar yuwuwar Abu abune me sauqi kiga ya yuwu nidai roqona ki kwantar da hankalinki ki toshe kunnenki ki tsayar da ra'ayinki kinji?"Yanda ya qarashe mgnr da sigar rarrashi yasata jan zuciya tace "ok na gde Mr Ja'afar Allah ya qara girma yaja kwanan me martaba" murmushi yayi ganin ya sameta da sauqi yace "yawwa koke fah kadafa ki dauki kalamai na na dazu kisasu a ranki tsokanace kawai Bestienmu ki huta sai anjima"

Dariya abin yabata a ranta tace "haba kokai fah Amma da ka fara fadarmin da gaba" sallar La'asar tayi ta fita zasuyi group discussion ita da abokan karatunta suka zauna sunata fama hankalinsu gabadaya ya tattara a discussion din saboda wani practical zasuyi me wahalar gaske sai shidda suka tashi mazan suka nufi nasu hostel din matan su uku Suma suka rankaya nasu suna tafe suna hirarsu yunwa takeji shiyasa tana zuwa ko wayarta data sanya a charger bata waiwaya ba ta nufi inda take girki ta kunna gass ta dafa indomie da taji ganyen alayyahu da albasa da kifin gongoni ta juye a flat ta dauko lemo cikin kayan daya kawo Mata ta zauna bayan ta dauko wayarta tanaci tana duba wayar saqonni ne guda uku.

Budewa ta farayi tana dubawa na farko sallama ce kawai na biyu ne akace "ina fatan kadaitacciyar halittar da Ubangiji ya samar da ita domin ni kadai tana cikin amincin buwayi gagara misali" na ukun Kuma wasu zafafan word ne da suke nuna irin halin da zuciya take ciki a halin da taga abin buqatarta amma ta rasa yanda zatayi ta furta masa, girgiza Kai tayi tanabin number da kallo baquwa ce a gurinta batada ita a contact dinta hakan yasa ta miqe kawai taje tayi alwala ta dawo tayi magrib bayan ta idar ta sake zaman azkar tananan zaune har isha tayi tayi addu'o'inta ta dauki wani littafi tana nazarinsa ba ita ta kwanta ba sai kusan biyu da rabi na dare kasancewar ta saba idan ta gama karatu takanyi nafila da karatun qur'ani tare da addu'o'i yawa yawan addu'arta tanayinta ne akan Allah ya tsareta daga rudin zamani da mutanen zamani Allah ya jarabceta da qaddarar da zata iya takance Allan daya dauki rayuwar abin qaunarta daidai lkcn da tafi buqatarshi ya musanya Mata da wanda yafishi alkhairi.STORY CONTINUES BELOW

Wadannan sune manyan addu'o'inta saboda ita abinda ta sani Kuma ta dauka a ranta qarshen rayuwar jin dadin mace shine samun masoyi na gaske wanda tsanani da qunci ruwa da iska bashi sanyashi juya Mata baya, yana daya daga cikin dalilanta naqin kula samari saboda har yanzu tun bayan mutuwar Yassar bataga Wanda zai iyayi Mata sallamawar da Yassar yayi mataba bataga Wanda zai qaunaceta kamar yanda Yassar ya qaunaceta ba.

Lkcn da ta kwanta kamar koyaushe mafarkinta dai shine gatanan zaune tare da wani mutum jikinsa ke bayyana kyawunsa Amma fuskarsa ta kasa ganuwa a idanunta a gefe Kuma ga aminiyarta nan ta shigo da gudu da wuqa a hannunta tayo kanta wannan mutumin da bata ganin fuskarsa ya tashi ya dauketa da mari tare da janyeta daga inda take zaune inda ita Kuma Ni'imah ta daga wuqar ta sauketa a gefen cikin mutumin ya saki qara tare da sulalewa taga taga ya fadi tayi kansa da sauri tans kiransa fadi take "Beby ka tashi tashi Baby don Allah ka tashi...." Dakatawa tayi da mgnr jin saukar tsinin wuqar a nata cikin turtsetse da yake Shirin fitowa duniya kafin ta gama sulalewa taga itama Ni'imah ta daga wuqar ta cakawa cikintaDaidai lkcn ta farka a firgice tare da dafe qirjinta da yake bugawa da qarfi tana addu'o'in neman tsari saboda wannan mafarkin kusan kullum sai tayishi "to Wai me wannan mummunan mafarkin yake nufi ne?" Ta tambayi kanta tare da fara kallon dakin daga ita sai Nina taja fasali ta koma ta juya wani bangaren ta kwanta tun daga wannan lkcn baccin ya qauracewa idonta ganin bazata samu damar komawa ba ta tashi ta sake dauro alwala dake ta kasance me yawan tsaiwar dare batajin gajiya wajen neman kusanci da ubangiji Rafi'ah tana cikin mutane masu neman kusanci da ubangiji ta duk wata hanya da tasan zats kusantasu.

Ta Jima tana nafila takin tayi sujjada tana addu'a cikin larabcinta me dadi take roqon Allah ya juya wannan mafarki nata Wanda ya zame Mata na wajibi ya zama alkhairi ga rayuwarsu ita da bestie dinta ya bayyana Mata gaskiyar abinda ya dade yana nuna Mata a cikin baccinta samada shekara uku tun mutuwar Yassar ta fara wannan mummunan mafarkin da takasa dainawa har yanzu Kuma baya canzawa kullum iri daya takeyinsa gashi ta kasa fadawa kowa, abinda ta riqe a ranta kawai shine akwai wani Abu da zai faru a nan gaba Wanda ubangiji yake haskamata ta shiryawa zuwansa abbanta yasha fada Mata cewa mafarkin shirme baa riqeshi gabadaya dole sai an manta ko farkonsa ko qarshensa ko tsakiyarsa Kuma baa maimatashi in yatafi ya tafi kenan.
Kiran sallar asuba ne yasata ta qarayin kasaqe tana Kai kukanta gurin ubangiji yau zuciyarta ta gama karyewa da wannan mafarkin nata har kuka tayiwa ilahi tans roqonsa ya bayyana Mata koma menene tasanshi ko zuciyarta ta huta da tunanin menene, bayan tayi sallar asubarne ta koma ta kwanta tare da dauka wayarta abin mamaki dake a silent take sanyata idan zatayi karatu Kira 10 text 5 tagani duk da number daya guda biyu ne kawai bada itaba daya number Bestie dinta daya Kuma na Ja'afar ne tana tunanin wanne zatabi taji wani saqon ya shigo ta budeshi da sauri.

_"duk da nasamu lbrn cewa ke ma'abociyar tsaiwar darece Amma inayi Miki tuni da ki qara qaimi wajen kusanta kanki da ubangiji nima zanyi hakan duk da kasancewar inada iyali Amma bazanyi qasa a gwiwa ba zan raba lkc na uku kamar yanda ma'aiki ya kwadaitar damu zan bata daya zanyi bacci na huta a cikin lkcnta biyu zanyi amfani dasu wajen neman sahalewar ubangiji wajen mallakarki cikin sauqi"_Murmushi tayi ta duba lkc 1:24:am yayi Mata wannan saqon ta sauke ajiyar zuciya tace "na gde" ta sake bude wani ya rubuta _"ina addu'a Ina qara samun qwarin gwiwar fitowa takarar neman wannan babbar kujera da zata zamomin fahari a duniya tabbas idan na samu Rafi'ah matsayin Mata nasan Allah ya gama yimin arziqin duniya ko iya hakama yabarni na gode masa"_

Dariya tayi tana toshe baki tace "au haba da gaske?" Sake bude wani tayi _"Iya wuya zan jure kowacce kalma daga bakin duniya domin cikar burina kedin ke nakeso Kuma ke na faraso Rafi'ah meyesa bakizomin a farkoba kikazo a qarshe?"_ murmushi tayi ta bude wani Wanda dagashi sai na qarshen ya rubuta _"indai na kasance ni dake bana iya yaqar zuciya My Raf inada naci akan duk abinda zuciyata ta aminta tanaso Ina fatan bazan dameki ba kuma bazaki qosa dani ba ni namiji ne na gaske inada naci My Wife....."_


Murmushi tayi ta bude na qarshen _"Hi Assalamu alaiki Qurrah ki shirya tarata yau zan kawo miki ziyara yau bazan iya barin Bauchi banganki ba"_ zaro ido tayi tare da miqewa zaune tace "nashiga uku aa wlh yau inada lecture tun safe har magrib banida Interval" miqewa tayi ta fada wanka ta shirya cikin doguwar riga me masifar kyau dayi rolling kusan shigarta kenan ta dan gyara fuskarta tasa lipstick ta dauki littafanta ta fice ta nufi hall din da zasuyi lecture din mamakine ya kusa sata faduwa batayi nisa da tafiyar ba ta fara hango Ja'afar Wakil tsaye jikin mota shida wata budurwa ta duba agogo 8:30am taka zuciya yanda ya kafeta da ido bata Isa ta wucce ba dole jikinta a sanyaye zuciyarta a jagule ta matsa gabansu tace "Mr Wakil lfy da sassafe haka azare da Bauchi da nisa Ina Bestie na?" Kallonta yake yakasa qiftawa ganin yanda yake kallonta yasata duba jikinta tace "lfy Mr Wakil?" Murmushin gefen baki yayi ya kalli yarinyar ta matso gabanta ta Kama hannunta tace "morning princess Aunty Rafi'ah gsky Masha Allah sunana Fiddausi Muhammad Wakil ni qanwace a gurin Yaya Ja'afar Kuma autarsu....."

Katse Fiddausi yayi da cewa "ki manta kawai Little zata sanku a hankali ai tunda suka shigo fam dinmu wato admission nake nema Mata a makarantarnan shine mukayo sammako akwai wani abokina da mukayi zamu hadu yau bayan tafiyata jiya yacemin Nazo yau yanzu dai ya kk ya bacci?"


Wani mahaukacin numfashi tayi tace "fine Allah ya gida?" Lumshe idonsa yayi ya kada Mata Kai suka kalli juna da Fiddausi sukayi murmushi tace "yanzu yana Ina Mr Ja'afar Wanda zaka gani din muje na rakaku kasan makarantar tamu saimu" kallonta yake yanajin dadin yanda ta nuna kulawarta gareshi budar bakinsa yace "kinci abinci?" Dagowa tayi da sauri ta zuba idonta a nasa tare da basarwa tace "ah haba likita ai baya karyawa da wuri saboda tsaro"

Ga mamakinta sai taga ya daure fuska yace "for wht?" Shiga tayi taitayinta abinka da saraki badai kwarjini ba qasa tayi da kanta yayi murmushi yace "da wasa nake Miki muje Nima yunwa nakeji sosai" dagowa tayi arhar hawaye a gurin Rafi'ah kamar baure har idanunta sun kawo ruwa ta duba agogon hannunta Tara saura Kuma Tara zasu shiga lecture, zatayi mgn ya sake daga Mata zara zaran yatsunsa yace "muje banason musu.Turo baki tayi gaba taja da baya tana harararsa tace "to waikai Ina ruwanka da cikina ne nagadai banice Bestie ba da zaka ce sainabar lecture na nabika yawo nikam aa gask....." Numfashintane ya dauke jin qamshin jikinsa ya kusanceta sosai kafin ta gama bude idonta kawai saijin wani dumi tayi akan bakinta ji tayi wani Abu na yawo cikin bakinta daya sanya numfashinta daukewa cak na tsayin lkc daqyar ta tattaro qarfinta domin tureshi ta kasa kawai sai hawaye sharr jikinta ya dauki wata muguwar rawa.

Sai lkcn ya saki bakinta yana sauke wani nishi ya tura hancinsa kan wuyanta yace "zakije ko bazakiba..." Yayi maganar muryarsa na shaqewa kawai saita saki kuka me sauti tana tureshi shikuma yaqi sakinta tace "ka taimakeni ka sakeni don Allah ana ganin mutuncina a makarantarnan Meye hakanne Ja'afar meye hakanne banason haka don Allah wannan ai iskanci..." Saurin sake hada bakinsu yayi ya dagata cak yasata a mota ya kulle ya janye bakinsa daga nata ya juya ya dubi Fiddausi da itama jikinta yake rawa bata taba ganin wannan tantiranci ido da ido ba sai yau ita gabadaya yayan nata ya firgitata musamman yanda taga jikinsa yana rawa,


Tsawa ya daka Mata yace kin wani kafeni da ido kizo ki shiga muje mu dawo lkc yana tafiya" shiga tayi yaja motar da gudu ya fita daga makarantar itadai Rafi'ah tsoro da fargaba sun hanata Motsin kirki sai hawaye da takeyi tace "mijin aminiyata..." Batasan maganar ta kufce Mata ba yaci gaba da tuqinsa ya bude baki yace "kinsan cewa daga kallon farko a gurin dinner kika hadani da aiki kika jefani a komarki Rafi'ah kinsan cewa "kallon dana dameki dashi a ranar ba kallon rashin sani bane kallone na karbar saqo daga zuciya zuwa zuciya, kinsan cewa tun a ranar kika hadani da aiki bana cikakken bacci bana iya komai Saida tunaninki hatta qawarki idan ba hirarki takeyimin ba bana iya doguwar Hira da ita rafi'ah Hira idan har bataki bace gara abarni na zama kurma, shin ya kike tunanin zan kasance idan nace zanyiwa aminta biyayya na bijirar da abinda ya shiga zuciyata a karon farko?"

Tunda ya fara mgnr ta kafesa da ido hawayen ma da take fitarwa ya tsaya cak sai rawar jiki da bugawar zuciya da kawai takeyi, dauke idonsa yayi daga kanta yace "bandamu da mgnrki ba Rafi'ah buqatata itace ki yarda Kuma kiji cewa Ja'afar Wakil yanasonki so bana abota ba na aure aurenki zanyi Rafi'ah"........_Masu Bina suna cewa na turo musu daga farko kuyi hqr bazan iya bane duk groups din da kukaganshi to ku tambaya zaku samu abun zaimin yawa nayi typing nayi Post sannan nazo na rinqa binku one by one Ina tura muku please kada wata tace banida da mutunci wlh ko kin bini bazan turaba Amma fah kuyimin uzuri nima inada uzurirrika na na qashin kaina sannan wannan book din kyautane sadaukawa ga duk wani masoyina dake fadin duniya nasan addu'ar ku ke samamin kariya gurin Ubangiji Kuma Allah ya kareku daga bakin duniya😘_

____________________________

____________________________

Batare da yayi aune ba ko ya zata yaji saukar yatsun hannunta akan kyakkyawar fuskarsa me cike da saje abinda ya haddasa masa cin wani uban birki ji kaki qiiiiiiy! Abinda yasasu wata girgiza hakan baisa Rafi'ah ta daina tsumar da takeyi ba idanunta har yanzu na kansa ya saki baki yana kallonta rabon da asa hannu a mareshi har ya manta.

Bude qofar takai hannu zatayi yayi saurin danna pin din ta juyo cikin bala'i tace "zanci kutumar ubanka Ja'afar zan yaga alfarmarka da mutuncinka matuqar baka budemin motarnan ba...." hannu ya sa ya toshe kunnensa ta sake daga murya cikin qaraji tace "ka budemin mota nace stupid man kawa...." Bata rufe bakinta ba ya cafki bakinta da nasa ai baigama Kama harshenta ba ta gasa masa cizo a harshe dake cikkaken dan air ne ido kawai ya rintse ya sake tura harshen nasa cikin bakinta yana qoqarin sanya qarfi ya janyota jikinsa ta cure jikinta ta banqara ta kwace ta zame daga kujerar ta rushe da kuka tace "nashiga uku ni Rafi'ah wannan wacce irin baqar ranace Jama'a meye yake faruwa danine...." Bude motar yayi ya dube fiddausi yace "jeki little jirani...." Kafin ya ankara Rafi'ah ta bude qofar ta dire waje kamar wata mahaukaciya ta kwasa da gudun bala'i ta runtuma cikin daji.

+

Cikin tashin hankali ya fito yabi bayanta a guje dake dogone ita Kuma tsayin ba sosai ba sai gashi yacin Mata da taimakon bishiyar da tayi karo da ita ta caki goshinta tayi baya taga taga zata fadi ya tareta ta fada hannunsa ga matsanancin mamakinsa sai yaga ta fado hannunsa sumammiya abinda ya qara fitar dashi a hayyacinsa ya dagakai ya kalli Fiddausi data dafe qirji tanason mgn Amma tsoron jizginsa ya hanata yace "meye hakan Fiddausi saboda nace inasonta shine harta suma"

Cije lebe tayi tace "yaya abinda girma ka taimaketa ka kaiyi Mata urgent treatment" sabarta yayi a kafadarsa ya sata a mota ya shiga cikin garin Kai tsaye wani asibintinsa ya nufa sabone bai dade da budeshi ba ya dauketa kamar beby ya shiga da ita har dakin da zai dubata ya cire babbar rigarsa duk likitocin dake asibitin ya hanasu tabata dakansa yayi treet nata ya cire Mata iccen daya shiga goshinta ya wanke gurin da magani, yana tsaka da dressing din gurin wayarsa ta fara ring ya daga ganin number Ni'imah ya danna ok Bai bata damar mgn ba yace "naje cikin Bauchi ne inada wani petiant bama lallai tafiyar nan yau ba saboda yanada muhimmanci a gurina" yana Shirin kashe wayar yaji tace "sweet kaje gurin Bestie kace nace tabani abin dadi" duk da damuwar dake cinsa Saida yayi murmushi yace "insha Allah zanyi qoqari" yana fadin haka ya kashe wayarsa yaci gaba da abinda yakeyi.


Yana gama dressing din ta farka ganinta daure da drip yasata miqewa ta fincike allurar ta watsar juyowar da zaiyi yaganta tana daye dressing din da yayi mata ya nufota a guje yana cewa "kewai meye hakanne baki da hankali ne jibi yanda kika jiwa kanki ciwo kina tunanin hakanne zaisa na janye qudurina" wani matsiyacin kallo tayi masa ta nufi qofa ya nufota da niyyar hanata fita ta juyo tace "wlh tallahi ka qara matsata sai nayimaka ihu na tona maka asiri fajiri maci amanar qauna ka dauka ni yar iskace da zakazomin da wannan games din to kayi gaggawar lashe amanka kafin ka fuskanci qasqanci a gurina Ja'afar bana zama inuwa daya da maci amana maha'inci dan uwan shaidan me burin shiga tsakanin qauna,

Sakin baki yayi tare da rungume hannunsa a qirjinsa shi masifar tata ma burgeshi takeyi baitaba ganin mutumin da yake fada yana kyau ba sai ita yana wannan tunanin ta fice da sauri cikin saa tana fita ta fada napep ta fada masa inda zai kaita Koda ya fito baiga alamarta ba ya tambaya akace tahau napep kafin yaje ya dauko rigarsa ya nemo Fiddausi har takai school tana zuwa ta nufi hostel tanata wucce mutane bata gane su waye har ta Isa dakin ta fada gado ta rushe da kuka tana furta " Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirni fih musibati wa'akalifni khairin minha" ta jima tana kuka me dafa zuciya bata taba shiga tashin hankali irin na yauba ji tayi anzauna a gefenta ta tashi firgigit.

Ajiyar zuciya tayi ganin Nina ce tace "meye Kuma pretty?" Kukanta ta qarawa qarfi tanasa tisue tana tsane jinin da Bai daina zuba a ciwon ba Nina ce ta dauko wani dan qaramin akwati ta bude ta dauko auduga da magani tayi Mata dress na gurin tace "yanzu Mutuminnan na jiya yazo yabani magunguna yace na kawo miki garinyaya kikaji ciwo?" Dora Mata magungunan tayi a cinyarta tayi watsi dasu tace "kije kice masa banaso bana buqata ki hada masa da kayansa na jiya duka banaso ya fadi meye yakeso bayan wannan na fadawa abbana ya biyashi nidai roqona ya janye furucinsa, kwanciya tayi tace "Nina meye yasa mutane basusan girman aminta ba meyesa basusan darajar alaqa ba ? Meyesa Ja'afar zaiyimana haka wlh bantaba zatoba Koda wasa nayi tunanin duk abinda yakeyimin saboda Bestie na yakeyi min meyesa zaiyimin haka me yake nufi dani Nina ya cutar dani ko iya haka kalamansa suka tsaya na rantse da Ubangijin da yake rayani bayan ya kasheni a kowanne lkc nayi bacci bantaba jin tsanar wani mutum araina ba sai yau naji tsanar Ja'afar Wakil ta darsu a qoqon zuciyata natsani mutum maci amana"

STORY CONTINUES BELOW

Ta qarashe maganar tana shigewa jikin Nina tace "ko iya haka da wanne ido zan kalli Bestie mijinta yace yana Sona har ya hada bakinsa da nawa innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Hasbunallahu wani'imal wakil wannan masifa dame tayi Kama nikam na shiga ukuna Nina qaddarorina sunada wahala"

Miqewa tayi kamar zararriya ta kalli gabas tama manta da ciwon dake goshinta tayi sujjada tace "Allah inhar ka qaddara yankewar alaqata da Ni'imah alaqar daka sardata tun bamusan kanmu ba Allah kada ka yanketa ta wannan hanyar ka karbi rayuwata na tafi na barta da mijinta abin qaunarta farin cikinta Allah nafi kowa sanin cewa Bestie na tanason mijinta Allah kada kabashi ikon cutar da ita Allah ka cire masa so da sha'awar duk wata ya mace a ransa bama niba ya Allah idan kayimin haka ka gamamin koma...."


Ji tayi an rufe Mata baki ta dago Nina tace "meyesa kike roqon farin cikin wata har kike roqon Allah ya kasheki akan farin cikinta?" Share hawayenta tayi tace "ba wata bace Bestie nace wlh tafi gaban haka a gurina zan iya bata rayuwata matuqar zata rayu cikin farin ciki meyesa mijinta zaice yanasona Nina meye bambamcina da Ni'imah mutane suna cewa saboda aminta Kama mukeyi toshi meye yasa yakeson raba amintarmu?"

Murmushi Nina tayi tace "ai jiya dana fada Miki baki yarda ba Rafi'ah tun ranar bikin da kika gayyacemu na fahimci sinadarin dake fita a idonsa sone da zallar qauna Amma wanne mataki kika dauka?" Shiru tayi nadan lkc kafin ta dago tace "zan yanke mu'amala da matarsa na dan lkc idan burinsa kenan" girgiza Mata Kai tayi tace "kada ki fara hakan zaisa ta zargeki kici gaba da mu'amala da ita shikuma ki take Masa dogon burki kiyi duk meyuwuwa kiga kinsa masa tsanarki ta yanda dakansa zai janye Rafi'ah jiya dana fada Miki haushina kikaji har kina cewa bazai yuwuba to gashi dai kin gasqatani" Jinjina Kai tayi ta miqe ta fada bathroom tayi wanka ta dawo ta kwanta ranar duk wata lecture batayi ba tanajin wayarta tana ring taqi ko dubawa balle ta daga Nina ce ta zauna tanata rarrashinta tare da nuna màta bafa wani Abu bane latsine irin na mazan zamani yanzu haka ma bazai qara mgn ba tunda ta nuna masa batada mutunci,

Da wannan ta dan samu kanta harta dauki wayarta ta fara duba kiraye kirayen kiransa yafi hamsin da layin data sani saina dayan daya rinqa turo Mata saqo jiya Wanda shima yakai talatin saqonni kuwa sunyi ashirin batako dubaba tayi delete all ta watsa layukan a black list kiran Ni'imah ta gani har hudu tayi kamar ta share sai Kuma taga rashin dacewar hakan yau gabadaya basuji junaba zatayi tunanin ko ba Lau ba hakance tasata kiranta dagawa tayi cikin muryar kuka tace "inata Kiran wayarki kinqi dagawa Bestie kinsan Kuma bana samun nutsuwa idan banjiki ba har na fara tunanin ko wani abune ya sameki na kiraki sosai da wayar Sweet ma baki dagawa I hope fine dai?"

Ajiyar zuciya tayi tace "banji dadi bane Bestie kaina na ciwo sosai Amma nasha magani na samu relief Ina fatan kina lfy Ina unborn dina?" Dariya tayi tace "waye yace Miki inada ciki wlh banida komai yanzuma period nakeyi in fada Miki jiyama Saida mukayi fada da sweet wai saina bashi nutsuwa Wai Ashe akwai yanda akewa namiji ya samu nutsuwa ko ana halin haila?" Dariya Rafi'ah tayi tace "matsalace dake babba Bestie Ina littafin dana zauna na rubuta na baki harfa buga mikishi nayi saboda kinsan rubutunmu na likitoci ba kowa ke ganewa ba, idan kika duba book din Zaki samu komai har addu'o'in da zaki samu daukaka da soyayyar mijinki nabaki sannan ki cire ganda Bestie ki tallafi mijinki namiji da kike ganinsa bashida tabbas don Allah kada kibani kunya wlh a shirye nake na baki taimako ta kowanne bangare indai akan mijinki ne inason Kuma Ina burin ki zama tauraruwa a gurin mijinta"

Tabe baki Ni'imah tayi tace "ke nifa duk dare fada mukeyi dashi banason nacinsa shiyasa naso kizo kinqi zuwa wlh idan ya fara baya gajiya a dare sai yayi sau biy....." Katseta tayi da cewa "sheeet! Bestie banson ji don Allah haramun ne sirrinki ne ke dashi ki daina fada mijinki nakine ke kadai kiyi Masa komai babu komai Bestie your are educated meyesa kike Abu kamar tashin qauye duk wani farin ciki fa yana tare da aure duk da cewa aure ba dadi gareshi ba tsanani ne Kuma kinsa dama ita aljanna samunta ba abune me sauqi ba Ashe kuwa hanyar samunta bazata zama me dadi da sauqin biba please ki cire ganda Bestie don Allah ki tarairayi mijinki kinji?"

Numfashi Ni'imah ta sauke tace "nifa na rasa meye yasa wlh banason wahala kinsan ban sababa shi ya cika tsurfa wai bazaici abincin kuku ba saidai nayi masa Kuma idan nayi sai yace yaji ko yace magi yayi yawa shi komai baayi masa gwaninta ga izza da Isa kamar wani sarki Bestie Ja'afar fah inaga kamar ma yafi Muhammad Wakil Izza" murmushi tayi tace "haka zakiyi hqr baki bishi inda zaku daidaita bane komai yakeso bakiyi bakya dauke buqatarsa a bed baki kashe masa yunwar cikinsa baki zama kuyi Hira dasshi kina fama da waya Ina gani fah 24 hours datarki a bude kina online da anyi Miki mgn ki amsa why Ni'imah why da bazaki raba lkcnki ba kibawa mijinki kaso mafi rinjaye Ni'imah namiji zuciyar jariri gareshi Wanda yaje tattalinsa yake kula dashi dashi yake sabawa dashi yake tashi kibi a sannu ki fahimci mijinki ki haqura da chat matuqar kina tare dashi sannan ki fahimci dandanon mijinki ki daina cika masa magi da yaji a abinci kinji tawan?"


STORY CONTINUES BELOW

Jinjina Kai Ni'imah tayi tace "na gde Bestie ba komai zan iyaba Amma zanyi qoqari kinsan mazan ne sai a hankali Ja'afar ko kallo idan baqatarsa ce ta tashi ba ban isheshi ba yanzu ma yake tambayata wai dama kin iya ashar shine nace masa nidai bantabaji ba don ko wani yayi nasiha kikeyi masa ya Kuma cemin Amma ke masifaffiyace nace sanyinki yafi na ruwan freezer ko lkcn yarinta ni nake tare Miki fada ke mgn ma bata dameki ba don wani lkcn idan na dameki da surutu har kuka kikeyi hawayenki yafi komai arha shine yace yanason mace me saurin kuka nace to aikuwa ke sannu ma kuka sakesaki"

Haushine ya cika Rafi'ah tace "kewai bakida hankali ne kike yabon mace a gaban mijinki?" Dariya Ni'imah tayi tace "haba ai mace kikace ke kuwa jini daya nakejinmu nasanma bazaiji komai ba yasan ni dake Abu dayane balle wannan dan girman kan idanfa ya tambayeni na bashi amsa sai ya tabe baki yace meyesa ban zama kamr ke ba sai nace bansani ba kawai sai yace Allah ya kyauta yaci gaba da danna system dinsa" murmushin takaici tayi tace "ok ki daina ko Yusrah ki daina yabo a gaban mijinki ki rinqa yabon kanki kinsan zuciya tsokace batada qashi kinji Bestie na ki kiyaye harshenki don Allah ni zan kwanta kije ki shirya ki dauki littafin nan Zaki samu yanda zakiyi dashi a daren nan"

Ajiye wayarta tayi tana mamakin hali irinna aminiyar tata dole aiki ya sameta zatayi qoqari Koda bataje inda takeba take bata gudummawa domin da alamun da gaske tana buqatar kulawa so takeyi dole ta qarfi kamar yanda Ummanta take juya gidansu itama saita juya gidanta Wanda samun hakan da alamun zaiyi wahala.

Wata baquwar number taga an kirata da ita ko kusa ko alama batayi tunanin komai ba ta daga jin ajiyar zuciyar yasata kasa kunne domin sauraron jin dawa take mgn, a sanyaye cikin muryarsa me cike da kwarjini da qasaita yace "bestie meye ribarki don kinyi block mijinki kinajin na dameki ne? Ashe dai duk halinku daya da qawarki?"

Wani dogon tsaki taja ta kashe wayarta yakira yafi so goma taqi dagawa qarshe ma ta kasheta don da gaske ta fahimci akwai alamun tabuwar qwaqwalwa ga mijin aminiyar tata, washegari ta fice da wuri daga Hostel din ta nufi Venue dinsu ta zauna tana nazarin wani littafin biology taji an tsaya akanta bata dago ba da farko saboda tunaninta Nina ce dan dago idonta tayi ta cikin farin glass din dake sanye a idon nata ganin takalmi sawu ciki yasata dagowa tunaninta Taheer ne abokin karatunta da yake nacin sonta.Annurin fuskarta ne ya dauke ganin JM ne tsaye sanye yake da alqabba irin tasu ta sarakai hannunsa zure cikin aljihun alqabbar sai baza qanshin wani tsadaddan turare yakeyi me kwantar da hankali fuskarsa dauke da murmushin daya fito da siririyar wushiryarsa, sake tsuke fuska tayi ta fara tattare kayan karatunta zata fice ya ya dora qafarsa ya tare hanyar tare da cewa.

"Bestie kin tashi lfy?" Rafi'ah akwai Dara daran idanu hakan yasa harara bata Mata wuya aikuwa ta jefeshi da wata zazzafa da tasa zuciyarsa harbawa yayi qasa da idonsa tare da zama, zare glass din idonsa yayi yace "zauna muyi mgn don Allah meye kikejin tsoro ne nidai nasan babu macen data Isa tace batasona saboda duk inda namiji yake nakai please ki tsaya mu fahimci juna Rafi'ah muyi auren qauna kada wani qaramin dalili yasa ki bijirewa hukuncin Ubangiji to waima ni meye laifina ne da har kika daga hannu kika mareni kinsan jiya Marin nan ya hanani bacc...." Dafe kuncinsa yayi a karo na biyu data daukeshi da mari ya dade dafe da kuncinsa yanabin Hall din da kallo ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya ganin dagashi sai ita a hall din ta sake maida hankalinta a tattare kayanta kawai taji an ruqo weast dinta ta baya.


Ya dora hannunsa a saitin ask dinta duka biyun ya miqe lkcn da tayi mutuwar tsaye ya hada gabansa da bayanta qirjinsa yana gugar bayanta ya matseta tare da Dora kansa saman nata yaja fasali tare da sakin wata qaqqarfar ajiyar zuciya, sai lkcn ta samu damar dawowa nutsuwarta ta sanya hannunta domin bambare nasa Amma saima ya qara matseta ya janyo hannunsa sama daidai tushen qirjinta ya Kama sosai ya riqe yanda yasan duk qarfinta bazata iya motsi ba saboda wata matsiyaciyar kasala daya saka Mata ta bazata ya bude bakinsa muryarsa na shaking yace "ko kasheni zakiyi bazan fasa cewa inasonki ba Rafi'ah I really love you wlh tallahi ko zan mutu saina aureki"


Yanayin da takeji tasa ta kasa ko daga hannunta sai tafasa da zuciyarta takeyi dumin hawayenta da yaji a hannunsa yasashi juyota ganin yanda ta rintse idonta Zara zaran eyes lasher's dinta suka sauka kan beauty face dinta da hawaye yake wankewa yasashi cika da sauqi baisan sanda yakai bakinsa ya fara tande hawayen ba kawai sai shima yaji zuciyarsa ta karye daqyar ya daure ya hadiye nasa hawayen yanajin bugun zuciyarsa na qaruwa tunda yake baitaba ganin masifa irin wannan ba shekara da shekaru anaso ya nuna waccce yakeso ya kasa lkcn da Allah ya nuna masa abinda ya dade yana nema Kuma sai abin yazo musu a baibai tabbas akwai sarqaqiya cikin lamarin shidai duk juyin da duniya zatayi bazai janye qudurinsa ba saboda yasan hakan shine kawai zai dawwamar da zuciyarsa cikin fayyataccen farin ciki,

Janyewa tayi daqyar daga jikinsa ta durqusa a qasa ta kama qafarsa cikin kuka tace "don Allahu huwar Rahamanu Ja'afar Wakil ka daina bibiyata ka janye wannan mugun nufin naka akaina wlh ka dauko hanyar ruguzamin rayuwata ne please Ja'afar nayi maka alqawarin ko wani lapse kega Bestie na wlh da qarfin buwayar Ubangiji zata gyara nidai ka rabu dani Allah matuqar ace babu wani namiji bayankai daya saura a duniya to zan aminta na gama rayuwata babu aure...." Murmushi yayi ya durqusa ya sanya hannu ya Kama hancinta yana murmushi yace "nikuma ko duk duniya matane yanzu ke kadai nake muradi matsayin Mata wlh tallahi matuqar baki amsamin buqatata ba to kuwa zakiyiwa Bestienki asarar igiyar aurenta......."Da wani irin sauri ta dago ta kalleshi ya miqe tare da daganta gira yace “wannan shine matakin qarshe da zan dauka indai burina ya kasa cika to zan rusa farin cikin kowa Rafi'ah kinsani kinsan nasani aurena dake ba haramun bane shin bayan Allah da manzonsa wa kikeso ki birge, wa kikeson farantawa da zakiyiwa kanki asarar masoyi?"

Kallonta yayi na dan lkc kafin ya hadiye wani yawu me zafi yace “dole cikin sharrudana idan na kiraki ki daga indan kikaqi na rantse da kadaitar zati saina dawo Miki da qawarki gda domin batada wani amfani a gurina ba ita nake buqataba ke nake buqata haba haba Rafi'ah shin waima kintabajin inda akayiwa namiji dole ne nifa a duniya ke na faraso tayaya zanyi sake damata ta kufcemin?"


+

Baijira cewarta ba ya juya Saida yaje qofar hall din ya juyo yace “zan kiraki anjima ki kula da kanki" yana ficewa ta zube a gurin cikin toshewar qwaqwalwa da rashin madafa tabbas tana cikin ha'ula'i tama kasa tuna abinyi sai jujjuya biro da takeyi idonta hawaye nata sitirya tanajin yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi kwantar da kanta tayi saman kujerar tanajin wani zazzabi yana sauko mata ita dama bata iya sanya damuwa aranta ba yanzu zata fige ta lalace, tananan zaune kamar hoto batasan sanda hall din ya cika da mutane ba saiji tayi an dafata ta dago idanunta da yayi jajir saboda kuka ta saukesu akan Nina.

Nina tace “naga mayenki ya fita dame yazo?" Numfashi ta sauke tace “ya akayi yasan inda nake?" Shafa Kai Nina tayi tace “guy dinne kwarjininsa ya Isa yanda baka Isa ka Raina masa hankali ba wlh tambayarki yayi akazo aka nemeki baa ganki ba shine yace a samo masa wata da takeda kusanci dake so shine akazo aka kirani Ina zuwa na raina kaina Ashe ma Prince Ja'afar ne tabdi aikuwa kina ruwa don wlh soyayya da yayan sarauta bala'i ne baqin naci ke garesu indai su suka furta sunasonka Amma idan aka samu akasi Basu sonka ai ka kade har ganyanka"

Fasali ta sauke ta share hawayenta ta miqe saboda ta haqiqance komai ma yauma bazata gane ba wani garden ta nufa ta samu guri ta zauna ita kadai qwal kowa yana gurin daukar darasi ita kuma zuciyarta tanata kaiwa da komowa wajen tunanin mafitarta akan wannan sarqaqqen lamari daya tunkarota babu shiri tunda ta zauna ta kasa samawa kanta mafita ji tayi gabadaya makarantar ta daukar Mata wani masiffafen zafi idan taci gaba da zama komai zai iya faruwa da ita.

Wannan tunanin yasata tashi ta koma daki ta dauki hand bag dinta da kudade ta fice batare da tabari Nina taganta ba ta samu shatar mota har Azare babu zato kawai Ammi sai ganinta tayi Aunty Murja ta miqe ta tareta tana cewa “subhanallahi uwar manya meye ya sameki a goshinki haka?"

Fadawa tayi jikinta ta rushe da kuka ta kasa furta ka kalma daya hakan yasa tajata suka shiga ciki Ammi ta miqe tabi bayansu kanta ta dora a saman qafar Ammi tace “Ammi..." Amsawa Ammi tayi tana shafa kanta tare da zame Mata dankwalinta tace “kinasona Ammi?" Mamaki tambayar tabasu suka kalli juna anti Murja tace “to uwar manya waye zaice bayasonki wlh munasonki"


Ajiyar zuciya tayi tace “meyesa yakeson kasheni da kalamansa?" Abin ya daurensu Kai suka hada baki sukace “waye?" Kuka ta sake sawa tace “my Bestie husband" a razane suka dago dukkansu sukace me yayi miki?" Cikin matsanancin kuka tayi musu bayanin komai Ammi ta rinqa sallalami tana tafa hannu inda anti Murja tayi shiru itama tana mamakin wannan tashin hankali.

Dagowa anti Murja tayi tace “no wonder biri yayi Kama da mutum wlh tun ranar da yazo ya kaiki makaranta na fahimci wani Abu gashi kullum sai yazo yagaida abbanku" Ammi ce tace “tabdi Amma wannan yaro yakai mara kunya to yasaketa Mana ba kansa zaiwa asara ba shashasha ya dauka ke sakarya ce da zaki biye masa kuci amanar aminiyarki har wani da aure aa da uban aure yakesonki" fada Ammi takeyi ta inda tashiga ba tanan take fitaba kamar ta ari baki tare da yiwa yar tata kashedi me qarfi da nasiha Saida taga hankalinta ya dan kwanta sannan tace “kiramin shi na tsawatar masa" daukar wayar tayi da murnarta zata kirashi Aunty Murja tayi saurin riqe hannunta tace.


STORY CONTINUES BELOW

“Amma Hajiya kinsan cewa hakan ba haramun bane ko?" Numfashi Hajiya ta sauke tace “nasani qanwa to Amma Kuma ai kunya tanasa kabar halal yanzu idan mukayi sake mgnr nan ta fita da wanne ido zan kalli Hajiya Sahura ita Kuma Rafi'ah da wanne ido zata kalli Ni'imah haba tofin ala tsinen ma duniya kadai ai ya ishemu balle Kuma ga wannan aminci daya zama zumunci nikam gara a take abin tun anan namiji ba kunyace dashi ba" duk yanda Anti Murja taso hana Hajiya Ammi Kiran Ja'afar taqi ta dauki wayar Rafi'ah ta dauki number say ta kirashi jin muryar babba ce yasashi saita nutsuwarsa yana kallon Muhseen tace.

“Sunana Hajiya Amina nice mahaifiyar Rafi'atuh  yanzu da dawomin a hargitse tana kuka harma da alamun zazzabi a jikinta take fadamin abinda ke faruwa so don Allah a daina wannan wasan Ja'afar bashida amfani zai taba musu zumunci kasan Mata da kishi" numfashi ya sauke tare da sake saita muryarsa yace “ba wasa bane Ammi iyakar gaskiyata kenan wlh bazan iya hqr da Rafi'ah ba saboda ita nakeso qaddara ce kawai ta bani qawar....."


Katseshi Ammi tayi da tsawa tace “karna kumaji banason shirme kaima Ashe sakaraine haba Ja'afar ya zakabari shaidan yayi tasiri haka a kanka Ina zakakai haqqin raba zuciyoyi biyu Rafi'ah da Ni'imah abotarsu tun suna qananu girma da bambamcin ra'ayi da sabawar halaye baisa sun rabu ba saikaine zaka nemi rabasu to indai dama burinka kenan rabawar kafin ka raba ni na raba Rafi'ah tabar matarka har abada...."

Saurin kallonta Rafi'ah tayi tace “Ammi...." Hannu ta dora Mata a baki taci gaba da cewa saboda haka ka kiyayarmin yata bakai babu ita har gaban abada soyayya ta haramta gareku ko babu ran Ni'imah balle tana raye...." Yanason yin mgn Amma fir Ammi taqi bashi dama ta kashe wayarta tana tsaki ta dubi Rafi'ah tace “kekuma ki sawa zuciyarki salama ki janyewa Ni'imah har zuwa lkcn da komai zai daidaita dama bawai son naki yakeba so yake ya rabaku shine ya bullo tanan saboda haka kiyi cooling mind dinki kinji"


Jinjina Kai tayi ta miqe tayi wanka ta dawo ta kwanta wayarta tayi ring tana dubawa taga sabuwar number da yayita kiranta jiya ce ta kashe wayar gabadaya tayi kwanciyarta bacci ya dauketa ko babu komai zuciyarta ta samu nutsuwa bacci tayi sosai har yamma dake bata sallah ta tashi ta sake wanka ta zari key ta fice ta tafi gidan yayarta Raziqa acan ta qarasa yininta sai dare ta koma gida taci abinci ta kwanta zuciyarta ta samu nutsuwa tunaninta yana bata mgnr da Ammi tayi masa zaisa ya janye.

Bude wayarta tayi saqon farko da taga yana yawo akan sensor din ta bude shine ya rubuta Mata _“wahala zagi duka dauri a gdan yari bazaisa zuciyata ta hqr dakeba Rafi'ah inanan akan bakana inasonki Kuma aurenki zanyi ki haifamin kyakkyawar Baby kamarki"_ bata gama karantawa ba Kiran Bestienta ya shigo gabanta yabada wani rass tadai daure ta daga ta Kara a kunnenta tace “bestie da darennan haka...." Kuka taji ta fashe dashi tace “na shiga uku Rafi'ah Ja'afar ya sakeni wlh bansan me nayi masa ba..."


Batasan sanda ta hantsilo daga gadon ba tace “wht! Garin yaya?" Kukane ya hana Ni'imah mgn Saida tayi me isarta tace “wlh bansani ba nidai qalau muka rabu dashi kawai naga ya dawo yana huci ya shiga dakina ya Kama hadamin Kaya na biyosa Ina tambayarsa kawai sai cemin yayi gda zanje na huta idan ya dawo daga Abuja zai nemeni, inata murnata muka fito Saida ya kawoni gda ya zaro kudi yabani kinsanni da kudi kamar mejin yunwa da abinci na karba nayi godiya saiya zaro takarda ya miqomin yana murmushi nace tameye budar bakinsa sai cemin yayi nice katangar da nake neman kare mass cikar burinsa qila idan ya nesanta dani ya samu muradinsa.

Yana fadan haka yaja motarsa ya fice daga gidanmu yabarni tsayi Ina dubawa naga saki daya ya rubutamin wlh yanzu haka Ina asibiti Rafi'ah wai Ashe yanke jiki nayi na fadi, ya zanyi Rafi'ah inason mijina meye yasa ya yankemin wannan hukuncin?" Sosai Rafi'ah take kuka tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil a ranta tana Jinjina girman rashin mutuncin Ja'afar Ashe da gaske yakeyi zai iya sakin Bestienta to meye laifinta da zai hucce fushinsa akanta ya sawa aurenta rauni?

Ta tafi wannan tunanin taji Ni'imah tace “Rafi'ah kiyi wani abu don girman Allah yaqi daga wayar kowa na gdanmu qila ke ya daga taki please Rafi'ah ki taimakeni kada Ja'afar yayimin nisa wlh bazan iya rayuwa da wani namiji bashi ba" numfashi Rafi'ah ta fusgo tace “ok ki kwantar da hankalinki insha Allahu zanyi qoqarin ganin komai ya daidaita please ki daina kuka haka kada wani ciwon ya shigeki bari naji ko zan sameshi"


Kashe wayar tayi cikin dimuwa da gushewar hankali ta taqarqare ta runtuma ihu abinda yaja Ammi da anti Murja suka shigo dakin a guje har suna hardewa suka tarar da ita riqe da Kai tana ganinsu ta tashi tana jifa da abubuwa tana cewa “na shiga uku no Rafi'ah Allah meyesa kayimin haka ya saketa Ja'afar ya saketa akaina meyesa ya aikata haka...." Riqeta Ammi tayi tace “ya saketa fah kikace?" Dagakai tayi tace “wlh yanzu ta kirani tana kuka take fadamin Ammi ya zanyi ne ni Bestie tanason mijinta shikuma yana sona wlh ko mijina takeso zan iya sallama matashi balle natane ni Ina zansa kaina ta Ina zan fara ne?"

Zaunar da ita Ammi tayi tace “kai ni bantaba jin masifa irin wannan ba wannan wanne irin international dan iskane duk wata hanya ta maslaha kulleta yakeyi Kuma yana sane yake kulleta" numfashi anti Murja tayi tace “dama Saida nace kada ki kirashi Hajiya yanzu gashi an bata goma daya Bata gyaru ba kuma babu me gyara wannan barakar sai Rafi'ah daganan ne zuciyar mutane zata fara rawa a fara tunanin wanne irin matsayine da ita a gurinsa da iyaye zasu kasa sashi Abu ita tasashi Kinga sai a shiga komar bincike da an binciko gaskiya shikenan Abu ya lalace"


Kuka Rafi'ah takeyi kamar ranta zai fita itakam Ammi abin ya girmi tunaninta dole ta fice daga dakin anti Murja ce tayita rarrashinta bata gamayin Shiru ba wayarta ta fara ring ta dauko da sauri number Muhseen ta gani cikin zaquwa ta daga “ya haka suka tambayi juna a tare" taja numfashi tace “meyesa abokinka zaiyimin haka meyesa zai yiwa soyayyar Bestie na irin wannan mugun butulcin meyesa zai sanya rayuwata a kwale²n masifa wannan wacce irin lukutar jarabace Muhseen ya Ja'afar yakeso nayine wlh kaina ya kulle na rasa Ina zansa kaina ko babu Ni'imah Ja'afar baiyimin ba a matsayin miji balle tana tsakani tayaya yakeso na tunkari wannan gudumar masifar da ya jefani a ciki?"

Fasali Muhseen yaja yace “wlh akwai matsala Rafi'ah duk wata qofar alfarma Prince Ja'afar ya kulleta takice kawai a bude har gidansa naje yace bashida lkcna Kira kuwa nayi masa yafi dari yaqi dagawa don Allah ki kirashi qila ke a dace ya saurareki" shiru tayi ayyana ta inda zata fara kiransa katseta Muhseen yayi da cewa hakan zaki daure ki kirashi Rafi'ah Shirin barin qasar yakeyi idan muka sake yabar qasarnan baa daidaita komai ba tofa auren Bestienki ya hau gorar wahala tsakiyar teku domin ni nasan waye Ja'afar fiye da tunaninki wlh akan biyan buqatarsa baya duba alaqa kota kwabo Kuma bashida kirki indai akan ra'ayinnsa ne zai iya batawa kowa rai"


Jinjina Kai tayi cikin qoqarin aro juriya tace “sh...shikenan zan kirashi" kashe wayar tayi ta lalubo numbersa gabanta na duka ta latsa har tayi Ring ta katse bai dagaba ta sake Kira shima bai dagaba saida ta kirashi sau goma bai dagaba ta rubuta Masa gajeran saqo tace _“please Mr Ja'afar Wakil ka daga don girman Allah"_ cikin seconds saqonsa ya shigo kamar haka.

_"Gobe 7:30 zan wucce Indonesia banida lkcn daga wayarki idan kinason mgn dani dake kece zan iya baki 30 minutes cikin lkcna kizo gidana ki sameni yanzu ba dazuba ba anjima ba"_ zaro ido tayi waje tanajin wani tafasasshen gumi na karyo Mata bata gamajin zagayar kalamansa ba Ni'imah ta kirata ta daga ta fashe da kuka tace “Bestie yaqi daga wayata wai saidai naje gida na sameshi nikuma bazan iya zuwaba" wani kuka Ni'imah ta rushe dashi tace “kada kiyimin haka Rafi'ah ki taimaki igiyar aurena wlh Ja'afar ba dan iska bane bazaiyi Miki komai ba kije kijimin meye laifina ki bashi hqr da yawuna idan yabar qasarnan zan dade banganshi ba kije Rafi'ah please kije"...........


Post a Comment for "MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 1 BY REALFAUZAHTASIU"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...